Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanyi kuma da alamu su yake son insaka.Zira wandon nayi nagaza saka rigar mai hannun igiya ce,fitowa yayi ya iso gabana yana tsane jikin shi ya dauki jallabiya yasa ya sauwa boxes inajin yana shafa turare harya gama ya kuma dawowa wajena ya anshi rigar da kanshi ya zira mani nidai ban hanashi ba inaji ya kunce towel din jikina ya fadi kasa up and down yake kallona daurewa kawai nike bansan yaga na fiye complains saidai kunyar Ya Taufiq nikeji sosai narasa dalilin hakan.
Kama hannuna yayi yanata murmushi mai nuna tsantsar farin ciki gefen gado ya ajeni ya koma bathroom zai aje towels din.
Ta madubi na kalli kaina banda mararraba da banda kaya a jikina domin kayan masu tsantsine.

Inajin fitowar shi ya shimfida sallaya ta kabbara sallah sai nafilfili yake abin shi,niko kunya ta isheni yasan banyin sallah yanzun kallan da yake mani kenan.Yana gamawa yai mani nuni da hannu alamun inje.
Tashi nayi inadan sa hannuna a gaban rigata na isa gaban shi na zauna ina kauda kaina gefe kallon da yake mani yai yawa.
Addu'a yake tayi mana na zaman lafiya da zuriya dayyiba ina cewa ameen ya jima kafin muka shafa atare na sake holding hannayena a kirjina nai shiru shiko ya kafeni dana gani.zare hannuwana yayi yace.
"Idan kina gabana bansan kina boye mani komai ko kare mani komai daga jikin ki,ke da duk abinda kika mallaka nawane Minal kinajina."?
Eh nace ina sadda kaina kasa."Sannan bansan musu duk abinda ba umurceki kiyi indai bai sabama Shari'a ba."
Sake nudding kaina nayi nace toh."Allah yai maki albarka."
Ameen na amsa.
"Dago kanki ki kalleni."
Kallan sa nayi ido cikin ido munjima a haka nidai natakura yana mani kwarjini dayawa yace."Kidaina soke kanki kasa kidaina jin kunyata Minal ni mijinki ne komai nawa mallakinki ne kinji tawan."?
"Insha Allah naji zan daina."Kamani yayi muka koma tsakiyar dakin bisa kafat ya dauko tire dake dauke da kaji da drinks sai madara ya aje ya dagoni ya daurani saman ciyar shi yace.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E33&34



