Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi, bashi fah da wanda ta fiki, ko kin manta ke kika haifeshi?, zakiji dadi anty ta daina kula dake?

Girgiza kai tayi sannan tace a,a

Toh dan Allah kema ki fara yau idan zaki kwanta ki tafi dashi dakin ki, ki rungume shi har gari ya waye"

Toh aini bana kwanciya da yara"

Da sauri yace ki koya daga yau?

Toh tace sannan ta sunkuyar da kanta kasa dan tanajin wani irin kunyar shi

Muryan shi taji yana cewa kin min alkawari zaki bawa sadiq kulawan da uwa take ba danta ?

Eh ta fada tana wasa da hannunta"

Kura mata ido yayi sannan yace nifah? Wanne irin kulawa zaki bani ?

Shanyayyun idanun ta ta watsa mishi sannan tace"

Kaima kana so ne?

Inaso mana nihilah sosai ma"

Tana wasa da yatsunta tace, yanzun banda kulawar da naziya ke baka har kana neman wani?

Damm! Gaban faruq ya fadi dan shi kwata2 ya manta da wata naziya, kakalo murmushi yayi sannan yace"

Nihilah naziya kai tsaye bazakice mata anty ba?

Ni ba anty na bace, bamu hada komai da ita ba, kuma bazamu hadaba har abada"

Hmmm nihilah rigima, mubar wannan mgnr mudawa mgn mu na dazon, wanne irin kulawa zaki bani amatsayina na mijjn ki?

Hawaye ne suka zobo a idonta tasa bayan hannunta ta share sannan tace"


Yaya indai har kana bukatan kulawa ta toh sai dai in ka saki naziya












❄💦Mmn Yazeed❄💦
❄💦❄💦❄💦
*ASIRINSA YA TONU*
❄💦❄💦❄💦


❄❄❄❄💦
*By*
❄❄❄💦
*Fadeela Lamido*
❄❄💦

❄💦



❄❄💦
*Page 51 to 53*
❄❄💦






Zabura naziya tayi aguje ta nufi dakin"

Tana shiga ta same shi ya hada zuba tare da saka hannnun shi me lfy ya rike Mara lfy"

Ganin inda jikin shi ke rawa yasa hankalinta yayi mummunan tashi"

Sannu take mai amman be iya amsawa ba"

Waryarta ta dauka ta kira bashir ta gayamai abin dake faruwa"

Cikin kankanin lokaci saiga bashir tare da mlm salihu"

Faruq zaune dirshin akasa mlm salihu ya tsuguna agaban shi tare da duba hannun"

Juyawa yayi ya kalli naziya tare da fadin ke wacce irin yariya ce, tayaya kinsan kina da mara lfy zaki nisa kibar shi, haka ake jinya?

Sunkuyar dakai tayi tare da matso kwallah"

kayan aiki mlm ya fara fitowa dashi nan faruq ya tabbatar hannun shi ya turgude, yaufa akeyinta, ya fada azuciyar shi, domi yadda hannun nan yakemai radadin bazai so atabashi ba, dan ko yanzun daurewa kawai yakeyi bare kuma ataba mishi"

Ganin mlm ya nufa hannun yasa faruq daga ido ya kalli naziya sannan yace"

Naziya jiki"

Daki ta koma tare da tunanin kodai fushi yake da ita, tana cikin tunanin ta fara jin ihun shi"

Tausayi ya bata sosai sai dai har yanzun bata daina jin zafin zaginta da yayi ba"

Bayan mlm ya gama ya karawa naziya fada sosai sannan ya musu sallama ya tafi"

Bashir zama yayi agefen faruq suna dan hira jefi jefi, zuwa can ya mike yace zai tafi"

Godiya faruq yamai har yakai kofa faruq yasake kiran shi"

Cikin sauri ya dawo yana fadin wanne abu kk so?

Girgiza kai yayi sannan yace"

Kabawa naxiya hakuri dan na mata laifi, wlh nihilah ce ta batamin rai, kawai sai naji haushi komai nakeji"

Hmnn Faruq kenan anya kuwa zaka iya adalci kuwa? daman laifin wani yana shafan wani?

