Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'akinta."

Duk abunda sukeyi Alhaji Atiku yana kallonsu ta k'ofar d'akin sa yana kuma k'arewa fareeda kallo yana had'iyar miyau."

Misalin k'arfe 10pm kowa dake wurin ya shige ya kwanta, haka itama Fareeda bayan ta gama waya da mijinta taji ya sauka lfy, snn hnkalinta ya kwanta, suka gama hirarsu snn sukayi sallama."

Taja doguwar ajiyar zuciya,
Ta d'auko Ammar daga k'uryan d'aki ta shinfid'a katifa a falo ta kwantar dashi tare da bud'e k'ofa domin susha iska sakamakon zafin da akeyi kuma ba wutar NEPA."

Itama kwantawar tayi bata ankaraba bacci ya d'auketa."

A can cikin baccinta taji kamar ana shafata,
Da sauri ta bud'e idonta domin tabbatarwa kanta, ai kuwa ido biyu sukayi da Alhaji Atiku daga shi sai jallabiya da gajeren wando."

Zatayi yunk'urin guduwa ya tarota ya rungumeta yana sauke wani irin numfashi,

Yana fad'in "karki gujeni fareeda tun lokacin da na d'ora idona a kanki naji nakamu da matsannaciyar sha'awarki, ki Amince dani zakiji dad'ina,
Zan mallaka maki duk abunda kike buk'ata a rayuwa dake da iyayenki da mijinki sulaiman dukanku zakuji dad'i domin zan wadataku zan mayar daku abun kwatance a gari, daga wnn ranar bazaku tab'a tsayawa dogaro ga Albashin sulaiman ba."

Idan kuma kikak'i Amince mun to kisani rayuwar mijinki abun sonki sulaiman tana cikin had'ari mutuwa ko rayuwa."

A razane ta kalleshi, hankali tashe,

Snnu a hankali ta xame jikinta daga nashi tace "banason mijina ya mutu, INA son mijina."

Yasaki dariyar samun nasara, Dama duk matan da yake ma'amala dasu da mutuwar mijinsu yake masu barazana sai kuwa ya samu sa'ar miyan buk'atarsa."

Yace "yanzun kuma rayuwar mijinki tana hannunki."

Ta girgixa kai tace "na Amince bara namayar da Ammar k'urya na kwantar dashi na fito."

Yana murmushi yana lasar baki yace "ina jiranki."

Ta duk'a ta d'auki Ammar tanufi bithroom dashi, tana Shiga ta rufo k'ofa had'ida sanya sakata da key. Ta fashe da kuka tana fad'in Azzalumi Allah bazai barka ba."

Har Abada bazan tab'a amincewa da mummunan nufinka akaina ba",
kuma kasani rayuwar sulaiman tana wurin Allah ba wurinka ba fasik'i kawai mazinaci."

Alhaji Atiku yashiga dukan k'ofa yana fad'in fareeda bud'e kiji nafasa yimaki komai,

Sai ma tayi shuru ta daina yin mgana illah ta rungume Ammar taci gaba da kukanta."

Ganin batada niyar bud'ewa ransa ya b'aci ya juya ya kalli katifar da ta tashi akanta a dai dai Inda ya Tarar da ita a kwance,
Dai dai wurin yaje ya kwanta ya kefe yana kuma jin wutar sha'awarta tana fisgarshi."

Tanajinsa bai fita daga d'akinba tanajin yanda yake sauke wani irin nishi Wanda baya misaltuwa,

Har bacci ya d'auketa,
Sai kusan sallar asuba snn ya fita ya koma b'angarensa. Da sak'e sak'e a ransa, akanta, shine bai samu natsuwa ba sai da ya kwanta bacci yayi mafarkin fareeda yana biyan buk'atarsa da ita snn koda yatashi yasamu natsuwa."

****************


Rashin dawowar Abba da wuri shi yasanya mahmud ya kwana a garin kano."

Misalin k'arfe 10am yafito daga wanka shiri yakeyi domin ya tarar da Abba kadda ya kuma fita basuyi maganar da zasuyiba, domin yau yakeso ya koma bakin aikinsa."

Bayan ya kammala shiryawa yayiwa mommy waya yace "aturo masa dijama takawo masa break d'insa,

Mommy tace ai tunkafin ya tashi daga bacci dijama da fateema suka tafi makarantar islamiya."

Murmushi yyi ya kashe wayar domin ya gano dalilin sammakon zuwa makarantar nasu."

