Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wlh yaya."

Ya kafeta da ido yace "karkiyi mun kuka, kifad'a mun kawai abunda yake damunki."

Tace "wlh yaya ba komai k'azafi ne kawai likita yake mun."

Yayi shuru na d'an wani lokaci snn ya nisa ya kira sunanta yace "ki daina sanya damuwa a ranta, idan kina buk'atar wani abun kiyi mun magana zanyi maki shi komai girmansa komai tsadarsa kinji ko."

Ta d'aga kai alamar "to."

Yayi murmushi yace "yawwa 'yar k'anwata Allah ya baki lafiya."

Tayi "murmushi tana kallonsa,
Snn yace "bara nayi sallah na dawo,
Tunda naga ke bakyayi."

Taji kunyar abunda yace "tayi saurin rufe fuskarta tana murmushi."

Washe gari sauki ya samu ga dijama likita ya rubuta mata takardar sallama,

Suka nufi gida da zuwansu gida batare da b'ata lokaci ba mahmud ya shiga yi masu shirin zuwa Abuja domin saura kwana biyu a d'aura aure sa

KA San cewar ya saya wa su mommy gida wanda zasu sauka a cikinsa a can Abuja

Hakan kuwa akayi suka d'unguma gaba d'ayansu har da Abba khalil ne kad'ai yace shi sai gobe zaixo, tare da abokinsa Ahmad,
Dukansu suka shiga jirgi suka nufi garin Abuja."

********************

An d'aura Auren mahmud da Yusra akan sadaki naira dubu d'ari biyar,

Inda ansha shagalin biki musamman b'angaren gidansu Yusra."

Anyi wa Yusra jere a gidan da mahmud ya saya da kud'insa gida yyi kyau sosai biki na yar gata shalelen daddy."

Duk dinner da akayi dawani Abu can da sukeyi mahmud ko lek'a wurin baiyiba yana kwance a d'akinsa cikin bak'in ciki da k'unci."

Inda itama dijama daurewa kai takeyi tana shiga mutane amma jinta takeyi kamar ta fad'i saboda damuwa."

Khalil kuma ansamu abokanan Amarya yan hannu sai murza barikinsu sukeyi dashi da Ahmad."

Duk wanda yaga Yusra yasan tana cikin farin ciki ta mallaki abin sonta farin cikin rayuwarta."

Tun dare aka kawo Yusra
gidan angonta mahmud,
Wanda tasha gyara na fitar Arxiki domin ta d'auki niyar sai ta mallaki mahmud ko yana so ko baya so."

Ta rigada da ta gama tsuma jikinta da gyara yadda ya kamata ba irin shirin da tanadin da bata yiwa wnn dare ba da mijinta da ma rayuwar aurenta gaba d'aya."

Tunda mahmud ya saka ko Kansa a falon gidan Wanda yake b'angarensa mallakinsa yaji wani irin k'amshi mai kashe zuciya da ta da hankali yana shigar sa yana ratsa shi,

Tuni yaji jikinsa ya mutu ya tsinci kansa cikin wani irin hali na son kasancewa da mace."

Wnn jarabben k'amshin yaji yana d'aga masa hankali,

Ya dafe kai tare da rufe ido yana tunani a hankali yake tafiya, sai kuma jin wani sabon k'amshi na daban yana ratsashi, runtse idonsa yyi had'ida bud'ewa.
Hannu yaji yana bin jikinsa ana shafashi tare da wani sabon k'amshi na daban,
Hakan yasa yyi saurin juyawa dan ganin ko waye."

Yusra ce tsaye gabansa tana yauk'i tayi wani irin bala'in kyau tare da shiga mai d'aga hankali da tsuma zuciya tana masa wani irin salo tare da murmushi mai jan hankali."


Ido yasa mata yana kallonta daga sama har k'asa duk inda macce ta kai tq kawo Yusra ta wuce hakan,

Ga wani salo mai tab'a zuciya da jiki da take masa to amma Sam baya jinta a zuciyarsa ko kad'an saima tsanarta da yakeji.

Duk kau da kai da bala'in namiji da jarumtar sa bai isa ya kau da kai akan Yusra ba musamman ma a yanayin da take yanxun wani irin sexy dress da ta saka mai ta da hankalin."

