Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar cikin mafarki musamman dana fahimci inda nike gidan su Ya Taufiq aka wuto dani da sauri Usama da wasu soldiers ya bude mana kofa Anty ta rikoni nasaki hular rigata ina ganin mutane amman basu ganina sannu da zuwa sukai mana direct side din Abba aka wuce dani cikin tafkeken falorn shi za'a zaunar dani kenan wata mata kyakkyawa barumiya tace akaini cikin wani daki kana ganinta kasan kanwar Abban Ya Taufiq ce.

Ta wani Corridor akabi dani aka shiga dani sai baza uban kamshi yake mai dadi zaunar dani akai bisa gadon mai tsananin taushi kamar sun goyamu yanda suke mana sannu da hanya.

"Ina kishiyar tamu take inganta Allah yasa dai kyakkyawa ce."
Cewar wata tsohuwa

"Aikuwa gwaggo kyakkyawace son kowa kin wanda yarasa."
A"aa Aishatu daina zugata nasan wannan ruwan idon da Husseini ya tsayayi da wahala in zai samu kyakkyawa kamata."

Dariya sukayi suna.
"inda ba kasa nan ake gardamar kokowa inaji sun zame mani hular rigata ga wani irin haske da dakin yayi kai kace ba dare bane da sauri na dan sadda kaina kasa.

"Masha Allah tubarakallah shiyasa kenan mijin nawa ya rude tsabar haduwa saidai duk da haka kafata bata kama ba."
Dariya sukayi suna kedai kishi kikeyi gwaggo nidai murmushi nayi kaina na kasa
Sannu da zuwa suka sake yimana sannan suka fita sai a lokacin nayi ajiyar zuciya harnaji dadi dagani sai yan uwana suka hau fira da Baba Hindu.

Bada jimawa aka fara sallama dauke da jibga jibgan kuloli sai ajewa suke suna komawa haka aka tara kuloli agaban mu,godiya Anty Murja ke masu.

Bamufi minti gomaba sai gasu Zuwaira kawayena na Anka da sauran yan kawo amarya nanfa kowa ya zauna an kwaso gajiya.

Bamu jimaba Anty Aisha matar Ya Tariq suka shigo itada Fatash nan suka dinga zuba abinci ana ba yan tafiya.

Wata katuwaar kaza da wani lemu,Fatash tabani tace.
"Mum tace kimaza ki cinye yanzun zatazo ta iske filat."
Dan zaro idanu nayi waje dan tsoro,dariya akai mani ana saikin cinye shi,girgiza kaina kawai nayi nasan komi za'ayi bazan iya cinye shirgin naman ba.

Wata kula suka bude papper chicken ne kowa ya zuba akahauci gwanin birgewa.
Anci ansha alhamdulillah har goma sannan Anty Murja tahada mani ruwan wanka na watsa nasa wata riga mai kauri ta bacci na aza hijab akai,fira muka hauyi zuwa lokacin dangin Ya Taufiq sun rage shigowa ganina sai lokacin na sake sosai munsha fira Anty Murja tatafi wajen Mum bamu muka kwantaba sai 12 shima saida nayi waya da Ya Taufiq nace bacci zanyi nagaji da haka yace in kwanta mukayi sallama wannan kenan.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E25&26

_Sharhi iya sharhi fatan alkhairin ku na musamman ne akan Minal da Ya Taufiq muna fatan Allah yabada zaman lafiya,kuma Allah yasaka maku da alkhairi yabamu kwanciyar hankali baki ɗayan mu a gidan auren mu,wa'anda basu dashi Allah yai zabi na kwarai ameen ya rabbi🤲🏻_


★★ ★★ ★★
Washe gari da safe muna tashi kowa yai sallah daman ni banyi wanka na shiga ruwan kamshi Anty Mubaraka ta hada mani nai wanka sosai naji dadi wata atamfa ta dauko mani dark blue mai silver jiki sai ratsi golden na saka riga da sicket ne sun mamani das sosai,Zakiyya da Anty Samira suka kawo mana break fast suna ajewa Fatash ta kawo mana wata kular gaisawa mukayi sannan suka fita.

Dankali dakwai aii doya sai wani katan tire Sandwish ne sai tea da bread kowa yahaucin abinda yai mashi nidai tea nasha mai kauri sannan naci sandwish na koma gefe ina danna wayata nan naga ana status pictures dinmu duk kawayena sunsa ana congratulation Aminatu HML kowa dai yana fatan alkhairi saijin dadi nikeyi a cikin raina.

