Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya saki naziya ki zauna dashi ke daya?

Da saurinta tace eh"

Murmushi fatima tayi sannan tace nihilah kina ganin ke daya zaki iyamai maganin matsalan shi?

Cikin rashin fahimta tace anty aishi bashi da da wata matsala"

Baki fahimci niba ina nufin zaki iya daukan bukatan shi aduk lokacin daya gaiyaceki shinfidan shi?

Cikin sauri nihilah ta😳 sannan tace a,a anty shida yakejin shi kaman inji, wlh bana iyawa idan na gaji hakura yake"

Fatima taso yin dariya amman saita daure sannan tace to kinga amfanin mata 2 kenan, ranan da baya dakinki saiki dan huta na kwana 2 kinga kishiya abokiyar zamace ba ba abokiyar gaba ba"

Cikijin kunya tace anty nifah koni daya ce zan iya kulah dashi"

A,a nihilah yanzun fa kikace yanajinshi kaman injin"

Toh anty idan yaga ni kadai ce ai dole ya hakura"

Cikin murmushi anty tace toh ashe ba dai injin din bane, indai har zai iya hakura, ni abinda nake kuje muki yanzun amisali yaya faruq ya saki naziya bayan kwana biyu ya fahimci bazaki iya daukan dawainiyar saba yaje ya jajubo miki gogaggiyar yar duniya, kiyi yaya da ita?, barganin yana kyaunar ki, dole ya kulah da lfyn jikin shi, dan haka nake baki shawara kiyi hakuri ku zauna lfy"

Hawaye nihilah ta fara sharewa tace toh naji amman dan Allah kitayani addu,a Allah yayamin"

Sosai anty ta tausaya mata dan haka ta mika hannu ta jawota ajikinta tana rarrashin ta, suna cikin haka anty ta shigo taita mata nasiha sannan tace ta tashi taje falo faruq najiranta zasu tafi gida"

****


Tana isa falon ta hangoshi zaune ya daga kanshi sama, naziya nagefe ta takure, kai tsaye tanufeshi kanciyarshi ta zauna tare da shafa sajensa tadan huramai Iska afuskan shi"

Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya kama kanta ya kwantar akirjin shi yana fadin kinfara ko?

Kukan shagwaba ta fara tare da fadin toh ni me nayi"

Nandanan faruq ya fara fita hayyacin sa adaburce yace ya isa haka tashi muje gida"

**

Suna isa gidan ko wacce ta wuce barayinta yayin da zuciyar naziya ke dukan uku uku, dan batasan wani irin hukunci faruq zai yanke mata ba, dan ta tabbatar hukuncin akanta zai kare dan ta kula har tsoron batawa nihilah rai yake"

Shiko faruq addu'a yaitayi acikin zuciyar shi Allah yasa yafi karfin zuciyar shi yayi adalci"

Sai kusan karfe goma ya baro gidan anty dan haka kai tsaye dakin nihilah yanufah,

Samunta yayi ta cure waje daya tana rike da cikinta"

Dasaurin shi ya karasa yana fadin jikin ne?

Cikin shagwaba tace nifa yunwa nakeji cikina kaman babu komai nake jinshi, aini agidan umma su 4 take bani abinci arana dan likitama cewa yayi inci abinci sosai"

Shiru yayi harta gama sannan yace, naziya batayi girki bane?

Toro baki tayi sannan tace toh ni kotayi ma inaruwa na da abincinta danni baci zanyi ba"

Tamke fuska yayi sosai sannan yace, jiba nihilah banason rigima kisan dai ba girmana bane yawon suyo abinci bazaiyu inada mata biyu indinga yawon suyo abinci ba, duk abinda kikeson ci kishiga kitchen ki girka, amman yanzun tunda baki da lfy ki fada abinda kikeso insa naziya ta girka miki, kuma sannan inason na gargadeki akan shiga dakin mutun babu sallama, tayaya zaki shiga dakin naziya bazaki mata sallama ba sa,arkice ita kodan kinga ina lalabaki ne yabaki daman da zaki mata rashin kunya"

