Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fini dacen miji a fadin duniyar nan.Saidai kash tun bayan auren mu dashi ban taSa samun kwanciyar hankali a wajen dangin mijina ba kannen sa harma da mahaifiyar shi baki Wayan su suka tsaneni kullin banda bankaWa da tsina ba abinda nike sha a wajen kannen mijina harda wasu daga cikin DANGINMU haka suka shiga suka fita wajen haddasa musiba da bala'i a rayuwar aurena saidai duk abin nan Ya Nizam baisan abinda ake ba saboda aiki da yakeyi a kasar America wannan dalilin yasa mijina baida cikakkar masaniya akan abinda ke faruwa.Akwai wata rana da bazan taSa mantawa da itaba ranar da mijina ya tafi aiki bayan mun dawo daga rakiyar shi muka wuto gidan su,lokacin ina fama da kwaikwan ciki banda lafiya,ina cikin bacci naji surukata ta she™a mani ruwan sanyi a jikina haka ruwan ya zubo mani har cikin kunnuwa na,a firgice natashi duk na ruWe kamar wata zautatta dandanan sanyi ya rufe ni,nakama kyarma mai tsanani,ban aune ba naji kannensa sun hau dukana suna zagi na kamar wata baiwa,daga bisani muryar suruka tace ta maido ni cikin hayyacina jin abinda take cewa."Ke dan uban ki har kinada damar da zaki kwanta ki mike kafa ki a bacci a cikin gidan nan tunda mijin ki ya tafi bake ba wani baccin jin dadi tashi zakiyi ki girka mana abinci sannan ga wanki can naji ranki saura kiyi wankin banza,idan kingama ki tabbatar kin gyarama su Aisha Wakin su kina jina."?jikina na rawa nace."Toh Mommy."munafukar banza munafukar wofi auraka jakar mata."tabbas maganar ta taSaman zuciya amman ban nuna na damuba saboda nasan mutuqar mijina ya koma aiki ina shiga cikin iftila'i har sai ya dawo nike samun sassauci,haka naje nagama aikin data tasani tas,da kyal na samu waje na zauna ga inada karamin ciki bansan kanshin komai,amman a haka na girka masu abincin da zasuci,ranar ban samu na huta ba har saida aka kira magrib sannan na gama komai."
Hawayen da suka ziraro mata tasa hannu ta share taci gaba dacewa."Duk wannan wahalar da nayi bata kareba koda dare yayi kanwar mahaifiya ta, tazo gidan ta iskeni ina shara,jikina na rawa na dukawa na gaida ta,sai ta hau zagina tana tsinata harda duka,cikin kankanin lokaci DANGINMU dangin mu ssukai ta shigowa suna tsinata,mai dungurina nayi mai dukana nayi wasu na ceman shegiya yar iska,kuka nafara ina basu hakuri amatsayin su na 'yan uwana amma basu raga mani ba kuma bansan laifin da mayi masu ba tsabar dukan dana sha ko maganata da kyal take fita ga cikina ya kulle mani kamr zan mutu da kyal na riko hannun surukata nace."Dan Allah kuyi mani hakuri minayi maku kuka tsaneni,kada ku manta nima ´arku ce daga cikin ku nike dan Allah ku yafeman komi nai maku,dan Allah ku faWa mani abinda baku so wlh zan daina na tuba dan Allah kudaina dukana zan mutu...."ban karasa maganar da nike ba naji an wanke ni da marika har sau hudu frgici da azaba yasa ni sakin fitsarin wahala,kafa Fadila tasa ta halbani har saida kaina ya fashe,duk da haka ban fasa basu hakuri ba nagama tsorata da lamarin DANGINMU!har nike7ma kaina tambaya kodai ba daga cikin su aka haife ni ba."Kuka ta kece dashi na mintoci tanajan majina dake neman zubo mata ga jijiyoyin kanta sunyi raWo raWo banda sautin kukan ta ba abinda ke tashi a cikin Kotu saboda kowa yayi tsit dayawan su tausayin ta ya kamasu yayin da wasu kuma kejin haushin ta musamman wasu daga cikin dangin su..."Ke Kotu ke saurare Hajiya Nazima."cewar Barr Nakowa Wago kanta tayi ta daura mashi rinannun idanuwan ta taci gaba da cewa."Ranar wata juma'a ina zaune a Wakin da aka bani a gidan su Ya Nizam wanda baida