Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nace.

"Nayafe maka har abada Junaid Allah ya yafe mana baki ɗaya."
Yan siraren kwalla naji suna neman fitowa idanuna nasa hannu na maidasu,ansar Husna Ya Taufiq yayi yai gaba a sanyaye na zuge jika naba JJ kudi nace.
"Ga wannan kayi anfani dasu."
Bansan nawa naba shiba amman suna dayawa.

Amsa yayi yai mani godiya yace."ina kaunar ki beauty da sonki zanyi numfashina na karshe,saidai ina maki fatan alkhairi."jinjina kai nayi saboda kwallan da suka cika idanuna kallan shi nayi idanun shi kaina,juyawa nayi nafita haka shima yatafi yana.
"Ina maki fatan alkhairi Caranci."

Ina fita na shiga mota kallo ɗaya yai mani yace.
"Sai yanzun kikaga damar fitowa kinbar mani ya' sai kuka take."?
A fusace yai mani maganar."Kayi hakuri."
nace asirace ansarta nayi,muka tafi gidan Anty Zainab.
Washe gari muka shirya muka koma Kaduna jibi zan tafi bikin Zainab ana sauran sati ɗaya bikin duk da mungama siyan duk abinda yadace asiya na biki akowane bangare,daman jiya Mama sukazo Caranci tunda can za'ayi biki nima can zanje ba Anka ba,wannan kenan.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E49&50


_End⏱️_


Shirin tafiya biki nikeyi,gobe zan tafi gida shiyasa duk yau ban wani zauna sosai ba,Haidar ke kiran. "Ammi²."
Na'am na amsa shi ina yowa ƙasa dan ganin kiran mi yake mani a tunanina ko Husna ke kuka.
Tsaye nayi ganin Anty Wasila zaune saman kujera ta harde kafa ɗaya bisa ɗaya agefe guda Husna ke wasa da tarin kaya jibge agabanta.
A hankali na ida sakkowa ina riko hannun Haidar sannan na maida kallona wajen Anty Wasila alamun ko lafiya?

Mikewa tayi tazo gabana tana cika tana batsewa tace."Hakimamma yar wuce wuri waike kinsamu gidan Hussein kinyi lumi ko? Bari kiji ko gidan Yusuf Caranci ne sai kin barshi kota bala'i."
Ta ida maganar tana bugar mani kirji har saida nayi baya zan fadi,Haidar ya rike mani hannu duk da yana yaro kallan daya kema Wasila kadai ranshi ba dadi.

"Malama fitar mani gidan mijina ko insa anakaɗa maki dan banzan duka yanzun nan."
"Hahhha waza kisa su dukeni eyeh?zuwa nayi inmaki wani daddaɗan albishir,zuwa jibi kihada kayanki domin ranar zaki zama babbar bazawara domin saki ukku Taufiq zai ɗura maki sannan kuma zaki gantale a titi ki lalace sai kin zama abar tausayi a duniyar nan kowa sai ya tsaneki sannan ki haukace kinga karshen wulakanci kenan ya tabbata akanki."

A tsorace nike kallan Anty Wasila bako shakka fiskarta kadai zaka kalla ka tabbatar da kudirinta akaina dagaske ne, rasa abincewa nayi banda.
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un,aniyarki takoma kanki kuma ta Allah batakiba wlh saidai shirkarki takoma kanki sannan kijini dakyau nida Ya Taufiq har abada saidai bakin ciki yai ajalinki."
Fau! Haka naji saukar mari akunci cikin fushi tamareni danji take kamar ta shakeni,duke nike rike da kunci Haidar tallabe dani yana kuka yace.
"Muguwa kika mari Ammi na."
"Kai a suwa? Mi zan gani haka gidan ubanwa take uwarka waini ina aka samo wannan abun ik....
Saukar ƙarar razanannun marikan danaji su suka dagani dake dukewar dani har Haidar mikewa a tsorace Ya Taufiq ne ya kifa mata mari sanadiyar hakan har saida Anty Wasila tasaki lafiyayyan fitsarin ta a cikin wando.
Wani gigitaccen ihu ta saki mai razanarwa niko da ido nabishi dan bansan sanda yadawo gidan ba,gefenshi Anty Sajida ce tsaye atare suka shigo gidan.

