Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tare da hajiya mariya suka tafi, hajiya b taso ta bisu amman akace ta zauna da anty"

Cikin tsananin tausayi hajiya b take kallon anty hakika ta tausaya mata, haka kawai yariya daga zuwa makaranta adawo da ita an mata fyade, bema tsaya afyaden kadai ba harda tsaraba"

Tabe baki tayi sannan ta juya ta kalli anty tace"

Kinga wannan abun da kikeyi zai iya kawo miki illah, gara kiyi kukanki yafi miki"

Sai alokacin anty ta sauke wani nannauyan ajiyan zuciya, alokacin taji wani kuka yazo mata cikin kukan take fadin"

Nakasa kukan ne hajiya, wlh inason nayi amman yaki zuwa"

Daidai lokacin daddy ya shigo faruq da bashir suna binshi abaya"

Da dariyar su , suka doshi falon saidai tun kafin su karasa suka farajin kukan anty"

Da sauri suka karasa, har suna rige2"

Daddy ne ya tsaya ya kare musu kallo sannan yace"

Meya faru?

Shuru hajiya tayi domin ta rasa ta ina zata fara mai bayani"

Muryan anty tajuyo tana cewa"

Alhaji nashiga uku na lalace, Allah ka dauke raina na huta da wannan takaici, duniya tamin zafi alhaji ina cikin bakin cikin da bansan ranar yayewan shi ba"

Cikin dakewa da nuna jarumta daddy yace"

Dakata, meyayi zafi haka?

Tana kukan take fadin alhaji nihilah ciki gareta"

Gabayan su hada baki sukayi wajen fadin ciki?

Take faruq ya fadi ya suma, yayin da anty tayo kanshi tana kuka"

Shiko daddy banda kiran sunayen Allah babu abinda yake"

Bashir ma hannuwan shi ya zuba aka tare da fadin kashπŸ™†πŸΌπŸ˜¬"

Arude hajiya b ta dauko ruwa ta fara shafamai afuska"

Ajiyan zuciya ya sauke, sannan ya fara bin mutanen falon da kallo"

Cikin murya meban tausayi yace"

Anty dan Allah kiyafe min, daddy kaima ka yafemin, kai ni kowa ma ya yafe min"

Sai alokacin hawayen da daddy yake makalewa suka zobo, matsawa yayi gaban faruq ya dafa kafadar shi sannan yace"

Faruq kayi hakuri ka tashi, ni babu abinda kayimin, kuma inason ka yadda da kandara mekyau da mara kyau"

Daddy mutuwa zanyi nasan bazan rayu ba, rayuwata ta riga ta kare"

Share hawaye daddy yayi sannan yace"

Kai tashi maza bana son wannan sambatun naka"

Da tai makon bashir faruq ya zauna amman har yanzun fadi yake"

Kai kai nashiga uku"

Suna cikin haka su umma suka dawo"

Faruq dukar da kanshi yayi dan gani yake kamar yanzun nihilah zata iya shaida shi"

Bayan sun zauna falon kowa yayi shiru yayin da daddy ya kurawa nihilah ido"

Umma da hajiya Mariya ko daka kalli idon su, zakasan sunci kuka sun koshi"

Zawacan umma ta fara ma daddy bayanin an tabbatar musu nihilah nada cikin sati. 4 karashe maganar tayi cikin kuka"

gyaran murya daddy yayi sannan yace"

Bakomai Bilkisu zan dauki wannan kaddaran dan bani da yadda zanyi, Allah yasa haka shine mafi alheri"

Girgiza kai umma ta fara tare da fasa wani sabon kuka tana fadin"

Wlh alhji wannan ba alheri bane Sam, cikin da aka sameshi bata hanyar Aure ba , ina zai zama alheri?

Toh Bilkisu ya zanyi?

