Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake bukata
lokacin da ya iso wannan daki kai tsaye ya wuce izuwa inda tukunyar tsafin mahaifinsu take ya zura wata battarsa aciki ya cikata taf da tsumin tsafin
sannan ya koma cikin dakin dasu yarima saiman suke ya mika musu tsumin
cikin tsananin farin ciki
yarima saiman ya karba sannan yace mun gode da irin wannan gagarumar gudunmawar daka bamu
domin inba don ka taimake mu ba to ba shakka acikin wannan garin zamu mutu
dajin haka sai jurishan yayi murmushi yace
ni dai burina kawai shine ku samu ku kashe mahaifinmu
domin in bakuyi haka ba banida wata riba ataimakon danayi muku
yana zuwa nan azancensa saiya juya ya fice daga cikin dakin
fitarsa keda wuya sai saiman ya daga wannan battar ruwan ya sakata abakinsa yana sha
sai da yasha kamar kaso daya cikin uku sannan ya mikawa markazulu battar yace shima yasha kaso daya
dajin haka sai markazulu yaki karba sannan yace
ai ni yanzu banida wani buri arayuwa yanzu zuciyata ta canja daga yadda take ada ni kawai ina da burin in zama mai yi maka hidima don haka banida bukatar wannan tsumin
yarima saiman ya hade fuskarsa kamar zayyi kuka
sannan yace yakai markazulu wanne irin hukunci ka yankewa kanka haka
kana nufin kace duk wahalar da kasha ya dalilina ta tashi abanza kenan?
indai ba zakashaba to anan tafiyarmu dakai zata tsaya
koda markazulu yaga halinda saiman ya shiga sai nantake ya karbi tsumin shima yasha
sannan ya baiwa saiman ragowar tsumin
faruwar hakan keda wuya sai wani irin gagarumin karfi ya sake shiga jikinsu
nantake sarkokin jikinsu suka tsutstsunke Markazulu ya balle kofar kejin da suke ciki
suka fito daga cikin dakin suna fitowa sai sukayi arba da tsubi tsubin dakarun dodanni abakin dakin
nantake saiman ya nunasu da hannunsa wata murtukekiyar sarka ta dauresu
sannan kai tsaye suka fito izuwa wajen gidan sarautar suka kwallawa markazulu kira
kafin su gama rufe bakinsu saiga markazulu ya bayyana fuskarsa amurtuke kamar an aiko masa da sakon mutuwa
nantake suka ruguntsume da azababben yaki
su saiman suka saka garjaju a tsakiya suka dinga kai masa mugayen hare hare shikuma
yna karewa abinda yafi tayarwa da yarima saiman hankali shine
markazulu baya yarda takobinsa ta sauka ajikinsa
domin da zarar yaga zata tabashi sai ya bace ya bayyana a wani bangaren daban
duk wannan abu da yake faruwa gaba daya mutanen birnin
sun tsaya suna kallon wannan bakin artabu da akeyi wanda babu tabbacin ga bangaren da zaiyi nasara
awannan lokaci markazulu ya taka muhimmiyar rawa fiye da farko
sakamakon tsumin garjaju da yasha nan da guri ya hargitse
gumu yayi gumu duk abinda wani daga cikinsu
ya sara saidai kaga sun tsargeshi gida biyu koda kuwa katuwar bishiyace
kai tun dodannin suna tsaye suna iya kallo har ya zamana cewa
an fara yiwa rayuwarsu barazana suna hallaka don haka duk sun gudu
saida aka kwana aka yini ana wannan yaki sannan yarima saiman
ya shammaci markazulu ana cikin yakin kafin ya kula da motsinsa ya zabga masa sara da takobin sihirinsa atsakiyar kansa
nantake markazulu ya kwarara uban ihu sannan
jikinsa ya kama da wuta ya kone kurmus
koda ragowar dadannin wadanda suka labe suna kallon abinda ke faruwa ga abinda ya faru ga shugabansu
sai duk suka ruga aguje domin su tsira da rayuwarsu
koda mutuwar garjaju sai su saiman suka ruguntsume juna shida markazulu
suna masu farinciki
ba tareda bata lokaciba aljani markazulu ya sunkuya saiman ya hau gadon bayansa suka kama hanyar wucewa sansaninsu
LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEME

DOMIN SAMUN CIGABAN LITTAFIN SAI KU KASANCE
