Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dinka mijina."
"Miss you too my wife ya babyna hope tana cikin aminci."
Hannu na daura saman cikina daya tashi sosai nace."Lafiya lau yana gaida dadyn shi."

"Kice ina missing dinshi ki kula da kanki kinji tawan."Insha Allah saika dawo bye take care."
Okay bye."

Muna gama waya na mike cikeda kulawa nayi wajen wardrope ina duba kayan da zansa saidai narasa wa'anda zan fiddo nafi minti biyar a tsaye.

Kasancewar Kasar Turkey kasace mai dadin zama batada hayaniya kwarai sannan kuma kasace mai yawan sanyi musamman sinow dake yawan sauka shiyasa kayan sawar su ya kasance kanana sai katuwar jaket ta sanyi da hular sanyi shiyasa gidajen su duk akwai na'urar dumama gida dan samun sukuni.

Gidan mu bawani babba bane saidai yanada katan falo da turkish royal chairs akwai kitchen da store a falorn inda kabi ta Corridor akwai bedrooms ukku ɗaya na kallan ɗaya sai guda daban idan kayi bayan gida kuma garden ne haka gidan yake yai tsari daidai gwalgwado.

Ina zaune naji an rufe mani idanuna murmushi nayi baiyananne jin sanyayyen kamshin Ya Taufiq,cikin sanyin murya nace."My love u re wellcome."Kiss ya sakar mani a goshina yace.
"I love you my wife ya babyna."
Ya ida maganar yana shafa cikina wanda yake wata shidda cikin so da kauna da tausayawa yake shafa saman cikin nawa.Nima daura hannuna nayi saman nashi nace."Tana missing Daddynta."
A hankali na mike nace.
"Muje in shirya mijina ko."?

Hannun mu sarke mukayi bedroom dinshi muka shirya ya dauko rigar sanyi ya sanya mani dan yasan bansan sanyi.

Saboda kafin nasaba da yanayin kasar naba Ya Taufiq wahala matuka har Allah yasa na saba,tare mukafita har parking space ya bude mani mota na shiga,shima ya zagaya ya shiga muka tafi ba inda muka tsaya sai Mall.
Mukayo shoping ba abinda yake dauka sai kayan jarirai maza da mata nidai kayan turare nike dauka kala kala, sannan shima nai mashi siyayya da haka muka fito sai muka biya, *Buhara Ocakbasi Restaurant* mukaci abinci da lemo munjima a waje sai yanayin yai mani dadi musamman weathern garin bamu mukabar restaurant ba sai karfe goma muna tafiya ba inda muka sauka sai gida lokacin sha ɗaya tayi sannan muka kwanta cikin aminci,wannan kenan.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E45&46


NO EDIT❌

Tunda mukayi magana da Abdallah yace in saurare shi zuwa wani lokaci Allah yasa ya aminta da auren Rahima bakaramin farin ciki nayiba danaji ya aminta da kudurin iyayen mu.

Haka na sanarma Baban Husna yaji dadi kwarai dagaske hakama Baban Abdallah shima yai farin cikin jin wannan labari wata bakwai aka saka shima dan Rahima takusa gama wani karatu da takeyi kuma ƙa'idar Abdallah baison aikin gwamnati shiyasa yace bazai bar matar shi tana zuwa school ba hakan yasa iyayen ta sukace abari intagama karatun sai ayi bikin saboda darajar ilimi musamman ga ya' mace dole sai anyi aikin gwamnatiba anayi saboda tsaron lalura kodan ya'yan ta da wannan hujjar akabari saita gama karatun agidan iyayenta tinda mijin da zata aura bai bukakar hakan.


★★★★★
_ANKA_


A wajen iyayen Amina basu da wata matsala hankalin su ya kwanta musamman da suka dukufa da addu'a neman tsarin kaidin mutun daisa jan yau takama juma'a da misalin karfe ɗaya Alhaji Latib yazo gidan su da kanshi wajen Baba tara mai kyau Baba yai masu domin tinda suka riki Aminatu yake basu girma na musamman cikin aminci suka gaisa da junan su ɗan shiru ya kaure a falon kafin Alhaji Latib yace.

