Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasannin da nake miki, amman meyasa da kika zama mallakin zaki fara kokarin gujemin meye nufin Ki?

Shiru tayi kanta akasa harsai da ya kara maimaita tambayan shi sannan ta dan ruko hannun shi tana wasa dashi tare da fadin "

Yaya nifah wlh tsoro nakeji

Cikin ido ya kalleta sanan yace tsoron me?

Sunkuyar da ido tayi sannan tace"

Yaya cewa fah kawar khadi tayi wai saiya kaimin har makogaro"

Da mamaki ya kalleta sannan yace menene zaikai makogaro kuma?

Shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa"

Shima shiru yayi yana nazari zuwa can ya kwashe da dariya saida yayi me isarsa sannan ya kalleta"

Hawaye ya gani a idon ta dan haka ya jawota jikin shi ya rungume sannan yace"

Dama kina zama ana irin wannan hiran dake?

A,a nifah bana yi jinsu kawai nayi suna hiran"

Toh ke kuma dagaji anyi hira saiki hau ki zauna, ai irin wannan jarabawa zakiyi dan ki tabbatar"

Ceff nikam wlh bazan jaraba ba, tsoro nakeji"

Shiru ya sake yi zuwa can yace"

Nihilah ki kwantar da hankalin ki, karya sukeyi ba gaskiya suka fada miki ba, daman sun fahimci ke matsuraciya ce shi yasa suka fadin miki haka, yanzun kitashi kije kiyi alwala kizo muyi sallah"

Mikewa tayi sumi2 dan ta fahimci yau faruq bazai barta ba"

Faruq naganin fitowan nihilah ya mike ya shiga toilet din shima vejima ba ya fito"

Sallah sukayi raka,a 2 kamar yadda musulun ci ya tanadar, bayan sun ida ya mike ya nufi falon naziya"

Samun naziya yayi zaune ta rafka uban tagume har yaje gabanta bata sani ba"

Hannusa yasa ya zame mata tagumin zamura tayi ta dago tana kallon shi"

Ahankali yace naziya me kikeyi har yanzun bakije kin kwanta ba?

Hawaye ne ya zabo mata sanna tace"

Na kasa baccin ne tun dazun nake juyi agado baccin yaki zuwa, kuma kirji na wani irin zafi yake min"

Toh fah naziya duk meya kawo haka?, kodai dan yau ankawo miki amarya yasa ki jin haka"

Shiru tayi tana share hawaye"

Lallashinta yayi sosai sannan ya dauketa cekk ya kaita har kan gadonta sannan ya dawo ya dauki ledar da usman ya aje masa ya nufi dakin nihilah"

Gani yayi harta haye gado"

Bakin gadon yaje ya zauna sannan ya dago tare da fadin sakko kici abinci"

Kin sakkowa tayi haka faruq yaita naci har ya gaji ya Bari"

Tausayi nihilah ta bashi sosai saidai bazai iya daga Mata kafa ba, dan abin da yakeji idan ba sauke shi yayi ba bazaita samun natsuwa ba"

Kwanciya tayi shiko faruq mikewa yayi ya cire kayan dake jikin sa sannan ya haye gadon ya jawo nihilah jikin shi"

Nihilah tunda taji dumin abu ajikinta ta Fara fadi"

Innalillahi yau nashiga uku"

Bakin tq ya rufe da nashi ahankali ya dinga sarrafata tare da kara gigicewa"

Hawaye ne ke zubowa adon nihilah acikin zuciyarta take tunanin wai ita nihilah yayanta faruq yakewa irin wannan abubuwan, yaya faruq da nake ganin uwa daya uba 1 muke shine yau ya sarrafani son ransa, wata zuciyar ce tace kece kike Ganin abun sabo amman shi ba sabon abu bane awajen shi"