Hannun shi manuniya yake gwada Anty Wasila dake baje kasa tana ihu yace.

"Daga yau Wasila muddin nasake ganin keyarki cikin gidana wlh azim sainasa bindinga na halbeki kowa ya huta,bare wannan koɗadɗen hannun naki ya samu damar taba fuskar matata idanke bakisan darajar kanki ba ni nasan darajar matata.!"

Sakake tayi takasa ko furta uffan sai shafar kunci da takeyi.
Cigaba dacewa yayi.
"Haidar dakike tambayar waye shi,bude kunnuwanki kijini da kyau.
"Ɗana ne wanda kukai sandiyar rushewar jindadin shi tun yana jinjiri kuma Haidar yafi iko da komai na gidan nan saboda shidin dole nane keko ban hada komai dake ba amman kinzo kin zamemani bala'i da lalura,dan haka maza kibar mani gidana tunkan inkaryaki."
Mikewa tayi tana kuka tace.
"Akan Aminatu kasha marina Hussein,bayan hakan da kakeyi fitinace agareta dan ban yafiya,ke kuma Sajida agaban idonki ɗan uwanki ya mareni ina kanwar uwarki bakiji komai ba ko?kega dadi dan uwa to kisani duk wannan abun da nikeyi nima akan tawar yar uwar nikeyi kuma uwarki batawa uwarba,amman duk wannan abun ake wulakantani agaban idanunku baku iya tsinana uban komai ko?shikenan nagode,kai kuma Hussein wlh kaida Aminatu har gaba da abadan abada,ke kuma kijira ranar haukacewa."

"Ke Wasila har gidana zakizo kina jamani Jafa'i yau dinnan zanyi maganinki agidan nan."
Da gudu tayi waje wayar shi ya dauko yai dailing number ba'a daukaba ya kuma kiran wata number ana dagawa yace.
"Wata mata nanan zata fita waje bance kubarta tafita ba."
"Sorry sir ai tafita da gudunta."
Ajiye wayar yayi yana faɗa bisa l,kushin ya kalli Anty Sajida yace.

"Kiyi hakuri Anty amman wlh saina koyawa Wasila hankali ina dalili ta addabeni ta matsama rayuwar matata wannan wane irin bala'i ne."
"Kwarai kuwa ba Allah a cikin zuciyar ta kayimata duk binda kai niya mukam bamuyi dacen uwaba da dangin uwaba basuda halin kirki musamman Anty Wasila."
"Shikenan zata gane shayi ruwane."Yace rai bace.
Niko sai alokacin na zauna na gaida Anty shiko kallo ɗaya yai mani ya kauda kai har yanzun dai fushi yake dani tunda mukaje wajen JJ.
Nima sadda kaina nayi kasa a sanyaye Anty tace."Hussein."
"Na'am."
"Saurin fushi ba naka bane dan Allah kasaki ranka kuma kafahimci matarka bada wata manufa tayi hakan ba."
Kallona yayi niko naki yarda inkalle shi duk yanda yaso hakan.

"Anty minayi bakomai fa."
"Aaa nasan komai tunda kuka dawo gidan Yari kaki kasaki jikinka da yarinyar nan,tabaka hakuri amman kakiyi miye haka."?
"Anty dan Allah kifahimceni....
"Ya isa Hussein nasan waye kai nasan abinda zaka iya nidai nakashe wannan maganar kanajina."?
Ɗan shiru yayi sai kuma yace."Shikenan Anty komai ya wuce kuma bazaki karajin komai ba."
"Yauwa dlɗan kanina Allah yai maku albarka ya kareku daga sharrin mahassadan ku,ai kodan makiya kun dunga yima juna uzuri."Insha Allah."
Mukace tashi nayi nakawo masu lemo na zuba na bata sannan na zuba mashi suka amsa.
ta danjima sannan ta tashi zata tafi saiga Haidiza mai aikina tafito daga BQ har Anty ta shiga mota tace.

