Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fatana kada surukaina susan ban lafiya saina samu kaina inajin kunyar su.
Kira na biyu Ya Tariq ya daga."hello Ango kasha gara yakake ya amaryar tamu."
"Fine Hassan number Dr Nasiba nike bukata pls."
Dariyar shakiyanci yayi mashi yace ."Kace kayi aika aika illar tuzuru kenan ai."
Sosai yake ma Ya Taufiq shakiyanci nidai kunya takamani ina kwance bisa cinyar shi inajin komai suke cewa."
"Naji yanzun dai matsayin mu daya nazama magidanci pls Tariq turomani ita."
"Sorry tana Engla amman zan turo maka Dr Aziza insha Allah."
"Okay thank you Dr."
"Agaida mani da kanwar tawa sai munzo dubiya."
Kashe wayar yay, a shagwabe nafara kukan kissa nace.

"Kagani ko yasan abunda yafaru wai har dubiya zaizo."A kidime yake bani hakuri."sorry Baby kinaso inyi kuka bansan kukan nan yana hurting dina bari ince bamuso kada yazo kinji."
Shikenan."
Kiranta yayi waya ya sanar mata tace cikin 30mint zatazo insha Allah.

Bai jima da wayar ba mukaji anyi parking mota kallan juna mukayi ta window ya leka da sauri ya dawo yace."Inna ce Aminatu itada Anty Samira."
Inalillahi wa'inna ilahirraji'un nace jikina yahau bari kuka nafara nace.
"Asirina ya gama tonuwa Ya Taufiq ya zanyi."?
"Calm down zance baki lafiya ne zazzabi ke damunki."How bayan ka kira likita zasu gane."
Cikeda damuwa yace.
"Kiyafe mani Minal bansan haka abin zai kasance ba kidaina damun kanki pls."
Door bell mukaji da kyal yasamu nadaina kwalla ya sauka inajiyo shigowar su tana."ɗana ansha kyau masha Allah ina yartawa take tunjiya naso inzo mugaisa to nayi busy gashi yau zan koma gida."
"Oyoyo Innata takaina sannun ku Antyna ina kwanan ku."
"Yawwa kira mana Aminatun mana.?"
Sosa kai yayi yace.
"Zazzabi ke damunta bazata iya saukowa ba."

"Kamarya wane irin zazzabine kamar dai mai kwaikwai ai zazzabi bazai hanata saukowa ba muje dakin."
Inna..."kaga Hussein bani hanya inga lafiyar ya'ta."
Nidai na gyara kwanciyata sai addu'a nikeyi nagama tsurewa.

Dr Aziza ta shigo tareda Anty Samira Anty Murja na zaune gefena ko hada ido dani bansan anayi,inaganin Dr nakara shan jinin jikina.

"Aaa wannan wane irin ciwone harda likita sannu Aminatu gaskia kinajin jiki."
Saidai musaci kallan junan mu nida Ya Taufiq narasa yanda zanyi.
Hawowa Dr tayi ta zauna tace."Sannu Mrs Taufiq insha Allah zaki samu sauki kinji."
Kallan su tayi tace.
"Inasan dubata inba damuwa."
"Zazzabin harsai munfita kudai bokayen turawan nan kuncika abubuwa wlh koda yake itama duk kune jirgi daya ya jidoku."Cewar Anty Murja
Shidai Ya Taufiq a sanyaye yafita ko magana ya kasayi.
Banji wata kunyaba Dr tadubani sai jinjina kai takeyi.
It's internal injuried bamu bukatar dinki becouse ba kari saidai zakina bukatar hutu kona sati biyune sannan kisamu wata tazauna dake zan baki Suppliment."
"Okay insha Allah Dr."