"Alhaji Yusuf nasan zakayi mamakin ganina amman hakan ba abin mamaki bane duba da munzama yan uwa kuma abokai,saidai nazo neman alfarma agareka."

Jinjina kai Baba yayi cikin dattako yace.

"Inajinka Alhaji insha Allah wannan karan ban fatan kasake neman wata alfarma agareni in gaza yimaka ita insha Allahu inajinka."

"Toh naji dadin hakan saidai va wani abu bane daman nadawo nemawa ɗana Abdulmutallib izinin neman auren yarka Zainab."
Murmushi Baba yayi cikin gamsuwa da yabawa da halin dattako irin na Alhaji Latib yace.

"Tabbas kudin masoyan kwaraine duk da ɗanka yarasa Aminatu amman hakan baisa kayi fushiba ko datse alaqa damu sai gashi ka kuma dawowa wannan kadai ya nanuna zuriyar mu,kukeso naji dadin haka kuma na aminta nai mashi izini yazo yanemi so ga yarinya sannan zan shaida mata inason kubani lokacin nan da kwana ukku zakuji komai insha Allah."

Cikieda kwarin guiwa Alhaji Latib yace.

"Haba Alhaji akanmi zamuyi fushi ai tunfa kai mani bayanin komai akan Taufiq da Aminatu wlh banji komai ba kuma hakan da kayo shine dattako sannan haramun ne nema cikin nema,nagode da karamci Allah yabar zumunci.

Ameen ya rabbi haka suka taba fira sannan ya tafi yana maijin dadi aranshi.


_ISTANBUL_

Ina wajen exercise nida Ya Taufiq yanayin Jim wayata tahau ruri Babana shine abinda ya bayyana a wayana saidai ta yanke ba kirashi cikin jin dadi nike waya da Baba haka muka gaisa sosai sannan yace.


"Aminatu kinji abinda ke faruwa Alhaji Latib ya dawowa nemawa ɗansa auren kanwarki Zainab....

Haka Baba ya gama gaya mani komai,wani irin dadi naji dan nasan Zainab tayi dacen mij domin Ya Mutallib ba'a bayaba.

Cikeda jin dadi nace.
"Alhamdulillah Baba kaimasu izini domin mutanen kirkine gaskia naji dadin wannan labarin kaga sai ahade dana Rahima ayi rana ɗaya."

"Kwarai kuwa Mamana daman haka baban naku yace Allah kaimu lafiya."
"Ameen uwata takaina ya mijin naki ina fatan ba abinda ke damunki ko."?


"Eh bakomai Baba ina cikin kishin lafiya."
munjima munafira Baba haka yaba kaf kannena muka gaisa harda Mama ranar sayau haka nikejina sai farin ciki nikeyi na musamman.

Ba'a wani jimaba aka sakawa Zainab rana taredana Rahima za'ayi shi,abin gwanin burgewa komai yana tafiya yand yadace.


Bayan wata biyu,alhamdulillah cikina ya shiga wata takwas daidai tunda Mum ta fahimci cikina ya tsufa takafama Ya Taufiq dokar ya dawo dani gida batason in haihu ba kusa da itaba,daga ita har Abba maganar kenan.

Gashi kusan kullin inakan waya da sirikan nawa ba Abba ba ba Mum ba,sai ya kasance abin nasu kamar sabon shiga haka yazo masu kai kace babyn da zan haifa shine jika na farko da zasu gani a duniya dan kulawa suna mani ita iya karfin su duk da ban kusa dasu.

Shikuma abangaren Ya Taufiq yafiso in haihu a Istanbul kodan ɗan shi ya zama citizen biyu amman su abba sun hura wuta fafa ya maidani gida shiyasa yake jan jiki akan lamarin.


A wajen Anty Hafsat ba laifi kurajen da suka feso mata a jiki sun warke saidai wanda ba'arasa ba saidai tayi bakikkirin kamar ba ita.

