Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

turakar amatukar razana
Sai kuyanga
dayace ta iya jurewa ta tsaya jikinta na rawa ta dauki jaririn
Ta yanke masa cibiyarsa sannan tayi masa wanka
Koda wadannan
kuyangi suka ruga wajen wannan daki sai suka je suka sami yarima saiman sukace
Ya shugabanmu hakika wannan abu daya faru a wannan
kogon ba komai ne ya jawoshi ba face haihuwar matarka gimbiya suhaila
Yanzu haka ta haifi wani kyakykyawan jariri mai siffar sadaukai
kuma yanzu haka yana cikin wannan daki……
Kafin su
gama fadar abinda yake bakinsu tuni ya ruga da gudu zuwa cikin wannan daki
Ya dauki jaririn ya daga shi sama ya kura masa ido take kwalla ta zubo daga cikin idanunsa
Gimbiya suhaila wacce take kwance agefe daya koda taga
wannan kwallar daga cikin idonsa sai hankalinta ya tashi sannan ta rugo gareshi tace
Yakai abin kaunata menene yasaka zubar da hawaye
sakamakon ganin wannan jaririn nawa?
Kodajin wannan tambaya sai ya juyo mata da fuskar jaririn donta gani
Nantake itama ta cika da mamaki sakamakon ganin yadda
jaririn yake matukar kama da sarki abu saiman kamar an tsaga kara
Yarima saiman yace to wannan shine dalilin ganin kwalla a
cikin idona kuma wannan kwallar kwallace ta farinciki
Tabbas yanzu mun sami yaron da zai dawo mana da martabar masarautar mu
Kuma ya haye kankaragar kakansa koda kuwa mu bama raye
domin wannan alkawarine abin bauta ya dauka agaremu
0======(:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::>
Daga wannan rana suka ci gaba da rainon wannan jariri cikin
kulawar daya kamata iyaye su dinga baiwa jariransu
Kuma aka rada masa suna basdar
Har ya cika shekara hudu a duniya kuma tun a wannan lokacin
kyawunsa ya dinga bayyana afili har wasu suna ganin kamar
shi ba mutum baneba kamarsu domin wasu cewa suka dinga
yi waishi dane daga ubangijinsu Kuma awannan shekarun mahaifinsa ya fara koyar dashi yaki da bashi horo mai tsanani
Har ya zamana idan ya shiga cikin wadanda suka girmeshi da shekaru bakwai ma basa samun nasara akansa
Kuma kirar karfi ta dinga bayyana ajikinsa
Musamman
ma lokacin dayakai shekara goma a rayuwarsa sai mahaifinsa ya dinga bashi horo mai tsanani
Wanda harsaida wasu daga cikin mutane suka dinga cewa
Baya kaunar dansa domin abinda yakeyi masa wannan ya wuce soyayya
Saboda sai a sakashi yayita naushin karfe mai kauri
Har sai yan yatsunsa sun kakkarye sannan aje agyara masa
Wani lokacin kuma sai yasa a hanashi abinci tun safe harsai yunwa taci karfinsa
Sannan ace idan yana bukatar abinda zaici saidai ya fita daga
cikin kogon ya shiga cikin daji ya farauto naman jeji sannan yazo ya gyara shi yaci babu wanda zai taimaka masa
Kuma koda ace ya farauto idan ba irin manyan namun jeji bane
Take yarima saiman zai kwace shi ya ajiye shi a gefe duk tsananin yunwar da yake ji
Saidai ya koma cikin dajin ys farauto wata dabbar ita kuwa wacce
ya farauto da farko anan za'a barta har ta rube
Sannan a
daukeshi a jefashi cikin teku sai ya shafe dakiku masu yawa ba tareda ya dago ba
Idan kuwa ya dago za'a maidashi cikin ruwanne harsai ya
ninka lokacin da aka dibar masa da farko
A kwai ranar da akaje aka sami saiman aka shawarceshi
akan ya daina baiwa wannan yaro irin wannan horon yaki
Amma sai yayi murmushi sannan yace
Duk abinda kuka ga inayiwa basdar ba wai ina kinsa bane
