Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Dijama kuma ta mik'e tsam jiki ba kwari ta nufi d'akinsu,
Kai tsaye kan fado ta fad'a ta saki wani kalar kuka."

Tana Cikin kukan ne Mahmud ya kira wayarta, domain yaji su sauka lafiya?"
Ta d'auki wayar tana shishshikar kuka hankalinsa a ta she ya shiga tambayata abunda yake faruwa."

"Tabbas yaya da gaske ne sulaiman ya kawo kayan lefensa,
Na gansu da idona gasu can a falo."

"Kukanta yakeji har cikin ransa yayi saurin runtse idonsa yace "ki daina kuka na fad'a maki baxaki auri sulaiman ba,

Idan Abba ya keb'e shi d'aya kije ki fad'a masa bakyason sulaiman, idan kika fad'a masa daga k'arshe idan nazo garin nasan matakin da zan d'auka."

Anan ya shiga kwantar mata da hankali da kalamai masu dad'i har tayi shuru ta fara dariya ta manta da damuwar da take cikinta."

*******************

Kwanakin biki sai k'arasowa yakeyi dijama ta kasa tunkarar Abba da magabar bata son sulaiman,

Kullum cikin far gaba take bata cin abinci,
Duk ta rame kamar ba itaba."

Sai ta fito da niyar ta tunkari Abba da maganar saitaji nauyi da kunya Abba yayi Mata Duk kan komai a rayuwa bazata tab'a juya masa baya ba."

Babban tashin hankalita d'aya ne duk lokacin da takira wayar Mahmud a kashe take jinta,
Wanda hakan ya kuma Sanya ta shiga cikin tashin hankali har ta kwanta ciwo."

***************

Mahmud shima hakan takasan ce a garesa,
Baya Cikin kwanciyar hankali kullum tunaninsa yana wurin dijama, gashi yanzun baya da lokacin kansa aiki bincike sukeyi a gidan mata."

Shine babban a wurin domin ogansu ya lura da mahmud aiki yake a kan gaskia dan haka ya mayar da ragamar binciken gaba d'aya a hannunsa, kullum da zarar anyi sallar a suba yake fita baya dawowa sai 2am, kwata kwata ya manta a Inda ya ajiye wayarsa,

Wnn ne ya bawa Yusra da mar hurd'arta da Alhaji Yasir a yanda take so ba wani tsoro a tare da ita."

Yau dai sauran sati biyu auren su dijama, Wanda Kowa a gidan ya cika da mamakin rashin zuwan mahmud Kuma da zarar aka kira wayarsa a kashe."

Wanda a Ranar jikin dijama ya tsanta sai numfashi take saukewa sama sama tareda dafe zuciya kamar wacce ranta zai fita."

Mommy ta shigo d'akin domin ta Kuma duba jikin nata ta sameta a cikin Wnn halin da sauri ta juya ta kira Abba cikin Minti talatin aka nufi asibity da ita,

Cikin gaggawa likitoci suka amsheta emergency aka nufa da ita suka shiga bata taimakon gaggawa."

Wanda Khalil yana ganin hakan yafito ransa a b'aci ya shiga motarsa ya nufi gidan sulaiman,

Horn ya dingayi a k'ofar gidan baji ba gani,
Sulaiman dake Zaune a falo tareda yaransa suna cin abinci,
Cikin sauri ya mik'e tsaye tare da yiwa fareeda hannu alamar ta jira ya yadawo domin daga jin wnn horn d'in shi ake nema a waje."

Da saurin sa ya fito daga gidan yana mamakin wake nemansa haka?"
Khalil ya hanga a Cikin mota zaune."

Khalil kuma yana ganin fitowar sulaiman yayi saurin fitowa a Mota a fusace, ya tunkare sulaiman gadan gadan cikin hushi
yana zuwa ya cacume wuyan rigarshi yaci kwalarsa har sai da idanun sulaiman suka fito waje."

Yace "na rantse da Allah Duk kasake dijama ta rasa ranta akanka ka rubuta KA ajiye kai ma saina kasheka da hannunna."

Domin na fahimci bata sonka kawaicine kawai Abba yayi ya Baka ita
Wanda yin hakan yasa aka k'untatawa tawa rayuwa."
to barikaji koda ka aureta,
Ka kuma rubata ka ajiye sai dai Kowa ya rasa Dan Kuwa nafika buk'atarta nafika Sonta Dan babu Wanda ya isa yayi rayuwar aure da dijama sai ni."

