Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na dauki spoon nafara bashi abincin amsa yayi yanaci,niko kamar ana mani dole duk natakura banda dariyar mugunta ba abinda Fatash keyi ta kasan makoshi falor suka koma shiko sai yanga yake mani sake ɗebowa nayi na mika mashi ya rike hannuna,kallan kallo mukema juna idanun mu sarke dana juna yatsan shi yasa ya lagudi karan hancina yace."My Queen kinason kiyima mijin ki horo da yunwa ko."?
"Imm imm ba haka bane daman....
"Sheet."
Ya azamani yatsan shi bisa lip dina saitin kunnena yace.
"Kishirya zamuje Anka."
Ware idona nayi jin abinda yace domin inasan in tabbatar da gaskiar abinda yake faɗa.jinjina mani kai yayi alamun tabbatarwa.

Wani sanyayyen dadi naji bansan nayi hugging dinshi ba dadi har kasan zuciya ta haka naji.
"I love you my hero."
"Love u too my heroine."
Murmushi nayi cigaba da bani abincin yayi da kanshi yana mani fira.
"Princess"..."Uhmm Prince."
"kidinga cin abinci sosai bansan kibar mani babyna da yunwa."
Ya ida maganar yana aza habar fuskar shi saitin kafaɗata har kumatunmu na mannuwa dana juna.
Mamaki ya isheni idan suna cewa inada ciki nidai banji alamun inada komai ba.
"Yaya nifa banda wani ciki."Girgiza kanshi yayi yace.
"Bazaki gane abinda nike nufiba take care of your self my sweet heart."
Nidai da idanu naraka shi bance komai.

"Romeo and Juliet shanyar kuka shanya ta bushe zamu wuce gida."
Fatash tayi maganar tana dariya.
A sanyaye na mike bisa cinyar shi duk naji wani iri.,Shiko ko ajikin shi falor muka koma mukahau fira ko 30mint basu karaba driver yazo daukar su,rakiya mukayi masu sannan muka dawo ciki.
Bedroom muka wuce nataya shi rage kayan shi da haka mukayi wanka har muka shirya sannan muka zauna muna lido cikin so da kauna.
Sosai Ya Taufiq ke shagwabani shi ala tilas mai ciki,bai bari inyi Komai saidai mai aiki keyi abinci kuwa kodai yai mana Order ko kuma Mum ta aiko mana dashi.

Wani lokacin gidan Ya Tariq muke Lunch haka rayuwa ta kasance tsakanina da mijina saidai hamdala.
Nida iyayena kuwa muna kan waya haka gidan su Husna nida Mama kusan kullin sai munyi waya inajin lafiyar yarana su Mina.Mama tace suna Kano gidan kakanin su iyayen Abdallah.

Shima Abdallah mukanyi waya dashi yanzun kusan kullin banda zancen da nikema Abdallah irin yayi aure tunda Asma'u ta rasu yaki yayi aure hatta su Baban Husna sun mashi magana yaƙiyi hakama iyayen shi.

Hakan yasa akace indinga yimashi maganar kilan ya amince yayi tunda yanajin maganata ya zamar mani abokin shawara duk wasu matsalolin shi yakan kirani ya gaya mani komai amincin dake tsakanina da Asma'u shine yakoma tsakanina da Abdallah.

Duk yanda naso Abdallah yai aure yaki idan na takura mashi da zancen wanibi sai yahau kuka kamar karamin yaro hakan yasa Ya Taufiq yace inrabu dashi insha Allah komai lokacine zaiyi watarana nima da haka na hakura da maganar, ni kaina idan akace Abdallah yai aure wani kishin mariganya ke kamani saidai nasan komai rubutaccen al'amarine babu yanda za'ayi mutun magidanci kamar Abdallah yaki aure nima nasan rayuwa bata yuyuwa a haka,wannan dalilin kesa ina danne nawa kishin nike bashi shawarwarin da zasusa ya dangana yai aure,wannan kenan.

