Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukayi kowa na kallon ta Inna hajiyace tayi karfin halin cewa"

Ke bilkisu wanne irin aikine wannan nonon uwarshi fah?

Tana tafiya take fadin"

Inna hajiya kiyi hakuri nihilah bazata shayar dashi ba, jikinta nayin kwari aure zatayi"

Batajira me hajiya zatace ba tayi waje"



Bayan shekara 2


Hankalin nihilah ya kwanta tayi wani irin kyau nabam mamaki"

Bazaka taba cewa ta taba haihuwa ba dan har yanzun yariya ce har yanzun bata kai 19 ba"

Zuwa wannan lokacin hankalin faruq yadan kwanta kadan dan yana ganin nihilah kulum cikin kwanciyar hankali"

Sai dai daya tuna sadiq yake jin bacin rai, dan ma Allah yasa yana dadewa began shi ba, sai yaje gidan su umma so nawa be ganshi ba"

Nihilako duk Wanda yazo gurinta koranshi take ta hanya gayamishi abin daya sameta, acewar ta ko bata fada ba za,a fada mai"

Yauma kamar kullum nihilah ce tafe ta dawo daga gidan hajiya mariya tana kokarin shiga gida"

Wani zarkadeden saurayi taga yafito daga cikin mota dake tsaye agefe ya nufota"

Sauri ta kara tana dafda shiga gidan yayi mata sallama"

Tsayawa tayi ta kare masa kallo sannan tace lfy?

Murmushi yayi yana binda ta kallo yace ni sunana *Sultan jalaluddin* naganki tun kwanki da suka wuce, tunda Allah yasa naganki zuciyata ta kasa mancewa dake, duk dacewa naso hakan amma......

βœ‹πŸ»Dakata mlm nifah yar iska ce, har haihu fah nayi, yanzun kai sai kayi fatan hada iri dani?


Daure fuska yayi sannan yace"

Ki zubar da miyon bakin ki, dan nasan lbrn ki tsautsayi ne ya afka miki, kuma zan aure ki a haka"

Shiru nihilah tayi zuwa can ta murguda baki tace"

Nikuma wlh bazanyi aure ba, har sai ranan da nasan uban dan dana haifah









Mmn Yazeed
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 37 to 40*
β„β„πŸ’¦




Tafiya nihilah tayi zata fadi, daddy ya karasa da sauri ya tareta"

Yayin da anty da hajiya b suka tsare mutumin da ido"

Faruq ko tunda ya nuna mutumin da hannun haryanzon hannu na nan kame, gawani zufa dake karyo mishi"

Zuwa can nihilah ta sauke ajiyan zuciya tabude ido tana zazzare su"

Shima daddy ajiyan zuciya ya sauke sannan yace su koma falo"

Jiki asanyaye suka shiga ya rage daga mutumin sai faruq"

Cikin daure fuska faruq ya kalli mutumin yace"

Daga ina kake,? kaji tsoron Allah ka daina karya, me zakayi da yaron? Ina zaka kaishi? ninasan ba danka bane"

Gaban mutumin ne ya fadi, take wani tsoro ya shigeshi jiyaye kamar ya gudu, ace ba asan uban yaron ba, gashi wanna yaron yana nuna yana da tabbacin bani bane uban yaro, haka na nufin asirina zai tonu kenan"

Yana tsaka da wannan tunanin daddy ya leko yace ku shigo mana"

Jiki asanyaye suka shiga tare da zama kasa"

Gyaran murya daddy yayi sannan ya kalli mutumin yace yaya sunanka?

Jikin mutumin yarawa yake sosai cikin rawar baki yace"

Sunana aminu?

Aminu daddy yasake maimaitawa sannan yace"

Kace kaine mutumin da yayiwa yata nihilah fyade KO?