Karfe goma Anty Aishatu kanwar Abban Ya Taufiq tazo ta kamani gyale nasa bisa kaina ta wata kofa tabi dani a cikin side din Abba mika shiga wani makimancin falor mai yalwar kyau su Abba da Mum sai Ya Taufiq dake zaune gefen kafar Abba,zaunar dani tayi kaina kasa ina rufe fuskata.


Wasa nike da yatsuna sai naji wani iri duk nauyin surukan nawa ya kamani sai nazama kamar wata bakuwa a wajen su haka nikejina ga idanun Ya Taufiq sun takura mani kamar in nutse haka nikejina.
Gaidasu nayi cikin sanyi murya kamar maijin tsoron su haka naji.

"Ya'ta barka ya bakunta naga kinki sakin jikin ki Aminatu nan gidan kune kinji ki daukemu iyayenki kidaina dararewa banjin dadi inna ganki haka kinji ya'ta."

To Abba nace ina dukar dakaina kasa.

"Yawwa ya'ta kubani aron hankalin ku,inasan injaddada maku wata kalma yar karamace abaki amman mai girman gaske ce a zuci ba wani abu bane ina kara tuna maku jin tsoron Allah a cikin zukatanku saboda da zuci ake tsoron Allah ba aharshe ba kuyima junanku adalci ku rike junan ku bisa amana kunama junan ku uzuri Allah ya kareku daga kowane sharri wannan shine abinda zan iya cewa natabbata komi zance angaya maku daman tunine nai maku Allah yaimaku albarka yasa alkhairi ya wadataku da tsarkakekkiyar zuriyar mai tsoron Allah."
Ameen duk muka amsa.

Mum tace. "Bansan mi nikeji a raina ba tabbas nayi matukar farin ciki da Allah yakawo mana wannan lokacin fatan Allah yasa alkhairi ya albarkaci rayuwarku kai Hussein kaji tsoron Allah karike wannan amana ke kuma Aminatu kiji tsoron Allah kiyima mijinki biyayya Allah yaimaku albarka."
Ameen mukace nidai na sadda kaina kasa ina ta gefen Mum hakan yasa muke facing junan mu nida Ya Taufiq saidai naki yarda muhada ido da shi,najima har Yayar Abba saida taimana nasiha sannan aka maidani cikin dangina haka mukaita firar mu gwanin dadi har akayi azahur ankusan fara Walima sai shiri akeyi kowa da abinda ya dame shi.

Fatima ce tashigo cikin wani hadadden less milk and yolk mai kyau dauke take da ɗanta Fahad sai murmushi take saki tana isowa daidai saitin kunnena taimani raɗa harara na watsa mata ina ɗage kafaɗa alamun ban zuwa pls tahade hannayen ta sake noƙe kafaɗata nayi ina girgiza kai.

"Pls Minal dan Allah kije ba wani jimawa zakiyi ba."
tayi maganar a shagwabe.
Banzan nayi da ita.
"Wai ina zatajene Fatima."?
Cewar Baba Hindu.

"Ya Taufiq ke kiranta fa shine wai bata zuwa."
"Ke yar nan tun kan mubarki harkin fara saba dokokin Allah mijin naki yakiraki kice baki zuwa anya Aminatu kinma kanki adalci aure fa kikeyi maza tashi tunkan kifara daukar zunubi tashi nace ko in hanbareki sakarcin banza."

Mikewa nayi ina zumburo baki na dallama Fatash harara itako sai murmushin mugunta take aika mani debe kallabin kaina nayi na dauki jumbulelen hijab nasaka itadai Fatash batace mani komai ba kamar jira Baba Hindu tafara masifa.

"Kagane mani marar kirkin yarinya in zaki fita kina gyala gyale shine zaki wajen mijin zaki jibga hijabi."
Kai wannan tsohuwa masifa ce nace araina a zahiri nace.

"Haba Baba Hindu sakone fa kawai zan karbo kuma...
"Kuma me kindai ji haushi Aminatu."
Bin Fatima nayi ban kara kula Baba Hindu muna fita daidai Corridor nace.