Tunda su Dada sukazo mata visting ba wanda ta kara zomata.

Hakama Baban su Umaima anyi juyin duniya yaki zuwa dan dole aka saka mashi ido.

Itako Anty Hafsat batada matsalar da kowa saidai har gobe
basu zama inuwa ɗaya dasu magajiya saboda kullin sai sun gana mata azaba.


Dan kuwa itada Mami sun zama abokan gabar juna banda wulakanta juna ba abinda sukeyi,koda aka rufe Mami tana ɗoyi amman haka Anty Hafsat ke gasama Mami masifa da jaraba gashi ita daya kwal take zama.

halin da Mami ta tsinci kanta a ciki saidai muce inalillahi wa'inna ilahirraji'un Allah yaimana tsari da kariya ya tsarkake zukatanmu da kugun nufi Allah ya rabamu da cituttukan karshen zamani ameen.


Tun Mum nama Ya Taufiq maganar ya maidani gida har suka sama shi ido nima ba yanda banba amman yace bazan koma ba.

Shima Abba yace ya maidoni gida ba yanda zaiyi ya yarda acewar next week zai maidoni.

Ana sallar la'asar muka fita exercise nida Ya Taufiq a kasa kuke tafiya ina dan motsa jikina saboda danaje awo likita yace indinga jujjuya jikina shiyasa kusan kullin sai mun fita.

Tafiya mukayi sosai idan nagaji sai ya tsaya in huta haka mukai tayi sai karfe biyar muka dawo gida duk na gaji kwanciya nayi bisa kushin ina hutawa.

Bacci yafara daukata can naji muryar Ya Taufiq a hankali na bude idona ina kallna shi yana gefena zaune saman 3str.

"Wlh Alhaji nidai kacema Abba yabarta ta haihu nan daga baya sai in maidota gida nayi alqawali."

Inajin abinda yake cewa nagane da Alhaji Munzali yake waya banji abinda yace ba saboda wayar ba handfree take ba naji Taufiq yace.

"Eh nayarda da sharadinka Alhaji nagode sosai."
Da haka sukayi sallama.

Maido kallan shi yayi kaina wanda nima shidin nike kallo ina mashi kallan ko lafiya.

"Next week Anty Mubaraka zatazo har ki haihu in Allah yakaimu."

"Bazan koma gidan ba kenan."?
"Eh nafiso ki haihu nan."
"Dan Allah kabari inkoma kaga Mum tafi bukatar haka pls."

"Zan shawo kanta inason ɗan da zamu haifa ya samu indigene biyu shiyasa kikaji nace haka dan Allah wife kibar zancen nan."

"Shikenan Allah ta saukeni lafiya."
"Ameen summa ameen."

Dan shiru mukayi sai kuma nace.
"Ita Antyn tasan zatazo."?
"Aa Alhaji yabani wannan zabi indai bazan maidaki gidaki haihuba ya zama dole asamu cikin iyaye wata tazo takula dake,shine na hakaitu Anty Mubara nasan zata iya yanzun Innata zan kira inshaida mawa dan tasani,inason inji ra'ayinta."

"Hmm kaima kasan Anty Murja tana iya cewa dole saina koma amman ka gwada kagani."
"Okay bari muji abinda zatace."
"Allah yasa muji alkhairi."
"Ameen."

_KADUNA_

Tunda Mum tasan Aminatu bazata dawoba tafara shiri,hakama bangaren Maman Husna,domin ita tahaɗa kaf kan uwa tunda watan haihuwar Minal ya kama sun haɗa komai,jibi zasu tafi wajen Amina harda Maman Husna a ciki,da yamma Kabir yakai Mama Kano har Aminu Kano International Airport zuwa biyar na yamma jirginsu ya sauka *Kaduna International Airport* Tariq yaje ya daukota har gida suna isa,Mum taita murnar isowar ta,haka taba Mum kayan uwa data hadama Amina sunji dadi sosai washe gari zasuyi tafiyar harda Aisha da Auta Jidda sai Mama su,ukku zasuyi tafiyar har ticket duk Tariq ya siya masu washe gari zasu tafi.