Dasauri tace alhaji azufdashi kawai"

Sam daddy ya fada da sauri sannan ya kara da cewa ko mutuwa nayi ban yadda azubda cikin ba"

Cikin sauri faruq yace"

Daddy dan Allah dan darajan annabi azubda cikin nan wlh ina bakin cikin nihilah ta haihu batare da tayi aure daddy kafin naga ranar zan kashe kaina"





*Kuyi hakuri da wannan*







β„πŸ’¦Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 28 to 30*
β„β„πŸ’¦






β„πŸ’¦ Da sauri nihilah ta juyo ta kalleshi azuciyarta take fadin lallai bakaramin sonta yake ba dan ko ita da abin yake jikin bata kawo tunaninta kashe kanta ba"

Duk falon kallon shi suke lokaci daya ya zama kamar wani zararre, zuwa can daddy yace,

Faruq kana nufin bazaka yadda da kandara ba kenan har kake ikirarin zaka kashe kanka, toh bari na tuna maka duk wadda ya kashe kansa ya mutu kafiri, sannan idan ka kashe kanka nikaina bazan yafe maka ba, bare kuma mahaifiyar ka datasha matukar wahala kafin ta same ka"

Ganin inda faruq ya futuntuke yana kuka yasa daddy fadin"

Kamashi ka kaishi daki, ka kara mai nasiha dan naga idon shi ya rufe"

Bayan tashin su faruq daddy ya kalli su umma ya kakalo murmushin karfi da yaji yace"

Toh me kuke jira inace kun hadune zaku kai akwati"

Eh alhaji amman ai yanzun babu zance kai akwati dan gsky zuciyar mu babu dadi, cewar hajiya mariya"

Cikin rarrashi yace a,a karkuyi haka, tunda kun sanar musu gara kuje ku kai"

Haka suka tashi badan ransu yaso ba fuska babu fara,a su tafi gidan su naziya"

Tare da anty sukabar nihila, anty tasowa tayi daga inda take ta dawo kusa da nihilah, cikin sanyi jiki ta jawota jikinta murya adakushe tace"

Nihilah dan Allah karki tayar da hankalin ki, kinga yazun da da ba daya bane, yanzun da kisa damuwa komai na iya faruwa, nihilah banason narasa daya da cikin ku, idan kika kwantar da hankalin ki shima Yaro zai kwantar da nashi, kinga hankalin shi ya tashi sosai"

Wani guntun hawaye ne ya zobo mata, tasa hannunta ta share, sannan tace"

Anty yaya faruq fah aure zaiyi, ya tafi ya barni, nikuma wai ciki gareni , karashi mgnr tayi cikin kuka"

Itama Anty tana kuka tace"

Nihilah kema ai auren zakiyi dazaran Allah ya rabaku zakiyi aure da yaddan Allah"

Anty waye zai aureni, ai duk wadda yazo aure na aka gayamai na haihu bazai aureni ba"

Share fuska anty tayi sannan tace tashi muje muyi sallah lokaci yayi"


β„β„πŸ’¦

Tun daga ranar gidan ya zama kamar gidan mutuwa kowa zuciya babu dadi"

Lbr ya gama karade dangi cewa nihilah tana da ciki, sai awannan lokacin inna hajiya ta samu lbrn fyaden da akawa nihilah dan da boye mata sukayi, bakin ciki taji ba kadan ba, dan haka ta tattaro kayanta ta taho gidan domin ta kula da jikarta"

Dadi sosai daddy yaji dan ya dade yana son ta dawo gidan amman taki"

Tunda nihilah taga inna hajiya ta manne mata, kulum suna tare"

Shiko faruq ya zama kaman mara lfy kulum cikin tunani yake, bashir ne keta shirye2 shima jikinshi babu kwari dan wadda ya keyi sabo dashi baya karfafa mishi gwaiwa"

Gidan su naziya ko shirye2 suke sosai gashi yau bikin saura kwana biyu"

Naziya ce zaune cikin kawayenta, hira sukeyi amman bata sanin me suke cewa, hankalinta ya tafi gurin tunanin faruq, tare da fadi azuciyarta anya kuwa yana so na?

