Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da iyalinsa maganarsa d'aya ce a kan suyi karatu."

Abba bai tsaya wani tambayaba ya tura masa dubu d'ari a account d'insa,

Godiya Khalil yayi yaje ya ciro kud'in yakira Ashanty a waya tasame shi gidan Ahmad sai da suka gama shek'e ayarsu suka gaji snn daga k'arshe ya mink'a mata kud'in gaba d'aya."

yace "ina fata wad'an nan suna isarki wurin zubar da wnn shegen cikin tare da nuna cikinta da hannu Wanda ya fito ya bayya ba laifi."

Murmushi tayi tace "honey meyasa kake sheganta cikinka?"
abinda kai kasani nima nasani jininka ne?"
sai nake ganin ko haihuwarsa nayi bazaka so a kirashi da shegeba."

Da sauri yatse mata magana tare da kallonta yace "bazaki tab'a haihuwarsa ba."
dan kuwa abin kunya ne a gareni kamata a Ganni da d'an shege ace kuma nawa ne."

"Daina d'aga hankalinka honey ai bakada matsala indai akan wnn cikin ne kamar anzubar dashi angama."

Ta mik'e tsaye ta sanya kayanta ta d'auki kud'in da yabata ta saka ajaka tayi msa sallama ta fita tana masa murmushin mugunta, ta shafi cikinta tace "ina sonka baby nah baxan tab'a xubar da kaiba'
Zan d'auki duk wani k'alubale da tsangwama da zan fuskanta a wurin mahaifina."

Kasancewar mahaifiyar Ashanty ta rasu a hannun kishiyar uwarta take Wanda bata damu da tarbiyartaba, Dan ma mahaifinta malam Lawali yana tsaye tsayin daka ga iyalinsa, dan kuwa Ashanty ta taso cikin tarbiya da kamun kai had'uwarta da Khalil ne ya b'ata mata rayuwa gashi harda ciki ke gareta Wanda mahaifinta bai San dashiba,
Kasan cewar Ashanty bata da girman ciki kuma kullum da hijabi take xama a gida."

Hakan Ashanty ta dawo gida tare da kud'in da Khalil ya bata dama wad'anda yabata daga farko sunanan babu abinda tayi dasu ta ajiye, domin hidimar d'anta bayan ta haihu."

***************

Mahmud ya dawo gida a gajiye, ya tarar da dijama kwance a falo ita kad'ai tana bacci da murmushi ya nufeta ya zauna a kusa da kujerar da take fuskantarta kallon fuskar ta yakeyi yana murmushi domin ganin yayi tayi masa kyau, sai yanzun ya kuma tabbatar da tabbas kamarsu d'aya komai nasu iri d'aya babbancin d'aya ne ita macece shi kuma namiji."

Murmushi yakeyi sai ya d'aga hannunsa da niyar ya shafi fuskarta tareda gyara mata gashin kanta daya zubo saka makon d'ankwalin kanta da ya zame
Sai kuma ya sauke hannun, ya fasa yana murmushi

Fateema dake bayansa a tsaye tana kallonsa tana murmushi snn tayi gyaran murya tace "yaya sannu da zuwaa."

Firgigit yayi kamar Wanda ya tashi daga bacci ya d'an sosa kai ya mik'e tsaye,

Yusra ya gani a can gefe d'aya zaune ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana kallonsa tana girgiza k'afa cike da jin haushi.'

🌹 *DEEJAMAH* 🌹 ( _'Yar gidan tsohuwa_ )πŸ˜…




Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)






*57*






Wani kallo ya wurga mata mai cike da tsana,
Yayi wuce warsa."

Yusra itama ta murgud'a baki had'ida wurga masa harara tare da jan dogon tsaki, tace "ai dama nasan hakan Zata faru,

Kuma na rantse da Allah baka isa KA aureta ba saboda ina sonka, kuma daddy na bazai bari KA aureta ba."

Idan kuma KA kafe akan sai ka aure ta,

Har kabari aka kawota gidan nan to kasani dani da kai da ita duk sai na cin nawa kanmu wuta dukanmu mun k'une kowa ya rasa."

Dan kuwa babu wacce ta isa ta shigo gidan nan a matsayin matarka inaji ina gani kuyi rayuwar aure da ita."

Tsaye Mahmud yayi yana kallonta cike da mamaki irin yanda yaga tana masa magana cikin rashin kunya."