"My wife ya gajiyan hidima."?
Alhamdulillah nace ina murmushi,tareda sadda kaina kasa,Shima murmushin yai mani ya dibi nama ya miko mani abakina banyi musuba na karba nafara taunawa sai kallona yake yana smile nima maida mashi martani nikeyi cikin kaunar juna.dana cinye saiya kara dibo mani ya bani haka na dingacin nama kuma yana mani dadi sosai,nima dibar nayi nafara bashi shima karba yayi yanaci saina fara sakewa dashi ganin yau zan kwana free tunda ina fashin sallah saijin dadi nikeyi araina,saida muka koshi sannan yabani madara mai dadi nasha shiko lemo kawai yasha ya dauke tire din ya fita dasu baijima kwarai ba ya dawo ya daukeni mukahau gado muka kwanta ya janyoni jikin shi gam yasani a kirjin shi ya aza fuskar shi gefen kumatuna ya kwanta mu dukan mu munyi shiru kamar masu bacci amman kowa da abinda yake sakawa aranshi.
"Minal."
Na'am nace a sanyaye.
"Ina missing wannan daren namu mai albarka ba haka naso ya kasance mani ba Aminatu amman haka Allah yaso."Nidai shiru nayi araina ina ayyana Allah yasoni yau dana tantance kenan dagani mijin nan nawa bazai hakuri ba."Bakice komai ba Baby na."Kayi hakuri."nayi maganar amatukar sanyin murya
Ko bakison mu raya daren nan a cikin sunnah."Inaso nace a nauyaye."
Saka kanshi yayi tsakanin kirjina yana murza kanshi kadan kadan yace."Kwana nawa kikeyi kuma yaushe kikara fara MP din."?
zan mashi musu natuna yace baisan inmashi musu bai kamata inasaba umurnin mijina naba nace."Kwana biyar nikeyi ranar juma'a nafara."...."OMG dontworry yau saura kwana biyu kigama kenan."?
Eh nace nidai jikina yagama mutuwa musamman danaga yanda Ya Taufiq ya damu da lamarin.
Tsinkayar hannun shi nikeji yana yawo a cikina zuwa sassan jikina sai nayi kamar in rike hannun shi sai infasa ganin kada dukan yai mashi yawa ga baicika burin shi ba ga inaneman yimashi rowar kaina saina kyale shi.
Ajiyar zuciya kawai yake shidewa yanaci gaba da safata son ranshi nidai hannuna na cikin sumar kanshi ina murzawa,jikina yai matukar sanyi.
Dage rigata yafara zuwa sama da alamun so yake ya fiddata sai lokacin na rike hannun shi alamun yayi hakuri kallona yake idanun shi sun kada jajir dasu."Pls Minal help me i need u more than everything in my life."
Wani irin tausayin shi yaka mani sosai cire hannun nawa yayi ya saka mana dump light kana ganin komai saidai ba sosai ba ya zare mani rigar tawa yafara shafa cikina yana kissing dina nidai nagaza komai,kamar in kurma ihu haka nadingaji wani yanayi mai wuyar fassara,ranar dai Ya Taufiq yajima yana birkitani kamar bashi ba har nafara tsorata ni yanayin shi,yajima yana abu daya har jikina yafara zafi hakama lips dina kamar ba nawaba.Dan dole nace
Zafi Ya Taufiq nafada mashi cikin kunnen shi kamar bazai barniba sai kuma ya sake maidani jikin shi kamar za'a rabamu haka muke like da juna kowa na shide numfashi kamar wa'anda sukai kokowa,Inajin yajamana bargo ya rufemu saina fahimci kamar rawar ɗari yakeyi.
A dan tsorace nace.
"baka lafiya."
Nudding kanshi yayi yace."Zazzabi ya shido mani."
Sake rungumeni yayi tsam saidai jikin shi ya dauki zafi sai numfashi dayake shidewa wani iri.
hannuwana nasa ina shafa bayan shi a hankali a hankali bamujima ba naji shi shiru,kallan fuskar shi nayi naga tayi fayau dashi yana sauke numfashi a hankali alamun bacci yai gaba dashi kokarin mikewa nayi naji yasake maidani jikin shi sake kwantawa nayi,ina pillow da hannun shi mudukan mu mukayi bacci cikin aminci,wannan kenan.

********

Koda aka kama Mami ba inda aka zarce da ita sai gidan Yari kamar yanda Alqali ya tabbatar matsawar ta dawo da kanta ba kamata akaiba zatayi life prison, idan kuma aka kamata ba ita da maido kanta ba za'a kasheta ta hanyar rataya,shiyasa basu bata lokaci ba aka kaita gidan Kaso na Kurmawa itako ba abinda takeyi banda zabga ihu tana kururuwa tana kiran nabani na lalace asirina ya tonu ina zan saka kaina asirina ya tonu Alhaji Mukhtar ya sakeni Taufiq ya auri Aminatu sai nayi ajalin ku watsastsu haka aka bata uniform sannan aka watsata cikin daki aka rufeta tana kuka tana komi.
tana ganin yanda zata bude sabuwar rayuwa.