********
Bayan kwana biyu muka shirya zuwa gidan Mum,farin less nasaka mai ratsin lemon green a jiki riga da siket ne sun mani kyau shima Ya Taufiq farin wani yadine yasa mai santsi sai black din hola da takalma, muna fitowa compound din gidan Usama ya iso da sauri ya bude mana mota hannunmu sarke dana junahar gefen mota muka tsaya

"Usama kaje Company sannan ka tafi da wannan motar bada ita zan fita."...."Okay Sir."
Yace yana kamewa kamar wani soja.
Wajen wata bakar mota muka isa da kanshi ya bude mani gidan gaba na shiga ya rufe shima ya zagaya zai shiga da sauri Usama ya bude mashi ya shiga sannan ya rufe yana ɗaga mana hannu,saida muka fita sannan shima ya shiga yai Company,muko ba inda muka isa sai Unguwar Sarki har gidan su,mai gadi ya bude mana muka isa har Lot yayi parking mun dan jima cikin mota shi bai fita kuma ya hanani fita,kasancewar hannun shi na cikin nawa yana murzawa a hankali kamar mai mani tafiyar tsutsa haka nikeji massaging din da yake mani."Babyna."
Na'am."
Na amsa batareda na kalle shi saboda yanda naji muryar shi a sanyaye."gaskia yinin nan da zamuyi gidan Mum zan missing dinki sosai."
Sai lokacin na kalle shi nace."Haba my hero ai muna tare ko."?
Nayi maganar kamar bangane manufar shi.
Uhmm yace ya fita ya bude mani muka fita side din Abba muka nufa.

Cikin private falor dinshi muka same shi yana karanta News hannun shi rikeda Jarida.
Tunda ya amsa sallamar mu bakin shi ke washe kamar auduga sai jindadi yakeyi muna isa gaban shi muka duka ƙasa kuka gaida shi cikeda girmamawa,Da sauri yace."Sannunku da zuwa yan albarka ya'yana abin alfaharina ku zauna."
Ya ida maganar yana nuna mana bisa kushin wadda yake a sama three sita.
Nidai kaina kasa inajin nauyin sirikin nawa.
Zama Ya Taufiq yayi agafen damar Abba niko na kasa zama gefen shi tsabar nauyin shi da nikeji.
"Ya'ta."
Yace yana riko hannuna da alama Abba baijin wani kunyata ko kaɗan dan dagani shi ya' ya daukeni kamar Taufiq.
Zaunar dani yayi gefen shi na haggu sai ya kasance mun saka shi tsakiyar mu,sai naji wani iri a raina.
"Ya'yana."Ya kira sunan mu cikin sanyin murya da tausasawa.""Na'am."
Muka amsa har bakunan mu suna haɗuwa.

