Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta saka da karfi sultan tsayawa yayi yan sauraron zuwa can yace menene abun kuka kuma?

Tana kuka take gayamai dalilin ta nakin aure ayanzun"

Wani gutun murmushi yayi sannan yace"

Har yanzun mgn Allah ya isan tana nanne bata wuce ba?, nace miki kimishi kodaga nan ma zai same shi aduk inda yake, kuma nima ina tayaki dan kullum nayi sallah sainayi addu,an Allah ya saka miki"

Kukanta tacigaba dayi tare da fadin nidai nagaya maka gaskiya kuma wlh idan har akamin aure ahaka bazakaji dadin zama dani ba"

Dan zare ido sultan yayi sannan yace Ok toh naji zantaya ki addu,an Allah ya baiyana miki shi"

Dahaka, sukayi sallama"


bayan sati 1

Nihilah ce zaune agaban umma sai kuka take"

Yayin da umma ke rungume da ita tana bubuga mata baya"

Zuwa can umma ta dago nihilah sannan tace nihilah tashi ki koma gida gobe zanzo nasamu daddyn naku muyi mgn kuma karki sake cewa wai ke bakison aure, kinji ko?

Tana share hawaye tamike ta gyara lullubin ta tayi waje"

Nihila na kokarin shiga layinsu taga motar sultan ta gilmata da sauri, mamaki abin ya bata, yaya sultan zai wuceta haka ? Toh ko beganeni bane, da wannan tunanin taci gaba da tafiya, saidai tanashi harabar gidan taga motar faruq"

Daga cen gefe kuma wani mutumi ne fari tas rigarshi duk ta yayyage babu takalmi akafarshi ya rufa dawani farin yadi, zabura nihilah tayi takoma baya arude dan gani take kamar itakadai ce take ganinshi, saida takai gurin megadi tukuna ta tsaya tace"

Baba wancen wanene?

Bakon ki ne, gurinki yazo tun dazon keyake jira"

Dafa kirji tayi tare da fadin ni? gurina? Cike da karfin gwaiwa ta koma dafda mutumin sannan tace"

Mlm lfy?


Eh toh lfy amman balau ba, wani babbab kuskure na aikata yanzun kuma nayi nadama dan haka na dawo na neme gafara, Aisha nine mutumin dana miki fyade shekara uku dasuka wuce kuma nasamu lbrn kin samu ciki harkin haihu , yau gani agaban ki kimin hukunci daidai da laifina amman inna rokoki idan zakuyi hukucin ku duba halinda nake ciki na kangin talauci ku tausaya min dan nasamu na rayu da dana"

Tuni network din nihilah ya dauke yau Allah ya tona asirinsa ya kawo kanshi da kafafuwan shi, jiri taji yana dibanta dan haka ta kwallara kara"

Gaba daya mutanen dake falon suka fito ciki harda faruq"

Nihilah nuna mutumin take tana fadi gashinan shine, baban sadiq ne, ku bashi danshi banason nasake ganin wannan mummunan fuskar agabana"


Baban sadiq ? Faruq ya fada yana me zare ido









0701419755
CommentπŸ‘†πŸ»
Banda cewa na turo daga farko dan nariga nayi nisa, wadan da sukamin mgn pc cewa na tura musu farko suyi hakuri bazan iya bin mutane 1 da 1ina tura musu ba idan ko akace hakane toh lallai typig din ma zai gagara da fatan zakumun uzuri 😍😍😍












β„πŸ’¦ Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 48 to 50*
β„β„πŸ’¦



*_Ina mika godeyata ga dubin masoya masu bibiyar novels nawa kowani lokaci, akoda yaushe sakunan ku yana zuwa gareni, kuma Ina tsinta kaina cikin farinciki aduk lukacin danaga sakon wani masoyina, ina muku fatan alheri kamar yadda kuke min😘_* *ALLAH KA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA*πŸ™πŸ»