Cikin matsanancin mamaki nihilah ke kallon shi cikin tunzura tace au goyon bayanta kake kenan nida ta zageni fah cemin tayi fah dabba"

Shima cikin zafi wadda batasan yanashi akantaba yace nikikewa tsawa? nihilah ina mgn kina mayar min, bayan kice baki da gaskiya duk sunan da ta kiraki dashi aike kijawowa kanki, daga yau kuma karki kara shiga part dinta batare da kin mata sallama ba, abinci kuma nata zaki rankaci bazan kara zuwa soyo abinci ba, sannan indai kinason farin cikina kiba naziya girmata dan Allah nihilah badan halina ba kibata girmanta kuzauna lfy kwatar da murya yakarayi sanna yaci gaba da cewa nihilah dan Allah kitaima keni nasan inasonki fiye da inda nakeson kaina, dan haka inason kibani goyon baya nayi dalci atsakanin ku, tare da kara sakani kan hanya idan kinga inashirin kyaucewa, nihilah ko kinason sanadin rashin adalcin danakeyi makomata ta zama wuta ne?

Cikin kuka ta girgiza kai dukda magan ganunshi na farko sun tsaya mata arai amman daga karshe ta tausawa zancen shi, dan haka ta daukan ma zuciyarta wani alkawari dan ganinta hakan ne kwanciyar hankalinta"

Shima hawayen yake sharewa amman yana fakan idonta karta gane halin da yake ciki, zuwa can ya dake yace nihilah kin min alkawarin kwantar da kanki ku zauna lfy na naziya?

Tana goge hayen ta daga kai alamar eh"

Murmushi yayi sannan yace nagode Aisha Allah ya miki albarka har naji sunki ya kara nukuwa azuciyata, dan mirgonota yayi jikin shi sannan yace bari naje na karbo miki abinci ko zakizo mujene muci tare"

Gargiza kai tayi dan haka ya mike tare da sun batan ta akumatu ya fice"

Yana fitowa ya daure fuska sannan ya nufi part din naziya"

Tunda ta kalli yanayin shi gabata ya fadin, dan haka ta mike da saurinta tana kokarin shiga toilet"

Cikin fada yace idan kika matsa anan gurin sai ranki ya baci, yau daga ni sai ke babu me ceton ki"

Ja tayi ta tsaya dan bata da bakin mgn illah rawa da jikinta ya fara"

Takowa yayi har ya iso gabanta batai aune ba saijin saukan Mari tayi akuncen ta, kafin ta ankara ya kara mata wani"

Agigice ta tsanyara kawara tare da fashewa da kuka dan saida taga gilmawan wasu wayoyi, sabo da radadin da taji"

Cikin fada yace wannan yazan na farko kuma na karshe da zaki dake nihilah duk abin nihilah tamiki kiyi hakuri harna dawo, bance ki hukuntata ba, dan aurenta nake kamar yadda nake auren ki, yarki ce ita dazaki rufeta da duka?"

Kuka kawai naziya keyi harya gama babatun shi ya fice"

Dakin nihilah ya koma dauke da kulolin abinci saidai yana shiga ya sameta kwance kamar me bacci, dan girgizata yayi ta bude ido yace oya sakko kici abinci"

Cikin yanayi irin na me bacci tace yaya likita yace idan nayi bacci adaina tashina kumani yanzun banjin yunwan ka ajiyemin ka tafi abin ka anjima zanci"

Tana mgrn tana lumshe ido kamar mejin baccin gaske dan haka ya kyaleta gadon ya haye ya jawota jikinshi wasa yasoyi da ita amman taki yadda duk nacinsa saida ya gwada akanta dan dai ta bashi hadin kai amman taki, dan haka abun yai matukar bashi mamaki domin ita mutunce meson wasanni amman yau daga yakai hannun jikinta saita goce, daga karshema kudunnewa tayi cikin bargo tabarshi agefe"

Ido ya zuba mata kamar me kallon TV acikin zuciyar shi yace me yariyar nan ke nufi ne? Zuwa can ya kula kamar baccinta yayi nisa dan haka ya mike ya fice"

