Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne wanda baisan tsoro ba kuma kana da matukar sa'a
da rabo adukkan abubuwanda kasa agabanka
ni ina da tabbacin duk irin tsananin wahalar da zansha
dole zan rayu to amma fargabata akan abu dayane
wannan abu kuwa ba komai baneba face rayuwar jama'ar kasar mu aduk lokacin dana tuna da halin da kasar mu take ciki da kuma wasiyyar da mahaifina ya bar mini sai naji gaba daya rayuwar bata mini dadi.. ...
koda yazo daidai nan azancensa sai kwalla ta zubo masa don haka sai ya yi shiru
ya wuce izuwa tantin da matarsa take
koda gimbiya suhaila taga yanayin da yarima saiman ya shigo dashi saita taho da sauri
ta ruko hannunsa ta jashi izuwa kan shimfidarta sannan tasa hannu ta share masa hawayensa
tace
haba yakai mijina gwarzo guda daya tak acikin mazajen duniya
ka tuna fa kaine fasa taro
kuma sa gudu maganin ki gudu
bai kamata karamin abu ya dinga saka gwarzon jarumi kuma uban jarumi kamar ka kwalla ba
ka sani cewa komai na rayuwa kaddarace take tafiyar dashi
don haka sai kayi kokari ka manta da duk kaddarar data faru abayanka
ka tunkari ta gabanka don hakane alamar cika gagara badau
k0dajin wannan batu sai yarima saiman ya dago da idanunsa ya dubeta yace
haba tayaya kike tunanin zan manta da mahaifata da aka haifeni acikinta?
kuma tayaya zan iya mantawa da mahaifina wanda tundaga randa aka haifeni gado daya muke kwana tare dashi har izuwa sanda mahaifiyata ta mutu?
wannan abune wanda bazai taba yiwuwaba awajena
farinciki na guda daya ne arayuwar nan
sannan kuma burina shima guda dayane
farincikin nawa kuwa shine samunki amatsayin matar aure domin wannan babbar nasarace agareni
burina kuwa shine naga jama'ar mu sun isa kogon awaisul masawi lafiya har ki haifi jarumin d zaizo ya dauki fansar abinda akai mana akan boka ulumanu
koda yagama fadin wannan zancen saiya kishingida bayansa ajikin wani matashin kai
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA YARIMA SAIMAN BAYAN YA SAMI NASARAR MALLAKAR TAKOBIN SIHIRI
Acan dajin da dodo garjaju yake kuwa dajine mai
matukar ban tsoro irin wanda komai hatsabibancin aljani yana shakkarsa
saboda komai na dajin siffar ban tsoro ne dashi
fiye da shekara dubu uku baya sawu ya dauke awannan daji
mutane da aljanu suka daina shigarsa saboda har ikirari ake masa da dajin mutuwa
koma duk duniya sun canfa cewa babu halittar da zata iya shiga wannan daji ta fito araye
kai hatta kananun halittu irinsu kuda, cinnaku, sauraye, da kiyasai basa wucewa ta cikin wannan daji
wannan daji shine ya zamo duniyar dodannin da suke rayuwa aduniya
duk wani sarki mai jida karfin mulki azamanin sa to yana iya aiko da wasikar sihiri wannan nahiya don neman aron dakarun yaki acikin wadannan dodanni idan sarkin dake mulkin wannan nahiya ya yarda amma da zarar sarakuna sun aiko aljani ko bil'adama ko kuma yazo da kansa wannan daji to bai isa ya fita araye ba
wannan daliline yasa sarakuna da bokaye suke aikoda wasika kadai ba tareda manzo ba
ba kowa ne ke mulkin wannan daji ba face dodo garjaju
dodo garjaju ya kasance hatsabibin dodo jarumi kuma sadauki mai tarwatsa maza
kuma mai tsananin karfin sihiri
duk tsananin jarumtakar jarumi ko kuma sihirin mai sihiri yana matukar shakkar tunkararsa
shikadai yana da jarumtakar da zai iya yakar duniya shi kadai
bakomai ne yasaka shi kebance kansa awannan daji ba face
yayi bincike ya gano cewa bazai taba samun nasarar mulkar duniya ba face ya mallaki kwayar idon bil'adama guda miliyan biyu
da kuma na aljanu guda miliyan biyu ya hadasu da tsumin tsafinsa
tsawon kwanaki dari da casa'in da tara acikin tukunyar tsafinsa yana dafa su sannan zai sami nasarar mallakar duniya
