Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutun batareda yasan hakan ba saidai kawai mugodema Allah shi kadai yasan dalilin nuna mana wannan lokacin."
Jinjina kai kawai nayi ina jin dadi araina.


"Bari akawo maku juice saiku kara gaisawa ko."?
Toh cewar Ya Taufiq.
Fita tayi nidai ina zaune duk lakkata ta saki sai kasala da nikeji kadan kadan.

"Minal dan Allah dagaske kukan da kikeyi ba wani abu ya sameki ba."?
Kallan shi nayi yana gabana duke ashe ya shido bisa kujerar da muke zaune.

"Ya Taufiq da ace ada irin waɗannan kwallan nikeyi abaya tabbas danayi dace da hawaye masu sanyaya zuciya saidai ina bahaka bane,inayin hawayen nan ne tsabar farin cikin daya mamayeni wanda bantaba jin makamancin shiba nasoka masoyina na kaunace ka kamar in rasa raina harna sare daga samun ka ashe lokacin ne Allah bai kawokaba sai nikejin fargaba kadan araina inama yanda Abba yasamaka albarka a cikin lamarin nan nima Baba zai saka mani albarka cikin sanyi dajin dadi danafi kowa dacen masoyi wanda ya soni a duk yanayin dana tsinci kaina baka taba gudu naba Ya Taufiq asalima ta silarka ne na fito daga ramin dana afka ka maidani na zama yantatta a cikin dubun na mutane musamman yan uwana,inama Husna taga wannan lokacin wannan shine cikar burin kawata taganmu tare a matsayin ma'aurata saidai Allah bai nufa ba...

Kuka nahauyi a hankali inajin wani iri araina.

"Kidaina kuka matata insha Allah zan sakaki farin cikin da baki tabajin makamancin shiba a wannan rayuwar zan zamar maki jigo bango abin jinjina zan zama bawanki zan maki hidima Minal,zan soki kuma nasoki zanci gaba da sonki har abada ina fatan Allah ya hadamu a gidan aljanna amatsayin ma'aurata kaunarki tana tareda bugun numfashina Allah ya cika mana burin mu na alkahiri."

Ameen cewar Anty Murjanatu data aje mana ruwa da lemu tace.

"Kudai kuci gaba da gayama Allah kukan ku insha Allah komai ya kusan zuwa karshe ku dage da addu'a ba dare ba rana Allah shine maijin rokon bawa."
Insha Allah,mukace na dauki ruwa nasha,wayata tahau ringing naga Baba ya bayyana dagawa nayi yace.

"Mamana kina tareda Hussein din."?
"Eh Baba."
"Yawwa yaka mata kije ki sayo kayan tun kinga kinje Katsina kinadawowa saiki dinka kinga munkusa tafiya Anka."
"Insha Allah zamu biya."
"Yawwa ya Antyn taku."?
"Lafiya lau take"
"ki gaida mani da ita." yace,sannan yai mana fatan alkhairi ya yanke kiran.
Maida kallona nayi wajen Ya Taufiq nace.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E9&10



Ina kara miko sakon ta'aziyya agareki Zainab Yar gatan Maman Sultan Allah yakara bada hakurin rashi yasa aljanna firdausi ce makoma agaresu da dukkan daukakin al'ummar musulmai baki ɗaya🤲🏻


★★★★
Maida kallona nayi kanshi nace.
"Ya Taufiq zaka kaini kasuwa zanyi siyayya kafin mu wuce gida."
"Okay bari muje yanzun idan muka gama saimu biyo tanan mu wuce."
"Tohmuje."tashi mukayi baki dayan mu,yana gaba ina baya har muka fito Compound din gidan daga can gefe cikin Kanofi Anty ce zaune da Jidda bisa roba Chair sai fira sukeyi, kallan mamaki kawai take mana har muka isa gabanta.

"Kufa ina zuwa ko abinci baku ciba"?
"Zamuje kasuwa Baba yace inje insai kaya,kinga nayi zuwa ɗaya basai na kuma dawowa ba."
"Gaskia kam amman kubar mani Jidda kuje sai kundawo."