"A kullin idan na tuna kuna tare a matsayin ku na ma'aurata kuma ya'yana nakan samu kaina cikin farin ciki marar misaltuwa nakan godema Allah SWT a kowane lokaci,ina rokon Allah yaima rayuwar auren ku albarka ya azurtaku da zuriya ɗayyiba Allah yakareku daga sharrin shaidan da duk wani makiyin ku idan an ƙulla maku Allah ya warware maku ya'yana Allah yaimaku albarka."
"Ameen."Mukace ina karajin so da kaunar Abba har cikin raina sai nikejin shi kamar mahaifina najini tabbas wa'anda ke cewa iyayen miji ba iyaye bane tabbas sun tabka babban kuskure nidai nayi dacen iyayen miji inajin su kamar iyayena sunan iyayena sun mani nisa amman tunda na auri Ya Taufiq banta6ajin nayi rashin iyaye ba kullin burin su,su kyautata mani,gaskia saidai ingode ma Allah banda wata damuwa daga dangin mijina har iyayen shi kowa yana sona hatta dai ya'yan Mami su Anty Sajida suna kyautata mani alhamdulillah.
"Hussein inada yakini araina baka bukatar jaddawa game da amanar da Allah yabaka ta Aminatu kowa ya shaida kana son Amina kuma zakayi adalci akanta saidai ita tunatarwa tana anfanar mumini zan tunatar dakai da abu ɗaya shine Hakuri duk yanda so da kauna yakai so daga inda akai aure ba abinda ke rike da ma'aurata illa hakuri,kasama ranka hakuri,juriya da gabata akan al'amuran mace saboda rauninta inafatan zaka kasance mai yawan hakuri."
"Insha Allah Abba zanyi duk abinda ka umurceni."
"Naji dadin haka Allah yai maka albarka."
"Ameen."...."Ya'ta."
"Na'am Abba."
"Kema ina yimaki nasiha da yawan biyayya ga mijinki, shi zaisa mijinki ya soki fiye da yanda kike zato kuma shi zaisa yaji tausayin ki a kowane lokaci,kuma zai baki kulawa a kowane lokaci kinji ya'ta."...."Toh Abba insha Allahu zanyi kokarin kiyayewa."
"Ina alfahari daku akowane lokaci Allah yaimaku albarka."Ameen muka amsa.
Haka Abba yaita mana nasihohi da labarai sai ya koma mani kamar wani bako,yanda yake mana huduba baka cewa nidin ba sirikar shice ba atakaice munkai one hour a Part dinshi da kanshi yai mana izinin tafiya sannan muka shiga side din Mum lokacin kuwa ana kiran sallar azahur ba kowa cikin falorn ta sai Aisha da gudu ta rugo ta rungumeni."Oyoyo Antyna."
"Oyoyo Auta."
Muka rike junan mu,munjima a haka sannan ta sakeni mukayi sama har falorn Mum.
Itako waya muka iske tanayi."Yeeh Mum ga Anty."
Aisha tayi maganar da karfinta kamar wata yarinya karama graduate sun kutukum da ita amman ta shagwabe intana wani abun ko Jidda batayin shi.

"Ka kira Hassan saika sanar mashi gaskia danaji dadin wannan lamarin Baban yara,ya'yan nakane sukazo anjima munyi magana."

Inajin tace haka nagane da Baba takeyin waya.
Tana kashe wayar ta rungumeni.
"Oyoyo Mamana sannu da zuwa."Sai nan da nan Mum take dani kamar ta goyani ko motsi nayi tace mani sannu ya'ta kamar wata mai lalura nidai har mamaki take bani.

Shiko Ya Taufiq tunda suka gaisa da Mum bata karabi ta kanshi komi ni sai fira take mani.
Tada ikimar salla aka fara mikewa yayi yace.
"To Mum da alama dai kin dainaji dani ko kulani bakiyi komi Minal shikenan idan natafi sallah bazan dawoba."
Ya ida maganar shi dole yai fushi,Murmushi tayi tace.
"Haba ɗan Hussainin Mum baka ganin ita tana bukatar kulawa kaifa haba na Hassanu."
Murmushi yayi yace.
"Shikenan na gane Mum takaina."Da haka ya tafi masallaci nima sallar nayi na zauna bisa sallaya.
Najima sannan Mum tasa muka sauka ƙasa zamuyi lunch.
"Mi kike shi'awarci Mamana."?
"Komi zanci Mum."..."Aaa ya'ta kifaɗi komi kikeso."
"Bakomi komae zanci."
Nace ina zuba shinkafa da miya.Nahauci domin yunwa nikeji sosai,mikewa Mum tayi ta shiga kitchen ita da mai aikinta.
Muko mukaci abincin mu,muna fira jefi jefi da Aisha,shiko Ya Taufiq aiki yafara a system dinshi hankalin shi bai kanmu.
Sallamar Anty Aisha mukaji matar Ya Tariq.
Wani dadi naji har raina,daidai lokacin Mum sun fito da wainar filawa(kalalla6a) ga yaji(tashshi) tayi kyau sosai,ina ganin ta naji yawuna ya tsinke ture shinkafar gabana nayi kamar jira Mum na zuba mani nahauci sosai nikejin dadin ta har cikin raina,ita Anty Aisha zama tayi mukahauci muna fira sai labari ya kaure harda Mum sai fira muke kamar ba Sirikar muba,su Ya Tariq kuwa suna gaisawa suka koma falor shida ɗan uwan nashi sai Aira dake rike hannun Ya Taufiq.

