Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saidai mutun ɗaya,yana fita Mama ta shigo fuskarta cikeda annuri."Sannu da arziki Amin dagona yar Mama barkan mu."
sunkuyar dakaina nayi ƙasa alamun kunya domin nauyin Mamar naji ya lullubeni.

"Abani kishiyar tawa inga akwai hanci kodai mummunace."Irin wasan jika da kaka takeyi da jikar tata.

Mika mata ita nayi cikeda girmamawa,ta karba tanasa albarka sosai take mata addu'a tsawon mintoci sannan tace."Kishiyar nan tawa akwai hanci dandai nafita kyau."Murmushi nayi nace
"ina ruwan Asma'u."
"Asma'u."?
Ta maimaita a bayyana cikeda farin ciki da tsantsar jindadi."Eh Mama."

"Allah Sarki Asma'ul-Husna,mai babban suna Allah yarayaki bisa suna yasa kizama abin alfaharin al'umma,lallai kam kice ya'ta ce."ta ida maganar a raunane.
Jinjina kaina kawai nayi inajin dadi saidai yanayin Mama ya nuna tashiga yar damuwa nadan lokaci tace.

"Allah yayi gaskia dayasa lokaci domin yazama abin kiyayewa da lissafawa akan kowane ɗan Adam,sannan ya halicci amana ya sakota a cikin mu,saidai ba kowa ke iya rike amana ba,sai wanda Allah ya za6a,yasanya mana tausayi da kauna a cikin zukatanmu har suka koma aminci na har abada,gaskia Aminatu,kedin kin cika ya' harda rabin ya' kin rike amana da abota da zumuncin dake tsakaninki da mariganya,kin kula da zuriyar ta,sannan kin maidamu iyayenki najini daman kince zaki maye mani gurbin dana rasa gashi kuwa kullin ganin Asma'u nike maki dole injijina maki Aminatu samun kawa irinki sai antona,Ya Allah kaima wannan yarinya albarka Allah ya dawwamar dake cikin farin ciki keda zuriyar ki baki ɗaya Allah yaraya abinda akasamu yasa tafi mai wannan suna alkhairi da kyawawan halaye."
"Ameen Mama."
Nace ina share hawayen idaninta wanda nima su nike zirararwa munjima ahaka sannan Dr Gursum tazo takara dubani ta sallamemu tareda magunguna duk da banjin ciwon komai saidai wanda ba'arasaba.

JMuna fita su Jidda suka taremu mukayi wajen da akayi parking mota.
Bada jimawa ba,Ya Taufiq ya iso hannun da ledoji sai murmushi yakeyi ya bude mana baya muka shiga Jidda gefena Aisha gaba a hankali yake dirabin har muka koma gida.

Komai fes sai kamshi yake bazawa su Jidda sun gyara komai sadda ya dawo gida daukar mana kayan sawa yatafi dasu asibitin direct dakina aka wuce damu,na zaune bisa kujera.

Barka suka shiga yima juna tsakanin Mama da Ya Taufiq kowa sai farin ciki yake,nan su Aisha aka shiga daukar baby.

Haka Mama takirawo Mama,ta shaida masu na haihu,hakama Mum.
Haka akaita yaɗa haihuwar cikin kankanin lokaci,shima Ya Taufiq abokansa yaita sanarwa sai abokan kasuwancin sa sunsa albarka
Kowa yai farin ciki.

Haka nai waya da Mama hakama Mum su Anty Murja kowa sai farin ciki yake.

Da dare kuwa kowa ya kwanta,Ya Taufiq yai mani suprise zuba mani hannu jari yayi cikin companyn shi,saboda narasa aikina na asibiti da nikeyi,murnar danayi bansan adadin taba,haka naita mashi godiya shike juya mani kudin yana bani ribar yace inyi hidimar abokan arziki da ita.

Ya Taufiq yai murnar ganin kyautar da Allah yai mana ta samun karuwa,wannan kenan.