Nidai bawannan na tambaye ka ba kawai dai nace kabata hakuri"

Kunkunai bashir ya fara yana fadin haba yariya nada karamin ciki amman kai da kanka kana tayar mata da hankali"

Cikin fada faruq yace"

Au zakamin rashin kunya ne? Kaifa kanina ne"

Bawani kani, d'a ma yana saka ubanshi ahanya idan yaga uban nashir kaucewa"

Wani haushi ne ya kama faruq dan haka yace"

Kazo ka dakeni ne yafi"

Bashir juyawa yayi ya fita dan yaga faruq nema yake yamai da abin fada"


Yana fitowa falo ya samu naziya zaune ta yafa mayafi"

Tana ganin bashir ta mike tare da fadin dan Allah bashir kasaukeni gidan anty"

Kallo bashir yabita dashi sannan yace"

Keda kk da mara lfy me zai kai ki fita"

Hawaye ne suka fara zubowa a idonta zuwa can ta fashe da kuka cikin murya me ban tausayi"

Barinta bashir yayi tayi kukan sosai yana sauraron ta zuwa can yace"

Naziya dan Allah kiyi hakuri ki daina kuka, kome faruq ya miki nasan me girma ne, kuma yayi nadama"

Cikin kuka tace"

Bashir wlh bazan iya ba zagina fa yayi, nayi kokarin daurewa amman na kasa, tunda ya fara,a zagina nan gaba ma dukana zai yi, bare kuma ace nihilah ta tare"

Lallashinta yayi sosai tare da kara kwantar mata da hankali, har yaga ta natsu sannan ya mata sallama"

Faruq har dare bega shigowan naziya ba, gashi anhanashi motsa hannun bare ya lallaba ya tashi"

Ga tunanin nihilah ya dameshi babban burin shi yaya za,ayi yaga nihila tare dashi, yana cikin wannan tunanin naziya ta turo kofar tare da sallama"

Ahankali ya amsa sannan ya zuba Mata ido"

Ganin inda ya kureta da ido yasata sunkuyar dakai, sannan tace"

Kana son wani abu ne ?

Dan murmushi yayi dan ya kula har yanzun cikin fushi take, murya kasa2 yace"

Eh akwai shi ?

KO kallon shi batayi ba, tace toh ka fada nakawo maka"

Kara kashe murya yayi sannan yace"

Kwanciya zaki gyara min"

Takawa ta farayi harta isa gaban shi tana zuwa gaban shi, ya janyota jikin shi ya rungume, da hannun shi ya fara shafa bayanta yana fadin"

Lufff lufff Allah ya huci zuciyar ki, daman haka kike da fushi?, horon ya isa haka indai ba kina son zuciyata tayi bindiga bane"

Wani sanyi naziya taji azuciyarta da ace kullum haka take samun wannan tarairaya ai da ta more, ajiyan zuciya ta sauke da karfe batare da ta shirya ba"

Shiko faruq fadi yake yauwa amaida zuciyar bazan kara ba"

Lufff tayi ajikin shi kamar mage, zuwa can ta farajin hannun shi nayawo ajikin ta, jitayi yana neman wuce gona da iri, dan haka ta rike hannun, tare da fadin kai da baka da lfy"

Akunnenta ya rada mata ai zan iya, ki dai taimaka kawai Ki cire kayan jikin ki"

A,a nifa jinyarka nake yi"

Daga murya yayi kadan sannan yace"

Nace miki zan iya sai dai in hanani hakkina zakiyi"

Ba yadda ta iya dolle tabarshi yayi yadda yaso da ita, saidai tasha bakar hawahala dan yadda faruq yake nuna hadama kamar wanda ya shekara beyi ba"

Gefe ya koma yana maida nunfashi zuwa can ya fara kuka da hannun shi"

Wani mugun zazzabine ya kama shi, hannun shi ko jiya yake kamar ya cire ya aje agefe, dan azaba"

Naziya ko jikinta ne yayi tsame gawani mugun bacci da takeji, dan haka tanajin yadda faruq ke rawan sanyi amman takasa tashi, Azuciyarta tace"