Zaune yake a falonsa yana goge takalminsa yana kallon talabijin."

Sallamar Abba yaji ya turo k'ofa yashigo,
Da Sauri ya mik'e tsaye cike da girmamawa ya amsa masa sallamar gabansa na fad'uwa."
Saboda yasan ba k'aramin Abu zai kawo Abba har ciki d'akinsa ba."

Abba ya wuce kai tsaye ya samu kujera ya zauna yana murmushi,
mahmud yaje ya durk'usa k'asa ya gaidashi
Tare da cewa "Abba lafiya kazo da kanka aida kabari Nazo nasameka shirin da nakeyi kenan."

Murmushi Abba ya kuma yi yace "nasan da hakan Mahmud domin duk a cikin 'ya'yana INA Alfahari da kai,
Naxo ne da kaina domin nuna maka mahimmacin maganar da zamuyi da kai."

Anan Mahmud ya sunkuyar da kai ya kuma natsu yana sauraren Abba."

Abba yace "Mahmud inaso ka natso kayi dogon tinani akan Alhaji Atiku,
Ya kyautata mana fiye da tunaninka Wanda koda husaini na raye a duniya iya abunda zaiyi mun kenan."

Alhaji Atiku ya bijiromun da wata magana Wanda nakasa yimasa musu akanta saboda diboda d'inbin Alherinsa garemu,

Alhaji Atiku ya nunamun cewa yana so ya had'a aurenka da 'yarsa yusra domin muk'ara dank'on zumunci a tsakaninmu, na Amince masa da hakan wnn dalilin yasa nace ya turomun kai naji ra'ayinka in har baka buk'ata na rantse da Allah mahmud bazan tab'a yi maka abunda baka soba, sai dai Alhaji Atiku da 'yarsa su hak'ura."

Kansa a sunkuye yaji Ransa yayi mummunan b'aci, wani irin b'akin ciki da zuciya yaji yana taso masa amma sai ya daure yayi k'ok'arin saita kansa ya d'ago kai had'ida murmushin k'arfin hali domin kadda Abba ya fahimci wani abun."

Yace "bakomai Abba tunda har ka amsa masa da cewa ka Amince,
Nima na amince zan aureta tunda kana son ayi hakan."

Abba yayi murmushin jin dad'i yace "Allah yayi maka Albarka Allah ya d'aukaka a duk inda kake."

Ameen yace "yaji dad'in Addu'ar da Abba yayi masa, babban burinsa a kullum shine ya dinga ganin farin ciki a kan fuskar mahaifan nashi, indai zasuyi farin ciki akan Abu to ko maiye shi zai iya aikata masu."

Bayan Abba ya fita mahmud ya koma ya kwanta a kan doguwar kujera zuciyarsa cike da bak'in ciki da b'acin rai, idanunsa jawur zuciyarsa na bak'i bbu alamar farin ciki ko kad'an a Tare da shi, shi kad'ai yasan wane irin b'acin rai ya binne a zuciyar sa,

Sai da ya samu natsuwa snn ya mik'e ya d'auki key d'in motarsa ya fita, yayi wa mommy sallama da Abba suna sanya mashi Albarka yafito ya shiga motarsa ya d'auki hanyar Abuja."

Yana fita a guje da motarsa SU dijama suna dawowa daga makaranta."

Dijama tabishi da kallo ganin yanda yake Jan mota duk saitaji ba dad'i a ranta domin ta fahimci akwai abunda yake damunsa,
Tasan yaya mahmud baya gudu da mota wani lokacin har shikeyiwa Khalil fad'a idan ya kamashi a hanya yana gudu da mota."

Tsaye tayi tana kallonsa har sai da ya b'acewa ganinta snn ta girgixa kai ta tsinci kanta da fad'in "Allah ya tsaremun kai yaya mahmud a duk inda ka nufa."

Juyawar da zatayi tayiwa fateema magana,
Tuni fateema tayi shigewarta gida tana murna yaya mahmud yayi tafiyarsa bai dakesuba ya manta."

Khalil tagani tsaye a gabanta ya tsura mata ido yana kallonta kamar yanda yasaba a duk lokacin da ya ganta a cikin gida ko a waje."

Dogon tsaki taja had'ida kai masa harara tayi wucewar ta cikin gida, bata kuma bi takansa ba."

Bayanta yabi tana tafiya yana kallonta yana kuma jin wani zazzafan sonta yana fisgarsa."