_JAIL_


JJ ne cikin tasasar prisonors a dining kowa yana kokarin samun abincin da zaici aganin su kamar zai kare hakan kesa suna buga wawa da kokowa kamar dai ba abasu komai na dangane da abinci.
Kowa yasan gidan Maza ya banbanta dana Mata hakama yanayin tsagerenci da tsananin girman kai gami da ta'addanci da bushewar zuciya.
Kurmawa Male Prison kenan inda faɗa ya rankame da JJ tareda wani jibgegen matashin saurayi wanda sukewa laƙabi da Ilah.

Rigimar tafarune sanadin abinci inda ilah ke saman ruwan cikin Junaid yana ɗuma kamar Allah ya aikoshi.
ilah(isma'il) ya kasance hatsabibi wanda bai tsoro ko shakkar kowa a gidan gashi ba Sarkin gidaba amman kafi Sarki hatsabibanci ya addabeni kowa cikin gidan daga ma'aikata har yan uwan shi prisonors.
Tunda aka kawo Junaid yake matsa mashi da bala'i,duka,tsangama kyara gami da hantara.
Saboda ila,JJ yasha kwana baiciba baida wani sukuni a gidan sai ya zama mujiya cikin tsuntsaya.

Ya kasance azzalumi kuma macuci sannan yanada gant takowace kusurfa a gidan Ɗan Kande/gidan Maza,kowa na shayinsu.
Tunda ya haye saman JJ yana dirka tun yana ramawa har saida ya sumar dashi bakin shi hanci gami da fuskar shi ba abinda ke zirara sai jini face face.
Ma'aikata sukazo rabawa a ciki kuwa harda Oga Adam dutyn shine ya juyo dashi Male Wins.
Daukar shi akai ba rai zuwa wata inuwa aka hau yimashi fita,wasu na zuba mashi ruwa saidai kamar ya mutu danko motsi baiyi.
Har anfidda rai Junaid ya saki uwar kara mai razanarwa gami da firgita a lokaci ɗaya,saidai kallo ɗaya zakai masa ka kauda kanka sannan zaka kara tsoron Allah a cikin zuciyar ka.
Junaid Jamil Kano daya kasance hadadde mai ji da naira,gami da gadara yaushe abin wulakantawar a gidan maza ya watse ya lalace ya rame yayi bakikkirin dashi in bakai mashi mugun saniba bako shakka bazaka shaida JJ ba tsabar lalacewa.
Farine mai jiki amman duk jikin nan ya ziganye gami da lalacewa a cikin shekarun da basufi ukku ba amman kamar wanda yai shekara shabiyar.

Kuka yake yana neman tserewa dan rudu dakyal suka rike shi,gashi ba wanda ya isa yaima ilah maganar banza ko ihimm yaci dubu si ceto.
Shiko Oga Adam bai wani zafafa case dinba musamman dayaga JJ saboda yasan waye shi.
Haka rayuwa rayuwa takasancewa Junaid kullin cikin wahala ga yunwa kuncin rayuwa abu sama da ishirin sun sha mashi kai ainun.

_ANKA_

Kamar yanda aka sama Zainab rana hakama Khadija yar wajen Anty Hafsat itama wani babban yaron Baba mai kular mashi da manyan shagunan shi yace yana son aurenta.
zuwa yanzun Baba ya zama babban dan kasuwa sosai a cikin garin.
yace komai baison a wuce sati biyu zuwa ukku za'ayi bikin duk da yana da mata ɗaya da ya'ya ukku amman yanada rufin asiri sosai sannan yace kowa gidan shi daban.

Khadija tayi na'am da Yunus sosai hakan yasa iyaye suka shiga cikin zancen har aka tsaida lokacin biki cikin wata ɗaya saboda kanwar Khadija Hajara itama tasamu mijin shine Mama tace ahaɗe dana Khadija sai ayi bikin tare aiko mahaifin su yayi amanna da hakan sosai.

Yunus da Khadija sun saba sosai sannan dawowarta gidan su Aminatu harta kammala Jami'arta tayi Masscom cikin rufin asirin Allah.