Part din naziya sake komawa dan gaskiya mutun neshi mabukaci yaso ya rage dare gurin nihilah amman taki amincewa , dan haka dole ya aje fushinshi agefe yaje gurin naziya"

Toron kofar naziya taji anyi daker ta iya daga idonta da jini ya kwanta ta kalleshi, wani haushi ne ya rufeta jitake babu wadda ta tsana aduniya kaman shi, kumatun ta ta dafe wadda ya kunbura yayi suntun"

Shima tunda ya shigo yake kallonta saidai taki bari su hada ido, cikin gadara yace ke naziya kisame ni adakina kiyi sauri karki batamin lokaci........





β„πŸ’¦Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 97 to 98*
β„β„πŸ’¦





Bejira me zata ce ba yayi gaba abinsa"

Itako naziya mamaki abin ya bata lallai mutumin nan da karfin hali yake, ya gama dukana kuma yacemin wani wai na sameshi adaki, tsaki taja sannan ta mike ta isa gaban madubi, gani tayi gaba daya ta canza kamanni gaba daya fuskanta ya kunbura gawani jini daya kwanta gefen idonta guda 1, hawaye ne suka zobo mata tasa hannunta ta share wani irin zuciya ne ya bijiro mata dan haka ta mike afusace"

Kitchen ta nufa ta dauko zandareriyar wukanta, sannan ta maida hannuwanta baya ta nufi dakin faruq"

Ahankali ta tura kofar daidai lokacin da faruq din ya fito wanka yana daure da towel akugun sa, hannun sa daya dauke da turare yana fesawa asako da lungu na jikin shi"

Wani Mayataccen kallo yabita dashi rigar bacci ce me dan karan kyau ajikinta iya daidaita gwuiwa, sai yanzun ya kula da kunburin fuskanta, saidai yadda yaga tamaida hannuwanta baya ya dauke masa hankali dan betaba ganinta tayi haka din ba"

Idanunta ta kafeshi dashi tana kallon shi dan haka ya shiga kallon jikin shi ko zaiga me take kallo, iya dubanshi bega komai ba dan haka ya maida hankalin shi wajenta"

Ahankali ta fara tahowa gabanshi dan haka ya kafeta da ido, tana zuwa dafdashi ta tsaya cikin ido takaleshi sannan tace malam *ka sake ni*"

Bangane na sake ki ba daman na rikeki ne?

Cike da kwarin guiwa tace ina nufin ka sauwake min auren ka, bana yi"

Hmmm toni inayi, idan kuma sakin ahannunki yake sai nagani"

Zabura tayi sannan ta fito da wukar dake hannuta ta mika mishi tare da fadin amshi ka karasani na huta da bakin cikin auren ka, wlh ina me tabbatar maka idan baka kasheni ba ni zan kasheka, dan bana sonka na tsaneka, ka sakeni inhuta da zaman takaici da bakin cikin gidan ka, tana mgnr ne kaman zararriya tare da kara nufarshi da wukan"

Sosai hankalin faruq ya tashi daganin halin da take ciki tabas ya fahimci bata cikin hayyacinta kuma ayadda yaga yanayin ta babu abinda bazata aikata ba"

Mike mishi wukar take tare da kara matsawa kusa dashi"

Daker ya bude baki yace toh duk me ya kawo haka?

Bana sonkane kawai ka sakeni ko kuma ka kashi ne ka huta dan na taren maka rawar gaban hantsi, karashi mgnr tayi tana mika mishi wukan, dan haka ya mika hannu ya karba"

Kura ma wukar ido yayi sannan ya dago ya kalleta sosai sannan yace"

Naxiya yanzun dan namiki fada shine kikayi fushi haka? , naziya kina da hankali kuwa?, wuka fa kika bani, ni kikecewa na kashe ki?