DA SHAFIN WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG AKODA YAUSHE
BAKAR GABA
Kashi na uku 3
Littafin habibullah Muhammad kabara
Ebook created by Shuraih Usman
Published at WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG










BAKAR GABA
PART 11
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
lokacinda markazulu ya suri yarima saiman a gadon bayansa
saiya kasance yana mai tsala azababben gudu
cikin 'yan dakiku suka iso kusa da dan karamin
garin da yarima saiman ya sana'anta
koda
ya rage saura baifi taku hamsin ba atsakaninsu
sai aljani markazulu ya saki fukafukansa ya sauko
kasa ahankali koda saukarsa sai yarima saiman ya sauko kasa daga
kan gadon bayansa
sannan sukayi bankwana da aljani markazulu ya tashi sama ya bace bat da gani
nantake yarima saiman ya nufi sansanin nasu da sauri
da isarsa bakin kofa saiya ratsa ta ya shiga cikin birnin kamar yadda haske yake ratsa gilashi
awannan lokaci mutanen garin kowa yana tafiyar
da harkokinsa na yau da kullum
koda suka ga yarima saiman ya bayyana agabansu tsulum
sai suka kamu da tsananin farinciki
tamkar wanda yayi shekaru dubunnai bai dawoba
nantake suka rugo gareshi suka shureshi suka dagashi
sama suna farincikin dawowarsa tamkar dan karamin yaro
saida aka shafe sa'o'i ana wannan shagali na murnar dawowar yarima saiman
sannan yarima saiman ya juyo zuwa inda dakarunsa
wadanda ya aika suke ya kare musu kallo dakyau
yana maiyin nazari, daga can sai yayi murmushi
ya dubi jarumi zamnal yace naga duk abinda ya faru ga ku ayayin tafiyar da kukayi izuwa birnin askandariya
lallai na jinjina maka sannan kayi matukar kokari da ka iya rufe mana sirrinmu
domin mutanen birnin askandariya duk da irin amanar da suka nuna muku to su mutane ne masu matukar son kudi
domin akan kudi babu abinda bazasu iyaba
ma'ana zasu iya cin amanar ku idan suka san ko ku suwaye
dajin haka sai mamaki ya kama su zamnal
saiman yace to yanzu ina aiken da nayi muku yake?
dajin wannan tambaya sai zamnal ya baiwa wasu dakaru
umarnin su fito da keken dokin, nantake suka umarni
sukaje suka janyo keken dokin suka kawo shi gaban saiman
saiman ya karewa keken dokin ido sannan yayi murmushi yace
lallai kun iya zabe domin wannan keken dokin
zaiyi kwari sosai, don haka nima ga sakayyar da zanyi maka
nantake yarima saiman ya janyo jarumi zamnal gefe daya
sannan yasa hannu ya kwanto battar
da tsumin dodo garjaju yake ciki ya mikawa zamnal yace
wannan shine abinda zan saka maka dashi
domin ta sanadiyar nemansa saida na kusa rasa rayuwata
don haka duk wanda na baiwa mutum ne mai matukar daraja
dajin haka sai jarumi zamnal ya kamu da tsananin farinciki
har yana faduwa kasa yana yiwa yarima saiman sujjada
koda yarima saiman ya mika masa wannan battar
bai tsaya jiran komai ba daga gareshi saiya wuce
izuwa tantin matarsa gimbiya suhaila
awannan lokaci gimbiya suhaila tana kwance tanayin barci
batama sanda dawowarsa ba
yarima saiman yasa hannu ya kara hannunsa akusa
da fuskar gimbiya suhaila alokacin da takeyin wannan barcin sannan ya fita daga cikinsa ya sami waje ya buya
koda ta shaki kamshin hannunsa tana cikin yin barcin
saita mike zumbur domin tagani ko da gaske shi dinne
amma koda ta bude idanunta sai taga bata ganshiba
nantake tace azuciyarta
lallai gaskiyane wannan ba mafarki baneba masoyinane ya dawo kuma yana kusa dani
cikin sauri ta fito wajen tantin ko zata ganshi amma kuma ta rasa shi
kawai saita dubi wasu dakaru guda hudu da suke gadin tantin nata ko sunganshi
amma sukace basu ganshi ba
dajin haka sai gimbiya suhaila ta daka musu tsawa tace
saboda me zakuyi mini karya ko kuma a hada baki daku domin a tayar mini da hankali?