Mahmud bai kauda kai gareta ba kamar yadda ta zata sha wuya kafin shawo kansa da Jan hankalinsa,
Sai taga tun a matakin farko ta tafi da imanin sa ya biye mata yana mqta wani irin Shafa da sarrafa jiki wanda yafi wanda ita take masa."

Bata San cewa bayan jarunta da halitta mai kyau da Allah ya masa ba, yana da wani irin sirrin da duk 'ya macce da ta samu miji irinsa yana sarrafa mata jiki haka to bata da sauran wani damuwa a duniya."

Tabbas yasan sirrin tafiyar da jikin macce.

tuni ya gama rud'ata ta fita hanyacinta tana fitar da wani irin numfashi mai cike da shauk'i da sha'awa son kasancewa da shi."

D'agata yyi cak tana wani irin yauk'i da fitar da numfashi mai ta da hankali mai sauraro, d'aki ya nufa da ita ya jefa ta bisa gado ya ci gaba da sarrafata
jikinta ya gama mutuwa bata ko iya motsin kirki ba abin da take buk'ata illa taji mahmud a jikinta."

A lokacin da ta gama fita hayyacinta sha'awarta ta kai k'ololuwa wurin tashi ya zame jikinsa daga nata tare da mata wani mugun kallo ya juya yayi tafiyar sa ya fita ya bar mata d'akin."

Mahmud don Allah kar
kai min haka."

Bai saurare ta ba Ya mik'e ta bishi tana manne masa yayi saurin yakice ta ya jefar sai da tafad'i k'asa, tasa masa kuka."

Mahmud zan mutu in ka kyale ni a wnn halin. Zan mutu.
Mahmud ka taimakeni ni ga soyayyqrka ga sha'awarka ta d'aga min hankali fiye da tunanin KA."

Ya juyo ya kafa mata idanun da suke k'ara haukatata tuni ta k'ara rikicewa ya k'ara haukatata tuni ta k'ara rikicewa da shi."

Ta zurawa labbansa da faffad'an k'irjinsa ido tana kallo tana jin wani irin abu a jikinta hankalinta na kuma tashi."

Kuka takeyi sosai tana rok'on sa ya kasance da ita tasamu sauk'in abinda takeji."

Mugun kallo ya mata yace wnn abinda da kikeji sai dai ya kasheki ba wnn Daren kad'ai ba a ko wanne dare a kowanne lokaci da yanayi a cikin gidan nan haka zaki kasance cikin shauk'i da sha'awa baki da wanda zai kawar maki da ita,

Hakan zakiyi ta kasan cewa har sai ranar da kika gaji kika hak'ura da aurena,
Kije ki nemi wanda kika San zai iya kashe maki wnn wutar sha'awar da kullum sai na kunna miki ita a gidan nan sauk'in ki d'aya kiyi nesa dani zaki samu sauk'in jarabar dake damunki amma muddin kikayi kuskuren zuwa gabana zaki ci gaba da kasan cewa cikin wnn halin."

Ina so kisani har abada ba komai ake nema ake samuba,a rayuwa
Ni mahmud har abada ba baxaki tab'a samuna ba."

Shalele kike ko meye sunanki tun da har kina iya Neman Abu kuma ki sameshi ki bugawa mahaifinkin waya ki fad'a masa cewa a buk'ace kike."

Yana gama fad'i ya shigewarsa d'akinsa, yace "bazan rufe k'ofa ba in kina nemawa kanki wani tashin hankalin ki biyo ni."

Da gudu ta bishi tana fad'in " KA tausaya mun mahmud sai ta so ta shiga d'in sai kuma dawo Baya
tana magiya."

Ta duk'e k'asa tana murk'ususu wutar sha'awar mahmud tana Azalzalarta

Cikin hasata tace "sai na samu abinda nkeso mahmud ni ba mazan da nake muradi a waje a yanzun, mijina nakeso kuma shi nake sha'awa da muradi."

Mahmud sai na sameka sai KA kusanceni sai na mallakeka,
Sai na mallaki zuciyarka da gaggar jikinka ko ta tsiya kota arziki ko ta bala'i kota girma ko arziki KA saurara KA gani."