Kaduna
tunda gari ya waye nagama shiryawa kafin Ya Taufiq yadawo daga masallaci sai karfe kusan takwas ya shigo ina zaune a falo inajin kira'ar suratul bakara ahankali take tashi hankali ya kwanta sosai koda naji anrufe mani idanuna a hankali na shafa hannun shi tareda sakin murmushi.
"Good morning Hayati."
Morning too my life,sorry nabarki ke kadai ko? Am so sorry Babyna."
Janyo shi nayi ya zaune gefena muna kallan junan mu cikin tsantsar so da kauna maihade da shauki na masoya hannuna na aza gefen sajen fuskar shi nashafa a hankali nace.
"Well come I miss you."sakar mani cool kiss yayi a kumatuna a hankali ya zame ya kwanta yana aza kanshi bisa cinyata shafa sumar kanshi nikeyi cikin raɗa nace."Ko mijina yayi wanka.?"
Shima shafa fuskata yayi yace."Matata nike jira taimani nagaji dayawa"
Murmushi nayi inajin kaunar mijina bance komai ba.tashi yayi ya kama hannu ba musu nabishi zuwa bedroom dinshi mai kyau komai na ciki is white sai paint dinshi blue, daga mani hannun shi yayi,nagane manufar shi ,a hankali na zare mashi rigar shi na aje gefena dukowa yayi yace.
"Am ready mujeko"
Kallan tuhuma nai mashi ,shima ni yake kallo bai ko kyaftawa sai murmushi da yake mani.
Shiga mukayi bathroom din na hada mashi ruwan wanka muna tsaye a bath kasancewar glass ke zagaye da sorrounding din ba kwami bane cire singlet dinshi yai ganin da gaske yake na kirkiro tari bako kakkautawa a kidime ya rikoni."sannu Baby na bari inkawo maki ruwa."
Riko shi nayi ina girgiza mashi kai a dan sarke nace."Fara wanka bari inje bansan ka fita ahaka."
Banjira cewar shiba na fita ina janyo toilet din nayi bedroom dina ina dariyar mugunta da haka na shantake kamar bansan ni yake jiraba,kwantawa nayi ina game abuna almost 15mint jinayi ya yarfa mani ruwan kanshi ya tsuke fuska yace.
"Ni kika shanya ko Minal."Marairaicewa nayi nace."Sorry sweet heart yanzun nasamu relief pls." a sifar shagwaba nayi maganar ina karye kaina gefe.
Uhmm yace ya kamani muka koma saman stool ya zauna yana kallan madubi ya miko mani mai karba nayi na diba nafara shafa mashi yana waya da Ya Tariq.
"Hassan anjima sai Amma (Anty Aisha) haka suke ce mata,takawo mata haka za'ayi."
Nidai bansan mi za'akawo mani ba harna gama shafa mashi mai fesa sure yayi ni kuma na fara zabar mashi kaya milk shadda da aikin coffe din zare,zame towel din yayi na taimaka mashi nataya shi saka kayan har nagama shirya shi kamar wani karamin yaro sannan mukayi kasa muna rungume da juna yana mani fira karfe tara tayi knocking tashi yayi ya bude Aisha (Auta) da Maryam diyar Anty Murja dauke da katon basket.
"Oyoyo auta da Ummi kune tafe."
Nace ina murmushi sainaji dadi nasamu yan hira.Kallona yake saijin dadi nikeyi.
"Eh Anty ina kwana."
"Lafiya lau ya Mum."?
"tana gaidaki ga kalaci tace akawo maki."
Amsa nayi inajin dadi.

"Lallai kam ni bata gaidani kenan kuma kalacin ita kadai aka hadomawa ko? Bakomai nima da Mamata na kusa dani da ba za'aimin hakaba."Yace a sifar wasa.

"Sorry Yaya kila tamanta shiyasa batace mugaidaka ba."
Dan zaro idanu yayi waje irin shock dinnan yace.
"Wato Mum dai tamanta dani kenan bakomai."
Dariya mukay,a dining suka aje kayan kamani yayi muka zauna sai manne mani yake ko kunyar kannen mu baiji saidai nidake dan janyewa zuba mani kalaci yayi arishi and egg sai kuma ya zuba mani ferfesun kifi dibowa yayi yakawo mani abakina na kauda kai gefe ina murmushi.
"Ummi muje kinga Abba ke kirana Anty jibi zamuzo yimiki yini fa."
"Toh auta sai kunzo amman aida kun mani tun yau ko."?
"Aaa Abba ke nemana shiyasa."
"Okay kugaida mani da yan gidan."
da toh suka amsa sannan suka tafi.
Kamar jira Ya Taufiq ya maidoni kusa dashi,nima na saki jikina sosai ban wani darareba na saki jiki mukaci abicin mu muna shan love dinmu saida na koshi sannan muka koma falor muna kalll ina kwance nayi matashi da cinyar shi.


_KURMAWA_

Aiki suketa jibga kamar ba gobe kana ganin su kasan sungama gajiya magashiyan musamman Mami wadda bata saba da wahala ba sai abin yazo mata wani iri akasalance takeyin shi tana zage zage wanda ya zamar mata kamar ruwam dare kuma ba wanda take jama Jafa'i irin Aminatu da Taufiq sai Mum datake alwashin kota halin kaka na kayi bata ba mallakar Major kowa ya rasa tunda ya saketa,wanibi kuma taita kuka duk ta lalace yan kwanakin datayi kwana na hudu kenan.
tana zaune bakin wata bishiya itada Anty Hafsat suna cece kuce.

