Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

order din abinci kada muyi nida kawayena duk zaikawo mana da drinks.
Naji dadi sosai godiya nahau yi mashi yace bakomai yima kaine da haka mukayi sallama inajin firar su Zuwaira sama sama har bacci ya daukeni.

Washe gari karfe bakwai kuwa mungama kimtsawa munyi kalaci kowa ya fiddo kayan shi ansa a boots mota biyar mukayi awadace daga Anka har gida Baba ya biya komai,daya ce kawai ta gidan mu saura shata yayi mana haka muka tafi yana mana sallama cikin aminci har muka fito Anka mukahau titin zuwa Katsina.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E21&22


A wajen JJ tunda aka akishi gidan yari abubuwan duniya sukai mashi cinkus komai ya mashi tsaye duk watannin daya kwasa a yari banda azaba da wahalar rayuwa ba abinda ke dawainiya dashi matar shi tazo mashi ziyara ita da ya'yan ta guda hudu biyu mata biyu maza,suna zuwa akira shi yana zuwa suka gaisa cikeda tausayawa matar tashi ke kallan shi banda kuka ba abinda takeyi haka shima daya rike yarsa yana tsananin jin tausayin su.

"Ina Amira."? Ya tambayeta araunane.
Kukane ya kubce mata tace.
"Tarasu yau wata biyu kenan." wani irin abu ya soki zuciyar Junaid yace.
"Miya sameta Zainab."?

"Fya fya.....a raunane yace."kiyi mani magana mana."?

"Fyade mai gadin gidan mu yai mata sannan ya gudu shine silar mutuwar ta." a razane Junaid ya tashi tsaye yana zubewa kasa ya saki uwar kara da kuka mai sosa zuciya,hakan ya janyo attention din Adam da duty ya dawo dashi side din maza yace.


"Baiwar Allah taya zakizo ki daga mashi hankali bayan halin dayake ciki."?
"Ba daga mashi hankali naiba yarsace ta rasu."
Ya tausayama halin da Junaid ya afka shiba mutuwarta ke daga mashi hankaliba fyaden da mai gadin gidan sa yaima yarsa shine babban tashin hankalin shi Oga Adam yace amaida shi daki dan ya huta,a kidime ya dago da rinannun idanun shi yace.
"Barni Adam kaicona da ganin wannan rana Zainab abubuwan dana dinga yima ya'yan mutane shine yadawo kan ya'yana fyade fa kikace akaima Amira harta rasa ranta amman Muntari ya zalince ni Allah ya isa wayyo Amira ni naja maki Allah ya jikanki,Zainab kiyafe mani domin nasn bakisn halin da kike ciki tabbas inafama da lalura shiyasa kikaga na lalace nayi baki ankaini asibiti anmani gwaji inada cutar Kanjamau (HIV AID) kema natabbta kinada ita da Amir saboda shine haihuwar mu ta karshe ku yafe mani na cutar daku dan Allah Zainab."


Ba Zainab ba hatta Adam saida ya mike tsaye jin ashe harda iyalinsa ya gogama cutar inalillahi kawai suka dauka.


Kuka Zainab ta saka tana."banyafe maka ba Junaid ashe alfasha kake aikatawa ga ya'yan mutane nima abin yafara bibiyar ya'yana gashi ka goga mani cuta harda da'na Allah ya isa banyafe ba ka zalinceni nayi dana sanin auren fasiki irinka."

Kara ta saki take tafadi kasa sume kanta yayo a rikice gadirobas suka kamashi akai ciki dashi sai kuka yake yana."na shiga ukku ni Junaid na lalace kiyamata ta kama wayyo Alalh kaicona."!

Haka aka maida shi daki aka rufe,itako Zainab Gandirobas suka samata ruwa ta farko suka lallasheta sannan suka tafi gwanin tausyi sai kuka take tana jin kamar ta mutu haka takeji musamman dataji abinda yake aikatawa.


★★ ★★ ★★


Karfe shabiyun rana muka iso Caranci cikin ikon Allah daman Mama tasan da zuwan mu sungyara komai kuma ranar za'a kawo lefena tun muna Katsina tace ankawo lefe suna gidan su Husna fatan alkhairi da addu'a Mama tayi muna isa su Kawu Ali suka taremu da Anty Mubaraka sai Anty Rukayya wani katon daki aka aje bakinmu na Anka bamu jima da zamaba Anty Murja ta iso da nata zuriyar dan tayi zuwan biki kenan sai yaba kyaun da nayi sukeyi cewa suke kada inyi make-up haka nafi kyau,nidai bance komai.