Duk abinda uba kema ya' Baban Aminatu yaima Khadija haka gudunwa sosai Aminatu da mijinta suka turo masu hatta kayan daki Baba yai masu harda Hajara,gara ce kaɗai mahaifin su yai masu,sannan Mama tayi kayan uwa tas su duka biyun taimawa.

Lokacin biki kawai suke jira amman sungama komai shima Yunus yai mata lefe akwaiti ukku kamar ba bazawara ba,ita kuma Hajara seti akai mata,wannan kenan.


_ISTANBUL_
Banfi yan kwanaki na warke saboda gyarea da kular da Mama ke mani akoda yaushe ranar da mukayi sati biyu Ya Taufiq ya haɗa mana kwaryakwaryar walimar suna da yan uwana sai matan abokan aikin shi musamman na company yawanci duk yan kasar ne, sai mutanen mu wa'anda ba'a rasaba.
Park jugunanne ya kama mana acan za'ayi bikin sunan,already yai mani yankan rago ɗaya anan istanbul yasa Ya Tariq yai biyu anan gida gun su Mum ɗaya sai Anka ɗaya haka suka rabama dangi kowa yasa albarka.

A *Yildiz Park* akayi lunch din sunan Asma'u wacce nikema laƙabi da *Husna* taci komai na mamanta mariganya.
Doguwar riga nasha Ash ta material sai gold nasama wuyana,Jidda da Aisha anko sukasa hakama Mama tasha kaya masu kyau, *Buhara Ocakbasi Restaurant*,sukai mana ordern abinda zamuci a Park din kowa yazo da matar sa sannan sun mani alkhairi,yaransu suke mani na turkish wani inji in basu amsa wani saidai in mayar masu da turanci.
Anyu hotuna sannan muka tafi gida kafin magrib cikin amincin Allah,duk gajiya ta lullubemu baki ɗaya.

Haka rayuwa ta kasance wasawasa satina ukku cir da haihuwa kuma wanka Mama ta koya mani harna warke garai sannan ta gyarani sosai dan jikina yabani hakan duk burin Ya Taufiq mukai wata kafin indawo gida tun Mama na kawaici har tai mashi magana da kanta,ba yanda ya iya ya hakura tace bata wuce jibi agarin nan litinin kenan ba shiri yafara sai mana ticket yana mana booking.

Washe gari yace zamu mifita amman Mama tayi fir tace bata fita dole muka kyaleta,da ta amshe Husna da kyal ta hakura muka tafi siyayya yai masu na tsaraba dan kowa yanada 48kg na jirgi shiyasa yadan yimasu siyayya da dan yawa.

Har zamu dawo gida auta Aisha tafara hada yayan nata da Allah kada akoma yakaisu yawan karshe musamman wajen ruwa suga beach.

Turkey kasace mai yalwar ruwa musamman beach suna dashi kam,da yaki daya gaji da mita yakaimu *Viaport Marina* wajene mai dauke da ruwa yawanci anfi zuwa musamman idan kai ma'abocin daukar hotone,munfi zuwa nan nida Ya Taufiq da munacin amarcin mu saboda dadi da natsuwar wajen sai wanda yaje.

Bamu jimaba ko pictures kadan mukayi ya tada wuta dole saida muka koma gida kowa yahau parking kayan shi,nidai na bukata kawai ya ware mani domin kayana na hausawa suna gida saidai wa'anda nike mashi kwalliya agida inyana bukatar ganina cikin shigar.
Na dauki kayana da nike using nan na parka hakama kayan Husna na zuba amman kadan dan Mum tace Abba ya hadamana kayan sawa.

Tun dare nike waya da Mum hakama Mama suna kewata,musamman Husna da kowa ke daukin gani, kowa ne bangare gidan mu da nasu.

Sai Ya Taufiq ya koma mani wani iri saboda badashi zamu tahoba can zamu barshi akwai aikin kwangilar da zaiyi wanda baifi sati da samun taba,kuma alhamdulillah zai samu alkhairi matuka,shiyasa Qasim yace ya tsaya shima yana zauname da iyalan shi a Istanbul din,ba yanda ya iya dole ya hakura.

