Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita kasan ni bana kyamatar duk abinda ya shafeka."

Yace 'Nasani mana"

Tace "kayi magana tana jinka,

Mahmud cikin fad'a da masifa harda dukan teburin da yake gabansa ajiye yakeyi

"Yusra kinajina umurni na baki ba kuma zan had'aki da Allah ba,
Kije ki d'auko ruwa ki bawa dijama, tasha
kiyi mata duk abinda takeso,
idan ba hakan ba,
duk kika kuskura kika bari na dawo baki aikataba saina lahira yafiki jin dad'i."

K'awayenta suka zuba mata ido cike da mamaki,
suna kallon ta tafiya zatayi ta d'auko ruwan tabata kuwa?"

Yusra kuma sanin halin mahmud da tayi ba k'aramin abu bane a wurinsa idan ya dawo yasami labarin bata aikata abinda yace ba, k'aramin aikinsa ne ya mata rashin mutunci

Kuma ita dai tana sonshi bazata iya rabuwa da shiba."

Ta janye wayar a kunnenta,
dijama ta sanya hannu ta karb'e wayarta tana kallon yusra tana murmushi,

Yusra ta mik'e tana d'ingirsa k'afarta tanufi frege ta d'aukowa dijama robar ruwan faro ta kawo mata."

Shewa abokananta suka shigayi suna fad'in wlh ke kin bada mata,
yanzun kamar wnn yarinya ta isa ta sanyaki abinda bakiyi niyyaba

Yusra batayi magana ba, zuciyarta cike take da bak'in ciki,
Zata zauna dijama tace "hy Yusra kin manta baki d'auko mun cup ba."

Shuru tayi tana kallon dijama cike da tsana jitakeyi kamar ta hauta da duka,
Ta kauda idonta daga kallonta,
bata niyar tashi."

Dijama tace "OK baxaki d'auko ba kenan?
Ta kuma d'aukar wayarta zata kuma kiran yaya mahmud ta fad'a masa."

sai gani tayi Yusra ta mik'e da sauki tanufi hanyar kicin."

Duk abinda akeyi fateema tana kicin tana kalllonsu tsoro ne fal a ranta."

Yusra tafito da cup rik'e a hannunta ta ajiyewa dijama a gabanta,
Dijama ta kalleta tace "kizuba mun kibani da hannuna na sha."
Hakan zaisa naji dad'i kin karramani."

K'awayenta sukace "kadda kibata kada Allah yasa tasha ruwan idan har sai kin zuba mata."

Suka wurgawa dijama harara sukace Banxa 'yar k'auye."

Dijama ta d'aga kai ta kallesu,
Tace "ya kamata Ku iya bakinku kusan abinda kuke fad'a idan ba hakan ba, idan kuka kuskura kuka k'ureni tare da b'ata mun rai yanzun zan nuna maku irin nawa k'auyancin zan nuna maku cewa "eh lallai ni 'yar k'auye d'in CE."

Ta juyo wurin Yusra tace "madam Yusra kizuba mun ruwa a k'ofi nasha."

Tace "bazan zuba ba sai dai kada kisha."

K'awarta tace "wlh karki zuba mata"

Dijama ta d'aga hannu ta buge bakin k'awar wadda ta lura tafi kowa rashin kunya a cikinsu,

Ta cire glass d'in idonta ta ajiye Jakarta a gefe tace yanzun zan nuna maki cewa ni 'yar k'auyen ce."

Rik'e bakinta tayi da taji yana mata wani irin zugin zafi duk a tunanin hak'oranta sun zube."

Hankalinta A tashe ta shiga janye a hnnunta daga kan bakinta tana nunawa 'yar uwata. Tace "diba mun kigani hak'ora na suna nan?" Ko sun zube."

Ta diba mata tace suna nan basuyi komaiba."

Dijama tana nan tsaye rik'e da k'ugu tana jiran Wanda zai tunkarota ta masa shegen duka."