Maganin ka kenan kwadayin ka ya jawo maka"

Baccine me dadi ya kwasheta, cen tsakiyar dare taji muryan faruq yana kiran sunanta"

Ahankali ta bude ido ta kalleshi, hannun taga ya kunbura har wani kyalli yakeyi, saboda kunburi"

Dasauri tashi ta zauna, tanabin hannun da kallo"

Naziya matso ki hura min, wlh azaba ya isheni"

Hurawa ta fara kamar yadda yace, tun tanayi da marmari harta gaji, gashi bazata iya cewa ta gaji ba, zuwa can hawaye suka fara zubo mata"

Jin saukan ruwa ahannun sa yasa shi kallota tare da fadin kingaji ko?, bashi haka kwanta kiyi bacci"

Gefe ta koma ta kafeshi da ido zuwacan yace"

Naziya kira min anty na"

Da sauri ta kalleshi tace kasan KO karfe nawa ne yanzun, gaskiya ka bari saida safe"

Naziya kisan abinda nakeji kuwa, kiramin ita kawai"

3:13am wayar naziya ta shiga wayar anty"

Karan wayar ne
ya tada anty daga bacci, gabanta ne yayi mummunan faduwa lokacin da taga kiran naziya"

Jiki na rawa ta dauka muryan faraq taji yana fadin anty nagaji fah, hannun ya matsa min"

Innalillahi wa Inna ilaihir raju,un ta fada sannan tace"

Yaro kasake faduwan ne?

A,,a amman dai ya matsa min"

Cikin tausayawa tace"

Yaro ka daure da safe zanzo, bari nagayawa daddyn ku"

Tana aje wayar takalli daddy da tun kiran wayar ya tashi ya zauna, bayani ta faramai"

Bayan ta gama yayi shiru zuwa can yace"

Inaga abin da ya kamata mu dauko faruq mudawo dashi gida dan jiyan shi bana mutun daya bane, kinga idan ya dawo gida sai su hadu da nihilahn da naziya safi jin saukin jinyar"











❄💦Mmn Yazeed❄💦
❄💦❄💦❄💦
*ASIRINSA YA TONU*
❄💦❄💦❄💦


❄❄❄❄💦
*By*
❄❄❄💦
*Fadeela Lamido*
❄❄💦

❄💦



❄❄💦
*Page 54 to 56*
❄❄💦




SADAUKARWA


Maman hanan
Ummu affan
Fareedaht
Madam jaanah
Maxxyluv
Suhaima
Zainab
falhat
Haleemah
pretty
Zainab idris Ibrahim
queen Ajeebo😜
Maman saif
Mmn mu'alim
Aisha Muhammad alkali
Roubeika






❄💦
Asuban fari anty tamike ta zura hijjabi, sannan tacewa daddy alhaji tashi muje mudauko yaro"

Tashi daddy yayi ya zauna yana fadin"

Meyasa kk cika wutan ciki ne, kibari mana muyi sallah "


Lallashinta daddy yayi daker da bari garin ya fara haske kadan sannan suka kama hanya"

Suna isa anty sauka da sauri daddy ya bita da kallo"

Kofar falon ta fara bugawa har sau 3 amman shiru"

Sakkowa daddy yayi daga cikin motar yana fadin KO sun samu bacci ne"

Daidai lokacin aka bude kofar naziya ce tsaya jikinta daure da towel, ta bude kofar ta koma ta rave, abayan kofar"

Ganin haka yasa daddy yaja da baya , yayin da anty ta shige ciki"

Kallo tabi naziya dashi ganin inda ruwa ke diga daga gashin naziya yasa ta wani tunani daban"

Bata kara tabbatarwa ba saida suka shiga dakin da faruq yake" domin hango kayan nashi tayi yashe akasa gefen da faruq ke kwance kuwa ga bra dinta nan"

Itama naziya sai allokaci ta kula da haka, dan zaro ido tayi sanna ta fara yan soshe2"

Kallonta anty tayi sannan tace"

Naziya saka kaya maza kizo ki gyara wajen nan, dan daddyn ku zai shigo"

Toh kawai naziya tace yayin da anty ta fito falo ta zauna"

Tunani anty tafara acikin zuciyarta lallai idan akabar yaro agidan nan hannun shi bazai warke ba, dan hakama yanzun saidai awuce dashi dakinta"

Tana cikin wannan tunanin naziya ta fito tace nagama"

Toh zo mana naziya anty ta fada tana mika mata hannu"

Cikin kunya naziya ta taho jikin anty tare da sunkuyar da kanta kasa"

Ahankali anty tace naziya daman mun yanke shawaran tafiya daku can gida ne dan adinga taimaka miki da kula dashi, ko me kk gani ?

