Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka gwaru da wata bishiya .nantake
kashin bayansu ya karye .
cikin karaji ya hausu da sara da suka tako
ina sai ga kawunan bila'adama yana yawo a
sararin samaniya .
jini Kuwa yadinga yawo kamar anbude
idaniyar ruwa .
sassan yadinga yawo kamar ana sassabe
agona .
sai gashi mutun daya ya zamewa mutane
dubunnai alakakai tamkar guguwar zame masu guguwar annoba.su kansu
sunsan cewa yau sun hadu da gamonsu rana
ta baci domin basu taba haduwa da wani
jarumi ba kwatankwacin sa.domin fada
yakeyi tamkar ba jikin jini da tsokane da
shiba.
kafin cikar sa'a biyu ya karar da rabinsu.
koda shugaban yan fashin ya lura da abin
dake faruwa,sai ya daka musu tsawa.
nan take kuwa suka dakata da fadan.
shugaban nasu ya matso inda yarima yake ya
tsaya agabansa,sai ga yarima saiman ya
zamo dan kankani agabansa.
shugaban nasu ya dubi yarima yace
tabbas jarumtakarka ta burgeni don haka ina
gayyatarka daka shigo cikin kungiyarmu,zan
baka babban mukami idan kayarda.
idan kuwa kaki ni da kaina zan kasheka.
koda jin haka sai yarima ya daka masa
tsawa yace
kai lalataccen banza kune kuka bata mana
nahiya da kashe kashen rayukan wadanda
basu jiba basu ganiba.
don haka nadau alkawarin ganin bayanku
babu wani sulhu a tsakaninmu.
da gama fadin haka sai ya afka masa suka
kachame da azababben yaki fiye dana farko.
ya zamana suna kaiwa junansu sara da suka
cikin kwarewa.sai gashi yarima yazama dan
karami agaban wannan dan fashi amma
abinda zai baka mamaki shine.
a fannin iya yaki yarima ya tattaka dan
fashin.
wohoho hakika jarumtaka baiwace wanda
allah ya baiwa ya huta
duk da tsananin karfi irin na wannan dan
fashi sai ya zama na banza domin kokarin
kare kansa yake yana neman hanyar tsara.
koda yarima ya fuskanci nufin wannan dan
fashi sai ya shammace shi yasa takobi ya
sare masa kai.
nantake gangar jikin ta fadi kasa.
koda raguwar yan fashin sukaga gawar
shugabansu akasa .sai duk suka zubar da
makamansu suka ruga da gudu.
nanfa yarima saiman ya dinga bin dakarun
daya bayan daya yana kashesu har sai da ya
karar dasu gaba daya sannan ya dawo wajen
sansaninsu.
da isowarsa sai ya tarar da dakarunsa da
jama'arsa suna ihun farinciki. a gaban
dakarun kuwa babu kowa sai gimbiya
suhaila.
tayi shigar wata jar riga mai tsananin
kyau.ta daure gashin kanta agadon bayanta
sai sheki da walwali yakeyi.
cikin murna ta jawo hannun yarima saiman
izuwa cikin tantinsu,sannan ta dauko wani
daddadan abinci ta ajiye masa.
nantake kuwa ya faracin abincin cikin nishadi
da annashuwa.
da gamawarsa saita dubeshi tace ina tayaka
farin cikin samun nasararka a wannan yaki.
ya dubeta yace nayi wannan aikine domin
kare mutuncin al'ummarmu.
don haka yanzu zamu tashi mubar wannan
guri muci gaba da tafiya don biyan
bukatarmu.
yana daga cikin tantin nasa yakira shugaban
dakarunsa mai suna zamnal.
cikin kankanin lokaci shugaban dakarunya
iso cikin tantim dare da fadin gani ya
shugabana.
yarima yadube shi yace inaso ka umarci
dakarunmu dasu gaggauta hada kayansu don
muci gaba da tafiya.zamnal yace angama ya
shugabana.
nantake zamnal ya tashi ya fice daga cikin
tantin nasu.
cikin kankanin lokaci kuwa suka hada inasu
inasu suka cigaba da tafiya izuwa hanyar da
zata kaisu dajin kurusul saudam saida suka
shafe lokuta masu tsawo suna tafiya sannan
suka iso wata mararrabar hanya wacce ta
kasu kaso hudu.
nantake sukaja birki suka tsaya sukayi cirko
cirko cikin rashin sanin hanyar da yakamata
subi
ana cikin wannan hali sai yarima saiman ya
tuna da maganar da mahaifinsa yayi masa
akan zoben hannusa.
koda gama wannan tunani sai ya zaro zoben
daga hannunsa sannan ya murza.
faruwar hakan keda wuya sai wani haske ya
fito daga jikin zoben ya nuna musu hanyar
data nufi yammcin dajin.
inda yake musu nuni da cewa itace hanyar
dajin kurusul saudam.
koda ganin haka sai yarima saiman ya juyar
da linzamin dokinsa zuwa hanyar da hasken
ya nufa.cikin tsala azababben gudu.