Itako Jidda Sarkin yawo harta marairaice kamar zatayi kuka.
"Haba autar Baba zan maki tsaraba,cewar Ya Taufiq.
Murmushi tayi taji son banza tace.
"Sai kundawo Allah ya tsare."
Ameen muka amsa mata muka shiga mota yaja muka tafi sai Central Market.

Sosaima kasuwar ta sauya mani inada yakinin inda ni kadai ce nazo tabbas zan iya cewa makuwa nayi gashi ta cika tab da dan Adam sai cinikayya akeyi,wani katafaren shago muka shiga zan iya kiran shi da super market sabida babu ce kawai babu a cikin shi amman komai saidai ace masha Allah.

Kaya nafara dubawa shima Ya Taufiq wani sashen yayi yaba zabar kaya kowa da hidimar shi.

Atamfofi masu kyau na dauka kala biyar sai lace ukku material biyu kala goma dai na zaba masu kyaun gaske zuwa nayi na dauki inners dayake a side din akwai Cashier na biya na inners din sannan nazo wajen da zanyi payment din atamfofi na biya aka sakamani aleda Ya Taufiq na tsaya jira wajen 10mint bai zoba nakira shi waya bai dagaba har zan tafi neman shi sai gashi yataho da kaya a basket kallon shi nike daga rakiya ya bige da daukar kaya,costimetics ne sai turaruka sai wata leda a hannun shi lissafawa akayi yace a hada da atamfofina.
Nabiya akace mashi yana gama payment suka daukar mana kayan mu zuwa boot sannan muka shiga muka tafi.
Kowa yai shiru a cikin mu daidai zamu shiga Goriba road yace.

"Ke harda wani saurin biyan kaya ko."?
"Aaa bahaka bane gani nayi tunda inadasu duk dayane danna biya."
"Uhmm to daga yanzun indai muna tare karki kuma biyan abu nine zan biya kinajina."
Insha Allah nace,ina murza yatsun hannuna har muka isa gidan Anty a falor muka isketa tana cin snack itada Jidda oyoyo cewar auta ta rugume ya Taufiq sannan ta rungumeni zama mukayi nan fa Ya Taufiq yabad
ta choculates yaba Anty wata leda nan fa na nuna mata kayana ta yaba sosai tasa albarka ana gama la'asar muka tafi gida sai albarka take samani sai naji inama itace yayar Mamata ance dangin uwa sunfi son ya'yan yan uwan su amman nidai dangin ubana sune yan uwana domin sunfi rufa mani asiri, dangin mahaifiyata ɗaidai kune masu kaunar mu da nuna mana tsantsar kauna irin ta dangin uwa da sukema ya'yan yan uwan su.

"Babyna ina zaki kai dinkin?"
"Zankira toiler inbashi measurement sai yai mani anan Katsina yake sunan shi SHUGABA ya iya sosai."

"Okay kibani rabin kayan inkaima toilor din su Fatima shima ya iya bazasu jimaba sai kimani text din Measurement dinki."
Okay shikenan haka za'ayi."
Daidai Haidar ya saka hancin motar shi cikin unguwarmu karfe biyar saura muka shiga gida sannu da zuwa mama ke mana yawwa mukace sannan muka shiga falorn Baba.

"Oyoyo ya'yana abin alfaharina sannun ku da hanya ya kuka baro Ummar taku."?
"Lafiya lau Baba tana gaidaku,inji Ya Taufiq.

Gaidashi mukayi yace ya Taufiq ya zauna gefen shi,a kunyace ya zauna sai naga yafara jin nauyin Baba ko miye dalili.

Kayana na fiddo ina gwadama Baba saiga Mama ta shigo da dambun nama sai lemu ta aje mana ta zauna tana ganin kaya sai albarka take sawa jidda kuwa ta choculate take tana murna Ya Taufiq ya siya mata.