Juyawa yayi ya kuma kallon fuskar dijama dake bacci gani yayi da zarar ya biye mata yana iya tayar da ita daga bacci da takeyi,
ya girgiza kai yayi juya yayi shigewarsa d'akinsa."

Ta dawo kan fateema ta wurga mata harara tace "ke kuma muna fuka kinsaki ido wuk'i wuk'i kina kallona wuce ki zubo mun abinci naci yunwa nakeji."

Fateema itama ta wurga mata harara tace "aikece babban funafukar kuma abinci bazan zubo ba dan kuwa bake kika girka shiba."

"Keni kike fad'awa magana?"
Ina matsayin matar yayanki?"
Wanda muke kwana a gado d'aya dashi ai kuwa yau zanyi maganin rashin kunyarki."

"Anfad'a maki kema ai yanzun kika gama yiwa yaya rashin kunyar."

Yusra ta d'aga hannu zata kaiwa fateema mari,
Sai gani tayi dijama tayi sauri ta rik'e hannun."

Dama dijama ba bacci takeyiba jin tsayuwar motar mahmud ce yasa tayi saurin rufe ido kamar wacce takeyin bacci."

Duk abinda Mahmud yake mata tana kallonsa."

Ta murd'e hannun Wanda sai da Yusra tasaki 'yar k'ara snn dijama ta kwad'a mata mari har sau biyu."

Bak'adan Yusra taji zafin marinba Wanda yasa ta kama dijama da kokawa."

Sai da dijama ta d'agata sama ta kayar da ita k'asa, ta haye kanta tashiga dukanta, dama tana da haushinta."

A guje fateema ta ruga ta fad'owa mahmud,
Da sauri ya fito ya tarar da dijama a kan ruwan cikin Yusra sai dukanta takeyi."

Da kyar mahmud ya samu ya b'anb'ari dijama a jikin yusra Wanda ta daku iya dakuwa sai shisshikar wahala takeyi."

Tana ganin mahmud ya janye dijama daga kanta tayi saurin mik'ewa tsaye tana wurga masu harara gaba d'ayansu,

Dama nasan mahmud baka sona ka kuma tsaneni amma kasani bazan gaji da furta maka Kalmar ina sonka ba."
Koda zakayi gunduwa gunduwa da naman jikina,

Kema 'yar k'auye mai k'arfi kamar namiji kisani baki daki banza ba,
Ni nasan matakin da zan d'aukar maki a cikin gidan nan."

Dijama Ta kuma yin kanta zata kuma dukanta mahmud yayi saurin rik'o hannunta ya nufi d'akinsa da ita."







*kuyi hakuri da wnn da babu kwanda kad'an*πŸ‘ŒπŸ»

🌹 *DEEJAMAH* 🌹 ( _'Yar gidan tsohuwa_ )πŸ˜…




Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)






*58*






Akan kujera ya d'orata yaje kusa da ita ya zauna,

Ganin ranta a b'ace yake ya mik'e tsaye ya nufi frege ya d'auko ruwa masu sanyi ya zuba mata a cup ya kara mata cup d'in a baki ya shiga bata ruwan da kansa."

Sai da ta shanye, snn taja doguwar ajiyar zuciya
mahmud ya ajiye cup d'in a gefe d'aya."


Ido ya kafeta dashi yana kallonta jiyakeyi kamar ya rungumeta ya lallasheta."

Cikin murya k'asa k'asa "yakira sunanta "dijama wai meke faruwa ne?"

Kallonsa tayi ido cikin ido Wanda shima ita d'in yake kallo,
Sai da suka d'auki kusan minti biyar a hankan ko wannensu ya kasa d'auke idonsa daga kallon junansu,


Mahmud yayi k'arfin hakalin janye idonsa daga kan nata,
Yace tambayarki fa nakeyi."

Ta turo baki cikin shagwanb'a tace "Allah yaya kajawa matarka kunne ta daina shiga shirgimu idan taga munayi a gidan nan."

Idan ba hakan ba Allah kafin na bar gidan nan sai nayi mata shegen dukan tsiya na koya mata hankali."

Dariya taso ta sub'uce masa yayi saurin dannewa yace "ai kuwa bazaki yiwa matata duka a gaban idona ba."

Da sauri ta juya ta dubeshi ta kuma had'e fuska tace "ni ina ruwana da matarka ce,
Bakaji abinda take cemun ba ne?"

