Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk abinda yakamata ayi Alhaji Abubakar da Hassan zasuyi komai kisa aranki kamar biki aka gayyaceni amman ba wata matsala."
"Allah yakaimu da rai da lafiya."
Ameen ya rabbi."

"Mamana ai ba abinda ke damunki ko.?"
"Eh Baba ba komai."
"Alhmdulillah haka nikeso,saiki gayama iyayen naki duk abinda kike bukata asai maki kinji kada kiji kunya ko nauyi idan dake za'azaje saiki zabi wanda kike bukata."

"Insha Allah Baba nagode Allah yakara arziki."
Ameen Mamana."

Fira suke niko chat nikeyi da Angona wai kada inje Anka intsaya gida wajen Mama sai begging dina yake naki yarda dan dole ya hakura haka mukaita soyayyar mu sai goma na sauka na kwanta duk nagaji saboda zirga zirga da muka sha kuma goma na safe da wuri zamutafi Anka.

"""""" """"""" """""""
Washe gari kuwa da safe na tashi tareda Anty muka hada kalaci dankali da kwai sai costard kowa yai kalaci wanka nayi na shirya cikin abaya milk sai ratsin baki a jiki Mama da Zainab suma sun shirya sadda bakwai zatayi Maman Husna ta shigo gidan mu mikoma Mama wata jikka tayi tai mata bayani karfe tara daidai muka fito zamu tafi, Anty Mubaraka dasu Dada sukai mana sallama muka shiga motoci biyu daya Baba kejanta daya kuma Ahmad ina gaba wadda Ahmad keja,tareda Anty muka tafi sai daga mana hannu yan unguwa keyi haka muka dauki hanya muna isa Katsina muka sauke Anty Murjanatu tana daga mana hannu muka kama hanya har jibia nanfa muka dauki hanyar Zamfara cikin aminci wannan kenan.

_ANKA_

*Commenters and Posters Allah yabar zumunci🥰*

_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E17&18



_ANKA_


Alhamdullah karfe biyu daidai na rana muna cikin katon gidan mu na Anka gwanin birgewa tun daga Compound din gidan nike ganin tsarin shi dan ya burgeni sosai bawai irin gidan nan bane wanda ana gani za'asan cewa mutun ya amsa sunan shi na cikakken attajiri ba, Aa gidane hadadde na mai rufin asiri akalla mota ukku zata iya parking a compound din gidan sai hannunki na dama nanne side din saukar baki,wanda ke kallan ki kuma nan ne part dinmu sai wani kami manci a gefen dama zan iya kiran shi BQ sai flowers dake gefen gate sunyi kyau haka muka shiga ciki mai gadi wanda naji Baba ya kira da M.Nafi'u sai sannu da zuwa yake mana yana tayamu shigar da kayan mu ciki,har muka iso cikin falorn gidan mai yalwar girma zaici sate na kujeru biyu amman mu daya mukasa leader chairs bakake masu kyau ba laifi dakuna biyu ke jikin falorn dakin su Ahmad sai kuma daki daya spare sai kitchen duk a cikin falorn idan kabi wani Corridor daki na kallan ka center dinka na Baba ne sai biyu suna kallan juna daya na Mama daya namu haka gidan yake baida wata hayaniya sosai dakin mu Zainab tajani wanda kw dauke da gadaje duda ukku maki manta kowane da katifar shi wannan ya nuna ni daya Zainab daya sai auta jidda sai wardrope din bangon mu fantin dakin pink ne,haka nasu Ahmad ma irin namu ne saidao gado biyune shida Abdallahi fantin shi blue.


Wanka nayi ina fitowa Zainab tashiga wadda ta zama budurwa shirin zuwa Jami'a takeyi tace bataso Midwifery (Unguwar zoma)takeson yi da yanzun tajima dafara karatunta amman Baba na nema mata a Sokoto tunda zaman mu zaifi karfi a zamfara.


Ina fitowa na bude akwati nasa doguwar rigar atamfa sabuwa dal da ita taimin kyau masha Allah.
Kallan gidan kawai nike sai inga kamar almara wai mune zaune wani gari kuma agidan mu halak malak abin kamar mafarki,Mama naji ta kirani.
Aminatu,Na'am shine abinda nace na tafi dakin da naga ta shiga.