Haidar dan Anty Murja ya shigo da kattin kuloli abincine tayo mana da kaji kowa ya zuba ga uban kunun aya da zobo,kowa ya zuba harna zuba tabani wani hadin nama sai baza kamshin daddawa yake tace inci nawane sai kunun aya kyal dashi ansa nayi nahaucin abuna yai dadi sosai,Rahima ta shigo suka rungume juna itada Zainab kusan amintar da mukayi da Husna irinta sukeyi dandai tamu tafi karfi itama kula ta aje mana masace da miya Mama ta aiko mana saida muka gama abinci aka huta sannan bakin mu sukaje ganin kayana lefena Anty Rukayya ta rakasu nikam daki Anty Murja takaini can kuryar Baba tace.

"Ko waje bance kifita kada inji ko ingani."
A gajiye nace.
"Wai Anty boyon mi ake mani har haka pls."

"Amarya saida sitirtawa kodan baki wani zai yabeki bai iya cewa masha Allah ba'asan bakin shiba shiyasa."

"Toh idan ina bukatar wani abu wazai bani.?"
"Gani ga Anty Mubaraka zamuyi maki komai koda yake gobe zanje Kaduna wajen Anty amman jibi zan dawo."

"Ba Ummi zataje canba.?"(Anty Zainab ta kano)
"Eh yauma ta tafi daga kano ko nan bata biyo ba."

Araina cewa nike daman ke kikatafi Kaduna inasan ganin Ya Taufiq kin hanani haba!

Azahiri nace shikenan Allah yadawo dake lafiya.
Ameen yar albarka."
Zama nayi gefen gadon Baba ina raba ido kamar wadda tayi karya yanzun inanan zaune har tsawon kwana hudu nashiga ukku da Anty Murjanatu.

Chat nahau kona samu sauki naga sakon Fatash ina budewa naga lefena taturo mani gwanin kyau guda goma ne kowane biyar kala biyu da pich sai kuma royal blue sai wasu jikkuna katti guda biyu sosai naji dadi anyi kaya masu yawan gaske gaskia sunyi kokari sosai.

Murna nayi da Emojis ina rawa dan rashin kunya irin tawa.
Kiran wayar angona nayi kamar jira yake karaf ya daga yana sauka numfashi yace.

Ya gajiyar tafiya.?"
"Alhamdulillahi,daman inason...
Sai nayi shiru inajin wani iri.
"Tell me pls mikikeso."?
"Nagode kaya sunyi kyau sosai Allah yakara arziki."
Ameen yace yana dariya.

"Gaskia ana amaren zamani ko kunya bakiji kikaje gidan su Husna ganin lefe anya beauty.?"
"Aaa wlh Fatash ta turomani su wlh banjeba."

Sake dariya yayi shi dole ni naje ba yanda banba yaki yarda saida yaji kamar zanfara kuka sannan yace.

"Is ok nayarda gabana tayi snap dinsu saida nace kada ta turomaki taki Allah ya shiryi Fatash."

"Ameen nace inajin kunya."
"Yau Ummi ta iso bada jimawa."
"Kace tasha hanya."
"Aikuwa,ina inna ta.?"
Tafita inanan ta kunshe daki wai kada infito waje.

"Kai inna matsala wlh shiyasa bazan zoba sai daurin aure ta tsawwala ni bansan wannan al'adarba."

"Anty ce fa kasan halin ta Allah ya kyauta."
Ameen yace muna cikin fira naji Tariq na mashi magana yanke kiran yayi nima naci gaba da abinda nikeyi.

Hidima akeyi sosai tsakanin gidan mu da gidan su Asma'u kace can ake bikin kusan komai can akeyin shi yau ake jere tun safe su Anty Mubara suna gidan Mama ana fiddo kayan kitchen aka goge komai saboda wani yajima aje wasu kuma sabbine Mama taje kano da Anty Rukayya suka siyo kafin mudawo daga Anka sun hada komai saidai akai mota biyu takayan kitchen kawai furnitures dina daga Company direct gidan miji sukayi andaice kala ukku akai mani Baba yai mani gado sai kujeru biyu Mama tai mani gado daya sai baban Husna yaima sate din gado shima, kayan kitchen babu ce kawai ba'asamani ba,duk yanda Abban Ya Taufiq yayi da Baba kada yasai mani komai amman yaki saida yaimani duk abinda uba kema yarsa lamarin Babana yana bani mamaki shidai mutun nai zuhudu shiyasa yake rayuwar shi cikin sauki.