"Metace maki ni banjiba illah kawai abinda naji cewar da tayi wai taga alamar sonki nakeyi. Kishi kawai takeyi saboda tana son mijinta."

"Ta kuma had'e fuska "meye ruwana da son da take maka bazai haka na nad'a mata shegen duka ba, Wanda har saitayi fitsari."

Ya kuma danne dariyarshi yace "ni kuma idan kikayi mata duka
Naje na sami sulaiman shima na nayi masa shegen duka kamar yanda kikayi mata, saikiji idan da akwai dad'i."

Mere baki tayi☹ tace "a haf idan karik'ashi kasheshi kawai kada ka barshi da rai."

Dariya ta sub'uce masa yace "saboda me mijinki fane Wanda kikace kina Sonshi za'ayi maku aure Nanda wata biyu."

Harara ta wurga masa ta gefen ido, tayi shuru bata bashi amsaba."

"Kikace na kasheshi bakyason shi kenan?
Nan ma tayi shuru ba amsa."

"Dariya ya kuma saki yace "ina ganin dai dijama ta zama kurma, da har yaya mahmud yake. Tambayarta tayi masa shuru kamar batajinsa."

Ta kalleshi tace "inJinka, matarka ce abin sonka ta b'ata mun rai, idan kuma ta sake maimaita hakan hmm ta yi shuru."

D'an karamin bakinta yake kallo Wanda yake bashi sha'awa,
Yace "ni kuwa banga abinda tayi maki ba,
Illah kawai kishine taga mijinta yana sonki,
Ke kuma na san bakya sonshi."

Gabanta ne ya fad'i tayi saurin kallonshi "eh hakan ne mana yanzun kin daina son yaya mahmud d'inki, Wanda a lokacin baya
bakya iya cin wani Abu batare da kin ajiye munba."

Bazakiyi bacci ba har sai nazo kusa dake. Na lallasheki." a lokacin bazaki tab'a barin na janye a kusa dake ba kullum muna tare, duk wani Abu da kikeso nasani amma banda yanzun da kika daina sona kika manta dani kike yimun wani kallo na daban Wanda ada bansanki da shiba."

Gashi yanzun har zakiyi aure Yaya Mahmud d'inki bai san Wanda zaki auraba sai daga baya,
Bayan ank'are shirya komai har antsaida ranar bikinku."

Ya zakiyi da shakuwar yaya mahmud dake cikin ranki?"

Mahmud ya zaiyi da shak'uwar k'anwarsa
Idan wani ya d'auke masa ita."?"

Dijama kinban mamaki da har kike iya b'oyemu abinda ke cikin ranki."

Wani abu yaji yana masa zafi a ransa, cikin minti biyu idonsa yayi ja, da Sauri ya tashi daga kusa da ita, ya koma kan gado ya zauna tare da dafe kai."

Idonta ya cika da hawaye tayi saurin mik'ewa tsaye taje kusa dashi,
Ta durk'usa tare da rik'o k'afafunsa hawaye na zuba a idonta.

"Yaya kayi hak'uri, ba daina sonka nayiba asalima sonka ya kuma lunkuwa a raina sama da Nada,

Kayarda dani, ka yarda da abinda zan fad'a maka bansan sulaiman yana sona ba,
Sai da naji a bakin Abba bayan yariga da ya amshi maganarsa

Amma ni ba wai ina son sulaiman bane har cikin raina,
A'a kwakwata babu d'igon sonshi a rayuwata zanyiwa Abba biyayya ne na aure shi domin farin cikinsa koda hakan zai zamo rugujewar nawa farin cikin."

Zaiyi magana kenan yaji kiran wayar Abba yana shigowa wayarsa."

D'auka yayi tare da sallama,
Ya gaida Abba Cikin girmmawa da biyayya."

Abba ya amsa mashi yana murmushi da sakin fuska snn yace "gobe idan Allah ya kaimu su fateema sudawo gida,
Domin shirye shiryen bikinsu kasan lokaci yana tafiya gashi har ankawo kayan lefen dijama saura na fateema,

Sulaiman yayi k'ok'ari sosai KA kirashi a waya Kayi masa godiya."

Runtse idonsa yayi yanajin saukar magagganun Abba kamar yana Daka masa mashi a xuciya."

Cikin wata kasallaliyar murya ya amsawa Abba da "to."

