Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kwaWa wanda ya dawo da kowa duniyar dimauta da razana kamar zautatta tafara ruwan bala'i bakataba cewa uta aka saki."Alhaji Buhari ka saka da tsufana zaka wulakantani ni face uwar ´a´an ka!kuma kada kamanta nifa jinin kace Buhari...Bakomai kasa a ranka matukar na haihu ga jinin Maimuna sai kaga musiba da bala'i saidai idan ban amsa sunana indo ba wlh Buhari dani kake zancen kuma ba inda zanje nida barin gidan ka saidai idan gawata aka fidda inanan zama daram nida kai mutu karaba wlh."Kallo Waya Alhaji yai mata ya kauda kai bai kuma cewa komai...banda hakurin dasu Dady sukaita bashi dakatar dasu yayi ta hanyar Waga mashi hannu."duk wanda ya kuma magana a cikin ku sai ya gamu da fushina,dafatan fahimta."Allah ya huci zuciyar ka."Da haka Alhaji ya koma part dinshi
"Yanzun Alhaji nizaka cima mutunci ni zakasa akama Buhari ni zaka tozarta na shiga ukkuna ni Aisha."ko kullata baiba ya rufo kofa haka aka tisa keyar Hajjo aka tafi dasu police lamarin ba dadi.
Ummi taje wajen Hajja suka gaisa tace."Umma dan Allah kine mana alfarma wajen Abba yataimaka yasa a fiddo su Hajjo."da mamaki Hajja ke kallan Ummi tace."Hmm Maryam kenan keko mizaisa kidamu da wa'anda ke farautar rayuwar mahaifiyar ki,yanzun inda da karan kwana mi kike tunanin zai faru?nidai bazan jeba."marairaicewa Ummi tayi tace."Hajja dan Allah kije wajen Abba nasan insha Allah zai yarda da maganar ki kada mubiye ahinda suke mana mu sakanta masu da alkhairi kuma kinga yan uwana ne."shikenan Maryam zanje."nagode Umma."da gaka Ummi ta tafi..Hajja ta amince ne saboda tana ganin Ummi da mutunci... a marece taje wajen Alhaji Kabir Maikaba ta faWa mashi halin da ake ciki..kanine ga Alhaji Buhari saidai bai taba haihuwa ba...."dan haka shine nazo dan in sanar maka halin da ake ciki."numfasawa yayi yace."Hajiya Hafsat kenan saidai kace bakisan wacece Hajiya Indo ba ki kyaleta akoya mata hankali."Haba Kabiru miyasa zakace haka ko saboda ya'yan ai anfitar da ita ga mahaifin su ya zuciya yace duk wanda yaje belin ta saiya hadu da bacin ran shi."kedai ki rabu dasu matar nan bata da ragi ko kadan jiba kiga yanda ya'yan ta suka zama hatsabiban gaske a cikin zuriyar mu sun addabi kowa nidai bazan shiga shirgin su ba."shiru Hajja tayi kowa ya nitsa a sakar zuci tace."ka dubi girman Allah da darajar zumunta Alhaji Kabir."shikenan tunda kince Allah magana ta kare muje wajen yayan...da haka sukaje part din Alhaji suna gaisa a mutunce Alhaji Kabir yace."yaya nasan zakayi mamakin ganin mu a wannan lokacin dama munzo neman alfarma awajen ka."dakata Kabir idan har kasan maganar indo zakaimin kada kufara ku tashi ku tafi."Haba Yaya taya zaka ce haka kana uba kuma zaka dauki zafi karfa ka manta kai ubane kuma akwai ya'yan ka a cikin wannan case idan kayo fushi dasu mi kake tunani."wannan dalilin zaisa na manta dasu bansan cin amana ace da ya'yana za'a ha'ince ni."Alhaji kayi hakuri tabbas ba dadi amma haka Allah yaso sai atari gaba kayafe masu."cewar Hajja."yaya ka dubi girman Allah kasa a sake su kayafe masu."shiru Alhaji yayi kamar mai nazari yace."Naji aje a sako su amma banda Hajia indo."taya za'a sako ya'ya abar uwar su a rufe haba Alhaji ai ko mutuwa nada kara tsakanin Wa d mahaifi kaimata kara mana."ajiyar zuciya ya sauke yace."naji amma kuja mata kunne kada ta kuskura ta dawo gidana."wannan karan ba karamin mataki ya daukarma fuskar shi ba dab dole sukayi shiru sannan sukai mashi godiya suka tafi....koda Hajja ta dawo gida sawa tayi aka kira mata Ummi ta faWa mata Alhaji ya yarda bakaramin dadi taji ba."nagode Umma Allah yasaka da alkhairi."ameen Maryama."tashi Ummi tayi zata tafi Hajja tace."koma ki zauna."zaunawa tayi Hajja tace."ki kara hakuri da dangin ki Maryama insha Allah bazaki taba ganin tawaya ba keda zuriyar ki."insha Allah Umma zanyi iya yina dan hakuri da yan uwana."Allah yai maki albarki jeki."ameen."da haka Ummi ta tafi....itako Hajiya tana gidan Baba Gambo ana bata kulawa Alhamdulillah jikin ta yai kyau sosai kamar ba ita ba Dady yasa aka gyara mata sashen ta ya saka mata sabbin kayan Waki da dukkan kayan bukata tana kara kara hutawa Baba Gambo ya maidata part dinta.