tsananin soyayya ce tasa nake masa domin babu abinda zai
sa mutum ya haifi da da jininsa kuma yakishi saidai da wani dalilin
Idan har banyi masa hakaba to bazai zama irin danda muke bukata ba
Kai har saida takai cewa wannan yaro ya saba da duk abinda aka koya masa
Ya zamana idan ya naushi karfe komai kaurinsa da kuma kwarinsa saiya lankwashe
Ko kuma ya loba ciki
Idan Kuwa ya fita farauta baya shakkar shiga cikin garken
manyan namun daji irinsu zakuna ya tarwatsasu da karfin tsiya kuma ya kama adadin wadanda yakeso
Idan kuwa sukaji wahala suka gudu saiya bisu daya bayan daya
ya kure musu gudu ya kamosu sannan ya dauresu da sarkoki
ya jawosu gida ba tare daya gajiba idan kuwa yayi nitso akasan
teku yana iya shafe sa'a biyu ba tareda ya dago da kansa ba
Kuma yana iya daukar dutse mai nauyin daukar katti hudu shi kadai ya yini yana gudu dashi akafadarsa
Sannan yazo gitfawa ta gaban yana iya kamashi ya hau komai girmansa da kuma santsinsa
Kuma ko kadan wannan yaro bayajin tsoron tsoron mutuwa
Domin kullum idan ya fita farauta yana shiga cikin manyan dajijjika ne masu hatsari
Wannan baiwa tasa ba karamin baiwa mutane mamaki takeba
Domin ko a tarihi basu taba jin yaro mai irin shekarunsa da wannan baiwarba
Har saida takai cewa idan ya fita daji idan dabbobi ko wasu mugayen
halittun suka ganshi saidai kaga suna tserewa
Idan kuwa yarima saiman yana bashi horo sai kaga duk irin wahalar
da zaisha take yake jureta saboda allah ya halicceshine amatsayin mai kwarin kashi da kuma juriya da kaifin kwakwalwa
Soyayya kuwa mahaifinsa suna nuna masa ita sosai idan aka gama bashi horon yaki
Aka shiga domin shimfida daya suke kwanciya da iyayensa
Kuma komai yake da bukata sai anyi masa ba'a kinyi
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN SU YARIMA SAIMAN BAYAN SUN TSIRA DAGA GUDUN TSIRAN DA SUKAYI
0======[]:::::::::::::::::::::::::::::::::::::>
Al'amarin boka ulumanu kuwa bayan ya sami nasarar cin birnin ramlatul saif da yaki
Sai ya koma cikin fadarsa cikin farinciki bisa sanin cewa ya sami abinda yake da bukata
Take ya shiga cikin dakinsa na tsafi ya zuba jinin wannan
macijiyar wacce mutanen birnin ramlatul saif suke bautawa
Domin ka idane cewa sai wannan jinin yayi mako biyu acikin
wannan tukunyar tsafi sannan zaisha
Daga wannan rana hankalin boka ulumanu bai kara kwanciyaba
Sakamakon mugayen mafarkai wadanda ya dinga yi
Kullum acikin barcinsa sai yaga an nuna masa wata gagarumar
wuta tazo har cikin gidansa ta konashi da dukkan abinda yake cikin gidan
Haka yake gani acikin mafarkinsa kullum ba'a taba samun bacin ranaba
Wannan mafarki ba karamin tayar masa da hankali ba
Kuma saidaya yi bincike acikin hallarar tsafinsa ko zaiga fassarar
wannan mafarki amma sai tsafin nasa yaki ya nuna masa komai
Daga baya sai ya gayyato dukkan manyan matsafan da suke nahiyarsu dama wasu nahiyoyin domin suzo su taya shi bincike
Lokacin da suka gama hallara suka dukufa gaba daya wajen yin bincike saida suka kwana suna yi amma basu sami fassarar wannan mafarkiba
Abinda kawai suka gani shine
Dolene boka ulumanu yayi hakuri zuwa sanda zai kammala sihirinsa
Na tsafi to sannan ne zai iya sanin fassarar wannan mafarki
Daga wannan rana kullum boka ulumanu yazauna jiran lokacin da zai kammala sihirinsa
Haka kuwa akayi bayan mako biyu ya gama kammala sihirinsa
