Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son nuna isa."

Fateema tace "to Abba yaushe zamutafi?"

Abba yace "kushirya gobe dafe saina kaiku domin akwai abinda zankoma idar."

Dijama ta d'aga kai ta dubi Abba, tace "Abba ni dai ayi mun hak'uri ba'a gobe zan tafiba, saboda kwana nan da ciwon kai nake kwana, idan Fatima ta tafi nan da kwana biyu zan biyo bayanta."

Abba yace "kina shan maganinki kuwa?"
Ta d'aga kai alamar "eh."

Ya dubi fateema yace "kishirya da wuri saboda tafiyar safe zamuyi."

Misalin k'arfe 1:30pm Abba ya isa garin Abuja, sai da ya fara biyawa ta gidan mahmud ya sauke fateema a lokacin mahmud baya nan yana wurin aiki
Dama baya so su had'u saboda yasan k'orafin mahmud d'aya ne a kan dijama wnn dalilin yasa jiya yayi tafiyarsa batare da sunyi wata doguwar magana ba,

Kai tsaye gidan Alhaji Atiku ya nufa domin aiwatar da abinda ya kawoshi."

Da sallama fateema tashiga gidan, ta tarar da Yusra zaune a falo sanye da dogowar riga kanta babu d'ankwali ta k'ure volume tana kallo."

Sallama fateema taketa famanyi Yusra bata san tanayiba, sai da taje kusa da ita ta dafata tana murmushi."

A razane cikin tsoro Yusra ta zabura ta zafga wani irin ashar tana kallon fateema cike da mamaki tace "ke kuma daga ina kika shigo mun gida ba sallama sai dai na ganki a gabana."

Fateema tace "yi hak'uri Anty nayita sallama bakijiba kin k'ure volume, ni sunana fateema ni k'anwar yaya mahmud ce, Abba yace bakida lafiya shine naxo na ganki ya jikin nki?"

"Naji sauk'i tace "aiko bakiyi mun bayaniba naga kama a fuskarki, ya hanya?" Dan nasan tafiyar mota kikayi ba ta jirgiba."

Fateema tace "Alhamdulillah, ina yaya mahmud?"

Yitayi kamar batajitaba taci gaba da kallonta,
Itama fateema kallon takeyi tana mmkin hali irin na Yusra na wulak'anci."

Fateema macce ce Wadda batason fad'a da tashin hankali tana da sanyi sosai gaba d'aya itace ta d'ebo halin mommy duk a gidan."

Suna Zane a hakan ba Wanda ya Kuma yiwa wani magana a cikinsu."

.Mahmud yayi sallama ya shigo

๐ŸŒน *DEEJAMAH* ๐ŸŒน ( _'Yar gidan tsohuwa_ )๐Ÿ˜…




Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)






*52*






Kai tsaye wurin kayan kallon ya nufa ya cire jonin gaba d'aya
ya juyo a fusace cikin masifa,
Karaf yayi ido biyu da fateema wanda tunda ya shigo bai lura da ita ba."

sakin murmushi yayi cike da mamaki ya shiga waige waige kamar Wanda yake neman wani abin."

Murmushi takeyi tace "yaya sannu da zuwa."

"Yawwa yace yana murmushin jin dad'in ganinta."

Baki Yusra ta saki tana kallon fuskarsa ganin yanda yake murmushi yana fara'ar
ganin k'anwarsa. ta karkace kai tana kallon fuskarsa tana murmushi domin murmushin da yakeyi ba k'aramin kyau yayi masa ba."

Ido suka had'a yaga ta kure shi da ido kamar wata mayya ya wurga mata harara yaje kusa da FATEEMA ya mik'a mata hannu yace "taso mushiga daga ciki k'anwata."

D'akinsa suka shiga tambaya ce tab a bakinsa,
Kan kujera yayi mata nuni da ta zauna."

Shima yaje kan gado ya zauna yana fuskantarta, "yaushe kika zo?"