LKiran Ya Taufiq tayi ya shigo tace.
"Ur wife need some relief for two weeks sannan dole asamu mai zama da ita tana kula da ita ga list na Suppliment kasiyo mata."
"Aaa Dr ni zan kula da matata ban kukatar kowa."
"Aaa wannan sai mace Arthector Taufiq kayi hakuri."
Musu sukafara har Anty ta shigo shi yanakin hakan ne dan yasan bansan kowa yasani ita kuma tana nuna mashi amfanin hakan acewarta zataima Mum magana yanda ta fahimta kamar bazamu iya maganarba munajin kunya ne.

"Lafiya mikefaruwa."Anty Murja ta tambaya.
"Bakomai yace.
Doctor Aziza tagaya mata komai tas.
Dan murmushi Anty tayi tace.
"Aiba matsala indai wannan ne Dr ni aikin ni nike ko gida nakoma bawani abu zanba daman kanwar Babanmu mukazo dubawa a zariya shine na wuta ganin ya'yana kisha kurumun ki ni zan zauna imma gida zamu koma duk dayane."

"Aaa Anty pls kiyi shiru dan Allah."
"Mai garin ku nace."Dakuwa tai mani.
Godiya taima Dr nanfa Anty taitai tarairaiyata kamar kwai badan Ya Taufiq yaso ba ya kyale Anty waya tayi aka biyota da kayanta na tabbata Mum taji abinda ke faruwa,abinci kuwa dagacan ake aiko mana dashi kulawa ta musamman Anty kemani.

Har mukayi sati alhamdulillah na warke amman Anty taki tafiya tafara yimani gyara nidai harna gaji sosai nike shan gayara ko minti goma bata bari inyi da Ya Taufiq bawan Allah harya fara damuwa da lamarin.

Yau kwanan mu goma da Anty Murja nidai nasan na gyaru jikina ya gaya mani hakan nima nafara bukatar mijina amman Anty tazamar mana lalura kai kace ba muharaman junaba daya fara magana tace bata warkeba sati biyu Dr tace,dole yasa ido har yar rama saida Ya Taufiq yadanyi haka nima ji nike ba dadi araina yaudai kwanan mu shabiyu raban da mu kebe da junan mu.
Ina chat naga yai mani magana da sauri na bude.
"Hi My life am tight i cant live without you pls help me i need u more Minal."
"Anty Murja tahana."
"I beg karki dauki hakkina dan Allah kizo dakina pls." Emojis na beging ya turo mani ,kiyawa nayi ina sake dubawa ya sake turo mani Emojis na tausayi."Karta ganmu Ya Taufiq kai hakuri saura kwana biyu fa."
I" cant Minal kinsan mine bazatace mana komai ba wlh wai haramun zamuyi nidai nagaji haba."

"Ki aje wayar nan hakanan Aminatu kina bukatar hutufa."
Sauka nayi ina dalla mata harara a kaikaice.
Koda dare yayi Anty tanata bacci na zame sai dakin Ya Taufiq kamar jira ya taroni ko zama banba mukahau farantama cikin kankanin lokaci mun afka duniyar mantuwa kiran waya mukaji inasan induba mai kira ya hanani haka mukaita farantama junan mu rai saida muka raya daren aranar albarka kuwa shata wajen mijina sai banji zafin farkoba atakaice saidai aka kira asuba muka tsarkake jikin mu sannan ya tafi masallaci sadab na koma daki inajin karar ruwa toilet na leme cikin blanket inajin fitowar ta tana bubbugani kamar mai bacci na tashi wani kallo ta aika mani na sauke kaina kasa tace.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E37&38