Yana shanye jinin take yaji jikinsa yayi karfi sosai kamar zai iya daukar duniya gaba dayanta
Nantake ya dauko madubinsa na tsafi ya shafeshi bisa mamaki sai yaga s wannan lokacin madubin ya bude masa abinda yake da bukatar gani
Saiga hotonsu yarima saiman tun daga lokacin da suka fita daga birnin ramlatul saif zuwa sanda suka suka isa kogon darul sihir hardama jaririn da suka haifa wato basdar
Koda ganin wannan al'amari sai boka ulumanu ya takarkare ya kwarara uban ihu
Take ya tashi da nufin ya fita yaje ya yaki su saiman a can kogon
Kawai sai yaji wata murya ta fito daga cikin madubin tsafinsa
Tace kada ka kuskura kace zaka fita kaje ka tunkari wannan kogon dutsen
Domin ba makawa kana zuwa zaka hallaka domin sihirin da yake cikin wannan kogon dutsen yafi na jikinka karfi
Saidai ka jira idan basdar ya girma shi da kansa zai fito nemanka
A sannan ne zaka sami damar hallakashi tareda iyayensa
Koda gama sauraron wannan zance sai hankalin boka ulumanu ya kwanta
Daga wannan rana yaci gaba da yakar kasahen da suke nshiyar
Yana kwace karagar mulkinsu da karfin tsiya bayan ya kashe sarkin garin sai ya dora wakilinsa agarin
Sannan ya kara gaba ya nufi wata kasar
Saidaya cinye kasashen da suke nahiyarsu kaf
Harya shiga wasu nahiyoyin duk karfin mulkin sarakuna suna tsoronsa
Kuma babu yadda basuyi ba akan su kare kansu amma sun kasa
Saidai kawai kullum suji ance musu su kara hakuri akwai lokacin da wani zaizo ya taka masa birki akan abinda yakeyi
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA BOKA ULUMANU
0====={{::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::>
Sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade ba'ajeba
Kuma kowanne abu idan aka saka masa lokaci to tabbas wannan lokacin zaizo
Kamar yadda aka fada afarkon labari cewa basdar bazai sami dama tunkarar boka ulumanu ba saiya cika shekaru ashirin a duniya
Saboda tsabar karfin damtsensa daga awannan lokaci idan ya naushi dutse saidai kaga hannunsa ya burma jikin dutsen ya nutse
Ahaka jikinsa ya murde tamkar curin duwatsu da tarin kwarjini
Kuma gashi da tausayi da girmama na gaba sannan baya yarda yaga ana zalunci a ko ina
A ranar da ya cika shekaru ashirin din ne yana cikin barci
Yayi mafarki a cikin mafarkin aka nuna masa
Wata irin macijiya tana bin mahaifinsa da gudun tsiya tanaso ta kamashi
Shi kuma yana ta tika gudu don ceton ratuwarsa
Da kyar ya samu ya shige cikin wani kogo ya buya ita kuma macijiyar ta tsaya a bakin kogon tana jiran fitowarsa
Koda yazo daidainan acikin mafarkin nasa saiya farka a matukar razane
Take mahaifinsa suka fito daga cikin dakin da suke kwance
Alokacin tsufa ya fara kamasu suka taho dakinsa suka sameshi
Suka tambayeshi abinda yake faruwa
Take ya kwashe labarin komai ya fada musu
Koda sukaji haka sai suka girgiza kai
Sannan saiman yace
Yakai dana hakika lokaci yayi da zamu fada maka sirrin da muka boye maka
Kuma shine dalilin dayasa muka dinga baka horo mai tsanani har wasu suke zaton bama kaunarka
Nandai suka kwashe labarin komai suka fada masa tarihinsu da birninsu da dalilin dayasa suka gudo wannan kogo
Koda gama jin wannan labari sai idanunsa suka ciko da kwalla
Yaji ya tsani boka ulumanu fiye da komai aduniya
Nantake ya mike tsaye da nufin fita daga cikin kogon
Take suhaila ta ruke masa hannu tace
Ina kuma zaka?