"D'azun misalin 1:30pm."

"Waye ya kawoki?"

"Abba ne kuma yayi tafiyarsa."

"Ina dijama meyasa bakuzo tare ba."

"Da a tare zamuxo tace "batajin dad'i ta fasa zuwan."

"Meyake damunta ne."

"Wlh yaya nima cikin 'yan kwanakin nan narasa abinda yake damunta wani lokacin ta zauna ita kad'ai tayita kuka sai na lallasheta tare da bata hak'uri snn takeyin shuru"

"Karya kikeyi kinfi kowa kusanci da ita tunda a tare kuke kwana dan haka kinsan abinda yake damunta."

Shuru tayi batayi magana ba."

Yace "yawwa zan tambayeki kuma idan kika kuskura kikayimun k'arya daga baya na bincika nagamo gaskiya saina b'ata maki rai."

Ta d'aga kai alamar "to."

Yau she ne Abba ya sanya ranar bikin sulaiman da dijama?"

"Wata biyu."

"Harda ke za'a had'a yaushe kika samu miji?" Waye she?"

Ishaq ne d'an gidan Alhji sanusi."

Shuru ya d'anyi yana tunani."

Snn ya nisa yace "ita dijama tana son sulaiman d'in?"

Shuru fateema tayi ba batayi magana ba,

Tsawa ya doka mata yace "na fad'a maki muddun kikayi mun k'arya saina sab'a maki."

"Allah yaya bata sonshi kullum cikin kuka take akan za'a aura mata shi duk ta rame baka gantaba."

"To Waye take so?" Ai nasan bata rasa Wanda take so a ranta kuma nasan kinfi Kowa saninsa."

"Wlh yaya ban San kowa ba, bansan Wanda takeso ba asali ma duk Wanda yazo wurinta korarshi takeyi tace "anyi mata mijin aure."

Amma kuma na fad'a mata ta kwatar da hankalinta muddun kasan da cewa bata son sulaiman baxaka bari a aura mata shiba."

"Meyasa bata kirana a waya kuma idan na kira wayarta bata d'auka, sai dai ma daga k'arshe ta kashe wayar gaba d'aya?"

Ina ganin tun lokacin da ta tab'a kiran wayarka Anty Yusra ta d'auka, ko mai ta fad'a mata nidai bansaniba naga ta ajiye wayar tana kuka to tun a lokacin ta kashe wayart a gaba d'aya bata kira ba'a kiranta."

Mamaki yashigayi kwakwalwarsa ta d'au zafi, to me Yusra ta fad'awa dijama ne?" Da har ya sanyata kuka."

Uban waye ma yasanyata ta d'aukar masa waya?"
Yau zata gane kurenta Dan sai ta fad'a masa abinda tace mata idan ba hakan ba jikinta ne zai fad'a mata."

Tunani ya shigayi ta hanyar da zai b'ullowa lamarin."

Can yaja dogon nishi ya kuma kallon fatema yace "kinci abinci?"

Ta girgiza kai alamar A'a yace "OK tashi mutafi gidan abinci muci abinci daga nan nayo siyayyar kayan abinci,
tunda sai an kwana biyu zaki koma gida."

Kallo tabishi dashi cike da mamaki tace "yaya gidan abinci Kuma?"


Yace "eh ko bakyaci ne kin k'oshi?"

Tace A'a na dai ga Anty Yusra zaune a falo bata dafa bane?"

Dogon tsaki yaja yace "ke bana son yawan tambaya kinsan halina."

Zamanta kenan 'yar gatace babu abinda ta iya sai kallo."

Ya mik'e tsaye ya fita tabi bayanshi, a inda suka bar Yusra a nan suka same ta ta d'an gincira a kan kujera tana latsar waya da alama chatting takeyi tana murmushi."