Tafiya takeyi jikinta duk a macce yake hakan tashiga falon gidan kamar wacce kwai ya macewa a ciki. Mommy tasama zaune akan kujera tana kallo,
Azahiri zaga ganta tana kallo amma kwata kwata hankalinta baya wurin TV, ya yatafi can wurin tunanin Mahmud da aure masa yusra da za'ayi Wanda itama kwata kwata bata son auren Dan dai ba yanda zatayi ne sai dai kawai Addu'a."

Dijama ta kalli mommy tace "mommy naga yaya Mahmud ya fita, ina zaitafi?"

Mommy ta k'ak'ro murmushi tace "wurin aiki zai koma kuyi masa Addu'ar sauka lafiya."

Dijama tace "Insha Allah lfy glau zai isa, Allah ya kaishi lfy."

Mommy tace "Ameen."
Had'ida kallon dijama cike da kulawa."

*****************

Abba na zuwa office ya d'aga waya yakira Alhaji Atiku yake shai masa yayiwa mahmud magana ya Amince Dan Haka asanya ranar auren domin ayi a huta.'

Alhaji Atiku yaji dad'i Sosai Wanda hakan yakasa b'oyuwa a kan fuskarsa."

Anan take suna tsaida ranar aurensu nan da wata hud'u masu zuwa, daga k'arshe suka yiwa junansu sallama suka kashe wayar."

Alhaji Atiku yana fad'awa yusra zokaga murna da farin ciki sai dariya takeyi tana rawa Dan dad'i zata mallaki abinda tafiso akan komai a rayuwarta."

K'arfe 5: pm Mahmud ya sauka garin Abuja, lfy kai tsaye d'ansu yanufa wnda a ynxun shi kad'ai yake zaune cikinsa,

Kai tsaye toilet ya fad'a ya yyi yasakarwa kansa ruwan sanyi ko da zaiji dad'i a ransa, yana fitowa ya shinfid'a darduma domin yyi sallah."

Bayan ya kammala sallar ne wayarsa ta d'auki k'ara yana dubawa bak'uwar number ya gani sai da yayi kamar bazai d'auka ba, sai kuma ya yatsinci kansa da son ya d'aga yaji ko waye."

D'auka yyi ya kara a kunne,
Wata murya mai taushi yaji tayi sallama,
_"Assalamu Alaikum yaya da fatar ka sauka lafiya."_

Ajiyar zuciya ya sauke domin ko a mafarki yaji wnn murya yasan dijama ce,

Lumshe ido yayi ya saki murmushi yace "lfy glau, ai dole kikirani tunda kinji dad'i Kin tserewa hukuncina.' To bnmanta ba zandawo."

Tasaki dariya mai sauti Wanda sautin muryarta sai da yasanya yashi lumshi ido da sauri ya kashe wayar ya ajiyeta gefe."

Still mmurmushi yakeyi ya rasa dalilin murmushin nasa."





_hmmmmm muje zuwa aboka naina Ummu Safwan CE_

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_) 😅






Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)






*35*






Wayar sa yaji ta kuma yin k'ara yayi saurin kai hannunsa da sauri zai d'auka domin a tunaninsa dijama ce ta kuma kiransa."

Yana murmushi ya d'auki wayar,
Abba yagani, a kasalance ya d'aga wayar yakara a kunnensa had'ida yin sallama."

Cikin natsuwa Abba ya amsa sallamarshi yace "Mahmud ina fatan ka sauka lafiya."

"Lafiya k'alau Abba,
yace had'ida yin murmushi."

Abba yace "yanxun muka kammala waya da Alhaji Atiku, mun tsayar da ranar aurenku nan da wata hud'u masu xuwa ko hakan yayi maka?"

Sai da gaban mahmud ya fad'i jikinsa ya soma rawa saboda bak'in ciki,
ya zaro ido waje yyi shuru na tsawon minti biyu,
Snn yayi k'ok'arin saita muryansa yace "Abba duk yanda ka yanke dai dai ne bana da ja, hkan da kuka sanya yayi Allah ya nuna mana lokacin."

Abba yaji dad'in kalamansa yace "Allah ya shi maka Albarka mahmud hak'ika zakaga haske a rayuwarka."