Tsaitsaye sukayi suna kallonta ko wannensu tsoron tunkararta yakeji."

Ta kuma kallon yusra tace
" ki salami k'awayenki su bar gidan nan tunda ba gidan ubansu bane."

Idan ba
hakan ba tayi shuru ta d'auki wayarta ta danna kiran number mahmud.'

Mahmud da yake kan hanyar zuwa gida

ya wani kiran dijama ya shigo,
Da sauri ya d'auki wayar
Yace "bata baki ruwanba?"
.kibarta kawai ganin k'arasowa gidan yanzun INA kan hanya."

Yusra najin hakan ta juya tA kalli k'awayenta ta shiga rok'onsu dan Allah su taimaketa suyi tafiyarsu tin kafin Mahmud ya shi go ya samesu."

Kallonta sukeyi a alalace suka had'a Baki gaba d'ayansu sukace Yusra mu kike kora?"


hak'uri take basu jikinta na rawa ta dinga mink'awa ko waccensu gyalenta da jakarta,
Karb'a sukayi sunasakin baki suna mamakinta
Ta yanda sukaga dinga ganin jikinta narawa kamar wacce taga mala'ikan mutuwa."

Turasu ta shigayi da hannuta
ganin basu da niyar tafiya,
Dakatar da ita sukayi a fusace,
"Dallah malama ki daina turamu ai ko baki turamuba dole ne mubar maki gidanku,
Amma kisani indai kina tare da mahmud wata rana sai kin nememu."

Suna kaiwa nan ko waccensu ta fita a fusace."

Dijama na zaune a kan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya zuciyarta fal da farin ciki, sai murmushi take saki a fuskarta."

Ta kuma kallon Yusra tace "asirinki ya rufu tunda kika kori Wad'an nan 'yan Iskan k'awayen naki,
Amma fa har yanzun baki zuba mun ruwa nasha ba."

Ta Kuma wurgawa dijama harara cike da tsana,
Ke Baki isa kisanya na kori k'awayena ba,
na koresu ne saboda wani dalili nawa,
Taja wani dogon tsaki "banxa 'yar k'auye,
tajuya xata tafi"

Dijama ta sanya k'afa ta hankad'eta ta fad'i k'asa rufda ciki,

Tace "yanzun zan nuna maki abincin k'auye dana birni ba d'aya bane,
Ina ganin bakisan ko wacece dijama ba,
da baki isa ina fad'i kina fad'iba."

Yusra dake kwance rufda cikin a tsakiyar falo k'afarta mai ciwo ta shiga yi mata zugin zafi,

Cikin zafin rai ta mik'e daga kwance ta tunkaro dijama tana wani huci, ta d'aga hannu zata kwad'awa dijama mari."

Dijama tayi saurin rik'e hannun da hannunta d'aya ta murd'e hannun, sai da Yusra tasaki yar k'arar wahala

Dijama ta kuma d'aga hannu d'aya ta d'auke yusra da mari a fuska sai da gaba d'aya falon ya amsa da k'arar marin ji kakeyi tasssss....

Wanda yayi daidai da shigowar Mahmud falon shima yaji k'arar saukar marin,
Dijama na ganin yaya mahmud tayi saurin sakinta tarik'e kunci tana matsar hawaye tace "ni zaki mara daga nace kixubamun Ruwa nasha?"
Menamaki?"
Me natare maki a gidan nan daga zuwa na yanzun ko hutawa banyiba?"

Ta matso hawaye k'arya a idonta tace "Kiyi hak'uri idan zuwan da nayi gidan nan natare maki wani abun yanzun zan juya na koma Inda na fito."

Mahmud dake tsaye ya k'urawa dijama ido, yana ganin zubar hawayenta jinsu yakeyi har Cikin ransa,
Jikinsa har wani rawa yakeyi akan b'acin rai da jin haushin yusra."