Kallon fatarta tayi sannan tace"

Meye makusa ajikina, kodan yana ganin shi fari ne sol nikuma baka, hakika gidan su faruq babu baki, daka manyan su har yaran su, kuma kyawawa ne saidai wani yafi wani bama kamar wannan shegiyar yariyan nihilah, duk ta fiso kyau ga shegen iyayin tsiya"

Tunanin da naziya keyi kenan, kare tunanin tayi da fadin, toh ai nima koda nake baka ai ina da kyau"

Tashi tayi tacigaba harkokinta kamar yadda kowacce amarya keyi"

Anna gobe daurin aure bashir yazo ya kawo mata duk wani abu da zata bukata sai dai lokacin da yake kokarin tafiya yaga kamar tana share hawaye dan haka yaja ya tsaya"

Ido ya zuba mata sannan yace naziya lfy kuwa"

Wani hawayen ne ya sake zobo mata
sannan tace"

Tunfah da aka fara mgr auren nan kwata2 sau 2 Faruq yazo"

Shiru bashir yayi dan yasan za,ai haka, cikin rarrashi yace"

Toh kiyi hakuri keda zuwa gobe ya zama naki, shima yana son zuwa bashi da lfy ne, ki kara hakuri komai zai wuce"

Daha bashir ya lallashi naziya, harta dan saki jikinta"

Washegari da misalin karfe 2:30pm aka daura auren faruq da naziya"

Kowani ango ranar auren shi zakaga fuskan shi dauke da murmushi amman banda ta faruq domin fuskarshi daure take daka kalle fuskarshi zakaga kamar zai fashe da kuka"

Nihilah ko duk da tana cikin matsala taji bakin cikin auren naziya da yayanta yayi, tana jin yan daura auren sun dawo ta shige daki ta fasa kuka"

Dadaddare bashir ne yazo daukan faruq domin ya rakashi gurin amarya, saida faruq ya gama bata mai lokaci sannan ya mike"

Dakin anty suka shiga domin mata sallama, ahankali suka tura kofar tare da sallama"

Anty dake kokarin shiga toilet ta amsa sannan ta shige ciki"

Nihilah na zaune akasa ta tasa danbun zogale saici take"

Tafiya faruq yayi har gabanta ya zauna tare da mika hannun sa cikin danbum"

Tunkafin hannun Sa yakai cikin kwanon ta dauke sannan ta mike da sauri ta nufi dakin ta"

Baki faruq ya sake, tare dabin bayanta da kallo"

Anty ce ta fito tana fadin me kuke jira har yanzun baku tafi ba"

Da sauri faruq ya dukar da kanshi kasa, bashir ne yace anty aike muke jira, Ki mana addu,a"

Kunya ce ta kama anty daker tace toh ai dama kullum muna addu,a Allah yasa azauna lfy, kuje dare nayi"

Bayan sun fito falo faruq yace ina zuwa bari naga nihilah"

Mota bashir ya shiga ya zauna yayin da Faruq
ya nufi dakin nihilah

Yana tura kofar yaga nihilah kwace jikin inna hajiya tana fashafa gashin kanta"

Kujeran dake gefe ya nufah yayin da inna hajiya ke fadin, a,a wannan wani irin suko ango ne har yanzun baka tafi wajan amaryan ba?

Fuskar shi daure yace bakya kishi kenan harma kosawa kk yi na tafi?

Wanne kishi zanyi miji ba cefane"

Au haka kk ce
, ni Yan zun bani da lokacin ki, yanzun dai tashi ki bamu guri zamuyi sirri da kanwata"

Kafin hajiya ta bude baki nihilah ta riketa sosai tare da fadin babu inda zata jeka kawai"

Shiru faruq yayi yana kallonta fuskarshi cike da damuwa cikin sanyin jiki yace"

Jiba nihilah taso mana kinga bashir yana jirana"

Rufe ido tayi kamar me bacci"

Faruq ya kasa tafiya jiyake kamar ya hadiye zuciya wai yau shi nihila takewa gaddama , betaba tunanin haka ba arayuwan shi"

Juyawa yayi yakalli hajiya da tajuyar da kanta kamar bata kallon su yace ,

Inna hajiya kicewa yariyar nan ta tashi inason zanyi mgn da ita "

Kai! kai faruq kaima da dan banzan naci kake saika ce kuturo, cewar inna hajiya sannan ta kara da cewa tace kaje abinka natabajin irin wannan naci?