Leda Mama ta dauka tace wannan fa mike ciki.?"
"Aa ta Ya Taufiq ce."
Nace ina kallan shi harara ya dallamani take nagane nufin shi,sai kuma nace.
"Siya mani yayi."
Budewa nayi turarukane da kayan shafa a ciki sai sarka sosai Baba yasa mashi albarka kamar wani bako haka akai mashi godiya nima godiyar nai mashi yace bakomai fita waje Baba yayi itama Mama dakinta ta shiga tareda Jidda mu biyu suka bari kamar jira yace.

"Ke ko inkikazo hannuna sai kinyi bayani wai kayana ni mace ne."?
Dariya nayi nace,da kayi kyau sosai inka zama mace."
"Hmm Allah ya shirya mani ke babyna."
Ameen sweet heart."
Murmushi nayi nafara cin dambun nama,kallona yake can ya anshe flat din marairaicewa nayi nace"Pls kabani wlh bai isheni ba yayana."

"Ke ga kura ko bazan bada ba."
Ba yanda banba ya hanani dole na kyale shi sai dariyar cuta yake mani shima ci yayi ji nike kamar in fada ciki,amman yai biris dani saida ya kusa cinyewa ya mikomani.
"Amsa idan ba halinkiba."
Amshewa nayi ko kunya banjiba naci abuna shidda dai dai ya mike na bashi dinkin ya tafi nan yaima Mama sallama yace zai kwana kano gobe zai wuce Kaduna,da haka suka tafi shida Haidar, ina dawowa daga rakiya wanka kawai na shiga duk nagaji.

Bayan kwana biyu zaune nike bisa sallaya nagama sallah ina tasbihi Zainab tazo tace,Mama nakirana mikewa nayi naje atamfa da shadda tabani tace inkaima Dada.
To nace da ita,ina gama shiryawa na saka jihab dita red na tafi sai gidan Dada.

A florn na isketa ita da Alhaji Baba.
"Oyoyo ga amaryata sannu da zuwa lale marhabin."
Murmushi nayi nace.
"Tsoho mai ran karfe na gaishe ka kyauta."
"Na amsa Aminatu yar masu gida ya iyayen naki."
Alhmdulillah suna lafiya.

zama nayi muka hau fira da kakannin nawa gwanin ban shi'awa Kawu Ali ne ya shigo rike da leda mikawa Dada yayi.
muka gaisa shima cigaba da firar mukayi dashi.
Tire na daukoma Dada ta zuba mana balango sai baza kamshi yake,baki dayan mu muka faraci bakaramin dadi yai mani ba,saida kowa ya tashi yabarni har mamakin kaina nike yanda nikecin nama bilhakki kamar bantaba ciba,saida na koshi sannan na kauda tire din nadawo.

"Kawu wannan nama akwai dadi gaskia kamar kada indainaci haka naji."
Murmushi dauke a fuskar shi yace.
"Wlh kam ai rabe ya iya nama sosai naso insiyo tsire yanzun yafara aikin."
"Ayyah kasan kuwa nafi son tsire amman wannan dinma yai dadi sosai."
Aikuwa cewar Dada.

Latsa wayata nafara ina Game.

"Aminatu inasan kibani aron hankalin ki akwai abinda nikeson gaya maki."
"Toh Dada inajinki."na aje wayar hannu ina kallanta.

"Ya kamata kiyi aure zuwa yanzun zamannan ba baki bane,Aminatu,ko kindaina son Husseinin din."?
"Kagane mani tsohuwa waya gaya maki nadaina son Ya Taufiq ina son shi mana."
Nayi maganar da sigar zolaya.

"Nasani ko angona yai maki kyau naga yau sai kyasawa kikeyi."
Uhmm kawai nace ina dariyata

"Dariya ma kikeyi dan dadin da kikeji kinsamu zankadeden ango ko.?"
"Haba ni mizanyi da tsoho saiku ni sabo dal nikeso a ledar shi"

"Yar nema naji,yaka mata yafito kiyi aurenki,idan kuma Baban naki kike tsoro kibari da kaina sai in mashi magana shikenan."