Magana ta k'arshe da zan fad'a maka itace tunkafin rayuka su b'aci kaje asibity a gaban bainar jama'a kafa d'awa Kowa cewa kafasa auren dijama idan ba hakan ba ni kad'ai nasan abinda zanyi maka Wanda sai Kayi Dana Sanin sani a rayuwarka."
Ya sakeshi da k'arfi Wanda sai da sulaiman yayi baya baya kamar zai fad'i Allah kawai ya tsareshi bai d'inba."

Ya bi Khalil da kallo yana murmushi yana mamaki."


Khalil kuma yaja mutarshi a fusace ya nufi asibityn."

*******************

Yau mahmud zasu kai hari gidan mata bayan sun kammala duk binciken da sukeyi akan gidan."

Sunyi shirinsu Cikin kayansu na sojoji ko wannesu d'auke da bindigarsa,
Hakan kawai Mahmud yake jin Kansa Duk a hargitse gabansa fad'uwa,
dijama kawai ke fad'o masa a rai."

Sai da suka bari misalin k'arfe biyu 2:30 na dare, lokacin da suka tabbatar da Duk wani d'an isaka Wanda ke zuwa wurin ya hallara."

Yau kuma Alhaji ATIKu yayi Sabon kamun wata baby kyakkyawa Wanda Alhaji Yasir ya had'ewa miyau ya dinga rik'on Alhaji Atiku akan ya d'an sammashi ya d'ana."

Alhaji Atiku yace "Sam ba zai bashi ya d'ana ba,
Sai dai shima idan ya Amince ya sammashi ta shi baby Wanda ya dad'e yana had'iye miyau shima ya d'ana."

Alhaji yasir yace "Eh ya yarda ya Amince, suka shirya yanda zasu b'atarwa da 'yan matan tunani,

Bayan Alhaji yasir ya kammala sarrafa Yusra misalin k'arfe 1:30am ya d'agata ya d'auki rigarsa yasaka
Yace tajira shi yadawo kada ta Sanya kayanta zaici gaba ne idan yadawo ya kashe wutar d'akin duhu ya gauraye ko ina yanda ko tafin hannunka baka gani."

hakan shima Alhaji Atiku abunda ya cewa babynsa kenan."

Suka fito a tare" kasan cewar d'akin da suka kama Jere da na juna."
hakan sukayi canjan d'aki Wnn ya fad'a d'akin wnn"

Kai tsaye Alhaji Atiku ya fad'awa Yusra ya shiga sarrafata Wanda ita kuma Yusra ta d'auka Alhaji Yasir ne, kasan cewar duhun dake da d'akin
Wanda shima Alhaji Atiku bai San 'yarsa bace yusra shalelen sa,

Basu ankaraba sai k'arar tashin bindiga suka rik'aji yana tashi,
Gaba d'akin da alamar ashigo kame gidan."










_labarin Wnn page d'an ya faru da gaske_

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_)😅




Written by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basher_)






*61*






Gaba d'aya sojoji suka zagaye gidan da bindigoginsu,

Aka dinga kama matan banza ana jefasu a mota, Mahmud tareda yaransa suke shiga d'aki d'aki suna fito da karuwai ana zubasu a mota.'

Alhaji Atiku da gaba d'aya hankalinsa a tashe yake daya fahimci halin da ake ciki jikinsa ya soma rawa domin yasan k'aryarsa ta k'are sunansa zai b'aci a gari."

Hakan ya lalubo rigarsa cikin duhu ya saka batare d yasanya wando ba,

Sanya rigarsa yayi dai dai da shigowar Mahmud d'akin d k'arfi ya banka k'ofar tare da kunna wutar d'akin."

Alhaji Atiku ya gani tare da Yusra akan gado d'aya ko wannen jikinsa sai rawa yakeyi.'

Salati mahmud ya saki ya dafe kai yayi saurin fita daya baya baya a d'akin tare da kaiwa zauna ya ajiye bindigarsa gefe d'aya."

Yaransa suka zagayeshi suna fad'in oga lafiya?"

Alhaji Atiku duk ya shiga cikin tashin hankali ganin da mahmud masa
ya kamashi dumu dumu da macce a gado d'aya kwata kwata bai juya ya kalli fuskar yarinyar ba bare yasan ko wacece."
Itama yusra haka saboda tashin hankali bata lura d ko waye a kusa da itaba."