Eh anty hakama yayi, cewar naziya tana mejin matsanan cin kunya"


Har ciki daddy ya shiga ya kamo faruq ya sashi amota sannan suka kamo hanya"

Bayan sun isa gidan afalo aka kwatar dashi, duk yan gidan na tsaye suna mai sannu"


Bayan kowa ya watse ya rage daga faruq sai inna hajiya"


Shiko faruq atsarge yake burin shi kawai ya tsarkake jikin shi"

Inna hajiya ce tayi zaune agefen agefen shi sai zuba mushi hira take yi"

Zuwa can ya kalleta yace inna hajiya ni naga kowa amman banga nihilah da sadiq ba"

Tabe baki tayi sannan tace"

Aikin kenan baka da zance saina nihilah yo wasani ma KO karyan ciwon hannun kayi dan kazo ka ganta"

Hmmm inna inaga dan bakisan azaban da hannun kemin bane, kawai daurewa nake"

Aikara dai ka daure karka zama ragon namiji, ina ka baro min kishiyata"

Tana gida anjima bashir zai daukota"

koda bashir ya kawo naziya anty bata barta taje wajan faruq ba saidai turamai bashir akayi amatsayi me tayashi kwana har Allah ya bashi lfy, ko ajikin shi hira suka shigayi da bashir, har lokacin da bacci ya kwasheshi"

Kwanan faruq 2 agidan amman har yanzun besa nihilah aidonshi ba,, sadiq ko harsun fara sabawa dan yanzun ya rage koke2

Naziya ko kullum dasafe take zuwa dakin faruq bayan bashir ya tafi aiki, sukan dan taba hira sanna ta koma gurin anty"

Kulum anty tana shiga dakin faruq su 4 ko 5 dan taji ko yana son wani abon"

Hakama daddy dasafe kan ya tafi aiki yake shi sannan da daddare ma ya shiga"

Satin 4 agidan hannun yayi sauki sosai saidai tunanin nihilah dake damun shi, gashi bazai iya kallon idon anty ya tambayeta nihilah ba hakama daddy, dan yanzon kunyan su yakeji sosai"

Da daddare faruq da bashir kwance akan gado kamar yadda suka saba kullum dare"


Hira bashir keyiwa baruq amman yaji yayi shiru baya cewa komai"

Da sauri ya juyo ya kalleshi dan gani yakeyi ko bacci ne ya daukeshi"

Idonshi ya gani kiri2 yana kallon sama"

Girgizashi yayi da sauri ya zabura"

Tunanin me kkyi haka"

Ajiyan zuciya ya sauke sannan yace bashir inason naga nihilah nafi fah sati hudu fah agidan nan amman ace haryanzun banganta ba"

Murmushi yayi sannan yace aidaman nasan cewa zakayi nihilah, nihilahn da bata damu dakai ba tanafa gurin umman bakaga yadda tayi kyauba ko tunanin ka bata yi"

Gabanshi yaji ya fadin wai me umma ke nufi ne, dawannan tunanin ya kwana"

Dasafe anty ta shigo kamar yadda ta saba, ta kula faruq yana cikin damowa harta tambaye shi ko akwai wani abu ?

Amman saiya boye mata dan haka anty na fita ta Kira naziya bayan ta zauna anty tace"

Naziya nakula Yaro yana cikin damuwa koya gayamiki abinda ke damun shi?

Girgixa kai naziya tayi tare da fadin begaya min ba anty nima haka na ganshi tun jiya"

Toh ke kuma baki tambayashi ba?