"Yanzun ke Aminatu har kinsan dadi miji?shine zaki kwashi kafa wai dan kinga ina bacci zaki tafi turakar miji ko."?
Sosa kaina nayi nace.
"Anty bacan naje ba cikin dare kishi yakamani sosai da yunwa shine naje kitchen nasamu abinda naci."
A kitchen din kika kwana kenan.?"Aaa Anty dakin kasa na kwana sabida nagaji shiyasa."
"Aminatu ni zakiyima wayau duk abin nan da nikeyi duk danjin dadin kune baki dayan ku,amman ni zakima wasa da hankali bayan agaban idon ki Dr tace sati biyu zakiyi sannan ki warke."Anty ba haka bane wlh..."yiman shiru nasan maganin ku da jibi zantafi inanan zama daram inga ya zakuyi dani tunda ku ya'yan zamani bakusan ta ido ba."Araina kuwa cewa nayi ba abinda zamu fasa."Magana kikeyi."?
"Aaa Anty daman sallah zanyi."
"Ayyo aiban hanaki ba."
Tashi nayi nasaka hijab nayi sallah lazumi nahauyi najima sannan na mike gaidata nayi na koma na kwanta dan nagaji sosai bacci ya daukeni.
Bani natashi ba sai karfe goma na safe wanka nayi na shirya cikin shadda doguwar riga na daura kallabi,sakkowa nayi zuwa dining dake ƙasa.Tunda na tunkaro wajen angon nawa ke mani kallo na musamman nima shi nike mashi anko muka buga na shadda iri daya kallan mamaki takemana tana."masha Allah zuciyar ku iri dayace komai naku iri dayane Allah yakara hada kanku."
Ameen muka amsa.
Batasan shiyai mani text ba ya gaya mani kalar shaddar daya keson insa shiyasa mukayi anko.
"Dan haka dole kusan yanda zaku tsara rayuwarku kuma ku kara dagewa da addu'oi na safe da yamma."
"Insha Allah inna."cewar Ya Taufiq.

Abinci na zuba nahauci faten ashir nasa da kifi ina sha sosai naci Anty ta mike tayi dakin kasa.
"Ta tambayeki inda kika kwana."?
"Eh."nace
"Inna rigima tasan ai baki wuce wajen mijin ki ko."?
"Kaima kasan rigimar Anty sai Allah."

"Uhmmm Hussein wancan dakin nan nikeson dawowa da zama zan kara hutawa kona sati biyu ne"
Kallan juna muke cike da mamakin Anty."Inna i think gobe zaki tafi gida naga aita warke ko"?
"Iyyeh lallai yauni kake kora agidan ka ko Hussein."?
"Ba haka bane inna kiyi hakuri Allah yakaimu saiki zauna."Yai maganar rai hade ko murmushi baiyi.

"Aaa nafasa ai tunda harkai mani musu da farko bazan zauna ba."
"Haba Inna bansan mi zance maki ba nace ki zauna ni ban isa in hanaki zama ba."

"Uhmmm Allah ya kyauta zamani kenan."
Mikewa yayi yace.
"Zanje wajen aiki saina dawo."Kallan shi nike nidai nasan ba wajen aikin da zaije dan yanzun amman mi zaisa shi fita.
"Allah ya tsare yataimaka ya bada sa'a"Ameen ya amsa bisa labbansa.
Allah ya tsare nace, kallona kawai yake harya juya zaifita.
"Tashi kikayi zaune mijin nakine bazaki rakaba komi kingane mani sakarcin banza."
Daman naki tashi ne gudun tsagumin Anty amman sai gashi da kanta tace inyi mashi rakiya.
Ajere muka fita gar alott gefen mota muka tsaya nace."My hero har angamacin amarcin zaka fita."Ba dole ba inna tai kane kane wai kinjima dawowa zatayi haba nidai zata takura mani"
''Haba mijina hakuri zamuyi minene aciki."?
"Nidai bazan iyaba dan haka next week zamu wuce Turkey kishirya yakamata insan abubuwan da Company ke ciki gaskia zamu koma can da zama."
"Nidai bansan inyi nisa gaskia."nace amatukar shagwabe.
"Haba Babyna kidaina cewa haka zamuyi magana anjima kije ciki kada Inna tace bina kikayi tunda na samu yar C.I.D a gidana."
Dariya nayi na juya ina waving dinshi ya shiga ciki,shi kuma ya shiga mota yai company.