WANNAN SHINE ABIN DAYA FARU GA
YARIMA SAIMAN AKAN HANYARSU TA
ZUWA DAJIN KURUSUL SAUDAM
++ +++ ++
Al'amarin aljani karkazulu kuwa lokcin daya
bar kogon daya kashe samriya da babanta
kuwa.
sai ya kasance yana tsala gudu nagaban
kwatance asararin samaniya ba tare da sanin
inda zaijeba.cikin jin izza da takama.
yana cikin tafiyarne ya fara tunane tunane
akan wanne shiri yakamata yayiwa kansa.
tabbas yanada bukatar karawa kansa shiri ta
yadda zai iya hallaka boka ulumanu cikin
sauki batare da wata wahalaba.
sannan kuma ya tuna da batun dodo garjaju
yanzu yana cikin fushi dashi.
yana cikin wannan tunanine kuma ya tuno da
batun yarima saiman.
i dan hada kai dashi to tabbas zai sami
nasara.sannan kuma bayan bukatarsa ta
tsira sai ya yaudari yarima saiman ya
hallakashi.
koda gama wannan tunani sai ya bushe da
dariyar mugunta.
sannan ya juya ya nufi hanyar dajin kurusul
saudam (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
LITTAFIN BAKAR GABA
PART 5
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
koda sarki abu saiman yazo nan azancensa
sai mutane suka kamu da murna har sunayi
masa jinjina
da kirari tamkar suna da tabbacin samun
nasara awannan yaki
koda ganin haka sai farinciki ya kamashi
sannan yace
daga wannan rana inason makeran dake
cikin birnin nan da su dage wajen kera
miyagun makaman yaki
wadanda zamuyi amfani dasu awannan yaki.
sannan mayakan mu su dage wajen baiwa
kansu horon yaki tare da sauran mutanen
gari
sannnan duk wanda yakasance yana da ilimi
wajen sanin tarkunan yaki ina nemansa
yanzu a tsakiyar fada
yana gama fadin haka sai dakaru suka dare
sai ga wani dattijo yafito fuskarsa cike da
furfura
amma da kaganshi kasan y asaba da
kwarmatsuw a filin daga.
sannan wasu samari guda biyu suka fito
daga cikin jama'ar gari suma suka tsaya
akusa da wannan dattijo.
dukkansu suka rissina agaban sarki.
dattijon ya rissina ga sarki sannan yace
ni sunana zamnur kuma ina daga cikin
manyan dakarun wannan birni
kuma ina da ilimi na musamman wanda na
koya a makarantar horon yaki tun ina
matashi.
dajin haka sai sarki yace
to wacce irin shawara zaka bamu game da
wannan yaki?
dattijon yace ina da wasu tarkuna wadanda
nake ganin zasu taimaka mana a wannan
yaki
sudai wadannan makamai bakomai bane face
wasu kananan allurai
wadanda ake daurasu asaman bishiyoyi.
dazarar abokan gaba sun iso sai a tura
dakaru kamar guda ashirin su watso
wadannan allurai
da zarar anyi haka zasu cake ajikin abokan
gaba ba tare da sun lura ba
saboda tsabar kankantar su.
saidai daga baya dakarun zasu dinga fadowa
daga kan ababan hawansu matattu
koda jin haka sai sarki abu saiman yayi
murmuashi yace
tabbas wannan dabara taka tayi dai dai don
haka zanuyi amfani da ita.
sannan saurayi na biyu yafito ya tsaya gaban
sarki yace
ni sunana ruslan da ga sarkin dajin wannan
birni
mu a gidan mu akwai sihirin tsafin da
mahaifin mu yabar mana na wadansu
kunamai maau fuka fukai wadannan kunamai
suna nan a cikin dajijjikan dake kewaye da
birnin nan
mahaifin mu a bincikensa ya gano da akwai
wadannan kunamai
sannan ya boyesu da karfin sihirinsa.