Ai anty idan na tambaye shi zai iya ya rufeni da fada, dan hakama bance zan tambaya ba"

Baki anty ta sake sannan tace"

Ke wacce irin yariya ce naziya? Keda mijiki? bakisan yadda zaki tambaye shi cikin dubara ba? ai ba zuwa zakiyi kice wane meke damun ka ba, cikin dibara zakimai tambayar saikiga ya fadi har abunda beyi niyya ba, tashi maza kije"

Mikewa tayi zuciyarta cike da yaba hali irin na anty


Tare da tunanin ta wacce hanya zata biyowa faruq batare da ya mata fada ba"

Saida ta dade tsaye abakin kofa tana karanta addu,oi sannan ta tura kofar tare da sallama"

Daker ya amsa sallamar sannan ya maida kanshi gurin sadiq dake zaune agefenshi"

Wayoyin faruq ne zube aganshi sai wasa yake dasu"

Bakin gadon naziya ta zauna sannan ta kurawa sadiq ido"

Ganin inda naziya ke kallon faruq yasa faruq ma ya kura mata ido, zuwa can yace"

Naziya me kk kallo haka?

Murmushi tayi sannan tace"

Gaskiya sadiq kyakyawa ne, bakaramin kama yake dakai ba da ace sa,anni kuke baza,a iya banbace kuba"

Dadi yaji sosai har cikin ranshi dan haka yasaki wani kayataccen murmushi sannan yace"

Nima naga haka naziya shiyasa ma nake dada jin sonshi nashiga zuciyata"

Hannu ta mika ta juyo da fuskan sadiq sannan tace"

Kasan meye ?

Saikin fada cewar faruq tare da zuba mata ido"

Atsorace tace abu daya ne afuskar ka yanzun haka wadda babu ita afuskan sadiq"

Menene shi?

Ahankali tace damuwa"

Shiru yayi kamar ruwa yacishi zuwa can yace"

Eh tabas naziya ina cikin damuwa amman aini da sadiq matsalar mu ta kusan zuwa daya da kadan nawa yafi nashi"

Shiru naxiya tayi domin bata gane inda zancen ya nufah ba"

jitayi yaci gaba da cewa dani da sadiq bamusan dadin uwaba, garamani nasha nono nakwana 2 amman sadiq uwarshi bata taba daurashi akan jikinta ba, kuma tana raye ba mutuwa tayi ba" ni yanzun babban abinda ke damuna nihilah ina matukarson na ganta kusa dani"

Shiru yayi zuwa can yace"

Naziya yaya za ayi ne yanzon dan Allah ki taimake ni"

Gaba daya jikinta sanyi yayi wani irin damuwa ya shigeta cikin sanyin jiki tace"

Toh kayiwa anty mgn mana"

Naziya wlh wani irin kunyan anty nakeji bazan iya gaya mata ba"

Shiru tayi zuwa can ta mike tare da fadin ina zuwa"

Tana fita hawaye ya zobo mata tasa hannunta ta share sannan ta nufi dakin anty"

Duk yadda sukayi ta gayawa anty yayin da ta kare mgnr da cewa"

Anty dan allah kiyi nihilah mgn ta dawo"

Hmmm naziya kenan cewar anty tare da yaba tarbiyan nadiya"


Washegari

Anty dakanta ta nufi gidan umma"

Nihilah naganin anty gabanta ya fadi"

Cikin sauri ta mike ta nufi bayan umma ko kallonta anty batayi ba ta neme guri ta zauna"

Bayan sun gaisa da anty umma tace"

Lfy na ganki afusace?

Lfy lau alhaji na nan ne"?