_KURMAWA_


Masu gari ne da kansu Sarauniya Magajiya (Cankwai) keta dirkar Mami kamar Allah ya aikota datafara ramawa amman kunsan ance ko a gidan giya akwai babba kuma ance babba da babban shi dole Mami ta saduda musamman yanda magajiya tasa aka dage mata ita tanata labta mata katon icce sai wulle wulle take tana rakaka ihu itako bata fasa bata kashi ba tana kiran zaki kara.
"Bazan karaba kada kikashe ni natuba nabiki zammaki biyayya Sarauniya."
Duk da hakan bata fasa zanetaba gashi ma'aikatan wajen duk basu kusa sai yan Click din magajiya wanda a halin yanzun Hafsat na cikin su duk da hakan har yanzun Cankwai cikin gana mata azaba take acewar munafuka ce,kuma ita bata ba munafuki har abada sai lamarin ya baka tausayi.

Itako Mami ta bugu kamar ganga harda fitsari saida tasaki tsabar azabtuwa da tayi,tayi bakikkirin da ita kamar mai HIV tagama lalacewa abin saidai dua'i amman tagama fita hayyacin ta, ta fige kamar bakar tantabara sai lokacin tasa aka saketa ta fadi kasa wabar tana maida numfashi sama sama itako Magajiya taci dubu sai ceto wadda ta kwashe shekaru aruaru a gidan ɗan kande ba kalar yan iskan da bata ganiba da fetsararru duk tayi karo dasu anbuga da ita anbarta hatta ma'aikatan gidan saidai rarrashi duk da kuwa wannan gidan yarin shine gida na kusa goma data zauna wanda yake shine parment dinta shiyasa kowa yasan Magajiya kuma dole kai mata biyayya koda kai mata biyayyar ma indai jinin ku bai haduba zata tsaneka ruwama saiya gagari mutun sha ko tari mai karfi mutun yayi zaisha kashi,haka takema Anty Hafsat tunda taji labarin case dinta tace munafuka ce ashe sune sukajama Dago sharri shikenan ta daura mata karan tsana dukan safe daban narana da dare daban gado kuwa bata taba kwanan shiba saidai kasan sumunti jikinta duk ya jeme yai bakin kirin dashi ga lalura tana fama da ita sama sama.

Itako Mami ba dakin su daya da Cankwai ba amman taba yan iskan gan kwangilarta har sunfi Cankwai zalinci itama kullin cikin ukuba take, bata bacci sai kowa yayi kuma ƙasa take kwana ɗan dining dinta a amshe mata yunwa duk tafara mata illah abinka da yar hutu sai ya zamana kamar tayi shekaru biyar a gidan Kaso duk ta lalace ta watse jikinta kuwa yagama jemewa da sahun bulalai abindai ba acewa komai.


Yau lahadi Mama sukaje ma Anty Hafsat visting ita da Khadija sai Umaima da Dada har gidan yarin sukaje sukayi sa'a aka basu izinin ganin ta, tana zaune abin duniya ya gama isarta sai kuka take akace Hassu da haka Cankwai ke kiranta shiyasa kowa na gidan kecewa haka,kizo ana kiran office din Oga.

To tace ta tashi a hankali take tafiya kana ganinta kasan ita kadai tasan azabar da takeji cewa yayi kije minti goma sha biyar wajen da ake ganawa da baki.

tana isa ta tsaya tana ganin mahaifiyar ta,yar uwarta da ya'yan ta,tun kanta iso ta kece da kuka mai sosa rai ta isa gunsu suna hangen ta saboda yar karamar katangar data rabasu amman zaka iya kama hannun dan uwanka,aikuwa ta riko Dada tahau kuka tana.