Masha Allah na furta a zahiri dan yai mani kyau gadonta royal mai kyau da wardrope din shi yayi kyau.

Mama ina kuka samu kudi harhaka jibi gadonki irin na yan gayu."
Nasamu kaina da tambayarta
Dariya tayi tace,kije Baban ki na kiranki anjima zanbaki labarin komai kinajina.?"
Eh nace natafi dakin Baba yana zaune bisa kujera dake kallan gadon dakin shi dandai nashi ba royal bane mai maballai ne ajiki coffee sai touching milk a jiki kama hannuna yayi ba zauna gefen shi ya shafi gefen fuskata yace.
Mamana.?"
Na'am Baba

Kinga munzo Anka ko? Anjima baki zasu dinga shigowa kuma rabi da kwata dan sugankine musamman yanda labari ya karade unguwar nan fa case din daya faru dayawa sunje Court Kano zanso kisaki jikin ki dasu kinsan ance shimfidar fuska tafi ta tabarma kinji ko.?"

Insha Allah Babana zan iya yina."
Allah yai maki albarka,Mamana."
Ameen

Harnayi shiru sai kuma nace.
Wai Baba wannan gidan duk namune kuma kayan ciki duk ku kuka zubasu ina kuka samu kudi har haka Baba.?"

Mamana abin alfaharina Ya' ɗaya tamkar da dubu Allah yasa yan uwanki subiyo halinki ba hakuri biyayya da kauda kai komai namune Mamana na saida gonakina kuma nasamu kudin aje aikina a Katsina shiyasa hatta shagunan waje duk na zuba akwai wani Kalama dan makwabcina suma sun mani karamci shike kulawa dasu sai kanin Amadu mutanen kirkine sosai Mamana kinji yanda akayi."


Allah Sarki Babana duk ni najefaku cikin hali dana saka kaina cikin...
Rufe mani baki yayi yace.
Ya isa na haneki da kalar zancen nan kinajina.?"
Eh nace kiran sallar la'asar yayi ya shiga yayo alwalla tare muka fito naga ana kiran shi waya Alhaji Tijjani dagawa yayi naji yace munjima da isowa mu hadu a masallaci da haka ya kashe wayar daidai dakin mu ya saki hannuna yace jekiyi sallah Mamana."
Toh nace na shiga cikin daki na iske Khadija harta gama sallah.

Namanta da Khadijan Anty Hafsat mukazo biyomu tayi wai in zamuje biki saita koma.

Haka kowa sai sallah sai santin gidan take tana Anty Aminatu wai Wannan din dagske gidan kune.?"
Eh shine abinda nace mata.

Ikon Allah lallai na yarda da wannan maganar Hassada gamai rabo taki ce,gaskia Allah shike komai, ikon Allah."
Haka taitata surutai tana mamakin rayuwa kai kace gidan gold taganmu a ciki sai tai shiru sai kuma tace

Kit ikon Allah arziki lokaci komai da nashi lokacin mahakurci mawadaci kudai kullin daukaka kuyi darajar ku na linkuwa kamar kunfi kowa ashe rashin hassada ce da bakuyima kowa shiyasa kukaci gaba har haka Allah yasa albarka."
Ameen mukace nida Zainab.

Zainab anjima kituna mani zan baku wani labari.
Insha Allah tace.

Mamana kufito anyi baki."
Cewar Baba daya leko yaga mana fuskar shi fal da annuri gyale na sa ajikina muka tafi zuwa falor da sallama a bakunan mu suka amsamu gwanin birgewa zama mukayo ƙasa muka gaidasu.

Mutane ne akalla sunfi ashirin sai murmushi sukeyi suna sannun ku da zuwa ya kukabaro Katsina munyi kewarku da yawa."
Alhamdulilah sun gaidaku mun sameku lafiya.?''

Alhamdulillah muka amsa.
Ina Aminatun take.?"
Wani mutun ya tambaya fuskar shi dauke da fara'a.
Gani nace ina sadda kaina kasa.

Masha Allah amarya sannu ya'ta muna maki barka da zuwa Anka fatan zakiji dadin kasancewa damu.?"
Eh nace ina murmushi.

Alhaji Tijjani kunga yarku da kyau tazo tagana daku kuganta tagan ku."
Aikuwa munji dadi kwarai Amina yar aljanna,Allah yai maki albarka yabaki zaman lafiya da mijinki yasa ace kwara da akayi."
Ameen suka amsa.