Yayi saurin kashe wayar tunkafin Abban ya kashe."

Dijama dake gurfane a k'asa tanajin duk abinda Abba yake fad'i,
Wani kuka tasaki mai sauti,
Mahmud Kuma ya runtse idonsa saboda wani zugi da yake jin zuciyarsa nayi masa,

Hannu ya sa ya d'ago ta ya mik'ar da ita tsaye ya zaunan da ita kan gado a kusa da shi tare da janyota a kan jikinsa,
ya shiga bubbugan bayanta alamar tayi shuru,
tare da sanya hannu yana share mata hawayen dake zuba akan fuskarta."

Dijama ta lafe kan jikinsa kamshin turarensa tashiga shak'a mai dad'in gaske,
Cikin minti d'aya ta name kukan ta rasa.
Sai sauke ajiyar zuciya takeyi,

Cikin dakakkiyar murya,
Wanda shima a yanda yakejinsa dama kukan yayi ko zai rage rad'ad'in zafin da yake damunsa a ransa,
Cikin muryar lallashi yake cemata "yi shuru daina kuka bana so Ganin zubar hawayenki,

Baxaki Aure sulaiman ba tunda bakyason shi,
Kin yarda da zab'ina."

Gabanta ya fad'i ta d'aga kai alamar 'eh."

Zan zab'amaki Mijin da zaiyi dai dai da rayuwarki Wanda zai kula dake ya Kuma tarairaiyeki ba kamar sulaiman ba."

Zan zab'a maki miji Wanda zakuyi rayuwar aurenku a nan kusa dani, inda akoda yaushe INA taredake."

Idan kika koma gida kifad'awa Abba cewa ke bakyason sulaima."

Ta d'aga kai alamar "to."

Anan dai suka dinga yiwa junansu musayar kala mai Wad'an da SU Kansu basu San abunda suke furtawa ba,
Saboda sunshiga Cikin wani yanayi na tashin hankali mai wuyar misaltuwa."

**************

Yusra tana Cikin d'akinta kwance tana kuka tarasa abinda zatayiwa mahmud ya sota."

Ta rasa ta hanyar da Zata b'ullo masa ya amshi soyayyarta ta tabbatar masa tana sonshi."

Amma a kullum burinsa a rayuwa ya ci mata mutumci ya tuzartata a gaban bainar jama'a."

Tana nan kwace tana kuka ta na jin son Mahmud yana Kuma dawo mata sabo a ranta."

Alhaji yasir yakirata a waya "yake. Shaida mata an jima su had'u a gidan mata."

Misalin k'arfe 7 na dare ta shirya kamar yanda ta saba yin shigarta kamar ba 'yar musulmai ba,
tafito duk a tunanin ta mahmud baya nan ya tafi massallaci kamar yanda ya saba,

Mahmud kuma yau zuciyarsa a da gule take bayan ya kammala sallar magariba a masallaci,
Kai tsaye gida ya dawo da sunan idan aka kira isha'i sai ya koma massalacin."

Yana Zaune a falo yaga fitowar Yusra cikin shigarda tasaba Wanda ga duk Wanda ya Santa ba wani abin mamaki bane garesa."

Tanufi hanyar FIta batare da ta lura da yana cikin falon ba."

Kallo ya bita dashi mai cike da kyamata da jin haushi, ya shiga maganar zuci
Wnn ce matarsa Wanda tagama tallar jikinta a titi kowa ya gama gani."
Allah ya kyauta."

Ya shiga tunanin to ko ina zataje a Wnn lokacin, wata k'ila gidan su ta nufa ta fad'awa ubanta halinda take ciki, Allah yasa yakirani a waya yace nakawo mata takardar sakinta da Kuwa nafi Kowa Murna da jin dad'i."

Mamaki ya cika shi da yaga bata d'auki Mota ba."

Ya mik'e tsaye tare da mere Baki yace ita tasani ko a kai zatayi tafiya."

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_)πŸ˜…

Written by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basher_)

*59*

A dai dai ta sahu tashiga ya kaita gidan matan."

A dai dai lokacin da Alhaji Atika ya d'aga da budurwarsa suka shige d'aki."

Alhaji yasir yana ganinta ya saki dariya kamar gonar auduga, yaje da sauri ya rungomota tare da kissing dinta ta ko ina."