Kasancewar gidan Ya Taufiq na malali ba nisa shida Ya Tariq saidai gidan su akwai babanci amman sunyi shige upstairs ne kasa daki ukku sama daki biyu sai falorn sama da kasa sai kitchen kato guda daya da store sai wani waje dayake dauke da kujeru na siminti anmashi deco da flowers shima dai falorn ne maki manci.

Leader chairs dina aka samani falorn kasa sai daki guda daya aka sa sate din Baba daya marar royal sai guda biyu akasa bedrooms din sama da royal sai normal gado kujeruna masu Royal falorn sama daki biyu akasa ba'asama kayaba iyakar karfin iyayena kenan daki ukku sukai mani kujeru biyu sai daki daya aka cika mani shi da trows flow da kafat mai kyau aka jere mani akwatuna na da fridge maki manci sai keken dinkina da kujeru na karfe guda ukku suka saka mani kamar dai dakin hutawa akai mani dayan akabar shi empty andaisa labule,haka aka gama jere sai Video sukeyi dayake Zainab da Rahima sai Anty Mubara sunje washe gari suka dawo saura kwana biyu biki tareda Fatash suka taho sai Anty Murja daman ta rigasu zuwa.

Haka suka dawo cikin aminci saijin dadin akeyi nan aka gwadama Mama gida saijin dadi takeyi tanasa albarka hakama Maman Husna yanda sukai mani hidima kamar iyayena sunbata gudunmuwa dan ita da Mama kusan tare suka hada kayan kitchen saboda abinda akaima Husna a kitchen nima shine banbancin kadanne ankara mani da kayan zamani saboda komai na sauyawa.

Ni kaina nagodema Allah ganin daular da iyayena suka saka mani sun fiddani kunya duk da bawani kudi Babana gareshi ba amman akwai zuciya.

Gadon dakina light brown da zaiba sai gadon dakin Ya Taufiq farine sol.

Kasa kuma black ne mai gold hakama kujeruna yadin su ligh brown ne and gold royal din kenan sai leader chairs dina black ne,duk da bani na za6a ba amman komai yai mani kyau masha Allah.


Washe gari daren biki Haidar yakaini kt saloon da yamma muka dawo mai lalle tafara zana mani saida taimani mai salatif daga Barno Anty Zarah tazo da ita kanwar Mama ce uban su daya ita taho ta tureren wutar da za'akai mani gidana harda na jiki duk ta siyo mani mai kunshi kanwar mijinta ce lalle take mani mai masifar kyau da ado daman fatana nada haske sai yayi shar dashi waida har sarkar wuya tace zatai mani nace banso kuma nace banson a cika mani hannu aiman kadan aiko ta tsara shi gwanin birgewa saida tafara mani na salataf sannan tai mani zane sai isha'i muka gama shi karfe sha daya na wanke shi sannan nayi wanka nai sallah inajin ciwon ciki sosai narasa na miye nidai ban wani dirki kayan mata sosai ba nafishan friuts bare ince ko sune hakadai nagama salla a dafe na kwanta inajin sai a slow.


Aikin biki akaraba kawowa kawai za'ayi tuwo da miya akeyi gidan Mama komai anbada aikin shi gwanin tsari kayan da zansa already ansa mani cikin katan akwati mai make-up Fatash tazo da ita amman Anty tahana wai kar aimani da kyal saida Umma (Mum) tasa baki sannan tace ranar daurin aure kawai zatai mani amman taima duk maiso da haka dai akabar zance saidai Fatash ta wurgama Anty harara tana zumburar baki tayi kate kate ko magana da anfara yimani yanzun zatace ba'ason amarya na magana mai karfi nidai saidai inyi murmushi sai akaci sa'a daman ina fama da ciwon ciki kuma a iya sanina ba period zanba akalla sai next week zaizo mani.