Bayan kwana ukku Alhaji ya haWa matan sa a falorn shi saida kowa ta hallara yace."Daga yau na datse wannan bakin kishin na kafurci a cikin gidana kuma duk wadda ta nemi raba kan ´a´ana saita gamu da fushi gwara tun wuri ku zauna lafiya da junan ku."insha Allah zamu kiyaye."da kun kyau ta.Da rana aka dawo da su Mommy gida kana ganin su kasan sun jigatu saidai duk yanda Alhaji Buhari yaja kunnen Hajia indo saida ta dawo gidan suna isowa ta bude part dinta ta shiga su Mommy suka biya suka gaishe da mahaifin su."kowa ya koma dakin mijin shi ke kuma Zaituna sai kisan yanda zakiyi tunda mugun halin ki yasa kin gaza zama gidan mijin ki sai kibi uwarki ku karata."kayi hakuri Abba natuba."dakata badai a gidana ba ban haifi yar da zataimin zaman yaji ba batreda kwakkwaran dalili ba maza ku bacemin dagani."yaya ka dauki lamarin nan da sauki kabar mahaifiyar yaran nan ta zauna tunda kaga tusfa ya kamata itama Zaituna ka barta daga baya sai Abubakar yazo ya maida matar shi."a fusace Alhaji ya mike yace."wato saida kadawo da Indo cikin gidana ko Kabir duk yanda na gargade ka."fuuuuh Alhaji ya fita zuwa sashen indo ya isketa zaune yace."ban fada maki ba kada kidowa gidana ba?tashi kifita."kamar wata sakarai haka Hajjo ke kallan Alhaji duk mamako da tsoro ya gama kasheta ba abinda dake daga mata hankali yanda Alhaji ya saketa da tarin shekarun ta na tsufa banda surukai da tarin jikokin da rabi da kwatar su duk suna ma'auri..tace."Karyane Buhari ba ind zanje zama daram duk tarin shekaru baka sakeni ba said na zama tsohuwa da tarin surukan nawa banda jikoki shine zaka cimani mutunci tsofai tsofai dani ya'yana goma sha biyu dakai Buhari gayaman wake gabana a cikin su shine zaka wulakanta kuma duk akan matar ka wato ga shafaffa da mai ko."?..."komi zaki ce saidai kice Indo bazan iya zama da wadda ke neman rayuwar iyalina ba nagama magana dole sai kinbar gidan nan."kuka Hajjo ta kece dashi tace."Allah ba inda zani."Abba kayi hakuri ko darajar mu ai Umma taci ko."?..."kaga Iliyasu bafa zan zauna da ita."Haba Abba mahaifiyar mu ce fa akan mi bazakai mana karaba kodan mu yanzun ya kake so muyi,ace uwar mu na zawarci tsofai tsofai da ita..."ya isheka Iliyasu wannan kuma ya rage naku."gaskia wannan ba adalci ba ne daman mun jima da sanin ba son mu ake ba muda uwar mu."cewar Mujahid...ranar karki so kiga kalar bala'in da akayi da Alhaji ya rufe ido dole sai Hajjo tabar masa gida.Hakama ya'yan ta kowa sai rashin Wa'a yakeyi rai ya baci,da ace Alhaji ya biyema zuciya tabbas a ranar sai yaima Alhaji Iliyasu da Mujahid baki...daman sune manyan ´a´an shi.