"Dada kiyafe mani naga rayuwa naji abinda akeji a wannan waje,nagane lallai Allah ba azzalumin bawa bane nayi danasani iya danasani inama ace banga wannan lokacin ba,duniya taimani atishawar kare!duniya tai mani daurin goro! ashe isa da gadara ko zalinci basu taba dawwama komai da nashi lokacin yau gashi ni Hafsat nice garkame a wannan gidan mai tarin kunci da fargaba Dada kali fatata yanda ta jeme ta lalace komai nawa ya koma baya,daman annabi yai gaskia da yace zalinci da azzalumai basu taba dawwama hakama wuya bata taba dauwama, karya fure take bata ya'ya sannan ramin mugunta yakan juye damai shi nidai gashi na afka cikin shi Dada kidubi girman Allah kiyafe mani kona samu incika da imani."

Sosai Hafsat ke kuka mai taba zuciya,suma su Dada kukan sukeyi tagaza magana sunjima sannan ta riko hannun yar tata tace.

"Nayafe maki Hafsatu duniya da lahira tabbas kin jefa zuciya ta cikin kunci nayi kuka ba iyaka duk a dalilinki ya'ta har kikaini karshe nayi tsunuwa agareki amman daga wannan ranar kullin da tausayinki nike kwana nike tashi araina na rokar maki Allah SWT ya yafe maki kurakuren ki ya'ta nima nayafe maki duniya da lahira."
"Nagode maki Dada Allah yasaka maki da alkhairi."
Ameen suka amsa,sannan tajuwo wajen Mamar Amina tace."Khadija bansan taya zan fara neman afuwarki ba kanwata na zalince ki,ada kinsan na soki na kaunace ki ban fatan inga bala'i ko musiba sun tabamin ke Khadija kema shaidace duk wanda yasan Khadija da Hafsat yasan soyayya mai karfi sukema junan su saidai kash shaidan yai tasiri a cikin zuciyata hassada da bakin ciki suka darsu araina dan kawai naga kinfini wadata bayan ada nice sama dake sai ya kasance kidin hadimata ce bayan nasan ba abinda ke dauwama arziki ko talauci basu dauwama kowa danashi arzikin amman na butulcema mahaliccina, na manta duk ni'imar da yai mani dan kawai nasamu sauyin yanayi namanta wanda ya jarabeni shine ya azurtaki dan yaga imanin mu amman na manta wannan ilimin nazama jahila ina yaki da ikon Allah gashi nafada a halaka na tsaneki da zuriyar ki alhalin bakuyi mani komai ba kullin burin ku, ku kyautata mani ni kuma kullin burina inga kun tagayyara ashe kuwa nidin ce zan tagayyara bayan Allah yazama gatan ku nifa? Khadija kidubi girman Allah kiyafe mani dan Allah kanwata."
Kuka sosai Maman Aminatu keyi tana tausayin halin da yar uwarta, ta kasance.
"Nayafe maki Antyna har abada bazan iya fadan munanan kalamai akanki ba kullin fatan alkhairi nike maki yar uwata ban taba kwana dakeba araina ko in kullaceki nasan koma minene kidin kin soni kin kaunace ni,yanayin rayuwane kawai ya maidamu haka,inada yakini ada ba wanda yakaini dacen yar uwa mai sona,wadda take sadaukarwa da gabata agareni duk kece Anty,sai yanzun dan soyayya ta zama kiyayya zan gujeki kullin inasawa araina zaki dawo gareni gashi kuwa Allah ya amshi addu'a ta dan haka nayafe maki Anty kisa aranki baki taba yima Khadija komai ba arayuwar mu ina kaunar ki Antyna."
Sharema Khadija hawaye Anty Hafsat keyi tace.

"Kayya Khadija kidaina kuka karki manta tun muna yara nasha gaya maki wannan kalmar bazan taba bari hawayen ki,su sauka a doron kasaba indai ina raye yauma na kuma maimaita maki wannan kalmar kanwata kidaina kuka nagode maki da kikayafe mani,nikam banda bakin da zance nayafe maku domin baku taba yimani komai ba Allah yabar zuminci Khadija,ina roko kicema iyalan ki su yafe mani."