Cikin muryar b'acin rai yace "baxaki bar gidan nan ba sai dai ita ta barshi tunda ba gidan ubanta bane."

Ya nufo Yusra cikin hushi yace "metamaki kika mareta lallai Kuwa yau zan Nuna maki cewa ke k'aramar Marar kunya ce."

Duk'a ki tsiyaya mata ruwa kibata tasha,
Idan ba hakan ba sai na lahira yafiki jin dad'i."

Yusra da ta daskare tsaye wuri d'aya rik'e da kunci tana kallon dijama cike da mamaki da Al'ajabi,
Wnn shi a kekira a dukeka kuma a
hanaka kuka."

Bata ankaraba taga mahmud ya Ciro belt d'insa na uniform d'in sojoji wad'anda ke sanye a jikinsa yanufo ta gidan gadan yana Neman dukanta dashi yana fad'in baxaki zuba mata ruwan tashaba?"

Tasan zafin dake tare da belt d'in saboda tana ganin daddynta yana dukan b'arayi dashi wanda da zarar yayi masu d'aya dashi sai jikinsu ya farfashe da jini"

Da sauri ta nufi wurin robar ruwa ta d'auki cup ta tsiyayawa dijama ta mik'a mata."

Mahmud ya tsurawa dijama ido cike da jin tausayi "Cikin muryar lallashi yace "yi hak'uri k'arb'i kisha."

Sai da ta juya ta koma kan kujera ta zauna snn Yusra ta Kuma matsawa kusa da ita ta mik'a mata cup d'in ruwan ta amsa ta kafa a bakinta ta shanye."

Mahmud yace "kink'oshi ko ta k'ara zuba maki wasu?"

Ta "girgiza kai a shagwab'ance tace A'a sun isheni."

Snn ya juya ya kalli Yusra yce kina iya wucewa ki kama gabanki."

Da gudu Yusra ta wuce tasaki wani irin kuka mai sauti, ta fad'a d'akinta."

Sai a lokacin FATEEMA dake lab'e wuri d'aya ta fito tana zarar ido kamar wacce tayi k'arya๐Ÿ˜…






*kuyi hak'uri da Wnn nayafi gidan biki sai na dawo*๐Ÿšถโ€โ™€

๐ŸŒน *DEEJAMAH* ๐ŸŒน ( _'Yar gidan tsohuwa_ )๐Ÿ˜…




Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)




*masoyan deejama 'yar gidan tsohuwa inajin dad'in yanda kuke bibiyar labarin nan comment d'inku yana sanyani nishad'i da dariya musamman 'yan group d'ina UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS Allah yasa ku anfana da darasin da ke cikinsa*




*55*






Mahmud ya matso daf da dijama itama dijama ta matsoshi kamar zasu rumgume juna saboda murna da farin cikin ganin junansu,

Kome suka tuna oho ko wannensu yayi saurin dakatawa, da sauri ta juya baya idonta ya cika da hawaye."

Cije baki yayi ya shafi gefen kan shi snn ya k'ak'aro murmushin dole yace "dijama 'yar gidan tsohuwa, Amaryar a wurin sulaiman barka da zuwa."

Gaban ta ya fad'i da taji yakirata da amaryar sulaiman."

Ta goge hawayen da suke neman zubo mata ta juyo da fuskarta tana kallonsa ta sauke ajiyar zuciya snn ta sauko daga kan kujera ta durk'usa k'asa tace "yaya ina wuni."

Murmurshi yayi yana kallonta cike da burgewa,
rabon da a durk'usa har k'asa a gaida shi har ya manta,
Yace "lafiya k'alau 'yar k'anwata, ya hanya?"

Tace "Alhamdulillah."

"Kiyi hak'uri da abinda ya faru kadda kice yau zaki koma gida dan nasan halinki da zuciya."

Taturo baki cikin shagwab'a tana magana k'asa k'asa "to ai halinmu d'aya dakai,
Yana jin abinda tace yayi murmushi ya girgiza kai yace "halin ya motsa yau kenan."