Basdar yace zanjene domin daukar fansar abinda akayiwa iyayena da kuma kasata
Kodajin haka sai tace ai wannan aiki bana gaggawa bane dole kayi hakuri gari ya waye mu zamuyi maka jagora mu tafi nemansa
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT TO ENTERTAIN YOU BAKAR GABA
PART 27
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Nandai suka kwashe labarin komai suka fada masa tarihinsu da birninsu da dalilin dayasa suka gudo wannan kogo
Koda gama jin wannan labari sai idanunsa suka ciko da kwalla
Yaji ya tsani boka ulumanu fiye da komai aduniya
Nantake ya mike tsaye da nufin fita daga cikin kogon
Take suhaila ta ruke masa hannu tace
Ina kuma zaka?
Basdar yace zanjene domin daukar fansar abinda akayiwa iyayena da kuma kasata
Kodajin haka sai tace ai wannan aiki bana gaggawa bane dole kayi hakuri gari ya waye mu zamuyi maka jagora mu tafi nemansa
Cikin sanyin jiki jarumi basdar ya fara yi musu magiya akan su barshi ya tafi amma suka ki
Da kyar suka iya shawo kansa ya hakura
Amma acikin wannan daren saboda tsabar kaguwar da yayi barci ma kasawa yayi sai ya zauna kurum yana jiran gari ya waye
Kashe gari kuwa da sassafe ya fito daga cikin turakarsa
Ya nufi dakin da iyayensa suke ciki
Koda ya bude kofa ya shiga sai yayi arba da mahaifan nasa
Azaune idanunsu sun kada sunyi jawur da alama suma a wannan daren basuyi barci ba
Koda sukayi arba da basdar sai suka taso da sauri suka tareshi
Fuskarsu cike da murmushi sannan suka ruko hannuwansa
Suka jashi sukazaunar dashi suka fuskanci juna sukace
Yakai basmar hakika wannan itace ranar da muka jima muna jiran zuwanta
Ayaune mukeso kayi mana aikin damu muka kasa yinsa
Kuma kai kadaine zaka cikawa jama'armu burikansu
Kafin yace wani abu sai suka kama hannunsa suka jawoshi waje daga cikin wannan dakin
Suka fita waje dashi suka nufi wani bangare daban na cikin kogon darul sihi
Shidai wannan waje tunda jarumi basdar ya taso bai taba zuwa gurinba
Asalima bai sanda shi ba domin kuwa wajen wata irin katangar sihiri ce ta katange gurin
Azahiri idan ka taba wajen ko kuma ka kalleshi zakaji katangace agurin
Amma bisa mamaki sai basdar yaga awannan lokaci ya sun ratsa ta cikin wannan katangar kamar yadda haske yake ratsa gilashi
Saida sukayi tafiya mai dan nisa sannan suka iso wani babban daki
Wanda ya fita daban da sauran dakunan da suke cikin kogon darul sihir
Komai na wannan dakin ba azaune yake bisa turba ba
Yana yawo ne akan iska amma hakan batasa wani abu ya lalace ba
Su kansu yayinda suka shiga cikin wannan dakin sai suma suka fara yawo akan iska kamar yadda komai na ciki yakeyi
Har saida yarima saiman yayiwa jarumi basdar nuni da wata rantsatstsiyar kujerar mulki wacce gaba daya an san'anta tane da lu'u lu'u
Kuma wani irin haske mai sheki yana yake fita daga cikinta
Sannan ya umarceshi daya zauna akanta
Dukda cewa jarumi basdar sadaukin gaskene wanda ya gaji jarumtaka ta gurin iyayensa da kakanninsa gaba da baya
Saida yaji zuciyarsa ta buga alokacin da yaji mahaifinsa ya umarceshi da zama kan wannan karagar
Sakamakon wasu irin birkitattun tunani da suka dinga zuwar masa a cikin zuciya
Saida yaji mahaifinsa ya daka masa tsawa yace tunanin me kakeyi ne?