Sai da ya gaji snn ya saketa yace "babynah barka da zuwa sarauniyar mata."

Yanzun nan babban aminina yayi ta jiran ki k'araso Ku gaisa."

Murmushi tayi tace "Allah sarki sai kuma wani lokacin."

Ya kuma bud'e baki yana dariya tare da d'aga gira yace "baby na yau kinfi jiya kyau."

Iska ta hura masa a ido tace "sirrin yana wurinka."

Bata ankaraba yana dariya ya d'auketa ya nufi d'akinsu da ita Inda ya kama."

A wann daren hakan sukayi ta aikata masha'arsu Wanda gaba d'aya Yusra ta manta da damuwar dake da munta.'

Alhaji yasir sai raba mata aiki yakeyi cikin kwarewa sai kuwar dad'i takeyi."

*****************

Bayan kwana biyu da rabuwar Ashanty da Khalil, kullum Khalil cikin kiran wayarta yakeyi sai yajita a kashe,
Tun abin yana damunsa har ya kai ya zubar da maganar da cewarsa wata k'ila ta mutu wurin zubar da cikin."

Murmushi yayi ya kuma gyara kwanciyarsa yace "ai gara ki mutu Ashanty da ki tuna mun asiri a idon duniya."
Ya rufe idonsa yana murmushi har bacci ya d'auke shi."

******************

Mahmud da dijama da kyar suka ga safiya ta waye masu ko wanne da abinda yake tunani a ransa."

hakan suka shiga shirya kayansu domin komawa gida."

Fateema ce ke shirya kayan Wanda dijama take kwance rufda ciki sai sharar hawaye takeyi,

Murmushi fateema tayi ta kalli dijama tace "wlh sis babu abinda yake damunku dake da yaya mahmud sai soyayyar junanku Wanda baku yarda da hakan ba."

Da zaku cire zurfin ciki Ku tunkari Abba da Wnn maganar da ya fi kowa farin ciki."

Dijama dake kwance tana jin duk abunda fateema ke fad'i,
Wanda ita ta dad'e da Sanin
Ta fad'a tarkon son yaya mahmud."

Bata tanka mata ba illah taci gaba da sharar hawayenta."

Mahmud shima kwance a kan gadonsa ya rasa abinda yake masa dad'I a duniya,
Sai tunani yakeyi yana magana da zuciyarsa kadai a ce son dijama yakeyi?"

Wata zuciyar tace "ai dama kana sonta tunda 'yar uwarkace, wacce kafi so duk a cikin k'ananka."

A nan kwance fateema ta fito da kayansu a falo ta kwakwasa masa k'ofa' ya tashi jiki ba kwari ya bud'e.'

Fateema ta d'an runsuna ta gaida shi snn tace "yaya mun kammala shiryawa."

"Ina dijamar take?" Ya tambayeta."

Tana ciki tana ta faman kuka na rasa abinda ke damunta."

Rab'a fateema yayi ya nufi wurin dijama kai tsaye ya tura k'ofa ya shiga d'akin."

Ya tarar da ita kwance tsakiyar gado tana sanye da doguwar rigar abaya bak'a Wanda tayi matuk'ar yi mata kyau."

K'amshin turarensa ya daka mata hanci ya tabbatar mata da shine ya shigo."

A hankali ta mik'e zaune tana sharar hawaye a idonta."

Hannunsa ya mik'a mata alamar tazo gareshi,
Jiki ba kwari ta nufeshi ta sauka daga kan gadon."

Mik'ewa tsaye tayi tanufeshi kanta a sunkuye,
Wani tausayinta yakeji a ransa tare da wani kalar Abu da yakeji yana fisgarsa a ransa."

_Hmmmm. So ne mahmud Wanda baka yarda dashiba_

Nufarta yayi ya janyota zuwa jikinsa, ya d'an d'aga kanta sama yana kallon fuskarta yanda hawaye ke kwarara,
D'an k'aramin bakinta kuma yana motsi alamar magana take so tayi kuka ya hanata."

Aljihunsa ya duba yaga baya da hankacif a ciki, bare ya goge hawayen."

Harshensa ya sanya ya shiga lashe mata hawayen da ke zuba a kan fuskarta
Bai ankaraba ya tsinci harshinsa cikin bakinta
karo na farko da mahmud ya taba shiga cikin wnn yanayin."