Ranar haka muka wuni gidan Mum har akai isha'i Abba ya shigo, aka hau maida yanda akayi nan Ya Taufiq yace.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E41&42





"Abba next week zamu tafi ISTANBUL insha Allah."Fuskar shi ɗauke da murmushi yace."Hussein kana ganin zanbarka katafi da ya'ta wani waje mai nisa aaa kabarta wajen Mum tabata kulawa musamman kai kaje duk bayan lokuta kazo kaduba iyalinka."Dandanan Ya Taufiq ya marairace yace.
''Abba dan Allah kataimaka mani Allah zan bata kulawa."..."Ya isa Hussein kabar wannan maganar a halin yanzun."Badan yasoba yai shiru cigaba da magana Abba yayi.
"Kaga dai Aminatu tana bukatar kulawa kuma kaida ita mi kuka sani da ace akwai mai kula da ita sai inbarku kutafi tare kai kaje wajen kasuwancin ka inka samu lokaci kadinga zuwa kana dubata."...."Shikenan Abba."
"Hakan ma yayi saita dawo wajena har Allah yasa yadawo."Cewar Mum."Hakan za'ayi isha Allah."Allah yasa cewar Ya Tariq.
Nidai duk abinda suke cewa ina sauraran su saidai Ya Taufiq kana ganin shi ya shiga damuwa ainun,Karfin hali kawai yakeyi.
"Gobe insha Allah zamu wuce Anka amman zamu tsaya ta Caranci."..."Allah yakaimu lafiya,ka kyauta Allah yasa kuje lafiya kudawo lafiya."Ameen muka amsa baki ɗayan mu.

"Ya Taufiq ina zuwa dan Allah."Cewar Auta.
"Okay kishirya sai mutafi tare."Aaa ba inda zata biku tabari tasamu lokaci taje masu hutu."..."Aaa rabi da ita tunda yace zaije da ita."Ba dan Mum tasoba ta kyaleta.
Shirin tafiya muka farayi nace."Auta haɗa kayanki mutafi gida."
"Toh Anty."
haka ta haɗo kayan ta a traveling bag.
Mum takiramu nida Anty Aisha tabamu wata jikka da kaya a ciki kowa ɗaya godiya mukai mata muka tafi har bakin mota Abba da Mum suka rakamu kowa ya shiga mota,muka tafi motar su Ya Tariq ke gaba sai tamu baya har muka isa gida muna parking mukayi cikin falor nan kowa ya zauna.
Aiki Ya Taufiq yahauyi da system dinshi nida Auta muka hau fira sai kusan goma sannan ta tafi daki ta kwanta,nima ɗaki na shiga na watsa ruwa fiddo kayan bacci nayi riga da wando purple masu Armles zama nayi bakin mirrow nafara shafa mai naji maganar Ya Taufiq sanye cikin coffeen Jallabiya,ta cikin mirrow nike kallan shi,kallo ɗaya nai mashi nagane tsantsar damuwar da yake ciki,maida kallona nayi bisa mirrow na dauki humra ina shafawa sannan na iso gefen shi na zauna ina daukar riga zan saka ya rike mani hannu cikeda damuwa yace."Yanzun kina ganin Abba yai mani adalci Aminatu."?
Inaga tunda Ya Taufiq ya aureni harna manta ranar daya kirani da Aminatu.
Cikin siffar kwantar mashi da hankali nace.
"Haba mijina kadaina damuwar kanka karfa kamanta gata Abba keson yai mana kayi hakuri mana."Ansar rigar hannuna yayi ya zira mani sannan ya kwance towel din jikina yace.
"Duk gata bai wuce yabarmu tareba nida kaina mai iya baki kulawane fiye da tunanin kowa."Mikewa nayi na ida zame towel din nasaka dogon wando nace."Hakane amman miyima iyayen mu biyayya haba my Hero."
Murmushi ya sakar mani a hankali ya janyoni jikin shi muka kwanta bisa gado yaja mana blanket kamar mai raɗa yace.
"Idan mun dawo Anka zamuje gidan Alhaji."
"Alhaji kuma."?
"Eh Alhaji Munzali mana."
"Okay Allah yakaimu lafiya."
"Ameen my wife."
Addu'a mukayi da haka bacci ya daukemu wannan kenan.