Ka gaggauta yin abinda na umarceka nantake yaji hantar cikinsa ta kada sakamakon jin irin kakkausar muryar da mahaifinsa yayi masa magana da ita
Don haka baisan sanda ya damki kujerar ba alokacin da suke yawo dashi da ita acikin iska ba ya zauna akanta
Faruwar hakan keda wuya sai komai na cikin dakin ya daidaitu suka dawo suka zauna bisa turba
Kuma wani irin haske mai karfi ya dallare dakin gaba daya
Nantake jarumi basdar yaji wani irin radadi a jikinsa kamar ana tsotse jinin jikinsa
Tareda wani irin zafi kamar an dorashi akan garwashi
Nantake ya fara rusa ihu alokacin da jikjnsa gaba daya ya fara karkarwa kamar mai jin sanyi
Haka dai ya kasance tun yana iyayin motsi da jikinsa har ya kasa
Faruwar hakan keda wuya sai kuma ya daina jin wannan abin da yake ji
Nantake yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi kamar zai iya nada gammo ya dauki duniya
Kuma yaji wani irin kuzari ajikinsa kamar idan akace yayi gasar tsere da iska zai iyayi
Su kansu iyayen nasa da suka lura da yanayinda yake ciki sai suka kamu da farinciki
Nantake suka rungumeshi sannan suka sumbaci goshinsa
Saiman yace yakai dana to yanzu ne kakai matakin da muke da bukatar kakai
Duk duniya babu wanda bazaiyi shakkarka ba amma duk da haka sai kayi kokari ka zage damtse sannan zaka sami nasara akan boka ulumanu
Kuma ina gargadinka da cewa
Ka zamo mai tausayi da jinkan talakawa da kuma ruke alkawari
Idan har ka ruke wadannan abubuwa musamman ma ka hada da gaskiya
To ina rantsuwa cewa babu wani abu da zai gagareka aiwatarwa a wannan duniya
Koda jin haka sai jarumi basdar yace
Ya abbana nayi alkawarin zan ruke wadannan shawarori naka
Saidai kuma ina jiran naji wadanda zasu fito daga bakin mahaifiyata
Kodajin haka sai gimbiya suhaila tayi murmushi yadda har saida hakoranta suka fito
Sannan tace
Ai duk abinda zan fada tuni mahaifinka ya fada maka saidai ina shawartarka daka zamo mai dakakkiyar zuciya acikin duk abubuwan da kasa a gabanka idan kayi haka to ina mai tabbatar maka da cewa bukatar ka zata biya komai wahalarta
Domin akwai abinda karfin dantse ko na sihiri basa yinsa saidai zuciyace take iya aikatashi
Tana gama fadin hakan sai suka juyo suka kamo hanya suka fito daga wannan bangaren da suka shiga
Koda suka dawo izuwa ainihin harabar kogon sai mutane suka dinga kallon jarumi basdar
Domin gani sukayi halittarsa ta kara wani irin kwarjini fiye da farko
Alokacin kowa yana waje suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum
Koda ganin haka sai yarima saiman yace dasu
Yaku mutanen birnin ramlatul saif
Inaso dukkanku ku shirya domin yanzune zamu koma izuwa can birnin mu na haihuwa
Don haka kowa ya hada kayansa
Koda suka ji abindaya fito daga bakin yarima saiman
Sai kowannensu ya kamo da murya suka fara shewa harda tsalle
Ba tareda bata lokaci ba suka shiga cikin gidajensu suka fara harhado kayansu duk da cewa a sannan mafi yawansu duk girma ya fara kamasu
Shi kansa yarima saiman a sannan shekarunsa sunkai shekaru hamsin da 'ya'ya
Cikin 'yan a wanni suka kammala hada kayayyakinsu