"Wlh Mufida insha Allah sai kinyi mutuwar wulakanci duk kece makirar da kika jefamu cikin wannan ukubar sai Allah ya wulakantaki haka zaki karata a lalace Allah ya isa tsakanina dake yau kimamamin watana bakwai a garkame amman ke sai kwanan nan aka kamaki dayardar Allah saina fita nabarki."ta ida maganar tana kuka mai sosa rai.

"Hahhhhh wanda ya tuba dan wuya ba lada wato harkin saduda kenan Hafsat aikadan kika gani da Mufida yar Shehu kike zancem kingani nan ni kaina ina tsoron kaidina bare kuma ke karamar kwaro wlh bari kiji Hafsat bantaba danasanij kasancewa nan gidan ba musamman da Alhaji Mukhtar ya sakeni da inrayu waje ba kalkashin inuwar auren mijina ba gwara na dawwama anan kuma abinda baki sani ba kina kukan munafunci waike mai imani kijini dakyau sunan ankama Mufida ne a zahiri amman a badini nabaro baya da ƙura dan wlh bazan taba barin Taufiq da Aminatu su zauna lafiya ba saidai in nidin yar zinace."da kausassar muryar tayi maganar tana dukan kirjinta.

"Azzaluma ta Allah batakiba nayi nadama nabiyema hassada na cuci kaina da kaina na zalinci Aminatu na wulakanta yar uwata uwa daya uba daya tana sona ina sonta kawai ciwon hassada ya kama kirjina zuciya ta,tayi tsatsa kaina ya daure Mufida sharrinki da tasirin dukiya da kika rudeni da ita ya halakar dani ina danasin sanin ki arayuwata Allah ya isa."
Kuka Hafsat keyi marar amfani domin anbaro bida baya.

"Ke Hafsat ki iya kalaman ki,ni nafi karfin ki har abada ashe kinsan ke karamar marar kunya ce har kika biyeni kuma wlh ni mai iya sawace abaddaki a gidan nan ko shakka banayi an batar da zanba ki kiyayeni nina wuce da ilimin ki."

Kuka Hafsat tahauyi tana danasani itako Mami ko ajikinta saidai wahala ake basu bata wasaba kuma kanta na hayaki gani take kaf gidan ba wanda ya isa ya takata ko ya gwadata da yatsa bata sauke shiba.



▪️▪️▪️▪️▪️

Bayan kwana biyu yau nayi wankan tsarki nagama al'adata saidai hakanan nasamu kaina da shakku araina sai nikejin kaina kamar na shiga wata sabuwar rayuwa ta daban daman jiya nasha da'ga wajen Ya Taufiq kamar wani yaro haka nasamu ya hakura akan kudirin shi,mita kuwa nashata hakurin shi yakare nidai lallabashi kawai nikeyi da yau bazai fitaba dalilin fitar tashi sakone Accounter dinshi na Turkey ya aiko a kamfanin shi dake kaduna na da yake aiki shine yaje meeting sannan zaima wasu files sign da yake yanzun zaman kanshi yake bai aikin gwamnati shiyasa baida wata matsala da zuwa aiki sanda yaga dama zaije yaga yanayin aikin Companyn shi,addu'a ta Allah yasa yauma in exkept wajen shi Allah yasani ina shakkar rigimar Ya Taufiq araina.

Sallama nagama ta sallar magrib ina zaune ina lazumi abuna nikadai a gidan inajin tsoro kadan kadan bacci yafara dibata daman banjima da gama waya da Ya Taufiq ba hakuri yaketa bani na makara da yayi baidawo gida da wuri ba,jinjina kaina nayi jikin gado inajan jarbi ko motsin kwarai bansanyi bacci kuwa yafara saceni kamar daga sama naji ana shafata unexpected wani uwar kara nasaki naji mutun rungume dani yana rufe mani baki sai lokacin nakara rungume shi zuciya nabugu da sauri da sauri.
"Sorry my queen bansan zaki tsorata ba pls forgive me."Dan dukan wasa nakai mashi a kirji nace.
"Idan kasa na mutu fa na tsorata dayawa."
"Shiit." ya daura yatsansa a bakin sa yaci gaba da cewa.
"bazaki mutuba matata kinji insha Allah tare zamu rayu mu mutu tare kidaina cewa haka."
Uhmm kawai nace.