Haka rayuwa ta kasance saidai godiyar Allah,ana kiran sallah ya shirya zuwa masallaci nima sallar nayi sadda bakwai zatayi har kalaci munyi karfe tara daidai yakaimu *Grand International Air Port Istanbul.*

Da kanshi ya rakamu mukayi boding muka gama aka bamu ticket cikin yarda Allah goma daidai aka nememu waving dinmu yake,wani irin tausayin shi yakama mu musamman daya miko mani Husna yana manna mata kiss a goshi sannan ya sumbaci hannuna cikin so kauna gami da tausayawa.
Ban kwana mukayi hakama Mama,sannan muka tafi aka gama checking daga nan muka shiga *Turkish International Airoplane* muka zauna nida Mama tare sit dinmu yake sai Jidda na gaban Auta daga gefen mu,na haggu haka muka kashe wayoyin mu bayan komai ya daidaita jirgin mu ya tashi zuwa kasata abin alfaharina Nigeria,cikin ikon Allah tsakanin *Turkey* zuwa *Nigeria* awa 7:42 ne haka muka keta hazo,tafiya mukeyi cikeda limana.

Husna kuwa na hannun Mama saidai in zan feeding dinta tabani ita kuma inta gama ta miko mani cikin yarda Allah har muka iso cikin *Kaduna State International Airport* ko awa bamu hadaba aka fiddo mana akwaitinan mu kowa ya dauki tashi,Mum da Abba da kansu sukazo daukar mu,rungumeni Mum tayi tana murna shiko Abba daura hannun shi yayi saman kaina yana samani albarka haka muka tafi gida cikin aminci har side din Mum.

Kowa in ya dauki Husna bai son ajewa sai tayi masu farin jini kodan tana jaririya.
Ranar haka akaita murna dawowar mu kowa yana nayi kyau masha Allah.

Ya Tariq kuwa ya kama ya',ya rike ya hana kowa dakyal yaba Ya Samir danko akwaiti guda ya hadama ƴar shi na kaya,sai yai mani less biyu atamfa biyu sai shadda daya,naji dadin kyautar shi agaremu sosai nai mashi godiya dangin mijina sun hada mani kaya naban mamaki kamar yau na haihu komai sai su mikama Mama matsayin ta na uwar mai jego ita ke taramin cikin jin dadi.

Itama sun mata alkhairi,washe gari naji Mum na magana da Ya Tariq da Ya Samir wai zasuyima Husna walima tunda ba nan akai suna ba,haka sukaita hidimar su,kusan komai Ya Tariq yayi shi,ko ɗan uwan nashi bai sani ba kwanan mu ukku da dawowa sukasa ranar walimar lokacin mun cika sati da dawowa,yan gidan mu sunzo da dangin Mama harda na Baba anzo sosai hakama dangin Ya Taufiq sai taron yakoma kamar na sunan sati.

A gida akai komai anci ansha komai yayi dadi alhamdulillah.
Nida Aisha matar Ya Tariq iri ɗaya mukayi har Mina da Haidar nasa Ya Abdallah yakawo mani kwanan su ukku akai sunan har dunkuna nai masu,angama komai dangina sun mani alkhairi suma.

Duk wanda zai koma gida saida Mum taimasu alkhairi da kayan suna irin bags,prayer mat da litattafan addini,sannan Ya Tariq sukai tashar motoci aka maida kowa har gida.

Itako Maman Husna Ya Samir da kanshi yai masu visa zasu sauka Kano sannan zai kaita har Caranci da kan shi,su Jidda kuwa antafi gida tabi su Zainab da Khadija.
Fatash kawata kuwa kwananta ukku yau ta koma gidan ta gwanin dadi.

Satin su Haidar biyu hannuna ayam saiga Abdallah yazo daukar ya'yan shi dan na lura Abdallah bai iya daukar dogon lokaci mai tsayi bai tareda ya'yan shi.