ba abinda suke cewa...ba inda mahaifiyar su zataje zaman su zatayi,hakan ba karamin Satama Alhaji Buhari rai yai ba ranar har saida ya mari Baba Mujahid sannan yace matukar ya sake magana sai ya barrantashi a cikin ya'yan sa.Banda kuka ba abinda su Momy.dan dole Alhaji Iliyasu ya tafi da hajjo gidan sa.
Bayan kamar sati da rigimar su Hajja suka kara zuwa bawa Alhaji hakuri amma fir yaki amincewa har saida Ummi tazo taba mahaifin nasu hakuri tana kuka ta rike kafar Alhaji tace."Dan Allah Abba kayi hakuri kayafema ´an uwana."banda aikin kallan Ummi ba abinda yakeyi taci gaba da cewa."Abba kace kafemasu sannan kabar Umma ta zauna damu."Murmushi kawai yayi ya tallabo fuskar Ummi sannan Wagota ya zaunar da ita gefen shiyace."Daina kuka ´ar albarka,nayafe maku baki Waya keda dangin ki, sannan zanbar Hajia indo ta zauna gidan nan saboda ke saidai inada sharadina."Abba minene."? "Bari insa akira mani Indo ita zan fadamawa."waya ya ciro ya kira Alhaji Iliyasu yana gamawa ya kashe kiran ya maida duban sa ga Ummi yace."kidaina kuka Maryama."cikin kankanin lokaci suka iso kowa ya zauna Alhaji yace."nasa akira mani ku saboda alfarmar da Maryam ta nema awajena akan na yafe maku sannan na maido da uwarku,kujini da kyau na aminta da zauna gidana badan kowa ba sai saboda Maryam...sannan vata damar cigaba da zama gidana bashi ke nuna shi nuna ta dinga shiga sabgar iyalaina bata ba shiga harkar matana kamar yanda kukaji nace na saketa kowa ya zama shaida."shikenan naji na amince."tace a susuce da kyal Alhaji Iliyasu yace ma Ummi sungode....danko su Hajia Na'ima kallan banza suke aikama Ummi mai dauke da tsantsar tsanar ta da haka Alhaji ya sallami kowa ya kama gaban shi amma su Mommy habaici kawai suke ma Hajia amman bata tanka suba acewar ta,ta gaji da fitina kuma tayi alkawali bazata kara tanka Hajia Aisha da haka kowa ya tafi sashen shi,ranar kamar anyi mutuwa a cikin family din mu duk wanda kagani sukuku.....