Sojoji suka shiga d'akin suka fito da Alhaji Atiku da Yusra waje."

Adai dai lokacin da aka fito da Alhaji Yasir da budurwarsa."

Sai lokacin Yusra taga Alhaji Yasir anfito dashi daga wani d'akin tayi saurin juyawa ta kalli to waye take tare dashi,

Wanda shima Alhaji Atiku juyowar da yayi kenan dan ganin fuskar ko wacece."

Ido biyu sukayi da juna a zabure yaja da baya yana nunata cikin tashin hankali, a rud'e yace
"Yusra kece kika fito a d'akin nan?"

Itama cikin tashin hankali tace Daddy kaine?"
Wayyo na shiga uku na lalace."

Alhaji Atiku ya d'ora hannu a kai ya kai durk'ushe yana fad'in kaico duniya, nayi dana sani."

Ya d'aga kai ya kalli Alhaji Yasir yace "Abokina kuma Amina na ya kad'aice da 'yata kwaya d'aya tilo wacce nafi so akan komai,
Nima mahaifinta na kad'aice da ita, nayi ma'amala da ita tamkar matata."

Gaba d'aya sojojin wurin suka shiga cikin Al'ajabi suna tsine masa Albarka."

Mahmud ya rutse idonsa zuciyarsa na k'una kwata kwata baya son ya bud'e ido ya gansu."

Kuka Yusra takeyi sosai tana fad'in "kaico rayuwata ni dai banyi sa'ar uba ba Allah
KA k'arb'i rayuwata na mutu na bar duniyar idan ba hakan ba ina zankai wnn abin kunyar."

Daddy KA cuceni KA cuci rayuwa,
baka bani tarbiya ba, ka sangartani KA koyamun duk abinda nake so zan samu a duniya ka koya mun intaka duk wanda nakeso duk ynda naga dama.'

Ga irinta nan ga irin tarbiyar da kabani yau na wAyi gari tare da kai a shinfid'a d'aya munyi ma'ala irin ta dabbobi da akuyoyi d'a yabi uwarsa uba yabi 'yarsa kaico rayuwatah."

Alhaji Atiku kuka yakeyi kamar k'aramin yaro yana doka kansa a gini sai gani sukayi ya fad'i k'asa jini yana zuba ta hanci da baki da kunne."

Da sauri sojoji suka sanya su Yusra a bayan mota tareda 'yan uwanta 'yan iska,
Alhaji yasir shima sai kuka yakeyi gashi Zaune a bayan mota da matsayinshi da komai. Yanaji yana gani aka wuce da shi."

Alhaki Atiku kuma cikin wata mota aka sanyashi aka nufi asibity dashi."

Sai da aka kammala kamen gaba d'aya duk mutanen dake gidan ankamasu antafi dasu snn mahmud ya tashi daga Inda yake yana Jan k'afa yashiga mota suka tafi."

Magana yaransa suke masa amma ina yana cikin tashin hankali mahmud ya zamar masu kurma."

Ana shiga asibity da Alhaji Atiku wuyansa ya kare harshensa ya fito yashiga fisge fisge snn rai yayi halinsa."

Dafe kai Mahmud yayi yana kalmar shahada,
Ji yayi gaba d'aya duniyar tayi masa zafi,
Alhaji Atiku ya rasu ya amsa kiran ubangiji."

Hakan aka d'auki gawarsa aka nufi gidansa da ita,
Kai tsaye mahmud yaje office d'insu inda aka rufe su yusra domin a hukuntasu ya fito da ita batare da yayi mata maganaba bare ya kalleta dan ko son ganinta bayayi ya d'auko ta a motarsa ya nufi gidansu da ita."

A bakin k'ofar gidansu ya ajiyeta ya d'auko takarda saki uku ya mik'a mata, ya kalleta da rinanun idanunsa da sukayi jajir yace "Yusra dama bantab'a sonki ba ko da da sau d'aya, bantab'a yimaki kallon macce kirkiba Dibo da yanayin rayuwarki da ta mahaifinki.
Hakan na daure cikin rashin son da nake maki na zauna dake ashe kina can kina tarrayya da mahifinki kin zama a kuya kowa binki yakeyi mahaifinki ya biki abokinsa ma ya biki da duk wani wanda yake buk'atarki,

Yusra na sakeki saki uku ko a hanya bana fatan Allah ya Kuma gad'ani da ko mai kama dake ne."