bata tsaya jin amsar wannan tambayarba ta juya ta koma cikin tantinta
ta zauna ta kifa kai da gwuiwa tana kukan bakin ciki
tana cewa
tabbas ina daf da haukacewa saboda soyayya
amma kuma ni ina da tabbacin masoyina yana raye kuma akusa dani
inma dai bashi bane to ruhinsa yana tareda ni
idan kuwa ruhinsa ne to shi yamutu kenan?
tana cikin wannan zancen zucine sai taji an dafa kafadarta ta baya
koda ta dago kai sai tayi arba da yarima saiman
sai tayi tsalle ta rungumeshi tana cewa
saboda me zakayi mini wasa da hankali?
ka sani cewa tun daga lokacin da ka tafi kullum zuciyata cikin begenka take
sannan kuma inayi maka fatan nasara
domin azahiri ka tafi ka barni ne agida amma zuciyata tana tareda kai aduk irin halin daka shiga
dajin haka sai yarima saiman yayi murmushi tareda shafa gashin kanta yace
lallai maganarki gaskiyane ki sani cewa aduk lokacin da jikina ya gaji sakamakon wahalar dana shiga
to tunaninki ne yake karfafa mini gwuiwa
koda kuwa faduwa kasa nayi sai naji muryarki akunne ne tana cewa
ka kara taku daya tak domin nasara tana tareda kai
ma'ana dai duk wata nasara danake samu to kece sila
haka dai su yarima saiman sukayi ta hira har barcin dare ya sacesu basu saniba
++++ +++++ ++++++ ++++
al'amarin boka ulumanu kuwa bayan yaje ya samu nasarar hadin kan da aljani harisul mar'uf
akan yarjejeniyar cewa aljani harisul mar'uf bazai taimaka musuba wajen yaki da mutanen birnin ramlatul saif ba sai dai in sun gama yakin shi zai kashe musu maciyar da mutanen birnin suke bautawa
sannan ulumanu zai mai dawa mahaifiyarsa ainihin siffarta daga siffar da aka tsafanceta ta gunki
zuwa ainihin siffarta ta aljana, bayan harisul mar'uf ya kashe macijiyar da birnin ramlatul saif
sai nantake boka ulumanu yayi tsafi suka dawo izuwa fadarsa
inda anan ne yake tara dakarunsa na yaki wadanda adadinsu ya wuce
dubu dari biyu wadanda suka hada mutane da aljanu
koda bayyanar boka ulumanu tareda aljani harisul mar'uf
sai duk gaba daya dakarun suka fadi kasa suna masuyi masa sujjada
ulumanu ya dubesu sannan ya nuna aljani harisul mar'uf yace
wannan shine sadaukin aljanin da nake baku labarinsa
kuma duk duniya shikadai ne wanda zai iya kashe macijiyar da birnin ramlatul saif suke bautawa
don haka yanzu bada jimawaba zamu dunguma
gaba ki dayan mu domin muje mu baje birnin ramlatul saif domin biyan bukata yana zuwa daidai nan azancensa
saiya rufe idanunsa tareda karanta wadansu
dalasiman tsafi marasa dadin ji