More information contact this number 08160508316 kada kiyimin magana idan ba siya zakiyi ba
_____________
_Akwai ingantaccan maganin<Ø4ß<Ø4ß gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci=ØOÞ<Øûß_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
&&&
*Sdeendtm*
I'm sell data to all Nigeria network

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I'm
selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp 08066268951
____________
_MT COLLECTIONS<Ø?ß&þ_
_Ina kuke mata ´an ™walisa masu son ado na kece raini kiji next year Alhaji yayi mai kyautar ´ar moton nan ko yace Hajiya na biya Maki kujerar Hajj ,nan dai ko wa ke fatan yagan sa yaje Kuzo ga kayan gyarar Aure daga taskar mu MT, matsalar ki yamushewar jiki , rashin ™iba kema so kike duk inda kika je ace ga Hajiya tazo ku bata wuri , ko matsalar infection ke damunki , rashin ™arfin Wa namiji saurin gajiyawa ke Kuzo akwai ingantattun kayan mata dana gyara Suplement wanda zai gyaraki kiyi caras abunki , idan ™iba ne tayi maki yawa kisha kiga kin koma dai dai Waukar oga>Ø‹Ý=ØGÜ ._
_Infection na buda gaban mace taciki yabar wajen a tsuke a matse kullum kina zaune kina cewa kefa a matse kike alhalin Mai gidan hkr yake<ØÃß<Øûß
@&þ_

_Ina macen da batada shaawa kwatakwata ke bakijin feeling toh wlh kixo Kisha infection set dinmu Dan girman Allah inkinsha kitafasa ma oga infection flusher kibashi ya subhanalillahi Ranan kam saidai kukawomun yarana ajiya in ana sallah baa magana daga wanan ranan zakisa mene ne wanga Abu kenufi kinji_

_Infection nasa ruwa agaban mace tsinkakken ruwa Wanda shi Sam baida yauki toh wanan fa ba ruwan niima ba ne ruwan niima shine Mai yauki hajaju kizo Kisha infection set kirabu da sharrin infection Dan Allah_

_infection set dinmu zai wanke miki Mara zai share yakwashe duk wani sanyi na jiki dana mara_
_ina mai famada ciwon Mara mai tsanani lokacin alada zokisha toilet infection dinmu wannan ciwon yazama tarihi.._
_Ba'anan Mt collections ta tsaya ba , muna sai da liquid soap mayuka na haWi , turaruka ,shu'umin humra , colecture shampoo conditioner da dai sauran su ...mayukan Suplement wanda zasu dawo maki da martaban fatar jikin ki yasa jikin ki tayi sumul kiga fata na she™i yana glowing ,kar ku manta ku biyo mu a shafikan mu na=ØGÜ_
_INSTAGRAM#MT COLLECTIONS_
_FACEBOOK #MT COLLECTIONS_
_WHATSAPP>Ø€Þ 08081202932_
CALL&þ _09060703187_
_Muna bada sarin kayan mu a ko'ina Waya ko sari... Zaku samu shagonmu a nan cikin garin Zaria City babban dodo benen Yahya AminuMT COLLECTIONS 015_
_MT COLLECTIONS TAKU CE&þ_


_Yar Mutan Kankia cec'þ_


*_DANGINMU NE SILAR KOMAI_*

By
Yar Mutan Kankiac'þ

*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*

*_BISSMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM_*

Free Page 19
*Na kudi ne akan farashi mai sauki for more information contact this no 08160508316.Acct details 0777512438 Access Bank,Jamila Abubakar Bello*