Shiko faruq yayi nisa gashi tunda ya kama bakin nihilah yaki saki, nihilah ko duk abin da yake tana kallon shi, tsoro ne ya Kara kamata dan ganin faruq tayi kamar ankara masa girma gaba daya kirjinshi ya rufeta, jin inda faruq ke nurfarfashi yasani kada bujena nayi waje "

Ban sake komawa ba sai washegari da misalin karfe 10:30am atunanina duk jarabar faruq yanzun yabar nihilah, amman saina same shi rungume ta ita kuma har yanzun bakin shi na cikin nata, da alma dai sunyi wanka dan har sun canja kaya kuma dakin ma gyare yake tsaff yana zuba kamshi"

Naso na juya amman wata zuciyar tace ki tsaya kiga abinda ya turewa buzu nadi"πŸ˜‰

Ina kallo ya fara tura hannu cikin rigarta"

Cikin sauri nihila ta tare hannu tare da zare bakin ta daga cikin nashi"

Kallonta ya tsayayi sanan yace menene haka?

Nan danan hawaye ya zubu mata cikin kuka tace"

Waikai baka gajiya ne?, tun dare fa kake abu daya wlh nagaji jikina fa duk yayi tsami"

Murmushi yayi sannan yace"

Yi hakuri ki bari nadan kara ko so daya"

Cikin kuka tamike zaune tana cewa haka fa kaketa cewa tun jiya ni wlh na gaji"

Fuskarshi dauke murmushi yace"

OK toh shikenan na hakura"

Komawa tayi ta zauna sannan ta zuba uban tagumi"

Kallonta yayi yace toh meye kuma?

Sunkuyar da kanta tayi kasa sannan tace"

Nifa yunwa nakeji wlh cikina kama babu hanji"

Dan murmushi yayi kadan tare da mikewa tsaye yana fadin niko ko wuni zamuyi adaki indai tare dake ne bazanji yinwa ba"

Bejira me zata ce ba ya nufi falon naziya"

Samunta yayi zaune akasa tana cin abinci, cinyanta ko nihilah ce sai cilcillah kafa sama take"

Hannu ya mike ya dauki yariyar sannan ya zauna agefen naziya"

Gaisheshi tayi ya amsa tare da lakace mata hanci yana fadin jibeki kamar ba kece jiya kike kukan kishi ba"

Kauda idonta tayi sannan tace ya amarya ta kwana

Lfy lau take"

Shiru sukayi zuwa can yace"

Naziya kanwar ki fa najin yunwa baki shirya mata abin karyawa bane?

Kalon shi tayi akarka ce sannan tace"

Aidai kasan jego nake"

Bangane jego kike ba?, wannan abincin dake gabanki waye ya dafa miki ?

Ni na dafa amman daidai cikina na dafa idan kuma zakaci ne kasa hannu"

Azuciye faruq ya mike sannan yace OK Nihilan ce bazaki ba abincin ba kenan?, to nima bana ci, bazanci ba....









Mmn Yazeed
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 75 to 78*
β„β„πŸ’¦



Cikin zafi ya nufi part din nihilah har yana huci dauke da nihilah karama"


Bayan shi tabi da kallo sannan ta mike ta shiga kitchen, zuwa can ta fito da kulolin abinci ta nufi part din nihilah"

Shiko faruq yana shiga dakin ya sakarwa nihilah murmushi, ahankali ya isa gabanta ya daura mata yariyar akan cinyarta yana fadin"

Amshi takwarar ki, be kalli fuskan nihilah ba dan haka besan wanne irin roko ta mata ba, ya fara nannade hannun rigar shi yana fadin"

Me kike son kici naje na dafah miki?

Jinta shiru yasa shi dagowa ya kalleta, zaro ido yayi ganin 'yar sa na shirin faduwa"

Karasawa yayi ya dauketa sannan yace"

Menene kuma haka...