Ranar kusan kwana sukayi suna fira da Mum,da safe misalin karfe goma jirginsu zai tashi Abba yasa drivern su yakaisu har cikin Kaduna State International Airport suna zuwa basu bata lokaci ba sukayi boading aka basu ticket dinsu.
da bata lokaci da komai karfe goma da rabi daidai Jirginsu ya ɗaga sararin subana ba inda sukai landing sai *Istanbul Havalimani International Airport.*

After 30mint aka fiddo masu kayansu,basu jima sosai ba Taufiq yaje ya dauko su,har gida ya kawo su.

Da sallama abakin su,suka shiga cikin kamilallan gidan nasu marar hayaniya.

Ina saka doguwar riga naji shigowar Ya Taufiq waigowa nayi da murmushi fal afuskata duk da yanayina ya nuna mamakin dawowar shi dayayi da wuri iya sanina sai bayan isha'i zai dawo.

Waving dina yayi ya bude hannayen shi alamun intaho aiko yai hugging dina.
Raɗa yai mani a kunnena hakan yasa naɗan waro idanuna waje.
Nudding kanshi yayi dan tambatar da abinda ya faɗamani cikeda kosawa nace.

"Tell me the suprise pls."?
Kamo hannuna yayi batareda yace mani komai ba mukayo falor,nidai shi nike kallo.
Hannun shi nabi da kallo dan ganin abinda yake nuna mani.
Bansan sadda na saki karar murna ba da sauri nayi falorn ina rungume Mama ina murna marar misatuwa,itama rungumeni tayi saijin dadi mukeyi.
"Sannun da zuwa Mama."

"Yauwa ya'ta ya jikin naki ina fatan ba abinda ke maki ciwo ko."?
"Eh Mama babu."
"Masha Allah."
Komawa nayi wajen su Jidda da suke tajin dadin nace.
"Oyoyo sannun ku da zuwa 'yan kannena."
Na ida maganar ina rungume su tsam ajikina."
Suma saijin dadi sukeyi ranar haka muka jima muna murna.

Ya Taufiq ya fita bayan sun gama shiryawa,ɗaki nakaisu dansu huta.
Wanka sukayi sannan suka dawo falor muna hutawa coffee na haɗa masu mai dadin gaske da saukaka gajiya kowa yasha yanajin dadi har wajen karfe takwas.

Ya Taufiq yadawo dauke da kattin ledoji yayo mana order din abinci.

Oyoyo su Jidda ke mashi,a hankali na mike nataro shi tareda ansar ledojin Pizza ce sai Shawarma da Kaji,a wata makimanciyar leda kuma ice cream ne.

Flats Aisha ta ɗauko aka zubawa kowa sannan na dauka nakaima Mama,a dakin da suka sauka.

Da sallama a bakina ta amsa,isketa nayi zaune bisa sallaya tana lazumi.
"Ya'ta sannuki miyasa zakiba kanki wahala maimakon kibasu Jidda sukawo haba Aminatu."

Murmushi nayi na zauna gefenta nace.
"Aaa Mama aiba wata wahala kuma likitama yace in yawaita motsa jikina."

"Ai hakan yanada kyau motsa jiki gamai juna biyu yanada mahimmamci musamman idan ciki ya tsufa."

Murmushi nayi nace.
"Mama yasu Mina da Haidar."
"Suna hannun Baban su,kinsan ankoma makaranta shekaranjiya Kabir ya maidasu Kano."
"Wlh Mama inason Ya Abdallah yabani Amina,amman yaƙi yarda."

"Hmm Aminatu kema kinsan Abdallah bazai iya bada Amina ba,ba yanda banba akan yabar mani ita kodan kamar da take da mariganya yaƙi yarda."

"Sai hakuri wlh kaunar da yakema mahaifiyar ta,shine ya koma kan Mina kuma ganinta nasa yaga kamar Husna ce."
"Gaskia kam Allah dai yai mata rahama."
"Ameen Mama,dan Allah kici abincin kada yai sanyi."
"To kefa kinci."?
"Aaa yana falor zanci."
"Kinga muci wannan abincin yai mani yawa."

