Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaya sannan tasa akai mani lalle nida Aisha na salataf mai kyaun gaske,aka yarfa mani kitso ga dilka nasha jikina yakara kyau sosai,yau kwana ukku ban kwana dakin Ya Taufiq ba tunda sai daren da zamu koma na kwana ranar kuwa ya nuna jin dadin kyan danayi musamman kunshina domin yanason Jan lalle sosai,koda gari ya waye goma nayi muka shirya zamu tafi haka makota suka fito akaita ban kwana kamar kada arabu,ɗaga mana hannu sukai tayi har motar ta 6ace inajin kewar yan gidan mu sosai,tafiya mukai sosai ba inda muka amsa kira sai Kano,kasuwa mukaje wani Mall nasiyarma Mina da Haidar kaya na sawa yan kanti masu kyawun gaske na zuba cikin akwati sosai na zabar masu kaya harda takalma duk nasiyar masu sannan na haɗama Mina kayan shafa cikin leda nasaima kakarsu turmin atamfa da leshi,ba inda muka amsa kira sai gidan iyayen Abdallah har cikin falorn Iyah.
tarba ta musamman sukai mana cikeda karamci bamu jima da zamaba Abdallah yataho daga kasuwa daman munyi yawa yasan da zuwan mu,zama yayi suka gaisa da Ya Taufiq sosai suke fira bayan mun gaisa.

Munkai awa ɗaya sai gasu Mina da Haidar sun dawo daga makaranta tana ganina taganeni kaina tayi ta rungume tana."Oyoyo Momi."
Nima rungumeta nayi inajin so da kaunar su har kasan zuciya ta musamman Mina dake mani kama da Husna copy tabbas Asma'u ta tafi amman tadawo domin Mina bata da banbanci da masoyiyata mariganya Husna.

Riko Haidar nayi na azashi bisa cinyata shima ya zama saurayi masha Allah saidai yafi yanayi da Abdallah.
Dadin danaji bana wasa bane inajin nishadi araina kasancewata da ya'yana."Ya School kuna gane karatu ko."?
"Eh Momi nike mana na ɗaya a Class dinmu."
"Good girl."Na ida maganar ina shafa sumar kanta,nace kaifa Haidar."?"Nima ina ganewa sosai."
"Na nawa kakeyi."?
"Na ukku."
"Good boy ajinka nawa."?
"Primary 2."
Haidar zaikai shekara takwas saboda yana da kusan 2yrs mariganya ta rasu ni kuma saida nayi 5yrs gidan yari koda sakina gidan Yari nakusa shekara,ita kuma Mina tanada shekara 11yrs a halin yanzun nace.
"Mina ajinki nawa."?
"Primary 5 mun kusa common interest."
"Allah ya taimaka yai maku albarka."
Ameen suka amsa ranar najima ina fira da ya'yana sannan mai aikin su ta tafi dasu domin shirin islamiya haka nabasu kayan makulashe sannan naba kakar su tsarabar kayan dana sai masu.
Bude akwatin tayi tahau dubawa tana cewa.
"Kuzo kuga kayan da Momin ku ta sai maku."
Murna sukai tayi duk aka gwada masu sun masu cif ranar farin cikin dasu Mina sukai bana wasa bane,hakama Abdallah saidai yace.
"Allah yasaka maki da alkhairi amaryar karni Allah ya saukeki lafiya."
Na shiga ukku nace araina miyasa kowa ke gane inada ciki ohni Aminatu a zahiri cewa nayi."Hmm amaryar kamshi zakace dai."
Dariya akayi sosai muka ta6a fira nace."Abdallah inasan zanyi magana dakai amman zan kiraka waya."Shikenan Allah yakaimu."
Tashi mukayi har zamu tafi Baban su ya shigo sannu da zuwa mukai mashi.
"Aaa kuce gidan namu munyi manyan baki Momin Mina ce gaskia kudawo mugaisa."
Shiga mukai dakin shi,muka gaisa nan yake gaya mani maganar da mukai da Baba akan maganar Abdallah da Rahima yaci gaba dacewa.
"Dan Allah Aminatu kitaimaka kima Abdallah magana kila ya amince.
"Insha Allah Baba."
Haka muka gama gaisawa sannan muka tafi suna waving dinmu.