Tanajin fitowarsu ta d'aga kai ta kallesu ta taci gaba da abinda takeyi Dan tasan halin mahmud yanxun tana masa magana zai disgata a gaban k'anwarsa ta renata."

FATEEMa tace "Anty muntafi sai mudawo."

"Adawo lafya tace ta kalli Mahmud tace dear ka yomun tsaraba."

"To yace batare da ya kalle inda takeba yayi ficewarsa,
Ko amsa mata d'in da yayi Dan ganin fateema ne saboda baya so ta fahimci irin zaman da sukeyi."

Gidan abinci suka nufa sukaci abinci suka k'oshi,
snn ya biya kasuwa ya sayo kayan abinci wad'anda fateema zata dinga dafa masu kafin ta koma ya San cikin "yan kwanankin da zatayi a gidan kud'insa zasu d'an huta da sayen abinci."

Koda suka dawo ana kiraye kirayen sallar la'asar,
Yusra bata falon tare suka shiga kitchen yanuna mata yanda zatayi aiki da kayan wurin,

Har zai fita ya kuma dawo yace "muje na nuna maki d'akinki kishiga kiyi sallah, dan nasan Yusra bata nuna maki."

Bayan ya kwada mata ne,
Yace "tuwon shinkafa nakeso kiyimun miyar wake,
Kuma ki tsaya Ki kwantar da hankali yanda zaiyi dad'i Dan nasan dijama tafiki iya abinci."

Turo baki tayi tace "Allah ni dai bata fini iyawaba sanin da kayi mun."

Murmushi yayi ya fita tare da janyo mata k'ofa." Yanufi masallaci."

Bayan ta kammala girkin ne tajera a kan dining taje d'akin Yusra domin ta kirata."

Da sallama ta shiga d'akin tareda tura k'ofa,
Kwance take akan gado tana waya tana dariya da Alama da k'awayenta takeyi, tana ganin FATEEMA tace "gata nan ma tashigo har d'akina ina zuwa bari naji abinda ke tafe da ita, sai anjima sai goben idan kunzo dan Allah kuzo gaba d'ayanku. Snn ta kashe wayar."

Gaban fateema ya shiga fad'uwa dan ita har ga Allah tsoron Yusra takeji, ta d'an runsuna tace "Anty Yusra kifito muci abinci."

Ta ya musta fuska tace "wni irin abinci kuma?"
Nifa banacin wani kalar abinci idan bana gwangwaniba,

Amma kije gani nan zuwa."

Har Fatima ta kai k'ofar d'aki Yusra tace "Am meye ma sunanki fateema ko?"
Idan kink'are cin abincin kizo ki gyaramun d'akina."

To fateema tace a ladafce snn fita."

Bayan sungama cin abincin ne, wayar fateema dake kusa da yaya mahmud ta d'au ringing da sauri ta mik'a hannu ta d'auka Dan tasan dijama ce ke kiranta ringing d'inta daban yake."

Mahmud shima ya fahimci dijama ce ke kiran, ya gyara zama ya k'ure fateema da ido yana son jin abinda suke cewa."

Jiyayi fateema na fad'in lafiya k'alau' yaya mahmud gashi nan zaune,
Ya fahimci wato tambayarsa takeyi, amma bata iya kiran number sa kuma shi idan ya kira tata a kashe yakejinta, me take nufi ne?"

Yana cikin tunanin yaga fateema ta mik'e tana magana da ita tanufi hanyar d'akinta tana dariya, binta yayi da kallo ya girgiza kai ya tashi ya fita zuwa massallaci domin yin sallar magariba."

Dijama take tambayar fateema ya taga yanayin gidan,
Ina wnn marar kunyar take?"
tana nufin Yusra."

Ai Kuwa fateema tashiga bata labarin tin zuwan ta gidan ko wurin zama bata bataba sai da ta zauna dan kanta bare tabata ruwan sha ko abinci,

Wlh sis kwata kwata yaya mahmud baiyi dacen Mata ba, bata da mutumcin ko kad'an keni wlh har tsoronta nakeji."