"Ahhh masha Allah kinga yanda hijab din nan yai maki kyau tubarakallah ga annuri a fuskar ki sai kyalli kike kingana da mahaliccinki, eyem ba Baby na takaina yan matana angirma."
Murmushi nayi nace."Sanyi nike danji shiyasa na saka hijab."

Hade rai yayi yace."What do you mean.?"
"Am off insha Allah by tomorrow."Wlh banyardaba Allah Minal tell me the truth"?
tsuke fuska nayi nace dagaske nikeyi."
"Let me check."
Waro idanuna nayi ganin ya zare mani hijab kamar baby ya cillani kan gado yai mani runfa kokarin tashi nikeyi ya daura mani dukkan nauyin shi dole nai lakwas dan ban iya kwakkwaran motsima dage mani riga yafara wai shi zai duba."aya wlh karya nike kayi hakuri ka dagani nagama sallah zanyima yanzun.!"a matukar tsorace nayi maganar,Lakatar mani hanci yayi yace.
"Matsoraciya ga barazana da antaba tafara dan Allah Ya Taufiq kayi hakuri."
Dariya nayi na zauna na kwanta bisa kirjin shi nace."Wash wallahi ka gajiyar dani dayawa bacci zanyi."
"Allah ko?"
Ehmana am tight.
"Okay i will give a suppliment kada kidamu yau zaki warke,tashi muyi sallah bari inyo alwallah ko.?"

Murmushi ya kuma sakar mani yai bathroom baijimaba ya fito ya shiga gaba ina baya zai tada nace."Banyi isha'i ba"Nima ai ita zanyi.''Tada ikama yayi mukayi isha'i muka gama sannan yace muyi nafila sake janmu yayi muna idawa ya matso gabana ya daura hannun shi saman kaina yanata addu'oi nasan dai yau itace ranar da ake cewa ranar wanka ba'aboyon cibi yau nasan duk rigimata Ya Taufiq yafini ai naga hakurin shima haka yagama zabga mani addu'oi sannan dagani tsaye ya zare hijab din jikina up and down ya kalleni ya.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E35&36