Girgiza kai Mama tafarayi tace."Anty ya'yana sunyafe maki kefa uwace garesu karki manta wannan kidaina damun kanki dan Allah."
"Aaa Khadija karki arar masu baki kici masu albasa musamman Aminatu yanada kyau tayafema Hafsatu abubuwan da tai mata da bakin ta kamar hakan zaifi ni anawa tunanin kenan."
"Shikenan Dada amman sauran ya'yana sun yafemata ba aran bakin su naiba hatta mijina."
"Nagode yanzun ina Aminatun take."?
"Tayi aure Umma."
Cewar Khadija dake kuka.Jinjina kai tayi tace.
"Ashe dai Mufida bata zauce ba dagaske take Aminatu tayi aure kuma Taufiq din ta aura kodai zaucewa tayi."?tayi tambayar da matukar mamaki a fuskar ta.
"Wlh Umma dagske Ya Taufiq ta aura bata zauce ba."

Maida kallan ta tayi sama tana kallan sararin samaniya tace."Allah mai iko Sarki buwayi gagara misali Sarki mai lokaci kuma yana rantsuwa da lokaci sannan komai bai wanzuwa sai lokacin shi yayi tabbas duk abinda bai faruba a duniya to lokacin shine baiba amman idan lokacin shi yayi ba makawa saiya faru na yarda abinda ya hanani mutuwa shine ya hana Taufiq da Aminatu aure da wuri,ba wani bane,wato lokaci Allah natuba kayafe mani akan jayayya da kudurin ka da muka dingayi akan hassada wadda ga mai rabo takice inai maki fatan alkhairi Aminatu tabbas ni Hafsatu nayarda komai Lokacine Dada."tagama maganar tana kallan mahaifiyar tata.

"Hakane ya'ta Allah yasa mudace ya yafe mana baki daya."
Ameen suka amsa baki dayan su.
"Umaima,Khadija kudaina kuka kune manya ku dauki qaddara sannan ku rike Khadija matsayin uwa kamar ni nahaneku da bakin ciki da hassada musiba ne sannan kamar karmami suke suna cinye kyawawan ayyuka suna maida zuciya tai tsatsa ina mai yimaku nasiha kuji tsoron Allah kuyima zumunci hidima komai zakuyi kusa aranku dan Allah kukeyi shine ke sakawa mutane da alkhairai kunajina."?
"Eh Umma insha Allah munji,daman ni yanzun ina hannun Mama."cewar Khadija.
"Auren naki fa."?
"Ya sakeni Umma ga cikin nan damman na kusan haihuwa."
"Allah ya zama gatan ku yayafe maku kurakuren mu baki daya,duk alhaki ne kebibiyar mu, saidai kunyi hakuri ku dauki qaddara kuna neman gafarar Allah insha Allah zaku samu sassaucin rayuwa."Allah yasa Umma sukace suna riko hannun mahaifiyar tasu,dafa Mama Anty Hafsat tayi tace.

"Khadija nagode maki da kika rike mani iyalina amana Allah yabar zumunci."
"Ameen Antyna."
Shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa aranshi kafin tace.
"Umaima kucema mahaifin ku yataimaka yakawo mani ziyara inason ingana dashi kinji."
"To Umma insha Allah zamu samu yazo yaganki."Toh idan ma yaki zuwa nidai kuce yayafe mani."
"Umma insha Allah zaizo."araunane sukayi maganar.
"Allah yasa Umaima."
tace tana kuka mai dauki da tarin bakin ciki da nadama dan tabayyana a fuskar ta.
Sako suka bata abinci da kudi sannan sukai mata sallama kowa na kwalla haka suka baro Anty Hafsat ba dadi aransu,wannan kenan.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_



Komawa yayi ya zauna Alqali yace."Kotu taji koken ka Barr Hashim saida amsa laifi da Ahmad yayi bashi ke nuna laifi zai rataya kanshi ba kai tsaye duba da kare rayuwar shi yazoyi har hakan ta faru saidai idan shaidar dayake ikarari yanada ita batada wani mahimmacin da zamu iya wankesa sannan laifin kisa ya tabbata ga Ahmad,amman Kotu mai adalici ce zata duba kowace hujja yanda yakamata,sannan wannan shine zaman karshe da wannan Kotu zatayi akan case din kisan da kaiwa Jamilu Adam,sannan next week zamu dasa zama Shari'a akan zamba cikin aminci dacin amana da Bilkisu Bala tayima mijinta Alhaji Kabir tareda yaronsa Ahmad Musa insha Allah."