"Hmmm bazakiji mutuwar Sarki bakina ba nidai Ya Taufiq nikeso."
"Allah yatabbatar da alkhairi."
Ameen."

Shiru mukayi,kwanciya nayi nacigaba da game dina kirana akayi a waya sabuwar number ne ina gani tayi miscall saidai akara kirana sannan na daga.

"Kawata kin yadani shiru."?
Ajiyar zuciya na shide jin Fatash ce.

"Haba Fatima ina zucin insa number dinki inkira wayarki kuma kinga ban jima dayin wayar ba shiyasa."

"Wlh nima jiya Ya Taufiq yakawo mani kaya akaima Lawalli dinki shine yace in tambayeki wane irin style za'aimaki."?

"Kowane aimani ina so shadda aiman doguwar riga inaga zaifi."
"Shikenan insha Allah zan sanar mashi."
Yawwa nagode nan muka kara taba fira sannan mukayi sallama.

Ranar haka na wuni Dada nai mani maganar aure dan haka da kanta zatazo taga Baba ayi abinda yaka mata.
Nidai saidai in maida abin wasa ina zolayar ta,har saida akayi sallar magrib sannan na koma gida.

Wanka nayi ana isha'i nayi sallah fitowa nayi sitrum din Baba aka hau fira dani sai labarin Anka Zainab kebani da kawayen ta da tayi acan munjima muna fira sai karfe goma na koma daki sakamakon kiran da Ya Taufiq yai mani ne,ina shiga daki nahau wayata sai soyayya muke sha mai saka nutsuwa labari yake bani mai dadin sauraro musamman rayuwar da yayi a Turkishi wani inji tausayin shi wani kuwa dariya nike mashi,munjima muna fira sannan mukayi sallama 11 pm na kwanta bacci ya daukeni mai dadin gaske.


Washe gari kuwa da misalin karfe goma shugaba yazo gidanmu nabashi kyana da measurement dina nace yaima ya'ta dinki a ciki,haka na sallame shi kudin shi ya tafi.



****** ******* *******
Kaduna

"Fatima kinyi magana da Aminatu ya kikayi da ita."?
"Mum nayi amman maganar dinki nai mata."

"Kinji Abban ku yace jibi za'aje nemawa Hussein izinin aurenta kuma harda sa rana duk za'a hada."

"Alhmdulillah,saboda maganar nan tun jiya na matsawa daddyn Amna zanzo gida dan inji yaushe zasu tafi,to Allah yakaimu lafiya daman ance komai lokacine."

"Kwarai kuwa Fatima wani lokacin sai inga kamar a mafarki wai yau mahaifin ku da kanshi yayarda Hussein ya auri Aminatu ko a haka aka tsaya dole mukara godema Allah."

"Gaskia kam Mum Allah abin godiya."
"Amman kina ganin tasaki jikinta da Hussein din kamar da."?
"Eh akwai kyakkyawar alaka tsakanin su Mum amman miyasa kika tambayi hakan.?"
"Ina tsoron kada Aminatu taki Hussein musamman idan ta tuna irin tsanar da Abban ku yai mata ina tsoro kada taki shi.!"

Mum tayi maganar cikeda damuwa.
"Aaa Mum bazataki shi ba wlh suna tare har yanzun."

"Nasani Fatima baki tunanin ko soyayyar yan uwantaka take mashi kinga duk jarabawowin data fuskanta a rayuwar ta duk ta silar shi kodan hakan ina zatan son shi na iya fita aranta."

"Mum dagske har abada Aminatu nason Ya Hussein kidaina jin tsoro."
Allah yasa Fatima,ameen ya rabbil alameen.

Ina yima Jidda karatun Qur'ani Fatima ta sake kirana dagawa nayi nan take tambayata wai ya huddarmu da Ya Taufiq akan batun auren mu.

Sosai kaina ya daure bansan mi zance mataba.
"Minal kice wani abu mana."

"Miyasa kika tambayeni Fatash.?"
"Wlh Mum ce ta daga hankalin ta banjima da barin gidan ba can na wuni nan ta gaya mani komai da Mum ta fada.