Yana kashe wayar idonsa yayi jawur ya burxar da iska mai zafi,

Ya D'aga kansa sama yana kallon silin zuciyar sa tunkushe da bak'in ciki, da takaici,


*****************

Tunda sulaiman yatafi kullum sai Alhaji Atiku ya isko fareeda a d'akinta yana mata maganar banza,

Amma bata kulashi sai dai tayi shigewarta d'aki ta sanya key tayi kwanciyarta tana jinsa a falo sai kusan asuba yake fita."

Satin sulaiman biyu a inda aka turashi, amma baiga alamar za'a janyeshi a wurin ba, gashi kullum da tunanin fareeda yake kwana dashi yake tashi."

Yana samun sauk'in tunanin ta ne a duk lokacin da yakira wayarta yaji tace tana cikin k'oshin lafiya."

Wanda ita kuma fareeda tana b'oye masa abunda Alhaji Atiku yake mata ne saboda kwanciyar hankalin sa, yasamu na tsuwa a wurin aikinsa."

Mahmud yyi mmki sosai ganin har yanxun sulaiman bai dawoba,
Idan yatafi ya tambayi fareeda ko tana fuskantar wata matsala a gidan sai tace masa A'a ba wata Matsala."

Yana yawan sanya ido akan Alhaji Atiku koda zaiga wani alamar da zaisanya ya fahimci wani abun tsaninsa da fareeda,
Amma abun mmki baya ganin wata alama,
Abunda Mahmud baisaniba Alhaji Atiku dare yakebi idan kowa ya kwanta ya isko fareeda

Domin Alhaji Atiku da zarar mahmud na tare dashi suna aiki duk wata hanya da zaisanya yagane wani mummunan Abu a tare dashi a dannewa yakeyi."

Amma duk da hakan mahmud bai barshiba yana sanya ido akansa."

Duk wata hanya da Alhaji Atiku zaibi, duk wani tsoratarwa da ya kamata yayiwa fareeda domin ganin yasamu biyan buk'atarsa yayi amma bawani haske, hakan yanuna masa da cewa fareeda taurin kai ke gareta tafison mijinta ya rasa ransa akan tabada kanta."

A wnn Daren ya mamayeta ta mnta bata rufe k'ofa ba, yasameta ya fad'a mata kai tsaye aikuwa suka dinga kokawa har Allah ya bata sa'arsa ta turoshi waje ya fad'i k'asa yayi targad'e a k'afa, bata damu da hakan ba,
ta rufe d'akinta."

Alhaji Atiku Yaji bak'in cikin jimuwar da yayi, a k'afarsa ta kumbura tayi haushi Wanda ko takalmi baya iya sanyawa,
A maimakon ya hak'ura da mugun nufinsa akanta , saima yaji wata wutar sha'awarta tana ruruwa a zuciyarsa,

Wanda a yanda yakejinsa ko ta tsiya ko ta arziki sai ya ku sanceta yasamu biyan buk'atar sa a kanta."

Washe gari safiyar Monday ko wanne ma'aikaci shiri yakeyi domin ya tafi wurin aikinsa."

Alhaji Atiku a office d'insa mahmud ne zaune a gefensa yana rubuce rubucen takardun wani kes da akeyi wani yaro da yayiwa wata k'aramar yarinya fyad'e."

Alhaji Atiku yana kan babban kujerarsa yana juyata idonsa sanye da glass,

Tunda mahmud ya yasanya ido ya ganshi a hakan ya San da akwai abunda ke damunsa, ya mere baki domin a duniyar nan babu abunda ya tsana sama dashi."

Gaidashi kawai yyi yawuce ya zauna akan kujerar da yasaba zama yaci gaba da aikinsa."

Wani dogon numfashi yaji yaja da k'arfi,
Wanda sai da mahmud yyi saurin juyowa ya kallesa,

ya sanya hannu ya d'auki wayar dake a jiye a gabansa,
Number sulaiman ya shiga kira,

Sulaiman dake can cikin 'yan uwansa abokanan aikinsa suna aiki."

Sai ganin kiran Alhaji Atiku yayi da Sauri ya d'auki wayar ya kara a kunnensa cike da girmama yake gaida shi."

A taik'aice Alhaji Atiku ya amsa masa,
Wanda yin hakan sai da gabansa ya fad'i."

Yace "sulaiman duk abunda kakeyi kazo yanxun nan ina nemanka."

Cikin girmamawa sulaiman yace "to ranka ya dad'e." Ya kashe wayar."

Ba'ayi awa biyu ba sai ga sulaiman ya iso gaban Alhaji Atiku."