D'azun da nashiga d'akinta nafad'a mata tafito muci abinci, waya na sameta tanayi ina ganin da k'awayenta takeyi ai kuwa ta shiga fad'a masu ganinan na shigo a nan take sukayi sallama a kan sai gobe zasu zo nan gidan."

Tsorona Allah nidai kada suzo suyi mun duka."

Dijama ta lalubo wani ashar ta zunduma tace "amma wlh sis ke banza ce, matsoraciya."

Banyi niyar zuwa garinba saboda wani dalili,
amma yanzun kinsa naji inaso na ganni a cikin garin."

Waye ita zata hana maki wurin zama bare ruwan sha."

Na rantse da Allah mudun nazo gidan da hannunta sai ta d'ebo ruwa tabani nasha."

K'aryar rashin kunya takeyi, ko a cikin marasa kunyar ita ba komai bace."

A da na cire rigar rashin kunyata na ajiye,
Amma gobe zan d'auketa na saka na taho garin abuja da ita,
Kuma karki kuskura kifad'awa yaya mahmud zanzo."

Batajira amsar da FATEEMA zata bata ba ta kashe wayar."

๐ŸŒน *DEEJAMAH* ๐ŸŒน ( _'Yar gidan tsohuwa_ )๐Ÿ˜…




Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)






*53*





Fateema kuma jikinta ne ya soma rawa jin dijama tace "zatazo gobe,
tasan halin dijama bata d'aukar raini ita kuma bata son tashin hankali."

Wayar dijama tashiga kira ta fad'a mata kartazo tayi zamanta
tajita a kashe kamar yanda tasaba kashe waya a koda yaushe sai dai idan ta buk'aci neman mutum xata kunna ta kirashi da zarar sun k'are maganar da sukeyi zata kasheta gaba d'aya ta ajiye,
to ko yanzun ta kashe wayar gaba d'aya."

Ta gumi ta rafka kamar wadda akayiwa mutuwa tana tunanin zuwan dijama a gobe.'

Tana hakan yaya mahmud ya turo k'afa ya shigo d'akin kai tsaye wurinta ya nufa ya zauna a gefen gadonta yana kallonta yace "fateema d'axun da dijama naga kuna waya metace maki."

"Fateema ta d'an kallesa,
tana nazarin wani abu a ranta tace "shi dai yaya mahmud da zarar ya zauna baya da wata fira sai ta dijama,
To yanzun kuma meye ruwanshi da maganar da sukayi a waya?"

Katse mata tunani yayi da yace "amma ina ganin ke ba kurma bace bare na tambayeki kiyi banxa da ni."

Ke wai meyasa meki naganki a lokaci d'aya duk kin firgice kamar ba'a hanyacinki kike ba, lafiya?" meyafaru?"

"Ba komai yaya cemun tayi tana gaida kai kuma idan zan dawo nayo mata tsaraba."

"Batace zata zoba kenan?"
Tayi masa shuru ba amsa sai zarar ido takeyi kamar wacce tayi k'arya."

"OK kiramun ita da wayarki kibani muyi magana ko Zata d'auka,

Ba musu ta d'auki wayar ta danna number dijama had'ida danna hands free
" sweech of ake cewa wayarta a kashe take."

Runtse idonsa yayi cike da jin haushi da b'acin rai,
Babu Wanda yakejin haushinsa sama da Yusra Dan duk ita ta janyo masa haka."

A fusace ya juya ya fita daga d'akin kai tsaye d'akin Yusra ya nufa Wanda bai tab'a shigarsa ba tunda aka kawota gidan"

.Tana kwance tana chatting a wayarta, sanye take da wata fitinanniyar rigar bacci da ita da babu duk d'aya."

Tana ganinsa tayi saurin ajiye wayar tana murmushi jin dad'in ganinsa har cikin d'akinta."