Tare mukaci abinci cikin kwanciyar hankali,munjima munajin abincin kiran Ya Taufiq nagani murmushi nayi nabasar kamar banganiba tana gefena aje.

"Aminatu bakiga ana kiranki ba."?
"Am Mama bakomai fa."
"Aaa kiɗaga ba dadi ana kiran mutun yaki dauka."
Tsinkewa tayi sai kuma aka kuma kira,ɗagawa nayi.

"Kinga Mama shine kika manta dani ko."?
"Aaa bahaka bane."
"Yane faɗaman."?

"Bakomai."
"Inajiranki ɗakina."
Shiru nayi na aje wayar.
"Kamar Hussein ko."?

Gyada kaina nayi.
"tashi kije kiran mijinki,kinji ya'ta."

tashi nayi nace.
"Bari inzo muyi fira."
"Sai kindawo ya'ta takaina."
Ina fita nayi falor na iske su Jidda suna kallo,ɗakin shi na shiga yana zaune gefen gado yana waya.

Zama nayi gefen shi,ɗagoni yayi ya zaunar dani saman cinyar shi.
"Aaa Hassan kanar Inna mungama magana da ita gaskia."

Inajin haka nasan da Ya Tariq yake waya.
"Okay nayi tunanin da Aira za'azo."

Shiru yayi sai kuma yace.
"Okay shikenan haka za'ayi,sai anjima ina gaida little Major."
Bye.
Yana kashe wayar yace.
"Kibar mijinki da yunwa kin kyauta."
yai maganar da alamar fushi.
"Sorry my love."
"Uhmm bazanba sweet heart"

"Bari inkawo maka sorry pls."
"Okay naji kawo mana."

Kitchen naje na duma mashi nashi abinci sannan nakawo mashi tareda coffee.
Stool na janyo na aza sama sannan na zauna saman gado ina kwantawa.

Coffen yafara sha yadan kalleni yace.
"Wife taso kici abinci kinji."
"Nakoshi."
Ina ɗan yatsina fuska ga bacci nafaraji har naji gajiya kafata tayi mani nauyi sosai.

"Mi kikaci da zakice kinkoshi."?
"Tareda Mama nayi dinner."
"Iyeh masu Mama kin kyauta."
Yanda yai maganar yasani dariya nidai bance komai ba.
Bacci yafara ɗaukata sama sama,da haka nayi bacci.

Washe gari da safe Ya Taufiq yatafi Company,ina zaune a gefen Mama,tana ɗan danna mani jikina muna fira mai dadin gaske.

"Aminatu idan kika haihu da sati biyu zamu koma gida,naso Mubaraka tazo dandai bata lafiya,wlh duk ji nike na takura,zama gidan suruki sai hakuri."
"Haba Mama ki saki jikin ki,kuma ainan din gidan ɗankine bawai gidan sirikiba dan Allah kidaina cewa haka."
"Hmm ya'ta duk da haka akwai nauyi."

"Wai miyasamu Antyn ne."?
Nayi maganar dan kauda zancen Mama.
"Zazzabi take fama dashi shiyasa."
"Allah yabata lafiya."
"Ameen ya kikejin jikin naki."?
"Banji komai Mama alhamdulillah."
"Allah ya saukeki lafiya."
"Amin."

Haka zaman yai mani dadi sosai musamman idan naga su Mama kusa dani.

Wasa wasa kimamin kwanan su Goma a Istambul watan haihuwata ya tsaya dan zai iya haihuwa kowane lokaci tsakanin kwana biyu zuwa ukku masu zuwa haka EED dina ya nuna.

Da yamma Ya Taufiq yace mu shirya zamuje yawan shakatawa,banyi gardamaba saboda nima inason in yawata kodan jin dadin jikina.

Shiryawa mukayi nasa Jallaya Black and pink su Jidda kananan kaya sukasa da Jacket ta sanyi,Mama itama abaya tasa.