banbanci da gidan Yari a wajena tunda basu bari in koma gidana idan mijina bai nan basu bari in koma Wakina sai ana gobe zai dawo nike samun yan'ci na har in koma Wakina ina cikin nazarin duniya bansan surukata takirani ba kuma yayar mahaifiya,ashe kirana tayi,tana shigowa tahau yimin masifa dandanan jikina yahau Sari take nafara kuka ina bata hakuri dan nasan yanzun ya'yanta zasuzo su fara dukana,ina cikin bata hakuri naji ta hau dukana da bulala duk yanda naso guduwa nakasa ina mikewa tasa kafa ta taWeni na faWi ruf da ciki wata uwar kara na kwaWa ban kuma sanin inda kaina yake ba,nafi awa hudu a sume,ta kira family doctor ya dubani koda na falko ashe cikin jikina ya zube saida akasa mani drip kwana na hudu sannan na samu kaina."numfashi mai zafi ta fesar tace."Kasan abinda yafi bani mamaki a wannan lokacin Barrister."?
Kallan ta Barrister yayi yace."Aa saikin faWa."numafashi taja taci gaba da cewa."koda Doctor ya gama treatment dina,naso su maidani gidan mu,amma mahaifiya ta tace in zauna wajen iyayen mijina ba yanda na iya haka na zauna dasu a Warare saidai abin dayai bala'in daure mani kai sun daina takuraman suka fara bani kulawa ta musamman,ashe duk kulawar da suke bani ta riya ce,mijina ne zai dawo,ba karamin dadi naji ba tunda Mommy ta sanar mani niketa murna har nafi kowa zakuwar dawowar shi,saboda Mommy bata bari ko waya inyi dashi koda kirana yayi zata amshe wayar ta kasheta,sai taga dama take bani mu gaisa shima ta wayarta,duk ranar da nace mashi banjin dadin jikina ranar sai nasha dukan tsiya shiyasa bani iya fada mashi damuwata saidai inyi shiru,ko abincin bata bani inci in koshi asalima mijina zai bada kudi a dinga sayen abinda nikeso na kwalam kasancewar ina yawan kwaikwai ba komai nikeci ba sai tace ko zan mutu ba zanci abinda nikeso ba asalima saidai su cinye ita da ya'yanta ya zama haramiya ta,abinda surukata ta tsira bata tashi kuntata mani sai taga abinda banso ci ko kamshin sa sai tace sai naci shi koda zan mutu haka taita gallaza min azaba banda dukan yau daban na gobe daban,wannan dalilin yasa zuciyata ta shiga kokonto danaga suna bani kulawa kodan sunyi silar zubewar cikima ne shiyasa suke mani haka oho?ashe saboda mijina zai dawo shiyasa na kasance cikin farin ciki marar misaltuwa ranar ko bacci kasayi nayi washe gari ya dawo naita murnar ganin shi,shima haka sai jindadi yakeyi sai dare muka muntafi gidan mu muka cigaba da zamammu cikeda so da kaunar juna bayan kwana biyu, nafara ganin banbanci a wajen mijina sai yafara kyara ta dandanan na shiga matsananciyar damuwa nafara tambayar shi ko lafiya cikeda fada yace."Miyasa zakiyi mani ganganci da ciki,akan mi ba zaki kulaba har cikina ya zube."?bantaba ganin fushin sa ba kamar ranar na shiga rudani saidai nasan tuggu ne aka hada mani amma bam fada mashi sune silar zubewar cikin nawa ba."kayi hakuri bazan kuma yin ganganci da nayi ba."barin gidan yayi yana fada ko magana ya daina yimin kowa ya haWe mani kai gwara Salma ita ke bani kulawa da hakuri a koda yaushe saita kasance ko hidima ban son ta samu a cikin dangin mu,da an haWu hidima za'a dinga yadamani habaici ana zagina ana musguna mani saidai yan uwana suke shigarmani ko mahaifiya ta saidai tace inyi hakuri da kaddara ta saboda haka DANGINMU suke,saina kara jajircewa abinda taje yawan cemani kenan,haka naita hakuri da rayuwa harna samu kan mijina ya dinga kulani har lokacin komawar shi yayi nayi kuka saboda nasan kwanan zancen,haka ya dinga kwantar min da hankali har na dangana washe gari ya koma wajen aiki a yinin ranar saida Fadila,Nafisa da sauran yan matan