adalilin hakane yayi shiri da kansa da nufin fita farautar bil'adama da aljanu domin cikar burinsa
amma koda yazo daidai iyakar wannan daji da suke rayuwa shida dakarunsa da nufin su fita
sai sukaji kamar ana watsa musu ruwan dalma bisa dole suka koma cikin daji
dodo garjaju ya cikagaba da binciken hanyar daya kamata yabi domin samun biyan bukatar sa
acikin binciken nasane ya gano cewa bazai taba samun damar fita daga wannan dajiba shida jama'arsa gabadayaba sai daya daga cikinsu
wannan kuwa ba kowa bane face dodo sarmanu wanda shine dan auta ga dodo garjaju
koda yagama wannan bincike saiya kwarara uban ihu
saboda duk cikin 'ya'yansa babu wanda yakeso sama da sarmanu
kuma sarmanu shine mafi rauni acikin 'ya'yansa don haka bayaso abinda zai taba lafiyarsa ko kadan
dakyar da sidin goshi ya hakura ya yarda sarmanu ya fito farautar bil'adama da aljanu
amma kafin sannan saidaya tsumashi acikin tsumin tsafinsa
bayan tafiyar dodo sarmanu kullum sai garjaju ya dauko madubin tsafinsa yaga halinda dansa yake ciki
sannan yake samun kwanciyar hankali da nutsuwa aransa
to ana cikin wannan hali wata rana dodo garjaju ya dauko madubin tsafinsa
ya shafeshi don sanin halinda dansa yake ciki
koda ya shafi madubin tsafin saiyaga irin kisan da aljani markazulu yayi masa tareda 'yarsa
saiya kwarara uban ihu
wanda karar ihun nasane yasa dajin gaba daya ya kama girgiza
su kansu dodannin da suke rayuwa awannan daji saida suka shiga tashin hankali
domin gaba dayan birnin babu wanda baya tsoronsa
wasu atake suka dinga haukacewa wasu kuma suka dinga kurmancewa saboda tsananin karfin ihun nasa
koda yagama wannan ihu saiya fashe da kuka
sannan ya daga kansa sama yace lallai wannan aljani yayi matukar kuskuren da sai ya yi madamarsa arayuwar sa
farinciki na daya ne shine shida kansa zaizo wannan daji shida sabon abokin tafiyar daya samu da zummar diban tsumin tsafina
dolene sainayi masa kisan gilla kisan da ba'a taba yiwa wani mahalukiba
lallai sai yayi nadamar abinda yayi mini
lokacin da yake fadar wannan magana akwai babban dansa awajen wanda ake kira da jurishan
koda dodo jurishan yaji maganar mahaifinsa saiya dubeshi yace
ya abbana wane irin kisa zakayi musu?
dajin haka sai garjaju ya bushe da dariya yace
zan kamasu ne gaba daya na tsoma su acikin tsumin tsafi su zama mulmulallu kamar kwallo sannan nasa a ajiyesu ababban fili dodanni suyita bugasu da kafafunsu
bayan nan sai na sake mayar dasu sandarar ru dodanni suyita dukansu da manyan bishiyoyi
hakadai zanyita canja musu halitta har tsawon kwanaki goma sannan na hallakasu gaba daya
koda yagama wannan bayani sai dodo jurishan ya bushe da dariya sannan yace
ya abbana lallai wannan hukunci ya dace dasu gaskiya nayi farinciki da haka
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU ACAN DAJINDA DODO GARJAJU YAKE DAJINDA SHINE WAJE MAFI HATSARI A RAYUWAR DUKKAN HALITTA
LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMELITTAFIN BAKAR GABA
PART 7
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Al'amarin yarima saiman kuwa lokacin da suka kadaita acikin tanti shida matarsa
sai yarima saiman ya zauna yana ta tunani tsawon yan dakiku
sannan ya shafi zoben da yake hannunsa
nantake wani dan siririn aljani dan siririn aljani ya bayyana
shidai wannan aljanin yakasance dattijo
fuskarsa rafkekiyace
yana da idanu kwala kwala kuma yakasance mai cikar kwarjini
dan gajere
koda bayyanar wannan aljani saiya sunkuya yayiwa yarima saiman sujjada sannan yace
ya shugabana mai kake da bukata na biyamaka
koda jin wannan tambaya sai yarima saiman yace
yakai aljani zulkam tundaga lokacin da mahaifina ya damka maka ni
ban taba neman wata bukata ba awajenka sai wannan karon idan na tambayeka zaka biya mini ita?