FATAN ALHERI

Ummu abdulnasir
Mmn kharat
Maryam shattima
Sadiya Rabiu Rano
Queen ajeebo
Hadiza duguwa
Husaina faji
Falhat
Rashidat
Mmn saif
Mom mubeena
Hauwa
Hannatu Adam
Hafsat Yusuf
*Da sauran su*





Ke bana son mgnr banza, yanzun ke duk wannan abin daya faru baki tsorata ba, nihar yanzun wlh atsora ce nake, idan kk kureni zan zame hannu na acikin al,amarin ku kamar yadda umman ku tayi"

Turo baki nihilah tayi sannan tace"

Toh kizo muje tare aikema bakije ba"

Bazani ba tashi maza kishirya idan kuma niman abokin tafiya kk ki dauki Sadiq"

Mikewa nihilah tayi ranta abace, daki ta koma ta ceza kaya sannan ta dauki babban hijjabi ta zunbula, ta nufi dakin anty"

Kallo anty tabita dashi tana mamakin dan tasan nihila ba gwanar sa hijjabi bace idan ka ganta da hijjabi kuwa toh tsakanin 2 ko sallah ko islamiyya"

Ahankali tace natafi"

Toh nihilah adawo lfy sadiq din fah"

Ni gsky bazani dashi ba"

Harara anty ta bita dashi tare da fadin kedai kk sani"


Hartayi nisa da tafiya ta fara tunanin kodai ta biyya gidan su shamsiyya ne tace ta rakata"

Dasauri tayi kwana tana zuwa kofar gidan sukaci karo da shamsiyya"

Mamaki ne yaka mata ganin nihilah agidan su danta dade rabon ta da gidan"

Cikin wasa da dariya suke tattaunawa irin na kawayen dasuka dade basu hadu ba zuwa can nihilah tace"

Nifa zuwa nayi kirakani gidan yaya faruq"

Tafff nima fah yanzun gidan yaya na nake tunda umma tayi tafiya yanzun ma karya na mata cewa zandau wasu kayana"

Nidai kizo muje yanzun nan zamu dawo bazama zamuyi ba". ❌

Shiru shamsiya tayi zuwa can tace muje amman idan muka dawo zaki rakani gida ❌

Eh naji muje"


Cikin kankanin lokaci suka isa gidan faruq, suna zuwa kofar gidan gaban nihilah ya fara faduwa, jin muryan shamaiya tayi tana cewa Allah yasa matar yayan ki ba yar Iska bace kalan matar yayan na"

Wani kallo nihilah ta watsa mata sannan tace"

Caffff nizatawa iskanci Allah ya kiyaye wlh, aini ba irinki bace, dazan zauna matar wa ta gasani, bari muje ki gani"

Lokacin da suke kokarin shiga falon nihilah ta kama hannun shamsiya sannan tace"

Karka kice zaki gaidata kisa ta rainani"

Kafin shamsiya bude baki nihilah ta tura kofar"

Atsorace naziya ta fito daga kitchen tana raba ido taga waye ya fado musu gida haka"

Ginin nihilah ce saida gabanta ya fadi, duk suna tsaye kan shamsiya akasa yayin da nihilah ke kallon sama tana girgiza jiki"

Kakalo murmushi naziya tayi sannan tace, a nihilah ce toh ku zauna mana"

Bazama nazo ba nihilah ta fada tana ciga da girgiza jikinta"

Ok toh ki shiga yana ciki"

Takawa nihila tayi ta nufi hanyar da naziya ta nuna mata tana fadin aini bama saikince na shiga ba, bukata ta kawai nasan dakin daya ke, nibana son shishshigi, karashe mgnr tayi da cewa, shamsiya taso muje"

Bude baki naziya tayi tace"

A,a nihilah kishiga ke daya man......