Ya juya kalli fateema da tayi tsaye tana kallonsu kamar gunki, yace "ke bakiga 'yar uwarki bane kika wani toge wuri d'aya kina zarar ido kamar wacce tayi k'arya."

Sai a lokacin fateema tayi dogon motsi domin jinta takeyi kamar ba'a hanyacinta takeba akan tsoro,
Ta matso kusa da dijama ta rik'a hannunta tana "fad'in sis sannu da zuwa."

Dijama tayi murmushi tana kallonta tare da binta da hararar wasa, tace "sai yanxun kika ganni."

Mahmud yace "ki kaita d'akinki tayi wanka ta huta snn kufito muci abinci."

Ta rik'o hannun dijama ta d'auki Jakarta suka nufi d'akin."

Suna shiga d'akin kai tsaye dijama ta fad'a kan gado tana fad'in "wash Allah na sis na gaji da yawa driven akwai wahala."

Fateema ta sauke ajiyar zuciya ta zaro ido tace "yanzun da kanki kika tuk'o mota tun daga kano har Abuja?"

Dijama ta mirgina ta janyo filo ta d'ora kanta a kai,
Tace "kin d'auka Kowa irinki ne ma tsoraci?

Fateema taja dogon nishi tace
"sis wlh naji dad'i da kikaci uban k'awayen Anty Yusra,
Kekinji irin magagganun da sukeyi suna zugata tare da bata shawarar banza."

Ashe dama yaya mahmud ba sonta yakeyi ba ya aureta."

Dijama tayi saurin mik'ewa zaune tana kallon fateema tace "bangane ba sonta yakeyiba."

Anan tashiga bawa dijama labarin duk abinda taji yusra na fad'awa k'awayenta a kan Mahmud."

Wani irin farin ciki dijama taji ta a cikinsa Wanda har ya kasa b'oyowa a fuskarta, tace amma fateema nayi mamakin jin Wnn maganar."

Ba abin mamaki bane da kanki zaki ganewa idonki a cikin gidan nan."

Fateema ta kuma nisawa ta kalli dijama tace "ni kuwa sis wnn irin kallo da naga kuna yiwa junanku dake da yaya mahmud na meye?"

Sai naga saura kad'an ku rungume junanku, ni dai fateema yau naga abin mamaki iri iri a gidan nan azal ta kawoni."

Dijama tayi dariya tace "ba wani kallo da kikaga munayi. illah gaisuwar da mukayi.
To kona ma kallesa ya kalleni sai me?"

Yaya mahmud nefa jinina,
d'an uwana Wanda nafi shak'uwa da shi akan kowa, karki damu da irin kallon da kikaga munayiwa junanmu."

Fateema tace "uhm ai na dad'e da gano ku mudai idan tayi wari maji."

***************

Mahmud shima yana shiga d'akinsa kai tsaye kan gado ya fad'a yayi rigingine yau jinsa yakeyi cikin farin ciki,
Wanda yasa shi ya manta da rashin kunyar da yusra tayi."
Babu abinda yake hangowa sai kwayar idon dijama a lokacin da ta kafeshi da su tana kallonsa,
Wani abunda yake hangowa a cikin idonta mai wuyar fasaltawa."

Kuma mirginawa yayi ya janyo fillow ya rungume tare da runtse idonta yana murmushi."

******************

Yusra kuka takeyi kamar zata had'iye zuciya ta keji, irin wulak'ancin da Mahmud ya mata a gaban wata banzar k'anwarsa wadda take zargin sonta yake."

Zata iya d'aukar ko wanne Irin wulak'ancin sa,
idan daga Ita sai shine a gidan,

Amma bazata tab'ata d'aukar yana wulak'anta ta a gaban mata 'yan uwantaba."