Falor na sauko muka gaisa nan ya dauki Husna dayaketa daukin gani,yajima yanai mata addu'a kafin yabani ita yace.
"Amaryar karni sannunki uwar ya'ya nazo in rage maki su Haidar."Kallan shi nayi nace.
"Dan Allah Ya Abdallah kabar mani Mina."
Shiru yayi yace."Kiyi hakuri Momin Mina wlh banji zan iya nisa da ya'yan nan musamman Mina,alqawali naima mahaifiyar su,tana yawan gaya mani ko bayan raina karike mani amanar ya'yana Abdallah dan Allah kada ka auro wadda zata wulakanta mani su,dan Allah Abdallah kamaye masu gurbina kasasu a cikin ruhinka na rokeka mijina."
Hawaye masu ɗumi suka saukar mashi a ido nima haka yaci gaba dacewa.

"Ashe tafiya zatayi tabarni shiyasa take yawan yimani wannan wasiyar sannan ina son ya'yana uwa uba Mina kodan kamarta da mahaifiyarta kema shaidace Minal kinsan irin son da nikema Matata har abada banji zan samu wadda zanma irin shi."
Hmmm naja numfashi mai tsawo nace."Hakane kaima kasan bazan taba cutar da jinin Husna ba to dan Allah tinda baka iya bani Mina kataimaka kabani Haidar,inason ya tashi hannuna sannan idan san samuna ne,idan Allah ya raya mana su Husna inta girma in aura mashi ita inason in hada jini,na har abada da Husna."

Kallona yake sai kuma yai murmushi yace.
"Minal kenan yariyar dake tsumman goyo,Haidar ya gitta goma kike wannan maganar andaina haka yanzun,kada ta girma tace bata yardaba,koshi amman harkin fara wannan dogon tunanin."?

"Ya Abdallah kenan wannan bawai tunanina ne kadai ba,hardana Ya Taufiq kuma munyi alqawali matukar basu amince da hakan ba,baza'ayi masu dole ba,kai mikace."
"Hakan yayi domin wannan burin naki shine na kawarki Asma'u yana daga cikin dalilin dayasa ta matsu taga jininki dan hada iri da zuriyar ki,kuma gashi Allah ya nuna mana yarmu Husna fata Allah ya raya manasu bisa sunna ya nuna mana lokaci kuma Allah yasa su aminta da zabin iyayen su,kuma suso junan su tun kuriciya."
"Ameen ya rabbi."
Cewar Mum da Abba tare suka shigo suna murmushi,da alama sun tari zancen mu,kuma sunsan abinda muke cewa,Mum tace.
"Iyaye na gari Allah yacika maku wannan burin naku na alkhairi."
"Ameen Mum."
Mukace,sannan tace.
"Abdallah kabarma Taufiq ya rike Haidar watakil hakarmu ta cimma ruwa kuma insha Allah duk abinda uba zaima ɗa Taufiq zai masa tunda da kanshi yace yana so,kuma yasha neman wannan alfarmar."Ajiyar zuciya yayi yace.
"Shikenan Mum naji ga Aliyu nan Allah yatayaku riko."Ameen."
Wani dadi ya rufeni saida ya huta sannan ya tafi da Mina,dakyal suka rabu da Haidar domin sun saba sosai kuma yana son kanwar tashi sosai,har bakin mota muka rakasu ya mikomin katuwar leda kaya ya saima Husna,godiya mukai mashi,wannan kenan.

Bayan wasu watanni komai yana tafiya daidai harna manta dana koma gidana saboda mijina yadawo saidai akai akai yana komawa Istanbul,yanzun zamana yafi nan Mum tafison taganni kusa da ita,har karatun Haidar dacan Istanbul Ya Taufiq zai samar mashi school,amman Abba yace abar shi nan Kaduna kusa dani,saidai indan zai tafi university idan rayuwa takai saiya kai shi can Haidar Js level zaije Mina kuma JSS tayi,inajin dadin zama da Aliyu baida wata matsala saidai rashinji wanda yagaji sunan Ali sai yai kiriniya.