nantake aka fara wata irin walkiya mai matukar firgitarwa
saida aka shafe 'yan dakiku anayi sannan komai ya lafa
saiga wani irin katon tsuntsun tsafi ya bayyana
tareda wadansu ingarmun dawakai wadanda zasu ishi gabaki daya bil'adaman
da suke wajen, sannan boka ulumanu ya bushe
da wata mahaukaciyar dariya mara dadin ji tareda umarta dakarunsa
da kowanne ya kama doki guda daya ya hau domin tafiya wannan yaki
domin yakine za'ayi irin wanda ba'a taba yin kamarsaba atarihin duniya
nantake kuwa dakarun suka cika umarninsa
sannan boka ulumanu ya shige gaba akan
tsuntsun tsafinsa tareda aljani harisul mar'uf saboda sune shugabannin wannan tafiya idan babu daya daga cikinsu tafiya bazata yiwuba
bayansu kuma dakarun bil'adama ne sannan aljanu akarshen sahu
sai suka nufi hanyar da zata kai su birnin ramlatul saif
idan mutum yagansu awannan lokaci zata zaiyi gaba daya dakarun duniya ne suka hadu awaje guda
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU AFADAR BOKA UULUMAN BAYAN SUN FITO YAKI DA BIRNIN RAMLATUL SAIF
++++ +++++ ++++++ +++++
acan birnin ramlatul saif kuwa bayan sarki abu saiman yayi zaman majalisa tareda mutanen birninsa
an yi shawarwari akan yadda za'a bullowa wannan yaki
tun daga wannan rana hankalin kowa ya kwanta
tamkar babu wani tashin hankali da yake kusanto su
tundaga wannan rana mutanen birnin suka dage wajen kera sababbin makaman yaki
〇 da kuma mugayen tarkuna suna zuwa suna binnewa a iyakar dajijjikan da suke kewaye da birnin
awannan lokaci kuwa sai abu saiman da kansa
yake baiwa dakarun birninsa sababbin horon yaki dare da rana
cikin kwanaki kadan dakarun suka kware a dukkan fannin da ake koya musu
sai da ya zamana gaba daya mutanen birnin ramlatul saif sun daina tsoron mutuwa
ana cikin wannan haline wata rana sarki abu saiman
ya shiga cikin halwar tsafinsa yana bincikensa
kwatsam saiyaga hoton boka ulumanu da aljani harisul mar'uf
tareda dakarunsa mutum dubu biyu
sun nufo birnin ramlatul saif
koda ganinsu sai sarki abu saiman ya kwarara uban ihu
sannan yace hakika karshen birnin mu da kuma karshen abar bautar mu
saboda haka dolene muje mu fita mu kare kimar kasarmu
cikin gaggawa sauri abu saiman ya fito daga cikin dakin
halwar tsafinsa ya tara gaba ki daya dakarunsa
wadanda adadinsu bai wuce dubu sittin ba
ma'ana basufi kaso daya cikin ukun suba
abu saiman ya dubesu yace. yaku ahalin birnin ramlatul saif
zaku iya sallama rayuwarku domin kare kimar kasarku da kuma abin bautarmu?