Tausayin ta naji ya kamani ganin ta shiga damuwa akan alakata da Ya Taufiq saidai abinda bata saniba son Ya Taufiq a jinina yake daga Allah ne

"Fatima dan Allah kice tabar damun kanta nida Ya Taufiq tafiyar Allah ne kuma ba wani abu da zaifaru ta samana albarka amman bansan inga taba damuwa."
"Shikenan kawata Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Ameen nace da haka mukayi sallama nan mukaci gaba da karatun mu,muna gama karatu,na shiga ban daki ina fitowa Mama takirani ina zuwa tace.
"Aminatu naji kina magana da Fatima mike faruwa."?

"Wai Mum ke tsoron kada ince ban son Ya Taufiq shine take mani maganar."
"Allah Sarki Umma nasan abinda take nufi kada ta damu kanta,addu'a zamucigaba dayi insha Allah wannan lamarin alkhairi ne ni tuni inajin hakan a cikin zuciya ta Allah yasamana albarka."
Ameen."

"Sannan inasan inkara jan hankalinki Aminatu kikara sa hakuri a cikin zuciyar ki da dangana kinji."
"Toh Mama insha Allah zan kiyaye."
"Allah yaimaki albarka."
Ameen Mama."


"Mamana takaina yar Baba fira akeyi."
"Eh Baba sannu da zuwa."
"Yawwa Mamana inafatan kin gama shirya kayanki ko."?

"Eh Baba nagama hada komai dinkuna kawai nikejira gobe za'akawo mani."
"Allah yakaimu lafiya Mamana."
Ameen."
"Wai ina Ahmad."?
Cewar Baba."Na aike shi Kano."Cewar Mama.
"Allah ya maido shi lafiya."
Ameen muka amsa baki dayan mu, abinci Mama takawoma Baba mukaci gaba da kallan news daga karshe nakoma daki.

*_A KURMAWA PRISON...._.*



_Yar mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E11&12


*_A KURMAWA PRISON_*
Anty Hafsat ce keta jibgar aiki ita da prisonors daukar itace kawai sukeyi suna kwasar duwatsu banda duka da suke sha idan mutun yatsaya hutawa kuka kuwa tayishi harta godema Allah,ga yunwa ka kishirwa duk tabi ta addabeta basu suka gama ba sai yamma sannan aka sallame su suka wuce dining aka basu abinci wanda gwara babu dashi tana zama zataci masu gari suka kwace (Cankwai) kowa yasan wacece Magajiya basai mun tsaya fadin itadin wace ba.

Tanaji tana gani suka cinye shi tas banda duka da zagi ba abinda Anty Hafsat kesha a wajen su Cankwai abin mamaki kayan da Amina ta aje sune akaba Hafsat duk wani tashin hankali da azaba wadda Amina ta fuskanta ta koma akan Anty Hafsat bakaramin bakar wahala take sha ba.

Tunda Magajiya taji labari itace taima Dago sharri sai ta dauki karan tsana ta azamata bata da ikon magana saita hantareta banda duka da zagi datake yawan yimata abin ba'a magana.

Yauma da kanta taba Hafsat wankin lalataccen kewayen su mai bala'in zarni da karni haka tasa ta wanke shi tas, sannan tasata dibar ruwan wanka banda tausa itakema Cankwai ita har sai tayi bacci sannan zata barshi.
Gashi bata da ikon kwantawa akan gado saidai kasan siminti wanda duk ya fashe tsabar lalacewa datayi.

Idan kaga Hafsat bazaka gane taba duk ta jeme ta lalace kamar ba ita,kwakwata ko wata biyu bataiba amman duniya tai mata daurin goro.

Ba wanda ke kaunarta ta zama mujiya a cikin tsuntsuye hatta Oga Adam tunda akayi shari'a yaji alakarta da Aminatu,saiya kara tsanarta hakama Atika.

Danasani iya danasani Hafsat tayi shi ga ciwo ya kamata inyau lafiya gobe ba lafiya haka take rayuwa a gidan Yari lamarin ba'a cewa komai.