Yyi mata wani matsiyancin kallo yace "Abbanki zaki fad'awa ya fad'awa babana cewa nak'i kwanciyar aure dake, yasani na kwanta dole dake?"
Ko boka zaki bi ko malamai

Idan kina tunanin hakan kinyi a banza domin kuwa baki San ko waye mahmud."

Tasowa yyi ya zo daf da ita ya janyota ya rungumeta ya sanya harshensa a kunnenta ya shiga wasa da shi cikin wani salo, ai kuwa ta kuma birkicewa tana fitar da wani numfashi sama sama snn daga k'arshe ya yi jifa da ita gefe ya rufe d'akinsa yana jiyo nishinta da magiyarta."

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_ )😅




Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_ )





_BARKA Da Sallah my friends da fatan kowa yayi sallah lafiya cikin Aminci, Allah ya k'arb'i ibadunmu_



*Dedicated to*
*Autar Ummah*
*Manshart*
*Mariam Tijjani*
*Mum Muhibbat*
*Maman Fatima*
*Maman Sadeeg*
*Sarah*
*Billy Shantaly*
*Aisha A mohd*
*Biebedie*
*Salma*
*hafsy Mijina*
*Leemart*
*Maman Elham*

_Da duk wad'anda ban ambata ba kuna raina da fatar kunyi sallah lfy?"_






*38*

Nishi takeyi mai had'e da gurnani idonta a lumshe cike da sha'awa."

Da kyar ta d'aga kai ta kuma kallon faffad'an k'irjinsa Wanda ya ke kuma ta yar mata da wutar sha'awarsa, tayi k'arfin hali cikin zafin zuciya tace "Ba boka ba malami ba kuma zan fad'awa daddy naba, amma namaka Alk'awarin sai na samu abinda nakeso daga gareka."

Wani kallo ya kuma watsa mata mai d'auke da manufar bakida hankali,
Yace "Ina nan ina jiranki Yusra inga ta inda zaki mallaki ko da k'ara min yatsa na balle gangar jikina da zuciyata, kina da aiki babba kifitar min daga b'angare ina son inyi bacci."

Ganin bata niyar tafiya ya turo k'ofa ya rufe da k'arfi tareda wurga mata harara cike da tsana da kyamata."

Kai tsaye toilet ya shiga ya sakarwa kanshi ruwan sanyi tare da sauke ajiyar zuciya,
Yana tunanin abubuwan da zai dinga yiwa Yusra da zai sanyata da kanta zata nemi rabuwa dashi."

Wanka yakeyi yana jiyo sautin kukan ta tare da magiyarta a k'ofar d'aki tana dukan k'ofa a kan ya tai maketa ya kusance ta ko sau d'aya, ne,
ya fitar da ita cikin matsananciyar sha'awar sa wadda take addabarta takeji idan bai d'add'ana mata zumarsa ba a wnn Daren a yanda takeji bazata iya kai safe ba."

Ganin baya da niyar taimaka mata bare ya ji tausayinta hakan ta hak'ura ta nufi b'angarenta mararta na mata ciwo sai murk'usu takeyi."

A wannan daren Yusra tayi kwanan bak'in ciki da b'acin rai Wanda bata tab'ayi ba tunda uwarta ta haifeta, tashiga damuwa sosai kuka takeyi tana dukan gado,
jitakeyi kamar ta d'auke numfashi a she aduniya akwai abunda zata nema ta rasa?"
Meyasa daddy yayi mata k'arya yace duk abunda take so zata sameshi."

Ta d'aga murya da k'arfi cikin muryar kuka tace "daddy ina son Mahmud kazo kabani mahmud,
Mahmud ya zama nawa ya kusance ni a Daren nan."

Hakan ta cigaba da kukanta, har tagaji tayi shuru ta Shiga k'ullawa,
ta kunce ta sak'a wancan duk inda ta b'ullo sai taga ba fita."

Duk yadda ta d'auki Mahmud ya wuce hakan, Namiji ne namijin gaske kuwa ba k'aramin Abu ne zai iya tab'a shi ba."