Bayan kowa yafitone sai yarima saiman ya dauko wannan takobin sihirin
0======={}:::::::::::::::::::::::::::::::::::>
Ya mikawa jarumi basdar ita sannan yace
Wannan takobin saboda kaine naketa ajiyarta tun tsawon shekaru
Don haka yanzu lokaci yayi da zan mallaka maka ita
Dajin haka sai jarumi basdar ya karbeta da hannu biyu
Sannan yarima saiman yace dashi
Saika shiga gaba domin yanzu bani bane shugaban wannan ayari ba
Kaine saboda haka alhakin kare wadannan mutane gaba daya ya dawo kanka
Ba tareda gardama ba juwa jarumi basdar ya shige gaba suka kama tafiya
Sai gashi wani abin al'ajabi yana faruwa
Domin hanya kawai sukaga yana bi tamkar damacan yasan taswirorin wannan daji
Kuma komai yawan manyan dabbobin daji da manyan aljanu
Idan sukayi arba da jarumi basdar tun daga nesa saidai kaga suna rugawa da gudu
Domin kowa yana shakkar tunkararsa idan kuwa sukayi kuskuren aikata haka to sunsan dayansu bazai tsira da rayuwarsa ba
Idan kuwa sukazo giftawa ta gaban dutse ko wani tsauni
Sai kaga ya tsage gida biyu ya basu hanya sun wuce
Idan kuwa kogine ko teku sai su dinga taka ruwan suna tafiya akansa kamar suna tafiya akan kasa
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU BAYAN SU YARIMA SAIMAN SUN BARO KOGON DARUL SIHIR ABISA JAGORANCIN DANSA WATO MATASHIN JARUMI BASDAR
0======(:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::>
Acan fadar boka ulumanu kuwa cikin watanni kadan ya gama cinye kasashen da suke nahiyar da yaki
Ya zamana cewa kowanne sarki akasansa yake kuma sunayi masa biyayyar dole
Sannan ya kammala hada sihirinsa na tsafi
Wannan ne ya bashi damar yin abinda yakeso da karfin sihirinsa
Wata rana kawai yana zaune a cikin dakin tsafinsa kawai saiya tuna da batunsu yarima saiman da kuna dansu jarumi basdar
Koda gama tunawa dasu sai ya mike ya shiga bincike akansu cikin madubin tsafinsa
Nantake yaga cewa yanzufa sun fito daga cikin kogon darul sihir sun nufo nan fadarsa
Koda gama ganin wannan al'amari sai ya bushe da dariyar farinciki
Domin yasan idan ya kashesu bashida sauran fargaba
Yana gama wannan tunani sai yace azuciyarsa
Dolene naje na taresu tun akan hanyarsu kafin su iso wannan kogon
Yana gama fadin haka saiya tashi sama kamar dama can yanada fuka fukai
Take ya ratsa ta cikin ginin saman fadar tasa ya fice
Daga cikin fadar ya luluka acikin gajimare cikin tsala azababben gudu kamar na tauraruwa mai wutsiya
Sai gashi cikin cikin kankanin lokaci yaje gurin da suke ya tare su
Alokacin suna cikin wani daje mai yawan bishiyoyi da kuma duwatsu
Kawai sai gani sukayi wata irin bakar guguwa ta taso ta tokare sararin samaniya kai kace hadarine ya hado za'ayi ruwan sama
Kura ta turnuke dajin gaba daya har saida dawakan dasu yarima saiman suka hawo suka fara ja da baya kamar zasu zubar dasu a kasa
Har saida jarumi basdar ya daka musu tsawa sannan komai ya tsaya ya koma yadda yake
Bakar guguwar itama ta disashe kamar bata taba samuwa ba
Dawakan nasu ma suka nutsu kamar wani abu bai taba samunsu ba
Ba komai ne ya janyo haka ba face bayyanar boka ulumanu
Cikin gagarumar shigar yaki taban tsoro tamkar wanda zai yaki duniya