"Wlh kinbani Fatash mugun hali gareki nace ban zuwa saida kisa waccen tsohuwar taitayi mani yamaɗiɗi kibar hali kici me banza"
"Naji dai indai zakije kiran Yayana kowama zan iya fadamawa."
"Mtsw wai ina zaki kaini nifa bazan bar part din Abba ba kije kice yazo nan din.!"
Na tsaya cak ina hade rai.
"Mijinki zakicema haka anya Minal?naji amman ba nisa dan Allah muje na rokeki."

"Ina zamuje gayamani yana ina."
"Lambu nefa muje muna fita shikenan kema kinsan ba nisa."
Toh nace mata mukayi lambu a jere muke tafiya sai kare fuskata nike da hijab musamman idan naga dangin Ya Taufiq sai innoƙe kamar munafuka,har muka iso lambu shiru tayi nace.

"Yana ina."?
"Nima nan nabar shi bari inji."
"Kinga ko kin jawoni shi yai tafiyar shi Allah kin kyauta."

"Yaya muna lambu kazo dan bazata shigo ba."
Kashe wayar tayi ina binta da kallo nace."kamarya bazan shigo ba dama ba alambu yake ba."?
Banza tayi mani,naji ance.
"Muje ko."
Da sauri na waigo tsayake yai holding hannayen shi,cikin wani dakakken boyel milk."
"Ina zamuje."?
Nayi maganar raina hade
Shima hade fuska yayi yace.
"Saidaki zanyi ai ance dakai da kaya duk mallakar wuyane."

Kallan shi nayi zan mashi musu sai kuma na kasa sanadiyar kafeni da idanun shi da yayi binshi nayi nacema Fatash muje kirjin biki."
Juyawarta tayi tabi ta side din Mami tai tafiyar ta,niko ya tisa keyata gaba kamar barauniya har muka shiga side dinshi falor ya zauna inatsaye kiƙam kamar soja

Kallo yakeyi nima tv nike kallo bansan ina hada ido dashi sai inji wani iri.

"Mrs Taufiq wife kodai kema kin zama Soja ban saniba come and seat."
Kin zama nayi ina wasa da yatsuna.

"Minal zo ki zauna nace."
Muryar shi kawai naji nasan ba wasa alamarin takowa nayi na zauna two seater dake facing dinshi kamar marar gaskia.

Banza yayi dani yana danna wayar shi still yana kallo,ni kuwa a takure nike ta kasan hijab nike aika mashi da kallan harara.

"Kitaimaka kada eyes din su faɗo kasa natuba."
Kunya takamani ashe yana kallona sake sadda kaina nayi ina murmushi.

Jinayi ya kama hijab dina zai cire a firgice na rike hannun shi dan bansan ya iso wajena naba.
"Saki mana minene haka Minal."?
Yai maganar cikin sanyin murya.
Gabana na duka nace.
"Banda kaya jikina Ya Taufiq."
A tsorace nai maganar zama yayi gefena ya janyoni jikin shi sosai yai mani kiss a goshi yace.

"Karki damu ko kin manta nidin mijinki ne,miyasa zakiyi yawo ba kaya cikin gida ana hidima bakisan kedin kin taka next level ba."?

Nasani nace a ruɗe naki sakin hannun shi.
"Cire hannun ki."
A dake yai maganar har bansan yai mani using husk voice dan ba wasa a cikin ta a raunane na kalle shi bako alamun murmushi saman fuskar shi bansan na cire hannuna bisan nashi ba,abinda nafahimta har yanzun akwai sauran tsoron sa a cikin zuciya saidai abin time to time ne.

Inaji yana zare mani hijab dina saidai still kallan juna mukeyi harya cireta tas,sai lokacin ya saki murmushi yana kallona up and down.
Riga da sicket ne jikina na atamfa sun kamani sosai saidai ba kallabi akaina.
Aza lips dinshi yayi a wuyana yana mani kiss mai sanyi da sauri na rufe idanuna saitin kunnena yace.

"Ni zakima wayo daman da kaya jikin ki shine zakice haka."?
Sake rufe idona nayi bance komai sai addu'a nike Allah yasa yabarni intafi bansan tsaigumin Baba Hindu nasan yamadidin ta yanda yake.
Sukar bakinshi naji saman lips dina da sauri na waro idanuna waje nakasa komai sai ajiyar zuciya nike saukewa na tsoro,cool kiss yake sakamar mani mai nuna tsantsar so da kauna a hankali na zame lips dina hannuna nasa na tallabo face dinshi muryata na breaking nace.