*****Washe gari*****
haka muka kama hanya cikin ikon Allah har Caranci tunda Allah yasa muka shigo garin mu wani irin farin ciki ya mamayeni har cikin ƙoƙon zuciya ta haka naji ba inda motar mu tayi parking sai kofar gidan su Husna shiga mukayi bakowa Compound din gidan da alama suna cikin ɗakuna,sallama mukayi can najiyo muryar Mama na amsa mana koda ta fito oyoyo taimana ta rungumeni tsam jikin ta,tana."Sannun ku da zuwa ya'yana oyoyo Rahima kuzo ga Antyn ku tazo."Da haka takamani mukayi sitrum din Baba,muka zauna bisa kujeru saijin dadi mukeyi.

Baba ne ta fito daga Bedroom dinshi fuskar shi fal da annuri,baki ɗayan mu muka doƙa muka gaida shi."
Sannunku da zuwa ya hanya sannunku."
"Yawwa Baba barka da rana."..."Yawwa Aminatuna Ya Mum da yan gida."...."Lafiya lau suna gaidaku."
Rahima ce ta shigo hannun ta dauke da tire ta aje gaban mu."Ya Taufiq ina wuni."
"Lafiya lau Rahima ya gidan."..."Lafiya lau,Anty sannu da zuwa."Yawwa kanwata."Haka su Kabir sukaita shigowa suna mana sannu da zuwa gwanin dadi,Baba yace.
"Naji dadin zuwan nan naku daman inasan zanyi magana daku."
"To Baba."Rahima taja Auta suka fita zuwa ɗakin Mama.
"Aminatu."?
"Na'am Baba."
"Magana ce akan kanwarki Rahima ta taso akan Abdallah,mahaifin shi yai mani magana yana son Rahima ta maye gurbin ƴar uwar ta saidai matsala ɗaya dukkan su kowa yaki bada hadin kan lamarin nan,shine nace bari in maki magana ki kwatanta mata, sannan kiyima Abdallah magana kiji ta bakin shi."
Jinjina kaina nayi nace.
"Masha Allah naji dadin wannan lamarin insha Allah zanyi iya kokarina wajen kwatanta masu musamman Abdallah insha Allah komai zaizo da sauki."
"Allah yasa ya shige mana gaba."
"Ameen Hussein insha Allah inaji araina akwai alkhairi a cikin wannan lamarin."Allah ya tabbatar mana dashi."
Cewar Mama.
Haka muka ta6a fira nafito zuwa ɗakin Anty na kira Rahima a waya tana dauka nace ta sameni ɗakin Anty.
To tace bata jimaba ta shigo ta zauna bisa kushin dake facing dina cikeda kulawa nace.

"Rahima akwai maganar da nikeso inyi maki a matsayinki na kanwata inafatan zaki fahimceni."
"Insha Allah Anty inajinki."
"Maganar Abdallah ce inason ki dauki lamarin nan da mahimmanci ma'ana kima iyayen mu biyayya ki auri Abdallah kamar yanda mahaifin shi ya buƙata."Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya tace.

"Anty banki takuba saidai dan Allah kuyi hakuri wlh banjin zan iya auren Ya Abdallah,sai nikeji kamar naci amanar yar uwata ne infact ina ganin Ya Abdallah matsayin yayana Kabir ina girmamashi fiye da duk wani tunani banji zan iya auren Abdallah dan Allah kiyi hakuri Anty."
Kallan Rahima kawai nikeyi ina karantar yanayin ta ƙin Abdallah kawai takeyi ko kuwa tanajin bazata iya auren mijin yayar tabane a hankali na sauke ajiyar zuciya nace.

"Mi kike zato idan Baba yaji wannan maganar kin bijirema umurnin su."?
"Hmm Anty wlh da akwai yanda zanyi in tursasa zuciya ta tabbas danayi kodan cikar burin Baba saboda yana son Ya Abdallah kuma shidin mutumin kirkine kodan inci gaba da rike ya'yan yar uwata zanso hakan."