Bata saurari naziya ba ja hannun shamsiya tayi suka shige"

Duk abin da suke faruq najin su, dariya yayi sosai dan shi kome nihilah tayi burgeshi take, jan bargo yayi ya rufe jikin Sa"

Shiga sukayi tare da sallama, sannan shamsiya ta gaisheshi tare damai yajiki, nihilah ko gefe ta koma ta kasa cewa uffam"

Kallon ta faruq yake yana murmushi, jibeta kamar ba ita ta gama rashin kunya yanzun ba, afali kowa cewa yayi nihilah sarkin hankali, bazaki gaisheni bane?

Ya jiki ? ta fada tana kauda ido"


Kin amsawa yayi zuwa can yace kuje fallo ganinan zuwa"

Juyawa suka yayin da faruq ya bi nihilah da kallo tafiyanta ma burgeshi yake, yaso ace ita kadai tazo dan yanason suyi mgn"

Mirginawa yayi tashi sannan ya kwalawa naziya Kira"

Shigowa tayi da sauri, faruq ya kura mata ido tare da dan sakar mata murmushi, sannan yace"

Daukomin riga mara nauyi"

Jallabiya ta dauko me gajeren hannu ta dawo gabanshi ta tsaya idonta akan rigar tace"

Ina zaka?, baba fah yace ka daina yawan motsaya hannun ka"

Kura mata ido yayi sannan yace"

Bawani guri zani ba, iyakata falo"

Toh tace sannan tayi dage ta ziramai rigar a wuyan shi"

Bayan ta gama daidaita mishi rigar, yace sannu naziya amman dai kin gama aikin ko?

Jikinta asanyaye tace"

Nadai kusa"

Kallon cikinta yayi yace"

Gaskiya kibar aikin nan haka, kidinka zama kina hutawa"

Murmushi kawai tayi dan taga yau wani kulawa yake son ya bata wanda ada baya bata"

Ahankali tace toh kadaiyi sauri kar nihilah tayi fushi"

Roko hannunta ya yayi suka fito sai dai yana turo kofar da zata sada su da falo, ya janye hannun shi daga na naziya"

Kujeran dake kallon tasu nihilah ya zauna tare da fadin nihilah inna anty na fah?

Idonta akasa tace"

Tana gida tace agaishe ka"

Inna amsawa, sadiq fah meyasa baki taho dashi ba?

Anty ce bata matsamin sai na taho dashi ba"

Da sauri ya kalleta sai dai idonta akasa yake, ahankali yace,

Kina nufin sai anmatsa miki zaki taho dashi?

Eh dan da ba,amatsa min ba yanzun ma bazaka ganni ba"

Wani haushi ne ya kama faruq dan haka ya daure fuska tare da fadin "

Toh tashi ki tafi dan babu lada.....

Begama rufe baki ba taja hannun shamsiya ta karfin tsiya "


Kallo kawai ya bita dashi cike da takaici, suna fita yaja tsaki"

Naziya daga kitchen ta jiyo tsakin shi, azuciyar ta tace"

Kasan bakason ta tafi meyesa ka koreta, tsaki taja itama batare da tasan lokacin fitowan shi ba"

Afusace Faruq yamike cikin fada yake fadin"

Dan ubanki wa kikewa tsaki"

Da sauri naziya ta tonshe bakin ta tare da fadin"

Wlh ba dakai nake ba niban masan nayi ba"

Dallah rufemin baki munafuka kawai ni zakiyiwa rainin wayo"

Take ran naziya ya bacci daman cike take fam dan haka ta fashe da kuka"

Jin sautin kukan naziya hankalin faruq ya tashi sosai"

Shiru yayi yana kallonta zuwa can ya matsa murya kasa2 yace"

Naziya yi hakuri ki tashi raina ne ya baci"

Banza tayi dashi babu abinda yafi bata mata rai irin ubanta daya zaga"

Zuwa can ta tashi fuuuu ta wuce shi"

Bayanta yabi da kallo afili yace"

Toh fah, kema haka kike da fushi"

Dakin shi ya koma ya kwanta tare da jin haushin kanshi"

Nihilah ko gidan umma ta wuce bayan ta raka naziya gidan yayanta"

Tun aharabar gidan taga motar daddyn ta dan haka ta wuce falon alhaji ibrahim kai tsaye"

Sallama tayi ta shiga, alhaji ibrahim ne tare da daddy ka dai afalon"

Bayan ta gaidasu alhaji ibrahim yace daga inna kike?