"In ta™aice maki Nabila, bamu kara samun sukuni a cikin family din muba...danko Hajjo ta kwantar da kanta kamar komai ya wuce ko motsin ta ba aji a gidan Alhaji Buhari,ashe ba'a ga komai ba sai wasan ya koma a wajen ´a´an ta,su suka zama karfen kafa a cikin familyn Alhaji Buhari har zuwa yanzun musamman Hajia Zaituna itace shugabar su, koda suka raka Hajjo part dinta ba yanda Momy batayi ba dan takoma gidan ta amman Dady ya™i yace badai gidan shiba tunda har zata iya kisa kan...shi bazai iya zama da ita ba ranar munga ikon Allah baki Wayan su suka tiso Daddy gaba saida yai masu wankin babban bargo da sukaga lamarin yafi karfin su sai suka saka mashi ido tunda yaki maidata...Familyn mu na bala'in shakkun Daddy baida wasa koda sukaga yaki basu hadin kai sai ta tafi wajen Hajja ta faW mata halin da ake ciki sannan su Baba Iliyasu suka kai karar Daddy wajen Alhaji Kabir a cikin daren yakira Dady koda yaje bai mashi wata magana ba sai bashi umurnin tafiya da matar shi gidan da yayi ba yanda Daddy zaiyi kuma bazai iya musu da kanin mahaifin shi ba...kuma abun mamaki uban su Waya da Alhaji Buhari amman kansu haWe yake basu ´an ubanci da junan su...ainahin ´an ubancin danginmu daga gidan Alhaji Buhari yake kuma Hajia Aisha itace asalin haddasa shi saboda kiyayyar da takema Hajia Amina duk kakannin su Waya baki Wayan su daga tsatsan Maikaba zuka fito kinji ainahin kiyayyar su Ummi ba komai bane ya haddasa sai tsantsar yan ubancin dake tsakanin su duk dasu Mommy sune manyan ´a´an Alhaji Buhari sai yan Wakin su Ummi....Umurnin tafiya Alhaji Kabir yai masu sannan sukai mashi sallama suka tafi koda Momy ta dawi Wakin ta, amman Daddy bai kulata,sunan ta dawo gidan ta....Shima Abba ba karamin tsauri yasama Ummi ba ko fita bai bari tayi koda kuwa gurin Hajja ne,haka rayuwa ta kasance ba wata jituwa a tsakanin iyayen mu.....Nauyayyar ajiyar zuciya ta shide tace."kinga Kawata idan muka biye wannan firar zakiyi dare dan ba karewa zatayi ba nasan Mum najiranki a gida."da sauri Nabila tace "Aaa sis ki idamani after magrib sai in tafi."shikennan."cewar Nazima tacigaba da cewa."Bayan rigimar datafaru tsakanin su Ummi bada jimawaba sai du Ya Nizam suka shirya zasu tafi Masters din kasar Holland tunda suka fara shiri Ummi ta gaza zama sai haWama su Ya Nizam kaya takeyi haka ta gama hada masu kayan bukatata basu,tunda suka fara shiri nike wasa boyo da Ya Nizam ko a hanya bani bari mu hadu,Washe gari da safe kowa ya fito a compound din main house dinmu.an fiddo motoci na alfarma zasu rakasu Air port...Abba yace in shirya dani za'ayi rakiyar nace masa ban lafiya bazan samu damar zuwaba Daddy yace a kyaleni tunda banjin dadi duk da yanayin Ya Nizam ya nuna bai aminta da magana taba da haka kowa ya fito rakiya bandani,zama nayi falo hankalina kwance ina kallona baki daya na maida hankali a tv ina watching film din Bagusery ban ankaraba naji an rike mani hannu bakaramin tsorata nayi ba waigowar da zanyi naga Ya Nizam ya sakar mani murmushin daya kara kawata kyawun shi murguWa mashi baki nayi yace."Shine kikace baki lafiya ko."?.."eh mana ba gashi kagani ba."jaman hanci yayi ya murda har saida na saki yar kara nace."Ya Nizam da zafi fah."okay dan kada kiyiman rakiya shine kike pretending?wai miyasa kike da rikon abu na fahimci baki son yayan naki yanzun kowa nabani gift amman ke bazaki bani komai ba kuma ba zakiman rakiya ba."