A hankali komai ta lafa har boka ulumanu ya bayyana yadda kowa yana iya ganinsa
Wohoho nanfa aka fara kallon kallo a tsakaninsa dasu yarima saiman
Daga can sai yarima saiman ya kalli boka ulumanu cikin murmushi
Sannan yace
Ka gaji kenan da zaman jiran mu fadarka shine yasa ka kawo kanka zuwa hallakarka
Gaskiya na jinjina maka wannan kasadar da kayi
Koda jin haka sai shima boka ulumanu ya bushe da dariya yace
Gaskiya indai kayi wannan tunanin ka yaudari kanka domin mahaifinka ma yayi mini irin wannan cika bakin da kayi amma duk da haka saida naga bayansa
Kodajin haka sai shima ya kyalkyale da dariya sannan yace
Ai yanzu ba dani zaku fafata ba da dana ne don haka nida sauran mutanena 'yan kallo ne
Yana gama fadin haka saiya koma da baya shida sauran jama'arsa
Ya zamana anbar boka ulumanu da jarumi basdar a tsakiyar fili
Suka fara kallon kallo na tsawon 'yan dakiku daga can sai jarumi basdar da ulumanu
Suka falfalo da azababben gudu suna kwalla ihu wanda ya razana kowa da yake wajen
Nantake suka ruguntsume da azababben yaki na gaban kwatance
Sai gashi suna kaiwa junansu mugayen hare hare masu matukar razanarwa
Duk sanda suka kawowa junansu hari idan ya goce duk abinda suka samu saidai kaga ya dagagaje kamar an nuka gari
Idan kuwa makamansu suka hadu da juna sai kaga tartsatsin wuta yana tashi
Sai gashi sun hargitsa dajin gaba daya dabbobi suka fara gudun ceton rayukansu
Tsuntsaye suka fara canja sheka
Bishiyoyi kuwa suka dinga karyewa suna zubewa akasa
Dukda cewa dajin cike yakeda bishiyoyi saida sukayi masa fata fata
Ya zamana cewa gaba dayansa sun mai dashi fili fetal babu sauran bishiya guda daya a tsaye
Tun suna wannan gumurzu a doron kasa saida ya zamana sun daina
Suka tashi sama akan iska sannan suka ci gaba da wannan fada
Kuma kowa acikinsu ya kasa samun nasara akan abokin gwaminsa
Koda ganin haka sai suka fara jifan junansu da sihiri kala kala
Duk wanda ya jefi wani da nasa sihirin idan ya goce saidai kaga ya fada kan dutse
Duk abinda sihirin ya fada kansa take yake ruburbushewa sannan ya kama da wuta
Kai saida suka yini suka kwana suna wannan fafatawa amma babu wanda ya sami nasara akan wani
Ganin hakane yasa sadauki basdar fusata yaga cewa ya za'ayi ace shi amatsayinsa na matashi ya kasa samun nasara akan wannan tsohon mutumin
Koda yin wannan tunani
Saiya kara zage damtse ya dinga kai masa mugayen hare hare
Cikin bakin zafin nama, juriya da bajinta tamkar jikinsa bana jini da tsoka bane
Sai gashi tun boka ulumanu yana iya kare hare haren har ya zamana cewa ya kasa saidai kokarin kare kansa
Yakeyi wannan ne ya baiwa sadauki basdar damar yiwa boka ulumanu mummunan yanka a kan damtsen hannunsa na dama
Nantake boka ulumanu ya kwarara uban ihu sakamakon zafi da zugin da yaji
Nantake yaji wani irin mummunan dafi ya shiga jikinsa har idanunsa suka fara lumshewa
Koda ya tabbatar da cewa idan akaci gaba da wannan gumurzun a haka bazai sami nasara ba a wannan yakin sai nantake ya shammaci jarumi basdar ya ruga aguje domin ceton rayuwarsa
Har basdar ya yunkura zai bishi sai yaji mahaifinsa ya daka masa tsawa