Haka muka fita ba inda muka amsa kira sai.
*Nezahat Gokyigit Botanik Bahcesi* muna zuwa Park ɗin kowa yai inda yake bukar zuwa dan yaba idon shi abinci.

Mun yawata sosai sannan mukayi hotuna baki ɗayan mu,nayi nida Ya Taufiq sannan mukayi tare da Mama muka sata tsakiya,danagan mukaje *Grand International Zoo* ,mukayi kallan namin dawa kala kala abin gwanin birgewa,munfi jimawa a can har magrib nan mukayi dayake akwai masallaci sannan muka fita har zamu wuce gida yace bari muyi order tun a mota ya gama mana komai,after 30mint sukace komai ya zama ready.

Haka muka isa har *Mesopotamian Terrace Restaurant* ,muna zuwa muka zauna masu aikin Restaurant din suka taremu cikin girmamawa suka kawo mana tea a cikin kofunan glass,wani irin daddaɗan kamshi ya baɗe wajen take naji inason shan tea din,kasancewar Kasar Turkey kasace mai albarkar kayan tea kala kala koda bakasa suga ba idan akai maka wani haɗin sai kaji dadin shi,duk inda kaje zaka iskesu da kayan tea kamar daimu Buzaye suma haka Allah yaimasu asirin shan shayi,shiyasa abin yazo mana adaidai antuna mana asalin mu na buzanci.

Kowa yasha tea din cikin jin dadi,kamar yanda suka ɗibar mana lokaci haka suka kawo mana Order dinmu su Jidda suka ansa sannan muka tafi gida ana isha'i.

Salla kowa yayi sannan mukayi dinner atare saidai Mama atakure takecin abincin ita da gaske nauyin Ya Taufiq takeji amman shi baijin kunyarta danshi Ya Taufiq baida soke soke wai surikanci shi baida bakunta ko kaɗan.

Muna gamawa ko firar kirki ba wanda yayi kowa yai daki,daukar abincin nayi naba Jidda takaima Mama dan akwaita da kawaici sosai.

Da haka nayi daki,na iske gogan nawan yana aiki a system zama nayi ina taya shi ta hanyar yimashi fira wani yai dariya wani kuma yadan kalleni,irin shirmamman nan har goma sannan muka kwanta.


_JAIL_

Ma'akaitane dauke da Hajia Mufida duk sun dade hancin su da marufin fuska ba inda suka amsa kira sai asibitin da suka ware dan kai mararsa lafiyan su.

Koda aka kai Mami duk gwaje gwajen daya kamata ayimata dan gano lalurar dake addabarta amman abu ya faskara,daman akwai wanda ke communication da Ya Samir,shima yaje asibitin shida Tariq halin da suka ga Mami yakara ɗunguza hankalin su makura har lamarin ya ta'azzara fiye da lokacin da sukazo mata ziyara banda aikin wari da kudaje dake addbarta ba abindake dawainiya da Mami,ga idanunta ba fitar da wani ruwa marar kyawun gani.

Bayanai likitocin sukaima ma'aikatan da suka kawota sukace basuga cutar dake damunta ba,nan likita yaimata tambayoyin lalirar jikinta,nan tagaya masu sababin cutar sihirine yadawo kanta,kowa ya tsorata sosai.

Haka likita ta sallamesu aka maidata gidan Kaso banda hantara da wulakanci ba abinda ma'aikatan ke mata suka maidata gidan Yari su Samir naji gani ba yanda suka iya.

Koda aka maidata prison sai dode hanci yan uwanta keyi suna tsinemata suna kaikayi koma kan masheƙiya har aka wurgata dakinta tana kuka tana kome abun duniya yaima Mami kunci,hatta aiki an hanatayi ko abinci saidai akawo mata aturo mata kwanon abarta ciki taci haka akemata saidai lalura sannan za'a budeta taje ta biya bukata,haka rayuwa ta kasancewa Mami,kullin ji take kamar ta mutu inama hanging dinta akayi da azabar da takesha ta rayuwa saidai muce inalillahi wa'inna ilahirraji'un.