Shawarar k'awayenta ta fad'o mata a rai, idan soyayya kike nema an bud'e wani Sabon gidan mata akwai maxa duk irin wad'anda kikeso wad'an da zasu kasheki da soyayya har sai kin suma kindawo baki sani ba
a kan dad'i."

Murmushin da yafi kuka ciwo ta k'ak'aro tace "bana son ko wannen namiji mahmud nakeso Mahmud nake so na mallaka shi kad'ai nakeyiwa kallon namiji,

Amma yau zan tafi wurin dan naganewa idona ko dan nafita daga cikin b'akin Cikin da ke damun zuciyata."

Ta d'auki wayarta ta kira k'awayenta ta shiga basu hak'uri, a kan abunda ya faru tace suyi mata kwatancen inda gidan matan yake gata nan zuwa anjima."

Kuwa suka d'auka da shewa suna fad'in ko kefa, amma yaushe zaki zauna bak'in cikin d'a namiji ya kasheki da gatanki da kyawonki da komai naki."

Haba komai ai yawuce Sai kinzo hajiya kizubo kud'i a jaka dan hutawa, murmushi tayi tace "kud'i ba matsalata bane." Snn ta kashe wayar."

Misalin k'arfe 7:50pm
Mahmud yana masallaci domin Al'adarsa kenan duk lokacin da yatafi sallar magariba baya fituwa a masallaci sai anyi sallar isha'i,

Sai da Yusra ta kwatanci baya nan yana masallaci snn taci kwalliya ta fitar rai Cikin wasu k'ananun kaya Riga da wando wad'anda suka kama jikinta saika rantse da Allah kace ba musulma bace."

Gaba d'aya jikiรฑta sai da ta wanke she da turarunka snn ta d'auki wani d'an figigin gyale ta yafa a kanta ta sanya talkaminta masu tsinin gaske ta d'auki Jakarta tafito.

Gaba d'aya falon ba kowa a cikinsa suna kitchen suna hidimar abinci mahmud yace adafa masa tuwon samo da miyar kub'ewa d'anya,
dijama ce yau ke girkin gaba d'aya gidan ya d'auki k'amshi."

Yusra tayi ficewarta ba tare da Kowa ya gantaba,
Bata tsaya d'aukar motaba saboda mahmud zai gane gidan ya duba wurin ajiye motoci bai ga mota d'aya ba."

Hakan ta dinga tafiya a bakin Layin kasancewar unguwar GRA ce ba mutane sosai a cikinta,

Waya ta d'auka ta kira k'awayenta akan suzo da Mota su d'auketa gata nan a kan hanya tafito,

Ai kuwa Cikin minti 30 ta gansu a gabanta suka d'auketa suna Shewa suka nufi gidan Mata da ita."

Gidan mata babban gidane wanda baya misaltuwa a kan girmansa, da fad'insa kota INA d'akunane birjek da kayan more rayuwa a cikin su."
Gidan cike yake da Samari da 'yan mata ko wanne yana holewarsa,

Wurin ajiye motoci sukayi parking suka firfito Yusra sai kallon wurin takeyi kota ina tana mamaki domin wurin ya burgeta sosai."

A can ta hango wani shuga daddy babban mutum ya rungume budurwarsa ya matseta gam a jikinsa sai shinshinarta yakeyi ko ta INA ajikinta, yana kissing d'inta,

Runtse idonta tayi da ta kalle su' wani abinda taji har cikin ranta,

K'awayenta suna lura da yanayin da tashiga,
Sukace kisaki jikinki ki holewarki kinga irin shuga daddys d'in can sunfi Kowa iya kashe macce a soyayya saboda sunsan jikin macce, sunsan lungu da sak'o na macce. Sunsan inda zasu tab'owa macce taji dad'i harta some."

Kidiba kiga wancan yanda yake ma budurwasa harda fa lasheta yakeyi ta ko ina."

Yusra ta kuma tsuma a nan take sha'awarta ta motsa dama tana da buk'atar d'a namiji."