"Alhamdulilah bansan wane irin farin ciki nikejiba bansan ya zan kwatantamaki yanda nikejiba Aminatu yau nice tareda iyalina a cikin wannan dare mai alfarma niki kokarin raya sunnar ma'aiki a cikin wannan ni'imtaccen dare mai tarin alkhairi wanda ya kasance dare na musamman agaremu bantaba kasancewa a farin cikiba kamar na wannan ranar ba,ina rokon Allah ya sadamu da alkhairan dake cikin wannan dare yarabamu da dukkan sharri ina rokon Allah ya azurtamu da tsarkakakkiyar zuriya mai yawan tsoron Allah da ambaton shi ina kaunar ki Minal da kaunar ki nike fidda kowane bugun numfashina Allah yabaki hakuri da juriyar daukar lalurar mijinki Aminatu nima Allah yabani ikon sauke maki duk wasu hakkokin ki dake wuyana yabani ikon faranta maki."Sunkuyar dakaina nayi nace ameen ya rabbi."
Saitin kunnena yai mani raɗa.Murmushi kawai nayi nidai zuciya ta nadan bata sauti ina jin tsoro kadan araina dakewa kawai nikeyi ina imagining taya zan kasance da Ya Taufiq a wannan dare nidai kaina bazai iya daukaba am shock riko hannuna yayi muka zauna gefen gado yasa hannun shi bisa zip dina yana janshi kasa a hankali nidai ban hanashi ba saidai duk nasha jinin jikina.
"Muyi wanka ko."?
"Nayi gab da magrib banjima dayiba."
Nace a kasan labbana kamar mai tsoron magana.
"Okay bari inyi wanka ina zuwa kinji Baby na."
Gyaɗa mashi kai na iyayi bathroom ya shiga yadan jima ya fito daure da towel a wist dinshi muje in dauko underwares dina ko"?
Hannun mu cikin na juna muka nufi bedroom dinshi yana murza hannuna a hankali bude wardrope dinshi yayi duk yai hanging dinsu ya zaro boxes da singlet ya saka gabana yazo ya duka yai lining yace.
"Inafatan amaryata tana farin ciki da wannan daren ko.?"
Eh nace ina murmusawa.
Jinjina kai yayi ya bude karamin fridge ya dauko madara a roba ya zuba mani a cup yabani amsa nayi inasha daman yunwa nikeji sama sama najima ina yanga duk dan inbata mashi lokaci,shiko bai mani korafi ba har saida nagama sannan yasha yana shafa sumar kaina yace.
"My world mu kwanta ko."?ba dakina zamu kwanaba?"
Girgiza kanshi yayi yace.
"This is special room everything is white."
Jinjina kai nayi bance komai ba.
"Shiyasa nikeson mu kwana anan komai farin cikine agaremu komai yanada mahimmanci agaremu."
Hakane nace ina sosa keyata."Good girl."
Yace yana kamani saman gado muka zauna ya zare mani fashion yan kunnen dake kunnena sannan yafara kasa da zip dina harya zare mani rigar dagani sai inners ajikina underware sai bra.
Hura mani iskar bakin shi yake mai kashe mani jiki yana murza yatsuna a hankali yafara kunsanto da fuskar shi gab da tawa yana lasar lips dina harya fara kissing dina kamar yana tausayina komai a sannu yakeyin shi,munjima haka saidai bancika maida mashi martani ba haka yahauni da kisses yana wasanni da sassan jikina zuwa cibina wuyana harzuwa kunnuwana jikina ya dauki rawa sosai wasanni miji da mata harna sake dashi amman dai tsoron bai fita jikina ba sai lokacin yacire mani iner dita yana placing hannun shi bisa nafilani na yana sarrafawa nidai kamar gawa jikina yai sanyi,bansan sadda ya rabani da komai nawa ba fatar jikin mu nagame dana juna muna jin wani irin yanayi nai wuyar fassara danshi harya fara sakin zance iri iri.
Almost 30mint muna romans juna musamman shi nidai yar karace dan banda wani hope bangama gigitaba saida naji yagama karanta addu'ar kusantar iyali a lokacin nagane mi akeyi nashiga tashin hankali kamar zan mutu haka nikeji saida nasaki kara sosai na kadaddabe shi ina kuka duka nike kaima bayan shi ina kuka kamar zan mutu,baisan inayiba ranar nashiga tashin hankali azaba da wahala nashata iya wahala ranar na tantance mine aure nasha wahala hannun Ya Taufiq nidai banda wani karfi ko kuka na zuci na komayi tun inayin kuka hari nakaiga banyi komai bansan inda kaina yake ba,Wani wahalallan kuka nasaki muryata ko fita batayi tsabar wahala bangani sosai bishi bishi nike ganin shi a kidime ya rungumeni jikina yana lallashina nidai kuka nikeyi mai ratsa zuciya Allah yasani nadauka na mutu."Minal sorry pls matata daina kuka am so sorry."
tureshi nafara ina yunkurin tashi yanda naji kasana saida na tsorata domin sign kadai naji nasan Ya Taufiq yajiman ciwo inalillahi nikeyi araina shikenan inba sannuba asirina saiya tonu kilan sainayi jinya kowa sai yasan halin dana tsinci kaina.Sake rungumoni yayi ina kuka yafara goge mani kwallana yana bubbuga bayana a hankali yana shafani."Bazan kuma ba my life banso nai hutting dinkiba pls my wife sorry."
Nidai nasan aikin gama ya gama gashi har yanzun banda komai jikina ga kunyar shi inaji so nike ko blanket inrufe jikina amman nagaza ban iya tsinanama kaina komai.
Inajin shi ya tashi kan gadon ya kunna light haske ya gauraye dakin yanayin dana ganm saida na rufe idona tsabar tsorata da kunya ta isheni.
Inalillahi naji yaja a razane ganin aika aikar da yayi wannan karan dakyal muryar shi ke fita ya tallaboni yana.
"Aminatu minayi haka sannu matata banso nai hutting dinki ba i loss my control forgive me pls."
Araina cewa nike illar auren tazuru kenan nasan bayin kanka bane!
Kwalla nike sosai fita ya kunna a toilet sai lokacin nasamu damar rufe jikina inajin jikina yai zafi ringis shi kanshi Ya Taufiq din tabani kadai da yayi nafahimci shima zazzabi yake dan nashi yafi nawa zafi sosai yake zazzabi daurewa kawai yakeyi.
Daukata yayi mukayi toilet ya hada ruwan wanka cikin wani bath cast ne ya zaunar dani arazane nike neman tashi da karfi ya zaunar dani ina kuka yana share mani hawaye kamar zai tayani kuka najima yana sauya mani ruwa saidai naji dadin ruwan saidai yaimani rauni dubawa yafara ina hanashi harna fama kuka nasaki yace.
"Bari insa Tariq ya turomani doctor Nasiba kiyafe mani Minal sorry."
Da sauri na rikoshi ina girgiza mashi kai ina kwalla.
"Why dole kiga Doctor bazan jure ganin ki hakaba matata."
"Pls kabari nidai bansan kowa yasani su Mum na iyaji kadaina Ya Taufiq."
A shagwabe nayi maganar ina kuka sake saman ruwan yayi yakara gasani atare muka tsarkake jikin mu inajin nauyin shi sosai abin wani iri yake zuwar mani akaina,shiko baijin kunyata sam,har ya daukeni ya zare bedsheet ya sauya wani sama sama ya shimfida wani dan ba wani iyawa yaiba.
Shafa mani mai yayi yaje dakina ya dauko mani doguwar riga mai saukin nauyi nasaka manj ko bra hanani sawa yayi sai underwire nasa shima badan yasoba karfe bakwai mukayi sallah danni bansan anyi asuba haka shima.
Ruwan zafi yakawo mani black tea ya tallaboni yana bani amsa nayi saidai ban kallan idanun shi kamar munafuka haka nakoma sukuku nika dai nasan azabar da nikeji nima nasan dole inga likita inba dinki tabbas za'adaurani bisa Suppliment ina bukatar taimako.Dago habar fuskata yayi yana kallona yace.