"Ranka shidade akwai babban al'amari da idanuna suka gane mani ɗazun."Anty najin haka ta fito daga mota."
Kusan atare mukace "miyafaru."?

"Ɗazun naga wannan Antyn taku tana binne wasu layu ta cikin lambu sannan ta shigo cikin gidan inaji tana magana da Hajia shine nazo insanar maku."

Jikina yahau rawa kamar mazari ko ɗaga kafara ban iyawa Anty tace suje wajen da aka binne layar aiko suka bita,najima ina addu'a ji nike kamar zan fadi kasa dan jiri dake neman kadani.

Salatin da suka rafka shine ya kara gigitani bansan na isa wajen ba,layune guda bakwai sai fidda tiriri suke kamar an dafasu a cikin wuta,Ya Taufiq zai dauka Anty tai saurin rike mashi hannu tahana kowa tabawa waya takira Abba ta sanar mashi halin da ake ciki ko minti shabiyar ba ahadaba saiga Abba da Mum da Ya Samir kowa hankali tashe har lokacin layun suna hayaki amman sun fara sauya launi,waya Abba yakira wani mutun yace.
"Akaramakallahu dan Allah taimako nike nema inbada damuwa zansa ɗana yazo daukarka zai kawoka gidan Major Hussein akwai matsala."
Bansan miyace mashi ba naji yace.
"Nagode kwarai."
Sake kiran waya yayi yace.
"Hassan kaje ka taho da malam Tasi'u yanzun nan."Nidai ina jikin Mum banda hawaye ba abinda nikeyi Haidar dauke da Husna dan mun rude ita kadai muka baro,kuka take kwalawa Hadiza ta amsheta ta goyata kowa yai jigum tsabar razana.
Motar Ya Tariq ta shigo tareda wani kamilin dattijon mutun mai cikakkar kamala,Abba ya taro shi suka iso wajen nan Abba ya gwada mashi abin da muka gani.
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un."Shine abinda yaketa maimaitawa sannan ya duka yayi addu'oi ayatulkirsiyu,ikilas,falak da nasi sai wata addu'a yayi ya jima sannan yai bissimillah ya dauki layyun still suna hayakin su.
Kallan mu yayi yace.
"Ina Aminatu."?
A matukar tsorace nace "gani nan."
"Alhaji zamuje a warware wannan aikin muga mike cikin shi,saidai inda hali muje da Aminatun domin ga sunanta nan ajiki."
"To ranka shidade zamu iya zuwa baki dayan mu."
Cewar Ya Taufiq yai maganar cikeda da damuwa.
"Eh bissimilla zamu iya zuwa."
"Baki dayan mu kowa yai mota katan Hijab ya dauko mani nasa muka tafi gidan malamin dake dauke da almajirai masu yawan gaske babban mutun mai shekaru.

Wani ɗaki ya shiga ya jima mudai muna zaune a wani katan waje dake shinfide da tabarmu kowa yai jigum dashi.
Yafi minti talatin ya fito hankalin shi a matukar tashe ya zauna yana facing dinmu ya kallemu yace.
"Alhaji Mukhtar wannan yarinya Amina tayi babban arziki domin da ace aikinan yaci nan da sa'a ashirin,abu na farko aurenta da mijinta zai lalace har abada,na biyu zata haukace ta farraka,kuma ba wanda zai kara tada labarinta koda iyayenta,mijinta ko ya'yanta ne har abada."
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un."Mukace kowa jiki ya mutu ba mai katabus,Ya Taufiq yace.

"Dan Allah malam kataimaka mani wlh inason matata minene mafita."Allah yataimakeka yaro ni ba abinda zan iya maka sai abinda Allah ya qaddara maka,ƙa idar aikin muddin wani mahaluƙi yaga abin to aikin ya lalace sannan zai koma kan mai shi,wannan shine."