"Wai inna miyasa kika kara tsanani akan tsaron amarya kin zafafa na Minal fiye dana kowa miyasa.?"
Cewar Fatash.
"Kinsan komai dole akula saboda yan hassada shiyasa bansan tana fita addu'a kawai muke mata ayi bikin nan lafiya agama kalau jinina kan akaifa yake wlh Fatima shiyasa."
"Allah yasa agama lafiya ya tsare mana."
Ameen mukace,saidai ina ayyanawa wazai bada matsala bayan makiyana duk ankamasu banji za'asamu damuwa.
Baccina nayi jin ciwon nawa ya rage.


"""""" """""""
Safiyar biki Baba ya shigo dakin ganin har bakwai saura bantashi ba ya tana dani cikin bacci naji yace.
"Mamana kinyi sallah kuwa tashi."
Mikewa nayi a hankali ina ganin ya dauki akwati da alama kayan da zai sane a daurin aure ya fita kewaye na shiga na tari ruwa nayi fitsari nayi alwallah nazo na tada sallah harna gama naci gaba da addu'oina.

Har sallar walha saida nayi sannan na mike nahau zabin kayan da sansa da safe.
Kiran Fatash ya katse mani hanzarina dagawa nayi tace.

"Minal make-up dinnan da wuri za'ayi kafin daya kinsan wuri za'atafi kaiki ko?"
"Eh nasani anjima zanyi wanka."
"Okay kizama ready."
Insha Allah,kiran Ya Taufiq ya shigo.
Fatash kashe,ya Taufiq nakirana."
Okay bye ta yanke.

Dagawa nayi yace first love hope kin tsantara mani kwalliya ko.?"
"Anty tahana."

"Banganeba mikenan."?
"Kwalliyar mana."
Dariya yaso bani jin yace.
"Kam ni mijinki inason ganinki da make-up."
"Ammin ka tace bataso."
"OMG gaskia inna ta daina jidani komai ta hanani nidai nagaji Allah."
Dariya nayi nace.
"Wai ita nafi kyau ba kwalliya."
"Yes offcourse shiyasa nikeson in banbance dakaina."
"Okay zan lallabata."

"Uhmm ni inna na ɗaure mani kai bansan mi zance mata ba Allah."
Basarwa nayi nace "mikakeyi."

"Muna hanya."
Duba waya nayi naga karfe tara daidai
"Tun yanzun.?"
"Almost three hours akalla sai one zamu iso karfe biyu a daura aure intafi da amaryata shine da wuri."?
"Allah yakawoku lafiya amman ka gayara bakin farin ya samu shiga kasamu akai maka n....
"Enough Minal nafi kowa iko dake wai miyasa komai sai kin nuna shamaki a tsakanin mu dan Allah kina tsinka mani zuciya."
"Sorry my king safetripe."
"Ameen take cake."

Fatash ta shigo da Anty Murja ta ware mani kayan da zansa less lemon green da touch din ash ya hadu sosai gownt ce ta fidda mani hips dina sosai kamar zani event ina dagata nace.

"Fatash wlh zata kamani sosai amman dagani anrage awon dana baku ko.?"
"Eh ganina nayi bazasuyi kyauba."
"Wai kina nufin kayan nan duk haka akayi mani su.?"
"Aaa guda ukkune amman sauran sunfi haka."
Jinjina kai kawai nayi basan mizance mataba nidai bansan matsatssun kaya Allah yasani amman ba yanda zanyi,sha daya aka fara make-up saida nayi wanka nayi alwalla sannan aka fara sai daya aka gama shi gaskia ta iya sosai nidai naga kyauna da make-up daurin kallabi zatayi nace tabari sai nayi sallah tafara yima Fatash

Kiran Ya Taufiq nagani ina dagawa yace suna gidan Baba Hassan inshirya suna dawowa daurin aure yana son ganina.
Toh nace mashi.

Gida ya dauki baki sosai abokan Baba da Abba duk anzo hakama na Baban Husna sai abun yakara yawa karfe biyu saura na tada sallar azuhur inata addu'oina daurin aure kawai muke jira wannan kenan.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E23&24


_*DAURIN AURE*_



Masallacin dake unguwar mu tamkam yake da dan Adam dayake katone ana gama sallar Juma'a aka fara shirin aure waliyina Baban Husna shiya bada aurena ga waliyin Ya Taufiq Baba Hamza akan sadaku dubu dari kowa yashaida mutane harbisa titi dayake masallacin bisa hanya yake,anci ansha,take away aketa rabawa ba yaro ba babba bare tsoho sai goro da alewa masha Allah komai yaji alhamdullilah.

Nidai ina zaune bisa sallaya dana gama sallar azahur kiran angon nawa nagani ina kyarma na daga yace.

"My wife yaudai burina yacika Aminatu kinzama matata halak malak sai nike ganin kamar amafarki Allah nagode maka daka nuna mani wannan rana lallai kam komai lokacine Minal."

Nauyayyar ajiyar zuciya na sauke nace.
"Alhamdulillahi mijina lallai kam komai lokacine Allah yasa mana albarka a cikin tarayyar mu yakare mu daga kowane sharri komai kankantar shi."
Take muryata ta sauya naci gaba da cewa.
"kinyi gaskia Asma'u daman kince ko baki raye zance kin tabace mani komai lokacine yau gashi burinmu ya cika ada na dauka kalar mijin da kike roka mani yai mani nisa yau gashi kusani dani harna mallake shi, kinsha gaya man kinaji aranki Ya Taufiq shine zabin Allah gashi yatabbata Husnata inama ace kina rayeda yau kika samu cikar naki burin amman bakomai tawan Haka Allah Yaso Allah yaimaki rahama Asma'u."
"Ameen matata,tashi kiyi nafila komai kika roka ba shamaki daganan kimata addu'ar rahama Allah yajikan Asma'u."
A"meen mijina."

"Inkin gama kikirani inasan ganin sereously."insha Allah."

Tashi nayi na kabbara sallah ina kukan zuci nahau nafilfili inajin Anty tana ya isa kizo kigaisa da iyayenki Aminatu nidai tunda na saka goshina ƙasa ga sujudar ƙarshe ba abinda nike roko sai rahama nikema kawata fata nasan da tananan kuguna kugunta wannan ajetake.

Ya Allah kajikan Asma'u kaimata rahama Allah kasa aljanna firdausice makoma agareta kasa mutuwa tazama hutu agareta Allah ka shirya zuriyar ta kaimasu albarka.
najima inamata addu'a sannan nafara yimana addu'ar zaman lafiya nida mijina da zuriya dayyiba.


"Ya Allah kasa auren nan da aka daura ya zama alkhairi tsakanina da mijina ka azurtamu da zuriya dayyiba ka kade mana duk wata fitina ka iya mana abinda bamu iyawa komai kankantar sa sannan na shafa inama annabi salati haka naima iyayena da yan uwa musulmai baki daya addu'a ina gamawa naɗago bakowa sai Fatash sai mai kwalliya daurin dan kwalli tafara yimani tana gamawa ta gyara mani yan kwallan da suka shido mani zama nayi biyu da rabi mai kwalliya tafi zataima su Zainab itama Fatash fita tayi zataje wajen Abdallah zata shigo dashi sitrum din Baba, dan kwantawa nayi sanadiyar murdawar da cikina yayi, tashi nayi naje toilet da kyal na dage riga ina Allah wadarai da dinkin nan less mai kyau amman Fatima tasa anman komai das ina amfani,ina dukawa naga Period dina gabana ya fadi sosai inalillahi wa'inna ilahirraji'un nace,saboda ba lokacin bashi wane irin kayan kunyane wannan saida aka daura mani aure zaizo ya zanyi da rikicin Ya Taufiq Allah yasa yafahimta ya zanyi banda part ohni Aminatu lalurar ya' mace bata taba karewa sai rai yai halin shi, fitowa nayi na dauki waya na kira Fatash tana dagawa nace.

"Fatima dan Allah kada kigayama kowa ko Anty bansan tasani part nikeso pls."

"Kema kinsan Anty sai tabi diddiki tasan mi zanyi wajen ki ai ita haka takema amarya shiyasa ake ajeta gun amarya ina dalili wlh bata bari inzo hakanan,bayan gabanta muka fito da mai make-up amman da kanta zata fiddoki kijira kawai."

"OMG miye haka Fatash On fa nace maki so kike inyi staining ko minene?"
"Ganinan Abdallah yakawo Saveniers hadda abinci da za'aba kawaye."
"Nagode zanzo mugaisa nidai kiyi sauri kar asirina ya tonu."
Kiran Ya Taufiq ya shigo naki dauka,sai gata tashigo da jikkar part ansa nayi naje na kimtsa jikina nasa sauran akwati ayam saiga Anty kamani tayi mukaje gun yan uwa sai masha Allah akeyi anasa albarka wajen Abdallah naje muka gaisa yana zolayata.
"Mrs Taufiq Allah yayarda gaskia saidai agodema Allah."