_Ya Allah kai mana tsari kabamu ikon aikata alkhairi a duk inda muke ameen ya rabbi_


***** ***** *****
*Caranci*

Alhaji Hamza inajinku ai kuba baki bane bare kuce zakuji nauyin gaya mani abinda ke tafe daku ."
Cewar Baba
"Hakane Alhaji Yusuf bawai nauyi mukeji ba,bamusan taya zaka dauki maganar tamu ba,amman ance ranar bikin dole sai dole kuma ranar wanka ba'a boyon cibi muna neman alfarma agareka munzo da kokon barar mu agareka muna nemawa ɗanmu Husseini izinin neman auren yarka Aminatu,wannan shine bukatar mu agareka Alhaji,kuma in ka amince mana munason asa ranar ayau nan da mako biyu ayi bikin."

Kalan su kawai yake yana mamaki aranshi duk da yasan ba abin mamaki bane saidai yana ganin abun kamar a mafarki taya hakan zaifaru anya ba gizo suke mashi ba?

"Kayi shiru Alhaji Allah yasa ba damuwa."?
Baba Hamza ya tambaya a raunane,murmushin karfin hali yayi yace.

"Akwai matsala gaskia."
Tame sukace suna hada baki a lokaci guda.

"Eh kowa yasani Aminatu da Hussein suna son junan su,a shekarun da suka shuɗe amman a halin yanzun bamusan wace alaka ke tsakanin ya'yan namuba sai munji ta bakin su tukunna,duk da nasan mahaifin Hussein yasa albarka wannan dalilin yasa kukazo neman izini."

Damama sukayi sai sukaga kamar mahaifin Amina yana ganin mahaifin Taufiq har yau baison alakar ya'yan nasu.

"Hakane Alhaji Yusuf saidai kasani mudai ɗanmu har gobe yana son Aminatu kuma mahaifin shi da kanshi yatadomu dan nemawa Hussein izini agareku ku iyayen yarinya amman bamu saniba ko ita ta sauya ra'ayiba sannan in san samune munaso a sa rana ayau din nan domin tafe muke da kayan sa ranar mu."

"Bamu tunanin haka Alhaji Hamza akwai kyakkyawar alaka tsakanin Aminatu da Hussein."
Cewar Baban Husna.

"Gaskia kam amman nidai inason abari in zauna da yarinya aji ra'ayinta kunga abubuwa da dama sunfaru bansan in sake shiga hakkinta yanada kyau muji ra'ayin ya'yan mu,dan haka kubawa Alhaji hakuri amman nayi mashi alkawali insha Allah zai jini daga baya nagode Allah yabar zumunci."
"Ameen munji hanzarin ka Alhaji Yusuf amman zamu iya aje kayan sa rana""
"Aaa ba dole sai ankawo kayansa rana ba kuma bazanso aje kayaba,koda kayansa rana ko babu idan naji tabakin Aminatu zan sanae daku sai atsaida lokaci,kuma kaganni nan jibi zan koma Anka yanzun can nakoma da zama baki daya shiyasa kukaji nace kada ku aje fatan zaku karbi uzurina."

"Badamuwa Allah yakaimu lafiya mudai muna jira dafatan zamuji alkhairi."
"Insha Allahu."
Ruwa suka sha sannan suka tafi gida.


"Haba Alhaji Yusuf miyasa kaki karbar bukatar su bayan kasan cikar burin Aminatu bai wuce taga ta auri Hussein,mikakeyi haka."?
Baban Husna yai maganar a zafafe.

Dafa shi Baba yayi yace.
"Abinda yasa ban karbi bukatar su ba inada nawa dalilin nafarko kai shaidane yanda mahaifin yaron nan ya dinga gitta rai ɗansa bai auren Aminatu duk da nasan bawai yana kintaba dan ya tsaneta ba,Aaa yakita saboda kin umurnin shi da ɗan nashi yakiyi kamar yanda take awajena,inason sukoma mashi ba'asa ranar ba nasan zai biyo ba'asi in yaso in suka dawo zuwa na biyu sai asaka ranar kuma kaga koba komai na daukarma ya'ta mutuncin ta,ni kaina burina kenan a duniya inga Hussein da Aminatu sunyi auren su kaima shaidane shaidane abokina."