Wani haushi ne ya kamashi da sauri ya juya zai fita, harya kai kofa yaji muryan nihilah tace ka gaidata"

Bece komai ba ya fita abinshi"


β„β„β„β„πŸ’¦



Tundaga ranan faruq ya kara tsunduma cikin kogin tunani, amarya naziya ko bata samun kulawa daga wajen faruq, tun da ta tare agidan kullum sai dai yace beda lfy, tayi2 ta shawo kanshi amman ta kasa"

Gado daya suke kwana amman babu wani abu daya taba shiga tsakanin su, duk da cewa naziya tana shige mashi sosai tare da wanka najan hankali, amman ko yayi kamar zai biye mata sai kuma yaja dogon tsaki"

Abin ya dame ta matuka dan haka ta gayawa bashir"

Lokacin da bashir yayiwa faruq mgn fada ya fara kwata2 ya hana bashir mgn"

Bashir be sake cewa komai ba yaja bakin shi yayi shiru"

Koda faruq ya koma gida rufe naziya da fada yayi cikin fushi yake fadin kinkai karana wajan bashir, bashir din uba nane?

Shiru tayimai harya gama sannan ta bashi hakuri"

Tunda ranan ta rage shige mai ahaka har suka kwashe tsayon Wata 8, zuwa wannan lokacin naziya ta fara fahimtan cikin da nihilah keda shi ne yake damun shi dan soda yawa idan yana bacci yakan tashi azabure yana kiran sunan nihilah"

Ita kanta yariyar ta na bata tausayi dan cikin wani irin girma yayi naban mamaki"

Sai dai abinda yake bata mamaki ta kula nihilah dataga faruq take tashi ta shige daki sabanin da dasuke balakin shiri sosai"

Yau faruq gaba daya ya kasa tashi saboda wani azabeben ciwon kai dake damun shi"

Naziya nason tambayan shi ko beda lfy ne amman tanajin tsron fada dan haka yake mata data fara mgn be ma bari ta karasa yake rufeta da fada"

Kwatsam Bashir ya fado gidan, ganin halin daya yake ciki yace ya tashi suje asibiti"

Amman kememe yaki zuwa"

Bashir yasake cewa karfa hawanji ya maka illah"

Aigara yamin illah kaini inda ma zan mutu da nafi so "

Cikin fada bashir yace toh wai kai kafi kowa son nihilah ne?, toh nidai naga kowa ya hakura yabar ma Allah Ikon shi amman banda kai, duk kabi ka takura rayuwar ka duk ka rame ka lalace, haba faruq yaushi yabon ka dakayi aski , wlh ko nihilah da cikin ke jikinta bata irin wannan abun da kake"

Shiru faruq yayi kamar yana bacci dan haka bashir ya mike yana fadin wlh nina gaji ko mutuwa kayi ma ni bazanyi kuka ba, tunda baka daukan shawara"

Damisalin karfe 11:00pm faruq yana kwance yaji kaman muryan nihilah tana ihu tana kiran sunan shi"

Azabure yamike jallabiyan shi ya zura ko takalmi babu yayi waje"






β„πŸ’¦ Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 31 to 33*
β„β„πŸ’¦




Tashin motar faruq ne ya tada nadiya daga bacci" da gudu ta nufi window gani tayi har ya riga ya fita dan haka ta dawo bakin gado ta zauna tare da daura ta gumi"

Shi ko faruq gidan daddy ya nufa da isan shi ya fito daga cikin motar cikin sauri ya shiga cikin gidan"

Ya kusa isa kofar anty ya farajin kukan jariri"

Gaban shine yayi mummunan bugawa ahankali yake tafiya harya tura kofar"

Dagowa sukayi suna kallon shi, cikin mamaki Anty tace"

Kaifa daga innah,?