Ta kai durk'ushe a gabansa tana kuka tana magiya "mahmud ina Sonka baxan tab'a daina Sonka ba,
Ina rok'on Allah ya kasheni da sonka a rayuwata."

Wani kallo ya wurga Mata mai cike da tsana da kyamata yaja motarsa yayi tafiyarsa."

A Daren ranar a yanda yaga dare haka yaga safe,
Cikin tashin hankali da tunani Dan shi tunda Allah ya halicceshi bai tab'a ganin Wnn rayuwarba."

Sai da aka kira sallar asuba bayan yaje masalaci ya dawo sai a lokacin ya tuna da wayarsa ya lalubota ya kunnata ai kuwa ya dinga ganin sak'onnin dijama kala kala akan yayi Sauri Yazo za'a aura mata sulaiman."

Zai kira wayarta kenan sai ga Kiran mommy ya shigo cikin Sauri ya d'auka ya gaida ita cike da ladabi, mommy ta Shiga yimasa fad'a INA ya Shiga kwana biyu ayita Neman wayarsa a kashe,

Hakuri ya Shiga bata tare da nasar da ita aikine ya rik'eshi."

Mommy tace 'dijama na nerman yafiyarka don Kuwa a yanzun hakan tana kan gadon asibity Cikin mawuyacin hali rai ko mutuwa."

kansa ya juya cikin hanzari da tashin hankali yace "mommy meyasa meta?"
yaushe ciwon ya kamata?"

Ji kawai yayi mommy ta kashe wayar,

Da sauri ya mik'e tsaye ya Shiga shirya kayansa ya fito ya shiga motarsa ya d'auki hanyar kano,
Sai dai idan ya tafi ya kira oga ya fad'a masa daga baya."

Alhaji Atilu anyi masa wanka anshirya shi Cikin suturarsa akayi masa sallah aka kaishi ma kwancensa na gaskiya."

Wanda Yusra babu abinda takeyi sai aikin kuka suma Kuwa tayi shi ba iyaka."

Hakan mahaifiyarta tun da taji abinda ya faru bata kuma yin magana ba, illah jawai ta dinga bin kowa d ido tana kallonsa."

Tana Ganin anfita da gawar Alhaji Atiku ta rafke jiki ta fad'I a nan take ciwon sashe ya kamata."

Yusra ta kuma fashewa da kuka ta Kuma shiga Cikin wani tashin hankali Wanda ta gwamma ce mutuwarta da rayuwarta."

****************

Khalil sai safa da marwa yakeyi a Cikin asibity,
Wanda aka hana Kowa ya shiga cikin d'akin da dijama take saka makon dibata da akeyi."

A can ya hango sulaiman ya shigo da motarsa a harabar asibityn, wani jin haushinsa da takaicinsa suka Kuma taso masa domin ganin yakeyi Duk rashin lafiyar da dijama takeyi sulaiman ne ya haddasa mata ita."

Wurin sulaiman d'in ya nufa kamar wani zaki ya tunkareshi, sulaima dama yana da haushinsa a yanda ya iskoshi har k'ofar gidansa yayi mashi rashin kunya,

Yana zuwa daf dashi yashiga hararar sa,

sulaima, kuma
Alurar soja ta motsa, ya juya cikin b'acin rai ya kalli Abba da mommy da tsohuwa,
Ya damk'i hannun Khalil cikin hushi ya janye shi daga Inda su mommy zasu iya ganinsu, yana rik'e da hannun,sa

Khalil sai k'ok'ari yakeyi ya kwace hannunsa amma ina ya kasa,
Sai da ya kaishi Inda ba mutane sosai
Sulaiman ya kaishi jikin bango ya Sanya k'afarsa d'aya ya take masa k'asa,
Still hannunsa yana rik'e da hannunshi ya murd'e shi sosai babu abinda ya ke fita a jikin Khalil sai gumi gashi ya kasa kwace kansa,

Sulaima yace " meyasa kake so ka kaini bango ne Khalil?"
Na lura da rashin kunyar ka gare ni, ina d'aga maka k'afa ne saboda halaccin Abba da mommy da kuma abokina mahmud kana so kasanya ni nayi butulci garesu."

Zanyi maka gargad'i na k'arshe
ko hanyar da nabi idan KA kuskura kabi ta wurin Saina Karya maka kafa daya."