Muka shiga mota shi kuma Abdallah ya tafi dasu Mina zai kaisu islamiyya nan nacema Ya Taufiq dan Allah mu biya gidan su Ya Mutallib da yaƙi yarda sai muka ya amince.Koda muka isa Salima da Ummi sai Daddy muka iske sunyi murna ganin mu sosai.
Haka mukai fira gwanin birgewa saidai Ya Mutallib bai nan yaje India,munjima Daddy yana mana addu'a hakama Ummi sai biyar din yamma muka tafi suna mana addu'a gidan Ummi muka sauka nan aka dasa daga inda aka tsaya dayake jirgin dare zamubi sai karfe sha ɗayan dare jirginmu zai tashi zuwa gida,haka kuwa akayi koda mukaje wajen Boding aka sikelin kayan mu saida muka biya domin sunfi 20kg haka muka gama sai 12 na dare jirginmu ya tashi har Allah yasa muka iso Usama yazo daukar mu,sannan muka isa gida kowa yagaji,wannan kenan.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_



S5/E43&44



Washe gari da misalin karfe ɗaya muka shirya mukaje gidan Alhaji Munzali kakan Ya Taufiq.
Tunda muka shigo falorn shi yake farin cikin ganinmu hakama iyalan shi,sannu da zuwa suke mana musamman shi dake kishingiɗe yana hutawa.Zama mukayi baki ɗayan mu agafen shi nidai kaina na ƙasa ina watsa da yatsun hannuna.
"Sannunku da zuwa ya'yana,Husseini na,yau kaine tafe da iyalinka."?
Yai maganar fuskar shi ɗauke da murmushi.
"Ai kuwa Alhaji tazo ta gaida tsoho mai ran karfe kaga amaryata kyakkyawa ko."?
Dariya akayi inda wata tsohuwa ke cewa.
"Ina ai duk kyawunta bata kaini ba kake wani kuri."Aaa gwaggo aiko yarmu tafiki kyau."
Cewar wani dattijo mai kama da Abban Ya Taufiq.
"Ina matana sunfi wannan kyau nesa ba kusaba daina zugashi kaji."Inji Alhaji Munzali.
Dariya akayi haka dai tsohon yaita tsoka narmu da wasa da dariya kowa saijin dadin yake,haka akaita zuwa sashen Alhaji kowa yanason yaga matar Taufiq.nidai kunyar su nikeji banda Alhaji Munzali daba ruwan shi domin ya'ya yake daukar mu.

Alhaji Munzali dattijone dan kimanin shekaru ɗari da ɗauriya a duniya farin Barumaye ne kyakkyawan gaske domin yana kama da Ya Taufiq kwabo da kwabo dandai shi ya tsufa.

Alhaji Munzali ya kasance mai wasa da raha duk daya tsufa amman hakan bai hana shi gane ya'yan sa da jikokin sa ba, koda ya manta indai ance wane ɗan gidan wane ne zai gane mutun duk da yawan shekarun shi.
Matan Alhaji ukku da tarin ya'ya mata da maza.
Ya Taufiq yace, muje mugaida sauran dangi amman Alhaji ya hana saidai yace duk maison ganin ta yazo ya ganta a sashen shi,aiko wa'anda kenan haka sukazo har gida suka ga Aminatu.
Ranar munjima muna fira da Alhaji har mun kusa dawowa Ya Taufiq yadan shafi keyar shi yace.

"Alhaji daman ina neman wata alfarma gareka idan badamuwa."?
Murmushin manya yayi yace."Inajinka Hussein minene."?"Daman inason kasa baki dan Allah kace Abba yabarni intafi da matata wajen aikina."
Dan shiru Alhaji yayi yana nazartar jikan nashi sannan yace.