kafin ya mutu saida ya barmana turaren da
za'aje akunna shi acikin daya daga cikin
dajijjikan wannan kasa.
da zarar anyi haka bayan sa'a uku wadannan
kunamai zasu baiyana su cigaba da aikin su
na tsaron wannan birni.
koda ya gama fadin haka sai ya koma kusa
da tsoho zamnur ya tsaya.
sai saurayi na uku shima ya fito gaban sarki
ya tsaya yace
nine sadauki huskan masanin taswirar
dajijjikan dake wannan kasa.
sannan nasan wadansu tarkuna da ake binne
su a karkashin kasa.
sudai wadannan tarkuna za'a hadasune da
wani sinadarin magani wanda ake jikashi
acikin sanan a sami manyan tuluna azubashi
aciki
sannan a sami igiyoyi adaure tulunan dasu.
bayan anyi haka sai asami wasu dakaru su
hau saman bishiyoyi da zarar abokan gaba
sun iso sai suja wadannan igiyoyi.
nantake tulunan zasu watsawa maykan
ruwan dake cikin tulun.
da zarar ruwan ya taba jikinsu
nantake jinin jikinsu zai kafe su zama
gawarwaki.
koda wadannan mazaje suka gama fadar
fasahar su sai sarki abu saiman ya bushe da
dariya
sannan yace
tabbas kun bada shawara mai kyau,da kuma
babbar gudun mawa
don haka zamuyi amfani da ita.
nan take ya sallami jama'ar gari baki
dayansu sannan sannan ya shige cikin gidan
sarauta
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN
RAMLATUL SAIF BAYAN SARKI ABU SAIMAN
YA HADA ZAMAN FADA
++ ++ ++
al'amarin yarima saiman kuwa lokacin da
suka durfafi dajin kurusul saudam kuwa
sai suka kasance cikin tsala azababben gudu
saida suka shafe kwana goma suna tafiya
sannan suka iso dajin kurusul saudam
suna isowa sukayi arba da wasu dogayen
bishiyoyi wadanda sai an daga kai sannan
ake ganin karshensu
suna isowa daidai wannan guri sai yarima
saiman yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak
sannan jama'ar dake bayansa suma suka ja
nasu linzaman dawakan.
yarima saiman ya juyo ya dubesu yace
wannan shine farkon dajin kurusul saudam
don haka nanne gurin da zamu rabu daku
nina tafi izuwa naman takobin sihiri
bana bukatar taimakon kowa daga cikin ku
har naje na dawo.
taimako daya kurum nake nema agurinku.
shine ku kula da lafiyar gimbiya suhaila har
izuwa lokacin da zan dawo.
koda gama fadin haka sai yarima yaga
zamnal jikinsa yayi sanyi
kawai sai yaji tausayinsa ya kamashi.
nantake ya matso kusa dashi yace.
kayi hakuri ka zauna kusa da jama'ata bana
son arasa ko mutun daya daga cikin ku.
don haka nake kokarin hanaku shiga cikin
abubuwa masu hatsari.
yana gama fadin haka sai ya nuna jama'arsa
da hannunsa
nantake wata raga mai kamar kejin karfe ta
fito daga cikin hannunsa ta kewaye su yadda
babu wanda zai iya fitowa daga cikinsu.
sannan yace dasu daga yanzu babu wani
hatsari dazai sameku har naje na dawo
yana gama fadin haka haka sai ya juya da
nufin ya shiga cikin dajin kwatsam sai yarima saiman yaga sararin
samaniya tayi duhu.
kawai sai ga aljani markazulu ya baiyana a
saman kan yarima saiman.
nan danan aljanin ya sauka a gaban yarima
sainan
nanfa aka soma kallon kallo atsakaninsu na
tsawon lokuta
sanan yarima saiman ya dubi markazulu
yace
kai kuma me ya kawo ka wannan dajin?
kodajin haka sai markazulu yace
nine markazulu tsohon hadimin boka
ulumanu
nazo gurinka ne don na nemi hadin kanka
mu yaki boka ulumanu.
kodajin haka sai yarima saiman ya turbune
fuska
sannan yace dashi
bana bukatar taimakonka har abada don
haka nan ne wajen daya kamata mu rabu
dakai.
bana bukatar na sake haduwa dakai nan
gaba domin bazatayi kyauba.
yana gama fadin haka sai ya kada linzamin
dokinsa ya shige cikin dajin yabar markazulu
atsaye.
nan take ya bace bat tamkar bai taba
wanzuwab.
shikuma yarima saiman kutsa kai cikin dajin
cikin gaggawa.