Khalil ya zaro ido waje zufa sai wanke mata fuska takeyi."

Snn kuma bazaka tab'a Auren dijama ba,
Domin bata dace da da kaiba ba."
Snn idan ka kuma Shiga gonata Saina d'auke maka kai da bindiga kowa ya huta da halinka."

sann ya d'aga masa k'afa tare da sakar masa hannu yayi tafiyarsa."

******************

Misalin k'arfe goma mahmud ya isa garin kano.
Kai tsaye asibity ya nufa hankalinsa a tashe

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_)😅




Written by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basher_)





*62*






Da sauri yayi parking cikin Hanzari ya bud'e motarsa ya fito,

Abba ya hango a bakin k'ofar d'akin wnn ya tabbatar masa a nan d'akin aka kwantar da dijama."

Wurin Abba ya nufa ya gaida shi ya kallesa cike da mamaki, yana tambayarsa ya hanya?"

Lafiya k'alau yace "hankalinshi ba a kwance ba yana k'ok'arin shiga cikin d'akin."

Tura k'ofa Yayi ya shiga da sallama gaba d'aya d'akin cike yake da mutane mommy tsohuwa Khalil sulaiman fateema sai kuma Abba da ya biyo bayansa."

Idonsa a rufe suke,
Babu abinda yake kallo sai gadon dijama da ya ganta kwance kamar wacce ta mutu,

Duk ta rame ta fita hanyacinta ruwa kawai ake k'ara mata,

Ya gaida su mommy da tsohuwa cikin tashin hankali ya nufi gadon dijama,

A gefen gadon ya zauna ya zuba mata ido cike da tausayi da kuma so da k'auna,

"Mommy meyake damun tane?"

Mommy tace 'wayasa ni,
dijama gata nan dai kullum Cikin tashin hankali take da tinani, daren
Jiya suman ta biyu duk a tunaninmu rai yayi halinsa."

"Da sauri ya juya ya kuma kallon dijamar saka makon wani juya ido da takeyi Alamar wani suman ne ta kumayi."

Gaba d'aya d'akin suka mik'e tsaye sukayo kanta,
Abba ya fita da sauri ya tafi kiran likita."

Mahmud ya cire robar ruwan da ake k'ara mata ya janyo ta gaba d'aya a jikinsa akan k'afarsa ya kwantar da ita,
Yana "fad'in Khalil mik'omun ruwan robar can,

Cikin tashin hankali Wanda baya misallatuwa Mahmud ya shiga girgiza dijama yana 'fad'in Kitashi Dijama kadda ki mutu kibar yaya mahmud d'in, ki tashi dijama mahmud yana sonki,

Bakinsa ya sanya a cikin bakinta ya shiga hura mata iska da k'arfi,

Anan take tayi saurin sauke ajiyar zuciya,
Yana ganin hakan ya kuma rungumeta ajikinsa yana fad'in "bud'e idonki ki kalli yaya mahmud d'inki nine a gabanki."

Dijama ina sonki, yaya mahmud yana sonki pls kadda ki mutu kibarni."

Hakan yayi dai dai da shigowar Abba da likita Mahmud ya kalli Abba yace "Abba ina son dijama KA aura mun dijama,
Na dad'e da soyayyar dijama a raina,

Dan Allah Abba kada Ku aurawa sulaiman dijama saboda bata son shi ni take so Nima ita nake so
Abba kada Kuyi watsi da soyayyar da tun k'uriciya mukeyiwa junanmu ita,
Wanda Allah ne kad'ai ya had'ata kuma ya san manufar yin hakan."

Turus Abba yaja ya tsaya mommy tacika da farin ciki hakan tsohuwa sulaiman hakan da sai murmushi yakeyi,

Khalil kuma sai zufa yake fitarwa akan tashin hankali da gid'e mewa."

Dijama suka gani ta bud'e idonta fuskarta d'auke da murmushi ta kuma k'ank'ame Mahmud ta rik'eshi gam alamar kada yatafi ya barta."
Mahmud shima ya kuma rungumeta kamar zai maida ita a ciki."

Mamaki suka shigayi suka kalli junansu ko wannen da murmushi a fuskarsa."

Sulaiman ya matso ya matso kusa dashi ya dafa kafad'arsa yace "Abokina kwantar da halinka a duniya babu abinda bazan iya sadaukar maka dashi ba,
Dama abinda muka dad'e muna jira kenan, na bar maka dijama dijama ta zama taka Allah ya Baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyaba."