Wata matace fara mai kyau sai zolayata take da yarta budurwa saidai zata dan girmi Zainab sai nanike mani take irin mutanan ne masu son jama'a.

Nima saina saki jiki da ita abinci suka taho mana cike da katuwar kula shinkafa da miya da salad sai kuma wata tuwon shinkafa miyar gyada abinci iri iri daga gidaje sai zuwa ake ana mana sannu da zuwa gwanin dadi.

Gaskia mutanan Zamfara sun karrama mu,musamman yan Anka kamar wasu Katsinawa haka sukai mana kara,take naji ina kaunar yan garin har raina.

Garine mai kyau da tsari daidai gwalgwado kuma mutanen cikinta sunada karamci sosai,dole su shiga ranka haka suke girmamamu kamar yan uwanmu na jini haka suja dauke mu,sunjima gidan mu haka akaita shiga da fice muda makotan mu saidai muce Allah ya hadamu a aljanna.

rayuwa mai dadi mukeyi cikn garin ga shagunan Baba na kofar gida guda ukku cike suke da kaya kuma ana ciniki sosai alhmadulillah.


Abinci mukaci sai wanda kakeso duk abokan arzika suka kawo mana kayan sa ranata biscuit Mama tabawa maƙota aka sa albarka.

Koda dare yayi kowa yahau bisa gadon shi ya kwanta Jidda dakin Mama taje ta kwanta saboda Khadija tahau gadon ta kusa dana Zainab nawa nagefen nasu inata harkokina da wayata naji Khadija nabawa Zainab labarin wahalar da take sha agidan mijinta hakan yasa na maida hankalina kansi amman ba lallai su fahimci su nike sauraro ba kasancewa ina dann wayata.

Wlh Zainab bakaramar wahalar Muntari nike shaba dukan safe daban na dare daban ga yaran nan dake gareni ko darajar su banci ga wannan uban ciki amman haka Muntari zai kamani ya shirga kamar bani a kowa inashan bakar wahala agidan mijina kishiyoyi biyufa Muntari yai mani minene laifina Zainab mike banda shi kyau usuli minarasa amman yasa sun rainani suma har zagina suke banda azaba ba abina nasani a gidan mijina kina ganin duk aikin gidan shifa nikeyin shi koda ba ranar aikina bane wannan wace irin rayuwace muka tsinci kanmu ga halin da Umma tajefa kanta hardamu ga Umaima batanan batacan yawon banza gani badace gidan miji kannen mu da suka rage duna hannun Baba shima matar da ya auro ba sauki taita dukar mana kanne da anyi magana sai yace ba wanda ya isa ya raba shi da matar shi ga gori in Baba yana mana kince bashi ya haifemu ba wai mun gaji halin uwa wannan abu ba damuna Zainab ni wlh auren nan kashe shi zanyi nagaji wlh."

Hmm amman Nana baki ganin idan kika kashe auren ki ina zakije kinfison ki koma gida kuna fada da matar Baba.?"

Allah yatsareni ina ganin irin wannan daula ina ni ina komawa gidan mu nan zan zauna wajen kanwar uwata ina dalilin bala'i inanan kannena kuwa inna samu dama na tamake su."

Allah ya kyauta niko sai inga inma daukane ai karami ake taimakawa wanda baida yanda zaiyi bawai babba ba wanda yasan halin da yake ciki,mi zai hana adauko Ihsan."


Aaa nafsi nafsi ni nasan abinda nagani kuma nasan ukubar dana shiga ko ya'yana wlh can zan barsu ban daukar kowa nima inji dakaina baccin wannan qaddararran cikin ai da ban yarda in shekara gida zan kuma aurena in huta."

Amman kinsan komai lokacine kuma sai yayi ko zakiyi wani auren ko.?"
Gaskiane hakane nima shaidace gun Anty Amina gashi yanzun nata lokacin yayi kuma jinkiri alkhairi ada muna ganin wai Bakin Jini ke gareta ashe munyi kuskure gashi mu masu Farin Jinin munyi muna shan ukuba tayau daban ta gobe daban Allah muntuba."