Dijama kuma ta runtse idonta hawayen da ke zuba a idonta suka tsaya cak."

Sai da suka d'auki kusan minti goma a hakan snn Dijama ta ankara da yanayin da suke ciki tayi saurin janye jikinsa daga gareshi."

Wani irin nauyi da kunya suka ziyarcesa yayi saurin juya bayansa yanufi hanyar fita yace "kifito kutafi Wanda zai kaiku ya dad'e da zuwa."
Ya bud'e k'ofa ya fita."

Shafa bakinta tayi tasaki murmushi snn ta mik'e jiki ba kwari, ta fita."

Gaba d'ayansu suna wurin mota ita kad'ai ake jira tafito."

Cikin tafiyarta mai cike da yanga da k'asaita ta fito

Ido mahmud ya zuba mata yana kallonta har ta k'araso wurin,
Wanda tuni FATEEMa. Ta bud'e Mota
Tayi shigewarta."

k'ara sowarta wurin mahmud yayi dai dai da shigowar Yusra gidan a can ta kwana duk a tunanin ta,
Mahmud ya tafi wurin aiki."

Ganinshi da tayi sai da gabanta ya fad'i,
Mahmud kuma yi yayi kamar bai gantaba ya bud'ewa dijama marfin mota tashiga cike da kulawa tana kallonsa yana kallonta,
suna d'awa junansu hannu direba yaja suka tafi tare da yi mata Alk'awarin zaizo k'arshen watan nan komai zai kai k'arshe."

D'akinta Yusra ta. Nufa hankalita a tashe duk a tunaninta mahmud zai biyota da masifa ya tambayeta gidan wa taje harta kwana."

Sai safa da marwa takeyi a Cikin d'akin gaba d'aya cikinta a k'ulle yake."

Amma abin mamaki sai jin k'arar fitar mahmud tayi, da sauri ta fito ta d'an lek'a kanta ta hangoshi sanye da uniform d'insa zai shiga mota da alamar wurin aiki zaitafi."

Wata ajiyar zuciya ta sauke takoma falo ta zauna yau gida nata bakowa a cikinsa."

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_)πŸ˜…




Written by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basher_)






*60*






Lefe ne Wanda ya amsa sunansa lefe mommy da Abba suka had'owa dijama da sunan sulaiman ya kawo mata."

Babu abinda babu a cikinsa,
Kaya ne masu tsada tareda gwala gwalai da zinari duk Wanda yaga lefen yasan kud'i sunyi kuka a wurin."

Tsohuwa da tazo domin ganin lefen kallon kayan takeyi taga sunk'i su k'are saboda yawansu rik'e baki tayi πŸ€” tace
"Wnn ai b'arnar kud'i ne,
kayan lefe shago d'aya wad'an nan kaya ai saitayi haihuwa goma bata d'unke wasu daga cikiba."

Mommy tayi dariya tace "Inna ai yanzun zamani ya canza wad'an nan kayan ba komai bane idan kikaga wand'ansu kayan."

"To Allah ya kyauta
Ta kalli Abba tace "Hassan wai har yanxun mamuda bai baiyana yana son dijama d'in ba?"

Abba yayi murmushi yace "kinsan halin d'an gidan naki,
Akwaishi da zurfin ciki.

Amma ko ya fad'a ko karya fad'a lokacin da muka sanya na biki bazamu janyeba, kuma bazai san dijama matarsa bace sai ranar d'aurin Aurensu a lokacin idan yajiyewa kunnensa an d'aura da shi"

Allah Inna na kasa samun suk'uni a duk lokacin da na tuna da Alk'awarin da na d'aukarwa d'an uwana akan auren dijama da Mahmud."

Tsohuwa ta girgiza kai tace "haka ne, hakan da kayi shine dai dai,
Domin Kuwa idan kafito kanunawa duniya cewa dijama matar mahmud ce zaka haddasa k'iyayya a tsakanin 'ya'yanka
musamman idan kayi diba da yanayin Khalil akan dijama, ina lura dashi naga alamar sonta yakeyi, dan ma baya samun goyon baya a wurinmu,

Da anfito fili annuna masa dijama matar mahmud ce da ba'asan irin k'iyayyar da zai d'orawa d'an uwansa ba,
Irin hakan ne kakejin labarin
wa ya kashe k'anensa,
Ko k'ane ya kashe wansa,
Duk akan abinda suke so."