Ajiyar zuciya ya shide a hankali yace.
"Nafahimci ka yanzun Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya nuna mana lokaci lafiya."
"Ameen aminina Allah yabar zumunci."
Ameen ya rabbi."
Da haka sukaci gaba dafirar su ta abokai.


Ada hankalina yai masifar tashi danaji Baba yaki amincewa da bukatar iyayen Ya Taufiq amman tunda mukaji uzurin shi sai hankalin mu ya kwanta nida Mama saijin dadi nike hankalina kwance kamar tsumma aranda.

Bayan sallar isha'i nagama salla kenan naji kiran Baba.
"Aminatu."
Na'am nace natafi zuwa falorn shi,gani nace mashi.

Zama nayi ƙasa Baba yace indawo gefen shi inzauna.
Zama nayi ya rike hannuna yace.
"Aminatu nakiraki ne dan insanar maki iyayen Hussein sunzo neman aurenki amman nace masu zanji naki ra'ayin kin amince zakiyi rayuwar aure da Hussein."?

Yai mani maganar yana karantar yanayina.
Wani irin dadi naji ya lullubeni kamar ansakani aljanna wai yau ni Babana kema maganar auren Ya Taufiq kamar amafarki anya ban zauce ba.
"Aminatu mike faruwa kiyi magana diyata."
Murmushi nayi nagaza magana.
"Kin amince Aminatu."?
Cewar Mama.
Ɗaga kaina nayi ina zare hannuna cikin na Baba bai yunkurin rikeni ba,ina zamewa na gudu zuwa dakina saijin dadi nikeyi.

"Alhamdulillah ashe da rabon zanga wannan ranar ni Khadijatu gani nike kamar ba dagaske ba."

Murmushi Baba yayi yace.
"Dagske ne Maman Jidda ni kaina sai inga abin kamar almara Allah muntuba shiyasa ba'aima Allah shishshigi munyi kura kurai iri iri acikin lamarin nan mun shiga hurumin daba namu ba fata Allah yayafe mana kurakuren mu."
"Ameen Baban Zainab."
Niko ranar haka na kwanta nagaza bacci tsabar jindadi da murna daya addabeni a cikin zuciya ta.


Washe gari da yamma na shiga gidan su Husna "oyoyo ya'ta."Mama taroni muka shiga falorn Anty muka gaisa saijin dadin zuwana suke babu yanda ba'ayi daniba amman naki zuwa sai inga kamar zanga Asma'u haka nikeji araina,fira mukafara da Mama takara yimani maganar aurena da Ya Taufiq.

Narasa dalilin dayasa mutane dayawa ke mani zancen aure daman ance in lokacin abu yayi haka yake.
"Baban naki ya amince ko."?
"Eh Mama amman bansani ba koya gaya masu yace sujira."
"Allah yatabbatar da alkhairi ya nuna mana lokacin lafiya."
Ameen Mama."


Kabir ne ya shigo dauke da Mina ya siyo mata sweet.
"Oyoyo daughter." na rungumeta jikina inakara jin so da kaunar yarinyar a raina inaji inama inzan aure abani ita danaji dadi.

Ina Haidar na tambaya.
Jiya kanin Daddyn su ya dauke shi."
Cewar Anty.
Allah sarki aida anbar shi wajen Mina nace ina shafa gashin kanta kamanin ta dana mahaifiyar ta kullin kara bayyana suke,shiyasa nike kara kaunar yarinyar araina.

Jikka na dauko na fiddo dunkuna guda biyar wanda nayi duk nasa anmata riga da sicket biyu sai doguwar riga ukku na gwada mata kuma sun mata kyau sosai masha Allah.