cikin hadin baki gaba daya dakarun suka amsa
mun yarda mun amince
sarki abu saiman ya sake cewa to yanzu haka dakarun boka ulumanu suna kan hanyar zuwa birnin nan
saboda haka inaso gaba daya muje mu taresu kafin su iso nan birnin sannan ya umarci kowa yaje yayi nasa shirin
yana zuwa daidai nan azancensa saiya juya ya shiga cikin gidan sarauta
yayi shigar yaki
farin sulke sarki abu saiman ya sanya
tareda farar hular
sannan ya rataya wasu zabga zabgan fararen takubbai guda biyu agadon bayansa
kallo daya zakayiwa sarki abu saiman awannan lokaci
ka fahimci cewa lallai ya cika sadauki mai tarwatsa maza
hakika sarki abu saiman yana da matukar kwarjini
da cika ido domin duk inda ake neman jarumi idan aka same shi to bukata ta biya
atarihin jarumtakarsa bai taba jagorantar yakiba face an sami nasara
kuma tunda yake fita filin daga bai taba haduwa da masifar data sanya shi ya ja da bayaba
koda kuwa tazarar taku daya
sau ashirin yana shiga gasar jarumtaka ta nahiyarsu yana cinyeta ajere
kai duk wata kalma ta tsoro sarki abu saiman baisanta ba
don haka akace barewa batayi gudu ba sannan kuma danta yayi rarrafe ba
ma'ana dai shi yarima saiman ya gado afannin jarumtaka
lokacin da sarki abu saiman ya gama yin shirinsa na yaki
saiya fito kofar fadarsa ya tsaya kyam yana jiran dakarunsa su gama shirinsu
suzo su same shi anan wajen domin su tafi yakin dake gabansu
cikin rabin sa'a dukkan dakarun birnin ramlatul saif suka gama hallara
nantake suka dunguma gaba daya suka nufi hanyar
fita daga birnin ramlatul saif
tafiyar sa'a biyar sukayi sannan suka fita daga birnin sannan suka kafa sansani
suna jiran abokan gaba sannan sarki abu saiman ya sana'anta wasu mutum mutumi na tsafi
ya tura su izuwa dajin farko su jira zuwan abokan gaba
da zarar sunzo sai su tura musu da kibiyoyin tsafi
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A BIRNIN RAMLATUL SAIF
BAYAN SUN FITO JIRAN ABOKAN GABA
+++++ +++++++ ++++++
acan sansanin su yarima saiman kuwa lokacin da barci
sacesu basu farkaba sai da safiya tayi suna
farkawa sai suka tarar da abinci anzo an ajiyesu musu tareda abin sha
kafin su fara cin abincin saida suka zagaya kewaye sukayi wanka sannan suka fito suka kamacin abincin suka cika cikinsu
bayan sun sami nutsuwa sai yarima saiman ya
fito bakin tantin nasa ya tsaya sannan ya tara gaba daya mutanen da suke
tareda su awaje guda
bayan kowa ya hallara sai ya fara jawabi kamar haka
yaku ahalin birnin ramlatul saif a yaune zamu
nufi can birnin hamshak ne inda acan ne zamu
samo makallin miftahul darul sihir
wanda dashine kadai za'a iya bude kofar shiga kogon tsafin boka awaisul masawi
inaso ku sani cewa zuwa karbo makullin kogon darul sihir
afadar sarkin aljanu na birnin hamshak daidai yake da mutum
yace zaije farautar ajalinsa da kansa
domin duk abinda kake takama dashi
walau karfin damtse, iya yaki, ko karfin sihiri
to da zarar kaje wannan fada shikenan kaje gidansa da kanka
duk masifar dodo garjaju bata kai rabin ta fadar sarkin aljanu na birnin hamshak ba
don haka awannan karon nikaina banida tabbacin zan tsira da rayuwata
don haka nake me rokonku daku dage dayi mini addu'a akan abinda zan fita nema
yanzu sai kowa ya hada kayansa domin a yanzune zamu bar wannan birnin
mu shiga daji mu ci gaba da tafiya