"Bangane wajen aikin kaba daman ina aka taba yin haka miji na wani gari mata na wani gari ai katafi da matarka saidai in ba halin hakan,amman inda kana da yanda zakayi ai kafarka kafar matarka dan haka kada kadamu,amman ba nan Kaduna kake aikiba."?
Aaa Alhaji ai na aje aikin da nikeyi yanzun ina aiki a Company a kasar turkey."
"To nagane duk da haka bai kamata matarka tayi nisa dakaiba kuma in banda abun Muntari a wane dalili zaice haka kaga anshi wayar nan kamo mani shi yanzun nan."
Amsar wayar Ya Taufiq yayi ya kira Abba yana ɗagawa ya mikama Alhaji nidai ina gani karfin hali irin na Ya Taufiq.
"Alhamdulillah daman inason in shaida maka na kashe wannan maganar kabar Hussein yatafi da iyalin shi wajen aikin shi kanajina."?
"Baba bawai naki yarda bane naga yarinyar nan tana bukatar kulawa kasancewar tanada ciki shine nace Maryam ta kula da ita kaji dalilina."
"Dakata Muntari angaya maku shi Husseinin bazai iya kula da iyalin nasaba iyeh?dan haka kabar wannan maganar yatafi da matar shi duk inda zaije kanajina."?
"Toh Alhaji yanda kace haka za'ayi kayi hakuri."
"Shikenan Allah yaimaka albarka ya shirya zuriya baki ɗaya."Ameen Alhaji nagode kwarai."
Sanyayyar ajiyar zuciya Ya Taufiq ya shide,yana kallan Alhaji da yace.

"Kai kuma saika kula da kyau kaji abinda mahaifin ka yace Allah yatsareku yakaiku lafiya yasa kudawo lafiya yabaku abinda kuke nema baki ɗayan ku."
"Ameen Alhaji"

Da haka kowa yafara tafiya kasancewar ana kiran sallah nima salla nayi sai gab da magarib muka wuto gida a gaggauce Ya Taufiq yasa nafara parking kayana,kusan duk shi ya hada mani kayan bukata haka shima,sai kusan 12 muka kwanta cikin farin ciki.

_WASHE GARI_

da safe Mum tace tana neman mu,muna gama shiryawa muka tafi,Falor muka taddata tana waya zama mukayi hannuna ta riko ta zaunar dani gefenta tana gama wayar ta kalleni kallan dake nuna tsantasar so da kauna irin ta iyaye tace.
"Yawwa Hussein naji dadin zuwan ku daman inason in baki wani sakone sannan inkara tunatar daku wasu abubuwa masu mahimmanci.
Kaga Taufiq mahaifin ka ya amince zai barka katafi da Aminatu badan yaso ba dan dai kawai umurnin Alhaji ne dan haka ka kula da yarinyar nan sosai kuma ka dinga fita hakkinta musamman abinda kasan tana so,ke kuma Mamana kiyima mijinki biyayya ko yaushe Allah yai maku albarka."
Ameen muka amsa.
Riko hannuna tayi tace.
"Muje ɗaki inason ganin ki ya'ta."
"Wato Mum yanzun dai bakiji dani komai saiki ce yarki ko?shikenan nima ai inada Mama ta mai sona."
Yai maganar waishi mai kishi,Murmushi Mum tayi tace.
"Eh naji mugani a ƙasa anata sabo wake ta tsoho."
"Wato Mum nine tsohon kenan."?
"Eh mana da baka saniba."Shikenan Mum tunda bakiji dani."
Wayar shi ya daga yace.
"Usama ka kawo kayan cikin side din Mum."
Mudai sama mukayi muna shiga ɗaki Mum ta zaunar dani gefen gado jawo wata loka tayi ta fiddo wata leda sai jarka tace.
"Ya'ta kinga wannan maganine ki dinga sha a cikin madara shi kuma wannan da zuma zaki haɗa shi akalla kisha shi sau biyu a rana.
Insha Allah zai kara maki cikakkar lafiya sannan zaki kara samun kuzari dan haka ki kula kiyi amfani dasu yanda na gaya maki."