"Alhamdulillah."
Muka furta ina kwalla yace."Dan haka ku kara dagewa da addu'a Allah zai zama gatanku."
"Nagode maka akaramakallahu Allah yasaka maka da alkhairi."
"Kagodema Allah Alhaji Mukhtar."
Munjima sannan muka tashi tafiya alkhairi Abba yai mashi yaki karba,can mukabar Abba muka dawo gida kowa jiki mace.

Har dare ko bacci nakasa jinayi antabani bansan na rungume Ya Taufiq ba nasaki kuka mai tsuma rai."Minayi masu suke son suga bayana?mina tsare masu basu kaunata?miyasa suke son su raba tsakanin mu?miyasa suke son sabauta mani rayuwa."?

Sake rungumeni yayi yana buga bayana munjima a haka yace.
"Duk wannan wahalar da sukeyi sai Allah (SWT) ya zama gatanki majibincin lamuranki saboda kinsa tsoron shi a cikin zuciyarki kuma insha Allah ba wanda ya isa ya raba tsakanin mu,kisa aranki komai ya faru dake rubutaccen al'amarine tun daga *Alqalami* badan kedin mai *Bakin Jini* bace saidai koma minene yana cikin *Qaddararki* ba wanda Allah baiso yake jaraba shi saboda *Haka Allah Yaso* kuma komai daren dadewa komai zaizo karshe tunda komai *Lokacine* gashi a hankali Allah yana kawo mana lokacin azzalumai marassa tsoron Allah ina sonki matata kuma ina kaunarki ke tawace har abada da izinin Allah."

"Inason ka mijina dan Allah kadaina fushi dani idan nai maka laifi."
"Naji daina kukan, kalaman da Junaid ke makine sukai mani tsauri dayawa amman komai ya wuce kinji tawan."?
"Nagode I love you."
"Love You too,gobe sai Caranci ko."?
"Eh da safe ne tafiyar."
"Allah yakaimu zanyi missing dinku sosai."

"Zanzo daurin aure dan Allah kikula da kanki sannan kada kimani sakaci da ya'yana."
"Insha Allah zan kula."
Da haka mukayi bacci.

★★★★★
_CARANCI_
Tunda muka sauka ina gidan Mama nan na aje kayana duk da cewa gidan cike yake da dangi hakama gidanmu dankare yake da dan Adam.
Amare kuwa suna gidan Anty Mubaraka can mai gyara ke gyarasu har kunshi da komai can za'ayi masu.

Kowa yaji dadin isowar mu tuni muka shiga akaita hidima damu duk da kana ganina kasan ina cikin damuwa.
Mama taimani tambayar duniyar nan,akan mike damuna naki sanar mata komai gudun kada ta shiga damuwa gashi tana hidima.
Shiyasa naki gaya mata itama kyaleni tayi,hidima muka sosai da yamma na koma gidan su Husna wajen Mama can na kwana dakinta,kuma ranar Anty Murja tazo ana jibi biki itama gun Mama ta kwana haka suka tisani sai nagaya masu damuwata.

A-Z nagaya masu banda salati ba abinda sukeyi take suka shiga cikin damuwa.
"Gaskia mutanen basu da imani Allah ya maida masu aniyar su musamman Wasila itace hatsabibiyar."cewar Anty Murja.
Ameen muka amsa.
Kwantar mani da hankali sukayi har naji damuta ta ragu sosai da haka muka kwanta.

Washe gari su Mum Anty Sajida da zuriyar su kaf harda dangin Abba sukazo bikin ana gobe daurin aure.
Murna mukeyi musamman danaga harda Fatash sai nakara sakin jikina,fira muke sosai dasu Anty Aisha matar Ya Tariq.
Kullin ina kan waya da Ya Taufiq gani yake kamar za'a biyomu a illatamu kullin cewa yake inkula dasu Haidar.