"Allah yaimaki albarka Aminatu kinbani wata kyauta mai dinbin daraja da martaba wadda bantaba sa rai zan samu kwatan kwacin taba kin maidani nazama Sarki a cikin Sarakuna kin bani abinda bansan taya zan biyakiba kisama mani farin ciki a cikin wannan daren ya zama dare mafi kololuwar daraja da rahama agareni kin goge tabon daya jima agareni na kalmar tazuru ashe da cikin bala'i da masifa nike zaune ashe jin dadin duniya da nutsuwar ta yana cikin rayuwar aure,kin zama duniyata kuma rayuwata Allah yasaka maki da gidan aljanna yasa ko acan kizama matata Minal ina kaunar ki uwar ya'yana."

Bansan nayi murmushi ba mai yalwa ina shafa gefen fuskar shi wani sonshi nakara ratsa indai wannan shi ne farin cikin mijina badan ina cikin ciwo ba tabbas zan mutu ina farantama mijina banda buri daya wuce inga farin cikin Ya Taufiq musamman idan na tuna wahalhalun da muka fuskanta arayuwar mu dole zamu zamo masu sadaukarwa domin farin cikin junan mu.
Shima fuskata yake shafawa sai smile mukema juna nakasa mashi complains akan ciwon dayaji mani nidai jin dadin shi da farin cikin shi,shine nawa nasan nayi dacen miji lallai wani jinkirin alkhairi ne kuma komai lokacine.

"Ina sonka mijina kaine jigona suturata abin alfaharina ina kaunarka ina fatan Allah yasa mana albarka arayuwamu i love you with all my heart my hero."
Hade bakinmu yayi yana mani kiss mai rudarwa munjima sannan ya zare lips dinshi cikin nawa a hankali yace.
"Love u too my life."
Sake rike mani hannuna yayi yace.
"Pls wife kibari a dubaki wlh na tsorata akwai ciwo jikin ki."Yai maganar cikeda damuwa.

"Yes i know but bansan kowa yasan miyasameni daka bari nagaya maka sunayen maganin da zansha kamar zaifi."
"Aaa Babyna i dont think kamar da kari yakamata Dr Nasiba she's a ganycology tasan komai we need her ur Health is very important to me pls kibari tazo har gida ta dubaki."

Jinjina kaina kawai nayi bance komai ba

Please Login or Register in order to submit comment