Mik'ewa tayi zaune ta kuma zame rigar baccin daga k'irjinta boobs d'inta gaba d'aya suka bayyana, tana wani lankwร sa da jiki tace "dear lafiya kaxo da kanka aida kirani nazo."

Kallon tsana yabita dashi ya kuma matsawa kusa da ita ya sanya k'afarsa wadda yake sanye da talkami ya take d'aya k'afarta "yace ubanwaye yasa kika d'aukar mun waya da har za'a kirani ki d'auka."
Me kikacewa dijama a waya lokacin da takirani."

Ya kuma danne k'afar da k'arfi ya murza."

Wata wahalalliyar k'ara ta saki tana "fad'in waye dijama ni ban ma santaba, kuma ni ban d'auki wayarka ba."

K'ara take k'afar yayi ya sanya Hannunsa ya janyo gashin kanta ya rike da k'arfi, ai bata San lokacin da tasaki k'araba."

"Fad'a mun abinda kikace mata a waya?"

"Wayyo Allah na na Shiga uku sakeni xan fad'a maka."

Yak'i sakinta "cemata nayi baka da lokacin ta saboda kana kan network."

Dan Allah kayi hak'uri, kada karyamun k'afa."

Ransa ya kuma b'aci ya kuma murza k'afar da k'arfi tare da fisko gashin kanta snn ya d'agata ya kalleta a wulak'ance yace "idan ke mayyace sai dai ki mutu ko kuma kicinye kanki dan kuwa bazan tab'a ciyowa gareki ba,

Dubeki kidubi nakasasshen jikin nasha fad'a maki babu abida zanyi da jikinki bare har na hau network d'in da banaji bana gani."
Ita wacce kika fad'awa hakan nafi son talkaminta d'aya a kanki."

Ya fito a fusace yafad'a d'akinsa had'ida turo k'ofa da k'arfi."

Kuka takeyi sosai k'afarta na mata zugin zafi, tare da kanta,
Ga kuma zafin kalaman da mahmud ya fad'a mata,
Talkamin wata 'yar k'auye yafita daraja a wurinsa."

Wani irin tsanar dijama taji ta kuma lunkuwa a ranta."

****************
Dijama kuma tana gama waya da fateema jitayi gaba d'aya ciwon da takeji ta warke, burinta d'aya ta ganta cikin garin Abuja."
.
Durowa tayi daga kan gadon da take kwance a kai ta nufi falo domin sanarda Abba cewa tanaso taje gidan yaya Mahmud gobe kuma da kanta take so tayi driven."

Abba da mommy da Khalil suna zaune a Palo Abba yana tambayar Khalil ya jarabawa Khalil ya sunkuyar da kai cikin ladabi idan kika ganshi sai KA rantse da Allah ko hannun a ka Sanya mashi a Baki baya.iya Cizo,
Yace "Alhamdullillah Abba ai munkusa kammallawa."

Abba yace "Allah yasa a fito da sakamako mai kyau."

Ya 'amsa da "Ameen."

Dijama CE ta fito sanye cikin hijabinta har k'asa tana ganin Khalil ta had'e fuska bata ko kalli Inda yakeba saboda ta tsani irin kallon da yake mata kamar wani maye."

Khalil yana ganin fitowarta ya k'ureta da ido yana kallonta "shi dai a duniya yana tsananin son Dijama,
Sabida na tsuwarta da kyawonta uwa uba tana da cikar halitta irin na manyan mata wad'anda namiji zaiji dad'in hutawa dasu,
Snn tana da wani sirri Wanda ba Kowa ya San dashiba sai wanda ya kware wurin sanin macce."

Kusa da Abba ta zagaya ta zauna ta runsuna ta gaidashi tare da mommy ta d'an juyar da kanta wurin Khalil shima ta gaida shi tun kafin ta rufe bakinta yayi saurin amsa mata gaisuwa tare da tambayarta ya hutawa?"