Allah ya kyauta yakawo maki sauki cikin wannan lamarin."
Ameen tace tana goge kwallan idanun ta.
Ni kaiba dake sauraron su naji tausayin Nana kwarai da gaske amman ai wuya bata kisa sai kwana sun kare kuma komai lokacine Allah yakawo mata mafita da haka naci gaba da chat da fans dina wata number naga anyi mani sallama ance hi amaryar Taufiq barka da dare."

Dubawa nayi nace lafiya lau alhmdulillh.
Kin gane mai magana kuwa.?"

Aaa bangane ba."
Emojis na sad mode☹️ aka turo mani alamun fushi.
Sorry kasan sabon sim ne shiyasa."

Okay angon karni ne."
Dan shiru nayi ina nazari sai Abdallah ya fado mani araina,wani dadi ya lullubeni nace

Daddyn Mina kaine😁
Shima cikin dadi yace nine amaryar kamshi kafin ki zama ta kamshi ashe ansaka mana rana jiya na dawo daga Lagos Mama ke gaya mani."

Aikuwa ansa rana ya kasuwanci."
Alhamdulillah munatayi ya kwana biyu nayi missing aminiya ta,yanzun minene plains dinmu?"

Jiki sanyaye nace,wlh bana plaining komai banda wata idea."
Okay zuwa gobe zan shirya maki abinda nikr ganin ya kamata muyi ko.?"
Shikenan Allah kaimu lafiya."
Ameen kigaida mani da Mama."
Zasuji ina Mina da Haidar."
Mina na Caranci Haidar kuma yana wajen Mommy."
Inagaida shi.
Okay saida safe bye."
Na sauka online sai naji dadi araina Abdallah naneman taka role din Husna ta koba komai zai rage mani radadin danike a raina shiyasa banda wani hope akan bikin nan nasan da tananan tabbas danasan inda hidimar ta sauka daman Allah na kawoma bawa mafita ta kowane fanni da haka na kwanta ina tunanin rayuwa wannan kenan.

ashe gari da safe sanda na tashi harsu Nana sungama komai ina wanka kalaci kawai nayi kalallaba nikeci(wainar filawa) ina waya da Ya Taufiq yana tambayata kalar paint da za'ai mani a gidan da zai sakani.

Yayana kayi unique color wlh ko furnitures ban san color din da zan dauka ba kawai kayi color mai kyau.

Okay as u wish madam amman banda purple da pink komai za'ayi insha Allah mi kikeci."

Wainar filawa."
Aaa aci dadi lafiya yaushe zaki dawo inasan ganin kifa.?"

Yaufa kwanan mu biyu Ya Taufiq Allah garin akwai dadi."
Ohoo kin manta dani ko ni awajena daidai duke da wata biyu gaskia ina missing dinki jibi zanzo inganki."

Saika nemi izini ba ruwana."
Kina matata haba babyna.

Kyabari adaura ko? Ina masoyiyar ka kanwar ka."
Uhmm naji Baba zan tamabaya.?"
Aaa Anty Murja."

Uwar dakina kenan banda matsala sai nazo."
Allah yakaimu."
Mun jima muna fira kafin mukai sallama.....




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️

_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E19&20



Mai dilka Mama tasa aka dauko mata wani daki dake cikin falorn mu aka ajeni tafara yi mani dilka gashi kullin sai anbani hadin kaya wanda Maman Husna taba Mama itama matar tana bani nata wani ba dadi wani kuma akwai dadi harda kayan fruit akaita bani da madara aikina kenan ko abinci banci sosai sai fruits nima nafijin dadin su saboda nasan amfanin su ajikin dan Adam.

Cikin ikon Allah gyara yafara karbar jikina daman tun agida Maman Husna tafara yimani gyara ita da Anty Mubaraka shiyasa jikina ya saba da gyara fatana har glowing yake masha Allah.


Tunda muka fara yau kwana ukku kenan ko waje ban fitowa ina cikin dakin ko sallah zanyi akwai toilet tareda ita muke kwana a dakin kamshi kawai gidan mu ke saki mai dadin sanyi abincina kuwa daga nama sai madara da fruits akwana atashi yau kwanan mu biyar cif da fara yimani gyaran jiki amman kace mun sati biyu gaskia da ta iya gyara sosai.
Da yamma ina zaune Ya Taufiq yace wai Anty Murjanatu ta hanashi zuwa ganina niko abin nema ya samu sai dariyar mugunta nike mashi daman nasan da wahala tabar shi kullin sai tace ko yawan waya in rage dashi taya zata bari yazo daman da kamar wahala bakaramin haushi yajiba the first time naga fushin shi akan karamin abu dan ni aguna bawani abu bane dan ta hanashi ganina, ana magrib Mama ta shigo dakin hankalin ta adan tashe ina zira jallabiya kenan na mike tsaya."lafiya Mama."?