Babban bak'in cikinta yadda soyayyarsa da sha'awarsa ke nuk'urk'usarta, hakan ta kasance tsawon dare ba bacci ta kunce ta k'ulla, bata da yadda zata samu sauk'i sai dai ta rufe ido tana tuno yanayin da Mahmud yasa ta ciki a lokacin da yake sarrafa jikinta."

A b'angaren Mahmud shima baiyi bacci ba, babu abinda yake tunani sai dijama a lokacin da yakeyiwa mommy sallama tana kusa da ita gani yayi ta sunkuyar da kai k'asa takasa had'a ido dashi hawaye na zuba a fuskarta."

Meyake damun dijama take kuka?"

Me akayi mata ne Wanda take shiga cikin damuwa, kadda ciwon zuciyarta ya tashi."

Da sauri ya lalubo wayarsa domin yana son ya San halin da take ciki a yanzun
number ta yashiga kira Wadda yake tinanin iyanzun tayi bacci."

Dijama kuma tun lokacin da mahmud yayiwa mommy sallama ya tafi,
Ta tsinci kanta cikin tashin hankali da damuwa, wanda ta rasa dalilin shigarta."

Kuka takeyi sosai fateema tayi tambayarta abinda ke damunta,
Kanta ke ciwo kawai tace mata."

Misalin k'arfe 2;30am kowa a gidan yyi bacci amma bnda dijama dake aikin kuka, tana tunanin yaya mahmud yau ne Daren farko sa yana can tare da matarsa cikin farin ciki."

Wayar ta taji ta d'auki ringing a k'ark'ashin pillow,
da kyar ta mik'a hannu ta d'auka tana mmkin waye mai kiran nata a cikin Daren nan?"

Sunan yaya mahmud tagani a kan screen d'in wayar,
Wata kalar ajiyar zuciya taja da k'arfi tasaki murmushi, kafin ta d'auki wayar har kiran ya tsinke."

Can kuma wani kiran ya kuma shigowa, da sauri ta danna wayar ta kara a kunnenta, gaba d'ayansu suka sauke ajiyar zuciya a tare snn.....

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_ )😅




Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_ )






*39*






Sai da suka d'auki tsawon minti biyar a hakan duk kaninsu suna jin saukar numfashin junansu a waya."

Snn mahmud yaja wata doguwar ajiyar zuciya Wadda ta sanya Dijama saurin runtse idonta ta lalubo pilow ta rungume a jikinta."

Da kyar ta bud'e baki Cikin dasanshiyar murya tace "Assalamu Alaikum."

Jin sautin muryarta d'auke da sallama yasa shi yyi saurin mirginawa daga kwanciyar da yake Zuwa rufda ciki snn ya amsa mata sallamar."

"Me yasa bakiyi bacci ba?"
Kin kuwa San ko k'arfe nawa yanzun?"

Shuru tayi batayi magana ba, tana tunanin to shima mai ya hana shi yin baccin bayan yau ne daren farkonsa tare da masoyiyarsa."

Jin tayi shuru, ya kuma nisawa ya kira sunanta cikin kulawa "Nana Khadija meyake damunki kike shiga cikin damuwa?"

Me kikeyiwa kuka d'azun a lokacin da nake yiwa mommy sallama?"

Me kike so?" Me yake damunki wanda yake sanyaki shiga cikin damuwa Wanda bazaki fad'awa kowa ba daga ciki kuwa har dani."

Shisshikar kukanta yaji yana tashi a kunnensa,
A razane ya mik'e zaune cikin tashin hankali
"Meya faru?" Ki fad'amun abinda yake damunki Wanda yake sanya ki damuwa kike kuka."

Cikin da sasshiyar murya tace "ba komai yaya."

K'arya kikeyi dijama akwai abinda yake damunki,
Karki manta da Wanda kike magana kike fad'amasa haka,

Muhmud ne Wanda ya reneki kamar yanda kika San uwa tana renon d'anta, ya ciyar dake ya shayar dake na kuma goyaki a bayana, to kisani nafi kowa sanin farin cikinki da damuwarki."

Nafi kowa sanin jin dad'inki da rashinsa, nasan abinda kikeso da Wanda bakyaso, nasan farin cikinki nasan bak'in cikinki."