"Ya Taufiq kabari jirana Anty keyi pls."
A shagwabe nayi maganar danji nike kamar nayi mashi kuka nafahimci ba rabuwa zaiyi dani ba.

Ajiyar zuciya yake shidewa a hankali kamar wanda yai wani uban aiki sannan ya kalleni da rinannun idanun shi.
"Haba my life wake jiranki bayan kina wajen mijin ki."?
"Anty Murja mana shirin Walima zanyi pls."
na hade hannayena sifar roko.
Jinjina kai yayi daukar hijab din yayi ya zira mani yana shafa gefen fuskata yace.
"My cute baby tashi inraka ki."
Zanyi magana kenan wayar shi tahau ringing Bloody ya bayyana a screen din wayar.

"Ya Hassan kana ina."?
"Gani nan zan shigo gida kana side dinka ko kana gidan ka."?
"Aaa ina side dina."
"Ina zuwa nida Ya Samir."
"Okay."
yace yana maido kallan shi kaina,Inajin ya yanke wayar da sauri na mike duk na rude idanuna sunyi raurau nace.

"Dan Allah Ya Taufiq kabarni in tafi idan suka iskeni nan ya zanyi harda Ya Samir fa nidai taya zanbar nan bansan kowa ya ganni fa."kamar in kuka haka nikeji har idanuna sun sauya kala.
Murmushi kawai yake ko ajikin shi.
"Pls kayi magana mana."
"Saimi dan sun ganki zunubi kika aikata da zakice haka."?
Rai hade yayi maganar yana kada kafafun shi.

"Aaa nidai rakani inwuce kunya nikeji."
Juyawa nayi zan fita Allah yasani inajin kunyar su iskeni wajen shi musamman Ya Samir tunda case dina da Mami yafaru nauyin shi nikeji sosai.
Janyo yayi jikin shi yace.
"Ba inda zakije tinda kunya kikeji."
"Aaa nadaina kabarni Ya Taufiq."

Kama hannuna yayi tabaya mukabi sai sinne kai nike ga mutane anfara taruwa saida yakaini gab da side din Abba na fada ciki duk na kama kaina taho mugama mukayi da Anty Mubaraka.
"Lafiyarki Aminatu tun dazun nike neman ki gashi har hudu ta kusa muje kishirya har Mum tazo neman ki wai ina kikaje."?
Sosa keyata nayi bance da ita komai ba.

"Muje Allah kin cika wauta Aminatu."
Muna isa kowa yahau cewa.

Amarya ina kikaje daga kawoki kinhau yawo cikin gidan surukai baki gudun dangin angon suce kin cika rawar kai.
Abokan wasana ke cewa haka sunacin abinci banda Fatash dake mani dariyar mugunta ni kuwa duk na gama kulewa kamar in kwala ihu haka nikeji.

"Ke kuwa Aminatu baki data ido daga kije wajen Husseini saikije ki shantake kega mai miji ko."?
Baba Hindu keta yimani shela tana fada kamar ba ita tasani zuwaba amman ta dawo tana cewa wajen miji na gudu waini dadi miji.
"Dan Allah Baba Hindu kishafa mani lafiya kefa kikaita bala'i sai naje kuma danna gaisa da abokan shi laifine."?

"To tijara ai sai ki babbaka kishirya ko kwantawa zanyi ki bigeni."
Turo baki nayi, nayi gaba toilet ina sane na halba kafar Fatash ita nike blaming.
Ban jimaba na fito nan nafara shiri sai kiran sallar la'asar akeyi

Cikin less pich and gold na shirya bakaramin kyau nayi ba masha Allah.
Na sakar gold sai takalmi da fost dina duk gold karfe hudu da talatin Anty Zainab (Ummi) tazo takamani sakar mani gyalen dake kaina tayi ya rufe mani fuskata aka kaini wani katan fili yasha kafat da tabarmi sai mutane dayawa dangin Abba dana Mum harda dangin Mami duk suna wajen hatta Anty Wasila tazo itama, tsakiya aka ajeni wajen dangina su Mum ansha kayan alfarma kowa ya hadu Anty Murja da Anty Rukayya sai Anty Mubaraka sun aje uwayen kayan kore Maman Husna ke zaune kusa da kayan dagani koren dangin miji zasuyi tunda walima ce nidai kaina na kasa sai rangaɗa guda akeyi.
Kirana Ya Taufiq yake naki dauka ganin mutanen dake wajen bazan iya waya dashi ba.