Bata da niyar mgn saima rufe ido tayi tana huci kaman kububuwa"

Shima shiru yayi yana kallonta zuwa can yace naziya bude idonki ki zauna muyi mgn"

Bata bude idon ba kuma bata zauna ba tsaye take kawai kaman gunki"

Hankalin faruq kara tashi yayi dan haka idon shi sukayi jawur kallonta ya sakeyi sannan yace toh shikena tunda hukuncin dana miki be miki dadi ba Allah yabaki hakuri, wannan irin zuciya haka! Kefa daman baki iya fushi ba, dan Allah ki bude idonki indai nine natuba kiyafeni, hannun sa ya mika ya tabata da niyar jawota jikinshi zafi yaji rau ajikinta, hakan ya tabbatar mishi zazzabi ne ajikin dan haka ya dauketa cak yasata agado yana cigaba da fadin mutun bashi da lfy amman ya iya neman jafa'i"

Ciccijewa take tare da kokarin kwacewa ganin haka ya sakkan mata karfin shi gabadaya yana cigaba da fadin nace kiyi hakuri ko?, ni banason irin wannan fushin naki, Allah ya baki hakuri, haba naziyata, dan Allah ki huce haka nan ya isa"

Wani dan sanyi taji azuciyarta ganin inda faruq ya marairaice mata dan haka ta fara sauke ajiyan zuciya"

Ganin ta fara saukowa yasahi mikewa, inda yake aje magani ya nufa, zuwa can ya dawo hannun shi dauke da magani da ruwa gaban gadon ya zauna sannan yace sakko kisha magani"

Kin tashi tayi, yayi magana harya gaji dan haka ya dauko cukali ya dama, bata ankara ba saijinshi tayi yana dura mata, ruwa ya bata ta kora sannan ta koma ta kwanta hawaye na tsiyayo mata ta gefen ido"

Ahankali ya hau gadon cikin dibara ya daurata akan kirjin shi, cikin masifa takaimai duka akirjin tare da kukarin sauke kanta"

Dasauri ya rike hannuwan ta sannan ya kara mannata da jikin shi yana fadin, haba naziya zaki kashe ni ne?, ki kwanta kiyi bacci kinga jikin ki yayi zafi sosai"

Kwanciya tayi tai lamo dan ji take kaman an mata duka, ta dade kwance jikin shi amman bacci yaki zuwa mata"

Duk halin da take ciki faruq najinta dan shima yau idon shi kwata2 babu bacci, dan yadda naziya tamishi yau ya nunamai tana cikin mummunan hali, beji dadin halin dayaga tashiga ciki ba, jin yadda hawayenta ke sauka akirjin shi yasashi wani tunani anya kuwa naziya ba aljanu gareta ba?, yin wannan tunanin yasashi ya Fara karanto addu'oi yana tofa mata, cikin kankanin lokaci bacci me nauyi ya kwasheta"


Washegari


Tunda faruq ya tafi sallah ta wuce dakin ta, alhamdulillahi jikinta yayi sauki sosai dan fuskanta harta sabe, tsintan kanta tayi cikin farin ciki sosai dan yau har gari ya waye faruq beyi baccin kirki ba, daga ta motsa zatajishi yace sannu jikin ne? Zaki sha ruwa ne ko wani abu kike so?, tunda take da faruq bata taba samun irin wannan kulawa daga gareshi ba, koda ta kwanta agadonta bacci gagaranta yayi data rufe ido daren jiya take tunuwa"

Da misalin karfen 8:00am faruq ya shigo dakin, jallabiya ce fara sol ajikinshi, bakin gadon ya zauna sannan ya tura hannun shi cikin rigarta yana duba zazzabinta, tare da fadin yajiki?

Daker ta bude baki tace da sauke"

Murmushi yayi kadan sannan yace toh Allah ya kara sauki, waya taga ya kara akunnen shi zuwa can taci yana cewa"

Anty ataimaka mana da breakfast wlh matan gidan duk basu da lfy"

Bataji me akace ba zuwa can taji ya sake cewa wlh anty ba nihilah bace batama san nakira ba, yauwa anty mungode "

Kashe wayar yayi sannan ya kalli naziya ahankali yace"

Naziya naga jiya kinyi fushi sosai ina fatan zuwa yanzun kin huce? , karashe mgnr yayi tare da kafe ta da ido"

Mata da miji sai Allah ganin inda ya marairaice yayi matukar bata tausayi dan haka ta mika hannunta ta roko nashi, tare da kurawa hannun nashi ido, shiko fuskanta ya zuba ma ido yana murmushi, ganin bata da niyar mgn yasashi fadin bakice komai ba?