"Shikenan saidai bazan maki tilas ba amman kiyi tunani kafin wani lokaci zan sake waiwayarki akan wannan maganar kuma ina bukatar jin good news."Shikenan Anty."Da haka na mike nakoma wajen Baba bamu jimaba muka tashi zamu tafi."
Wata bakar leda naba Mama da Anty kowa guda sai naba Kabir dasu Rahima kuɗi,shima Ya Taufiq kuɗi yaba Baba da yaki kar6a da kyal ya amsa,kamar kada mu rabu haka muka tafi gidan Dada.

Itama taji dadin zuwan mu sai murna takeyi yan uwana anata zuwa ganin mu nan na iske Umaima da bangane taba sai daga baya duk tayi bakikkirin da ita gwanin tausayi,amman isakanci nanan a gadarance ta gaidamu muka amsa bayabo ba fallasa.

Munjima dakin Dada sai albarka take saka mana tana mana addu'ar zaman lafiya da zuriya ɗayyiba,su Kawu Ali da Usman duk sunzo akai fira da Ya Taufiq bakacewa sirikin sune daga dakin Dada mukaje bangaren Alhaji Baba shima yaji dadin zuwanmu munkai 30mint muka tashi shima Ya Taufiq yaimashi alkhairi hakama kannen mahaifiyar tawa duk yai masu alkhairi da Dada nima nabata leda atamfa guda biyu ke ciki sai Less guda da dubu ashirin haka nabata da abokan zamanta hatta Umaima saida nabata,amman kamar ta anshi kashi haka ta rike ledar fuskar ta murtuke kamar nai mata dole,nidai bandamu da yanayin taba,duk inda mukaje abinda nike badawa kenan har gidan su Babanmu naje suma sunji dadi karshe mukaje gidan Anty Mubaraka kadaddeni tayi,tanata murna."Ya'ta sannun ku da zuwa Auta Aisha yar Mum sannunku."
Haka Anty taitajin dadi hakama ya'yan ta,kowa yaji dadi itama munjima wajenta daga nan muka tafi Katsina gidan Anty Murja karfe biyar na yamma muka isa gidan nata,lokacin taje kasuwa Central Market.
Zama mukayi da Maryam yarta mukaita fira haka takawo mana kayan drinks.Ita da Aisha suka tafi ɗakinta dagani sai Ya Taufiq zaune a falor.

"Minal mi kika fahimta gameda lamarin Rahima da Abdallah."?
Tashi nayi nakoma gefen shi na zauna nace.
"Rahima batason alaƙar nan saboda kwayar idanun ta kadai ta nuna mani hakan."Minene mafita."?
Kallan shi nayi nace.
"Nabata lokaci inaga kila ta canza shawara."
"Allah yasa ta aminta gaskia Abdallah mutumin kirkine."
Jinjina kai nayi nace.
"Sosaima kuwa."
Sallamar Anty Murja mukaji tareda Haidar ya riko mata kayanta.
"Sannunku da zuwa ya'yana na tsaidaku dayawa"
"Sannu Inna."Cewar Ya Taufiq.
Nima sannu da zuwa nai mata,zama tayi ahaka hau maida yanda akayi sai labari take mana rabi da kwata duk kwatanci take mana zaman yau da gobe,daman Anty ta iya Lecture sosai kuma ta maidamu kamar abokanta haka take janmu a jiki shiyasa mukafi sakewa da ita sosai muma haka muka dauketa wasa wasa har akai isha'i duk bamusan ankira sallah ba dan dole muka yanke shawarar kwana gidan Anty dare yayi bazamu iya tafiya Zamfara ba.