Anfara kore saiba dangin shi da uwar miji ,uban miji kaya ake hakama dangin Ya Taufiq sai Kakanni sosai aka rabama masu kaya iri iri ana gama KORE Maman Husna takamani za'a damka amanata wajen iyayen Taufiq sannan zasuyi buɗar kai mikewar da zanyi naji anshako wuyana an ingije Maman Husna tafaɗi kasa.
mata aka hau salati da sallallami.
Da karfi ta fisge gyalen dake rufe da fuskata ta bankani jikin bango sosai ta shakeni har numfashina yana neman daukewa.
Sauran Mata akayi kanmu za'a ansheni a hannun ta,ni kaina na firgita gami da tsorata ganin......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E27&28



Mami dake neman kasheni bil hakki da gaske take neman raina kawai take duk matan dake fisgata a hannunta sun kasa ansata ni kaina kokarin ansar kaina nikeyi nagaza saboda ba rikon wasa tai maniba fasa ihu mata sukayi sai zunduma ihu sukeyi kafin kace kwabo maza sunfara shigowa cikin gidan kai kace gobara takama gidan baki ɗayan shi saboda wasu harda abubuwan kashe wuta sukazo da sauri Ya Taufiq dasu Abba sukayo kanmu nikam nafara ganin mutane bishi bishi harna galabaita.

"Saina kasheta ku kyaleni wlh saita tafi barzahu badai harta auri Taufiq ba, yau bata kwana duniya ai nayi alqawali saidai inna mutu zasu mallaki junan su badai da raina ba basu ba mallakar juna har abada na tsaneki Aminatu ban kaunarki ban kaunar mai kaunarki."

Kadan kadan nikejiyo maganar ta tana shake dani.
Fas fas fas haka Ya Taufiq ya wanke Mami da kyawawan maruka har guda ukku saida ta saki razanannar kara tsabar maruwa da sauri ta sakeni nayi kasa luuuu zanfadi naji antaroni sai alokacin nadan bude idanuna da nikejin su kamar zasu tsinke dan wahala Ya Taufiq rike dani yana."Aminatu tashi nazo gareki karki barni matata."

Maida idanun nawa nayi na rufe,su Anty suka ansheni a hannun shi sukahau yi mani fita inajin abinda akeyi amman sama sama numfashina nai mani barazanar daukewa sai zirarar kwalla nikeyi.

"Hussein nika mara wlh sainayi ajalin ku kaida Aminatu baku ba mallakar junan ku har abada kuma wannan auren yau saiya warware koda kunkai kashin awayaki mannewa tsinannu."

dauketa da wani sabon marin Abba yayi yana gwadata da yatsa yace.
"Kece tsinanniya Mufida badai ya'yana ba,kuma aure anyi angama igiya ukku ke saman kan Aminatu ke kuma a yayin da taki igiyar auren ta kubuce maki dan haka bake ba zuriyaa na sakeki saki biyu daman can baya akwai daya ya tashi ukku bani bake bake ba zuriya ta natsaneki."

"Wayyo Allah ni Mufida nabani na lalace Alhaji Mukhtar ni zaka saka shikenan alkadarina ya kwance asirina ya tonu nashiga ukku na lalace jama'a kutaimaka mani."

A haukace take zunduma ihu tana ta shiga ukku alkadarinta ya kare.
Su Wasila,Samira,Sajida da Zakiyya sai kuka sukeyi ganin uwar su cikin tashin hankali sai lokacin na sauke idanuna kan mutane dake kaina ba laifi idanuna sun saki kadan a rude Ya Taufiq ya rungumeni kamar wani karamin yaro niko duk kunyar mutane takamani fara tureshi nikeyi amman kamar chewgam ya nanike mani dole na sama shi ido kamar za'akwaceni haka ya rikeni.

"Alhaji katausaya mani kaine gatana karka rabu dani na rokeka."
Mami keta faman magiya wajen Abba.
"Bani bake Mufida na tsaneki azzaluma wane irin makirci da tuggune baki hada mani agidana ba,kin tarwatsa mani duk wani farin cikina sai yanzun dana samu na koma mutun zaki dawo dan sake tarwatsa mani sauran jin dadin daya rage mani kijini da kyau ba wata alaka tsakanina dake kuma kijira hukunci abinda kika shuka banyafe maki ba Mufida inama banda zuriya dake."