Hawaye suka shiga wankewa Khalil fuska wad'anda bai San lokacin da suke fitowaba,
Shi dai yasan yana son dijama so mai tsanani amma ya zamar masa dole ya hak'ura ya sadaukarwa da d'an uwansa ita,
yana son Mahmud sosai kuma tun tashinsa yaga Mahmud da dijama a tare,
A tare ya sansu a tare yake ganinsu duk hotunan da yake gani lik'e a falo mahmud ne da dijama."

yayi saurin share hawayen fuskarsa Dan kada Wani ya lura dasu,
Mommy tana lura dashi Karo na farko dataji Khalil ya bata tausayi."
Ta girgiza kai tayi kamar bata gan shiba."

Ya tako yazo wurin mahmud ya Dafa kafard'arsa yace "Tabbas d'an uwana Kaine KA dace da dijama,
Domin Kuwa kafi Kowa Sanin abinda take so da Wanda bata so,
Dijama tana sonka kaima kana Sonta sai dai muyi maka Addu'a Allah ya baku zaman lafiya a rayuwar aurenku."

Gaba d'aya d'akin Kowa yayi shuru zuxiyar Kowa cike da farin ciki,
Sai a lokacin tsohuwa tasamu damar bud'e baki tace "idan kowa ya Amince da aurenka da dijama ni ban Amince ba saboda anriga da ankarb'i kayan auren sulaiman."

Dijama tayi saurin d'agowa daga kwance da take a kan k'afar mahmud ta kalli tsohuwa"
Tsohuwa tace kalleni da kyau marar kunya,

Dama ciwon da kikeyi na mahmud ne kwananki biyu baki San Inda kanki yake ba har suma kikeyi kina tashi,
Amma yan zun dibeki zuwan Mahmud gaki nan kin tashi har kina iya d'aga ido ki kalleni."

Muna funcin banza muna funin wofi,
Wazaku nunawa zurfin ciki to kubari kuji saina ga Wanda zai d'aura maku Aure,
Sai dai ko wannenku ya had'iye zuciya ya mutu akan soyayya amma baxaku Aure junaba Dan kuwa dijama ta sulaiman ce."

Dariya tsohuwa ta basu gaba d'aya d'akin aka sanya dariya,
Tsohuwa tace "oh ga mahaukaciya INA magana kuna yimun dariya."

Mahmud ya gyarawa dijama kwanciya ya kalli tsohuwa yace "ke dai nasan matsalarki d'aya ce goronki ne ya k'are, kibari idan natafi sayo goron d'aurin aure na zanbiyo maki da naki"

Anan Aka Shiga wata sabuwar hira, Abba yace "baxai janye ranar d'aurin aure ba domin Ya riga da yasanya sanarwa,
Kuma ya fad'awa mutane, har Iv ya fara rabawa,

Dama Alk'awari ya d'auka koda dijama tana saman gadon asibity sai and'aura aurenta illah so idan mutuwar ce ta mutu da igiyar aurenta a kanta."

Gaban mahmud ya fad'i jin Abba yace har anbugo invention,
Abba yaciro invention a Aljihunsa mai kyau ya mik'awa mahmud kamar yasan abinda mahmud yake fad'i a ransa."

Jiki na rawa mahmud ya karb'a ya shiga dubawa abin mamaki sunansa ya gani tareda na dijama ajikin Iv."

Murmushin farin ciki ya shigayi yana mamakin ya akayi hakn ta faru?"
Dama Abba ya San yana son dijama ne?"

Ya karawa dijama Iv ta gani itama murmushin takeyi tana kallonsa cike da farin ciki."

Abba ya lura da alamar tambaya a kan fuskar mahmud ya nemi wuri ya zauna ya shiga bud'e masu b'oyayyi yar wasiyar da mahifin dijama ya bari tun ranar da aka Haifeta."

Da dalilin da yasa sulaiman ya fito a matsayin masoyinta,
Zaune Khalil ya kai ya shiga nadamar rashin kunyar da yayi tayiwa sulaiman sai ma yaji wata sabuwar kunyarsa yakeji."

Bayan Abba ya gama fad'a masu Duk wani abinda basu saniba,

Snn daga karshe Abba yace "Allah ya sanyawa rayuwar aurenku Albarka ya Baka.ikon yin Adalci atsakanin matanka."