Hajiya b ma cewa tayi wanne gwanin ne ya fada maka"

Shide bece komai ba illah rarraba ido daya ke yana kallon kowa"

Zuwa can idon shi ya sauka akan jaririn dake hannun inna hajiya tana fadin tubarkallah yaro saikace faruq yayi kaki ya tufar"

Cikin sauri ya karasa hannu ya mikawa inna hajiya ta saka mishi yaron, sannan ya zuba mishi ido, kai yaro kyakyawa ne sai dai banyi murna da zuwan ka ba, naso ace ta hanyan aure aka same ka, abin da faruq ke fada azuciyar shi kenan"

Kallon yaron kawai yake yana hawaye , zuwa can aka fito da nihilah daga wanka, mikawa anty yaron yayi amman saitaki karban yaron dan haka ya mikawa hajiya b"

Gaban nihila yaje ya zauna sannan yace"

Sannu nihilah ya jiki?

Bata amsa ba illah cigaba da tayi da kuka"

Kara matsawa yayi kusa da ita ya kwantar da murya anhanli yace"

Nihilah dan Allah kiyi hakuri kimin mgn, haba nihilah kiji tausayi na mana, ni nasan ni babban me laifine awajen ki, inna rokon ki dan Allah kiyi hakuri kiyafe min, kalleni nihilah hankali na yaki kwanciya rabon daji farin ciki nadade nihila kullum jinake kamar na kashe kaina, dan Allah nihilah kiyafe min"

Bakaramin tausayi mgnr faruq tabawa nihila ba, dan haka ta mika hannun ta ta rike nashi"

Ajiyan zuciya ya sauke sannan yace na gode nihilah, ido yabita dashi gani yayi kamar tana shirin kuka, dan girgizata yayi kadan sannan yace"

Menene?

Yaya inason naga baban wancen yaron ne?

Me zaki mishi? Ya fada yana goge zufah"

Yaya danshi zan bashi sannan namai Allah ya isa"

Shiru yayi ya shiga kogin tunani anya kuwa bazai fadi gaskiya ba a mishi hukuncin daya dace dashi ai da kunyan lahira garata duniya, tashin hankalin ne ya sake dawo mai sabo , dan haka ya tashi ya koma falo kwana yayi babu bacci takaici kawai yake da danasani"

β„πŸ’¦

Washegar yana kidar da sallah ya nufi gidan usman"

Usman najin muryan shi yaji gabanshi ya fadi da sauri ya tashi ya zauna

Ganin inda faruq ya tara uban gemu duk yayi baki ya rame yasashi fadin"

Menene haka faruq kowa idan yayi aure yanayin kyau amman kai ka koma kamar wani zautatce"

Aini da haukan ce ma ta sameni zaifin sauki akan abun da ya same ni"

Gyara zama usman yayi yace"

Meya faru?

Hmmm usman nihilah ta haihu jiya da dadd are"

😳nihilah? daman tayi aure ne?

Hmmm karkace min ka manta abinda ya faru tsakanin mu"

Jikin usman rawa ya fara sannan yace"

Faruq ashe baka da hankali, tayaya zaka bari harta haihu, meyasa maka gayamin ba?

Hawaye ne suka zobowa faruq masu dumi sannan ya ce daddy mu yace"

Idan aka zubar be yafe ba"

Sunayen Allah usman ya fara kira zuwa can yace"

Faruq wannan abun ya bani tsoro sosai, kuma faruq kace kana da tabbacin uwa daya uba daya kuke kaida nihilah"

Cikin takaici faruq yace wai tantama kakeyi?