Suna nan tsaye gefe d'aya suna kallon duk Wanda ke shigowa da fita suna Kuma k'ara tsuma Yusra kafin sushiga wurin."

Alhaji Atiku ya shigo da motarsa a hankali Cikin gidan yanayi yana rage glass d'in motarsa yana kallon 'yan Matan dake zazzaune sunajiran masu tayasu."

A can nesa yayi parking ya fito da waya a kunnensa yana waya da wani abokinsa koma nace amininsa Wanda baya k'asar, jiya yadawo yake shaidawa Alhaji Atiku yadawo jiya yanzun hakan gashi a Abuja yaje gidansa anfad'a masa baya nan yanzun ya fito,

Dariya Alhaji Atiku yasaki yace "yanzun kuwa na fito daga gidan gani nan nataho wurin hutawa kashigo wurin kawai abokina kaima ka huta akwai mata kala kala masu zafi duk irin wacce kakeso sai ka darje. Ka zab'a"
Anan Alhaji Atiku ya shiga yimasa kwatance wurin, daga k'arshe sukayi sallama da cewa gayanan k'arasowa wurin yanzun."

Zaro ido Yusra tayi hankalinta a tashe ta Shiga Nuna Alhaji Atiku da hannu tana fad'in wanake gani kamar daddy na."

Suka had'a Baki sukace daddy ne mana,
Ai daddy yana zuwa wurin nan,
Ai wurin hutawar sa, kenan to Meye a ciki Dan kinzo a wuri daddy ya zo?"

Ai sai muke ganin ko wanne daga cikinku lalurarsa ta kawoshi Kuma ai bai gankiba kema ki d'auka Baki ganshiba,
Kowa tashi ta finsheshe,
Wlh daddy yana burgemu saboda kansa a waye yake, ba k'arya daddy yana burgemu."

Yusra bata k'ara tsinkewaba sai da ta hango budurwar Daddy ta rugo da gudu ta rungumeshi ai kuwa da sauri daddy ya kashe wayar hannunsa ya bud'e hannu biyu ya rungumeta,
Ya d'ago kanta ya Sanya bakinsa cikin bakinta,

Bata kuna tsinkewa ba sai da taga daddy ya d'auketa cak kamar jaririya ya nufi wani d'aki da ita yana dariya kamar gonar auduga."

K'afafunta suka kasa d'aukarta tayi saurin yin baya ta kai jingine jikin mota.

"Kinga yanda ake wayewa ko?"
Wlh daddy yayi rayuwar daddy tayi Kansa a waye yake inji k'awayenta."

Snn ko wacce ta nufi wurin saurayinta aka bar Yusra tsaye ita kad'ร i tana jimami."

Alhaji yasir naira abokin Alhaji Atiku ya shigo da motarsa cikin gidan, yashiga Kiran Alhaji Atiku ya fad'a masa gashi yashigo
amma ina Sam bai d'aukaba daddy ya hau network."

Wata kyakkyawar yarinya ya hango a wuri d'aya tsaye ita kad'ai,
Yayi parking da Sauri gefe. D'aya ya nufi wurinta yana lasar Baki,
Alhaji Yasir shima ba baya yakeba wurin Neman Mata fara gudu suke rabawa dashida Alhaji Atiku."

Kai tsaye wurin Yusra ya nufa d'auke da kalaman bakinshi wad'anda yake amfani dasu wurin yaudarar macce."

Cikin minti 20 ya saye zuciyar Yusra da kalamai masu Dad'i,

Anan take ya kama d'aki yarik'a hanun ta suka nufi d'akin,
Alhaji Atiku ya dawo cikin hayyacinsa ya yaga Kiran da abokinsa yayi ta masa,
ya tashi ya Sanya kayansa, ya d'auki wayarsa yafito yacewa budurwarsa ta jirashi yanzun zai dawo."