Yana mai umartarsa da kada ya bishi
Cikin sanyin jiki basdar ya dubi mahaifinsa yace ya abbana mainene dalilin da yasa ka hanani na bi wannan tsohon abokin gabar tamu
Dajin haka sai yarima saiman yayi murmushi yace
Ai bai kamata ka bishi ba a yanzu domin shima ya yarda yanzu cewa kai ba kanwar lasa bane
Nafiso mu bishi har fadarsa mu rusheta kamar yadda shima ya rushe birnin mu
Yana gama fadar haka sai duk su biyun suka sauko suka koma cikin tawagarsu
Sannan suka ci gaba da tafiya zuwa fadar boka ulumanu
Saida suka shafe yini guda suna tafiya har rana ta fara neman faduwa kawai sai suka yi arba da wata wata kyakykyawar budurwa
Ta sanya kaya wadanda suka rufe duk jikinta
A zaune gefe daya ta fuskanci gabas ta tattara hankalinta gaba daya aguri daya kamar wacce takeyin ibada
Koda sukayi arba da wannan budurwa sai gaba dayansu
Suka labe a wani sako na wannan dajin suna leken wannan matashiyar budurwa
Sai Jarumi basdar ya kalli mahaifinsa yace
Yakai abbana shin kasan irin wannan ibadar da wannan budurwa takeyi?
Dajin wannan tambayar sai yarima saiman yace
Gaskiya ni tunda nake ban taba ganin ibada makamanciyar wannan ba
Kai ni ko atarihi ban taba jinta ba amma bansani ba ko ita mahaifiyarka ta sani
Dajin haka sai itama suhaila ta gyada kai alamar bata santa ba
Sannan tace lallai wannan ibadar bantaba ganin ibada mai irin nutsuwarta ba
Kadai duba ka gani duk ilahirin jikinta ta rufe shi sannan ta zauna a guri daya ba tareda tanayin raye raye ba
Suna cikin wannan hali ne wannan budurwar ta idar da ibadar da takeyi
Sannan suka ga ta dauko wani dan karamin littafi ta fara karantashi
Saboda dadin karatun da takeyi saida sukaji gaba daya tsigar jikinsu ta tashi
Sukaji wata irin nutsuwa tazo musu wacce basu taba jin irinta ba
Don haka basu san lokacin da suka fara 'yan surutaiba har suka fara zubar da abubuwan da suke hannuwansu
Karar faduwar kayan ce tasa budurwar ta juyo baya da sauri don taga mene yake faruwa
Tareda karanta wani lafazi wanda basu san ma'anarsa ba
Koda taga su jarumi basdar a tsaye a bayanta saita mike da sauri
Tana mai ja da baya tareda fadin suwaye ku?
Ina mai rokonku da kada ku ce zaku cutar dani
Koda jin haka sai yarima saiman yace yake wannan budurwa
Kada ki tsorata damu domin mu ba masu cutarwa bane a gareki ba
Amma ina mai rokonki don girman abin bautarki da ki fada mana sunan wannan addini naki
Domin ko a tarihi ban taba jin labarin irin wannan addini naki ba
Sannan inaso ki fada mini sunanki da kuma abinda ya kawoki wannan nahiyar tamu?
Kodajin wannan tambaya sai wannan budurwa tace da farko dai kamar yadda ka tambayeni game da addini na
Shidai addini na shine addinin musulunci wanda ake bautar ubangiji guda daya
Wanda bai haifaba kuma ba'a haifeshi ba
Shine wanda ya halicci sammai da kassai da kuma abubuwan da suke cikinsu
Kuma ya haliccesu ne domin su bauta masa amma sai wasu daga cikin mutane da aljanu suka bijire masa suke bautar wasu abubuwa sabaninsa
Kuma yana sane da hakan kawai yana

Please Login or Register in order to submit comment