kodajin wannan tambayar sai aljani zulkam ya sake rissinawa yace
ai ni mai biyayyane agareka don haka ina sauraron duk bukatunka
dajin haka sai yace
shin kana da masaniya akan dajin ajali da abubuwan dake cikinsa
kodajin wannan tambaya sai aljani zulkam
ya takarkare ya kwarara uban ihu har yana birgima akasa sannan yace ya shugabana
dajin ajali dajine daya zamo kamar kushewa
mai cike da masifu da bala'o'i iri iri wadanda suka fi karfin mutum ko aljan
su ketaresu
kai wannan daji yana da duk wani irin kalar masifa wacce ake gudun shiga cikinta
su
ya shugabana zaka iya shiga cikin dajin ajali lafiya sakamakon wannan sihirtacciyar takobi daka mallaka
amma inda tashin hankalin yake shine shiga cikin fadar dodo garjaju lafiya harka iya debo tsuminsa
saboda duk abinda kake takama dashi dodo garjaju ya fika karfin damtse, sihiri, dabarun yaki
dodo garjaju ya kasance azzalumin gaske mara tausayi ko kadan
yanzu haka aljani markazulu ya kashe daya daga cikin 'ya'yan dodo garjaju saboda haka dole ne ya dana muku mugayen tarkuna
wadanda bai zama lallai ku iya wucewa lafiyaaba
idan harka sami nasarar shan tsumin tsafinsa
to tamkar ka gano lagonsa ne saboda duk irin abinda yake takama dashi to kaima saika sameshi
to amma ya shugabana inda matsalar take shine kan aljani markazulu
da alama shima yana da bukatar tsumin dodo garjaju
ka tuna cewa yanzu haka markazulu ya bujirewa maigidansa boka ulumanu
sannan kuma ya kashe daya daga cikin 'ya'yan dodo garjaju shiyasa ya zo wajenka ya rabeka
zargin da nakeyi anya kuwa baka ganin akwai wata makarkashiya acikin zuciyar sa?
dajin haka sai ya takarkare ya bushe da dariya
lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa sannan yace
yakai aljani zulkam indai akan maganar aljani markazulu ce karka damu ni nasan yadda zanyi dashi
to bukata ta ta biyu itace akan birnin mu na ramlatul saif
koda fadin haka sai ya yi nuni da hannunsa izuwa jikin bangon tantin da suke ciki
nantake sai hoton birnin ya bayyana da yadda ake ta tafiyar da harkokin yauda kullum
da zaman fadar da sarki abu saiman mahaifin yarima saiman ya yi da dukkan 'yan majalisarsa
koda gama ganin duk abinda ya faru sai yarima saiman ya juyo yaceda aljani zulkam
yanzu haka nasan boka ulumanu ya kusan gama
shirye shiryensa akan yadda zai yaki birninmu
bincike ya nuna cewa boka ulumanu ne yake da nasara
awannan yaki koda kuwa zamu tara dukkan
mayakan duniya acikin dakarun mu
yanzu haka boka ulumanu ya tafi neman aljani harisul mar'uf
wanda shine kadai zai iya hallaka macijiyar macijiyar da muke bautawa
to aikin da nakeso kayi mini shine ka taimaki
dakarun mahaifina yadda zakuyi boka ulumanu babbar barna acikin wannan yaki
saboda wannan yaki zai kasance yakin da ba'a tabayin kamar saba atarihin duniya
nasan cewa mahaifina jarumi ne kuma dan jarumai wanda baisan tsoro atarihin rayuwarsa
don haka dole kafin ya mutu saiyayiwa boka ulumanu babban tabon da harya mutu bazai baceba daga jikinsa
koda jin wannan batu sai aljani zulkam ya bushe da dariya sannan yace indai wannan ce bukatarka karka damu
koda gama fadin haka sai ya bace bat kamar bai taba wanzuwaba
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA YARIMA SAIMAN
*** ***** **** **** ****
al'amarin boka ulumanu kuwa lokacin daya
bace daga cikin jama'arsa bai nufi ko ina ba
sai dajin d aljani harisul mar'uf yake rayuwa
tamkar kiftawar ido haka ya baiyana agaban
harisul mar'uf.