Banza tayi dashi tayi kamar batajishiba."

Abba yace "Ummi ya k'arfin jikin?"

Tace "Alhamdulillah Abba naji sauk'i sosai babu abinda yake yimun ciwo a yazun."

Khalil "yayi karaf yace "Allah ya k'aro maki lafiya mai amfani."

"Gaba d'aya falon suka amsa da "Ameen."

Dijama tace "Abba zuwa nayi na fad'a maka tunda naji sauk'i
gobe INA so zanje Abuja gidan yaya mahmud nasamu FATEEMA a can."

Abba yace "ba komai Allah ya kaimu goben,
To amma sai dai Wanda zan samu ya kaiki saboda kinsan bana so kuna shiga motar haya."

Khalil yace "Abba kabarshi zan kaita goben."

"Jarabawar da kukeyi a makaranta fa?"

"Ai Abba ba matsala zan iya zuwa na kaita na dawo."

Dijama tace "Abba Wnn karon inason
Nayi driven da kai na yanda zan lallab'o har naga na kai."

Amma Abba idan akace yaya Khalil zai kaini ko mai zai iya faruwa domin ko shi kanshi idan yana tuk'i baya tafiya a hankali."

Abba yace "haka ne ummi,
Kuma kullum ina masa magana a kan yawan gudun da yakeyi a mota,

Tashi kitafi ki fara shirin gobe sai kiyi tafiyar asuba kafin Azahar kin kai, Allah ya kiyaye ya tsare hanya.

Abba ya kalli Khalil da yacika fam saboda jin haushi yace "kai Khalil kaje KA duba mata mortar da zatayi tafiya da ita goben mai lafiya idan babu mai kaje ka zubo mata Wanda zai kai ta ya kuma dawo da ita."

"To ya amsa." Tare da tashi ya fita yana turo baki. Cike da jin haushi."

*7:00am*
Dijama tayi shirinta cikin tamfarta mai surkin ja da tsanwa, d'inkin Riga da siket Wanda sukayi mata kyau d'inkin yayi dai dai da jikinta,

Bata d'aura d'ankwaliba illah ta d'auko d'an k'aramin gyalenta ja kalar atamfarta ta lullub'a akan gashinta wanda yasha kyara da mayukan gyaran kai masu kyau da k'amshi,
tajashi gaba d'aya a bayanta ta sanya babban ribon ta d'aureshi a tsakiyar kai yayi mata kamar tayi acuci maza ta d'auko Jakarta tare da talkaminta suma jajaye ta saka,
Ta kuma feshe jikinta da turarunka masu k'amshi snn ta d'auko wani k'aton glass d'inta ta saka a fuskarta Wanda ya Kuma fitar mata da Kyan fuskarta tafito hamshak'iya 'yar boko maiji da kanta."

Ta fito hannunta d'aya d'auke da hand bag d'aya Kuma janye da akwatin kayanta,

A falo ta Tatar da Abba da Momy suna zaman jiran fitowarta,

Suna ganin fitowarta suka rakata har bakin mota suna mata addu'a sai da suga tafiyarta suna d'aga mata hannu snn suka juya suka koma ciki "

Dijama tana ganin ta fito ta kunna wayarta ta kira fateema ta shaida mata yanzun ta taso tana kan hanya."

Fateema tashiga jin dad'i da murna wani b'angare kuma gabanta ya shiga fad'uwa ita dai bata son tashin hankali."

Yusra kuma koda safiya ta waye k'afarta ta kumbura a inda mahmud ya takata wurin yayi ja sosai ga wani irin ciwon kai dake damunta saka makon gashin kanta da mahmud yaja da k'arfi."

Duk yinin yau bata lek'o wajeba, fateema ce duk tayi aikin gidan,
Ta shiga hidimar d'ora abinci "yaya mahmud yace dambun shinkafa yakeso yaji kayan lambu irin yanda mommy takeyi."