Itako Anty Hafsat kamar banza haka takoma agidan yari batada katabus kullin cikin bin umurnin Cankwai take,duk ta lalace tajeme dan dai ita ciwon ta yai sauki duk kurajen jikinta sun mutu sai duhun da tayi.


_ISTANBUL_

Cikina ya katsa mani sosai na dafe cikina ina.
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un Mama....

Naja maganar a wahale bansan na dukeba ina sakin nishi mai wahalarwa take gumi ya gama rufeni salati kawai nikeyi.

Janyo wayata nayi na danna kiran Mama dana gani ɗagawa akayi.
"Aslm Aminatu ya kike ya jikin naki."?

"Wayyo Mama cikina ke ciwo dan Allah kishigo ban iya tashi zan mutuuuuu....

Naja kalamar da karfi ina hawayen azaba,kashe kiran tayi kamar daga sama naji anbako kofa Mama ce jikinta ko sai rawa yake tana salati.


"Aminatu maimakon ki kirani shine zaki ɗagama mutane hankali."
Inajin haka nagane Mamace nakira tsabar azaba da nikeji kamani tayi ta yafa mani gyalen ayabar jikina milk ta dauki waya tace akira Ya Taufiq.

Ana kira kamar jira ya dauka jin muryar Aisha.

"Auta ya jikin Antyn taki."?
"Kazo Ya haihuwa."
Ɗit ya kashe wayar niko cikin daya murda muka saiya lafa mani har nafara zubar da yanayin jinin haihuwa.

Ko minti goma bamu cikaba kamar daga sama Ya Taufiq ya faɗo da a firgice kaina yayi ya tallaboni ko ta idon Mama baibi ba,tashi Mama tayi muka fita kamar kwai haka Ya Taufiq yasani baya,sannan Mama ta shiga tana rungume dani muka kama hanyar aibiti duk da akwai yar tazara kaɗan,ba inda muka ansa kira sai *Acibadem International Hospital Istanbul Turkey*
Asibitine dake dauke da kwararrun likitoci ga karrama yan adam suna ganinmu aka daurani bisa gado dan danan suka shiga dani dakin Haihuwa kowace mace da nata a cikin matarnity department cikin ikon Allah kamar antado mani nakudar ciwo ya kaure gadan gadan sosai nike nakuda haka suka tant duka rufeni sai Dr Gursim itace wadda ta amshi haihuwata,banda inalillahi ba abinda nike zabgawa cikin ikon Allah fire ta fashe daganan haihuwa ta taho sosai da taimakon Allah na haihu duk wahalar danasha hankalina baibar jikinaba inaji na haihu kukan baby ya gauraye illahirin dakin.

"Alhamdulillah."
Shine abinda na furta.