Eh yananan bari akira shi"

Zuwa can alhaji ya shigo umma nabinshi abaya"

Da Fara,a ya kalli anty tare da fadin ai bansan kina son ganina ba, dasafe nashiga gidan naku"

Dan murmushi umma tayi sannan tace"

Dama akan mgnr nihilah da Yaro ne, narasa gane me Kuke nufi, shine nace bari nazo naji"

Fuskar shi cike da murmushi yace"

Ai mu munriga mungama mgn dazaran ya samu sauki zata tare agidanta saboda kinsan halin da yake cike ba,a dauki mata abashi ba, itama naziyan da cewa nayi abarta can gidan, saboda kisan halin yaran zamani ba hakuri garesu ba, kinga ai sanda yana gidanshi bini2 za ace hannu ya tashi, tunda aka dawo dashi gida ai hannun ya daina tashi"

Duk abinda ake nihilah na gefe tanaji, umma ma tanaji amman sai tana basarwa"

Anty ce tace ni kaina alhaji banason abashi mata amman ai yakamata ace nihilah nazowa tana dubashi, tunfah da Yaro ya dawo gida ko keyarta bamugani ba, ai KO babu auren shi akanta amatsayin shi na dan uwanta yaci ace tazo ta duba shi, amman dan bata da mutunci batasan darajan nagaba da itaba ta dawo nan ta tare"

Mai da wukar alhaji ya fada yana kallon anty sannan yaci gaba da cewa Aisha tayi laifi sosai bakadan ba, amman kinga me laifin nan "


Umma ya nuna da hannu sannan yaci gaba da cewa"

Inda tana turata zataje ko kuma idan ta tashi zuwa ta tasa ta agaba"

Da sauri anty tace ai itama bata taba zuwa dubashi ba bare ta tura wani, alhaji wlh gaisuwar yaro ma daker take amsawa, da wanne zaiji, juyawa tayita kalli umma sannan tace"

Ni kallonki kawai nakeyi, wlh kinban mamaki dan duk wadda yaki yaro ni yaki, KO kina tunanin dan kinbani yaro tun yana tsuma shikenan kin yanke alaka dashi? Indai ko hakane baki kyauta min ba, koko kina tunanin dan kin nunawa nihilah so zaki burgi ni ne" idan kinason ki birgeni kimin kara ki kyaunaci Yaro"

Shiru alhaji yayi sannan yace ashe akwai abunda yake faruwa wandda mu bamu sani ba, umma ya kallah sannan yace"

Me kuma ya kawo gaba tsakanin ki da faruq?

Alhaji kasan nifa bana son rashin kunya, shiko tun yana karami idon shi atsai tsaye yake bashi da kunya ko kadan"

Tunzira anty tayi sosai afusace ta miki tace"

Ga mara kunya fitsararriya nan agaban ki"

Itama umma mikewa tayi fuskarta dauke da murmushi kallon Anty tayi sannan tace"

Wata kilah kin manta shi ya raine ta, ai goyonsa ce, kinga ko dan tayi rashin kunya bata yar ba"

Gaban anty ne ya yanke ya fadi sosai aganinta da wannan mgn wani kundu memen zagine, fiiii tayi waje ta shike mota"

Alhaji ne ya biyota yana kokarin tsayar da drive amman kafin ya karaso sun fice agidan"

Falo alhaji ya koma yana shiga ya rufe umma da fada ta inda yake shiga batan yake fita ba jikinshi har rawa yake"

Da dai umma taga fadan yayi yawa saita fashe da kuka cikin kukan take fadin"

Alhaji ya batamin raine tayaya zai girma akarkashin su sannan ya lalata musu tarbiyan yariya, mahaukaci ne shi? Ita kadai fah suka haifa saboda mugun halyn shi har ya iya turmusheta tana amatsayin kanwar shi"

Kash😬 matalata dake idan kika rike abu kin rike kanan cewan daddy afusace yaci gaba da cewa karna karajin wannan mgnr abakin ki ta wuce kaddara ce, kuma kitashi ma ki dauko mayafi ki sameni mota, juyawa yayi ya kalli nihilah data manne jikin bango tana kuka yace"

Kema taso ki dauko gyale kukan ya isa haka"

Ko ahanya nasiha alhaji yayita ma umma tare dabata shawara"

Nihilako na gefe idonta duk sun kunbura saboda kuka, sai dai kuma idan ta tuna yau zataga faruq wani nishadi takeji"

Itako umma ta kuturta azuciyarta bazata taba barin faruq da nihilah su kebe ba, kafarta kafar nihila, dan harga Allah takejin zafin abinda yayiwa nihilah"

❄💦


Faruq

Please Login or Register in order to submit comment