Eh kuma nayi nadaman abinda na aikata inajin tsoron haduwata da Allah dan haka nayanke hukuncin zuwa na baiyana kaina tare da neman gafaran yariyar dan nasan idan ba haka nayiba Allah bazai barni ba"

Girgiza kai daddy yayi tare da gaskata gaskiyan mutumin dahar ya kawo kanshi"

Waya daddy ya daga ya kira alhaji ibrahim ya fada mai halin da ake ciki"

Faruq ko hankalin shi tashe yake jira kawai yake yaga wanne shawara daddy zai yanke"

Nihilah nakwance ajikin anty sai kuka take, itama antyn kuka take tare da tunanin yanzun wannan shine baban sadiq, hajiya b ma kurrr tamai da ido tana karewa halittan shi kallo"


Anty gani tayi daddy ya kasa cewa komai saidai ya kalli mutumin ya girgiza kai dan haka ta mike taja hannun nihilah sukaiyi daki"

Shiko faruq kallon kaji tsoron Allah yakewa mutumin suna cikin haka suji anturo kofar falon da karfe"

Gaba daya falon suka mike cikin figici"

Umma ce, daka ganta zaka tabbatar afusace take, cikin gadara take takowa saida ta isa gaban mutumin taja ta tsaya hannunta ta daga ta sharara mishi kyawawan marika har 3 ajere daga hannun ta sakeyi zata kai na hudu alhaji ibrahim dake shigowa ya daka mata tsawa"

Da sauri ta sauke hannun Sanan ta koma gefe ta zauna tana huce"

Karasowa alhaji Ibrahim yayi sannan ya kale daddy yace kaikuma kana kallon ta?, meza a daka ajikin wannan, aisai akarashi, jifa inda yunwa tamai lahani"

Shiko mutumin ban dan zare ido babu abin da yakeyi neman hanyar godu kawai yake"

Alhaji ibrahim ne ya sauke sadiq sannan ya turashi gurin mutumin yana fadin maza jeka wajen baban ka"

Tsayawa cak yaron yayi yana kallon mutumin yana shirin yin kuka"

Alhaji ibrahim ne ya kallin mutumin sosai yace kaga besanka ba, tsoron kama yake ji, yanzun dan Allah meye amfanin rayuwa irin wannan, nadade innacin burin duk ranar da akasamu wanda yayi mata wannan wulakancin kotuce zata rabani dashi, amman ganinka haka yasa nakasa abin da nayi niya yanzun inason nasan da wacce kazo?

Ya bude baki zaiyi mgn faruq daya gama kulewa ya mike yana isa gaban shi ya rufeshi da duka tare da fadin daddy wanna mutumin makaryaci ne, wlh duk abinda yake fada karya ne, ku daina saura ranshi"


Kokarin janshi su daddy keyi amman sun kasa saboda yadda ya kwakume mutumin"

Da gudu anty da nihilah suka fito anty naganin abinda faruq keyi ta koma jikin banko dan dasan za,ai haka yaddda faruq ya shiga tashin hankali har yanzun be dawo daidai ba, tayi mamaki ma da tun dazon bece zai dakeshi ba"

Sai da alhji ibrahim ya zafga mai mari sannan ya sakeshi yana cigaba da fadin kudaina sauraran shi makaryaci ne wlh karya yakeyi, ba danshi bane, kuma besan komai game dashi ba, zaiyi amfani da wannnan daman ne kawai ya sace yaron"

Mgnr faruq ta shigesu kowa ya shiga cikin dogon nazari amman banda daddy burin daddy kawai abashi yaron ya tafi dan yakosa ya daina ganin mutumin"

Itako umma tasowa tayi ta dauke sadiq dake tsaye yana kuka tasakashi abaya ta goya sannan tace, zanga me karban sadiq aguri na, yadda kazo haka zaka koma ko danka ne ayanzun yafi karfin ka , dan wlh ko sama da kasa zata hade bazan bada sadiq ba"

Kallon ta alhaji Ibrahim yayi sannan yace zama Ki sakkoshi ne, gara ya taso ahannun uban shi duk lalacewa dai ubanshi ne"

Rasa abunyi faruq yayi kuka zaiyi, ihu zaiyi, ya gudune, ko ya tsaya ne, ya fadi gsky ne ko yayi shiru, Allah ka kawomin mafita indai na bari aka tafi da yaron nan banzan samu kwanciyar hankali ba, tunanine zaiyi ajalina bayan zinah dana aikata da kanwata wadda muka fito ciki daya mukasha nono daya harta samu ciki, idan nabari akada tafi da yaron aka salwantar dashi, nima dasa hannu na aciki, gara na fada dakaina su kasheni dan ko ban fada ba tunani ne zai kasheni"