a wannan lokaci zuciyarsa cike take da
zumudin isa tsakiyar wannan daji don biyan
bukatarsa.
sai daya shafe sa'a shida yana tafiya acikin
dajin sannan ya iso karshensa tun daga nesa
ya dinga ganin dake cikinsa wasu irin many
manya
kirar mutanen farko
jikinsu amurde yake tamkar sassaka su akayi
da itace.
fuskokinsu cike suke da gashi kai kace
gwaggwan birine
suna da jajjayen idanuwa tamkar angasa dan
buda awuta.
koda suka lura da tahowar yarima saiman
sai daya daga cikinsu ya zaro wani kahon
giwa ya busa
nan take wata kara ta cika dajin gaba daya
tare da amsa kuwwa.
nan dan ragowar dakarun dake dajin suka
lura da abin da yake faruwa
nantake suka ruga da gudu suka soma debo
makaman yakinsu domin tunkarar yarima
saiman.
sudai wadannan arnan dajin sunada matukar
yawa domin zasu kai su dubu goma.
sannan suna karkashin mulkin wani
hatsabibin matsafi wanda yake
shugabantarsu.
kuma yasan dalilin zuwan yarima saiman
don haka yasananr da ragowar dakarunsu
don su san da zuwansa
yarima saiman yana isa kusa da inda
dakarun suke sai yaja linzamin dokinsa ya
tsaya cak
sannan ya budi baki yace
ku ma'abota rayuwar daji kananun jarumai
wadanda suke tsoron rayuwa da mutane yan
uwansu tamkar dabbobi
to yau ni saiman na zo wannan birni domin
na yakeku na zubar da jininku na hana
zuluncin da kukeyi adoron kasa da kwacen
da kukeyiwa matafiya akan hanyarsu.
nayi alkawarin saina hallakar daku muddin
bazaku yarda da sharadin danazo muku
dashiba.
sharadin kuwa shine
inaso ku mikomini takibin sihirin da kuke
bautawa cikin ruwansanyi domin mu rabu
lafiya daku batare da an zubar da jini ba…
kafin ygama fadar maganar dake bakinsa sai
su shugaban wadannan arnan daji yafito
asukwane bisa wani ingarman doki ya tsaya
agaban dakarunsa.
sannan ya bushe da dariya
ya dubi yarima saiman yace lallai kayi
kuskure da kake tunanin zaka kwaci
maigirma takobin sihiri a hannunmu.
inaso kasani cewa koda mutanen duniyane
zasu taru basu isaba balle kai mutum daya
tak
yana zuwa nan a zancensa sai ya umarci
arnan dajin dasu harbowa yarima saiman
kibiyoyinsu
nantake kuwa suka dana baka sukaharbo
masa .
saiga sararin samaniya tacika da kibiyoyi
sannan suka durfafo kan yariman saiman
nantake yarima saimanya zare takobinsa.
sannan yasawani silken sihiri ya lullube
dokinsa da ita gaba daya
sanna ya shiga kade kibiyoyin da suke harbo
masa cikin zafin nama,juriya da bajinta.
wohoho hakika jarumtaka baiwace duk
wabda allah yabaiwa ya huta.
wani abin mamaki shine gani yadda yarima
saiman yake kare hare haren da kibiyoyin
suke kawo masa cikin kankanin lokaci.
sai gashi anrasa kibiya ko guda daya wacce
zatq iya lakutar jikinsa.
sai bayan yan dakiku sannan kibiyoyin suka
kare.
nan fa dakarun suka rufo kansa aka kachame
da azababben yaki nagaban kwatance.
idan kaji ance ga ki gudu to sa gudu ne bai
zoba.
domin duk da karfin damtse irin na
wadannan dakru sai yarima saiman shi kadai
ya gagaresu suka rasa yadda zasuyi dashi.
domin yana wata jarumtaka ne taban al'ajabi
wacce na tsaya fasaltamaka itama bata
lokaci ne domin duk kwatancen mai kwatace
bai isa ya fasalta maka irin yaki da yakeyi
ba.
awannan lokaci kasa ta soma girgiza,kura ta
turnuke sararin samaniya saboda
kwarmatsuwar da suke yi akan kasa.
karar karafa ta cika dodon kunne,tare daihun
mazaje,jini ya dinga fallatsi akan kasa
tamkar an bude magudanar ruwa
awannan lokaci sabodane saboda tsananin
bala'i tsuntsaye suka dinga tashi suna
chanza sheka.