alokacin yana gaban mahaifiyarsa wacce
take cikin siffar gunki yana ta zubar da
hawaye.
amma koda ya jiyo motsi sai ya juya
bayansa yana mai zare takobi.
cikin mamaki sai yaga bil'adama abayansa
nantake ya share hawayen dake fuskarsa
yadubi boka ulumanu yace.
yakai wannan bil'adama menene yakawo ka
wannan daji mai matukar hadari alhalin ire
iren jinsinku basa iya shigowa cikinsa.
dajin haka sai boka ulumanu ya bushe da
dariya lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa
tamkar an aiko masa da sakon mutuwa.
sannan yace
nine boka ulumanu mai shirin mulkar
nahiyarnan baki dayanta
yanzu haka nazo wajenka ne don neman
taimakonka akan wani shiri da nake son yi
ina fatan zaka bani hadinkai
dajin haka sai harisul mar'uf ya turbune
fuska.sannan yace
nayi alkawarin har duniya ta tashi bazan
sake bautawa ga wata halittaba har sai
lokacin da mahaifiyata ta dawo izuwa ainihin
siffarta.
kodajin haka sai boka ulumanu yayi
murmushi sannan ya nuna mahifiyar harisul
mar'uf mai suna zalzila da dan yatsa.
nantake kuwa ta dawo izuwa ainihin siffarta.
sannan ya dubi harisul mar'uf yace juya kaga
abin mamaki.
cikin gaggawa sai ya juya,yana juyawa
saiyaga mahaifiyarsa azaune tamkar yadda
take kafin ayi mata wannan sihiri.
nantake ya ruga da gudu domin ya
rungumeta.kafin ya karasa sai ta sake
komawa zuwa siffar gunki
nantake boka ulumanu yasake bushewa da
dariya sannan yace da harisul mr'uf
kana tunanin zan mayar da mahaifiyarka
yadda take batare da kayi mini wani aiki ba,
dajin haka sai harisul mar'uf yace yakai
wannnan bil'adama me kakeso nayi maka n
arantse har da darajar mahaifiyata zanyi
maka wannan aiki komai tsananin wahalarsa.
boka ulumanu yace
yakai wannan hatsabibin aljani inasone
kataimaka mini na yaki wani birni da ake kira
madinatul saif aikin danake so kayi mini
awannan yaki shine ka kashemini macijiyar
da suke bautawa amatsayin ubangijinsu.
dajin haka sai harisul mar'uf yace tayaya zan
amince dakai alhalin ku bokaye baku da
amana?
sai boka ulumanu yace idan har na
yaudareka tsafina saiya daina tasiri domin
haka ka'idar sihirina take.
sai harisul mar'uf yace shikenan na amince.
nantake ya kwanta boka ulumanu ya hau
bayamsa sannan ya bude fuka fukansa ya
luluka cikin gajimare.