Yana cikin wannan tunanin ya sake wani gigitaccen kara, hankalin kowa ya dawo gare gare shi"

Daddy cike da tsoro ya kalle faruk yace"

Kai meyasa k k daukan abu da zafi ahaka karka jawowa kanka wata matsala fah, haba wanne irin zafin zuciya ne dakai haka da bakajin lallashi"

Hawaye ne ya fara zobowa daga idonshi, wayarshi ya dauko acikin aljihun shi ya fara dannawa"

Ga duk alama typing yakeyi yana dannah wayar hawaye na diga akanta"

Tsayawa sukayi gaba daya suka maida hankalin su kanshi"

Shiko bakon Allah Allah yake yabar gidan dan ya fahimcin akwai abin da faruq yasani game da lamarin"

Alhaji ibrahim ne yace"

Faruq idan bazaka iya zama ba katashi ka bamu guri muyi mu tashi, Inna faruq besan yanayi ba, wayar kawai yake dannawa hawayenshi na dika akanta"

Daddy ma kiran sunnan shi ya shigayi faruq faruq, inna haryanzun besan anayi ba"

Juyawa daddy yayi ya kalli bashir yace"

Bashir daukomin wayar hannun faruq"

Mikewa bashir yayi ya nufi faruq har yaje gaban shi besani ba fizge wayar kawai yaji anyi, bashir be tsaya ba ya juya ya nufi daddy, yayin da faruq ya mike da sauri yana zare ido"

Bashir ya kusa isa gaban daddy jiyayi yanason sanin me faruq yake rubutawa kuma yana kuka Wa yake rutamawa,? tsintan kanshi yayi da daga wayar"

Atsorace ya fara karantawa dan ji yayi gabanshi na fadi"

_Usman na yanke hukuncin gayawa iyayenmu abinda ke tsanina da nihilah, nasan idan nafada kasheni zasuyi haka kuma idan nayi shiru tunani ne zai kasheni, dan nariga dana tafka babban kuskure arayuta tundaga ranan dana kusanci nihilah amatsayinta na kanwata, ban sake samun farin ciki ba, usman dan Allah kazo ka taimakeni bazan iya kallon idon iyayena na........_


Sakin wayar bashir yayi da sauri ta fadi kasa sannan ya juya ya kalli faruq ya nunashi da yatsa,"

πŸ‘‰πŸ» kai ne baban sadiq? Kare tambayan yayi da daura hannaye akaπŸ™†πŸΌβ€β™‚"

Duk mutanen dake falon mikewa sukayi suna kokarin tabbatar ma kunnen sun abun da bashir ya fada"

Tsakiyan falon faruq ya dawo ya daga hannu wanshi sama alamar na mika wuya, hawaye be dena zuba a idon shi ba,

Daddy rudewa yayi dan haka yana zuwa gaban bashir ya zafgamai Mari, tare da fadin wanan wanne irin mugun alkaba,i ne?

Kukan da faruq keyi yasa daddy ya maida kallon shi gareshi"

Ganin inda faruq ya daga hannun shi sama ga hawaye yana zuba kamar anbude fanfu yasa daddy ya dauki wayar ya fara karantawa"


Innalillahi wa inna ilaihir raju,un itace kalmar datafara fitowa daga bakin daddy, tari ya fara babu kyaukyautawa ganin haka kowa ya shiga zare ido yana neman karin bayani, banda bashir domin tuni yayi mutuwar tsaye"

Alhaji ibrahim ne yamatso ya karbi wayar faruq dake kokarin faduwa ahannun daddy ya fara karantawa besan cewa da karfi yake karatun ba saida yaji salatin dasu ahajiya b suke zafkawa da tsohowa inna hajiya da fitowanta kenan taci karo da wannan kazamin labari"

Tunda anty tayi salatin bata sake motsiba, haka ma uwar gayya nihilah"