Bata bari ya rufe baki ba tace"

Yaya kai wai meyasa har yanzun baka san halina bane? Nifa bana son yara kwata2"

Cikin mamaki faruq ke kallonta saida ya gama kare mata kallo sannan yace"

Nihilah wannan yariyar fah 'yata ce nina haifeta, idan ma bazaki sota sabota mahaifiyarta ba toh dan Allah ki sota danni"

Kauda idonta tayi sannan tace nifa bawani abu bane kawai yara ne bana son su gaba daya"

Shiru yayi zuwa can yace har jinina?

Eh ta fada kanta tsaye"

Girgiza kai yayi tare da fadin Toh shikenan ba komai, yanzun me zakici na dafa miki?

Daidai lokacin naziya ta fara buga kofar ahankali"

Faruq ne ya nufi kofar da sauri, dan yasan babu me zuwa wannan lokacin idan ba naziya ba"


Yana bude kofar ya ganta tsaye da kayan abinci ahannuta, ido ya zuba mata sannan yace"

Yaya aka yi?

Kasa tayi dakai sannan tace daman abincin ne, na kawo"

Ok daman rainin wayo ne ya hanaki kawowa tuntuni?, toh bari kiji nagaya miki bazan dauki iskanci ba, daga gidan ubanki kika taho da abincin dahar zaki hana nihilah abinci? duk neman kudin da nake dan ita nakeyi itace farin cikina, bani da wani buri daya wuce na faranta mata rai, dan haka kijuya da kayanki bazataci ba"

Sai a lukacin naziya ta dago ido ta kalleshi wani kululun bakin cikine ya taso mata, bata taba jin haushin faruq irin nayau ba, cikin matsanan cin kuka ta saki kolulin kasa tanufi part dinta aguje"

Faruq bayanta yabi da kallo saida yaga kulewarta sannan yaja tsaki ya koma daki"

Naziya kuwa gado ta fada ta saki kuka me ban tausayi saida ta kwashe kusan awa daya acikin wannan halin, jin kiran sallan azahar yasata mikewa, mikewa toilet ta shiga zuwa can ta fito ta sanya hijjabi ta tada sallah"

Bayan ta idah zama tayi nan kan sallayan tana addu'oi zuwa can ta sake fashewa da kuka"

mgnr faruq ke mata yawo akai daya ke tambayanta daga gidan ubanta ta taho da acin dahar zata hana nihilah? Sai yanzun takejin matsanancin zafin sunan nihilah daya sa wa 'yarta tare da ganin soyayyar da yake nunawa yariyar bata Allah bace dan dai yasa mata sunan masoyiyar shi nihilah ne"

Mikewa tayi tsaye tana cije lebe hakaki da ace tana da yadda zatayi bazata sake cin abincin gidan faruq fah"

Bakin gadon ta koma ta zauna, zuwa can ta sake zabura ta mike tare da fadin gsky gidan mu zantafi"

Gyale ta yafa hartakai kofah taja ta tsaya tunani ta tsayayi anya kuwa mlm zai barni na zauna karfa naje ya koro ni, shiru tayi zuwa can ta koma bakin gado ta zauna"

Wayarta ta dauka ta fara neman no mahaifiyarta"

Bugu biyu aka dauka kuka naziya ta sake me ban tausayi, saida ta kwashe kusan minti 5 tanayi mama batace mata komai ba"

Zuwacan mama tace Naziya kukan ya isa haka, ki natsu Ki gayamin menene ya faru?

Cikin matsanancin kuka ta fara fadawa mama irin bakaken maganganun da faruq ya fada mata"

Runtse ido mama tayi, hakika ta tausayawa 'yar ta, ahankali tace"

Naziya faruq be kyauta ba, amman kema be kamata ace kin dafa abincin ba kuma ki kasa zuba mata"

Cikin shashshekar kuka tace mama wlh nasan Halin yariyar ne bata da kunya kuma nasan bazataci abincin dana dafah ba"

Shiru mama tayi zuwa can tace naziya inason kisan wani abu guda 1 abin da hakuri be baka ba rashin hakuri bazai baka ba, karki bari kishi ya rufe miki ido, kin san idan namiji yayi sabon aure dole saikin kyauda ido dan rawar kafa zaki gani iri iri, kiyi hakuri wata rana sai lbr"

Kuka naziya ta cigaba dayi zuwa can tace mama toh kicewa baba yasaimin kayan abinci"

Hmmm naziya yaushe kika canza hali daga me hakuri zuwa mara hakuri kibar wannan mgnr shima faruq din yayi mgnr ne cikin fushi idan bakici abincin gidanshi ba nagidan wa zaki ci?, naziya kodai kawaye ne ke zuga ki?