Banda faduwar gababa abinda Zainab da sauran dangin Ahmad keyi musamman dasu Abbas suka dawo daga dauko shaidar da Ahmad zai gabatar wadda itace matakin farko dana karshe dan kare kanshi,kowa yai shiru musamman Barrister Aliyu fatansa kaninsa Ahmad ya kubuta daga halaka maganar Alqali ta katse mashi tunani ta hanyar cewa. *BANIBACE* kenan wanda yake dauke da rikita rikita da katamurmura mai ban mamaki maza garzayo ki nemi naki danjin yanda zata kaya akan Naira 300 kacal idan kuma harda _Daukar Fansar Budurcina_ kikeso tuntubi wannan Number danjin yanda zaki biya 08160508316 *Daukar Fansar Budurcina da Bani bace* 1&2 ne danjin dadin karatu _Yar Mutan Kankiar ku ce_ dai wadda tasaba nishadar daku da fadakarwa sayen nagari maida kudi gida🥰



S5/E39&40


Wasa wasa saida Anty Murja takara kwana ukku muna tare da ita, ranar da Anty zata tafi gida da kanshi ya sai mata ticket ya rakata har Air port haka ta tafi Katsina.
A bangaren Mum kuwa da kanta take aiko mana abinci sau ukku a rana.
Break fast,Lunch and Dinner banda kayan makulashe,hakama matar Ya Tariq itama kusan kullin saita aiko mana da abinci.
Haka rayuwa ta kasance kulawa mukeba junan mu ta musamman kowa na kokarin faranta ran ɗab uwan sa.
Akwana atashi har munyi wata ukku da aure kullin ƙara shaƙuwa da juna mukeyi da soyayya mai tsari mukema junanmu.
Yau muka shirya mukaje gidan Mum yini shine fitata tafarko tunda nai aure idan mun fita saidai idan Park mukaje shakatawa ko wani Mall shima bayan isha'i muke dan fita sai yau da mukaje gaidasu Mum.

Tunda mukaje Mum da Abba ke bamu kulawa ta musamman kamar wasu baki haka sukaita riritamu musamman haka Abba ya siyo mani kayan makulashe iri iri sosai nikejin dadin zama da sirikan nawa.
Sai bayan la'asar mukayi shirin tafiya gida haka Mum ta haɗani da kayan gargajiya su Magarya,Taura,Goriba,Kurna,Aduwa da sauran abubuwa iri iri na na gargajiyawa.
Haka suka rakomu har saida sukaga tafiyar mu suna mana addu'a.
Gidan Ya Tariq ya ajeni kasancewar ankira shi Company akwai abinda zaiyi.Nan muka dasa fira da Anty Aisha gwanin burgewa mun zama yan uwa sosai ranar can na wuni saida akai isha'i sannan suka shigo gidan tare da Ya Tariq.

Nan mukahau fira sai karfe tara na dare muka koma gida,aiko duk na gaji wanka kawai mukayi na kwanta shima ya kwanta da haka bacci mai dadi ya kwashe mu cikin kwanciyar hankali wannan kenan.