Gaban mahmud ya fad'i,
Nan take ya canza fuska idonsa yayi ja da ya tuna da Alhaji Atiku da yusra,

Mamaki aka shigayi ganin Cikin Minti d'aya idonsa yayi ja ya canza fuska.'

Ya shiga fad'awa Abba duk abinda ya faru, har zuwa mutuwar Alhaji Atiku,
Salati Kowa yashigayi."

Abba yace "nayi Dana Sanin amincewa Alhaji Atiku akan aurenka da 'ayarsa."

Sai daga baya nagane d'ana baiyi sa'ar matar aure ba,
Mahmud kayafemun domin na San Baka son Yusra biyayya CE kayi mun ka aureta,
Kuma kayafewa Alhaji Atiku duk wani abu da yayi maka."

Sulaiman yace " k'arshen azzalumi da mazinaci baya kyau,

Allah ya yafe masa mudai mun yafe masa."

Anan aka shiga hirar biki, da abubuwan da za'ayi,

Mahmud yace 'walima kawai zaiyi ya godewa Allah."

A wnn yinin dai dijama sauki yasamu dan harda abinci take Wanda mahmud yake bata da kansa cike da so da k'auna."

Sai tarairayarta yakeyi yana lallab'ata ita kuma sai k'ara shagwab'a takeyi,
Mommy na ganin haka ta tattara kayanta ta tafi gida aka bar tsohuwa,
Babu abinda tsohuwa takeyi idan taga rashin kunyar tayi yawa illah ta mere baki☹ tace "Allah ya kyauta zamani ya lalace. Ai dai dole ka hak'ura har akai maka ita gidan ka"

Washe gari aka sallami dijama suka koma gida akaci gaba da hidimar biki, Wanda a yanzun tasaki ranta tana walwalarta duk wani motsi nata a kan idon mahmud Dan ma tsohuwa ta sanya masu ido."

Gyarasu kawai mommy takeyi da ita da fateema da kayan mata masu kyau 'yan zamfara."

********************

A shanty ta haihu d'a namiji kamarsu d'aya da Khalil."

Abin mamaki mahaifinta bai San da cikiba sai dai yaji kukan jariri yana fitowa a d'akinta,

Koda yake lek'awa ya ganta gurfane ta haihu a lokacin ba kowa a gidan

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_)😅




Written by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basher_)






*63*






Mamaki ya shigayi da Al'ajabi ya rik'e baki cikin bak'in ciki yace "Aisha kece kika haifar mun d'an shege a gida?"

Lallai kuwa zan kasheki na kuma kashe abinda kika haifa, idan har baki fad'a mun wanda yayi maki wnn cikin ba."

Yayi kukan kura ya shiga d'akin da niyar ya mak'areta, inna laure ta shigo gidan tadawo daga gidan bikin mak'ota, jin kuka jaririn da taji ne yana fitowa a d'akin Aisha yasa tayi saurin nufar d'akin da saurinta."

Mijinta tagani malam Abu yana k'ok'arin shak'e wuyan Ashanty tare da jaririnta."

Cikin sauri ta shigo d'akin ta fitar da malam daga d'akin
Yana fad'in na rantse da Allah muddun baki fad'a mun uban shegen d'an nan ba sai na sanya wuk'a na yankaki."

Inna d'aure ta Shiga salati tana fad'in yau me zan gani a gidan nan?"
Aisha kice kika haihu?"
dama ciki ke gareki shiyasa kike k'unshewa a hijabi?"

Kuka Ashanty ta fashe dashi tace "inna Laure ki taimakeni ki gyara mana jikinmu.
inna laure ta tausaya mata ta shiga gyara mata jikinta tare da jaririnta,
Abinda yafi d'aurewa inna laure kai shine duk wasu kayan jarirai Ashanty ta saya masu kyau, da tsada,

Wato tasan da tana da cikin kenan,?"
To meye ribarta da zata bari ta haifi d'an shege?"

Bayan inna Laure ta gyara mata d'anta ta karb'eshi ta kure shi da ido yaro sak mahaifinshi Khalil komai nasu iri d'aya,
Tayi murmushi tace "nagode inna laure."

Inna Laur ta rafka tagumi tace "amma dai Aisha kinbani mamaki, ina ganinki da natsuwa da kamun

Please Login or Register in order to submit comment