Naje gidan yaya faruq ne"

Yayi kyau cewar daddy"

Alhaji ibrahim ne yace"

Yanzun Iyayen sultan suka tafi, munkira sune mun basu hakuri"

Tambaya nihilah takeson yi hakurin me aka basu amman ta rasa taya zatayi tambayan"

Shiru tayi zuwa can tace"

daddy wani abu aka musu?

Murmushi alhaji ibrahim sannan yace"

Mun musu laifi mana tun da mun aurer dake ga faruq bayan mun musu alkawari"

Azabure nihilah ta mike tare da fashewa da kuka, tana fadin wlh daddy bana son shi, baba dan Allah ku warware auren , wlh bazan iya zama dashi ba, idan kuka tilasta ni auren yaya wlh bakin ciki ne zai kasheni"

Alhaji ibrahim ne ya mike ya taho gaban nihilah, yayin da daddy ya mike ya dauko takalmin sa ya nufita gadan2

Duk da cewa alhaji ibrahim yana kare nihilah amman saida daddy ya mammaka mata takalmin"

Kukan nihilah ne ya tada umma dake bacci"

Arude tayo waje daidai lokacin da bashir ya fito shima arude"

Kusan lokaci daya suka shiga falon umma na fadi wake uhu haka?

Ganin nihila da sauri umma tajuya zata fita, daidai lokacin da faruq yace"

Me tayi ?

Har umma tasa kafarta daya awaje taji daddy na fadi"

Wlh idan kika sake bude baki kk ce bakison faruq sai na kusa kashe ki"

Da sauri umma ta dawo da kafarta baya tare da fadin au dan tace bata son shi ake jibgar ta saikace wata jaka?

Duk juyawa sukayi suna kallon ta"

Hakane ya bata damar wucesu ta daga nihilah ta nufi kofar tana fadin"


Kin min daidai wlh duk wannan wulakacin daya miki, ba,a dauki wani kwakwaran mataki ba sai adauki yariya nan danan abashi, sai kace yar kaza, duk wula kancin daya mata ba,a gani ba"

Tana kaiwa nan ta fita afalon rike da nihilah"

Dakinta ta aje nihilah sannan taci gama da rarrashin ta, nihilah kiyi shiru ki daina kuka, aure dai babu dole, koda aka riga aka daura za,a iya warware shi wlh da kin amince dashi nayi alkawarin ko kallon Ki bazan sake yi ba tayaya zaki yadda da auren wadda ya lalata miki rayuwa"

Duk mgr da umma take bashir na tsayen bakin kofa yana jinta"

Zuwa umma taji muryan shi yana cewa"

Kai umma memakon Ki bata hakuri kuma sai kina zugata, itama dai wlh yariyar nan muna fukace"

Kai fita kabani guri"

Gyada kai kawai bashir yayi sannan ya fice,"

Yana komawa daki ya kira faruq a waya, bayan ya dauka bashir yace"

Ga nihilah fan ta hau buri"

Daga can cikin wayar faruq yace"

Wanne irin buri kuma?

Wlh ba wasa ba tanan dakin umma tana kuka wai ita batason ka"

Batasona? nihilar ta bude baki dakanta tace bata sona ?, dan Allah da gske KO wasa?