familyn mu sukayi mani wulakanci suna kirana da karya wai in rabi da Ya Nizam na nace mashi...kowa da abinda yakeyi banda damar tankasu gudun kada mommy taji labari nasan kashina ya bushe shiuasa bantaba rama abinda suke mani ba,bayan kwana biyu ana sunan diyar Ya Hafiz WanWan kanin Abban mu ne,ana cikin suna ina zaune nida Salma muna fira,bansan hawa bansan sauka ba naji sun watsa mani miya a jiki,duk abin nan agaban dangin mu suka watsamin miyar suka hauni da duka suna cemani"maiya kin samu jar miya sai haWama kikeyi munafuka bake ba Ya Nizam dole sai kinbar gidan shi ni Fadila nice matar Ya Nizam."ta ida maganar tana dungurina a ranar ne DANGINMU suka rabu kashi biyu wasu suka shigar mani aka dinga fada,har Hafsat kanwar mijina ta kamani da rigima bansan sadda nai mata maruka har biyu ba.yayyan mu maza suka raba faWan take tsoro ya kamani hakan yasa naki komawa gidan iyayen mijina ga gidan mijina sun rufe shi kuma key na hannun su, nasan muddin na koma gidan mu zan haWu da fushin mahaifina haka nakama laSe har akai isha'i karshe Isah mai magi ya rakani cikin gida tun a kitchen na hadu da Mommy,tun kan intashi daga du™iyar da nayi na gaida ta tafara duka na a gaban mai gadi,ranar saida sukai mani liqis wai na mari yarta Hafsat ranar ko abinci hanani sukayi haka na kwana ina kuka."tsaigaitawa tayi ta share hawayen fuskar ta tace."shin Barrister ko wannan dalilan bazai sa in nemi takardar saki a wajen mijina ba?ba dole naji ban son shiba?kuma dan nace ban kaunar shi nakishi saboda DANGINMU!nasan ko waWannan hujjojin zasu saa tausayama ni asa mijina ya sakeni."ta ida maganar tana kuka mai tsuma rai,shiko Nizam kamar gawa haka ya keta aikin kallan ta ko motsi ya kasayi tsabar mamaki da firgici. Barrister Nafi'u yace."Hakane saidai a wajen ki yake hujja a wajen mu wannan aiba wani abu bane da zaki tursasa mijin ki ya sake ki duba dashi yan sonki."sake mikewa barister Mukhtar yayi yace."Objection my lord yana da kyau lauyan wanda ake kara ya daina karyama mai kara guiwa dan ta fadi hujjojin ta duba da kalar kalubalen d ta fuskan ta dole ta bukaci saki wajen mijin ta,wannan kamar shiga hurumin shari'a ne da hukuncin Alkali,thank you my lord."Cikeda gamsuwa Alkali ya ce. "Ka kiyaye hakan Barr Nakowa,zaka iya cigaba da aikin ka."thank you my lord,sannan yaba Nazima damar zama banda shu'umin kallo ba abinda suke aikama juna musamman Rukayya shiko Nizam idan shi sunkaWa sai kallan Nazima yakeyi kamar wata bakuwa ta koma mashi,jin kiran da Barrister Nafi'u yai mashi yasa shi dawowa duniyar zahiri daga barin duniyar ruWani a hankali ya tashi yaje gaban Barr ya tsaya."Doctor Nizam kaji abinda matarka tace ko kayarda da abinda ta faWa."?Ajiyar zuciya ya sauke yace."naji komai saidai bazan ce ban yarda ba duba da duk abinda akeyi banda masaniya akai nayi takaicin jin wannan labarin."murmushi Barr yayi yace. "Zaka iya tsakinta kenan."Bazan iya rabuwa da matata ba nidai Allah yasani ina son ta kuma ina iyakar kokarina dan ganin na bata kulawar data dace matsalar dangi daban Barr ni da matata bamu da wata matsala Allah ne shaidana kuma ina sonta."jinjina kai yayi yace."kowama ya shaida haka Dr zaka iya komawa ka zauna."maida kallan sa yay ga Alkali yayi yace."Ya mai girma mai shari'a ko da waWannan hujjar ta Nizamuddeen nasan Kotu zatayi nazari akan abinda yace bai zaune duk abinda ya faru baida labarin shi bare har ya dauki mataki,sannan har mai kara zata samu damar hujjar da zatayi dogaro dashi bare har mijinta ya sake ta,dan haka nasan wannan Kotu mai adalci zata duba wannan hujjojina nagode."