Mahmud na ganin sulaiman ya kuma juyawa ya kalli Alhaji Atiku ya tabbatarwa kansa akwai matsala."

Ya kashe kunne yana sauraren laifin da sulaiman yayi wanda har ya b'atawa Alhaji Atiku rai hakan."

Sulaiman ya sarewa Alhaji Atiku cikin girmamawa da kwazo. Ya amsa masa tare da d'an sakin fuskarsa."

Yanuna masa kujera alamar ya zauna."

Sulaiman yaje ya zauna,
Alhaji Atiku ya cire glass din idonsa ya kalli sulaiman da kyau yace "kasan dalilin kiran da nayi maka kuwa?"

Sulaiman ya runsuna tare da girgixa kai yace "A'a ranka ya dad'e."

Alhaji Atiku yyi murmushi, yace "ina tayaka murna kayi dacen macce kamila wanda tasan darajar aure ta kuma rik'e mutumcin ta na 'ya macce."

Tabbas samun irin matar ka fareeda a cikin mata sai antona
Karkayi ko kwanto a kanta, a duk inda ka ajiyeta kayi tafiyarka a fad'in duniyar nan ni na tabbata fareeda zata tsare mutumcin ta da aurenta."

Mahmud ya zaro ido."

Gaban sulaiman ya fad'i. Yace "ngd ranka ya dad'e."

Alhaji Atiku ya kuma sakin dariya yace "d'auki wayarka ka kirata kafad'a mata cewa kadawo tasameka a office d'ina kana nemanta."

Sulaiman bai musaba ya d'aga waya yakira fareeda dake harhad'a kayanta tana kuka Ammar, goye a bayanta domin ta d'auki d'amarar daga yau tabar wurin nan kenan gida xata koma gaban iyayenta."

Sai ganin wayar sulaiman tayi.
k'ok'arin saita kanta tayi dan kadda ya fahimci wata damuwa a tare da ita, wanda zata tayar masa da hankali yakasa yin aikin sa."

Ta d'auki wayar had'ida sallama. Yanajin muryarta ya fahimci akwai abunda ke damunta."

Yace "fareeda kisameni a office d'in oga ina jiranki."
Bai jira amsarta ba ya kashe wayar."

Cikin minti biyar ta ta iso office d'in, tana zuwa tayi ido biyu da Alhaji Atiku ta wurga masa harara, bata gaida shi ba,
Ta kalli Mahmud dake zaune gefe d'aya yana rubutu amma duk ilahirin hankalinsa na wajensu."


Tace "mahmud ina kwana."
Sai a lokacin ya d'ago kai ya kalleta ya amsa mata had'ida tambayar ya Ammar?"

Tak'i gaida Alhaji Atiku sulaiman yayi mmki zaiyi mata magana akan ta gaida shi,
Alhaji Atiku ya katse masa hanzari da yace "malama fareeda ga wuri ki zauna."

Tak'i ta zauna tayi tsayenta tana hararar sa. Cike da tsana."
Da kyar ta bud'e baki tayi magana cikin muryar kuka tace "mazinaci baya da martabar da xai bani wuri na xauna."

Sulaiman yayi saurin kallonta ya kuma juya ya kalli Alhaji Atiku cike da ayar tambaya a fuskarsa."

Murmushi yyi ya kalli sulaiman yace "karkayi mmkin yanda kaji tana yimun mgna hakan da takeyi shi yake kuma sanyawa ina jinta a raina."

Tun lokacin da na turaka inda kake aiki a yanxun,
Nake bibiyar matarka akan ta amince mun na kad'aice da ita amma ta k'i."

Nayi mata alk'awari iri iri har na k'ara maka girma na kuma mallaka maka dukiya mai tarin yawa, amma matarka fareeda tak'i amin cemun."

Ni kuma Allah ya sanya min sha'awar matarka wanda a yanda nkeji idan ban kusance taba kamar zan mutu."

To shawara gareka ga matarka nan a gabanka ka sanyata ta amince dani a yanxun na kusanceta,
idan ba hakan ba kacire mun uniform d'in jikinka na koreka daga aiki."

Idan kuma ka Amince na kad'aice da ita,
To ka sanyawa rayuwarka gaba d'aya zuri'ar ku,
Kun warke daga cikin k'angin talauci





*hmmmmm talaka bawan Allah*😭😭

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_) 😅






Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)






*36*






Ido Suleiman ya k'ura mashi cikin bak'in ciki da ta kaici idonsa ya cika da hawaye jikinsa ya soma rawa,

Ya janyo fareeda ya rungumeta a jikinsa sai da suka d'auki minti biyu a haka snn ya janyeta a jikinsa."