Ahankali tace a,a


Toh natsu sosai kiji abin da zan gaya mike, karki yadda ki beyewa zugar kawaye su kaiki subaro, idan kika yadda wata tajaki gidan malamai Allah ya isa ban yafe miki ba, duk irin bacin ran da kikaji dauko Qur'ani kiranta ina me tabbatar miki zakiji sanyi azuciyar ki"

Hawaye naziya ta sake sharewa sannan tace mama nifa yar shishigi ce arayuwar su dan faruq dan nihilah kadai aka aka haliceshi"

Kash😬 naziya ya kike mgn saikace ba musulma ba, tabas nima shaida ce faruq na matukar son nihilah, haka itama nihilan, amman Allah daya sakaki a tsakiyan su shi yasan abin da yake nufi, inason kiyi hakuri kicinye wannan jarabawan, kuma ai daman rayuwa abinda kakeso ba lallai ne kasameshi ba, Allah yasa haka shine mafi alheri"

Dahaka sukayi sallama da mama, ajiyan zuciya taita saukewa dan gaskiya nasihar da mama ta mata ya kwantar mata da hankali"

Tafiya ta fara ji, da sauri ta mike dan ta tabbatar faruq ne, toilet tashige tare da murda key"

Koda faruq ya shigo bega naziya ba, zama yayi bakin gado yana jiran fitowanta"

Wasa yaitawa nihilah harya gaji da zama ya fara kwalawa naziya kira, amman taki amsawa"

Tunawa yayi da abinda ya faru tsakanin su dazon dan haka yamike ya kwantar da nihilah akangado sannan ya fara tafiya yana fadin"

Idan kingama iskancin naki ki fito ki dauketa, idan kuma har kikabarmin yariya ta fado wlh saikin raina kanki"

Sai da naziya ta tabbatar ya tafi sannan ta fito, kallon nihilah tayi sannan taja tsaki, hakika tana bakin cukin sunan da asawa nihilah, kuma idan har faruq yana son yaga fara,a ta to saidai ya canja mata suna😳

*****


Tun daga ranan faruq be sakebi takan naziya ba, haka itama ta dauke mai wuta, faruq ko part dinta be kallo"

Ya sake jiki da nihila sosai tana daga part dinta takejin guje gujen su tare da dararraku, sai dai ta kure mgnr tv dan ma kartaji bare ranta ya baci"

Ahaka har suka share sati 2

Wanda yayi dai dai da kwanan naziya 45 da haihuwa, tanason zuwa gida amman tana bakin cikin bin faruq ta neme iznin fita"


Ahaka suka kara samun sati biyu, naziya duk tayi baki ta rame yayin da nihilah tayi wani irin kiba tare da fari naban mamaki"

Kuma yau din ni nihilah tasawa faruq kuka saiya kaita gurin anty dan haka yace tabari saida daddare"

Haka kuwa dare nayi suka kama hanya, gidansu umma faruq ya taida motarsa sannan ya sakko ya dauki nihilah cek yayi ciki da ita"

Saida yakai kofar da zata sadashi da babban falon gidan sannan ya sauketa"

Hannun shi ya sagala cikin nata sannan suka shiga tare da sallama"

Umma ce kadai afalon tunda ta daga kai ta kallesu ta maida kai"

Faruq ne ya fara gaidata cikin girmamawa sannan nihilah,

Gaba daya amsa musu tayi ba yabo ba fallasa"

Shiru falon yayi zuwa can faruq yayi ta maza yace"

Umma baki tambayi kishiyar ki ba"

Dagowa tayi ta wurgamai wani kallo dayasa shi dole yayi kasa da ido, amman shifa so yake umma ta sake dashi dan haka ya sake daga ido yakali umman yace"

Umma toh ko dai kishi ne ya hanaki tambayan ta ?