Komawa yayi ya zauna Alqali yace."Barrister Mukhtar ko kanada abin cewai."?.."banda wata tambaya a hankalin yazun saidai ina so Kotu takara mani mako Waya dan sake wani bin cike a kan wannan shari'ar."
Shiru Alkali yayi sai kuma yace."duba da binciken da aka gabatar da yanda akaji daga bakin masu kara da wanda ake kara Kotu ta dage wannan zama nan da kwana bakwai dan kammala binciken da Barrister Mukhtar zaiyi kamar yanda ya buka ta."Buga court stick yayi ya mikeda haka kowa ya tashi saidai kowa da abinda suke cewa wasu najin tausayin Nazima da haka kowa ya kama gaban shi.......

*Sdeendtm*
I'm sell data to all Nigeria network

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I'm
selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp 08066268951
_____________
_Akwai ingantaccan maganin<Ø4ß<Ø4ß gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci=ØOÞ<Øûß_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_


_Yar Mutan Kankia cec'þ_


Share
Pls

*_DANGINMU NE SILAR KOMAI_*

By
_Yar Mutan Kankiac'þ_

*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*

*_BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM_*

Free Page 10

*It's not for free #500 via acct no 0777512438 Access Bank,Jamila Abubakar Bello show ur evidences through this no 08160508316.*

Gidan Nizam ta wuce kai tsaye,dan tasan muddin takoma gidan su kila sai anyi jana'izar ta,musamman yanda tasan dakun da mahaifin ta keyi mata,tana isa ta shige Wakin ta kamar marar lakka tafara rage kayan jikin ta sannan ta shiga bathroom bata tsaya wata wata ba ta sakema kanta ruwa masu masifar sanyi banda sauke ajiyar zuciya ba abinda takeyi a hankali ta fesar da wani irin huci mai zafin gaske daga cikin bakin ta,dafe kanta tayi ji take kamar zai rabe kashi biyu tsabar ciwon da yake mata,tafi karfin minti goma tana abu Waya kafin ta fita daga bath side din,daura towel dinta tayi a sannu take takowa zuwa bedroom dinta ta zauna gefen gado tana sauke ajiyar zuciya ga wani irin kunci daya mamaye mata zuciya tarasa dalilin dayasa tunda suka fara Shari'a ta gaza samun kwanciyar hankali.

A nashi bangaren koda aka taso daga Kotu ya rasa samun kwanciyar hankali kalaman Nazima keta dawo mashi a cikin kwakwalwar shi zuwa kasan zuciyar shi abokin shi Khalil ya shigo dashi cikin gidan shi har zuwa Wakin shi kamar marar lafiya ya zaunar dashi gefen bed a nutse yace."haba Nizam kadaina damun kanka dan Allah."a hankali ya maida duban sa ga Khalil kamar wanda zaiyi magana sai kuma ya dauke kanshi yana rufe idanunsa da sukayi wani irin Ja kamar rushi a hankali ya jinjina bayan shi da kan gado."Dr be a legand mana wannan ba girman ka bane."shiru yayi still baice komai ba a hankali ya bude manyan idanun shi ya azasu kan Khalil yace."bazaka gane bane shiyasa inaga ni kadai nasan kuncin da nike a cikin zuciya ta."cikeda tausayawa ya gyada kanshi ya dafa kafaWar abokin nashi yace."Sorry kadaina damuwa pls."ya hade hannayen shi kafin yace."am go sai munyi waya ko."jinjina kai yayi alamun."toh."da haka ya fita yanajin tausayin Nizam har kasan ranshi. Kanshi ne ke sara mashi kamar ya faWi kasa,tsabar a zaba a hankali ya kwanta ya rufe idansa.
yana saukowa daga side din Nizam daidai corridor ya hadu da Nazima,ita kanta har ta Wan saki kaWan gaisawa sukayi baice mata komai ba ya fita yana maijin haushin ta a zuciyar shi,
a Sangaren Hajia Zaituna tunda su Rukayya suka dawo suka kwashe komai suka faWa mata abinda Nazima ta faWa a Kotu...ai bata bari sun karasa ba ta saSi gyalenta ita da wasu kannen ta suka fisgi mota zuwa gidan Nizam suma su Rukayya maye masu baya sukayi kowa da abinda yake cewa.