"Wlh matar Nazifi ce zata haihu amman ta haifi ɗa daya sai uwa tayo gaba dan Allah kije kitaimaka idan akace atai asibiti kafin aje dan ko uwar na iya mutuwa saboda sun gama galabaita."

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un."nace gyalena kawai na gyala a bayata natafi ba nisa da gidan mu jikina har rawa yake ina zuwa na iske ankira wata nurse da box din aikinta tazo daman nawa yana gida banda shi handglov nasa da face mark banda kamshi ba abinda nikeyi komai nataba sai ya sauki kamashin jikina.
Kama mani tayi muka samu ta ida haifo dayan haihuwar dire tayi shiyasa ta galabaita saidai gudan kamar matacce allura nai mata tatada nakuda saboda baki daya bata iya katabus inba sannuba dole ai mata CS bata da karfi ko kadan.

Hankalina yai masifar tashi ainun addu'a kawai muke da kyal Allah yataimaka mani dan yai gaba uwar ta juye nishi take iya karfinta tana tsayawa saida nasaka mata hannu a hankali nike janyo dan harna samu kai yafito cikin dubara saboda nagama nasama raina gawa nikeja addu'ata ɗaya kada yasha ruwan mahaifa babban tashin hankalina kenan har Allah yasa na ida janyo shi itama tana nishi rigijib ta fadi i think ta mutuma na kidime amman rayuwar dan nikeson muceta shima numfashi yake dai dai kamar gawa ko kuka yakasayi saida na sadda kanshi kasa na jijjiga shi up side down amman ba alamun zaiyi kuka ko motsi yagazayi nagama rudewa hannu nasa nadan tafka mashi bugu a duwawu ina zazzaga shi cikin ikon Allah yasaki wani irin kuka baki dayan mu mukace alhamdulillah.

Saboda munsan yanzun zuciyar shi zata rufe saboda a bude take sai jariri yai kuka sannan zuciya ke linkewa shiyasa kukan jarirai keda matukar mahaimmanci likitoci basu da kwanciyar hankali idan aka haifi baby bai kuka,sai lokacin nurse din suka fara gyara jaririn daman anfama gyara nafarkon.

Kan uwar na koma naga da daren ta saidai batada a karfi kokadan taimaka mata nayi na gyara mata jikinta sannan yayarta takaita wanka suna dawowa nasaka mata driff nace su rike akaita asibiti taga Doctor tunda gida ba kayan aiki haka aka tallabeta ita da babies din zuwa hospital dan short note nabasu sukaima Doctor din da zai attending dinsu haka suka tafi gwanin tausayi danginta sai gyaran gida sukeyi biyar daidai na koma gida,ina shigowa falor naji muryar Ya Taufiq.

Mamaki kawai nikeyi ina kallan shi, shida Ahmad zaune suna fira suma ni suke kallo kamar wata bakuwa haka suke kallona ɗan shan kunu nayi zan wuce daki yace.

"Mrs Taufiq ba magana."
Tsayawa nayi ban juyoba nace.
"Waya baka izinin zuwa."?
"My Heart."yace atakaice
Kallan shi nayi nace
"Shikenan sai anjima."

Daki na shige nasaka lock na shiga bathroom na hada ruwan wanka na watsa na shafa wata humura wadda ta zama kamar itace maina ina gamawa nasa dogon wando da t-shart na zauna ina tunanin halin da matar ke ciki ita da babies dinta,kindawo tace mani farkawar ta daga bacci kenan.

Eh ta haihu amman suntafi asibiti."
"Allah yabasu lafiya."
Ameen."
Ya Taufiq keta kwalla mani kira miscall bakwai harda text daukar hijab nayi na zira na fita zuwa falor.
"Gani."nace ina kauda kaina gefe.