yana gama fadar haka sai nan da nan mutane suka fara har hada kayayyakinsu
kafin rabin sa'a sun gama
bayan kowa ya gama shirin tafiyarsa sannan kowa ya sami dokinsa ya hau sai yarima saiman ya sake karanta wadansu dalasiman tsafin akaro na biyu
yana gama rufe bakinsa sai wannan dan karamin gari ya nutse acikin karkashin kasa
sannan yarima saiman ya ciro zoben tsafinsa ya wullashi sama
nantake wani jan haske ya fito ya nuna hanyar yamma cin dajin
inda yake nuni da itace hanyar da zata kaisu birnin hamshak
nantake suka dau hanya suka nufi hanyar da zoben ya nuna musu
cikin azababben gudu
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A SANSANIN SU YARIMA SAIMAN
liҠɛ ąŋɖ Ćơmmɛŋŧ iŞ ơųř ɛŋĆơųřąɠɛmɛŋŧ PART 12
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Nidai rahoton dana samo akansu yarima saiman ayau shine
ku saurara kuji
Lokacinda su yarima saiman suka kama hanyar zuwa
birnin aljanu na hamshak sai suka wanzu suna
masu tsala azababben gudu kamar zasu tashi sama
yarima saiman ne ya kasance agaban wannan
tawaga sai kuma gimbiya suhaila wacce ta kasance
a hannun damansa acikin keken dokinta, daga barin hannun hagun gimbiya suhaila
dakarune atsatstsaye cikin shigar yaki rike da makaman yaki
abayansu kuma mutanen gari ne sannan su jarumi zamnal
ne don tabbatar da tsaro haka suka dinga kutsawa
ta cikin mugayen dazuzzuka masumatukar hatsari, wadanda sukahada da
mugayen 'yan fashi, manyan dabbobin daji da mugayen aljanu
amma cikin kankanin lokaci su yarima saiman suke gamawa dasu
akan hanyar sune ta tafiya birnin aljanu na hamshak suka iso
wani mummunan daji mai matukar hatsari da firgitar da duk wata halitta wacce ta kusanci dajin
shidai wannan daji yana cike ne da manya manyan duwatsu masu duhuwa yadda
ba'a iya ganin abinda yake cikin duhuwowin
sannan kuma duwatsun sun kewaye hanyar wucewa ta cikin dajin
sun zamewa hanyar kamar kofa, gabas, yamma,
kudu da arewa na dajin duk inda kake kallo
babu hanyar da zakabi ka wuce gaba
koda
suka iso daidai wannan wuri sai suka ja linzaman
dawakansu suka tsaya sukayi cirko cirko
ana jiran
maganar da yarima saiman zaiyi saboda shine shugaban tafiya
daga can sai yarima saiman ya dubi tsaunin sosai ya kare masa kallo yana nazarinsa
tsawon 'yan dakiku sannan ya juyo ya dubi jama'ar tasa yace
idan har munaso mu san hanyar da zamubi mu ketare wannan tsauni dolene na hau saman wannan tsauni
domin na samar mana hanyar da zamubi mu ketare wannan tsauni
don haka sai ku jirani awannan wuri ni zan
hau saman tsaunin dukkaninku kuna karkashin
kulawar jarumi zamnal yana zuwa daidai nan
azancensa sai ya sauko daga kan dokinsa
awannan lokaci gimbiya suhaila tana kwance
acikin keken dokinta bata ma san abinda yake faruwaba
yaje ya bude kofar keken dokin ya sumbaci goshin gimbiya suhaila sannan ya
maida kofar ya rufe kai tsaye yarima saiman
ya tunkari wannan tsauni ya fara kamashi yana hawa kamar bai kasance bil'adama ba
kayi zaton cewa kadangare ne shi ba mutum ba
dukda cewa dutsen ya kasance mai santsi babu kafar kamawa da yawa amma saboda tsananin
jarumtaka irin ta sa sai gari yana hawa kan
tsaunin cikin salo mai ban sha'awa saida yarima
saiman ya ya shafe sa'a hudu yana hawa kan tsaunin
sannan ya isa karshen wannan tsauni ya fara
tafiya asamansa domin ya samo musu hanyar wucewa
kash! !