Bakina ya mutu duk zolayar da za'ai mani saidai inyi murmushi.
"Ya Abdallah naga sako nagode Allah yakara arziki."
"Ameen aminis amaryar kamshi."
Dariya nayi kushugo naji Fatash tace Ya Taufiq ne da Ya Tariq cikin fararen kaya sunsha manya riguna sai kayi masu kallan kurilla zaka iya ganesu sai washe baki sukeyi nima kallan su nikeyi tsab sungane banbance su nikeyi,dariya na saki ganin kallan daya Taufiq yai mani nace.

"Ko acikin dubban taurari bakai mani batan dabo angona."
"Wow tagane zan baki special gift."cewar Ya Tariq

Gaisawa sukai da Abdallah mai hoto yai mana pic sannan yace zaije gun Mama zai huta godiya na sake yimashi yatafi.

Anty Murja takira Fatash da Ya Tariq bansan mi zasuyi mataba dagani sai shi najuya zanje gun kawayena ya rikoni gam jiki mace natsaya un expected naji ya sunsunar mani wuya kamar in suma naji da sauri na zauna cikin wata murya yace.

"Mrs Hussein kinyi kyau amman ban amince kikara ganin kowane namiji da wannan rigarba ki adanata zatai maki amfanin amman ba nan ba understood."?
Daga kaina nayi nagaza magana cikina ya murda na danne marata.

'Lafiya mike faruwa.?"
Arude yai maganar yana rikoni.
"Bakomai zanje in sauya kaya."
Nace duk na takura bansan ya gane halin da nike ciki, da kyal ya barni a mike ina fitowa Anty takirani shima a waya takira shi akaita hotuna da kawayena dangi da abokan arziki akai mani da Baba da Mama sai yan gidan mu sai Baban Husna da Mama sannan akai mani dasu Ya Taufiq shida Ya Tariq suka sakani tsakiya harna gaji da pictures da kyal na zille na shige daki wanka nayi na sake shiryawa cikin atamfa riga da sicket ba laifi basuyi mani tamauba ba make-up fuskata sai lipstick dana saka mai kwalliya tayi mani dauri,sannan na fito sai yabawa ake nanma na kara pic saiga Mina da Haidar duk munyi pics sosai kusan la'asar na koma ciki hadin madara akabani nashanye.

Jina nike ina roshin shiyasa duk bayan awa biyu nike yawan gyara jikina,yanzun ma sakewa nayi da bazan sauya kayaba Anty tabani less riga da sickt maroon nasa Baba Hassan yace akaini gidan Mama za'ai mani nasiha yanzun za'akaini gidan mijina sai lokacin naji cikina ya katsa duk tsoro da kewar gidan mu ya taso mani wata rigace kamar gadon gidan muce ta Buzaye dark blue ce idan za'akai ki gidan miji ita ake daurama mutun bisa kaya haka aka saman Anty Rukayya taka mani mukaje gidan Mama dakin Baban Husna aka ajeni dashi da Baba Hassan sai Baba da Alhaji Tijjani nidai ina bisa kafat kaina kasa Baban Asma'u yace.

"Aminatu ki saurarani da kyau kiji abun da zamu fada maki,yanzun dai kin shiga wata sabuwar rayuwa wadda kowa ke fatan bude wannan rayuwar saidai takanzoma kowa da kalubale iri iri walau na dadi ko akasanin haka,bakomai ke tafiyar da wannan rayuwar illa hakuri kuma wannan hakurin da zakisa aranki shine ribar auren sannan kiji tsoron Allah ki kula da hakkin mijinki ki mutuntashi sannan ki girmama iyayen shi makotanki da yan uwan shi kowa nakine kigani baki ganiba kuma kiji bakiji ba,wannan shine dabi'un mace tagari mai tsoron Allah,munai maki fatan alkhairi yau gashi Allah yakawomu lokacin da zamu kaiki dakin mijin ki sai mugode ma Allah baki dayan mu dayai mana wannan ni'imar Allah yai maki albarka."

Ameen Baba nace kwalla na ziraro mani bisa kuncina.