Daga gaske mana, ni umma ce ma tabani mamaki ta sata adaki sai kara zugata take"

Take gaban faruq ya fadi, besan lokacin daya furta bashir wai me nayiwa umma? tun fa da nafara rashin lfyn nan kowa yazo ya gaisheni amman umma ko aike gaisuwan ta bana samu, ada abin baya damu na, amman yanzun gaskiya ya dame ni, kiri2 taki daukan sadiq tabarwa anty kulum cikin kuka yake"

Shima bashir jiyayi babu dadi ahankali yace"

Umma nada zafi sosai har tsoro nake wani abu ya hadani da ita, amman ni shawaran da zan baka kasan yadda zakayi nihilah ta koma gida ayau, dan wlh indai ta zauna agidan nan auren sai ya mutu"

Bayan sungama wayar hankalin faruq yayi mummunan tashi, ji yake kamar bashi da kowa sai nihilah, shikenan na zama Mara gata, bani da wadda zankaiwa kukana, kira ya Fara kwalawa naziya, tanajin shi amman taki fitowa sabo da har yanzun fushi take"

Faruq yasan naziya na jin shi dan kirane yake mata bana wasa ba"

Zuciya ce ta debeshi ya tashi azabure batare daya tuna akwai karaya ahannun shi ba"

Zamewa yayi ya fadi timm tare da sakin wani gigitatcen kara










β„πŸ’¦Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 57 to 60*
β„β„πŸ’¦


GAISUWA DA FATAN ALHERI GAπŸ‘‡πŸ»RE KU

Suraiya
Hauwa
Salma Musa
Hadiza Tunau
Ummusulaim
Maryam Adam
Husaina Faji
Maryam tata
Zainab kid
Hannatu Adam
Mmn arfat
Hafsat Yusuf
Sa,adat
Mmn Teemah
Mmn abdulnasir
Mariya aliyu
Yahancy
Shemaprtty
Mmn imam
Deejarh
Meemie lubu



β„πŸ’¦ Zafi taji hannun nayi saboda nihilah ta riketa da karfi"

Juyawa tayi ahankali ta kalli faruq"

Shiko yi yayi kamar besan tanayi ba, jan nihilah yake duk da cewa tana tirjewa, har yayi nasaran mannata da jikin shi"

Itako nihilah fadi take umma kin ganshi ko?

Wani kallo umma ke watsa mishi wadda ada yake sakashi shakkan ta, ko ayanzun ma daurewa kawai yayi ya dauke idonshi amman gabanshi sai faduwa yake yi"

Nihilah bata daina kiran umma ba, furuq kuma be saketa ba dan so yake yau yaba umma kunya"

Muryan umma yaji cikin fada tace"

Kai sake ta?

Dagowa yayi ya kalli umma sannan yace"

Umma zan dan ganta ne, mint.....

Bekai ga karasawa ba nihila ta fincike hannuta da karfi wanda yayi sanadin faduwanta kasa"

Dasauri ya mika hannun shi ya rike kafarta daidai lokacin da ta mike tana kokarin guduwa"

Jitayi zata fadi dan haka ta fada kanshi"

Faruq najin nihilah jikinshi ya lumshe ido sanna yasa hannu ya zagaye ta"

Wani uban tsaki umma tayi sannan taja jiki ta fita da sauri har tana hada hanya"


Faruq najin fita umma yasaki ajiyan zuciya sannan ya kara kankame nihilah har saida ta tsorata"

Ajiyan zuciya yaita saukewa zuwa can ya fara sunbatan ta kamar zai cinyeta"

Tsoro abin ya fara bata dan haka tayi saurin tare kansa da hannayenta duk 2 ta kureshi da ido sannan tace"

Haba yaya menene haka ?

Nihilah nayi missing dinki ne sosai yaushe rabona dana taba jikin ki, hannun shi yakai ya zame dan kwalinta sannan ya tura hannu cikin gashinta yana fadin haryanzun dai kinanan da halin ki bakison kitso"

Hannunta ta mika ta zaro nashi daga cikin gashinta sannan ta kafe shi da ido tace"

Yaya ? , wai meye haka?

Kwace hannun yayi sannan ya tura cikin rigarta yana wasa da duk abin da yasoπŸ™ˆ"

Nihila jitayi jinta ya fara mutuwa wani irin abu takeji wanda ta dade bataji ba"

Kukun shagwaba ta fara ahankali muyar kasasa, yayin da kukunta ke tayar mai da hankali


Cikin dasheshiyar murya yace menene?

Cikin kukan tace dan Allah ka bari"

Saboda me ?

Sunkuyar da idonta tayi sannan tace"

Yaya wani irin fa nakeji ajiki na"

Murmushi yayi batare daya dainayin abin da yakeji ba sannan wace"

Nihilah kwatan tamin abinda kk ji"

Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta, zuwa can faruq yayi nisa duk ya fita hayyacin shi"

Nihilah ma daka kalleta zaka gane tana cikin wani hali murya kasa2 tace"

Na,am nihilah ya akayi?

Batasan lokacin data furta wlh yaya zaka rikita ni"

Hmmm nihilah kenan ai nafison Ki rikece, dan Allah kiyi sauri ki burkice"

Hawaye ne suka zobo a idon ta, da sauri faruq ya kankameta sannan yace"

Nihilah karki Hana zuciyar Ki abinda take so, ni mijinki ne kina da hakki akaina kamar yadda nakeda shi akan ki dan Allah duk abun da zuciyarki ta raya miki kiyi karkiji kunya"

kwance kawai take ajikin shi tana maida numfashi"

Jin inda kirjinta ke bukawa da karfi yasa shi tausaya Mata, Kara matseta yayi tare da lumshe ido, yana me sauke numfashi

Suna cikin wannan hali sukaji ana buga kofa"

Daker faruq ya iya bude baki yace waye?

Muryan bashir yaji yana fadin ni ne"

Shigo faruq ya fada yana me kara kwakume nihilah"

Turo kofar bashir yayi ya sauke idonshi akan su sannan ya tabe baki yace"

Toh ai saika sake ta tafiya zasu yi, umma na jiranta"

Fuskarshi daure yace aiko ka ta yi?

Eh tun dazon ita take jira"

Kaje kace mata tayi bacci"

Wanne irin tayi bacci da rana tsaka?

Ni dai nace maka kace tana bacci kawai babu ruwan ka"

Amman dai kasan halin umma tana da zafi fah"

Kash bashir nidai kaje ka fada mata kai ai babu ruwanka nikuma dama duk abin da nayi ba burgeta zanyi ba"

Shiru bashir yayi yana kallon inda nihilah ta manne ajikin faruq sannan ya sake cewa dan Allah faruq ka saketa jifah yadda kakema hannun ka sai anjima ka hanani bacci"

Kallon hannun faruq yayi sannan ya matsar da hannun gefe yace"

Bashir jeka mana tana jiran ka"

Tsaki bashir yaja sannan ya nuna nihilah da hannun yace"

Wannan yariyar wlh muguwar munafuka ce, ta gama cika baki bataso ka kuma ji inda ta lafe ajikin ka"

Umm bakomai faruq ya fada tare da leka fuskan nihilah"

Girgiza kai bashir yayi sannan ya Fara tafiya yana fadin ai wlh cewa zanyi tace ta tafi saita zo"

Zabura nihilah tayi ta mike tsaye tare da fadin dan Allah yaya bashir karkace haka muje gani"

Mikewa faruq yayi ya kara riketa sannan yace bashir wuce karka rudata"

Wucewa bashir yayi batare daya sake cewa komai ba"

Nihilah naganin fitan shi ta fara kuka"

Lallashinta faruq ya fara har tayi shiru sannan yace"

Nihilah sanda kk shigo kinga Sadiq?

Eh"

Kin dauke shi?

Ni ? Aini bana daukan shi"

Kallonta yayi sosai sannan yace"

Sabo dame?

Ganin inda ya tsare ta da ido yasata sunkuyar dakai sannan tace bakomai"

Shiru yayi zuwa can yace"

Nihilah dan Allah ki dinga daukan

Please Login or Register in order to submit comment