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA ALJANI
HARISUL MAR'UF DA BOKA ULUMANU
Al'amarin yarima saiman kuwa lokacinda suka rabu da aljani zulkam
saiya kishin gida ya kwanta barci domin ya huce
gajiyar dake tare dashi aikuwa nantake sai barci ya saceshi bai sani ba
koda gimbiya suhaila taga ya kwanta barci sai itama ta sami waje ta kwanta itama ta kamayin barci
basu farka ba sai bayan gari yayi haske sannan suka farka
gimbiya suhaila ce ta fara farkawa don haka saita tashi yarima daga barcin
yana farkawa
saiya dubi tagar dakin yaga hasken rana koda ganin haka sai yayi sauri ya fito daga cikin tantin ya fara duba jama'arsa
koda ya fito wajen tantin saiyaga dukkan su sun gama yin shirin tafiya sunci kalacinsu
su kawai ake jira suci nasu sannan aci gaba da tafiya
koda ganin haka sai yarima ya dawo cikin tantinsa
awannan lokaci tuni wata kuyanga ta kawo abinci
da abin sha ta ajiye
nantake yarima da gimbiya suhaila suka kimtsa cikinsu suka sha ruwa sannan yarima
ya mayarda kayan yakinsa jikinsa
sannan ya nufo kofa da nufin ya fita
bazato ba tsammani saiyaji an ruko hannunsa ta baya
koda juyowa saiyaga ashe gimbiya suhaila ce ta rukoshi
tana murmurshi sannan tace
yakai mijina karka mantafa idan ka fita daga wannan tantin bai zama lallai ba mu sake haduwa dakaiba sai rana ta fadi
kuma zuciyata zata kasance cikin kewarka da begenka awannan lokaci
don haka inaso kayi mini wani abu wanda zai rage mini zugin rashinka akusa dani
kodajin haka sai yarima ya buda hannayensa biyu
ya rungume gimbiya suhaila tareda sumbatarta agoshi
sannan yace yake
tauraruwar datake haske acikin zuciyata
ki sani cewa tun daga ranar dana fara ganin ki da idanuna
na kamu da sonki ban taba yin koda dakika dayaba
ba tareda tunaninki ba,
ki sani cewa kece bugun zuciyata
duk numfashin da yake fita daga cikin hancina sakamakon bugun zuciyata
yana fitane tareda furta sunanki
saboda burin ganinki ne ma yasa idan munje wucewa ta wani birnin agaban mu zan tsaya na saya miki keken doki domin ki dinga kasancewa atare dani
kodajin wannan magana sai wani hawaye mai zafi ya zubo daga cikin idanun gimbiya suhaila
sannan ta sakeshi ya fita daga cikin tantin
ya nufi inda dakarunsa suke
koda sukaga yarima saiman ya fito sai suka dare suna masuyi masa jinjina da kirari
yarima saiman ya matsa gabansu ya tsaya sannan yace
yaku ahalin birnin ramlatul saif ku sani cewa a yaune zamu doshi
dajin da yake gaban mu wanda akewa lakabi da dajin mutuwa
amma kafin mu isa dajin zamu wuce ta gaban wani birni agaban mu
wanda akewa lakabi da askandariya
birnin askandariya birninine wanda ya sha hara afannin kira
kayanda suke kerawa kayane masu inganci
don haka awannan abakin wannan birnin zamu rabuda shugaban
dakaruna. wato zamnas ya shiga wannan birni don samo keken dokin da za'asa gimbiya suhaila aciki
koda gama fadin hakan sai yarima saiman kama dokinsa ya hau
sannan ya cire zobensa daga hannunsa ya cillashi sama
nantake wani farin haske ya fito daga cikin zoben ya nuna kudancin
wamda hakan yana nufin nan ne hanyarda zata kaisu dajin ajali
sannan ya dake rikida ya koma zobe zoben ya shiga jikin hannunsa