hakika rashin sani yafi dare duhu inda ace yasan
abinda zai faru da baiyi kuskuren hawa kan
wannan tsaunin ba yabar mutanensa akasa
domin yana gama hawa kan tsaunin sai ga wasu
irin murtuka murtukan zakuna masu matukar
firgitarwa suna fitowa daga cikin duhuwowin dajin
koda bayyanar wadannan zakuna sai suka
fara yin wani irin gurnani wanda ya cika dajin baki daya
mutanen dake biye da yarima saiman kuwa
duk sai suka figice suka kama koke koke
koda
ganin halin da mutanen suka shiga sai jarumi zamnal
ya zare takobinsa tareda sauran dakarun suka
afkawa zakunan suka ruguntsume da azababben yaki
shi kuwa yarima saiman koda yaga abinda ya faru
sai hankalinsa ya tashi ya fara kokarin sauka daga kan tsaunin
yana cikin hakane sai ya taka wani waje mai santsi ba tareda ya sani ba
nan take kuwa santsi ya kwasheshi ya fadi
kasa sumamme sannan ya dinga gangarowa kasa
su kuwa su jarumi zamnal sai suka dinga fafata
yaki tsakaninsu da mugayen zakunan har tsawon sa'a biyu
amma sun kasa kashe koda guda daya kuma tun awannan lokaci
tuni dakarun sun gama gajiya jarumi zamnal
ne kawai yake iya tabuka wani abu awannan lokaci
da yawan dakarun duk sun sami mugayen raunika
shi kuwa jarumi zamnal ya kasa kashe ko daya acikin zakunan
sai yana iya yi musu mugun luguden duka
duk wanda ya daka saidai kaga ya tashi sama
kamar an janyeshi da majaujawa yaje ya gwaru da jikin dutse
amma sai kaga ya tashi ya karkade jikinsa ya dawo an ci gaba da yakin
hakika jarumi zamnal ya kasance jarumin gaske
mai ban al'ajabi domin shi kadai ya hana wadannan
zakuna cutar da koda mutum daya daga cikin mutanen da suke tareda su
ana cikin wannan azababben yaki ne sai su jarumi zamnal
suka ga wani katon aljani yana tahowa daga sama
koda suka ga wannan jibgegen aljani sai suka kara firgita domin a zaton su yazone domin ya hallakasu
ba zato ba tsammani sai suka ga wannan aljanin ya fada
cikin wadannan zakuna sun kara kachamewa da azababben yaki
sai gashi awannan lokaci fada ya canja salo domin sai gashi
ba kowa bane wannan katon aljani ba face
aljani markazulu sai gashi ya shiga cikin zakunan
yana ragargazarsu duk da tsananin yawansu
sai gashi ya zama na banza domin daga su ya
dingayi yana gwara su da juna duk wadanda
ya hada su gware saidai kaga suna kansu ya dagargaje kwakwalwarsu tana kwaranyowa kasa
koda zakunan sukaga yadda aljani markazulu yake ta ragargazarsu sai suka kara zage damtse
domin suna ganin ya hanasu cin abincinsu ne domin yanzu suna tsaka da matsananciyar yunwa
amma duk da haka sai hada karfin nasu ya zama na banza
domin bai rage musu komai ba face kara baiwa markazulu damar hallakasu
cikin kankanin lokaci ya gama hallakasu gaba daya
bayan ya gama kashe zakunan ne sai dakarun
da sauran mutanen gari suka kara firgicewa
banda jarumi zamnal domin shi kadai ne agaban markazulu
suna kallon kallo gaba daya mutanen da suke
wajen sunyi zaton cewa markazulu so yake
ya kashe su domin a zaton su shine yake mallakin wannan dajin da suke ciki
koda markazulu ya kula da yanayin da suke ciki
sai ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan
ya murtuke fuskarsa yace haba ahalin birnin zaharul maswur
saboda me zaku dinga firgita dani bayan kunga
kalar taimakon da nayi muku ayanzu
ai ya
kamata kusan cewa ni ba mai cutarwa bane ba agareku
domin tun farkon tafiyar ku ina tareda akan hanyar ku
na boyene saboda tsoron ku shiga irin halinda
kuka shiga ayanzu sakamakon ganina
kuma
shugaban ku ne ya bani umarnin buyan
amma
yanzu bisa dole ce tasa na bayyana kaina
sakamakon kuskuren da shugaban ku yayi na tafiya ya barku
anan shine naga kuna dafda hallaka ni kuma
nasan burin yarima saiman gaba daya akanku yake
ni kuma burina na gyara kuskuren da nayi abaya