Hajia Maryam Buhari mahaifiyar Nazima koda su Amina suka dawo faWa tafara yimasu tana cewa."Ku yanzun bakujin kunya kuke zuwa Kotu sai kace wani abun arziki kuke shukawa in banda mutuwar zuciya kamar Nazima takai mijin ta ™ara a Kotu wai tana son ya saketa dan rashin hankali ku kiyaye haduwa da mahaifin ku wlh zaku sha mamaki,sakarkarun banza ina laifin ku dinga bata hakuri baku dinga zugataba kuna tayata zaman Kotu,ko kun™i ko kunso Nizamuddeen Wana ne kuma jinina ne ta kowane Sangare wlh Khadija baku gajiya da kayan kunya mtsw."Cikin sanyin murya Amina tace."Haba Umma taya zamu saka ido ana cin zarafin ´ar uwar mu,ba dalili kinsan halin Inna Zaituna basu da ragi ko kaWan,kuma Ummi so kike ciwon zuciya ya kashe mana ´ar uwa."a fusace Ummi tace."Dallah yimin shiru indai kunsan kunya kun santa ace kuna yan uwa DANGIN KU Waya amman kuna shashanci wlh kuji tsoran Allah zumunci ba abin wulakantarwa bane, ku Saceman dagani ko in saSama maku."haka kowa ya tashi yayi Waki cikin bacin rai,itako takaicin ya'yan ta ya kashe ta.