ba tareda bata lokaci ba suka sake tattara kayansu
suka sake shiga cikin dajin yarima saiman ne agaba tawagarsa suna tare dashi
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME AKAR GABA
PART 8
LBR
HABIBULLAH Ҡცř
TYPING HABIBULLAH KBR
lokacinda suka zaburi dawakansu suna masu tsala
azababben gudu sai abin ya zama abin sha'awa
kuma abin al'ajabi domin cikin lokaci kankani
suka dinga shafe doguwar tafiya acikin kankanin lokaci
tamkar basu kasance mutane ba aljanu ne
ba komaine yasa hakan ba face tsananin karfin
sihirin da yarima saiman ya dinga amfani dashine ya jawo haka
saboda bashida burin da yafi yaga ya shiga dajin ajali ya debo tsumin
dodo garjaju
sannan yaje fadar sarkin aljanu ya sato makullin
kofar kogon darul sihir domin tsira daga sharrin boka ulumanu
haka suka dinga kutsawa cikin dazuzzuka masu
matukar hatsari amma cikin kankanin lokaci
yarima saiman yake gamawa dasu komai tsananin yawansu
saida suka shafe kwanaki biyar suna tafiya
basa tsayawa sai idan lokacin cin abinci yayi
sannan ake tsayawa kowa yaci yasha wanda kuma yakeda wata bukata saiya tsaya yayi
sannan atashi aci gaba da tafiya
akwana na biyar dinne suka iso bakin wata mararrabar hanya
wacce ta rabu kaso biyu
kaso na daya ya nufi kudancin dajin
daya kuma kason ya nufi arewa
koda sukazo daidai wannan waje sai yarima saiman ya ja linzamin dokinsa ya tsaya
nantake kuwa kowa ya tsayar da nasa dokin ana jiran aji mai yarima saiman zaice
koda kowa ya gama nutsuwa sai yarima saiman yace
yaku ahalin birnin ramlatul saif nan ne mararrabar hanyarda zamu
rabu daku
domin daga nan inda nake tafiyace ta sa'a uku da rabi zuwa dajin ajali
anan zamuyi bankwana daku ni na tafi aikin dake gabana
koda yazo daidai nan azancensa
saiya kwallawa jarumi zamnal kira
nantake kuwa zamnal ya fito gabansa ya tsaya yana mai rissinawa
yarima saiman yace
yakai zamnal yanzu zan baka kudi ka tafi izuwa birnin askandariya
inaso ne idan kaje kasan kalar dabarar da zakayi ka shiga cikin wannan birni
duk yadda za'ayi kada ka bari mutane kasar su san cewa
kai dan birnin ramlatul saif ne dakai da dakarun
da suke tareda kai inaso ku je ku dawo da wuri
ku tadda jama'armu awannan sansanin sannan ku jiramu
idan kuma mune muka riga ku dawowa zamu jiraku anan wajen
koda yazo nan azancensa saiya zabo wasu dakaru guda ashirin
sannan ya dauko dukiya ya basu yace
idan kuka shiga cikin birnin askandariya
inaso ne ku shiga kasuwar birnin
ku nemi gidan sarkin makera na wannan birni
ya nuna muku irin kalar kirar keken dokin da sukeyi da kuma
wanda yafi kowanne kwari sai kuyi cinikinsa
ku dawo kada ku bari ashaida ko su waye ku
nantake ya nuna musu hanyar da tayi kudancin dajin
sannan yace wannan itace hanyar da zaku bi don shiga birnin askandariya
da wannan furuci nake umartarku daku kama hanya ku tafi
aikindake gaban ku
kodajin haka sai wadannan dakarun suka rissina sukace angama ya shugabana
nantake suka kama hanya suka nufi birnin askandariya cikin azababben gudu
bayan tafiyarsu
sai yarima saiman ya runtse idanunsa tareda
karanta wadansu dalasiman tsafi
faruwar hakan keda wuya sai wani dan karamin
gari ya bayyana shidai wannan gari girmansa