Umma kuwa goyon sadiq ta sauke tayi jifa dashi sannan ta koma ta jingina da bango tana tsiyayan hawaye, hajiya b ce keta zagaye tana salati"

Inna hajiya ce kadai tayi jarimtam rufe faruq da duka, duk da cewa girma ya kamata"

Dagewa tayi tana dukanshi tana haki cikin kuka yarike hannun ta yace"

Inna hajiya kina ba kanki wahala ne dan Allah ki dauko wuka Ki cakamin a daidai nan, cikin shi yananu mata sannan yaci gaba dacewa"

Dan Allah kuyi sauri ku kasheni mutuwa ita ta dace dani"

Cikin tananin tari daddy yace faruq Allah ya tsenimaka albarka, bashir samomin itace me karfe"

Kitchen bashir ya nufa ya dauko wata doguwar tabarya yakawo ma daddy"

Inna hajiya ko ruwan sanyi ta debo ta shafawa anty da nihilah"

Azabure anty tamike ta nufi faruq tana fadin Allah ya isa tsakanina dakai bazanta ba yafe maka ba, duk wahalan da nayi dakai arayuwa har ka girma ban yafe maka ba, Allah ya tsine maka albarka"

Haryanzun umma na jikin bango tanajin inda anty da daddy suke tsenewa faruq albarka"

Daidai wannan lokacin daddy ya fara narkawa faruq tabaryan dake hannun shi, ya sake dagawa zai bagamai umma ta runtse idon ta"

Shima alhaji ibrahim runtse ido yake yana hawaye"

Shiko bakonka tuni ya sulale babu wadda yaga fitan shi"

Duka kawai daddy ke kaiwa faruq babu wadda yayi yinkurin hanawa"

Jijini ne ke zoba abakin shi tabaki ta hanci, jini har cikin idon shi, zuwa can daddy ya sake daga tabaryan ya rafka mishi ahannu jikake kassss, wani kara faruq ya saka me firgitarwa"

Dasauri umma ta bude ido ta sauke ahannun faruq dake reto dasauri tamaida idonta ta rufe"

Daddy be saurara mishi ba duka yakeyi yana karawa zuwa wannan lokaci faruq baya iya motsi saidai duk abinda ake yanaji"

Nihilah ce ta kwace daga hannun anty ta nufi faruq sai dai kafin dakai bashir ya riketa"

Daga tabaryan daddy yasake yi cikin sauri alhaji ibrahim ya rige tabaryan yana hawaye yake fadin kayi hakuri ka barshi haka"

Shima yana rike da tabaryan yake fadin alhaji wlh bazan bar faruq darai ba, kasheshi zanyi, meye amfanin haihuwan shi, d'ana ne fa, na cikina wlh bazan barshi da rai ba"

*FARUQ* ba dan cikin ka bane, d'ana ne"

Cikin matsanan cin mamaki daddy ya jefar da tabaryan sannan yace"

Dan ka?

Kwarai, faruq nine mahaifin shi"


Anty ce ta mike tana share zufa tace"

Danka? Kamar yaya, ban fa gane ba?










β„πŸ’¦Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 34 to 36*
β„β„πŸ’¦






β„πŸ’¦ Da saurin shi yace me zakimai?

Da kwarinta tace babban burina kawai naganshi namai Allah ya isa?

Murmushi yayi sannan yace, Aisha kenan ai Allah ya isa basai mutun yana kusa dakai ba , idan kayi ko a inna mutun yake zai same shi "

Nifa mlm ka rabu dani me kakason nacewa yaron idan ya girma ya tambaye ni baban shi"

Aisha ki nuna mishi ni amatsayin mahaifin shi, zan rikeshi kamar yadda ko wanne uba yake rike danshi, ni sonki nake tsakanina da Allah kuma kafin nazo nan saida naturo aka neman min izzini, amman daddyn ki yace na neme soyayya agurin ki"

Shiru yayi yana jiran yaji mezata ce, zuwa can dayaji bata da niyar mgn yace"

Aisha innajiran Ki fah kimin shiru"

Tsintan kanta tayi dajin nauyin shi tana wasa da hannunta take fadin aini nagaya maka dalilina, konayi aure hankalina bazai kwanta ba"

Shiru yayi yana kallon ta, zuwa can yace Aisha meyasa kk da taurin kaine?