Ya sauke hular kansa ya ajiyeta a kan tebur d'in Alhaji Atiku ya cire rigar jikinsa ya ajiye masa akai ya dubeshi da kyau yayi masa kallon tsana yace "wlh dana bari ka kusance matata a gaban idona gara Allah ya amshi rayuwarka."

Alhaji Atika na zab'i matata akan aikina, kuma kasani arziki da talauci duka na Allah, Allah ne,
Shike bawa wanda yaso."

Kana amfani da kujerar da Allah ya baka kana fasik'anci da matan aure, kasani ni sulaiman nine mutum na k'arshe da baxaka tab'a mntawa daniba."

Matata tafiyemun komai a rayuwata mutum cin matata fareeda yafiye mun duk wani Abu da mallaka a rayuwata."

mazina ci fasak'i wlh Allah ba zai barka ba, sai ka ga k'arshenka."
Sai kayi mummunan k'arshe,
Bara na fad'a mka magana ta k'arshe, ni da ka d'aukeni talaka har kakeso kayi amfani da talauci na domin ka ketawa matata handinta ka zalunceni,
To kasani bana zalunci kuma duk Wanda ya zalunceni wlh Allah ba zai barshiba,
bana boka bana malam amma KA rubuta KA ajiye yanda na ajiye aikina kai ma saika ajiye naka a lokacin da kake cikin jin dad'in sa."

Ynda nacire uniform d'in nan a gabanka, hakan za'a mik'o maka takardar sallama daga aiki a gaban bainar jama'a."

Sai a lokacin Mahmud ya wurgawa Alhaji Atiku kallon tsana, cike da k'unar zuci,
Ya kuma kallon sulaiman yace "sulaiman barshi a hakan,
Na tabbata abun da yyi maka bazai tab'a samun kwanciyar hankali ba."

Ya rubuta mashi cak d'in kud'i miliyan biyu tare da wata takarda ya mik'a mashi "yace ga wnn kayi amfani dasu,
Wnn takardar ka kaiwa Abba zankirashi a waya nayi bashi bayani."

Kud'in da na baka kayi amfani dasu kasayi gida a cikin garin kano, da kaida matarka,Ku zauna

Idan KA kaiwa Abba wnn takardar zai gane abunda nke nufi, zai yi amfani da ita ya d'oraka akan manajan kamfaninsa na sarrafa atamfofi na tabbata zakaji dad'i sosai
Kuma xaifi maka wnn wulak'antattacen aikin mai cike da cin amana da zalunci da kuma son kai."

Bantab'ayin nadamar kasan cewata a k'ark'ashin wnn azzalumin mutumin ba sai a yanzun."

Idon Mahmud sukayi ja ya taso yazo har gaban Alhaji Atiku cike da b'acin rai,
ya dubeshi ido cikin ido, yace kayi Arziki ni mai biyayya ne ga mahaifana, wlh da ba dan hakan ba Alhaji Atiku wnn ranar sai ka gane kuskurenka."

A hakan kake tunanin zan aure 'yar ka har na had'a zuri'a da kai mazinaci Azzalumi mai Neman matan Aure?"

A hakan kake tunanin nayi mka biyayya na d'aukeka a matsayin suruki Wanda zai aure karuwar 'yarka nakasasshiya Wanda tayi gadon hali irin naka?"

Kayi kuskure Alhaji Atiku, domin kuwa duk abunda kake ciki duk halin da kake ciki da irin mugayen abubuwan da kake aikatawa ina sane dasu."

Da sannu za'ayi walk'iya muganka a rana a lokacin ni da kaina zan kuma turaka a tsakiyarta domin ta axabtar da kai."

Alhaji Atiku sai zarar ido yakeyi duk da sanyin Ac da ke cikin office d'in amma sai zufa yake fitarwa."

Mahmud ya juya ya kalli Suleiman yace "abokina katafi ka sanya kayanka Ku d'auki hanyar kano, ya mik'a masa key d'in motarsa yace "kayi amfani da wnn kafin nazo kano."

Godiya Suleiman zaiyi masa Mahmud ya d'aga masa hannu yace "ba lokacin wnn kai dai kawai kaje kayi abunda nace."