Abunne yake bani mamaki faruq, indai ko haka ne, insha Allahu banzan kara shan giya ba, bare kuma har na nemi mace, lokaci yayi dazanyi aure dan gujewa mummunan kaddara irin taka, gaskiya kana cikin wani hali"

Cikin kuka faruq yace"

Ni babu abinda ya ke damuna kamar wancen yaro, duk da cewa yaron ya shiga raina amman inaji tamkar na kasheshi sai dai jna tsoron karna kara laife akan laife"

Shiru usman yayi domin babu wata kalma data rage mishi"

Sai kusan karfe 1 faruq ya koma gida, yanashi yaga naziya na kokarin fita , dasauri ya kauce sannan yace"

Gidan ubanwa zaki?

Wasa ta fara da hannunta tare da sunkuyar da kanta kasa sannan tace"

Daman naga tundare ban ganka bane kuma nakira wayar ka nagansu gida shine nakira bashir yace....... Shiru tayi takasa karasawa saboda yadda ya tsareta da ido"

Cikin tuhuma yace OK bashir ne yabaki izzinin fita"

Ton jeki tunda bashir ne ke auran ki".

Shiru kawai tayi zuwa can tace kayi hakuri, shima bacewa yayi......

Wata muguwar tsawa ya buga mata wadda ta sakata zabura da gudu ta fita"

Ajiyan zuciya kawai faruq ke saukewa, kujera ya nufa ya kwanta"

Itako naziya gidan su faruq ta nufa arude"

Afalo ta same su duk suna zaune ganin inda ta shigo arude anty tace"

Ke lfyr ki ? daga ina kike haka?

Zama tayi akasa arude ta shiga gaida su, kowa ya amsa amman umma saicin magani take

Anty tana son ta tambayi naziya me yake damun ta amman tanajin kunyan su umma, dan haka ta baza kunne taji ko zasu mata kara wajen tambayan naziya amman saitaga umma ta daure fuska"

Tashi anty tayi ta shige daki sannan ta kira wayar naziya"

Naziya naganin kiran anty ta mike ta nufi dakin"

Tana shiga tafara kokarin zama akasa cikin sauri anty ta bude mata hannu alamar tazo jikinta"

Cikin kunya ta mike ta nufeta"

Ajiki Anty ta mannata sannan tace menene ya faru?

Kuka naziya ta fara sai da tayi me isarta sannan anty ta ajiye ajiyan zuciya tace"

*Yaro* ne ko?

Cikin kuka ta daga kai"

Dasauri anty ta mika hannunta tana share mata hawaye take fadin"

Toh ya isa, ki daina kuka ki gaya min abin da ya miki?

Cikin kuka tafara fadawa anty irin zaman da sukeyi"

Sosai ran anty ya baci ahankali tace"

Toh kiyi hakuri zan mishi fada, duk da nasan kinyi hakuri amman ki kara akan wadda kika yi, bakomai ke damun yaro ba sai halin da kanwarsa take ciki, duk yabi ya takura rayuwar shi"

Lallashinta anty ta cigaba dayi har hankalinta ya kwanta"

Sai dare anty takira shi awaya bayan ta gama tsiyaya mai fada tace yazo ya dauki matar shi su tafi"


Bayan kwana bakwai da haihuwan nihilah daddy yazo ya samo anty yana tambayan ta wani suna ya kamata akira yaron dashi?

Shiru ta mishi domin inda yasan abinda takeji idan aka mata mgn dan nihila da be mata ba"

Hajiya b ce tace akirashi da *Sadiq* alhaji ibrahim ne ya kawo katon rago aka yanka amman nihilah kwata2 takicin naman, yaron ma sai antsaya akan ta take bashi nono dan haka umma tace abarta kar akara takura mata"

Lokacin da umma ta tashi tafiya zani ta ciro acikin jakarta ta goya sadiq tana fadin toni natafi zan tsaya ahanya nasayan mai madara"

Sakin baki

Please Login or Register in order to submit comment