Bayan sati biyu sosai kulawa ta musamman Ya Taufiq ke nuna mani haka nima ina bawa mijina kula yanda ya kamata yau yaje office tunda misalin karfe goma ya tafi ni kadaice zaune gidan nayi jigum narasa abunyi ga kallo na kunna inayi amman badan ina fahimtar abunda nike kallo ba,daukar wayata nayi nahau yin game,kamar daga sama naji sallamar su Fatash itada Zakiyya sai ya'yan su,wani irin dadi naji ya ziyarceni oyoyo nai masu sai murna nike baki dayan mu,muka zauna saman kujeru kowa sai fara'a yakeyi.
Kawata kinga madarar kyawun da kikayi kuwa gaskia ne Aminatu Yayana ya iya kiwo Allah dai yakawo kazantar daki musha suna."
Dalla mata harara nayi bance komai ba nasan halin Fatash zataita nanata maganar ne.
"Aikuwa Fatash nima dai ina tunanin da alama mun samu ƙaruwa Allah mungode maka zamuga jinin Ya Taufiq a duniya."

Zakiyya ta ida maganar tana murmushi.
"Uhmm sai akace maku ciki ne dani ohnni ya'su naga ikon Allah wlh Zakiyya kada kibiye ta Fatash zata kaiki tabaroki."
"Aaa wlh dagske nikeyi kamar mai shigar sabon ciki sai glowing kikeyi dole zamuyi murna."
"Hmmm naji dai tashi muje kitchen kikawo maku drinks."
"Lallaima Minal muna baƙin sai kin samu aiki dan kirki dayai maki yawa."Wani kallo nai mata nace.
"Ko?su baƙi anji jiki,sha zamanki kinga baƙi kuwa."
tafiya mukayi kitchen muka hau girki pride cus-cus mukayi fari da kayan lambu su carrot green beans da albasa sannan mukayi Sos da kifi a ciki dining Fatash ta dinga kaiwa tana jerewa sannan na haɗamana Mango and Pine apple juice mai aikin da Mum ta aiko mani jiya Malliya ita tahau kimtsa kitchen komawa mukayi dining mukafara cin abinci muna fira dasu Zakiyya baki taba cewa ubansu daya da Fatash sun haɗe kansu sosai bakamar sadda Mami ke gidan su ba.

Sallamar Ya Taufiq mukajiyo kamarin falor yara suna.
"Oyoyo Uncle."
Shigowa yayi dauke da Mus'ab ɗan Zakiyya direct dining din ya wuto dasu sannu da zuwa sukaima yayan nasu,yawwa ya amsa ya zauna kujerar dake facing dina yana sakar mani wani tsadadden kallo mai sakani natsuwa nima kallan shi nike tareda sakin smile a saman fuskata.
"Sannu da zuwa."
Nace ataikace bai amsa niba yace.
"Fatash kinji kawarki ko."Ɗan zaro idanuna nayi waje nace.
"Mi kuma nayi."?"Kinga yanda take tarbar mijin ta wai sannu da zuwa."
Murmushi sukayi baki ɗayan su."A gaskia Anty Minal bamu son haka akaraba yayan mu kulawa ta musamman."
Nidai murmushi nike masu nace."Fatash badai son kaiba naji mai yaya."
Dariya mukayi.
"Wife ya aiki hope bake kikai wannan girkin ba."?
Girgiza kaina nayi nace.
"Ba abinda nayi."
"Lah amman ba ruwana."cewar Zakiyya
"Ita tayi shi ko."?
"Aa bakajin mutuwar Sarki bakina."
"Zangane dakaina ai."
Yai maganar yana daukar wayar shi da alama da Anty Murja yake magana sunjima sannan yayi mata sallama.

Zuba mashi abincin nayi na aje mashi sannan na zuba mashi drink a glass cup.Latsa wayata nafara amman hankalina kaf nakan shi.
Kallan flat din yakeyi yaki cin abincin,dariya nike guntsewa dan nagane nufin shi.
Anshe wayar hannuna yayi sai lokacin na kalle shi amarairece nace.
"Pls give me my phone."
"Yunwa."yai maganar yana dan lagane kai.
Satar kallan su Zakiyya nayi saidai hankalin ta bai kanmu banda sa'idinawa su Fatash.

Shiko ya langabe kai kamar wani karamin yaro ko kunyar kannen shi baiji dan dole

Please Login or Register in order to submit comment