bai wuce na unguwa guda ba
koda bayyanr wannan gari sai yarima saiman ya umarce su da gaba dayansu su shiga ciki
shigarsu keda wuya sai kofar birnin ta kulle kanta
sannan ya sake ce dasu
wannan gari wajene mai matukar sirri da kwanciyar hankali
zaku zauna acikinsa har izuwa sanda zan dawo
babu wanda zai iya ganin wannan gari sai dan kabilar mu komai karfin sihirin mutum kuwa
don haka kada ku kuskura ku bude wannan kofa sai kunji
ana kwankwasata to da zarar kunji haka to nine ko kuma su jarumi zamnal
yana zuwa nan azancensa saiya juya ya nufi
kofar fita daga cikin birnin ba zato ba tsammani saiyaji ana kwalla masa kira
ba kowa bane ba face
gimbiya suhaila nantake ta rugo gareshi ta rungume shi tana cewa
akan wanne dalili zaka tafi ka barni ka sani fa kaine
kadai burina arayuwa
idan ka mutu babu shakka nima saina mutu
saboda sonka ne zai zamo sanadiyar ajalina
kodajin haka sai jikin yarima saiman yayi sanyi
sannan ya dago da fuskarta suna kallon juna
sannan yace akan wanne dalili zan mutu na barki
alhalin banga dana da yake cikin cikinki ba
sannan kuma ban cika mafarkin da mahaifina ya dade yanayi ba
dangane da rayuwar da samar anan gaba ba
ina tabbatar miki da cewa koda zan mutu
sai
bayan mun isa kogon tsafin boka awaisul masawi lafiya
yana zuwa daidai nan azancensa saiya hura mata wata iska daga cikin bakinsa
faruwar hakan keda wuya sai wani irin nan nauyan barci ya dauketa
koda faruwar hakan sai ya kira wasu kuyanginta yace su dauketa su kaita cikin turaka
nantake kuwa kuyangin suka cika umarni
tafiyar kuyangin keda wuya sai yarima saiman ya ratsa wannan kofar birnin
ya fita daga cikinta
kamar yadda ruwa yake ratsa kasa
ya fice bai bayyanaba sai abakin kofar birnin da tazarar tafiyar da
bata wuce taku hamsin ba
koda bayyanarsa a wannan waje sai ya bude bakinsa
ya kwallawa aljani markazulu kira
faruwar hakan keda wuya
sai wata irin iska mai karfin gaske ta fara kadawa
cikin dakiku kadan saiga aljani markazulu ya bayyana
bayyanarsa keda wuya sai ya dubi yarima saiman yace
ai tun daga sanda muka rabu dakai ina tare
dakai batareda ka sani ba duk inda ka shiga ina biye dakai
amma banda waje daya
wannan guri kuwa shine cikin tantin da kuka zauna kaida
matarka babu yadda banyiba akan na shiga ciki ba
amma na kasa shiga ko naji abin da kuka tattauna acikin sa
kodajin haka sai yarima saiman ya bushe da dariya sannan yace
to kai atunaninka bansan da haka bane?
kamar yadda kake kallona haka nima nake kallonka
abinda yasa kuwa ka kasa shiga cikin tantina
shine nine nayi amfani da karfin sihirina na hanaka shiga
cikinsa ko kaji abinda muke tattaunawa da ita
kuma babu wanda ya isa ya iya shiga cikin wannan tantin
nawa awannan lokaci face boka ulumanu saboda shima
yana da irin wannan sihirin
koda yarima saiman ya zo nan azancensa sai jikin aljani markazulu yayi
sanyi ya tabbatar da cewa lallai yarima saiman ya sha kansa abangaren karfin sihiri
don haka sai ya dakatar da wannan maganar
don gudun kar ya gane abinda yake cikin zuciyar sa
sannan yace ya kai abokin tafiya ta to ta wacce hanya kake ganin
zamu shiga cikin dajin ajali har mu debo tsumin dodo garjaju?