Ranar haka muka wuni ana fira gwanin ban shi'awa saida goma ta gota sannan muka kwanta washe gari da safe misalin karfe goma na tashi,na shirya sannan na fito falor lokacin su Ya Taufiq har sun gama break nima yinayi karfe sha ɗaya muka dauki hanyar Zamfara Gusau,sadda biyu zatayi har mun shiga cikin ANKA har cikin compound din gidan mu,mai gadi ya bude mana gate muka shiga parking kirki Haidar bai gamaba na sakko nayi cikin gida da guduna ina."Jidda,Zainab,Mama,Babana."
Ina shiga falor na iske Baba na kallan News kamar daga sama yajini jikin shi rungumeni yayi yana."Sannu da zuwa ya'ta yar albarka yar Baba."
"Yawwa,inafatan nasameka lafiya Babana."
"Lafiya lau ya'ta."
Daidai lokacin su Ya Taufiq sun iso janye da akwatina sannu da zuwa Baba yai masu yana riko hannun Ya Taufiq suka zauna bisa kushin.
Mama dasu Jidda suka shigo falor da gudu Jidda tayi kaina ta faɗo mani har saida muka faɗa bisa kushin itako Mama bakinta yaki rufuwa maganar Ya Taufiq tadawo dani duniyar farin ciki."Kai Auta Jidda sauki dai bi ahankali."
Kallan shi kawai nike shima ni yake kallo Baba ne yace."Indai Jidda ta cika wauta da ganganci."
Sai alokacin ya sosa keya ko maganar da yaine tasa shi jin kunya da alama dai.
"Sannun ku da zuwa ya'yana."Yawwa Mama."
Itama zama tayi tanata mana barka da hanya.
Zainab ta shigo da abinci ta aje agaban mu tana mana sannu da zuwa.
Kamar jira itada Aisha akahau firar su ta kawaye.
Ya Taufiq da Baba suma fira sukeyi kasancewar kujera ɗaya suke zaune da alama magana mai mahimmanci sukeyi hakan yasa Mama tajani mukayi bedroom dinta.
Muka zauna cikeda kulawa tace.
"Aminatu."Na'am Mama."
"Ina mai farin cikin ganin ki cikin kwanciyar hankali dajin dadi,yau kam da wahala inyi bacci tsabar farin ciki dajin dadi ya'ta"
Kwanciya nayi na daura kaina saman cinyarta,ina facing din face dinta nace.
"Mama tabbas nasamu kwanciyar hankali kuma hakan yanada nasaba da samun kulawar miji hakama iyayen shi da yan uwan Ya Taufiq kowa yana sona suna kyautata mani Mama."Tabbas yanayin ki kadai ya nuna haka Allah yasaka masu da alkhairi."Ameen ya rabbi."

"Kinsan ranar laraba zai koma Turkey wajen aikin shi."Allah yakaimu yasa albarka ke wajen Mum zai barki ko."?
"Eh haka Abba yace wai zanfi samun kulawa bazai bari yatafi dani ba."
"Yaka mata kisan cikin fari bai kamata abari ki dinga nesa da gida ba saboda kulawa."

Tashi nayi zaune na kalli lafaffan cikina sannan na maida kallona ga Mama nace."Wai Mama dagaske cikine dani."?
Kallan kuruciya take mani duk da baza'a kirani da mai kuruciya ba kuma ya kamata ingane hakan kodan fannin dana karanta kenan amman nidai banji komai ba kuma banji wani abu mai kama da laulayi.
"Kwarai kuwa Aminatu wannan dalilin yasa Abban ku yace bazaki bishi ba."
Jinjina kaina nayi ina mamaki nidake dauke da cikin bansan dashi ba sai wasu zasu gane,da haka na watsar da zancen araina,haka Mama taita bani shawarwari masu matukar mahimmanci,da haka mukayi sallah sannan mukaci abinci.

Ahmad da Khadija (yar Anty Hafsat) suka shigo tare lokacin karfe biyar na yamma shi yadawo daga aiki ita kuma tadawo makaranta UDUS nan aka samar mata admission saboda aurenta ya mutu tana jawarci harda maida ya'yan wajen mahaifin su,sai karamin shima yai wayau sosai shike hannun Mama,dayake gidan mu Khadija tadawo da zama sosai tayi murnar ganin mu, kowa sai farin ciki yakeyi musamman ni idan naganni cikin yan uwana,ranar munsha fira saida dare yayi aka fara tafiya ɗaki.