Dan zaman da yayi taredani ya saba da kowa hatta Husna haka yake renon kanwar tashi.
Tunda muka dawo saida naje Anka najima sosai har akai bikin Khadija da Hajara wanda su kansu sun kwashe watanni dayin shi yanzun shirin bikin Zainab da Rahima baifi sati biyu ba cikin ikon Allah.

Mum tace muje muyi zumunci tunda Husna tafara wayau nida matar Ya Tariq Usama yakaimu sai Ya Taufiq dashi muka tafi Caranci mukafara sauka gidan Mama,sannan mukaje gidajen dangi gidan Anty Mubara mukaje tunda suka dawo suna saida naje nayi sati biyu Anka itama taje lokacin suna shirin bikin Zainab daman Anty Rukayya takoma sai bayan biki zata dawo tunda mukaje ta karramamu tafara yimani maganar Anty Hafsat akan inyafe mata daman koda naje Anka kusan zaune muka kwana da Mama ba maganar da take mani sai inyafema Antyn ta,Allah yasani mantawa dasu nike a duniyar baki ɗaya sai yanzun da suka tado mani da zancen,haka dai har muka gama yawon mu,muka sauka gidan Dada ita da tafi kowa harda kukanta wai inyafema Anty Hafsat,take nakara yarda tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah,ranar saida Dada takusa sani kuka cewa take.
"Aminatu dan Allah kiyafema Hafsatu kibari daji da darasin rayuwa ki yafe mata."
Ya Taufiq yace.
"Ki daina kuka Dada insha Allah idan mukaje kano har ziyara zamu kai masu."
Taji dadin jin hakan ainun da haka muka dawo gida washe gari mukaje gidan Anty Murja Katsina kusan kwana mukai da Anty muna fira hakama Anty Aisha itama akwaita da fira.
Washe gari mukaje Kano gidan Anty Zainab shabiyu daidai muna gidan ta,ranar asabar har akai azahur sannan Ya Taufiq yace mu shirya muje prison akai juyin duniya nace banzuwa dan na tsani inga Anty da Mami uwa uba JJ dan dole aka kyaleni kwana mukai Anty nai manj nasiha da hudubobi har zuciya ta,tai sanyi ba laifi na fahimci Ya Taufiq yai fushi dani zuwa nayi naba shi hakuri sannan nai mashi alqawali gobe lahadi zanje yaji dadin haka,washe gari dani da Anty Aisha sai Haidar da Husna mukaje *KURMAWA JAIL* gidan dako sunan shi bansan inji bare in furta shi,haka mukaje tsabfin ma'aikatan da aka basu sani sun ganeni,hatta Oga Adam yai murnar ganin mu,sawa yayi aka fara kira mana Hafsat Shehu muna zaune a kushin ba'ajima kwarai ba saiga Anty Hafsat ta shigo cikin kayan yari tsaye tayi tana kallan mu ko keftawa batayi kamar mai neman gano inda tasanmu nima itadin nike kallo cikeda tausayi gami da tsoro.

ganin ta gaza shigowa Oga Adam ya daka mata tsawa yace.
"Ke Hassu shigo kikaima mutane tsaye kinyi baki Aminatu ce idan baki ganeta ba nagaya maki kosu waye."