"Insha Allah Mum zan kiyaye nagode kwarai."

"Sannan wannan na jarkar shima kama ruwa zakiyi shima zai kara maki lafiya kinji."?
Shima amsa nayi injin dadi araina nace.
"Allah yabarmin ke Mum ɗina nagode kwarai."
"Ameen ya'ta."
Haka taita bani shawarwari iri iri musamman na rayuwar aure na kamar ba surikata ba munjima sannan mukayi sallah muka dawo ƙasa.
Bamu jimaba Ya Taufiq ya shigo da Ya Samir nan yace.
"Mum ga tsarabar Anka inji Mamana"
"Kai amman mungode Allah yasaka da alkhairi gaskia munji dadi kwarai,Samir ku fiddo kayan ciki abawa kowa nashi."
Toh Mum cewar Ya Samir.
Gaidashi nayi bamu jimaba muka tafi,Mum taimana rakiya,muna fita mun dauki hanyar gida mukaga Ya Tariq shima zaizo gida horn mukai mashi sannan muka wuce muna isa gida na adana abun da Mum tabani cikin parking.

Zama nayi sai kuma na ɗauki wayata na kira Abdallah kira na biyu ya ɗauka bayan mun gaisa nace.
"Abban Mina dafatan kana lafiya."?"Lafiya lau amaryar kamshi ya gida."?Murmushi nayi nace."Alhamdulillahi ya ya'yana."?
"Suna lafiya qalau suna gaida Momin su."
"Ina amsawa."Ɗan shiru nayi sai kuma nace.

"Abban Mina daman inason inmaka wata magana saidai bansan ya zaka dauki maganar ba."
"Inajinki kifadi maganar ki karkiji komai."
Sanyayyar ajiyar zuciya na shide a boye nace.
"Maganar aurenka da Rahima ce shine nace bari in maka magana Abdallah ya kamata ace kayi aure zuwa yanzun kaga bai kamata ace kana zaune ba mata ba."
Shiru yayi na ɗan lokaci sai kuma yace.
"Hmm Aminatu bawai nakibin umurnin iyayenmu bane,saidai a halin yanzun banji zan iya wani aure gaskia."
Numfashi naɗan fesar nace.

"Kada kace haka Abdallah tabbas rashin Husna babban abune amman addu'a itace take bukata agaremu sannan auren ka nada matukar mahimmancin gaske kodan ya'yan ka."

"Hakane inajin nauyin auren Rahima hakan na tuna mani raɗadin rasa matata nidai kiyi hakuri bazan kara aureba."
Shiru nayi ina nazari nace."Kaga Baba yai mani wannan maganar kuma yaka mata ka dauki qaddara kada kamanta Rahima yarinyar kirkice sannan kuma ita kadai ce tafi dacewa dakai sannan zata maye maka gurbin daka rasa."
Wannan karon nauyayyar ajiyar zuciya yaja yace.

"Aminatu kenan banji akwai wata ya' mace da zata iya maye mani gurbin matata,sannan a halin yanzun banda wani buri da abinda nasa agaba irin inganta rayuwar ya'yana kosu kadai Allah ya raya mani naci ribar rayuwa ya'yana sune kowane burina zan tsaya tsayin daka in kula da duk wasu bukatu na ya'yana insha Allah."

"Gaskia ne saidai kasani duk yanda kakai ga renon ya'yan nan bakamar mace ba sannan Rahima ita kadai ce zata iya maye maka wannan gurbin kuma tanada hankali da tunani na tabbata zakaji dadin zama da ita insha Allah."