?wurga mashi harara nayi nace."banda komai nimi zan baka."da abinda zaki bani mana."banda shi fa."okay naji."yanzun dai mi zaki fadaman ko baki son na dinga tuna ki."kallan kyakkyawar fuskar ki nayi nace."Allah ya tsare banya yasa kudawo lafiya."murmushi ya sakar man yace."good zanyi missing rashin jin nan naki kanwata."sake murguda mashi baki nayi nace."nikam dai ba zanyi wani missing dinka ba."hararar wasa yai mani yace."good wato wannan dan karamin bakin naki bazai daina rashin kunya ba ko."?da zafi ya nizam ka daina."nace ina shafa bakina daya murda man."na lura idan na biye rashin jin nan naki sai Daddy yaimin fada bari in tafi take care of ur self kinji."gyada mashi kai nayi nace."okay Allah ya tsare."fiddo wani irin hadaddan zobe yayi ya sakaman a yatsana yace."ki rike alkawali."kallan sa kawai nike nagaza furta komai sannan ya fiddo na babban yatsana ya sashi a karamin ya tsanshi yace."Kinga wannan zoben bazan bari ya taba Sacewa ba kema karkiba kowa naki kinji."saina samu kaina da gyaWa mashi kai haka yaiman peck a goshi tareda rike hannuna....maganar Ummi mukaji da sauri ya sakeni yana waving dina suka tafi ya shiga mota ni kuma zamana saina samu kaina da kewar Ya Nizam da tafi musamman da dare yayi sai kewar shi takara cika raina daga bisani na manta da babin shi a zuciya ta daman can zalina yakeci kinji tafiyar su Ya Nizam karatu ni kuma alokacin ina Dr Halima Memorial School JS3."
Jinjina kai Nabila tayi tace."Ya kuka kare kedasu Anty Fadila a makaranta bayan tafiyar Ya Nizam."Hmmm kawata kenan kedai bari kawai ba karamin wahalar ta nasha ba har banson tunawa."kai gaskia anty Fadila bata da imani wlh."Hmm haka take,kibari zan ida baki wannan labarin kuma kinga next week zamuci gaba da zaman kotu idan zan tafi zan maki text...a can zaki idajin cikakkan bayi kawata nidai so nike kawai mijina ya sakeni"iskar bakin ta ta fesar tace."shikenan kawata Allah yakaimu lfy saidai ki kara kulawa sosai."gyada mata kai tayi zatayi magana sukaji shigowar Nizam a falo suna fira da Hajja."kai sai yanzun nike ganin ka Nizamuddeen."?.."kinji dalilin dayasa bana zuwa yanzun zaki fara faWan nan naki."oh nice mai fadan kenan ko."?"ai kinji matsalar yanzun mi kikeyi,kinga tsohuwa ina matata."ban sani ba aida yake ajiya kabani."kwarai kuwa ke nasani na iyalina."Wan nema Allah ya shiryeka yanzun dai tana daki kadawo ka sameni ehe."dariya kawai yai nata ya wuce jin hakan yasa Nabila Waukar handbag dinta tace."kawata zan wuce ga mijin ki yazo."okay."Nazima taimata rakiya zuwa falo nan suka haWe da Nizam ya tunkaro da™in,Nabila tagaida shi sannan ta tafi...kafe Nazima yayi da wani irin kallo mai dauke da ma'anoni yai mata ta juya yabi bayan ta zuwa daki samun waje tayi ta zauna kamar wadda akaima dole ta gaida shi.Cikin jin dadi ya amsa duk da fuskar ta ba walwala a cikin ta,tashi yayi ya zaune gefen gado ya rike hannayen ta cikeda kulawa ya kalleta cikin tausasawar murya yace."Heart beattt."ya kiran sunan ta a sayaye.Yanda ya kira sunan ta saida yasa gaban ta yafaWi,a hankali ta Waura mashi manyan idanun ta masu ruWar da shi."Ummin Sadiq kitaimakeni kidawo gareni nayi iya kokarina dan naga naba zuciyata hakuri nagaza bazan iyadangana da rashin ki ba Nazma,inajin zan iya rasa raina matukar kika rabu dani matata kema kinsan ina sonki so na ha™i™a ke tawace kamar yand nike naki miyasa zaki manta da alkawali.''?