Duk da tana yarinya amman taji dadi sosai sai zabga tsalle take tana murna dajin dadi.
"Thank you Ammi."
Rungumeta nayi.
"Allah yaimaki albarka."
Ameen suka amsa, najima wajen Mama tana bani shawarwari akan rayuwa musamman a gidan miji haka take mani Lecture sosai kuma ina fahimta saida akayi isha'i nayi sallah sannan na koma gida.

Koda nadawo gida inga kayansa rana ko alamun Abba yazo shiru sai naji ba dadi, hakanan na kwanta sukuku,saidai kiran Ya Taufiq nagani ina kyarma na dauka nace.

"Ya naji shiru lafiya."?
"Aminatu,wlh Abba ya karaya gani yake kamar Baba bazai bani aurenki ba waishi in bai aura mani keba kamar bai yafe abubuwan da suka faruba da kyal mukashawo kanshi."

Ajiyar zuciya na shide nace."Ya Taufiq Baba ya aminta fa,wai yafiso yaji ra'ayina shiyasa."
"Ke mikikace mashi.?"
Yai mani tambayar bazato ba tsammani.
"Na'amince nace haba Ya Taufiq kaima kasan ina kaunarka miyasa zakai mani wannan tambayar."
"Inajin tsoro kada asamu akasi kice kinfasa Aminatu daban san ya zanyi da rayuwata ba shiyasa kikaji nace maki haka."
"Indai hakane kadaina damuwa masoyina ina sonka kuma ina kaunarka dakai na shirya in rayu."nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace."Allah ya mallaka mani ke Minal."
"Ameen ya rabbi."mun jima muna fira sannan mukayi sallama da junan mu.


••••• •••••• ••••••••
Bayan kwana biyu muna tashi nida Ahmad sai Zainab mukaje gidan grandfa dinmu zamuyi masu sallama, Jidda kawai muka bari gida ita da Mama.
Koda mukaje Umma muka iske zaune tsakar gida zama mukayi akaita fira tana tsokanar mu,munjima a gidan nata har saida dare yayi Baba yazo ya dauke mu.


*KURMAWA*

Kwance take bata lafiya rai hannu ga Allah sai nishi takeyi ɗai ɗai,kwance magashiyan kasa duk jikinta yai ƙasa.

"Tashi munafuka wlh sai kin nemo wajen nan koda zakiyi mussai munafuka."
Cewar Mairo ta dungure Hafsat tana ta kyakkyawar ta kat kat kat tana fama sa rawar sanyi.
"Dan Allah kuji tausayina mutuwa zanyi na rokeku"
"Wlh saikin tashi,ke Mairo ɗago mani ita inci ubanta da hujja nafahimci batasan cewa Barno Gabas take."
Cewar Magajiya.
ɗagata Mairo tayi ba imani Cankwai taita wanketa da bulala saida taimata tas sannan ta saketa kasa rigijib haka Hafsat ta fadi batada marairaba da matata amman saboda bala'in Cankwai saida tasata aiki tare aka basu team work amman kusan ita kadai tayi shi ga jikin ta wasu kananun kuraje ne suka fito mata reras a fuska ba kyaun gani tabbas idan kaga Anty Hafsat saika zubda mata kwalla tsabar tausayi.

Haka rayuwa ta zamarma Hafsat agidan yari ba dadi kullin kuka take ba wanda ke bata hakuri gashi su Cankwai ba ragi ba ragowa dansu kashe mutun ba damuwar ta bane saboda sunsan mutuwa kadai zata rabasu da gidan.


A wajen Umaima kuwa rayuwa ba dadi ba abinda tasa agaba irin yawon banza kawai tasa agaba ba dare ba rana bata wannan gari bata wannan kauye gashi abin nataba aji kowane jik and jak yana tare da Umaima ta zama karuwar karfin dayaji mai zaman kanta.


Danko Khadija a gidan miji ba dadi duka yake mata bana wasaba gashi Muntari yai mata kishiyoyi sun sakata tsakiya sai gallazamata azaba suke duk bala'i da Jafa'i na Khadija

Please Login or Register in order to submit comment