Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga tension ba.

Daman nasan cikin yan biyu sudin na sakeyi saidai mace da namiji na haifa,ina ganin na haihu fatana inga ya'ta kada Husnata ta mutu kukan da nike kenan.
Rest room aka kaini nida ya'yana ina kuka.
Munjima Yan Taufiq yazo a sirace ga murna yanayi amman fargabar da yake ciki ya danne murnar da yakeyi.
Sannu yai mani sai huduba da yai masu yace.
"Ansamu Maryam da Abubakar."
Allah ya raya nace a sirace,Mum tazo tabna bani hakuri da sannu,wasa wasa ba asamu kan Husna ba saida ta kwana sannan tafara numfashi hankalinta kuwa saida ta kwana biyu asibiti sannan aka sallameta ban samu zaman jin dadiba saida tadawo.

Cikin daren nan nida Ya Taufiq bamu kwashe ta dadiba ban taba ganin bacin ran shiba kamar ranar ashe yanada tsananin fushi har saida su Abba suka shiga maganar sannan ya yafe mani sannan yace indai ba yan gidan muba,baisan kowane dangi a yan uwana ba ya nisanta ya'yan shi da kowa.
Inaji ina gani nahakura nasan yar uwata taja mani kuma banda gaskia.

Haka akai suna komai yai dadi haihuwata ukku gidan Ya Taufiq ya'ya biyar,yan biyu sau biyu nayi.
Itako matar Ya Tariq yan biyunta ukku,yan biyu kyautar Allah.

Bayan wani lokaci muna zaune na aza kaina saman cinyar Ya Taufiq Barr Bashir yakirawo shi waya suka gaisa yasa shi handfree nima nagaida shi yace.

"Major ashe Antyn Aminatu tarasu daga baya nikeji Allah yaimata rahama."
Ameen ya amsa suna fira yace.
"Wlh naje bincike gidan Yarin Maza akan wani case na wannan mutumin Junaid nan nikejin labarin."
"Junaid kuma ba yana yari ba."?
"Eh wlh a gidan yarin ya kuma wani laifi rigima ta hada shi da wani Isma'il daga yakaima abokin fadan nashi duka shine ya bugar mashi gefen wuya take rai yai halin shi wlh lamarin ya daga mani hankali abun sai hakuri ya tabbata shi ya kashe shi yayi faɗa da mai kararren kwana da ace baida laifin kisa akan shi da gidan yarin aka kawo shi to ga laifin kisan da yayi na Asma'u ga wannan daya karayi dole aka yanke mashi kisa ta hanyar rataya,yau kimamin wata biyu kenan da mutuwar Junaid."

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un."
Mukace bansan kuka ya kufce mani ba da sauri nayi daki,nan nabar Ya Taufiq yana taraddadin mutuwar Dr JJ.

Ranar sukuku nayini inajin ba dadi nidai zuciya ta mai rauni ce haka Ya Taufiq yaita hidimar shi kotani baibi koda yai wanka nasaba nike zabar mashi kaya amman naga da kanshi ya zabi abin shi kasa daurewa nayi nace.
"Amman kasan nike fiddo maka kaya shine zaka dauko da kanka."?

"Saboda inada hannu,ke dake kukan rabuwa da masoyinki ai kwara inbarki ki sarara tunda ko abinci kin kasanci."
Cikin fushi yai maganar,tasowa nayi zaisa riga na rike nace.
"Banda masoyin da yafi mijina kawai dai ita mutuwa ta gaji haka matukar kasan mutun zakaji na dadi wannan shi ne amman mijina shine rabin raina, masoyina,jigona abin alfaharina,kuma uban ya'yana akwai masoyin dayakai wannan."?

Ina shakkar botsarewar Ya Taufiq."
"Hmm dadin baki ko?miyasaki kike kuka bayan kinsan bansan kukan ki."
"Tausayine kawai amman nadaina."
"Yawwa ko kefa Allah yajikan shi da gafarta mashi."
"Ameen ya rabbil alameen."

Da haka nataya shi kimtsawa cikin so da kauna,muka koma falor cikin iyalan mu gwanin birgewa sai wasan su suke Haidar naima kannen nashi dariya musamman Husna dake soki burutsunta,tana mashi shagwaba shiyasa Abban su kece mata *Matar Haidar* sai ta dinga murna tana cewa nice ta Ya Haidar.