barewa suka dinga fadawa garken zakuna
basu sani ba don su ceci ransu.
duk inda yarima saiman yasa gaba saidai
kaga mazaje suna zubewa kasa tamkar ana
sassabe agona.
duk da irin wannan mummunar barna da
yake musu batasa sunja da bayaba.saboda
tsananin naci tamkar basu ake kashewaba.
sai wani irin karaji sukeyi suna dada kunno
kai cikin rashin tsoro da yarda dakai.
shi kuwa ya wanzu yana mai zare musu
ruhin numfashinsu tamkar mala'ikan mutuwa Sai da suka shafe sa'a uku suna fafat
wannan kazamin yaki tsakanin arnan dajin da
yarima saiman.
an rasa wanda zai sami galaba akansa
ana cikin wannan haline yarima saiman yaji
an gabza masa naushi da kafa agadon baya
saboda karfin naushin sai da yarima saiman
yayi tsalle kamar an janye shi da majaujawa.
kamar zai fadi kasa amma saboda tsananin
jarumtaka sai yarima saiman ya juya jikinsa
a sararin samaniya
sannan ya dire bisa kafafunsa.
amma kafin ya dawo cikin haiyyacinsa sai ya
sake jin an kara gabza masa wani sabon
naushin a kirji wanda yafi na farko.
saboda karfin naushin sai da yaji kamar
kashushuwan kirjinsa sun kakkarye.
bakowa ne yayi masa wannan duka face
shugaban wadannan arnan daji.
nan take ya takarkare ya bushe da dariyar
farinciki sannan ya dubi yarima saiman yace
lallai ka cika mai tsautsayin wahala tunda
har kake shirin raba mu da takobin sihirin
mu
yanzu kai a haka zakaje ka yaki dodo garjaju
har ka sami tsumin tsafinsa.
sannan kaje fadar sarkin aljanu ka rabasu da
miftahul darul sihir?
hakika yanzu zaka hallaka sannan naje na
kama ragowar mutanen da suke tare da kai
namai dasu bayin mu.
yana zuwa daidai nan a zanncensa saiya
zare takobinsa ya nufo kan yarima saiman da
nufin tsige masa kai.
ba zato ba tsammani sai yaji wata irin iska
mai karfi ta taso ta shureshi ta damfara shi
da kasa
bakowa bane yayi wannan aikiba face aljani
markazulu
nan take ya tashi yarima saiman zaune yace
kai jeka ka tari shugaban yan fashin
ni kuma zanje na tari ragowar dakarun in
yaso idan na gama dasu sai in taimakama.
yana zuwa daidainan azancensa sai ya shige
cikin dakarun ya hausu da sara da suka ta
ko ina babu kakkautawa duka inda ya nufa
saidai kaga arnan dajin na zuba a kasa
tamkar ana sassabe agona.
shi kuwa yarima saiman sai ya gyara rukon
takobinsa
ya nufi inda shugaban arnan dajin yake kai
tsaye.
nan fa aka soma kallon kallo a tsakaninsu
kai da gani kasan kar ce ta san kar.
har na tsawon dakiku daga chan sai suka ja
da baya kamar tazarar taku goma
atsakaninsu.
sannan suka gyara rukon takobinsu
suka rugo kan juna suka kacame da
azababben yaki mai matukar muni fiye da
wanda akeyi tsakanin aljani markazulu da
ragowar dakarun arnan dajin.
sai fadan nasu ya zamo abin tsoro kuma
abin sha'awa sakamakon yadda suke fadanda
dukkan karfin su.
shidai shugaban wadannan arnan daji wani
irin gabjejen mutum ne mai kirar muatanen
farko
sannan yana da manya manyan idanu jajaye
masu matukar kwarjini.
kirjijsa faffada ne cike da gashi.sai kace
zaki.
yana da manya manyan damatsa kamar
jerasu akayi.
kai duk inda mutum mai suffar karfi yakai to
wannan mutum yafishi cika ido
shi kuwa yarima saiman sai ya zama dan
karami akansa.
amma duk da haka sai gashi ya kasa samun
nasara akan yarima saiman saboda matukar
karfin damtsensa.
dajuriyarsa da kuma nacinsa.
hakika yarima saiman ya isa a jinjina masa
ganin yadda yake yaki da mutumin da ya
fisyi kwarjin da cika idanu.
dukkansu suna yi fadanne cikin mugun nufi
da burin salwantar da rayukan juna.
koda suka dau wani lokaci suna wannan
fafatawa .
sai dukkansu suka ja da baya.
suna hararar juna kamar zakaru.
daga chan suka sake falfalowa da gudu suka
sake kachamewa azababben yaki fiye da
farko.
sai gashi suna hadawa da sara da suka
sama da kasa.
har tsalle sukeyi suna kai farmaki ko kuma
wani lokacin kaga suna zamiya akasa.
awannan karon ma sai aka kasa samun
wanda zai nasara daga chan sai shugaban
arnan dajin yayi wurgi da takobinsa.
sannan yace da yarima saiman
tunda dai munga salon fadan namu iri
dayane to mai zai hana mu gwada karfin
damtsen mu banbance tsakanin aya da
tsakuwa.
kodajin haka sai yarima saiman yayi
murmushin yadda dakai sannan yayi wulli da
takobinsa.
nan take suka kachame da kokawa.
awannan lokaci sai fadan nasu ya chanja
salo domin ana fara fadanne kowanne daga
cikinsu jikinsa ya fara gaya masa.
duk sa'adda yarima saiman ya sami nasarar
dukan shugaban yan fashin sai kaga shima
ya rama kamar dama chan sun tsara haka
fadan zai kasance.
ana cikin haka yarima saiman yaga idan
suka ci gaba da fadan ahaka to zasu iya yi
ragas.
kawai sai ya shammaci shugaban arnan dajin
ya yi tsalle ya kama kansa ya murde sannan
ya wullar da gawarsa gefe daya.
koda ragowar arnan dajinsuka ga gawar
shugabansu a kasa sai suka zubar da
makamansu.
suka ruga da gudu nan take yarima saiman
ya tashi ya dinga taimakawa markazulu suka
dinga binsu suna rafkewa.
kafin cikar wasu yan dakiku sun gana
hallakasu.
koda suka karar dasu sai yarima saiman ya
juyo ya dubi markazilu sannan yace .
wai kai meyasa kake bibiyata ne shin ban
hanaka biyoni ba?
kodajin wannan tambaya sai markazulu yace
kayi hakuri yakai wannan jarumin jarumai
bana biyo ka bane don na cuce ka ba.
na biyo kane kawai don nasan ra'ayin mu
daya dani dakai ma'ana na yakar boka
ulumanu.
kodajin haka sai yarima ya sake tambayar sa
yace to menene dalilin da yas a kake da
burin yakarsa?
kodajin wannan tambaya sai aljani markazulu
yayi shiru kamar bazaice komi ba.
daga chan sai yace
mun sami sabani da uban gidanane
sakamakon nima na sami babban matsayi a
fannin sihir.
koda gama jin haka sai yarima saiman
jinjina kansa azuciyarsa yace tabbas akwai
wani boyayyan sirri a zuciyar markazulu.
don haka dolene nasa idanu aknsa.
kawai sai yace da markazulu.
shikenan na amince da tafiya tare da kai.
amma da sharadi.
sharadin kuwa shine bazakaci amanarmu ba.
kodajin haka sai markazulu yace na amince
da wannan sharadi naka.
nan take suka kama hanya suka shiga cikin
garin arnan dajin.
sai da suka wuce sa'a biyu sannan suka iso
kofar wani babbar fada.
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME
DOMIN SAMUN CIGABAN SAI KU KASANCE DA MU A KODA YAUSHE
DAGA SHAFIN WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
BAKAR GABA
Littafin HABIBULLAH Muhammad kabara
Kashi na biyu 2
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG










(IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
LITTAFIN BAKAR GABA
PART 6
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Ita dai wannan fada an ginata ne da zallar
duwatsun wuta.
kuma tana da girman gaske tamkar fadar
wata babbar masarautar.
kofar fadar an sana antatane da zallar bakin
karfe mai matukar karfi.
koda suka iso daidai wannan wuri sai suka
tsaya sukayi cirko cirko sakamakon rashin
sanin makullin da za'a bude wannan kofar.
daga chan sai yarima saiman yace da aljani
markazulu yanzu taya kake tunanin zamu iya
bude wannan kofar dajin haka sai markazulu
ya bushe da dariya sannan yace
don dai wannan kofar aini kadai zan iya
budeta.
nan take markazu ya karasa jikin kofar ya
tattara karfinsa ya kamata da nufin ya
budeta.
nan take jijiyoyin jikinsa suka tashi sukayi
burdin burdin
gumi ya dinga tsatstsafowa daga jikinsa.
amma saidaya shafe yan dakiku kuma kofa
taki buduwa.