Fitowarsa ya hango Alhaji Yasir da wata tsaleliyar budurwa sunjuya baya suna tafiya,
Da alama d'akin da ke gabansu zasu shiga,

Ido Alhaji Atiku ya kure budurwar dashi yaga yanda take juya mazaunanta, hankalishi ya tashi cikin sak'an d'aya yaji yana buk'atar shima ya ganshi Tare da yarinyar,

Dama sun saba hurd'arsu. A tare
Suyi tarayya da macce d'aya,
a lokaci d'aya idan Wnn ya sauka sai wnn ya hau."

Ya Kama lashe baki da ya hango yanda Alhaji Yasir ya fara shafar d'uwawunta snn daga k'arshe ya d'auketa cak ya shige da ita d'akin."

Cikin Sauri Alhaji Atiku ya d'aga waya yakira Alhaji Yasir yace "waton daga kwada maka hanya har kazama d'an gari,

Wnn kyakkyawar fulawar da na ganga da itafa?."
Amma gaskya ta nuna har tayi ja." Idan ka tsinke furen cikinta Ka d'an aramun nima na tsinka."

Alhaji Yasir yayi dariya yace wnn fulawar ko kallonta bazaka kumayi ba, bare har ka sanya ran zaka tsinketa don Kuwa wnn tawace ni kad'ai bana iya had'ata da kowa,
Ya kashe wayar ya shiga sarrafa Yusra."

Ranar Sai da Alhaji yasir ya mayar da Yusra tamkar matarsa sai sarrafa yakeyi a yanda yakeso."

Ita ma sai kuwar dad'i takeyi saboda Alhaji Yasir yayi mata a yanda take son namiji ya kasance mata a fagen soyayya."







*Fad'ar Annabi ce duk abinda kayi wa 'yar uwani sai anyiwa taka 'yar, yana can yana b'ata 'yar UWANI , shima ana b'ata tashi 'yar*

๐ŸŒน *DEEJAMAH* ๐ŸŒน ( _'Yar gidan tsohuwa_ )๐Ÿ˜…




Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)






*56*






Mahmud kuma bayan ya dawo daga masallaci yaji gaba d'aya gidan k'amshin girki ya gauraye shi,

Babu Wanda ya fad'o masa a rai sai mommy idan tana yiwa daddy girki hakan zaka dinga jin gida ya gauraye da k'amshi kota ina."

Murmushi ya saki dan yasan wnn girkin dijama ne bana fateema ba,

Bai k'ara tsinkewaba sai da ya hau kan dining table,

Wani yawo ya had'iye tare da gyaran baki, dan kuwa har yaga nawar abincin yazo bakinsa."

Dijama ta taso ta shiga zuba masa abinci,
Ido ya bita dashi yana murmushi,
bak'a ramin burgeshi tayi ba,
domn yana matuk'ar son ya ganta ta sanya dogowar riga bak'a,
Wani irin kyau yake ganin ta Kuma k'ara masa."

fateema na kallon sa tana murmushi da ayar tambaya a bakinta."

Bayan ta gama zuba masa abincin ta tura masa a gabansa tare da zuba masa sassanyan lemun kwakwa mai sanyi Wanda rabon da yasha irinsa tun da ya baro kano,
Babu abinda yakeyi sai murmshi, a fuskarsa tabbas dijama renon mommy ce duk wani nau in kalar abincin mommy ta iya shi."

Fateema ta mik'e tsaye tace "bara na kira Anty Yusra ta fito muci abinci."

Dijama ta wurga mata harara tace "wlh bazataci abincin nan ba, matar da ta hana mun ruwa,
Har zan dafa abinci na bata taci tabd'i jam sai dai tafito ta dafa da kanta."

Mahmud baice komaiba sai lomar tuwonsa yake kaiwa a bakinsa yana lumshe ido."