Koda Nazima ta fito falo takasa ko zama tunda taga Khalil ya kawo Ya Nizam ta tabbata baida lafiya tun a Kotu ta fahimci bayajin dadi ita kanta tasan bata kyauta ma Ya Nizam ba saidai bata da zaSi da ya wuce su rabu,tana zaune tayi nisa cikin tunani kawai taji anshe™a mata wani wulakantaccen mari sadda zata maida kallan ta ga mai marinta taji ansake zabga mata wani marin daga idon da zatayi taga Hajia Zaituna da Hajia Na'ima da ´an tawagar su,take gaban Nazima yai mugun faWi tsabar kaWuwa,daka mata tsawa Momy tayi tace. Ke karamar yar iska har kin isa kije Kotu kina mani tonan siriri da kika faWawa Alkali nice silar da cikinki zubewa ince cikin na Wana ne,kuma da cikin da mai cikin ai duk mallakina ne,dan haka yau din nan basai gobe ba ni Zaituna Buhari nace ki tattatara kayanki ki tafi gidan uban ki Abdulhamid tunda nan ba gidan uban ki bane."
Cikin kaWuwa Nazima tace."Momy dan Allah kiyi hakuri wlh bawai dan in maki talla na faWi haka ba dan in samu mijina ya sake ni dan Allah kiyi hakuri.....ai tun kan ta ida Hajia Na'ima ta Waura mata nata marin saida ta kwalla kara can cikin bacci Nizam yaji ihun matar shi jikin shi na Sari ya tashi ya afka bedroom din ta har toilet bai ganta ba da gudu ya sakko falon ™asa itama Goggo mai aiki falo tayo da gudu daga kitchen tasa wani abun ya samu Nazima saidai cikeda mamaki tayi turus ganin Hajia Zaituna da yan uwanta,shiko Nizam har tuntuSe yakeyi yana isowa falo bai kallan ko gaban shi ya rungume Nazima a jikin shi yana tambayar ta ko lfy, har sun bugar mata ido yayi jajir kamar jini kuma ya fara kumburi,magana yafara a kiWime."Heart beat dan Allah karki min haka miyasameki naga idon ki haka Ummin Sadiq ki bude idon ki mana fadaman minene kidaina kuka dan Allah konji matata ki..."Jiyayi an ingije shi tunkan yakai ayar zancen shi,a fusace ya mike zaiyi magana sai yaga Momyn shi da dangin ta sai sauran kannen sa,ai maganar da baiba kenan riko hannun Momy yayi yace."Momy dan Allah kitaimaka mani Ummin Sadiq bata lafiya dan Allah....a fusace ta fisge hannun tace."Sakar mani hannu sakarai wawa dakai akan wannan gantalallar yarinyar zaka dinga rawar jiki kamar wani karamin yaro,bayan taje kotu a gaban dubban jama'a tana aibata uwar ka da dangin ka amman ka kasa rabuwa da ita dan asara to wlh muddin nice uwarka ni Zaituna ya zama dole a zama na gaba ka saki wannan almurar yarinyar tunda ba uwar ka bace."dukawa yayi ya rike kafar ta yafara hawaye yana magiya."Momy dan Allah karki min haka wlh ina son matata dan Allah,wlh ina kaunar Nazma Momy."da yatsa ta nuna shi tace."Idan ka ™ara cewa kana son wannan yarinyar a halin yanzun wlh saina tsinemaka albarka,uban kowama ya huta kuma yanzun nan wannan almurar yarinyar sai tabar gidan nan inyaso daga baya idan an koma Kotu kabita da takardar ta gaban Alkali kamar yanda takaika can din, ina anfanin wannan zuri'yar ina bakin cikin ace ni Zaituna wai uwar wannan gantalallar Wiyar uban mu daya da ita...na fada maka ya zama dole ka saki wannan tsinanar yarinyar."
Tunda yaji mahaifiyar shi tace zata tsine mashi bai sake magana ba ba abinda yakara Waga mashi hankali da yaji tace saiya saketa sannan yau zata bar gidan shi take wani irin zazzaSi mai zafin gaske ya rufe shi sai kyarma yakeyi a gaban idon shi suka cigaba da dukan Nazima suna dungurin ta sai tsine mata sukeyi harda su Fadila da sauran kannen shi take yaji yakara tsanar Fadila a cikin zuciyar shi,itako Goggo kwalla sun cika mata ido da sauri takoma kitchen sai kuka takeyi,danko Nazima duk jini ya wanke mata fuska takasa ko magana sai ido danko fuskar ta harta kumbura,cigaba da magana Hajia Zaituna tayi."Maza ku fiddoman kayan shegiyar,makira mai hali irin na uwar ta yau saikin bar gidan Wana ba yanda za'ayi ace kina karar Wana sannan ki mike ™afa a gidan sa." haka su Fadila da Aisha suka dinga wurgi da kayan Nazima ko cikin akwati basu saka ba, danko Nizam kwalla kawai yaji sun zubo mashi yana san yai magana yana shakkar tsinuwar uwa,magana Nazima tayi cikeda karfin hali,tana kirkirar murmushi akan fuskar tace."Momy dan Allah ina neman alfarma a wajen ku,ku taimaka ku yafeman abinda nayi maku sannan dan Allah ina san ku ´anta ni cikin DANGINMU ko sau dayane kitai makeni nima in zama cikakkiyar ´a kamar kowa kune dangin mahaifiya fa Mommy dan Allah kitaimake ni konasan daWin dangina karku rabani da DANGINMU kada kusa in zama mujiya a cikin ku,koba komai daga jikin ku nike sannan zanyi komai dan farin cikin ku,zan rabu da Ya Nizam idan har zan samu ´anci awajen ku nima ince kune dangina ba tare da naji shakkar fadar hakaba na rokeku kudaina tsana ta,ku yafeman laifi na agareku Momy."wani irin bakin ciki ya tokare zuciyar Zaituna batasan sadda tasa ™afa ta halba Nazima ba...."Ke ga munafuka ko?wai dan muji tausanki ko?indai kalar wannan mugun halin nakine munsaba dashi yar gadan gado tun akan kakar ki Amina,muguwa dake mai muguwar aniya kika sake yiman wata magana yanzun nan zan saka kafa in sake halbaki sai inga daga ke har mijin naki da duk wani mai goyan bayan ki waya isa ya tanka,auraka jakar mata....dai-dai Salma ta shigo hannun ta rike da Sadiq Wan kimamin shekara biyar aduniya kyakkyawa ne yana kama da mahaifin shi kwabo da kwabo suna shigowa dda gudu ya faWa saman Nazima yace."Ummina mi'akai maki idon ki yayi jini?cikeda damuwa yayi maganar kamar zaiyi kuka Murmushin karfin hali Nazima tayi tana jin kewar Wanta nata sosai a cikin zuciyar ta yayin da son shi ke kara ratsa mata kowane sako da lungu na jikinta tace. "Bakomai Sadiq..."da karfi Mommy ta fincike shi daga Jikin Nazima ta mikama Hafsat shi,sannan tasha hannu ta dunguri Nazima tace."Wato har kinsamu damar taSa Sadiq ko?kega makwakwaciya kijini da kyau bake bashi har abada saidai kallo daga nesa wato so kike ki goga mashi kashin tsiya ko?kika kuma tabamin Wa saina illataki."banda kuka ba abinda Sadiq keyi yana kiran Ummi...itama hawaye takeyi marassa sauti kanta duke a™asa, haka Hajia Zaituna tasa aka fara kwasar kayan Nazma za'a fita dasu waje, Na'ima ce ta dafa kafadar Mommy tace.....


Sorry for night update abubuwa sukaimin yawa kuyi manage da wannan....ina karaba da hakuri akan rashin update na Izzah ko Mulki insha Allah zaku dinga samun posting thanks>ØpÝ

*Sdeendtm*
I'm sell data to all Nigeria network

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I'm
selling MTN data with

Please Login or Register in order to submit comment