bisa dole ya saki kofar ya koma gefe yana
mai zare idanunsa.
sannan yace da yarima saiman tunda dai
karfina ya kasa bude wannan kofar to mai
zai hana muyi amfani da karfin sihirin mu?
kodajin haka sai yarima saiman shima ya
matso kusa da markazulu yace to shi kenan
mu jarraba mu gani.
nan take suka bude tafin hannuwansu sannan
suka karanta wadansu dalasimai na tsafi.
nantake wata irin iska mai matukar.karfi ta
fito daga tafin hannunsu
ta tafi da gudu izuwa jikin wannan kofa.
koda saukar wannan iska sai wata irin tsawa
mai karfi ta tashi.
amma duk da haka ko kwarzane babu ajikin
kofar
koda ganin abinda ya faru sai yarima yace da
markazulu
koda ace zamu hada sihirin mu gaba daya
bamu isa mu iya bude wannan kofa ba.
don haka ina tunanin makullin wannan fada
yana jikin shugaban wadannan arnan daji
don haka sai mu gaggauta zuwa mu duba
jikinsa mu dauko makullin.
koda gama fadin haka sai markazulu yace
an gama
nan take ya bude fuka fukansa ya luluka
cikin gajimare
kafin cikar dakika uku yaje ya dawo da kubar
kogon
itadai wannan kuba yar mitsitsiyace kamar
misalin allura haka girmanta da kaurinta
yake.
koda dawowarsa sai ya mika wa yarima
saiman wannan kuba.
yarima saiman ya karbi kubar sannan yaje
jikin wannan kofa ya zurata sannan ya
murda.
nantake wata irin kara ta cika dajin gaba
daya sakamakon zarewar wasu manyan
sakatu.
koda kofar ta gama budewa sai suka kunna
kansu cikin fadar.
suna shiga cikin fadar sai suka cika da
mamaki domin fadar ta kawatu ainun fiye da
tunanin mai tunani.
saboda komai na fadar an kerashine da
zallar karfen zinare.
sannan kuma akarshen fadar an ajiye wata
karagar mulki ta alfarma sai kace fadar wani
babban basarake.
ahankali su yarima ci gaba da tafiya acikin
fadar har suka iso dai dai kan karagar mulki.
koda suka iso dai dai wannan karaga sai
yarima saiman yaga wani dan karamin.littafi
mai ban sha'awa kuma.littafin a manne yake
.ajikin wani dan karamin teburi dake gaban
karagar mulkin.
ma'ana shidai wannan littafin ba'a daukarsa
saidai duk amfanin da zakayi kayi dashi a
inda yake.
nantake wannan littafi ya baiwa yarima
saiman sha'awa don haka sai yafara duba
littafin shafi shafi yana karantawa.
littafin yana daukene da hotuna kala na
abubuwan ban sha'awa.
yana cikin karanta littafin ne sai yayi arba da
wani kyakkyawan fure mai jan launi.
babu abindaya bashi sha'awa kamar wannan
fure don haka yakai hannu ya shafa wannan
fure
yana shafarsa sai yaji wata kara ta cika
fadar gaba dayanta.
nan take kasa ta tsage
saiga wata siririyar hanya ta bayyana izuwa
wani gidan karkashin.kasa.
koda ganin abindaya faru sai aljani
marakzulu ya kalli yarima saiman cikin firgici
yace.
karka sake ka shiga wannan gida domin zai
kaikane izuwa ga hallaka idan zaka karbi
shawarata karka shiga cikinsa.
koda jin haka sai yarima ya bushe da dariya
yace
haba abokina kar ka bani kunya mana.
kadafa ka manta sadauki baya amsa sunansa
sadauki sai ya sha wahala a arayuwarsa
sannan kuma ni ina da tabbacin cewa a.cikin
wannan gidan karkashin kasa zamu samo
takobinda mukazo nema.
yana gama fadin haka saiya.shige cikin
wannan gida
nan take markazulu ya bishi a baya
suka.shige cikin wannan gida.
koda.suka.gama.shiga sai suka gansu a
wani dan karamin daki.
a tsakiyar dakin suka ga wani dan karamin
teburi na.dutsen lu'u lu'u
asamansa an ajiye wata takobi
wacce aka sana'anta ta da zinare
nantake suka karasa da sauri kusa da
takobin suna zuwa sai aljani markazulu yakai
hannu da nufin daukar takobin
koda.ganin haka sai yarimA saiman ya daka
masa tsawa yace
kana.taba wannan takobi zaka kama da wuta
ka kone kurmus
kuma.in baka yardaba sai ka.gwada
tofa.yawu ajikinta ka gani.