"Naji abinda kikace saidai inason kibani lokaci zakijini sannan kina ganin ita Rahimar ta amince da wannan maganar kuma zata yarda ta auri mijin yayarta."?
"Itama hakan take awajenta tana ganin bazata iya rayuwa da mijin yar yayar taba saidai kasani ranar dole sai dole kuma zataso ta rugumi zuriyar yar uwarta."
"Shikenan komai kenan zakijini tunda har wannan lamarin ta biyo ta wajenki."Wani irin dadi naji nace.
"Nagode kwarai Allah yasaka maka da alkhairi,Allah yaima mariganya Asma'u rahama yagafarta mata kurakuren ta kuma Allah ya shirya zuriyar mu baki ɗaya."Ameen ya rabbi."
"Wai ina angon kamshi."?
murmushi nayi nace."Ya fita."Ina gaishe shi."
"Zaiji insha Allah."
da haka muka taba fira sannan na kashe wayata cigaba da hada kaya nayi,wannan kenan


_JAIL_


Bayan wani lokaci mai tsawo a gidan Yari Hajia Mufida ce wajen iyalanta suka kawo mata ziyara.

Sajida,Samir,Samira,Fiddausi,Zakiyya,Anty Wasila harda Fatash a cikinsu.
Tunda sukaga mahaifiyar su a cikin mawuyacin yanayi hankalinsu yai masifar tashi,kuka suka fara baki ɗayan su.

"Mami miyasameki haka muka ganki cikin wannan wuyacin yanayin dan Allah kigaya mana."?
Cewar Samir dake kuka.
Itama Mamin kukan take tana tausayin kanta da kanta tace.

"Kunga halin dana tsinci kaina kunga yanda nakoma ku kalli jikina yanda ya lalace ga lalura ina fama da ita kowa ya gujeni hatta yan uwana prisonors kyamata sukeyi suna hantarata haka aka ware mani ɗaki ni kadai kamar mayya na shiga ukkuna."

Ta ida maganar tana aza hannayenta bisa kai tana kuka kamar ranta zai fita.

"Miyasameki kike fidda wannan mugun warin ya akayi wannan lalurar ta sameki dan Allah kiyi mana bayani bazamu jure ganinki a cikin wannan yanayin ba Mami ga rayuwar kunci kina fama da ita ga lalura miyasameki Mami."?
Fiddausi tayi mata tambayar a raunane.

"Wlh bazan iya gaya maku takamaimen wannan lalurar ba amman nasan koma minene yanada nasaba da alhakin mutane najima ina aikata miyagun ayyuka musamman a gidan mijina nakasance marar tausayi da tsoron Allah tabbas ban kasance mai kyautatawa ba acikin rayuwa ba."
Kuka sosai sukeyi kowa zuciyar shi ba dadi musamman Samir hatta Fatash saida ta zubda kwalla tsabar tausayin halin da Mami ta tsinci kanta ga azabban wari da takeyi mai masifar daga hankali da birkita hankalin kowane ɗan Adam.

Su kansu dandai ance uwa na uwa da bazasu iya kusantar taba bare har suyi magana mai tsayi da ita.

"Mami nayi imani da Allah,ubangijin mu bazai taba daura mana abinda bazamu iya ɗaukaba,domin wannan lalurar bata Allah da Annabi bace kiyi tunani ko akwai abinda kikayi daya janyo maki wannan lalurar kigaya mana ko mun san abunyi."Cewar Sajida itama kukan take.

Shiru Mami tayi tana nazari tace."Bazan iya tuna takamaimen abinda ya jaza mani wannan warin ba,abinda nasani na aikata abubuwa da yawa kinga bansan asalin wannan lalurar ba gaskia."

Shiru kowa yayi sai ajiyar zuciyar da suke shidewa suna mai tsananin tausan uwar tasu.
Wasila tace."Anty Mufida ina zargin wannan lalura taki,tanada nasaba da wani abu da muka shuka bako shakka."
Baki dayan su suka hada baki wajen cewa.
"Minene"?
Numfashi mai tsayi taja sannan tace.