"Gaskia ya'ta duk abinda za'agaya maki kiyi amfani dashi saboda kedin uwace ta wasu kuma kece makarantar farko ga ya'yan ki fatan zakiji nasihohin da iyayen ki suke maki Allah yabaku zaman lafiya,saidai zan maki nasiha daya ki kula da dukiyar mijin ki kada kizama almubazzara ,Allah yasa albarka."
Cewar Baba Hassan ameen suka masa Baba yaci gaba dacewa.

"Mamana kobance komai ba angrigada ance komai iyayen ki sun maki nasiha mai ratsa jiki fatan zakiyi amfani da ita,saidai ina jan hankali inakara gargadar ki da kiji tsoron Allah a duk halin da kika tsici kanki ina kara jadadda maki jiki tsoron Allah a duk al'amuranki Allah yasa albarka yabaku zaman lafiya."

Ameen nace ina kuka najima suna mani huduba kafin Mama tashigo itada Maman Husna tace.


"To Aminatu Allah yakawomu lokaci sai mugode mashi Allah ya albarkaci aurenku yasa kuzama abokan arzikin juna Allah ya kade fitina yabaku zaman lafiya Allah yaimaki albarka ya'ta."
Ameen na amsa saman labbana.
Itadai Mama batace komai ba saidai shafa kaina da tayi.

Kamani akai za'afiddani waje sai kuka nike.
"Allah yaimaki albarka Aminatu."
Cewar Mama,kukan nawa suka kara sauti Anty Murja rike dani itada kanwar kakata Baba Hindu cikin mota suka sakani tsakiya suka zauna gefena,inaji ina gani sun hanani komawa gida acewar su ba abinda zanyi inna koma.

Kukan zuci kawai nike inajin hawaye masu dumi na sauka bisa kuncina.
''Hassan muje ko wa'ake jira."?
Cewar Anty Murja.

"Baki daya mukeso atafi inna kuma Ahmad nikejira tare zamu tafi."
Cewar Ya Tariq.

Nidai nayi zugum sai nikega kamar mafarki wanice da auren Ya Taufiq kuma gidan shi za'akaini ikon Allah kenan.
Inajin Ahmad ya shigo cikin motar,muje duk kowa ya shiga."
Okay.

Jinayi mun tafi inajin muryar yaran unguwa suna.
"Anty Amina Allah yabada zaman lafiya yasa albarka."
sai bin motar mu suke har mukahau bisa titi,tafiya mukeyi cikin tsari saidai suna gudu da motocin kar zamubar kasar baki daya musamman da sukaga biyar din yamma tayi.

"Aminatu bude fuskar ki kisha iska nan ba wani bako kinji.''
Anty ta yaye mani hular rigar da suka azamani wani irin sanyin Ac ya daki hancika tareda kamshin turare mai dadin Shaka.

"Aikuwa Anty kwara ta wala amaryar Ya Taufiq sai dubu tataru."
Cewar Ahmad.
Dariya sukayi baki dayan su nidai bance komai ba shimaYa Tariq ya maida hankalin shi kan titi.

Waya aka kira shi tambayar Ahmad yayi mai kiran shi
Ya Taufiq yace.
"Daga sashi speaker."
Hak kuwa akayi yace.
"Hussein yadai."?
Ajiuar zuciya mai nauyi ya shide yace.
"Hassan kuna ina."?
"Toh bamujima da tasowa ba gaskia ko 1hr bamuyi ba kaidai kayi addu'a."
"Okay Allah ya tsare hanya ya baby na take."
Ya Taufiq yai tambayar cikin sanyin murya.

"U re in speaker kuma inna najinka zata baka amsa."
Ɗit naji ya yanke kiran dariya suka saka yana ɗan rainin wayo amaryar shi kadai yasani.
Nidai murmushi nayi.
"Ina ruwan Hussein yanada gaskiar shi ai."
Cewar Baba Hindu.

Haka dai sukaita fira nidai bance komai duk jikina yai sanyi lakwas kamar marar lafiya munyi nisa sosai har nafarajin bacci kuma nafara gajiya da zaman motar hakuri kawai nikeyi.

Jin bacci na neman kadani bansan na aza kaina bisa cinyar Anty Murja ba nafara bacciba shafa kaina ta dingayi aiko bacci yai awon gaba dani duk daba wani dadin shi nikejiba maleji kawai nikeyi.

Karfe takwai daidai muka iso cikin unguwar Sarki Kaduna koda Anty Murja ta tadani a hankali na bude idanuna nasha bacci sai naga

Please Login or Register in order to submit comment