Dijama akwai abinda kikeso Wanda kika kasa fad'i har yake Neman ya jefaki a damuwa."

Ki fad'amun shi, komai girmansa komai kud'insa komai mahimmancinsa nayi maki Alk'awarin a duk inda yake a duk inda ake sayar dashi ko ake nemoshi nayi maki Alk'awarin zan kawo maki shi domin farin cikinki

Kukanta ya tsanta tayi saurin kashe wayar gaba d'aya ta jefar da ita a gefen pillow taci gaba da kukanta."

Kiran wayarta yayi yajita a rufe,
Duk hankalinsa a she yasan tana can babu abinda takeyi sai aikin kuka agogon bango ya d'aga kai ya duba yaga k'arfe uku saura minti goma dare yyi sosai,
Jinsa yakeyi kamar yaje ya lallasheta tayi shuru ta fad'a masa damuwarta."

Hakan dai ya hak'ura ya kwanta cike da tunani da damuwa halin da dijama take cikinsa a halin yanzu."

******************

Washe gari tun k'arfe 8am ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda Wanda ta k'arfesa yayi kyau iya kyau sai k'amshin turare yake fitarwa,
ya fito, ya tarar da yusra zaune a pallow taci kwanliya cikin wasu k'ananun kaya wad'anda sukayi mata kyau Sosai rigar gaba d'aya k'irjinta a waje yake haka k'asan rigar duka cibiyarta a waje."

Tana ganin fitowar mahmud Wanda Dama shi take jira yafito ta nufeshi ta rungumeshi tare da sauke ajiyar zuciya."

Kallo d'aya Mahmud yyi mata cike da tsana yayi saurin cireta daga jikinsa tare da jefa ta a kan kujera yayi tafiyarsa."

Kai tsaye gida ya nufa masaukin SU mommy,
Da sallama ya Shiga gaba d'ayansu suna kan dining suna break fast,
Tsohuwa kuma tana kan kujera sai masifa takeyi a kan tunda suka taho garin Abuja bata sanya Khalil a ido ba."

Abba sai hak'uri yake bata yana kuma kwada kiran wayar Khalil ko Allah zai sa ya sameshi,
amsa d'aya ce wayarsa a kashe take."

Khalil yana can cikin hotel tare da abokinsa Ahmad hankalinsa a kwance 'yan mata uku ne a kansa ko wacce da inda take tab'awa a jikinsa,
Shima hakan gaba d'ayansu sai sarrafasu yake cike da kwarewa,
domin dukansu yana jinsu a dai dai a yanda yake son macce ta kasance."

Mahmud Ya durk'usa k'asa ya gaida mommy da Abba suka amsa masa cike da fara'a, snn ya juya ya gaida tsohuwa dake masifa tanayi tana cin goro."

Harara ta wurga masa snn ta amsa masa tace "kai kuma kamar wanda aka koro daga gidansa zaka yiwa mutane sammako hakan."

Yanzun nake cewa babanka ya kiramun wayarka kaida kasan cikin garin Abuja, kaje ka nemo d'an uwanka tun yinin jiya bamu sanyashi a idoba bama da labarinsa har kawowa yanzun da nake maka magana."

Murmushi Mahmud yyi yace "tsohuwa rigima to ki kwantar da hankalinki khalil yana masaukinsu lfy glau yake,
Yanzun safiya ta waye yanxun hakan bai tashi daga bacci ba, nan fa ba irin k'auye bane."

Ai kuwa ya kuma tunzura tsohuwa ta shiga masifa, "ai ko ubanka hassan gashi can a zaune a k'auye ya tashi."

Dariya mahmud yyi yace Allah ya baki hak'uri tsohuwa, tunda abin har da zagi
bari nakira maki Khalil d'in a waya yazo kibashi abinda zaki bashi."

Ya ciro wayarsa ya shiga kiran khalil, juyawar da zaiyi yyi ido biyu da dijama taci kwalliya cikin wata doguwar riga bak'a ta lullub'a d'ankwalin rigar Wanda yyi mata kyau kamar balarabiya, tunda ya shigo take kallonsa domin yyi mata kyau sosai, ido biyu sukayi tayi saurin d'auke kanta daga kallonsa ta sunkuyar da kai tace "yaya ina kwana."