don haka nazo domin na ceci rayuwarku
dajin
wannan batu sai jikin mutanen yayi sanyi
suka dan fara sakin jikinsu dashi don haka
sai zamnal ya dubeshi yace
yakai wannan jarumin aljani muna godiya da irin wannan taimakon da
kayi mana amma muna so musan ko wanene kai
sannan kuma munada tambaya guda daya
dajin haka sai markazulu yace ni sunana markazulu tsohon hadimin boka ulumanu bayan wannan kuma wacce tambaya ce
dakai indai na sani zan fada maka iyakar gaskiyar dana sani
zamnal yace menene ya sami yarima saiman
naga har yanzu bai dawoba domin na tabbata
indai yana lafiya bazai barmu mu shiga halinda muke cikiba yanzu
aljani markazulu yayi murmushi yace
me
zaisa ka tayar da hankalinka akan yarima
ina
mai tabbatar maka da cewa duk irin halin da
yarima saiman zai shiga dole ne ya tsira da rayuwarsa
domin mutum ne shi mai matukar sa'a da rabo a dukkan abubuwan da ya saka agabansa
amma dai bara na nuna maka halinda yake ciki
nan take aljani markazulu ya nuna jikin dutsen da hannunsa
nan take wani haske ya fito ya bugi jikin dutsen
saiga abindaya faru ga yarima saiman tun daga lokacin da yake hawa kan wannan tsauni
har zuwa lokacin da santsi ya kwasheshi ya fadi
kasa sumamme sannan ya gangara izuwa kasan tsaunin
koda hoton yazo daidai wannan guri sai hoton komai ya dauke
koda suka ga abinda ya faru ga yarima saiman
sai hankalinsu gaba daya ya tashi don haka
sai markazulu ya bude fuka fukansa cikin sauri ya tashi sama
ya hau kan tsaunin ya fara neman yarima saiman
amma sama da kasa ya kasa ganinsa
saida
ya shafe sa'o'I biyar yana nemansa amma
bai ganshi kuma baiga wata alama da zata
nuna cewa ga inda yakeba bisa dole ya sauko
daga kan tsaunin ya bude baki da nufin yin jawabi kenan
sai a daidai wannan lokaci gimbiya suhaila
ta farka daga barcin da takeyi tana farkawa
sai ta kwallara ihu tana fadin cewa
ina mijina yake !
ina masoyina tabbas wani abu ya faru dashi
nan take ta fito daga cikin keken dokin da take ciki
tana tambayar su zamnal ina masoyinta yake
amma aka rasa wanda zai wanda zai iya bata
amsa sai dai su sunkuyar da kansu sun kasa fadin komai
hawaye ya zubo mata sannan ta dubesu gaba daya tace
yanzu duk cikin ku babu wanda zai iya sanar
dani halin da yake ciki lallai inaji ajikina wani
abu ya sameshi amma duk da haka ina da
tabbacin cewa bazai mutuba domin masoyina
jarumi ne na gaske don haka nima dole ne asanar
dani inda yake yanzu. domin naje na taimaka masa
jarumi zamnal ya kalleta kansa asunkuye yace
ya shugabata yanzu haka ya tafine domin ya samo
mana hanyar da zamubi mu wuce wannan daji
,amma kiyi hakuri ba zamu iya fada miki inda
ya tafiba domin tsaron lafiyarki dajin haka
sai tayi murmushi tace yanzu na gane manufarka
wato kana nufin ya hau kan wannan tsaunin ne ko?
to inaso ka sani menene amfanin rayuta idan babu muradina
masoyina ne kadai muradin rayuwata don haka
koda na zauna anan indai baya raye to nima
bazan karasa kogon boka awaisul masawiba araye
to dolene naje na taimaka masa koma mene
zai sameshi saidai ya samemu tare kafin zamnal
yayi wani yunkuri ta shammaceshi ta zare
takobin da ke jikinsa ta falfala da azababben gudu ta nufi wannan tsauni domin ta hau kansa
koda ganin abinda yake shirun faruwa sai aljani markazulu ya ya hura mata wata iskar tsafi
faruwar hakan keda wuya sai barci mai nauyi ya sake dauketa
nantake kuyangi suka je suka dauketa suka kaita cikin keken dokinta suka ajiyeta
sannan markazulu ya kallesu gaba daya yace
hakika saiman yana cikin hatsari domin babu irin duban da banyi masaba
amma na rasa inda yake don haka nima bansan hukunncin da zan yamkeba akan dawowarsa
domin tabbas yana cikin halin mutuwa da rayuwa
dolene mu zage damtse mu

Please Login or Register in order to submit comment