"Natuba babyna zan koma tunda baki son ganina forgive me pls."
Sake daure fuska nayi nace.
"Gaskia katafi."
Amatukar mamaki yace.
"Minal dagaske baki son ganina kodai wasa kike mani."?
"Dagske nikeyi."
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un,minayi maki kiyi hakuri."
A sanyaye yayi maganar har tausayi yadan bani.

Dan murmushin gefen baki nayi nace."Ka ketare umurnin Anty shiyasa."
"OMG ta amince Ummi tace inzo Allah dagske miyasa kike zafafa abu,amman still akwai abinda ke damunki minene."?
Sanyayyar ajiyar zuciya na shide nace.
"Neighbour dinmu ce ta haihu to ansamu yar matsala shinefa nace suje asibiti tausayi tabani."

"Allah sarki, kidaina damuwa daman aikin asibiti ya gaji haka Allah yabata lafiya ya raya abinda aka haifa."
"Ameen ya rabbi."
"My Queen."
Yace.yana murmushi,nima maida mashi da martanj nayi nace.
"My King."
"Minene sirrin pls."?
A sifar zolaya yai maganar yana smile.
Kallan tuhuma nike mashi ina daga mashi kai alamun minene.

"Ur skin is so sensitive and glowing raɗa mani ba wanda zan gayamawa."
"Hhmmm."
Nayi murmushi ganin ni zaima wayo nace. "kwanciyar hankali nasamu."
Wow insha Allah zaki tabbata a cikin shi kinji tawan i love you."
"Love you too my hope."


"Amman kina baza wannan sihirtaccen kamshin kika fita waje."?
"Ehmana ai haka akeso."

Mur yasha yana tsare fuska yace.
"Bani bukata kada kikara fita waje kina wannan kamshin wlh haramunne."

"Aure gareni?wannan fatawar sai matan auren."nayi magana hankalina kwance.

"Alright bakomai yan mata aci duniya da tsinke."
"Aikuwa duniya rawar yan mata kwara muci zamanin mu."
Nayi maganar ina dariyar kasan makoshi ganin ya kule kirana mai dilka tayi nace.

"Zankoma office inzaka wuce muyi waya."
"Minal."
Juyowa nayi nace Na'am.
"Nalura So kike ki tarwatsa mani zuciya miyasa kike mani haka wulakantani zakiyi wato bankwana ma bazakiyi dani ba ko."?

Tausayi yabani girgiza mashi kai kawai nayi.
"To minene in laifi nai maki let me know wlh zan nemi afuwar ki bazan iya daukar wannan sauyin ba pls."
Kashedin Anty Murja nike tunawa kuma natabbata batasan yazoba sannan Mama bazata iya korar Ya Taufiq ba dan acewarta ai sirikine a wajen ta.

"Kayi hakuri nagaji da yawa shiyasa."
"Naji amman gobe kifito muyi sallama inhar da gaske bakomai din."?
"Allah yakaimu."
"Ameen take care."
Ciki nayi saida nabari yafita nashige dakin da ake mani dilka.

"Wai lafiya kika jima kinsan munan idan ana dilkan saida lalura ake fita ko ango bamusan yaga amarya sai ankaita gidan shi ko andaura aure dan Allah kidaina fita aikinmu na dawowa baya."

Toh nace,amman araina ina tunanin ya zanyi da Ya Taufiq inhar ban bankwana dashi ba,wata katuwar riga ta kufa mani ta zuba turare ta saketa a sannu hayaki ke tashi yana shiga cikin fatar jikina.

Washe gari kuwa da misalin karfe goma yakara doko mani kira ina gani na basar dan bakaramin warning Anty takankare maniba taji yazo Anka.

Yafi minti goma yana kirana text yai mani

_Kin kyauta Minal gudun da kike mani yakai haka zakikai karata wajen Anty bakomai Allah yabaki hakuri_

Murmushi kawai nayi wato shima saida tai mashi tas kenan hidimar gabana naci gaba dayi baki daya yau saura kwana hudu mutafi biki shiyasa aka sauya mani wani hadin acewarta idan nakoma gida humara da turaruka zan dinfa shafawa sai wani mai dazata bani tace kada inkara wata dilka wadda tai mani ta isa.

Haka mukeyi step by step ina mamakin matan SUKEZA sudai basu san komai sai kayan mata iri iri Original da Fake duk gasunan saidai addu'a.
Nima nashaida amman ni dilka nasha sai kuma kayan fruit bakomai take dirka mani ba.