Sake rakaka ihu tayi har saida na firgita,dagani Mami tahaukace abin nata bana lafiya bane kana ganinta kasan tagama zaucewa tsabar firgita ga bakin cikin ganin munyi aure nida Ya Taufiq sai abin zamar mata goma da ishirin.

Tashi tayi kamar zatayi waje da gudu sai kuma ta cafki Mum kamar yanda taimani,aikuwa ya'yan su sukai kansu Ya Tariq na neman anshe Mum hannun Mami su Sajida na rike Mami suna kuka daidai Ya Samir ya shigo gidan ganin abinda ke faruwa ya gigita shi a raunane yace."Mamiiiii!"
Ya furta yanajan haruffan karshe jiki mace ya karaso wajen yana kallanta kamar bakuwa,itako bala'i take tana.

"Wlh Maryam bake ba zama da mijina tunda harya sakeni dalilin watsastsan ɗanki saina kasheni baki mallakar Alhaji Mukhtar ke kadai saidai kowa ya rasa da raina wlh kinyi kadan saina kasheki Maryam natsaneki keda zuriyar ki."

Ya Samir ya fisge Mami ya riketa gam a kirjin shi,shima Ya Tariq rungume Mum yayi sai kuka takeyi tsabar tashin hankali.

"Mami ki nutsu dan Allah kidaina wannan kukan ina kikaje tsawon wata shidda baki ba labarin ki Mami."

"Bashi ke gabana ba Samir kabarni inkashe Maryam da Aminatu natsane su."
Dafe kanshi Samir yayi yafara kwararar da kwalla yace.

"Kin manta halin da kika jefamu ba Mami kin manta abinda kuka aikata yanzun haka hukuma ke neman ki shine zaki kuma jawo mana wani abun gorin Mami kaicona ina dana sanin da kika kasance mahaifiya agreni kin tsarwatsa mana duk wani farin cikin mu nida yan uwana Mami why miyasa zaki mana haka Mami."?

Kuka yake harda kwalla still yana rike da ita.
Itako kana ganinta tabbas ko kwakwalwarta bata tabuba to ta firgita sosai.

"Samir kana ganin uban ka ya sakeni shine zakace mani haka ni zakai danasanin haihuwar danai maka duk gatan da nike maka to indai abun magana ne yanzun zanfara jamaku shi,kuma yau Aminatu bazata kwana duniya ba basu ba raya wannan daren.

Shidai Abba yana gefe da alama waya yake sojoji biyu mata akasa suka riketa gam ko motsi takasa tsabar rikon da tasha amman bakinta yaki mutuwa kuma basu duketa ba sai lokacin Ya Taufiq ya sakeni yana goge mani kwallan dake shida bisa kuncina kwayar idan shi kadai zaka kalla ka gane tsantasar so da tausayin da yake mani.

Itako cewa take."Alhaji Mukhtar wlh kayi kadan ka sakeni ka karya mani alkadari na har abada nice gaba baidai nayi kasa ba,kuma kaida ya'yan Maryam sai kunga Jafa'i musamman Aminatu kai kuma Hussein sai kasan ka wulakantani."
haka taketa surutu tana kwarara ihu har biyar din yamma, jiniya mukaji tana tashi maigadi ya bude gate saiga police da Gandirobas cike da mota sun zagaye Mami unkwa suka saka mata sai bala'i take tana
"saina kasheki Aminatu bake bajin dadin duniya wayyo nabani na lalace ni Mufida alkadarina ya karebni na shiga ukkuna."

Mota suka sakata Ya Samir yana duke motsi ya kasa tausayin shi yaka mani,take Sajida ta sume Wasila kuwa rakaka ihu take tana birgima kasa Zakiyya takasa komi banda tagumi data rabka mata anyi jigum ana mamaki nidai ko hannuna da kyal na daga shi tsabar sanyi da jikina yayi na firgita da al'amarin Mami sai ajiyar zuciya nikeyi haka akatafi da ita sai kwarara ihu take tana alkadarina ya kwance ni Mufida na shiga ukku na lalace.