Runtse idanun ta tayi tanajin maganar Ya Nizam har cikin ™o™on zuciyar ta saidai a halin da take ciki batajin zata iya kasancewa dashi,kodan tsira da rayuwar ta.Sautin muryasa taji daidai saitin kunnan ta."Nazma na rokeki kitausaya mani."cigaba da murza hannunta yayi a hankali,yayin da idanun su ke sarke dana juna kowa da abinda yaje sakawa a rai tace."Ya Nizam kaima kasan ina son ka saidai bazan iya daukar kalubalen danginmu ba,dan Allah kabar wannan maganar saboda banda zaSin da ya wuce in rabu dakai kodan intsira da mutunci na."Mamaki ya gama bayyana a saman fuskar Nizam cikeda tuhuma yake kallan fuskar ta yace."Heart beat kifadaman minene hujjarki na neman saki a gareni bayan kinsan kece farin cikina."?Mikewa tayi a hankali ta tafi wajen madubi tana kallan shi ta cikin mirrow tace."Ya Nizam bazakaji daliliba sai nan gaba kuma kasan yanda na zauna dakai kana sona ina sonka shin a lokacin meya hana bakai tunanin miyasa na sonka ba ya sai yanzun dan nace kasake ni zakayi mamaki.? Ko saboda Mommy na ™ika Ya Nizam a gaban idonka minene baka gani ba."iskar bakin shi ya fesar yace."hakane amma ki aje zance Mommy kodan son da nike maki ki rayu dani komai wuya komai dadi kinjin Ummin Sadiq."girgiza kanta tayi tace."i can't bazan iya zama inuwar da ba a bukatata ba."wani irin kukan kura Nizam yayi ya sha™o Nazima kamar wani mai jinnu jikin shi har wani rawa yake ga idanuwan sa sunyi wani jajir kamar garwashi banda huci da yakeyi kamar wani zaki.Yanda Nazima taga yanayin shi ya sauya take jikin ta ya dauki kyarma tagaza ko kwakkwaran motsi yanda ya shake ta...da ™a™™ausar murya yace."zan iya halakaki Nazma ni zaki dinga cema baki so?zan halaka ki nima in halaka kaina kowa ya huta, da inrabu dake wani ha aura na gwammaci in halaki da kaina kowa ya rasa,kuma ina sonki ina sonki ina sonki na kuma faWa maki sannan ina kaunarki kuma bazan taSa rabuwa dake ba kwara kibar wannan maganar tunda wuri,koda zaki kaini Kotun ™olin duniya bazan yarda in rabu dake ba ki aje wannan a ranki."Hawaye masu zafi suka samu damar ziroro mata sannan ya sake ta yana fesar da iska mai zafin gaske....Duk idanunta sun sauya tsoro yakara kamata dan gani take kamar bashi kadai ne ba yanda taga Ya Nizam ya rikice ciki kankanin tari tafara ba kakkautawa da kyal ta saita kanta tace "Ya Nizam mike damunka dan Allah kadawo hayyacin ka kaima kasan hakanan bazan ce zanr abu da kaiba inada dalilina kaima kasani kafahimce ni mana.""Bazan fahimce kiba Nazma daman duk kiyayyar da kikeman baki daina ba kenan duk yanda na soki iyeh akan sonki na rasa duk farin cikina akan narayu dake nasara sukunina duk akanki nazama wani sauna shashasha saboda ke na zama sakarai duk akan son da nikr maki....alhali ba abinda Allah ya rageni dashi kyau,kuWi ko mulki uea uba lafiya ki faWaman mina rasa da kika tsaneni."? ya daka mata tsawar data kara kada mata yan cikin ta har saida ta runtse idanun ta duk jikin ya rikice da mazari."tambayar ki nake ki faWamani?ko son da nike maki na karya ne."? batasan sanda ta zube bisa guiwar taba ta rike hannayen sa tace."Ya Nizam ba abinda Allah ya rageka dashi kana da komai kuma ina sonka saidai kasani ban tsaneka dan ban kaunar ka ba sai saboda danginmu kuma yan uwanka basu son tarayyar mu akanka sunce zasu kashe ni dan Allah Ya Nizam karabu dani na rokeka."wani irin watsa mata rinannun idanun shi yayi kamar rushi yace."Dangi?dangin banza da wofi akan su zaki dinga ikirarin kin tsane tell me miyasa kika tsaneni dame na rage ki."?mikewa tayi tafara ja da baya ta rufe bakinta da hannun ta da gudu ta faWa toilet ta saka key ta jinjina da bayan ta jikin kofa ta rushe da kuka mai cin rai...shiko kamar gunki ya kasa motsi tsabar tsorata da firgicin kalaman da yaji Nazima ta furta mashi me take nufi da zasu iya Kasheta!wani irin zufa ya tsatsufo masa

Please Login or Register in order to submit comment