"Akwai wata rana Anty ta aikeni wajen boka,akan tana son ya tarwatsa tsakanin Aminatu da Hussein koda na gaya mashi bukatar mu saidai abinda ya gaya mana shi yai bala'in daga mana hankali,buɗar bakin shi sai cewa yayi.
Bazai iya,yimana wannan aikin ba saboda tsakanin Amina da Hussein akwai rabo mai karfi kuma ba wanda ya isa ya hana faruwar auren su,sannan ya shaida mani cewa duk wanda ya shiga tsakanin lamarin zai iya mutuwa ko ya haukace dan haka bazai iyaba saidai ilimin gaibu wanda Allah kadai yabarma kanshi faruwar lamarin.

Koda na dawo na sanarma Anty yanda mukayi da boka sai cewa tayi bata amince ba dan haka mutafi tare,bayan sati muka koma muna zuwa muka sake gaya mashu bukatar mu,sake maimaita mamu abinda yace mani yayi.
Budar bakin Anty sai cewa tayi.

Boka ban amince da wannan maganar ba dan haka inason kalalata mani lamarin nan idan kuma hakan ya gagareka inason ka tura mata wata lalura wadda zatasa ya tsaneta kwata kwata kaga mun lalata alakarsu."

Shiru boka yayi sai kuma yace.
"Zamu tura mata lalurar warin jiki wanda zaisa ya tsaneta ko sunanta baison akama kinji abunda zamuyi mata hakan yai maki."?
Eh muka hada baki wajen furtawa.

"Shikenan kuje komai kenan zakuga saka makon wannan aikin ku saurareni."

Koda muka koma gida haka muka yini muna tsara yanda zamu cika burin mu.
Bayan wani lokaci daya shuɗe muka sakejin shiru kamar aikin namu baiba,shiyasa muka sake komawa koda mukaje muka sake yimashi maganar bukatar mu,saidai abinda ya sake fada mana har yafi na farko daga mana hankali.

"Hajia munyi aiki saidai an samu matsala yarinyar nan Amina ba yanda bamuyi ba dan aikin mu yakamata saidai abun ya faskara saboda itadin mai yawan tsayuwar dare ce sannan kullin tana yawan luzimtar ambaton Allah,wannan dalilin yasa aikin yaki tasiri gareta saidai aikin mu bai taba faduwa kasa banza komai daren dadewa koda za'ayi shekaru dari idan aikin bai fada kan Amina ba zai koma kan mai shi."
Tabbas hankalin mu yakai maƙura wajen tashi saidai lokacin idanun mu sun rufe bamu da buri sai muga Amina ta wulakanta Anty tace.

Mun amince nayi imani dole aikin nan sai yaci Amina koma yaushe ne.

Aaa Hajjaju ba lallai ba domin ita yarinyar nan ko batada tsarki bata daina ambaton Allah zuciyar ta mai kyauce kuma Allah shike mata gata sannan kisani faɗa da ita kamar jayayyane da ubangiji tunda shine gatan ta sannan kuma duk abinda zai wanzu akan Amina sai yafaru da ita,sannan ki aje makaminki kuma aikin nan idan bai sauka kan Amina ba zai dawo gareki komai daren dadewa,musamman idan alqadarin ki ya kare."

Dariya Anty tayi lokacin tanaji da isarta girma nasaba da kudi tace.
"Bako alqadarin Mufida Shehu bazai taba karewa ba har abada."

Da haka muka taho bayan ta aje mashi makudan kudade daga lokacin ban kara sanin planing din Anty ba,saida aka yankema Aminatu hukuncin life prison koda na tambayi Anty cewa tayi sune suka hada komai kuma ita da fitowa gidan yari har abadan abada.

Daga lokacin sai hankalin mu ya kwanta ganin Aminatu na gidan yari sannan Taufiq ya farraka bazai dawo gida ba.

Bayan shudewar wani lokaci mai tsawon gaske har mun rufe babin rayuwar Amina da Taufiq saiga shi ya dawo gida ayam lallai hankalin mu ya ɗugunzuma musamman Anty,saboda taji Taufiq yace zai ɗaga ƙara sai ya kwatar ma Aminatu hakkinta sai ya wanketa a idon duniya koda zai rasa komai nashi.