A sanyaye Anty Hafsat ta iso ciki ta zube gabanmu da guiwowin ta tafara kuka mai sauti kallona take tana.
"Aminatu daman kece kika koma haka?da rabon zan sake ganinki kafin inbar duniya Allah nagode maka daka nuna mani wannan rana Aminatu na zalinceki a rayuwa na rokeki da darajar Allah kiyafemani ya'ta naga rayuwa naga ishara naga karfin ikon Allah da kudurar shi naga aya duniya ta juyamani baya ada damu take yayi yanzun kuwa mun zama zama yan kallo Aminatu....
Kuka yaci karfinta niko kallan tsana nike mata araina ina tuna lokutan da suke kawo mani ziyara da mugayen maganganun da suke aika mani shiyasa duniya abar tsoro ce idan zaka gina ramin mugunta kayi gajere kodan watan wata rana.
Saida tasha kukan ta taci gaba da cewa.
"Dan Allah kiyafe mani natuba Aminatu."
Anty Aisha kuka takeyi kowa yaji tausanta niko narasa mi nikeji nata nasan dai bana sonta yanda bata sona cewa nayi.
"Allah Sarki Anty Hafsat ni bazan kullaceki ba,kuma bazan iya gaya maki mugayen maganganu ba dan in muzantaki ba kodan insakaki cikin mawuyacin haliba sannan bazan taba nufinki da sharri ba kullin zuciya ta mai kyauce akanku,dan Allah zan yafe maki amman badan halinki ba,saidan albishir da Allah yakema masu hakuri da kuma ka6aki na lada daya tanadar masu dan haka kawai zan yafe maki sannan bansan atuna komai daya wuce har cikin zuciyata ni Amina Yusuf na yafemaki duniya da lahira ban rike dake saidai laifin kisan da kukai wannan tsakanin ki da halaccin ki ne,nidai nawa laifin na yafe maki dan darajar Allah da girman zumunci."

Rungume ni tayi nidai atakure nike banda kyari ba abinda take ga wani irin baki tayi marar kyau duk ta lalace amman ance dole sai dole duk lalacewar Anty Hafsat dolena ce tunda yayar mahaifiyata ce.

tajima jikina tana kuka sannan ta sakeni tace.
"Nagode maki Aminatu Allah yaimaki albarka Allah yakareki daga sharrin mutun da aljan nai maki sharri kin saka mani da alkhairi Allah yabaki lada."
Ameeen."nace.
Kukan take nidai nakasajin tausanta azahiri bare inyi kuka amman halin data shiga yana daga mani hankali ainun.

"Allah yaimaki albarka Minal Allah nason mutane masu yafiya kin kyauta."cewar Ya Taufiq
Ameen nace.

"Wai Aminatu keda Hussein yatabbata dai ma'aurata ne ko.?"
Murmushi kawai nai mata,Anty Aisha tace.
"Kwarai kuwa gashi harda ƴarsu Asma'u sun haifa."
Banda ambaliyar hawaye ba abinda Anty keyi haka tasa hannu ta dauki Husna tana kallanta kwalla na zuba a idonta tace.

"Allah Sarki ashe, mariganya akayi Allah yarayaki bisa sunnar ma'aiki Allah yaima rayuwrki albarka saboda rabonki yai sanadin ajalin mutane da dama,ya saka mutane dayawa garari shiyasa jayyayya da ikon Allah ba karamin bala'i bane Allah mun tuba,da mukai maka shishshigi Allah yarayaki Asma'ul-Husna."
Ameen muka amsa sai lokacin idanuna suka sauya launi.

Ya Taufiq yasa akira mashi Mami,ni kuma nasa akira mani su Cankwai.

Su,suka fara isowa murnar ganina ba kadan sukai ba musamman da sukaga nayi aure harda ya' daukarta sukayi sukace.
"Aminatu dagaske yarki? kice munyi ya'."

"Eh Sarauniya itace."
"Allah yarayata kice Taufiq din kika aura Allah yabaku zaman lafiya."
"Ameen."
Duk muka amsa.
Nan Anty Hafsat ke cewa in roka mata arziki wajen Magajiya dan Allah su ɗaga mata kafa tasamu ta huta da azabar su.

Dan murmushi nayi nace.
"Haba uwar ɗakina karki manta fa Anty na ce aimata lamani nimafa nayafe maki,nasan baki zama inuwa ɗaya da maci amana,amman kiyi hakuri."
"Angama Hajjaju yanda kikeso haka za'ayi an kyaleta taci darajarki."
"Nagode kwarai."
Itama godiyar tai masu.