Tana kitchen tana aikinta taji sallamar k'awayen Yusra sunshigo,

Tun daga kicin d'in tashiga amsa masu sallama tana masu snnu da zuwa."

Wani kallo suke jifarta da shi na wulak'anci,
Snn d'aya daga cikinsu Wanda daga ganinta tafisu masifa ta doka mata tsawa tace "ke INA matar gidan Wanda take da mallakin gidan bake ba 'yar ciku tsere."

Fateema tace "Allah ya baku hak'uri tana ciki ta Nuna masu d'akinta."

Tana ganin k'awayenta suka b'arke da kuwa da shewa, ta mik'e tana d'angisa k'afa suka fito falo gaba d'ayansu."

Cike da mamaki suke kallonta ganin k'afarta ta kumbura idonta yayi ja kamar wacce taci kuka ta gaji."

Suka Shiga tambayarta "meyake damunta tawani kod'e ta rame kamar wacce bata da lafiya. Ga Kuma ciwo a k'afarta wurin har ya kumbura."

"Hmmm nishi ta sauke tare da dafe kai,
Tace "ai kunfi Kowa sanin Matsalata a duniya mahmud ne."

Ina son Mahmud INA son in mallaki mahmud INA son mahmud ya zama nawa mallakina Amma mahmud baya sona,
Ku bani shawarar hanyar da zanbi ya soni na mallalesa na d'ad'dd'i zumarsa."

Mere Baki sukayi suna kallonta,

Suka had'a Baki suka ce "lallai kuwa kina da babban aiki a gabanki."

Yaushe Rabon da muga ana irin Wnn soyayyar wahala?"

idan kina ajiye wata soyayya can gefe kifito ki wataya ki ajiye,
Ga Maza nan a gari sai kin za b'a wad'anda kikeso kiyi huld'a dasu wad'anda zasu cire maki wani kwayin Mahmud."

Malama ki kifito muje ki wataya an bud'e wanin gidan mata,
Duk Kalar namijin da kike so zaki same shi a gidan,
idan kuma soyayya ce,
akwai Samari masu Jini a jiki wad'anda zasu kasheki da soyayya wadda har sai kin suma kin dawo Baki saniba akan dad'i."

Tayi shuru tana saurarensu da Alama magagganun su sun fara Shigar ta."

Me Kuma kika yimasa yaji maki ciwo a k'afa?"

Ai kuwa tashiga basu labarin dalilin "akan wata 'yar uwarsa 'yar k'auye baku ga pic d'inta wayarsa ba Wanda ya d'auke ta a k'auyen."

Tabd'i jam yanzun akan 'yar k'auye yayi maki wnn mikin?"

Allah ya sauwake mudai kunna nama kid'a mucashe kafin yadawo."

Ai Kuwa ta mik'e ta kunna masu suka rud'u gidan da kid'e kid'e kamar club."

Duk magagganun da sukeyi FATEEMA tana kicin tana saurarensu.
Cike take tana mamakinsu da ban al'ajabi, tana Gudun kartayi dogon motsi su sameta a kicin d'in suyi mata duka."

*1:30 pm*
Dijama tayi parking a harabar gidan mahmud,

tun daga harabar gidan kakeji duma na tashi kamar club,

Rik'e Baki tayi tace "ikon Allah lallai Wnn Yusra ba k'aramar shed'aniya bace."

Sai da ta gyara parking d'in motarta snn ta bud'e Jakarta ta d'auko turare ta kuma feshe jikinta da shi,
Snn ta kuma gyara zaman glass d'inta a fuskarta ta d'auko cingom a jakarta ta saka a baki snn ta bud'e mortar ta fito."

Tafiya takeyi Cikin isa da yanga hannunta d'auke da hand bag d'inta tana cin cingom tashiga gidan.

Kai tsaye babban Palon gidan ta dura Inda taji kid'a nata shi.