Washe gari da misalin karfe biyu aka daura auren Zainab da Ya Abdulmutallib,sai Rahima da Ya Abdallah kowa ya shaida ana gama daurin aure dadyn Husna ya kirani waya.
"Kisameni falorn Baba ina sauri zan wuce."

Ina zuwa na iske shi sukuku cikin farin yadi yai mashi kyau ainun.
"Ina kikabar Husna."?
"Suna wajen Anty Murja harda Mina suna mata wasa."
"Okay badai abinda ke damunki ko."?"Eh babu kaifa."Kewarku ke damuna,dan Allah Ammi kada ki wuce jibi garin nan."
"Habakace sati biyu zanyi yaufa kwanana bakwai fa."?"Eh nafasa nidai kidwo gida kedasu Mum."Shikenan insha Allah."
"Zan wuce ki kara kula banda sakaci."Kun gaisa da Mama."
"Eh dukkan su mun gaisa daga gidan nike."
"Abinci fa katsaya dan Allah."Aaa karkidamu su Abba da Ya Samir zanbi."
"Allah ya tsare."
Rakiya nai mashi mukayi kicibis da Anguna tare da amaren su gwanin birgewa.
"Angunan kamshi wannan kyau Allah yasa alkhairi."Cewar Ya Taufiq.
"Ameen."
Suka amsa suna dariya,hotuna akeyi nan akai mana baki dayan mu sannan su mazan sukayi tare muma matan akai mana tare,tafiya mukai har suka tafi sannan nadawo.

Bakaramin kyau amaren sukaiba komai iri daya suke sawa hatta lefe iri daya suka hada masu hakama angunan sunsha ankon su.

Kiran wayar Baba ya shigo wayata ina dagawa yace,insame shi dakin shi har kuryar shi na iske shi.Zama nayi gefen shi,bayan mun gaisa yace.
"Ashe Hussein din yatafi gaskia naso insake yimashi godiya akan dawaniyar dayayi mana Allah yakara rufa mashi asiri yakara arziki yakare shi da kariyar shi."
"Ameen Baba naso ya tsaya yaki wai yana sauri zaibi Abba ne."
"Gaskia mutanen nan sunsan mutunci Allah yabiyasu."Ameen."
Na amsa a sanyaye.
"Ya'ta tunda kikazo nike tambayarki mike damunki."?Da ban niyar gaya mashi ba sai kuma nasar mashi komai.
Yai mamaki saidai addu'a yaita yimana ta neman kariya sannan yace."Addu'ar iyaye bata faduwa kasa banza nasha gaya maki wannan kalmar ya'ta,duk wanda ya ƙulla Allah ya warware maki Aminatu insha Allah,baki taba ganin komai sai alkhairi dan haka kisaki ranki ko Mamanki bance tasani ba kinji."
"Toh Baba insha Allah."
Bayan ya sallameni naje wajen su Zainab nida Fatash muka rakasu wajen su Baba.
Huduba akai masu ana la'asar aka fara shirin kaisu gidajen auren su.

Ina shigowa gidan mu daga gidan su Husna na iske Umaima bayan gida zan dauki kaya tana shan banalin kayan maye sai wannan abu takeyi jikina yai sanyi sosai ganin lamarin Umaima gaba yakeci.

Zagina tafara tana.
"Sa'idinawa ba yanda zakiyi damu,munyi gaba na baya sai labari kuma zakiga bala'in da baki zato."
Nidai daukar abinda nai niya nayi bance mata komai dan dagani ko shakka banayi Umaima batada hankali addu'ar shiriya nai mata natafi.

_*KANO*_
Da kaina nakaimu Kano nasan da Ya Taufiq na nan bazai yarda intuki ba yafison ko ina zani yakaini ko yasa Usama yakaini.
Direct gidan Rahima na sauka dani da ya'yana Haidar,Mina sai Husna duk suna baya a gaba kuma Anty Rukayya ce.
Muna shiga gidan nata kowa saida ya yaba tsaruwar shi,domin sabon gida Abdallah ya kera mata nagani nafada komai na gidan yayi tsari daga furnitures har gidan kanshi gwanin kyau.
Ranar nidai can na kwana ina kwatantama Rahima ina bata shawarwari.