β„πŸ’¦Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 79 to 82*
β„β„πŸ’¦





β„πŸ’¦ Kai dan uban ka yaushe muka fara yar haka dakai?, tun da nake nataba wasa dakai ne?, ko angaya maka ni Sa,ar wasan kace?, maza tashi kaja matarka ku barmin gida"

Faruq be motsaba yana nan yadda yake ahankali yace"

Kai umma daga tambaya sai fada, naga idan naje gurin anty tana tambayan naziya da nihilah harda aisha, ke kuma naga ko aishar ma baki tambaya ba"

Kallon mamaki umma take wa faruq lallai yaga gadon baccin ta, cikin fada tace"

Kaidai wlh bakaji dadin halin ka ba, mutun banda rashin kunya babu abin daya sa agaba, tun wuri ka kiyayeni idan ba hakaba kuwa wlh zanci mutuncin ka"

Jikin faruq sanyi yayi amman duk da cewa fada umma ta mishi yaji dadin hakan dan tunda yake arayuwa betaba mgn da umma me tsayin nayau ba, jikinshi asanyaye yace"

Toh umma dan Allah kiyi hakuri zanyi kokari nagyara halina, mikewa yayi tare da kallon nihilah yana fadin tashi muje"

Hawaye yaga tana sharewa"

Hannu ya mika zai dagata, waigawa yayi yaga umma ta kafe nihilah da ido dan haka ya janye hannun sannan ya juya yana fadin kisame ni amota"

Saida umma ta tabbatar faruq ya fita sannan ta mike ta karaso gurin nihilah"

Dafata tayi sannan tace Aisha me ya faru kike kuka, ya miki wani abu ne kafin ku shigo?, ko yana takura miki ne?

Share hawayen nihilah tayi sannan tace"

Umma ai kece duk kin canza min, yanzun kin daina sona kuma umma har yanzun bakizo gidan yaya ba"

Hmmm Aisha kenan kice dai har yanzun banzo gidan ku ba, kuma ni ai bakiso naxo gidan ku ba, tunda kika auri wannan fitsararren yayan naki"

Wasa nihila ta shiga yi da hannun ta tare da fadin toh umma awar ware auren indai baza ki ringa zuwa ba"

Hmmm Nihilah kenan kuyi zaman ku bayan gashi nan naga kinyi kiba, hankalin ki ya kwanta kina tare da yayan ki"

Hannu tasa ta rufe idonta hakan yasa umma ta dan murmusa tare da fadin inna kika baro takwararki?

Wani haushi taji ya taso mata daker ta daure tace tana gida"

Da haka sukayi sallama da umma ta fito bayan sun dau hanya faruq yake tambayan ta kukan me take dazun"

Cikin kisisina take fada mishi dalilin kukanta har yadda sukayi da umma"

Dariya faruq yayi sosai sannan yace wato umma nine bata son naga fara,ar ta"


*****



Suna isa gidan daddy part din hajiya babba suka nufah bayan sun gaisa suka nufi gurin inna hajiya barkewa sukayi da hira tsakanin faruq da inna hajiya dan haka nihila ta barshi ta wuce gurin anty"

Bakaramin dadin anty taji ba ganin nihilah ta murje kamar alatsa jini ya fito"

Kwance tayi ajikin anty tana zuba mata lbr"

Zuwa can faruq ya shigo fuskarshi dauke da murmushi, zama yayi yana gaida anty"

Amsawa tayi cikin sakin fuska san tace"

Meya hana baku toho da naziya ba??