Bayan sun kammala cin abincin ne suka dawo falo suka zauna suna kallo,

amma hankalin mahmud yana wurin dijama motsi kad'an idan tayi idansa na kanta. Jiyakeyi kamar ya saceta ya gudu."

Anan suka raba dare suna kallo Wanda Mahmud ya lura da
baiji motsin yusra ba wata zuciyar tace masa "wata k'ila bacci takeyi."

Sai da dijama ta fara hammar bacci snn ya tashi ya kashe kallon tare da yi masu sai da safe, sai da yaga sun shige d'akinsu,

Snn shima ya shige nashi d'akin yana kallon fuskar dijama yana murmushi yau yasan zaiyi kwanan farin ciki,

da ace ba aikin bincike sukeyi a office ba,
To babu abinda zai fitar dashi aiki gobe ba."

Domin yanaso ya ka d'ai ce daga shi sai dijama dan yana da tarin magagganun da zaiyi da ita."

****************

A ranar Yusra a can ta kwana,
Alhaji Yasir yaji dad'in kasancewar sa da ita Wanda har yakejinsa baya iya rabuwa da ita,

Itama Yusra gareta hakan ne taji dad'in kasancewa tare da Alhaji.yasir amma ba wai yana nufin ta fara sonshi ba ne A'a ita dai zuciyarta tana wurin mahmud shi kad'ai takeso baxata tab'a son wani nmijin kamarsa ba."

Alhaji yasir ya cika wa yusra jakarta da kud'i wad'anda shi kansa bai san iya adadinsu ba."

Yace ta d'aukar masa Alk'awari bazata kuma kula kowa ne namijiba sai shi kad'ai, idan tamasa haka yayi mata alk'awarin zai mata duk abinda take so a rayuwarta."

Kuma kada ta kuma zuwa wnn gidan, ta bari idan ya shigo zaiyi mata waya ta zo ta sameshi."

Murmushi tayi ta girgiza kai tace "ta yarda ta amince."

Basu rabu da junansu ba sai da safe misalin k'arfe goma na safe snn suka fito daga gidan ya d'aukota a motarsa ya kawo ta bakin layinsu ya ajiyeta,
Hankalinta a kwance ba wani tsoro a tare da ita, saboda tasan a dai dai wnn lokacin mahmud ya tafi wurin aiki."

Kai tsaye cikin gidan, tashiga Wanda gaba d'aya gidan babu abinda kakeji yana yatashi sai k'amshin turaren wuta,
tare da karatun Alqur'ani,

Dijama da fateema suna falo zazzaune suna hira suka ga shigowarta cikin wnn shigar, Wanda bazaka tab'a cewa matar aure bace,
Bako sallama ta rab'asu ta wuce tayi shigewarta d'akinta."

Kallo suka bita dashi suna mamaki, dijama ta mik'e tsaye tace "lallai yau saina koyawa wnn yarinyar hankali da tarbiya ya zata shi go mana gida babu ko sallama."

FATEEMA tayi saurin rik'ota ta ta zaunar da ita, tace "rabuda da ita sis bakiga irin shiigar da ke jikintaba,
Ina ganifa ba a
Gida ta kwana ba."

Dijama ta zare ido tace. "To gidan ubanwa ta kwana?"

FATEEMA tace "oh mata amma dai ki kyaleta yanzun ki barta sai wani lokacin."

*****************

Abba da mommy suna ganin dijama ta taje Abuja suka shirya suka tafi Dubai domin had'owa mahmud kayan lefe."

*****************

Khalil kuma tun lokacin da Ashanty tayi masa waya akan cewa sai ya kuma bata wasu kud'i wad'anda ke hannunta basa isarta a zubar da cikin."

Cikin azama yaje wurin Abba ya shirya masa k'arya akan karatunsa, akan cewa makaranta sunce a bada kud'i, zasu saya wani abin."

Abba mutum ne Wanda yasan zafin ilimi da mahimman cinsa,
Dan haka a kullum idan yana tare

Please Login or Register in order to submit comment