Kallonta yakeyi cike da kulawa ganin tayi yar rama ta kuma yi fari tayi kyau,
ya amsa da "lfy glau."

Amsawar da yakeyi yyi dai dai da d'aukar wayar khalil yana fad'in Hello brother kuntashi lfy, yanxun muke shiri zamuzo mu gaida Anty Amarya kamin muwuce kano."

Mahmud yace kayi Sauri kazo gida yanxun hankalin tsohuwa ya tashi na rashin ganinka da batayiba tun jiya."

"Khalil yace "to meye ruwanta dani." nifa banason sa idon nan na tsohuwa fa, mahmud bai sarar ba Abba ya fisge wayar yace "khalil kanajina duk inda kake kayi maza kazo yanxun ina son ganinka
Cike da girmamawa yace "to Abba gani nan zuwa,
snn ya kashe wayar."

Mahmud ya maida kallonsa a wurin dijama dake zaune a kan kujera, akusa da ita yaje ya zauna k'amshin turarensa ya doki hancinta tayi saurin lumshe idonta,

Ya kafeta da ido yana karantar wani Abu a tare da ita, Wanda ita kuma tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa tana latsar wayarta a zahirin gskya gaba d'aya hankalinta ba a kan wayar yakeba yana kanta."

Cikin murya k'asa k'asa yanda ba Wanda ke jinsa yace "charting kikeyi da saurayinki Wanda yake sanyaki shiga cikin damuwa ko?"
Haba ni dai nasan kinfad'a tarkon so shiyasa kike ciwon zuciya."
Tashi kije ki had'o mun break fast snn kidawo ki fad'a mun ko waye shi snn a ina yake."

Narai narai tayi da ido cikin shagwab'a tace "wlh yaya ba dakowa nake chart ba diba KA gani,
Tashiga nuna masa wayar cike da shagwab'a."

Tsohuwa tayi ido biyu dasu tace "ke dijama tashi kibar masa wurin Dama nasan da zarar mamuda yayi ido biyu dake sai ya sanyaki kuka, ni dai narasa sanin dalilin da ya sa yake zaluntar ki. Kitashi daga kusa dashi nace,
Ko kallonta dijama batayiba hankalinta na wurin Mahmud tana nuna masa wayar alamar ya yarda da ita ba chating takeyi ba."

Mommy da Abba suna gefe d'aya suna kallon rigimar tsohuwa ba damar suyi magana."

Mahmud ya sanya hannu ya amshi wayar yace "jeki had'o mun break fast kidawo sai muyi maganar."

Da Sauri ta mik'e tsaye, tafara tafiyarta mai cike da rangwad'a da yanga,
Bata saniba ta taka talkamin tsohuwa tayi baya baya da sauri zata fad'i,

Hakan yyi dai dai dashigowar khalil cikin zafin nama mahmud ya rugo zai tareta amma ina khalil ya rigashi ya tareta ta fad'a kan jikin shi."

Ya mai da hannu ya rungumeta yana kallonta sama da k'asa cikin wani yanayi yana fad'in sannu Nana khadija."

Irin kallon da yake mata yasanya kowa hankalinsa ya koma kansa,
Wanda mahmud jiyakeyi wani abin yana taso masa kamar ya had'e zuciya yakeji.

Amma sai yayi kamar bai damuba ya koma mazauninsa ya zauna ya d'auko wayarsa yana dannawa."

Amma gaba d'aya hankalinsa yana wurin khalil da yake rungume da dijama."

Dijama ta rufe fuskarta saboda tsananin tsoro ta lafe a k'irjinsa duk a tunaninta yaya mahmud ne ya rungumeta,

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_ )😅




Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_ )




*wnn shafin gaba d'ayansa nakine Queen Mary UMMU SAFWAN nayinki kamar yanda kike yinta*






*40*





Tsohuwa ta zaro ido tare da rik'e baki tace "yau naga ikon Allah,
D'abi'ar yahodawa a gidan nan?"
abinda nake gani a TV nake tsinuwa akansa yau gashi a gaban idona.