Shima yanaji da ita fiye da sauran kannensa sunfi shakuwa da juna rayuwa muke cikin aminci nida iyali idan suka samu hutu sai muje Turkey idan yakare sai mudawo gida,wanibi Haidar yana zuwa wajen Mina hutu ko akawo mani ita zumunci da sahihin so da kauna ke tsakanin zuriyata data mariganya Asma'u komai gwanin dadi ta kowane bangare saidai ince Alhamdulillah.

*Tammatbillah🖊️*


_Godiya ta,tabbata ga Allah dayakawo mu wannan lokaci,yabamu ikon gama wannan book cikin aminci na Lokacine Allah mungode maka salati da daukaka,aminci su tabbata ga Baban Faɗimatu Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa,sahababansa baki ɗaya ameen🤲🏻_

*Jinjina da godiya mai tarin yawa agareku Masoyana yanda kuka bibiye wannan labarin tun daga* _Alqalami ,Bakin Jinina Yajaman,Qaddarata,Haka Allah Yaso_ *har gamu mun kammala* _Lokacine_ *cikin ikon Allah saidai ince Allah yasaka maku da alkhairi yabiyamaku bukatunku na alkhairi ya shirya zuriya yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali ameen.*

_*Posters* and *Commenters* Allah yabar zumunci, *Lokacine Fan Groups* ina jinjina maku,fatan alkhairi agareku masoyana inaganin sakoninku saidai ince Allah yabiya bukatu na alkhairi ameen summa ameen🤲🏻_


Tarin fargaba,firgici,tsoro tareda da ɗimbin zullumi sune suka taka rawa a cikin zukatan al'ummar wata Nahiya da suke fama da taraddadi kullin a cikin zukatansu na rashin yanci da halin ko in kula da Ƙasar su ke masu, hakan yasamu asali daga handama da babakere,zalinci da keta gami da mulkin zalinci da suke fuskanta ga shuwagabanin su, musamman matasan wannan Nahiya da suka rasa katabus ko hanyar dogaro da kafafuwan su, bayan sun kasance sune jigon al'umma,ko wace al'umma bata samu cigaba saida nagartattun matasa domin sune ƙashin bayan kowace al'umma.
saidai kash duk da wannan fargaba da wannan al'umma suka tsinci kansu a cikinsu ba'a rasa wa'anda suka jajirce ba,ba dare ba rana dan ganin sun inganta wannan al'ummar tasu taya hakan zai kasance?zasu samu cikar burinsu?miya jazama mutanen wannan Ƙasar wannan matsalolin?al'ummar wannan Nahiyar zasu samu cikar burinsu?wace sarƙaƙiya,ƙulalliya,
Kwamacala da katamurmura ke cikin wannan labarin?
tareda ɗimbin darasi,faɗakarwa,ilimantarwa,wa'azantarwa,nishaɗantarwa harma da tunatarwa duk zasu wanzu a cikin wannan daddaɗan labarin wanda ya kwashe shekaru a cikin zuciyar *Yar Mutan Kankia* a kullin idan ina bibiyar lamarin wannan littafin sai inyi dariya wani gu kuma in zubda kwalla gami da nishaɗi saidai al'ajabin dake ciki yafi nutsar da zuciyata musamman idan na duba sakon daya ƙunsa,sai nikeji kamar alqalami na bai taba hakaito labari makamancin wannan ba,duk da narubuta litattafai da dama masu dimbin darasi da faɗakarwa,sai nike ganin wannan daban yake da sauran nasan kun ƙagu kuji wanne littafine wannan,mai ɗauke da wannan darussan ba wani bane face *NAHIYATA AREWA* wanda zaizo maku nan da wani lokaci insha Allah saidai ban ƙayyade lokacin ba,Nahiyata Arewa ya kunshi komai da komai wanda zai saka mai karatu nutsuwa ya nusar da zuciyar shi daga abubuwan daya rafkana sannan zai saka zuciya natsuwa da nishadi dayardar Allah,bari dai inbarku kar incika ku da surutu,indaina lasa maku zuma a baki,ance duk wanda yace shine bashi bane kudai kuci gaba da bibiyar Yar Mutan Kankia domin samun nishaɗin ku.

Saidai Nahiyata Arewa na kuɗine,ina maku albishir bazakuyi danasin siyan saba,sayan nagari maida kuɗi gida,Allah ya nuna mana lokaci lafiya ameen🤲🏻kardai ku manta👇🏻



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment