Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har faruq ya sameta gidan nan kashinta ya bushi"

Nihilah naganin fitanta tamike itama tabar gidan"

Gaba daya yaran kida suka barsu dan lokacin barci suke"

Cikin kankanin lokaci naziya ta isa gidan iyayenta cikin kuka take fada musu abinda zuciya ta dabeta ta aikata"

Batakai ga karasawa mlm saluhu ya fito daga bayi butan hannusa yajefeta da ita duk ruwan ya sauka ajikinta cikin fada yace maza ki koma dakin ki, ya kasheki ma ni bani da asara, wanne karan banin yakaiki Ki dakarmai mata"

Gyalanta ahannu tabargidan, gidan anty ta nufa da kafa dan bata dauko kudi ba"


Nihilah ma da kuka tashiga gidan anty tun aharabar gidan take fadin abin da naziya ta mata"

Anty ce ta fito tana fadin tamin daidai meyasa bata fasa miki baki ba?, mazamaza ki fita kiban guri wlh kika kuskara kika shigo gidan nan saina barki kwance"

Ganin anty ta nufuta yasata fita aguje, daker ta karasa titin tana kokarin tsaida mota amai ya kece Mata.......






❄💦Mmn Yazeed❄💦
❄💦❄💦❄💦
*ASIRINSA YA TONU*
❄💦❄💦❄💦


❄❄❄❄💦
*By*
❄❄❄💦
*Fadeela Lamido*
❄❄💦

❄💦



❄❄💦
*Page 91 to 93*
❄❄💦


*Na sadaukar ga wannan shafin ga mosoya _ASIRINSA YA TONU_ gaba daya😘*




❄💦 Iya karfinta ta rike faruq, amman inaga faruq ya mance waye agaban shi, dan hankadata yake da iyakan karfin shi"

Da taimakon bashir suka samu suka tsaida shi, banda kerma babu abinda jikin shi keyi"

Dan haka anty ta saka kuka, ganin inda anty ke hawaye hankalin shi ya dawo jikinshi, cikin sanyin jiki ya zame daga rukon da bashir ya mishi ya tsuguna agabanta "


Idonshi ya bude akanta tsorata tayi ganin inda idon yayi kamar jini ya kwanta, har yanzun yana gabanta saidai bakinshi ya kasa cewa komai"

Zuwa can ya fara sauke ajiyan zuciya"

Itama anty cigaba tayi da kukanta bata da nigar saurarawa"

Bashi na gefensu ya rungume hannuwan shi"

Zuwa can faruq ya bude baki hankali yace, Anty dan Allah kidaina kukan nan, karya jawo miki wata matsalan"

Kamar jira anty take cikin kuka tace, au daman kasan kuka ka iya jawowa mutun matsala?, Yaro?, daman kasan kuka illah ce ajikin dan adam?, amman kake cutar da baiwar Allah shekara da shekaru ka kasa gane kukan ka iya jawo mata illah? Aiho Ashe babu dadi? toh bari kaji ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, akullum ka kuntatawa naziya jinake kamar ni ka kintatawa, yanzun baka tunanin nan gaba ayiwa yarka,? danme zaka dinga azabtar da yariya?


Shiru falon yayi illah sheshshekar kukan anty dake tashi shiko faruq hawaye ne suka fara zobo mishi"

Anty ce taci gaba da cewa toh indai inada daraja a idonka ban amince kakai hannunka jikin naziya dasunan duka ba, idan kuma sontane bakayi toh ka sauwake mata, dan wulahkancin ya isa haka"

Har yanzun kansa na kasa ya kasa dagowa ya kalli anty zuwa can ya share zufan daya keto mishi sannan yace"

Toh yanzun anty kina nufin naziya ta daki banza kenan?, nihilah fah ta daka, wlh anty sotayi ma takashe min ita, saboda bakin kishinta na jaraba' bayan kafin na fita saida naroketa tayi hakuri da nihilah har zowa sanda zatai hankali, danme zata biye mata"

Cikin tuhuma Anty tace, yaro Anya kuwa giyar da kasha ada bata juyar maka da tunani ba, kodai har yanzun kana Shane?

Da saurinshi ya girgiza kai tare da fadin ni babu wani abun da nake sha anty"

Toh inason zan tambaye ka kuma ka gaya min abin da ke zuciyarka tsakanin ka da Allah, waishin ita naziya babu ko digon sontane azuciyar ka?

Gabanshi yaji ya fadi dan be taba zatan irin wannan tambayan daga gurin anty ba, tabbas bazai iya bude baki yace beson naziya ba dan iya zaman shi da ita ya fahimci mutun ce ita me sanyin hali, dan haka bazai iya tattace son naziya yake ko kuma shakuwa ce kawai tazama gurin daya, shidai yasan yanason nihilah"

Muryan anty ce ta katse mishi tunanin da cewa dakai fah nake mgn"

Zabura yayi da sauri sannan ya bude baki cikin rudewa yace"

Anty ni bansani ba ko Ina son ta"

Cike da haushi anty ta kalli shi dan zuwa yanzun ta fara gajiya da halin shi jitayi kaman ta gunduma mishi zagi amman saita daure"

Shiko bashir murmushi yayi azuciyar shi yace munafuki, nasan maganin ka"

Shiru sukayi zuwacan anty tace toh shikenan tunda kace baka sani ba, na baka sati 1 kaje kayi tunani idan har baka sonta ta zuwa nan da sati 1 ka kawomin takkadanta, Allah ya hada kowa da rabonsa"

Cikin sauri bashir yace yauwa anty inaga hakan ma yafi, murmushi yayi sannan yace anty idan hakan ya faru ina cikin manema"

Cikin sauri faruq ya dago ya kalli bashir sannan ya maida idonshi kasa"

Anty ma yi tayi kaman bataji me bashir yace ba"

****


Bashir ne ya fara fita dan bayason su hadu da faruq, saidai yana dafda shiga motarshi ya hango faruq abayan shi, dan haka ya hada harta gudu ya fice agidan"


Ya koma gida babu dadewa yaji sallaman faruq lokacin yana zaune shida umma fada takemai danme yabari faruq ya shigan mata daki, Sallaman shi yasa duk suka maida hankalin su gareshi"

Idonshi kerr akan bashir saida yamai kusan kallon minti 3 sannan ya nufeshi gadan gadan wani wawan mariya ya daukeshi dashi tare da fadin munafukin Allah yau Asirin ka ya tonu ashe ka dade kana ha'intata, mika hannun yayi ya shakemai wuya tun bashir naganin abin wasa harya fara tari"

Itama umma da zama tayi kawai tana kallon ikon Allah, amman jin bashir na kakari ta zabura ta isa garesu faruq ta fara ja harda kaimai duka"

Ganin da tayi besan tanayi ba ga bashir ido duk suyo waje yasa ta kurma ihu, aguje nihilah ta fito ganin faruq shake da bashir yasata kurma ihu,

Umma gani tayi ihun bazai mataba ba dan haka ta dake kirjin faruq dakarfin da harsai da ya kalleta itama cikin idon ta kalli shi sannan tace idan baka sakeshiba Allah ya isa ban yafe maka b.....

Tunkafin ta karasa ya sakeshi ajigace bashir ya fadi kasa yana haki, nihilah ce ta nufeshi dagudu tanamai fifita da dan kwalinta"

Umma ko har yanzun bata daina dukan kirjishiba tare ta tambaya shi abinda bashir yamai"

Cikin karaji yake fadin umma *ASIRINSA YA TONU*, yana matsayin kanina wadda na yadda dashi nakesashi adukkan al'amurana amman yana ha'intata, yarasa wadda zai so sai naxiya sabo dashi maci amanane, wlh bashir saina kasheka"

Gaba dayansu shi suke kallo bama kamar nihilah data wangale baki, fifita takewa bashir amman hankalinta nagurin faruq hawaye harya fara tsiyayo mata"

Sai alukacin hankalin shi yakai kan nihilah wani haushi ne yasake kamashi cikin fada yace ke dan ubanki zoki wuce daki idan nakaraganin kinbi hanyar da bashir yabi ma saina jimiki ciwo, azafafe ya juya ya fita, yayin da umma tabishi da kallo"

Yana fita ta juyar da hankalinta ga bashir cikin fada tace bashir me ya kaika aikata irin wannan, ta yaya mace da mijinta zakace kana so kafa nemi tashin hankali"


Umma rabo dashi karyan iskanci yake, yaya za,ayi naso naziya daman gwadashi nake, dan na fahimci yana sonta amman yake wulakantata dan kawai yaga sonta yafi nashi yawa, yake wahalar da ita"

Ajiyan zuciya umma tayi sannan tace lallai bashir baka da hankali, waye ya gaya maka anawa namiji irin wannan wasan? Toh ai ko saurayi ne ya nemi buduwar suka rabu yaji wani ya aureta haushi yakeji, bare matar da take tare da mijinta harda haihuwa atsakanin su, gsky baka kyauta ba, yazun idan ba anci Sa,aba zumuntan ku ta samu tangarda kenan tunda kaga ya dauki zafi kuma banga laifinshi ba"


*****


Faruq gida ya wuce kangadon shi ya kwanta, babu abinda zuciyarshi take mishi banda tafarfasa mgnr bashir ke masa yawo akai Ashe daman bashir son naziya yake? Na sakan kance mishi, ashe neman dama yake, shedan ne yacigaba damai busa, acikin zuciyarshi yake cewa ko shiyasa bashir da naziya suke shiri sosai , yayin da nihilah kuma basa shiri da bashir dolene ya tsanta bincike har ya gano meye atsakanin naziya da bashir, dan alamu sun nuna akwai wata kullalliya"

Tunawa yayi ya baro nihilah gidan umma dan haka ya mike afusace dan bazai yadda bashir ya gama kallemai mata ba, dan yanajin nihila ne har cikin bargoshi, ko kallonta bashir yayi ya cuce shi, bare har ya jiyemai zazzakar muryanta"


Lokacin daya isa gidan babu kowa afalon dan haka ya isa dakin umma, shiga yayi tare da sallama"

Umma rungume da nihilah sai faman fifita take mata"

Afirgice ya karasa inaga ya mance waye agurin dumin kuwa hanun shi yamika ya rike nata" yana fadin nihilah jikin ne sannu ko Allah ya baki lfy"

Umma ya kallah sannan yace umma naZo tafiya da itane"

Zame nihila tayi daga jikinta sannan tace a,a kabari gobe iyayen ku zasu dawo dan namusu waya nagaya musu halinda kuke ciki sun kuma ce ajira su"

Shiru yayi zuwa can yace umma nifah bazan iya barin nihilah ta kwana gidan nan ba matsawar bashir na cikinsa"


Tsoro ne ya baiyana fuskan umma wato abin harya kai haka?, nunfasawa tayi sannan tace toh yanzun yaya kakeson ayi?

Umma tafiya zamuyi ko kuma nima nakwana anan"

Waigowa tayi ta kalleshi sannan tace Hmmm toh bissimillah, juyawa tayi tafice adakin"

Jawo nihilah yayi ya rungume zuwa can ya fara sunbatanta taren da tura hanunwan shi cikin rigarta"

Hannuwan shi ta tattaro duk ta fito dasu sannan tace, yaya ashe daman kanason naziya, kana kishinta kaman mahaukaci kazo ka shake bashir kaman zaka kash......

Hannun shi yasa da sauri ya bege mata baki cikin mazurai yace banason kina kiran sunan bashir da bakinki idan kika kara Allah ya isa, banason bashir na tsane shi, tunda na fahimci idon shi nakan gonata, nihilah ina da matukar kishi, da ace kece bashir yace yana so to da lallai zan kashe bashir, nihilah naziya fah matatace amman dan rashin kunya har yabude bakinshi yace zai aureta"

Yana mgnr ne yana shafa jikin nihilah zuwacan yace nihilah kisan abinda nakeso dake daga yau indai ina gabanki bason nasakejin kin kira sunan naziya, kisa kawai azuciyar ki ni faruq daki ne ke 1 kicire naziya azuciyar ki, idan kikai haka zan baki mamaki"

Ajiyan zuciyata sauke dan babu laifi tadanji dadin mgr shi"

Saida ya gama luguiguita ta sannan ya mike Bari naji na danyi wani bincike yanzun zan dawo"


****




Shika dai yake tafiyar shi cikin mota cikin minti 30 ya isa gidan, bayan ya faka motar shi ya tsaya yana tunanin yaushe rabon shi da gidan fatima tun nihilah na karama da take samishi kuka saiya kawota"


Yana kokarin sakkowa daga cikin motar mijin Fatima na fitowa daga cikin gidan"

Cikin sakin fuska ya karaso ya mikawa faruq hannun suka gaisa"

Bayan sungaisane yace ma furuq mushiga mana"

Faruq na murmushi yace, basaima nashiga ba, ta leko kawai mugaisa"

Beyi musuba dan surukuta yake da furuq sosai, dan shi befaye sakin fuskaba sabanin bashir dayake wankar"

Cikin sakin fuska nasir ya kalli fatima dake wanke2 yace toh saiki saki aikin yau babban yaya ya tunamu ya kawo mana ziyara"

Fara,a ta saki cikin sauri ta fara dauraye hannunta tana fadin"

Yaya bashir kenan Kuma fah munyi waya becemin zaizo ba"

Daidai lokacin da suka fito falo yace ba bashir bane faruq ne"

Baki fatima ta kama tare da😳 sannan tace badai yaya faruq ba, saidai bashir, shi wannan inbanda masifa me ya iya"

Hanyar fita tayi daidai lukacin da yake cewa kina nufin ni bansan faruq din bane?

Bakaramin mamaki tayiba ganin furuq jingine jikin motar shi, adan tsorace ta karasa tare da addu'an Allah sa karyai mata masifa kafin su rabu"


Ganin inda take dardar yasashi fadin ke dallah inzakizo kizo ni sauri nake"









❄💦Mmn Yazeed❄💦
❄💦❄💦❄💦
*ASIRINSA YA TONU*
❄💦❄💦❄💦


❄❄❄❄💦
*By*
❄❄❄💦
*Fadeela Lamido*
❄❄💦

❄💦



❄❄💦
*Page 94 to 96*
❄❄💦





Ahankali ta karasa gaban shi, kamar bazaiyi mgn ba, zuwacan ya nisa sannan yace"

Kinajina wani dan aiki Zan baki, nasan nihilah najin maganar ki, inason ki same ta ki mata dan nasiha ta dan rage xafin kishin nan nata"

Cikin mamaki fatima take sauraranshi yanzun shi da kanshi bazai mata nasihar ba saiya nemin wani duk masifan ashe na banza ne, lallai maza halinsu saisu nihilan gudawa nawa take, yariyar daya kusa haifa ya nuku gari ya taho man....

Muryan shi taji yaci gaba da cewa, fatima bana juran Ganin nihilah cikin damuwa, ina tsintan kaina nima cikinta har na kasa sararrafa kaina, ganin inda fatima ta sunkuyar dakai ya sashi dakatawa yana leken fuskanta, cikin natsuwa yace ke fatima kinajina kuwa?

Cikin nutsuwa ta dago kai tare da fadin inajinka yaya"

Toh mgn ne zanyi dake me mahimmanci, inason ki taimaka min na gyara gidana, ni yanzun bani da wani gata.....

Cikin sauri ta kalleshi tare da mamaki akan fuskanta, adan tsurace tace yaya ya zakace haka?

Eh gaskiya na fada fatima bani da gata haka kuma bani da abukin shawara, ita anty kulum cikin kushe nihilah take saikace ba itace ta haifita ba, amman ta iya yabon 'yayan wasu, kullum cikin yabon naziya take, umma ko dama can basona take ba, ta wareni acikin
yayanta, yanzun ne ma take dan min mgn, shiko bashir munafukine akwai wani abu azuciyar shi"

Kurrr fatima tamai tana mamakin yadda ya saki baki yana irin wannan maganganun masu kama da sambatu"

Cikin tsawa yace kimajina kuwa kin wani tsareni da ido "

Sunkuyar dakai tayi sannan tace, yaya ai duk naji abin da kace , dazun ma munyi waya da umma take gayamin abin dake faruwa inasha Allahu gobe zanje gidan kuma zan same nihilah kamar yadda kace"

Yauwa yar kanwata dako kin kyauta min amman ba fada zaki mata ba, karki yadda kisata kuka, indai kinga zatai kuka kibarta kawai dan bamata da lfy"

Cafff fatima ta fada azuciyarta afili kuma tace karka damu yaya"

Da haka sukayi sallama ya tafi, koda fatima ta shiga gida gadon ta fada tare da fasa kuka dan gani take yayan nata kamar ba cikin hayyacin shi yake ba, yace awa matarshi nasiha kuma yace kar asata kuka, wannan wacce irin soyayya ce"


Faruq ko gidan umma ya nufa, yana dafda shiga unguwar alhaji ibrahim ya kirashi awaya, gefen hanya ya koma ya tsaida motar sannan dauka"

Sallama yayi amman alhaji ibrahim be amsa ba cikin bacin rai yace kana inane yanzun ?

Cikin sanyin jiki yace ina kan hanyar zuwa gidan umma"

Uban me zakayi agidan? anya kuwa lfy fiya kalau kake?

Baba nihilah fa tana gidan, kuma ni gaskiya ban yadda da bash.....

Kunci ubanku kaida Aishan yazun in banda kai mahaukaci ne tayaya aure zaiyuwu tsakanin bashir da naziya bayan kana raye ba mutuwa kayi ba, ko ka mance uwa daya uba daya kuke kaida bashir?

Cikin rawan baki yace baba ainasani cewa babu aure atsakinin su, amman tunda har ya iya furtamin haka zai iya ha intata yamin zamba cikin abinci"

Shiru alhaji ibrahim yayi har ya gama sauraran sa sannan yace"

Faruq meyasa san zuciya yakeson ya rufe maka ido, duk cikin yaran nan namuu kaine babba meyasa kakeson zama me kawo mana matsala, bashir wasa yakeyi kuma al'ada akwai wasa tsakanin kani da matar wansa"

Baba shifa cewa yayi idan na saki yana cikin manema"

Kai faruq dadi na dakai naci kaman kuturu, yanzun dai ka kama hanya ka wuce gidan ka kakwanta ban amince maka kwana gidana ba, dan mahaifiyar ka tacemin kace can zaka kwana toh ban yadda ba, tun wuri ka wuce gidan ka, idan mun dawo gobe zanyi kiran ka"

Juyawa faruq yayi badan ransa yaso ba, ranan yadda yaga rana haka yaga daredare, zuciyar shi cike da takaici"

Dan haka washegari bece zashi office ba dan
Yasan ko yaje bazai iya aikata komai ba"

Da misalin 2:30pm faruq kwance akan makeken gadon sa, babu abinda yake sai tubka da warwara, ya saka wannan ya kwance wancen yana cikin haka wayarshi tayi kara, kira ne na gaggawa daga daddy dan haka cikin sauri ya tashi ya tafi"

Cikin kankanin lokaci ya isa gidan alhaji ibrahin, yayi mamakin ganin mutanen dake ciki kusan dangi ne gaba daya aciki, saidai yan kadan da basa gurin"

Bashir ne ya bude taron da addu'a bayan yagama daddy yace"

Nasan dukkanin kunsan abinda ya taramu gurin nan, kaman yadda kowa yasani abubuwa da dama sun faru, amman abinda yafi firgitani fada tsakanin bashir da faruq, kwata2 banji dadi ba, cikin tohuma daddy yajuya ya kalli faruq sannan yace"

Faruq meyasa idonka yakeson rufewa, yazun duk yadda kuke dakai da bashir?, banda shirmenka .me zai kawo zargi, tun
Wuri ka gyara tunanin ka bana son shashanci"

Anty ce ta katse daddy da cewa wlh yaro sai kun tasan mai tsaye kwata2 ya cenja hali yazama wani irin fitinanne, banda haka bashir fa cikin wasa yayi mgnr, menene abin tada hankali harda su duka"

Hmmm ai abin yama wuce duka shakeshi fah yayi kaman zai kashe, wlh da babu kowa kusa Allah kadai yasan me zai faruq, cewar umma da take kokarin mikewa"

Alhaji Ibrahim ne yayi gyaran murya sannan yace duk bawannan ba, kai bashir zo ka bashi hakuri kuma tunda ya nuna beson wasa daga yau karka sake mai irin wasan"

Murtuke fuska bashir yayi sannan yace, baba ai basai na bashi hakuriba tunda na fada cewa wasa nake, kuma shi kanshi yasan wasa nake kawai yaso cimin mutunci ne"

A,a bashir kabashi hakuri nace ai durkusawa wada ba gajiyawa bane"

Toh shikenan baba ahankali ya mika hannun shi ya rike faruq sannan yace"

Allah yabaka hakuri faruq ni wasa nake maka, wlh babu komai azuciyata"

Faruq bece komai ba illah kyauda kanshi da yayi gefe"

Alhaji ibrahim yace toh na kashe wannan mgnr karna sake jinta"

Sai kuma mgn akan matan ka da akace sun samu saba bani......

Cikin sauri faruq yace baba dan Allah ina neman alfarma abar wannan mgnr zanyi hukunci dakaina"

Lala sam ban amince ba hukuncin ka na hauka alhaji ibrahim ne ke fadin haka lokacin da yake kallon cikin idon faruq din"

Kara kwantar dakai yayi yace, baba wlh da hankalina, nasan abin da nake yi, wannan karon inason nayi hukunci da kaina......

Mlm saluhu ne yayi gyaran murya sannan yace"

Inaga kubarshi din, inaga zaifi, tunda yace yanason yayi hukunci dakanshi yana da kyau abarshi yayi din, dan shine yake zaune dasu yasan halin kowacce cikin su, kuma kunsan ance me daki shiyasan inda yake masa yoyo, duk wadda hunkuncin da zai yanke bemata dadi ba kunga gaba ta kiyaye"

Shiru falon yayi zuwa can anty tace nidai ban yadda ace wai yaro ne zaiyi hunci ba, dan Allah kar kubashi wannan daman, naziya wahala kawai take sha ahannun shi be bari hankalinta ya kwanta ba bare taji dadin zama dashi.....

Cikin sauri mlm yace hutu kuma? Aini banba faruq naziya aure dan ta huta ba, aure fa na turata wadda nake saran ta sanadinshi zata shiga *Aljannah* kuma akullum nasihata gareta tawa mijinta biyayya sannan tasa azuciyarta ibada take, ba zuwa ta mike kafafu tana jiran kyale kyalen duniya ba"

Gaba daya falon zancen mlm saluhu ya shigesu, kusan kowa idonshi cike yake da hawaye, anty da naziya ko tuni suka fara kuka"

Itama nihila dake dafda fatima ajikinta yayi sanyi sosai, shiko faruq sunkuyar da kanshi kasa yayi kaman mejin kunya"

Ahankali daddy yayi gyaran murya sannan ya kira sunan faruq ahankali yace"

Nasan kai ba jahila bane ilmin daidai gwargwado kana dashi, idan kaje yanke hukuncin kaji tsoron Allah kayi adalci, karkaga bamu agurin kace zakayi abinda kaga dama, kasani idan bama wajen Allah na kallon ka, kuma zaka tsaya agaban shi aranan da babu wani kalma da zaka iya kare kanka da ita"

Daddy narufe baki faruq ya fara musu godiya tare da kara tabbatar musu insha Allah zaiyi adalci,

Gaba daya mazan sukayi waje sanadin kiran sallan da sukaji"

Matan kowace haramar sallan sukayi"

Anty fatima da nihilah zaune adakin umma bayan sun idar da sallah, kallon nihilah tayi tace"

Nihilah wai meyasa bakison naziya ne, bayan tana da Kirki amman har yanzun naga jininku yaki haduwa duk da cewa ita bata nuna miki irin kiyayyan da kike nuna mata"

Shiru nihila tayi tana wasa da gefen hajjabinta"

Badake nake mgn ba Fatima ta fada bayan ta daure fuskanta"

Ahankali tace anty nidai da ace zata rabu da yaya to da zamu shirya amman ni gaskiya yanzun bansonta"

Kina nufin

Please Login or Register in order to submit comment