Washe gari Abdallah yakirani waya yazo muka gaisa ina kara mashi kwarin guiwa akan auren ba laifi ya saki jikin shi sosai kuma yana son Rahima, saida akai azahur sannan natafi gidan Zainab.

Shima gidan ta yai kyau dandai ita ba bene bane sabanin Rahima flat house ne amman yai tsari sosai nan na iske Salima kanwar Ya Mutallib sune masu hidima zumuncin mu yakara kwari sosai.
Gidan Zainab masha Allah saidai kaf furnitures din dake gidan Zainab suke gidan Rahima ba abinda aka banbantasu komai iri dayane gidane banbanci kowane da kalar kyaun nashi.

Ana gama walima muka fara shirin tafiya,tun Zainab na kuka har dai muka taho ana cemata kowa da haka yasaba.

★★★★★★
Bayan kwana biyu biki ya watse mukai shirin komawa gida,kunya ta kamani dan ansan sati biyu zanyi Mum tace saina ida kwanakin dana diba.
Baba Hassan yace inbi umurnin mijina haka kuwa akayi,Mama tahada mana kayan biki muka tafi gidan su Asma'u mukaima Mama sallama ita taimana alkhairi da haka muka tafi sai Kaduna.

Bayan Wani lokaci muna zaune a compound din gida bisa kujeru mukaji ana rafka mana jifa a gate dagani har Ya Taufiq muka mike sai Husna dake gujegujenta Haidar yatafi makaranta nima inada tsohon ciki,mai gadi ya bude kofa yana waye kemana jifa.

Gani mukayi an han kado shi yafadi kasa,Anty Wasila ce ta shigo daga ita sai ondi/buje kanta warwatse ta hargitse shi tanata wake wake tana soshe soshe ga yara bayanta suna mata ihu mahaukaciya³ itako sai dage ondi take tana binsu tana saina kasheta bata ba zaman aure.
"Komawa nayi bayan Ya Taufiq ina lekenta yowa tayi kanmu yasa securities suka riketa sai yaye ondi take tana ihu haka kayi waje da ita,inalillahi wa'inna ilahirraji'un nikeyi araina jikina ya mutu matuka dakyal na koma cikin falor, cikina na murda mani take nakuda ta kaure mani ba kakkautawa kamani yayi muka shiga ciki zai kaini asibiti,ai kafin ya dauko hijab yasa mani fire ta fashe mani,ina gani haka nayi karfin halin cewa yabarnu haihuwace zan iya yinta a mota.
Haka ni kadai sai shi dake dafani yana mani sannu,aiko haihuwa tataho gadan gadan banda azaba da nikeji har na haihu kukan jariri ya karade wajen harya kira Anty Sajida saboda tafi kusa damu tana zuwa bada jimawa ba cikina ya kuma murdawa na haifi wani ashe cikin twins gareni amman hoto ɗaya ya nuna,lallai Allah gwani,haka na haifi ya'yana duk maza zar Anty ta taimaka wajen gyaramu dagani harsu muna cikin koshin lafiya alhamdulilah.

Murnar da Ya Taufiq yayi ta dabance haka akaita murna kowa har gida su Mama sun sani,danko Husna nasan babies saijin dadi take,hakama Haidar kowa yanajin dadi.

Sati na zagayowa sukaci sunan Mukhtar (Abba) saiYusuf(Baba) anyi suna ansha shagali sosai su Zainab da Rahima duk sunzo suma da tsohunan cikkuna na wata bakwai zuwa takwas anyi komai angama cikin ikon Allah.
Haka rayuwa ta kasance gwanin dadi da salama.