Duk wanda kagani jiki ya mutu sosai musamman Mum daketa kuka har yanzun nasan hadda tausayin su Ya Samir ke damunta tabbas Mami ta jefa kanta cikin halaka,ta nuna karfin iko a cikin gidan Major Sarki tana ganin kamar komai bazaiyi karshe ba ashe abinda tamanta ɗayane komai Lokaci gare shi kuma duk abinda yai farko zaiyi karshe wuya da daɗi ba wanda zai taba dauwamuwa kowane yana da nashi ajalin wanda Allah ya dibar mashi yau ga Mami hannun hukuma a wulakance tana kwarara ihu kamar me,inada yakini ko uwarta akace ta mutu bazata kidime irin hakaba sai gashi dan kawai taji labarin aurena da Ya Taufiq tadawo a kidime tana bala'i inalillahi wa'inna ilahirraji'un ashe haka Mami ta tsani ganina tareda Ya Taufiq ashe ba karamar kiyayya take maniba ashe tafi kowa tsanar lamarin nan,Anty Hafsat romon baka tafita ita bata iya boye bakin cikinta a gaban kowa take fada itako Mami siyasa tafi Anty Hafsat bata nuna damuwarta gaban kowa ta iya tuggu ashe tafi kowa iya tuggu da munafunci yau gashi naga tsantsar kiyayyarta agareni banda inalillahi ba ainda nike maimaitawa araina.

Kamani Anty Mubara tayi da kyal na mike duk na hargitse kamar ba amaryaba tsabar shaka danasha wajen Mami,muka juya zamu shiga part din Abba.
"Kaita side dina Mubaraka."
Cewar Mum,juyawa mukayi zamu shiga side dinta,taremu Anty Wasila tayi tana watsa mani kallan tsana tace.

"Ke ko?akan ki aka tozarta mani yar uwa ko? wlh Aminatu sai nasa kinyi danasani kibar ganin kin auri Taufiq kinajin dadi wlh saina zame maki masiba da bala'i saina jefaki cikin Jafa'in da har ki mutu bazaki taba fita daga cikin shi ba,dani kike zancen! kiyi zaman auren ingani saidai inban haihu da jinin Shehu ba."

Tana gama fadar haka ta ingijemu tayi side din Mami wanda nan danginta suke zaune suma sunzo biki.

Anty Mubara zatayi jacking dinta na hanata ta hanyar riko mata hannu muka shiga cikin side din Mum.


Kai tsaye bedroom dinta aka wuce dani banda ciwon kai ba abinda ke dawainiya dani har bansan sadda kaina kasa sai inji kamar zai faɗo kasa.


Wanka na shiga ina fitowa nazira hijab saboda banda kayan da zan saka a dakin,waya naima Fatima nace taje ta dauko mani kayana takawo mani.

Ban wani jimaba takawo mani toilet na koma na saka always na shirya jikina sannan na zira gownt ta material ko brezia ban sakaba dayake riga is tihgt ba agane ban sakaba.

Kwantawa nayi inajin kaina na ciwo wayata ke silent inajin vibration dinta alamun kira ɗagawa nayi ganin me kirana.

"Ya Taufiq kaina keman ciwo inason hutawa."
"Ayyah sannu my life Allah yabaki lafiya mi kikeson ci."?
"Bakomai."
Nace a matukar sanyayye saboda bansan magana mai yawa.
"Aaa Minal karki zauna da yunwa pls tell me."?
A raunane yayi maganar cikeda da damuwa.
"Kabari inna tashi bacci zan gaya maka yanzun bani bukatar komai."
"Okay take care i love u."
"Love u too."
Nace ina aje wayar gefena.

Maida idanuna nayi na rufe inajin Mum nacewa abar mani dakin inhuta a fita akoma gudan bedroom dinta,haka aka fita ta saka mani Ac kadan suka rufo mani kofar, aiko naji dadin kebeni da akayi baccina nahau yi gwanin dadi saidai still ina fama da ciwon kai sama sama.

Bani nafarka ba sai isha'i alhamdulillah da sauki kan ya saki brush nayi na fito makimancin falorn ta na zauna ina jiyo hayaniyar su a babban falor nidai naki tashi ina zaune nakira Mama waya ta daga.
"Matar Taufiq ya gidan ya Mum."?
Murmushi nayi wai Mama ita ke cemani matar Taufiq ko kunyata bataji.
"Minene abin kunya Aminatu keda kikeso wannan burin naki yacika kuma ya tabbata akanmi zanki faɗa maki kedin ta Taufiq ce Allah yaimaku albarka yabada zaman lafiya."
Kunya takamani ashe

Please Login or Register in order to submit comment