Amma da ace mahmud ya fito ya nuna soyayyarsa gareta a fili da abin xaizo da sauk'i."

Mommy tace duk da hakan a yanda nake ganin Khalil sai an zaunar dashi anyi masa bayani yanda zai fahimta,
Domin Khalil yana da xafi sosai akan abinda ya keso."

Tsohuwa tace "Allah ya kyauta,
Insha Allahu abin zaizo da sauk'i."

Idan kuma akaga abin zaizo da wani matsala da tashin hankali sai a aurawa Khalil d'in ita, ai da Khalil da mahmud duk d'aya ne.
Wata k'ila mahmud d'in kulawar da yake mata da nuna soyayyarsa gareta Duk na 'yan uwantaka ne da zumunci,
Ba wai yana sonta ba ne domin ya aureta."

Tsohuwa tace "ranar auren tana nan yanda aka sanya ta?"

Abba yace "insha Allahu baxamu janyeba, saura sati shidda kenan.
Duk Wanda ke da rabo a wnn lokacin tsakanin mahmud da shi Khalil d'in za'a d'aura dashi, ni dai burina d'aya ne na sauke nauyin dake saman kaina na d'an uwana."

Sallamarsu dijama ta katse masu hirar da sukeyi,

Dijama na ganin tarin kayan lefe a gaban tsohuwa tana kallo,
gabanta ya fad'i jikinta yayi sanyi ta dake,
Suka shigo da sallama gaba d'ayansu."

Fateema tana murmushi ta nufi wurin kayan lefen domin sunyi matuk'ar bata sha'awa ta shiga dubawa tana murmushi,

Dijama kuma ta durk'usa ta gaida Abba da mommy da tsohuwa,
Suka amsa mata suna murmushi da sakin fuska tare da tambayarsu ya hanya."

Tsohuwa tace " dijama kin manta dani idan ba zuwa nayi garin nan ba baxakije ki diboniba, tunda kika bar k'auye kwatakwata zuwanki biyu."
Shi kuma mamuda ba'a maganarsa dama kece kike kaishi garin,
tunda kuma kika dawo kusa dashi ban kuma k'ara ganin k'eyarsaba bare yanzun da yayi mana nisa."

Murmushi tayi tace "yi hak'uri tsohuwa kinsan banda kamarki,
makaranta ce kawai take hanani zuwa amma yanzun idan zaki koma k'afata k'afarki a tare zamu tafi"

Tsohuwa tayi murmushi ta gutsara goronta tace
"Buba yace a gaidaki tare da k'awayenki suwaiba da lantana."

Dariya tayi tace Allah sarki Lantana da suwaiba 'ya'yansu nawa yanzun wai?"

Tsohuwa tace "uku uku ke garesu, Buba kuma d'an sa biyu matarsa uku yace "yana nan yana jiranki har lokacin da kika kammala makaranta kika dawo snn zaicike ta hud'u dake."

Fateema tasaki dariya tace "mutuwa kenan dijama a k'auye."

Dijama tace "to meye Dan nayi aure a k'auye a kusa da tsohuwa a can fa naso nayi wayo a can Sam ni bazan tab'a raina k'auyeba."

Khalil ya shigo yaci karo da kayan lefe ajiye,
Zaro ido yayi yace wad'an nan kayan fa na waye?"

Tsohuwa tayi karaf tace "ba'a sani ba tunda babu Wanda ka ajiye a nan da zaka shi go mana d'aki babu ko sammala bare gaisuwa,

Dafe kai yayi Dan ya manta kwatakwata baiyi sallama ba,
Yace "Allah ya Baki hak'uri tsohuwa Ashe kinxo?"

Bansani ba tace had'ida wurga masa harara,

Sai da ya koma ya Kuma shigowa da sallama snn aka amsa mashi tare da gaida su,
Snn ya samu wuri ya zauna idonsa na kan dijama yana kallonta."

Fateema ya kalla yace "FATEEMA wad'an nan kayan waye ko ishaq ne ya kawo maki?"

Tace A'a yaya Khalil kayan auren dijama ne sulaiman ya kawo mata,

Anan take ya canza fuska ya mik'e tsaye yace "da gaske yakeyi kenan." Ya fita a fusace."

Dukansu suka bishi da kallo snn mommy da Abba da tsohuwa suka had'a ido suka kalli junansu."


Please Login or Register in order to submit comment