koda jin wannan tambayar sai yarima yayi murmurshi sannan yace
lallai baka san ko waye dodo garjaju ba
duk abinda kake takama dashi to dodo garjaju ya sha kanka
abinda nakeso dakai kawai shine ka zamo mai juriya acikin duk wahalar da zamu fada ccikinta
koda gama fadin haka sai ya ya kama hanyar shiga dajin ajali gadan gadan
batareda fargabar komaiba
koda ganin haka sai aljani markazulu ya bi bayansa
da sauri saida sukayi tafiyar sama da sa'a uku
sannan suka iso kusa da iyakar dajin aajali
koda sukazo daidai wannan guri duk sai suka cak
yarima saiman ya dubi markazulu yace
ba zamu shiga
cikin wannan dajinba kai tsaye
dolene muyi amfani da karfin sihirin mu don mu isa karshen wannan dajin da wuri
ba tareda an farga da zuwanmu ba
abin da zamuyi kuwa shine duk mu biyun zamu rikide mu koma siffar kibiya
sannan mu cilla kanmu cikin tsananin gudu
duk abinda kuwa ya shiga gabanmu to mu hudashi
mu wuce koda kuwa ginine
koda jin haka sai aljani markazulu ya bushe da dariya
domin shi azatonsa yarima saiman wasa yakeyi
haryana birgima da kasa
koda ganin haka sai ran yarima saiman ya baci
nantake ya soma karanta wadansu dalasiman tsafi
faruwar hakan keda wuya sai duk su biyun
suka rikide suka zama kibiyoyin bakin karfe
sannan kibiyoyin suka cilla kansu suka tashi
sama suna masu falfala azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya
haka suka dinga gudu acikin sararin samaniya
duk abinda suka tarar agabansu nan take suka dinga hudasu
komai kwarinsa koda kuwa ya kasance karfene
koda dodannin suka lura da abinda ke faruwa sai
suka taho gaba dayansu suka dinga kawowa
kibiyoyin sara amma kafin ya sauka ajikin kibiyar
saikaga sun wuce da gani tamkar anyi ruwa an dauke
nan da nan suka dinga huda kirajen dodannin suna wucewa da karfin tsiya
kafin cikar 'yan dakiku sun iso inda gidan sarautar
wadannan dodannin yake
ba zato ba tsammani sai sukaji ansa kafa an buga su da ita
nantake duk kibiyoyin biyun suka ja da baya
kamar an janyesu da majajjawa saboda karfin dukan da akayi musu
suka je suka gwaro da wani dutse
nantake duk su biyun suka dawo izuwa ainihin siffarsu
lokacinda suka ji kamar an balla kashushuwan bayansu
lokaci guda suka dago kawunansu domin suga
wanda yayi musu wannan mummuna duka
bakowa baneba face dodo garjaju
shidai garjaju yakasance babbar halitta mai matukar tsawo da kauri
idan suka kalli tsawonsa sai suga kamar ya hade da sararin samaniya
tsawon hannunsa kowanne guda daya yakai tsawon babbar bishiyar dabino
kaurinsa kuwa yafi kaurin katuwar bishiyar kuka
yana da jajayen idanu kamar an gasa dan buda awuta
kai duk inda siffar jarumta da kuma rashin imani takai
to dodo garjaju ya wuce wannan siffa sai abinda idanu suka gani
akansa
nantake ya tsaya ya karewa su yarima saiman kallo atsanake
sannan ya bushe da dariya yace
yaku wadannan kananun halittu yan da wannan
kankanuwar jarumtakar taku kuke tunanin har zaku iya
fadata domin diban tsumin tsafina?
lallai tsafinku ya yaudareku tunda har ya turo ku
inda ajalinku zai riskeku tunda sauran kuruciyarku
kodajin haka sai yarima saiman ya daka masa tsawa
yana mai cewa kai tsohon azzalumi karyarka tasha karya
kai waye da har kake tunanin zaka hana mu biyan bukatar mu?
ka sani zalunci baya taba dorewa don haka karshen
zaluncinka ne yazo ayau dinnan wannan ce ma silar da tasa muka shigo cikin wannan daji
na rantse da abin bautana bazan fita daga cikin dajin nan ba harsai na debi tsumin tsafinka koda kuwa ban sami nasarar hallaka ba
kodajin wannan batu sai dodo garjaju ya bushe da dariya sannan yace
kai yaro lallai maganar ka ta burgeni da kuma izzar da kake da ita
don haka zanso na gwada jarumtakar ka akan ta dakaruna
domin naga iyakar jarumtakar da har kake takama da ita
koda gama fadin hakan sai ya umarci wasu zaratan dakarunsa dasu kamo masa su yarima saiman
nantake kuwa dakarun suka afka musu aka ruguntsume
da azababben yaki na gaban kwatance
fara yakin keda wuya sai suka tashi kura ta cika dajin har bama ka

Please Login or Register in order to submit comment