Ranar daya dawo Anty tasake tadani naje wajen boka koda na shaida mashi halin da ake ciki cewa yayi.

"Nagaya maku wannan lamarin ikon Allah ne banda ikon taimakon ku dan haka bani ba sake maku aiki."

Lallai zuciya ta,ta zafafa take na gayama Anty sakon boka sadda sati zatayi muka koma tare saidai abinda nagani yai masifar daga mani hankali matuka mun ɗimauta gami da razana da mukayi tozali da gawar bokan namu a wulakance rai yai halinsa banda tsutsotsi ba abinda ke fatali da gagan jikinsa ga wari daya kaure wajen,dole muka dawo gida haukane kawai bamuyi ba a wannan ranar.

Juyowa tayi ta kallesu daga bayan data basu tace.
"Bako shakka Anty wannan lalurar tanada nasaba da asirin da muka turawa Amina shine ya juyo kanki shiyasa kike wannan bala'itaccen warin mai zautarwa."

Kuka suke sosai baki dayan su Samir yace.

"Amman kin zalincemu Anty Wasila muna danasanin kasancewar ki kanwar uwar mu domin keba yar uwace ta rufin asiriba miyasa tun lokacin baki sanar mana halin da Mami tajefa kantaba sai yanzun da komai ya lalace bazamu taba yafe maki ba har abada."

"Kayya Samir kuna tsammanin alhaki nan kan Anty kawai zai sauka ni kaina bansan abinda zan girbaba nan gaba tun ranar da aka kama Antyna na sama raina ɗaukar fansa akan Aminatu ban zaune kullin inabin bokaye da malamai akan a haukata mani Amina domin bata ba kare rayuwa gidan Taufiq a matsayin matarsa ta aure,tunda hartayi silar rayuwar Anty gidan Yari hakan kuwa akayi yanzun haka na aikama Amina bakin asiri duk yanda takai ga tsayuwa wajen neman kariyar ubangiji,na tabbata akwai ranar da zata gaza daga wannan rana asirin danai mata zai kamata kuma zata haukace tabi duniya wlhil azim na tsani Amina da dukkan zuriyar ta."

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un suka dauka baki dayan su.
"Amman Anty Wasila bakida imani ko kadan kuma insha Allah babu abinda kika isa kiyima yar uwata! wai mi Minal ta tsare maku ne?miyasa kuka tsaneta?miyasa kukeson kawo mata cikas a cikin rayuwar ta?miyasa kukeson lalata rayuwar ta? insha Allah saidai aniyarki ta koma kanki ba abinda kika isa kiyima Aminatu da izinin Allah."
Cewar Fatash tagama maganar a fusace.

"Gaskia ne domin kuwa kin zama annoba tare damu komai Mami keyi harda gudun muwarki yanzun taya za'ayi a lalata wannan asirin."?
Samir yaima Wasila tambayar yana tsareta da idanun shi.

"Saidai mu rungumi qaddara domin wannan sihirin bazai lalatuba saboda bokan dayayi shi ya mutu."

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un Mami kinga halin da kika jefa kanki dan kinason kiga kin tozarta bawar Allah gashi yanzun kekika afka yanzun miye ribar wannan rayuwar."?

"Hmm Samir kenan tabbas rayuwa taimani daurin goro na zama abar gudu da kyama nayi zalinci aciki kuwa harda kisan kai inama ace da Alqali yata shi yimani hukunci rataye ni yasa akayi inama ace bani nadawo dakaina ba kamoni akai da ankasheni na huta da wannan matsananciyar rayuwar nayi imani da Allah kisa yafi sauki akan wannan darussan na rayuwa da nike gani narasa aurena ina takama nidin matar Major Sarki Mukhtar ce nayi izgilanci da nuna isa yanzun gashi ni kaina ina masifar kyamar kaina nasan badan kuɗin jinina bane tabbas bazaku iya minti goma atare dani ba,musamman idan ba bude baki zanyi magana azabar warin dake fita da duk wata huda ta jikina ta isa kowane dan adam tsorata dan haka wlhil azim yanda na tagayyara ta dalilin Aminatu nima bazan taba bari tayi rayuwar jin dadiba."
Ta ida maganar tana juyawa ta kalli kanwarta tace."Wasila idan kin haihu ga jinin Fiddausi tsantson Shehu na maki izini ki tagayyara rayuwar Aminatu."