Cikin kankanin lokaci nurse sun fara gyarani wasu na kimtsa baby bayan an bani ita tana cikin jinin haihuwa kur naima yarinyar da ido tsabar kamar da takeyi da mahaifin ta kamar yai kaki duk da tana jinjira amman kana gani zaka gane jinin Ya Taufiq ce,addu'a nahau yimata na daura daman kirjina fatar jikin mu ta gogu da juna.
Sosai nike mata addu'a Allah yakareta daga sharrin zama, Allah yatsareta da mugayen mutane mahassada da sharrin shaidanu addu'a nai mata sosai,wanda nikejin wani irin sonta.da kaunarta ba ratsani na musamman wanda bansan iya karshi ba,lallai soyayyar uwa da ɗa daga Allah ne shike sashi a kirazan iyaye,mikama Nurse ita nayi.

```Abu mai mahimmaci ga iyaye shine idan Allah yasa kuka haifi ya'yan ku,kuma kuna cikin tunanin ku da hankalin ku,ku daure kuyi masu addu'a a lokacin da suke cikin jinin haihuwa insha Allah ba shamaki kowace irin addu'a kukayi ,Allah yasa mudace.```

Bayan an gyara wajen aka maidani,rest room wajene mai dadin gaske gami da nutsuwa toilet na shiga na gyara jikina ga sabbin pant nan sai wanda ka zaba sannan ga parts nan kala kala sai wadda kikeso zakiyi anfani da ita dauka nayi na saka na gyara jikina,shigowa akai da babyna aka bani ita har an samata kayan jarirai hakan ya tabbatar mani Ya Taufiq ya koma gida kenan nima kaya nurse tabani na sauya na zame towel din jikina ta amsa takai toilet din komawa nayi na zauna sannan ta bani wani tea wanda sukeba masu haihuwa kafin kasha komai amsa nayi nasha bata jimaba saiga Ya Taufiq ya shigo idon shi kanmu sai murmushi yakeyi kana ganin kasan farin cikin dayake ciki bai misaltuwa yakai minti ukku tsaye sannan ya zube ƙasa yai sujudur shukur yajima sun kuya kafin ya ɗago sai ga kwalla idanun shi suna zirara ya karaso wajen mu,ya zauna gefena kamo hannuna yayi cikin nashi yana murzawa ahankali yace.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E47&48



"Allah ya tsundumaki aljanna matata,sannu da kokari yau nine zan dauki gudan jinina cikar burina rabin raina hasken rayuwa ya'ta abar sona Allah nagode maka ni Hussein nine na zama uba ashe da rabon zanga jinina Minal,Aminatu dagske kodai mafarki nikeyi."?
Murmushi nayi mai haɗe da zirarar da hawaye hannun mu sarke dana juna nace."Ba mafarki bane dagske ne Allah ya azurtamu da tsarkakakkiyar zuriya."
Hannu yasa ya amsheta sai mamular baki takeyi da hannu alamu yunwa takeji.Kur yai mata da ido, yana sakin murmushi mai nuna tsantsar farin ciki dajin dadi.

Gefen gadon da nike ya zaune ya dauki dabino na cikin kwali ya tauna ya saka mata abaki dandanan ta shanya sau ukku yabata sannan ya kafa bakin shi cikin kunnuwanta yai mata kiran sallah gami da huduba,harya gama sannan ya dago kanshi ya kalleni cikeda tsantsar farin ciki gami da kulawa yace."Allah yaraya mana Asma'u bisa sunna yasa mai jinkan iyayece Allah yarabata da sharrin zamani yasa ta dauki kyawawan halaye na mai wannan suna Allah yatsare gabanta da bayan dan darajar sayyidina rasulillah."
Baki ɗayan mu,muka ida da (SAW).
Baki ɗayan mu ya rungumemu banda tsirarar da hawaye ba abinda nikeyi musamman danaji sunan ya'ta,saboda bantaba maganar sunan da zai sama ya' ko ɗan da zamu haifa ba,saboda nasan indai mace muka haifa sunan Mum zaiyi haka inna mijine Abba ne,wani irin so da kaunar mijina yakara lullubeni gami da kaunar kyautar da Allah yaimana badan munfi kowaba saidan rahamar shi data wadatu akan kowa yau nice dauke da ya'ta kuma Asma'u sunan masoyiyata,aminiyata,yar'uwata kuma kawata tabbas,Allah shine abin godiya.

Dakyal na saitaita kaina nace."Dagaske sunan yarmu Asma'u."?"Kwarai kuwa masoyiyata Asma'u suna mafi daraja acikin sunaye tsarkakken suna,shine Allah yaci da ita."Allah mungode maka Allah ya raya mana bisa suna."Ameen matata,sannunki da kokari Allah yaimaki albarka uwar ya'yana abin alfaharina."
"Yawwa mijina."
Kuka Asma'u tafara ba kyakkyautawa da sauri nurse suka shigo su biyu suka karbi babyn nan sukace abata nono tasha.

Zaunar mani da ita sukayi ajikina Ya Taufiq ya tayani dage rigata nan nafara feeding dinta.

Da taimakon Ya Taufiq takama tafara sha bakina ɗauke da addu'a tajima tana sha sannan Ya Taufiq yafita,saboda ƙa'idar asibitin mutun biyu basu shigowa wajen patient

Please Login or Register in order to submit comment