Shiru Mami tazo amman kamar bata zuwa har zamu tafi nabawa Anty Hafsat kudi masu yawa,hakama su Cankwai naba kowa Anty Aisha ma,tai masu alkhairi Ya Taufiq shima yaba Adam kudi sai wata makimanciyar jikka yace tallafine arabama prisonors bansan miye cikiba amman nafi zargin kudine muna mikewa Mami na shigowa itama saida tajima sannan ta wayen cemu da yatsa take nunamu banda doɗe hancina da kowa yayi tsabar ɗoyi dake tashi azafafe tayo kaina tana cewa.

"Hussein,Aminatu kunzo dan kununa mani kunyi auren ko."?
Da sauri naja baya na koma bayan Ya Taufiq tsorona kada ta shakoni nasan bakai gareta ba.

"Eh munyi aure Mami gashi harda jininmu yarmu Asma'ul-Husna."Ya Taufiq yabata amsa.

"Ihuhuhu wlh saidai inba ran Mufida Shehu sai nayi ajalin ku baku ba auren juna bare har kuyi ciki,ku haihu,na shiga ukkuna ni Mufida ya zanyi nashiga ukku na lalace."

Dukkan mu kowa ya gaza magana karfin hali Ya Taufiq yayi yace.
"Yanzun Mami baki sadudaba bare kituba Aminatu ta yafe maki."

"Wlh har abada bani ba neman yafiyar wannan tsinanniyar saina kasheta kuma saina raba auren ku,kuta bala'i ne."

Kan Anty Aisha tayi takaima Husna cafka kamar kaftawar ido ya Taufiq ya fige yarsa tareda ɗaɗawa Mami mari yace.
"Yar isa ta Allah bataki ba saidai ki karata a nan."
Waje oga Adam yasa akayi da ita,kamar mahaukaciya.
Sallamar su Cankwai mukayi suna cewa zasu gyarama Mufida hankali agidan nan dasu take zancen da haka suka fita suna mana bye bye.

Zamu tafi Ya Taufiq ke tambayar Adam labarin JJ yace yana nan gidan Yarin Maza,bari ya rakamu lokacin anfara kiran la'asar koda mukaje wani office yakaimu baijima da fita ba saiga Junaid haryafi Anty Hafsat watsewa,cikin ikon Allah baifi minti biyu da zuwaba yaganeni a zabure ya mike yana dafe kirji yace.
"Caran caranci beaut...
Kasa ida maganar yayi ya barke da kuka mai tsuma rai.
Nima shi nike kallo cikeda da tausayi halin daya faɗa na ukuba,tattare jarumtar shi yayi yace.

"Beauty kece kika koma haka."?
"Ka iya bakin da aure akanta."Cewar Oga Adam.
"Wai wai dagaske kaita aura Taufiq."?ya jefama Ya Taufiq tambayar.
"Kwarai kuwa."Yace ata kaice.
"Ikon Allah kardai ace wannan jinin kice Caranci."?"Eh." nace ina kauda kaina gefe dan naga tsantsar nadama take a Cikin idanun Dr JJ gami da son dayake ikirarin yana mani acewar shi na hakika ne.

Ansarta yayi yana kallo yace."Bako shakka wannan jinin caranci ce ashe da raban zan dauki yar Mina da hannuna,Allah yaraki baiwar Allah minene sunanta."?
"Asma'u."Cewar Ya Taufiq.
"Allah Sarki amana sai Allah amman Aminatu kin rike amana Allah yajikanki Husna,duk da alhakin mutuwarki na kanmu amman na saduda kuma na tuba dan Allah Aminatu kiyafe mani ƙagen da nayi maki,badan furta kalmar so ga macen aure haramun ne ba dana jadaddamaki sonki yajefani cikin wannan tarkon dan Allah kigafarta mani."

Kallan Ya Taufiq nayi wanda fuskar shi ke murtur narasa abincewa ganin Junaid ya duka da guiwar shi kasa yana kukan hakan yasa

Please Login or Register in order to submit comment