Gaban shine ya fadi dan haka ya rasa wanne irin amsa zai bata, tsintan kanshi yayi da fadin anty ai jego take inace sai anyi arba,in ake fita?

Cikin matsanan cin furgice anty tace"

Yaro? Kana da hankali kuwa? arba'in din har guda nawa zatayi? , yaro anya kuwa awannan auren babu zallinci aciki?, yanzun kana nufin bakamasan tayi arba'in ba?


Shiru yayi sannan ya kasa cewa komai sai faman sosakai yake"

Nihilah ma jin anfara wannan mgnr ta takure aguri daya zucigarta cike da bacin rai"

Kallon shi anty tayi sannan tace kwana nawa nawa kakeyi.....

Tun kanta rufe baki yace 3 3"

Hmmm yaro kenan bansan ka da karya ba ka fadamin gsky kawai"


Kara shafo keyar shi yayi sannan yace"

Anty daman ni jira nake tayi Ar......


Hannu anty ta daga maiβœ‹πŸ» tare da fadin, wato kaidai mahaukaci ne baka da hankali, wannne irin rashi hankali ne wannan ina ka tabajin anyi haka?, toh bazai yiyu ba, yau basai gobe ba ka koma dakin naziya, kuma gobe ka daukota da wuri ka kawo min ita, idan ka wuce karfe 9 baka kawota ba zanzo dakaina"

Kunya ce sosai ta kama faruq dan haka ya mike tare da fadin bama sai kinzo ba zan kawota"

Juyawa yayi ya kalli nihilah sannan yace ke tashi mutafi"

Wuce kawai gobe idan ka kawo naziya sai ka wuce dasu a tare"

Juyawa yayi ya kalli anty sannan yace anty goben basai nakawo su tare ba"

A,a ka wuce kawai....

Bejira ta rufe baki ba ya wuce da sauri"

Nihilah ko mikewa tayi da sauri ta haye gadon anty ba tafiyan faruq ke bata haushi ba kadaicewa faruq da naziya shine babban bakin cikinta"

Faruq ya dade be wuce ba yana jiran ko anty zataji tausayin shi ta turo mishi nihilah, saida ya gaji da jira tukun ya wuce"

Damisalin 10:48pm faruq ya isa gida, part din naziya ya nufa ya tura kofar, jikin shi asanyaye ya shiga dan shima sai yanzun yake ganin abin da yayi be dace ba"

Babu kowa falon dan haka ya nufa dakin ta dai dai lokacin da naziya ke fitowa daga toilet, tana ganin shi ta hada giran sama data kasa"

Zama yayi yai shiru itama gadon ta haye tajawo bargo ta rufah"

Ahankali faruq ya miki hannun shi ya jawo bargon tare da fadin"

Ke me kike nufi da har zaki ganni ki kasa gaisheni?

Cikin halin ko in kulah tace au ashe mutun ne, ni ji nake ma inuwata ce"

Cikin ido ya kalleta dan yasan ta fadi haka ne dan ta bashi haushi, dan haka yace"

Ashe kinyi arba'in shine baki gayamin ba, nikuma ashe na bace a lissafi"


Waya ce maka nayi arba'in?, ai nima alissafi na banyi arba'in ba"

Shiru yayi yana kallonta tare da fadi azuciyar shi toh fah

ita fah naziyar nan idan tayi fushi bata da sauki, yanzun ta ina zan fara ne?


Tafin kafarta ya kama yana shafawa ahankali tare da fadin Allah ya huci zuciyar ki, nayi laifi dan Allah ki gafarce ni"

Rufe ido tayi, yaita mgn yaji shiru dan haka ya mike ya shiga toilet din dake dakinta"

Naziya dake kwance idonta rufe ta farajin karan ruwa, hakan ya tabbatar mata da cewa wanka ya keyi"

Kudundu newa ta sakeyi tare da kara jawo 'yar ta jikinta"

Zuwa can faruq ya fito daure da towel akugun shi,

Please Login or Register in order to submit comment