Tana wasa da hannun take fadin ya wuce Amman ni gaskiya bazan jurewa halin nihilah ba indai ta karamin rashin kunya bazan yadda ba"

Hmmm bazama ta kara ba dan itama jiya na mata fada, kuma ta fahimta, amman abu daya zan kara jajjada miki ban abince da duka ba, dan karfin ku ba daya bane kuma kinga ciki gareta yanzun da wani abu ya samu cikin kice me?, dan Allah ki dinga kokarin kina rage fushin ki"

Jitayi gaba daya jikinta yayi sanyi daman nihilah ciki gareta?, cikin sayin jiki tace toh kayi hakuri ni bansan tana da cikiba da bazan kulataba"

Dan murmushi yayi sannan yace bakomai naziya itama haryanzun bata san dashi ba, kuma naji dadi da kika fahimta Allah ya mike albarka, kuma kyauda idon sa'idawa akanmu😜

Ameen ta fada tana tura kanta cikin kirjinshi"

*Hmmm lallai naziya hausawa sunyi gaskiya dasuke cewa tsakanin mata da miji sai Allah*

Shima murmushi yayi tare da kissing dinta, afilin yace Allah ya hada min kanku"


mikewa yayi tare da fadin naziya bari na dubo jikin nihila"

****

Afalo ya samu nihilah ta daura kafanta daya kan daya, yana kallonta ya gane tayi kuka ta sanadin idonta daya kunbura, zama yayi dafda jikinta tare da jawo kafadan ta ta fada jikinshi, batai musuba saima Kara shigewa jikinshi datayi leken fuskanta yake yana fadin kinganni sai yanzun ko? Kiyi hakuri dan Allah naziya ce bata da lfy mun kwana bamuyi bacci ba, dan haka bayan nayi sallah na dan kwanta"

Hmmm bakomai"

Yadda tabashi amsa ne yamai wani irin dan haka ya kara cewa, ko baki yadda bane?

Yazanyin ince ban yadda ba yaya Allah ya bata lfy tunda yau baka da aiki ma kana iya komawa ka kwanta"

Hmmm nihilah kenan kodan irin kewannan tawa bazakiyi ba, har wani korata kike?

Murmushi tayi sannan tace nayi kewanka mana gashi ma nakwanta ajikin ka"

Ban yadda ba idan har kinason na yadda kinyi missing dina kitashi mushiga daga ciki"

Cikin sauri ta make kafada tare da fadin a,a nabarwa anty na"

Cike da mamaki ya kalleta Dan gsky tabashi mamaki, suna cikin haka naziya ta kirashi awaya take shai damai idi drive ya kawo sako daga gidan anty"

Cikin sauri ya mike yana fadin oya nihilah tashi muje muyi breakfast"

Batai musu ba ta mike tare da tura hannunta cikin nashi, ahaka suka iso falon, nihilah ce ta fara gaishe da naziya batare da ta kalleta ba"

Cikin sakin fuska naziya ta amsa karo na farko da nihilah ta fara gaishi ta kenan tun bayan aurenta da faruq"

Akasa suka zauna bayan sun kammala faruq ya kallesu ko wanne ya takure alaman rashin sabo, dan murmushi yayi sannan yace"

Yanaga duk kun takure ne , ku sake jikinku ku dan taba hira mana, ko na tashi na baku waje ne?

Kauda kai nihilah tayi can gefe sannan tace, nifa yaya bacci nakeji daki zani na kwanta"

Daure fuska yayi kadan sannan ya kyauda idonshi can gefe almar yayi fushi"

Murmushi nihilah tayi dan ta gane manufarshi, ahankali ta kali naziya tace , anty ina takwarata ?