Bayan wasu shekaru ina tareda yara suna wasa Ya Taufiq yana aiki a cikin system dinshi ina mashi dannar kafar shi nace.
"Abban Husna ina neman alfarmar ka idan badamuwa."
"Inajinki Ammin Haidar fadi bukatarki insha Allah zammaki."
"Allah yasa,daman inason indawo da Umaima hannuna kaga rayuwar datakeyi banjin dadi ga shaye shaye kilan idan ana bata kulawa da shawarwari kila ta shiryu."
"Ki canza wani abun banda wannan."?
A sanyaye nace.
"Miyasa.?"
"Bazan dauko abinda zai rusa mani farin cikiba kuma kada ki manta kwata kwata baifi sati biyu mutafi Saudia ba kina zatan zan iya barma Umaima ya'yana hidimar Hussein kadai aikine."

"Amman karka manta Umaima yar uwatace kuma ga gidan Mum sai mukaisu."
"Aaa bazan iya zama da itaba gaskia."
Raina yabaci saina danne naci gaba da abinda nikeyi ban kuma cewa komai ba.

Haka muka mai dasu Hassan wajen Mum muka tafi aikin hajji har mukayi aikin mu cikin aminci duk da bawani dadewa mukayi ba bamu wuce sati biyu har muka dawo nadan huta sannan aka maidosu mun danyo tsaraba kafin kaya su iso,shiko Ya Taufiq cewa yayi ibada yaje na sayen kayaba da kyal nasamu ya kara mani nawa zanzan kadai ya dauko.

Rayuwa nike gidana banda wata matsala nida zuriya ta,komai na tafiya yanda ya kamata,still bayan wani lokaci na sake yima Ya Taufiq maganar Umaima shima bai bada hadin kaiba saina kyaleshi.
ni inason in maido Umaima wajena insa akoya mata sana'oi na hannu sannan in Allah yabata miji tayi aure kamar sauran kannen ta yawon titi da shaye shaye ba abune mai dadiba amman yaki yarda kilan dan ba yar uwar shiba ce da ya yarda.

★★★★
Abubuwa da dama sun faru ina kwance kiran Mama ya shigo wayata kuka take sosai tabbas hankalina ya dugunzuma nasan ba lafiya.
"Mama miyafaru dan Allah kiyi mani magana."
"Aminatu narasa yar uwata,narasa Antyna inalillahi wa'inna ilahirraji'un."
"Mama wace Antyn dan Allah kidaina kuka."
"Anty Hafsat ɗita tarasu Aminatu."
Bansan na saki wayar ba ina kuka.
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un."
Akidime Ya Taufiq ya shigo saidai yanda ya ganni yasan naji labarin mutuwae kuka nike sosai hada mani kayana yayi dan ban iya komai sai kuka da nikeyi ko kaya ban sauyaba hijab nasa sai Airport yai mani komai nida Mum muka tafi.
gidn Fatash yakai yaran daman bani goyo nayaye su Hassan,tun jirgi nike kuka har Katsina Mum kebani hakuri mota mukahau ɗan Anty Murja ya daukemu muka hadu da ita sai Caranci gidan Kakanmu.

Sai koke koke aikeyi ashe kwanan keso tayi har an mata sitira gaban gawarta na iske Mama tana mata addu'a tana hawaye nima addu'ar nemata ina kwalla anbude mana fuskarta duk ta lalace tayi bakin wahala a cikin raina na kara jaddada yafiyar danaima Antyna nikeyi ina roka mata dacewa da rahamar Allah,su Umaima kuka take tana birgima Khadija da Hajara suma kukan suke sunama mahaifiyar su addu'a kowane da ya'yan shi a cikin su.
mahaifin su yazo akan gawarta ya yafe mata tareda addu'a da haka aka kaita gidanta na gaskia lamarin ba dadi kwanana ukku su Ya Taufiq da Abba sunzo sadarka ukku muka tafi tare saidai na takura Ya Taufiq dan dole yabarni na koma da Umaima badan ranshi yaso ba.

Haka nadawo gida har mutuwar ta lafa naja Umaima jikina sosai tasaki jikinta kuma tarage abubuwan da takeyi duk abinda takeso ina mata,na saimata waya na maidata KASU karatu Buss Admin takeyi inason takoyi kasuwanci.