Kasa cewa komai tayi sadai azuciyarta cewa take dan Allah ji Inda yake mgn kamar dan Iska yana namiji Amman yana kashe murya"

Sultan gajiya yayi da mgn dan haka ya mata sallahma ya tafi "

Tundaga ranan sultan yake kawo mata ziyara akai akwai tun bata kulashi harta fara kulashi"

Hira suke sosai amman dazaran ya Mata mgn aure saita hade fuska, dan haka yadaina mata zance"

Yauma kamar kulum, nihilah da sultan zaune suna hira, cikin nishadi"

Hira suke sosai yayin da sultan kebawa nihilah labaran ban dariya itako ta sake jiki sai kyalkyata dariya take yi"

Daidai lokacin faruq ya faka motar shi aharan gidan"

Zama yayi acikin motan ya kuresu da ido, wani irin haushi yaji ya kama shi, saida ya tsaya ya saita kanshi sannan ya fito"


KO kallon inda suke beyi ba ya shige ciki"

Itama nihilah tsayawa tayi tana mamakin yanzun yaya ya daina son ta"

Tundaga lokacin jikin nihilah yayi sanyi har sultan ya lura da haka"

Cikin ido ya kalleta yace lfy kuwa?

Lfy lau, bari na shiga gida sai yaushe kanan?


Au korata kk saboda kinga yayanki yazo?

A,a kwai kaina ne naji yanamin ciwo"

Jinta kawai sultan yayi badan ya yadda da abinda tace ba"

Da haka sukayi sallama cikin sauri ta nufi gida, yayin da sultan yabita da ido"

Faruq zaune agaban anty sai faman korafi yake yana fadin"

Haka kawai bakusan mutun ba kubar shi yana zowa, ni wlh banaso kwashe kwashe"

Murmushi anty tayi sannan tace"

Yaro sultan dinne kwashe2 mumfasan iyayen shi kuma gidan su akwai tarbiya, bezo gurin nihilah ba saida ya fara turo iyayen shi suka neman mai izzini agurin daddy Ku"

Kara daure fuska yayi yace"

Toh yazun dai daddy ya bashi ita kenan?

Eh ya bashi indai sun daidaita da nihila, kuma itama nafahimci ta amince dashi"

Shiru yayi zuwa can ya dago yace"

Anty yanzun dai gidan nan ancire dokar auren zumuncin kenan?

Tsintan kanta tayi da ce masa eh dan ya fara bata haushi"

Shiru yayi zuwa can ya sake cewa Anty toh inna alkarin da aka min cewa ni zan zaba mata miji"

Kaje ka tambayi uban ka, haka kawai zakazo ka tasani gaba kanamin tabayar kaka uwarka ta haife ka, toh waima tsaya me kake nufi, kana nufin kartai aure taita zama agida, mezata maka?, ai indai kai me kyaunar nihilah ne kamata yayi kamata fatan alheri"

Cikin kosawa yace nayi shiru Anty"

Nihilah ce ta shigo da yar dariyar ta, zama tayi kusa dashi tace yaya ai Ina kallon shigowan ka, kuma kaima ka ganni amman ka wuce abin ka"

Daure fuska yayi sannan yace sauri nake lokacin, nina ma manta anty naziya ce fa ta aikoni gurin ki"

Lfy anty ta fada yayin da nihilah ta daure fuska"

Cewa tayi wai ki bata kuka"

Kuka.?" yau kuma agarin, yaryar da ko na zoba mata cikin laida take dawo min dashi, mikewa tayi cikin sauri ta nufi kitchen"

Itako nihilah tuni idonta suka kada zuwa ja, sukuyar da kanta tayi dan batason ya gane halin da take ciki"

Zuwa can anty ta dawo dauke da kukan miya ta mikawa faruq"

Karba yayi ya mike sannan ya kalle nihilah yace"

Nihilah kozaki dan kada mana?