Cikin sakin fuska tace tana daki bacci take"

Yake nihilah tayi sannan ta sake cewa badai tun baccin jiya ba"

A,a ta tashi harna mata wanka, komawa tayi"

Farin ciki ne ya baiyana akan fuskan faruq acikin zuciyar shi yace alhamdulillah nihilah anfara hankali, afili kuwa kallon nihilah yayi sannan yace"

Ke ta gada ai gurin bacci, juyawa yayi ya kalli naziya yace jiya fah bataci abincin dare ba tayi bacci wai har tana cemin likita yace adaina tashinta idan tana bacci"

Murmushi naziya tayi sannan tace toh ai lalura ce, matsalan dai rashin cin abincin ki dinga daurewa kina ci, tunda baki daya bace"

Bani daya bace? toh ni da uban waye? abinda nihilah ta fada azuciyar ta kenan cikin sauri ta mike tayi daki"

Gaba daya binta sukayi da kallo, harta shige daki"

Mikewa yayi sannan yacewa naziya ina zuwa"

Yana shiga ya same ta tayi rufda ciki tana kuka, tseye yayi akanta yana kallon Ikon Allah zuwa can ya zauna sannan ya dagota jikin shi ya kura mata ido sannan yace"

Menene ya faru ?

Cikin kukan tace ai kanajinta tana cemin wai bani daya bace, me take nufi?, tana nufin ni mahau kaciya ce ?

Murmushi yayi sannan yace nihilah rima ce ke damunki, kina nufin yanzun baki fahimci abinda take nufi ba?

Banza tayi dashi tana cigaba da kukanta, dan haka faruq yaciga da cewa nihilah naziya na nufin ki dinga kula kinacin abinci saboda karki wahalar da abinda ke cikin Ki, ma'ana dan dazaki haifan mana nan da wata 7"

Cikin sauri ta kalleshi sannan tace to ni nace mata ina da ciki ne, ko ko ita tamin cikin dazata......

Cikin murmushi ya dakatar da ita ta hanyar fadin, a'a ba ita tayiba, nine na nayi"

Tashi tayi ta zauna sannan tace kana nufin dgsk ne ina da ciki shine baka gaya min ba amman ita ka gayamata?

Itama daliline yasa na gaya mata, badan haka ba saidai kawai kiga cikin na girma ajikin Ki tunda ke baki da wayo"

Shiru tayi bata sake cewa komai ba har aka dau tsayon wani lokaci dan haka faruq ya mike yace"

Bari naje nayi wanka na leka gidan anty, kuma yau ki shirya min tarba ta musanman, dan ina lissafe kwana na 2 adakin naziya dan haka yau anan nake"

Wani irin kallo tamai sannan tace yaya nifah na bar mata, dan haka basai ka dawo dakina ba, kayi zaman ka acen, ni babu abin da nake bukata idan kuma ina da bukata zanyi mgn"

Shiru yayi yana kallonta cikin baccin rai yace au tanan kuma kika bullo har ina murna kin fara hankali, to bari kiji wlh karki soma hanani kanki, dan bazan iya jurewa ba, wlh tun wuri ki canja tunani idan ba haka ba kuwa zan hadaki da daddy"

Turo baki tayi sannan tace toni me nayi ma, dan nace nabar mata ai ba dole bane ko?

Girgiza kai yayi kawai ya fita, adakin"

***


Da daddare banyan faruq ya kammala duk wani abu dazaiyi ya nufi dakin nihilah saidai yana tura kofar yajita kule, jikinshi asanya ye ya fara buga wa har ya gaji beji motsin kowa ba dan haka ya juya dakin shi cikin tsananin fushi"

Juyi yaitayi agado, besan me nihila take nufi da wannan hukuncin nata ba, koma dai menene, hukuncin yayi tsauri da yawa kusan kwana 3 kenan rabon da ya kwana kusa da ita, sannan gana hudu 4 zai tabbata, daman haka masu mata 2 sukeji wannan ta gara ka tacan wannan ta gara ka nan, Allah ka kawo min agaji"

Misalin karfe biyu yamike ya nufi dakin naziya"

Tana baccinta me dadi taji ana buga kofar, ahankali tace waye"

Cikin kausashiyar murya yace nine zoki budemin kofah"

Ahankali

Please Login or Register in order to submit comment