Hakan sulaiman ya fito office d'in Alhaji Atiku yana mai tsine masa Albarka tare da matarsa FAREEDA."

Mahmud ya dubesa cikin tsana yace "nima idan ka isa ka kureni daga bakin aikina a yau,
Dama domin Abba da mommy nke wnn aikin domin farin cikin su ba wai dan ina ra'ayiba."

Kuma idan har ka isa da 'yarka, kamar yanda mahaifana suka isa dani, idan har 'yarka tanajin maganarka kamar yanda nakejin maganar iyayena, ka fad'a mata ka kuma shaida mata ni mahmud bana sonta ta janye maganar aure na da take so tayi."

Idan kuma tak'ijin maganarka tafi k'arfinka tak'i yi maka biyayyah to ni zanyiwa iyayena biyayya zan aure ta amma KA iya tabbatar mata da cewa, har k'ara tayi zaman gidan yari yafi mata dad'i akan ta zauna a gida na a k'ark'ashin inuwata."

Yana kaiwa nan ya fita ransa a b'ace."

Alhaji Atiku ya dafe kai ya rasa abunda ke masa dad'i,
Idonsa yayi ja ya rasa abunda yake masa dad'i a duniya,

Meyasa mahmud yake masa hakan ne?"
Meyasa baya iya d'aukar masa mataki a duk irin abunda yake masa?"

Mik'ewa yayi a fusace ya nufi gidansa rai b'ace da ya tuna da magagganun da yayi masa akan Yusra."

Da shigarsa ya tarar da ita zaune a falo ta k'ure velume d'in TV sai wak'a take saurare tana kad'a kai, ta lura da shigowarsa amma sai tayi kamar bata ganshiba taci gaba da abunda takeyi."

Ransa ya kuma b'aci, yaje wurin TV ya kashe, ya juyo ya kalleta, ta turo bki shi take kallo, tace "daddy meye hakan xaka kashemun TV ina tsakiyar kallona?"
Rab'awa tayi ta gefensa zataje ta kuma kunnawa,

Ya doka mata tsawar da bai tab'a yimata makammaciyar ta ba, yace "karki kuskura ki kuma kunna tv nan, idan kuma kika kunna to ranki idan yyi dubu sai ya b'aci."
Ya wuce a fusace ya nufi d'akinsa had'ida fad'in ki sameni ina son magana dake."

Cike da mmki take kallon daddy,tana shakkun wai kuwa shine daddyn nata?"

Bayansa tabi ta sameshi a d'akin nasa kamar ynda yace, ta nemi wuri ta zauna a kusa dashi tana kallonsa tace "gani daddy."

Ya d'aga kai ya kalleta yace yusra,
Tayi sauri kallonsa jin ya ambaci sunanta rabonda ya yakira sunanta hakan har ta mnta."

"Yusra umurnin nake bki ba wai shawara ba,
daga yau bake ba mahmud ki fitar da mahmud a ranki domin kuwa bazaki aure shiba."

Yau mahmud yaci mutumcina ya wulak'antani yayi abunda har na mutu bazan manta dashi ba, ya kuma yimun mgna akan cewa in har na isa dake nyi mki mgana ki rabu dashi."

Yusra kifitar da Mahmud a ranki domin bazaki aure shiba."

Kuka ta fashe dashi tace "daddy Mahmud shine farin cikina rabani da Mahmud tamkar rabani da rayuwata ne, daddy Mahmud ko kasheni zaiyi yayi gunduwa gunduwa da naman jikina,
naji nagani zan iya zama dashi a hakan."

Duk abunda Mahmud ya maka daddy tsakaninku ne bai kamata ka sanya alak'ar aure mu a cikiba,
Wlh daddy muddun kayi sanadin da narasa Mahmud to kasani kashe kaina kawai zanyi kaima ka rasani."

Zaro ido yyi waje cike da tashin hankalin kalaman da take fad'i ya janyo ta a jikinsa yana fad'in "yi hak'uri shalele karki kashe kanki indai akan Mahmud ne tunda kinji kingani kin Amince zan aura mki shi."

Anan ya rungumeta ya shiga lallashinta har ta hak'ura, ranta yyi sanyi, anan take bacci yayi awon gaba da ita."

Ido ya tsura mata yana kallonta shine dai a rayuwa bbu abunda yake so sama da yusra,
Yana son

Please Login or Register in order to submit comment