kodajin haka sai markazulau ya cika da
mamaki sannan yace da yarina to menene
dalilin haka.
yarima saiman yace ai bakaine ka kashe
shugaban wadannan arnan dajinba nine na
kasheshi.
don haka nine nake da alhakin gadon
abubuwan daya mallaka.
yana gama fadin hakan sai ya je ya dauki
takobin.
faruwar hakan keda wuya sai kogon ya soma
girgiza yana shirin ruguzowa.
nan take su ka juya suka kama hanya cikin
tsala azababben gudu suka nufi hanyar fita
daga kogon.duk inda suka wuce saidai kaga
gini yana zabtarowa kasa.
cikin sa'a suka fice daga fadar ba tare da
wani abu ya sami daya daga cikinsu ba.
suna gama fitowa daga cikinta sai fadar ta
gama rugujewa gaba dayanta sannan ta
nutse a karkashin kasa.
nan take duk su biyun suka tsuguna bisa
kafafunsu suna haki kamar ransu zai fita.
sai da suka shafe yan dakiku suna hutawa
sannan yarima saiman yace yau na wuce
mataki na farkon wanda shine mai mugun
sauki don haka zama bai kamaniba yanzu
zan tashi na.koma cikin jama'ata
kai kuma markazulu sai kaje zan nemeka
nan gaba don indai ina tare da kai mutanena
bazasu taba samun kwanciyar hankaliba..
dajin.haka si markazulu yace nima dama
abinda nake tunani kenan dan uwana
sai an jima.ina yi maka fatan alkairi
yana gam fadin hakan sai ya bace bat
tamkar bai taba wanzuwa ba.
shi kuwa yarima saiman sai busa wani kaho
dake jikinsa.wanda yake kiran dokins.da shi.
kafin cikar yan dakiku saiga dokinsa ya taho
da gudu yana harbin iska.
koda yazo dai dai inda yarima yake sai ya
tsaya chak.
nan take yarima saiman yayi tsalle ya haye
kan dokin
sannan ya sakarwa dokin nasa linzami ya nufi inda yabar jama'arsa
cikin sa'a guda yarima saiman ya isa sansaninsu
koda jama'arsa suka ganshi ya dawo cikin samun nasara sai suka cika da tsananin murna suna shewa daga inda suke
domin basuda damar fitowa daga cikin ragar sihirin da yasaka su aciki
koda ya gama karasowa inda suke saiyaja linzmin dokinsa ya tsaya cak
sannan ya sauka daga kansa yaje gaban wannan ragar sihirin ya shafeta da hannunsa na hagu
nantake ragar ta bace bat
nantake jama'artasa suka kamayin tsallen murna har suna dagashi sama suna yi masa kirari
saida suka dan shafe yan dakiku suna wannan shagali sannan yarima saiman ya daga musu hannu
nantake kuwa wajen yayi tsit kamar mutuwa ta gifta
yarima saiman ya dubi gaba daya mutanensa yace
yaku ahalin birnin ramlatul saif kuyi sani cewa yanzu haka munshafe tsawon kwanaki muna wannan tafiya
alhalin anaso muyi wannan tafiyar acikin watanni goma
don haka ni bansan tsawon lokacin da zamu dauka awannan tafiyaba
saboda haka nake so mu tsawaita tafiya mu rage yada zango don mu isa da wuri
kuma
acikin wannan tafiya inaso idan mun isa bakin wani garin zan shiga na sayo keken doki saboda na baiwa matata cikakken tsaro
saboda duk burin mu gaba daya akanta yake itace nasarar tafiyarmu gaba daya
yanzu inaso mu yada zango awannan wurin zuwa gobe da safe sai muci gaba da tafiya gaba
koda yagama bayaninsa sai ya juya ya dubi shugaban dakarunsa zamnas yayi murmushi yace
yakai zamnas na sani cewa hakika kai kana daga cikin masoyana na gaskiya wadanda suke kokarin sayar da rayuwarsu domin tawa
tabbas ina godiya agareka sosai kuma ka sani daga wannan lokaci kana da damar ganawa dani aduk sanda ka bukata
saidai ina da bukata guda daya awajenka bukatar kuwa itace inaso ka kasance mai kula da bukatar jama'armu fiye da yadda kake kokarin kula da tawa
domin nasan kaima jarumi

Please Login or Register in order to submit comment