Sai alokacin ta dago jajayen idonta ta watsamai sannan tace bata da hannu ne?

Da sauri anty ta zaro ido, shiru tayi tanason jin me faruq za ice"

Ga mamakinta saitaji yace yi hakuri nihilah bata da lfy ne"

Mikewa tayi tana fadin aini ma ba lfyr nake dashi ba"

Anty ce tace ke yaushe kika zama fitsararriya haka, yayanki ne fah"

Toh anty aidama shine zaici sainamai amman ni inaruwa da matar shi yar aikinta ce ni?

Sakin fabaki anty tayi yayin da faruq ke murmushi yana bin nihilah da kallo"

Itako anty tsoro ne ya kamata idan har ba kuskuren fahimta tayi ba, yaran nan nihilah da yaro kishin junan su ke"

Mikewa anty tayi ta karbi kukan ta nufi kitchen zuciyarta cike da tunani barkatai"

Cikin kan kanin lokaci ta gama, bayan tafiyan faruq ne anty taitama nihila fada akan sabo rashin kunyan da nihilah takewa faruq"

Da daddare anty da daddy ne zaune cikin dakin baccin shi dan yau itace da girki, tattaunawa suke zuwa can anty tayi shiru har daddy ya kula da ita yace yaya dai"

Numfashi ta sauke sannan tace"

Alhaji wani abu ne yake dauremin kai, nayi2 nakyauda abin azuciyata amman nakasa"

Cike da kulawa yace minene shi?

Alhaji *Yaro da nihilah* kamar kishin junan su suke"

Ban gane kishin juna ba, daddy ya fada yana yamutsa fuska"

Alhaji nihilah kishi take da naziya sosai, kaduba fah kusa shekara 3 da auran Yaro amman nihilah bata taba zuwa gidan shiba, kuma ko gidan nan tazo bata mgn da ita, haka shima Yaro dazaran yaga wani yazo gurin nihilah ya dinga fada kenan"

Daure fuska daddy yayi sosai sannan yace"

Mekike nufi da wannan mgnr taki babu dadin ji, kina hauka ne? Da ace wanine yamin wannan tambayan bake ba da sai namai uzuri, amman keda bakin ki kike furta irin wadan nan kalaman, aikin ku kenan mata bakwa gajiya da gutsiri tsoma"

Kallon shi anty yi sannan tace alhaji nifa bawani abu nace ba"

Hararanta yayi sannan yace nakula kedai idan bagani kk yi nihila tayi aure ba hankalin ki bazai kwanta ba, dan haka zanwa me neman aurenta mgn ya turo"

β„β„πŸ’¦


Faruq ne zaune gaban naziya ya tasa mata towo agaba"

Kiyi sauri kici mana karyayi sanyi"

Turo baki tayi tana fadin nifah banaci miyar kawai zanshi"

Da zafinshi yace ke karfa ki maidani bawanki baki isaba wlh, sai kinci tuwon nan aike kikace zakici"

Tana shere hawaye take fadin toh ai nace nakoshi zansha miyar"

Mikewa faruq yayi sannan ya dauke miyar yana fadin wlh bazaki shaba"

Kuka take sosai dan cikine ta sameshi me tsurfan tsiya amman faruq baya raga mata ko yayi kamar zai tausaya mata saikuma ya hau Fada"


Daddy ko tun ranan yayiwa iyayen sultan mgn dan haka batare da wani bata lokaciba suka kawo sadaki"

Tunda nihilah ta fahimci sadakinta aka kawo hankalin ta ya Kara tashi"

Anty ta samu adaki cikin kuka take cewa"

Anty nafa gaya muku bazanyi aure ba sainaga baban sadiq, wlh anty idan banga baban sadiq ba rayuwata bazatai dadi ba"

Nihila kifah daina rantsuwa dan aure nan bi,izinin lahi sai anyi shi babu fashi"

Mikewa tayi sannan ta ruga dagudu ta shige dakinta"

Gado ta fada sannan ta dauko wayarta ta shiga kiran sultan"

Bugu daya ya dauka kaman dama jiranta yake"

Kuka

Please Login or Register in order to submit comment