Mama takirani tace.
"Aminatu ga ɗakinan kima mijinki magana sai ku kwana nan tunda akwai ɗakuna ko."?
Hakanan naji nauyin Mahaifiyar tawa nace.
"Aaa Mama tunda akwai inda ake sauke baƙi saiya kwana shida Haidar."
"Aaa Aminatu Hussein ba bako bane kuma kinga mijin kine,shi kanshi Aliyu ɗakin Ahmad zai kwana ba masaukin baƙi ba,ke kuma kije gun mijinki,Aisha kuma ɗakin Zainab kinji yanda za'ayi bansan musu."
Badan nasoba nayi shiruna fito zuwa falor lokacin Baba yana masu sallama zai shiga ɗakin shi yace.
"Mamana kuje ku huta kinga kun kwashi gajiya ko."?"To Baba saida safe."
Zama nayi,yi yayi kamar baiga zama naba,sai danna wayar shi yakeyi,sai Haidar da Ahmad dake fira suma basu jimaba sukai mana sallama sai lokacin ya kalleni yana ce masu saida safe.
"Wife ya da kallona."
"Hmm katashi inkaika masaukin ka."
Kallona yayi yace."Kedin ina zaki kwana."
"Ɗakin Mama."
Nayi maganar ina kauda kaina gefe.
Mikewa yayi ina gaba yana bayana har dakin mu,komai agyare yake masha Allah,yana shigowa ya rufe kofar harda saka key.
Kallan shi nakeyi nace.
"Ga gado nan ka kwanta."
Na ida maganae ina riko hannun shi ya zauna gefen gadon ya janyo na zauna yace.
"Ke bazaki kwantaba."?
"Eh yanzun zan tafi ai."
"Aaa tare zamu kwana ya zakibar mijinki shi kaɗai."?Marairaicewa nayi nace.

"Haba Ya Taufiq baka ganin gidanmu mukazo kawai sai in kwna wajen ka.""Harum ne."?
Girgiza kaina nayi nace.
"Ai da kunya ko."?..."Hmm ke kikasan ta."

Ya ida maganar yana daura tafin hannun shi saman cikina yace.
"Ki dinga kula dazun saura kaɗan Jidda tai mani ganganci da baby na."Mamakin Ya Taufiq nikeyi ashe abun na ranshi nace."Tunda ka nace inada ciki naji zan kula."..."Good girl."
Sai kuma yace.
"Minal kina daukar lamarin nan da wasa ko?ki tambayi Mama."
Ɗan zaro ido nayi nace.
"Kawai sai in tambayeta ai da kunya."Wani kallo ya watsa mani yace.
"Minal Allah ya shiryeki karki manta da ɗan halak ake ado ba wata kunya."
Kwantar da kaina nayi a kirjin shi ina lumshe idanona nace."Nagaji zanje in kwanta."
Gyara mana kwanciyar yayi yace."Kwanta idan kinyi baccin kin koma can ko baby na."
Murmushi kawai nayinaci gaba da baccina shiko bansan sadda yai nashi ba.


""""" """"""" """"""
Haka rayuwa ta kasance har ana gobe zamu koma gida shiri sosai Mama take mani daman tinda nazo tafara yimani gyara na musamman iri iri hatta maƙotan mu sun bamu kulawa duk mun shiga wurare da dama mun gaisa da jama'ar arziki gaskia mutanen Anka nada kirki sosai,har gidan Alhaji Tijjani aminin Baba saida mukaje Bakura Sokoto suma sun mana shatara ta arziki kowa yaji dadin ziyarar mu,hakama mutanen arzikin Mama kamar a Anka aka haifemu haka suke mana kara Kamar wasu Katsinawa sun karramamu fiye da tunanin mu,itama Mama ta rabama makota tsarabar da mukayi kowa yasa albarka.
Haka mukasha hutunmu kwanan mu biyar a gidanmu kulawa sosai nike samu daga wajen Mama har Baba hakama kannena koda mukafara parking ɗin komawa gida Kaya Mama ta haɗa mana da tsarabar da zamu kaima su Mum duk tayi mana katuwar gana mazgo dankare da

Please Login or Register in order to submit comment