Haka rayuwa ta kasance a Anka komai na tafiya normal kuma ba laifi nasamu kawaye harda kanwar matar Nazifi mai haihuwa tace zata bini garin mu Zuwaira sunanta jibi ake sunan babies sunci suna Abdulhamid da Abdulhakim.


*******
_Kano_

Ba laifi Hafsat tasamu sauki hatta kurajen sun disashe bakamar daba tazama mumuna komai a darare takeyin shi kana ganinta saita baka tausayi kamar ba itaba duk masifa da bala'in ta sun zama tarihi ta biyu wajen su Magajiya.

Tasha wahalar su cikima take kotayi laifi ko batayi sai anzaneta da safe hakama da yamma jikinta duk duka tayi duhu baka taba cewa tasan wani abu waishi hutu a duniya."

Raban da taci abinci mai nauyi harta manta a duniya anshewa su Mairo keyi yanzun ana bata tun a hanya take hannu baka hannu kwarya tacinye shi inta dawo empty da kwano suyi mata dirkar tsiya dan dolenta zata dinga basu hakuri kuma tai masu tausa har sai sunyi bacci itako tana ganin gadonta saidai tayi laying bisa siminti ta kwanta ko kwali Cankwai bata bari tasa banda kwari kanana suita binta tashiga rayuwa mai tarin kunci a gidan Yari ga tarasa albarkar iyaye ga alhakin data lafka banda hakkin rai data daukarwa kanta uwa uba ga miji ya saketa a wulakance abu sama da ashirin summa Anty Hafsat yawa dana sani tayi harba adadi intace zatayi kuka botikin elephant Cankwai kebata tace saita cikashi da kwalla inba hakaba tasa adageta ta zaneta shiyasa bata yarda tayi kuka agaban idon su sai dare ya tsalla inta kwanta tasha kukan ta abar tausayi.

Gashi abinda Magajiya ta tsiri yimata saita bari angama aiki anzauna inuwa saitace kunga wannan itace tai silar zuwan Dago gidan Yari kuma itace tabada kwangila sawa Dago guba a cikin abinci Allah yasa bata mutuba anajin haka zasu fara dungurinta suna zaginta harsai Gandirobas sun kwace ta suna sai sun illatata tunda tajama Dago sharri.

Haka Hafsat takoma mujiya a cikin tsuntsaye yauma tana kwance cikin dare tana kuka tace."Wane irin farin jini ke gareki Aminatu naso inga rayuwarki ta kaskanta ta wulakanta ashe ramin muguntar da muke ginawa mune zamu afka aciki Allah ya isa tsakanina daku Junaid da Mufida insha Allah duk inda kika shige a cikin duniyar nan kema sai kin dandani azabar dana sha bani fatan a kasheki a take inason kiji mi akeji agidan Yari."

Kuka tayi shi harba gobe tarasa ina zata saka kanta taji sanyi bala'in da takeji,wannan kenan.


** ** **
Bayan kwana biyu mungama shiri zamu koma CRC nida Mama sai Zainab da Khadija da Auta.

Sallamar mai dilka Mama tayi ta hada mani wani ruwa ajarka da wani sabulu tabani sai kayan humura kala biyar da baka ja sai farar humura da wani hadi na madarar turare duk ta hada mani sannan ta tafi kawayen danayi su wajen shidda sai ya'yan Alhaji Tijjani Bungudu su biyu suma sukazo gobe dasu zamu wuce sai makwabtan mu matan aure aminan Mama guda ukku suma zasubimu banda wa'anda sai ana gobe daurin auren zasuzo ranar gidan mu ya cika da bani Adam haka mukaita fira da daddare dasu.
danko Ya Taufiq tunda ya tafi bamuyi ban kwana ba yake fushi kona kirashi zaice lafiya?
Innace nabugo inji lafiyan shi a dakile zaice mani badamuwata bane yana da abinyi zai kashe wayar shi saina fara damuwa nayi dana sanin biyema umurnin Anty Murja so nike inkoma gida nasan zaizo ya ganni haka na kwanta ba dadi araina karfe tara Abdallah ya kirani dagawa nayi yace.

"Gobe idan nadawo zaizo gida mugaisa kuma yasa za'aimani

Please Login or Register in order to submit comment