Batayi sallama ba dan Tasan kotayi sallama bajinta zasuyiba,
Mata tagani cike a falon suna sharholiyarsu, basu ma ganta ba,
kai tsaye wurin TV ta nufa takashe."

Gaba d'aya ido yayi kanta suna kallonta cike da mamaki Kun San dijama jinin mahmud ce Allah yayi masu kwarjini,

Ido kawai suka zuba mata suna kallonta tana cin cingom.'

Itama kallon nasu takeyi cikin glass d'aya bayan d'aya, snn ta tako cikin k'asaita tazo kusa da yusra ta zauna."

Ta kalleta da kyau tayi murmushi tace "dama anfad'a mun idan bak'o Yazo gidan nan baya Samun wurin zama bare ruwan sha."

Nasan kobaki sanniba kinga fuskar mijinki a tare dani,
Dan kuwa idan kika Ganni tamkar kinga yaya mahmud,

Da farko dai ni sunana Nana khadija ni bak'uwa ce a gidan nan k'isa nakeji kibani ruwa na sha."

Yusra da ta cika tana kallon dijama, Dan ko bata fad'a ko ita waece ba ta gane ta.

Tace "ba sai kinyimun bayanin kankiba naganeki dijama 'yar gidan tsohuwa 'yar k'auye, sai Kuma me?"

Dijama tayi murmushi tace "naji dad'i da kika ganeni wnn ya nuna mun cewa kina da labarina
Hakan yana nufin inada matsayi a gidan nan."

Inajin k'isa kibani ruwa na sha."

"Baki isaba,
Baki isa naje ni yusra na d'ebo wa 'yar k'auye ruwa tasha ba."

Murmushi Yusra tayi tace "yanzun zan nunamaki cewa ni na isa."

Jakarta ta bud'e ta Ciro dalleliyar wayarta ta danna lambar yaya mahmud."
Ta sanya handsfree."

Mahmud dake Zaune a office yana aikin bincike,
Amma gaba d'aya hankalinsa da tunaninsa suna wurin dijama,
Ransa yana b'aci a duk lokacin da yakira number ta yajita a kashe."

Wayarsa yaji tana ringing sai da ja dogon tsaki snn ya cirota a aljihunsa Dan ganin ko waye ke nemansa."

Number dijama yagani a kan screen d'in wayarsa,
Wani murmushi ya saki had'eda sauke ajiyar zuciya,

ciki sauri ya d'aga wayar ya kara a kunnesa yana murmushi,

Muryar dijama yaji,,,,,,



*washi hannuna nagaji*

๐ŸŒน *DEEJAMAH* ๐ŸŒน ( _'Yar gidan tsohuwa_ )๐Ÿ˜…




Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)






*54*






Tana fad'in "Hello Yaya barka da hutawa ya aikin?"

Cikin sauri Mahmud ya kuma yin murmushi yace " my blood sister lafiya k'alau yakike?"

Tace lafiya k'alau,
Zai kuma yin magana tayi saurin ka tseshi,tace "yaya gani a gidanka yanzun na sauka na taho ina jin yunwa da k'ishirwa,
Amma Anty Yusra ta hana mun ruwan sha, bare abinci,

da nayi mata magana ce mun tayi ban isa ta bawa 'yar k'auye ruwan sha ba."
Wann ya nuna mun cewa bana da daraja da wani girma a gidan nan tun har za'a iya hanamun ruwan da zan sha a matsiyana na wanda tayi tafiya."

"What." Yace Cikin tashin hankali mahmud yace "dijama yanzun haka maganar da kikeyi kina cikin gidana?"

Murmushi tayi had'ida yin fari da ido tace "ina ciki yanzun haka yaya."

Yace "OK kije kusa da ita yusra ki sanya handsfree zanyi magana da ita."

Tace "ai ina kusa

Please Login or Register in order to submit comment