Haka na zauna da Umaima gwanin dadi bata nuna mani wani haliba tagoge sosai tayi kyau har takai aji biyu kuma ba laifi tana kokari sosai.

Lokaci ya shuɗe sai Allah ya kaddara mani samun ciki da wuri tsakanin haihuwar su Hassan da wannan ba wani nisa wasa wasa haihuwa ta ukku zanyi,saina dan damu amman Ya Taufiq abin nema yasamu dan murna har kyauta yaimani dagani har shi ba wanda yasan da ciki saidai naga sauye sauye ashe cikine haka naita renon cikina cikin aminci da kulawar mijina.
Umaima ita ke shirya Husna zuwa makaranta duk da naga sun saba amman tana yawan hantarar ta saita nuna wasan jika da kaka taje da ita saboda sunan kakarta kenan ta wajen uba shiyasa ban wani damuwa tafiyin ɗa sa Hussein.

Har cikina ya tsufa watan haihuwa ta ya kama mani inata shirin haihuwa kowane lokaci.

Akwai wata rana bazan taba mantawa da itaba ranar muka tashi da tashin hankali wanda saura kiris aurena ya mutu saboda fusatar da mijina yayi,mai aikin mu ta kama Umaima tazubama Husna guba a cikin abinci harta fara bata taci,shine ta shigo falorn taji warin gubar koda tahumi Umaima rigima ta kaure ina sama na yunkuro na taho ga tsohon ciki Umaima na ganina ta runtuma ana kare ranar Juma'a duk maza na masallaci shiyasa ta gudu da sauri na iso wajen har guba tafara dibar Husna bansan na tallabota ba idanun ta sun kakkafe kuka nafara nasa aka dauko madara saidai a bude in dure mata har gwangwani ukku wani irin kuka Husna keyi daukar waya nayi na kira Ya Tariq a dimauce yayo gidan mu ya sunkuceta mukayi asibitin shi l,aka sata emergency tun amota ta kece da zawo.
Na gaza tsaye bare zaune kuka nike bansan mi zancema uban yarinyar nan ba l,gashi yar uwata ce sila daman daya ya aminta ta zauna gidan shi na bani ni Aminatu abinda nike cewa kenan.

Banko dakin da nike zaune naji anyi Ya Taufiq ne idanun shi kamar rushi yayo kaina jikina yahau bari cikina ya katsa nafirgita da yanda nagan shi fizgoni yayi da karfi ya riko habata yace.
"Idan har wannan tsinanniyar yar uwartaki ta kashe mani ƴa wlh saina dauki mummunan mataki akanki kuma kinsan abinda zan maki.
Ya ida maganar yana turani akushin rike cikina nayi wanda haihuwa ko yanzun da alama Ya Taufiq ya haukace ya manta juna biyun dake jikina.

Kuka nike sosai Mum tashigo tana mashi fadi kamar zata duke shi,wani Doctor ya fito mukayi kanshi duk da tsohon cikina haka nike zarya har gudu dan fargabar rasa Husna ya girma azabar nakudar da nikeji sama sama ga barazanar saki ina fuskanta nasan shine hukuncin da mijina zai mani dan bai hada ya'yan shi da kowa ba.
"Doctor wane hali ya'ta ke ciki."?
"Kuyi addu'a ana kan cetan ranta amman gubar dataci tai mata illah."
Bansan sanda na yanke jiki na fadiba ruwa aka dinga saman farkawa nayi naganni jikin Ya Taufiq kowa ya rude kamar da nakuda nafarka akayi matarnity dani.
"Ya'ta ku kawo mani ya'ta dan Allah."
Abinda nike cewa kenan haka na shiga dakin haihuwa cikeda da fargaba ga bala'i daman tun ina budurwa idan bala'i yakai bala'i take period ke zo mani koda ba month dinshi bane ban iya

Please Login or Register in order to submit comment