Talkaminta ta lalubo ta wurgawa khalil tace "kai saketa Dan ubanka, KA ajiyeta nace,
KA wani rungumeta a gabanmu kamar zaka mai data a ciki."

Dijama najin hakan tayi saurin bud'e idonta sukayi ido biyu da Khalil tayi saurin fisge jikinta daga gareshi ta shiga ja da baya tana wurga masa kallon tsana, da gudu ta nufi d'akinsu kai tsaye ta fad'a kan gado ta fashe da kuka."

FATEEMA dake zaune akan madubi tana kwalliya ta juya ta kalleta tashiga tambayarta abinda ke faruwa,
Dijama tayi banza da ita taci gaba da kukanta, a ranta kuma tana tsinewa Khalil rungumar da yyi mata a gabansu mommy da Abba da kuma yaya mahmud

Tsohuwa ta kuma wurga masa harara tare da tsino baki tace "Harda wani zabura kakeyi domin katarota zata fad'i, kana tunanin
Kafi mamuda sonta ne, da kake k'ok'arin tureshi wurin tarbota."

Khalil ya juya ya kalli tsohuwa yace "tsohuwa matsala tsohuwa fitina, tsohuwa jaraba, inbanda sa ido irin naki meye laifina a ciki domin kawai na taimaki k'anwata zata fad'i don gudun kadda taji ciwo."

"Kai dallah rufemun baki marar kunyar banza da wufi
Ai duk laifin Hassan ne sai da nace ya had'a da kai da mamuda ayi maku aure yace kai baka isa aure ba."

To ai ga irinta nan idan kaje kajanyo masa magana ai sai yasan yanda zaiyi da kai."

Nidai idan zan koma k'auye k"afata k'afar dijama da ita zan zantafi Dan banga abinda ake tsinana mata a nan ba in banda mugunta."

Khalil yaja baya da sauri yaje kusa da Mahmud ya zauna yana fad'in "A'a tsohuwa karkiyimun baki,
duka duka ni shekarata nawa da za'ayimun aure, ni karatu nakeyi so nakeyi sai nafara yi maki Allura da kaina snn zanyi aure."
A lokacin matar da zan aura ta kammala karatunta."

Tsohuwa tace "sai dai kayiwa Hassan gaya can a zaune Allurar ba dai niba."

Abba ya nisa daga kallon da yakeyiwa khalil tun lokacin da ya rungume dijama yana karantar wani abin a tare dashi."

Ya shiga maganar zuci
Ko dai maganar mommy gaskiya ne da take cewa ayiwa Khalil aure."

Wata zuciyar kuma tace "khalil nawa yake,
meyasani a cikin aure,
Kawai taimakon k'anwarsa yyi batare da wata manufaba."

Mommy kuma tasan abinda yafi wnn ma khalil zai iya,
Sai dai ta furta a zuciyarta tace Allah ya shirya."

Abba yace "Allah khalil mudun ina kusa da kai idan KA kuma bari inna tana magana kana mayar mata sai na matuk'ar sab'a maka."

Sun kuyar da kai yayi yace Abba ayi hak'uri bazan kuma."

Snn ya durk'usa ya gaidasu suka amsa amma banda tsohuwa da sai masifa takeyi tana harararsa

Juyawa yayi ya gaida mahmud da ke ta faman dannar waya gaba d'aya ya rasa abinda yake masa dad'i, jiyakeyi zuciyarsa na suya.


Da kyar mahmud ya d'aga kai ya dubeshi yana murmushi ya amsa masa tare da tambayar abokinsa Ahmad da suka zo a tare,
Yace yana can masauki bai tashi daga bacci ba, nima tsohuwa nan ce ta tayar dani."

FATEEMA ce ta fito tayi kwalliyar cikin atamfa wanda tayi mata kyau,
ta durk'usa ta gaida mahmud da khalil,
Snn ta dubi mommy tace mommy mun shirya."

Mommy tace "ina ita ummin take ne?"

Fateema tace "tana d'aki yanzun zata fito
Bari naje na kirata."
Ta juya ta nufi d'akin."

Lallashin dijama tashigayi tare da kwantar mata da hankali ko da dai bata San abinda takeyiwa kuka ba, amma idan da sabo ta saba

Please Login or Register in order to submit comment