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un Mami kina cikin wannan halinki kike jefawa yar mutane Jafa'i yanya bakiyi kuskureba."?
"Ba kuskuren danayi Sajida na tabbata Allah bazai taba yafe mani ba, saboda tuni na dade da yanke rahamar shi agareni kunga abinda na shuka!taya kuke ganin zan rabauta gwara kowa ya tagayyara."

"Lallai Mami baki kyautawa kanki ba sannan kinyi mummunan fahimtar addinin musulunci,shi Allah gafurrur rahimne kuma yana yafe laifi koman girman shi domin shi mai gafara ne kuma mai rahama da kanshi yace kunemi tubata ni kuma zan yafe maku sannan ku roka awajena domin nine mai biyan bukata dan haka har yanzun baki makaraba ki tuba zuwa ga Allah sannan kinemi afuwar wa'anda kika zalinta domin bai yafe hakkin wani kan wani idan kikai haka tabbas kin rabauta Mami."
Sajida tayi maganar tana kuka.
Lokaci ya cika cewar mai kula da time.

Samir ne yace."Mami ina mai maki huduba da kiji tsoron Allah kidaina wannan mugun alwashin shi Allah tsayayyene kuma rayayye duk abinda kikeyi yana kallan ki,ki aje mugun nufi kuma ki tuba zuwa ga Allah nai maki alqawali zan tayaki neman afuwar Aminatu kuma dayardar Allah zata yafe maki."

"Bazantaba kaskantar dakaina ba wajen makaskanciya ba kamar Aminatu ba har abada."a fusace tayi maganar.

"Shikenan Mami ina fatan Allah ya ganar dake gaskia yabaki ikon binta kuma Allah ya yafe mana baki ɗayan mu, zamu tafi saidai kisani kinsa dukkan zuriyar ki cikin kunci da bakin ciki,ga wannan kiyi amfani wajen biyan bukata sai wani lokaci."

Kudi ya bata sannan kowa ya tafi zuciya ba dadi wannan kenan.

Bayan sati ɗaya Fatash ce taje gidan su wajen Mum suka gaisa nan take gaya mata abun da faru da irin kudure kuduren da su Mami da Anty Wasila keyi akan Aminatu.

Tabbas hankalin su ya tashi matuka haka sukaita taraddadin lamarin har Major Sarki ya iske suna maganar shima ya tsorata dayaji kudurin Mami hankali tashe yace.

"Kai Mufida bakida alqairi kullin kinabin zuriyata da mugun nufi ina takaicin kasancewarki uwar ya'yana dan haka bazan tana yafe maki duk abinda kikai mani ba,sannan insha Allah ba abin da Aminatu zata gani sai alkhairi sannan ki sanarwa iyayen ta abaza ayi rokon Allah,ya wargaza duk wani shirin su nima yanzun bazan zauna ba sai inda karfina ya kare nima zan sanya ai mani addu'a Allah ya nesanta duk wani mugun nufi na Mufida."

Aiko Mum ta kira Baban Amina tagaya mashi komai da abinda yafaru yai al'ajabi shima ya raba sadaka masallatai gidan marayu da tsangayu na almajirai haka sukaita addu'ar neman tsarin Allah.

_ISTANBUL_

Zaune nike bisa sallaya nagama sallar isha'i ina lazumi kira ya shigo wayata Ya Taufiq ke kirana ina dagawa yace.
"My life sorry nabarki ke kadai ko?aiki yai mani yawa ki shirya nakusa dawowa zamu fita."


"Allah ya maidoka lafiya nayi missing

Please Login or Register in order to submit comment