Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yusra yana son farin cikinta. Ya rasa dalilin da yasa Mahmud baya sonta."

Kalaman mahmud ya tuna dasu da yace idan har 'yarka tanajin maganarka kamar ynda nakejin maganar mahaifana kayi mata magana ta janye maganar aurena da takeso tayi.

Wato idan ba'a janye ba kenan haka yana nuna batajin maganar shi?"

Wai meyasa mahmud yake fad'amin magagganu wad'anda idan yana gabana nakasa ramawa sai dai idan nadawo gida su dinga damuna a raina?"

Meyasa idan mukayi ido biyu Da mahmud nakejina kamar bana cikin natsuwa ta musamman idan ya kafeni da manyan idanuwansa masu k'unshi da wani kalar kallo?"

Hmmm lallai kuwa mahmud kana cin darajar shalele nayi maka wani kalar so idan ba hakan ba da tuni anmanta da labarinka a doron k'asa."

Fareeda ta fad'o masa a rai
Yaji wani irin kunci ya fara danasanin nunawa sulaiman maitarsa a fili a kan matar sa yanxun gashi nan sunbar wurin batare da yabiya buk'atar saba, a kanta."

*****************

Akwana a tashi ba wuya a wurin Allah lokacin bikin su mahmud da yusra gaba tuwa kawai yakeyi,
shirye shiryen biki akeyi, a gidajen nan biyu musamman a gidansu yusra,

Duk da mahmud baya son auren
bai nunawa mahaifinsa ba, ko wasuba, ko a fuskarsa baxaka gane ba, hatta ita Yusra bai nuna mata komai ba ya bar abun a ransa."

Alhaji Atiku kuma jinsa yake babu Wanda ya tab'a aura da 'ya a duniya nan sai shi, kud'i yake kashewa sosai duk abunda shalele tace tana buk'ata saiya saya mata shi."

Gida ya k'era mata Wanda yake shine, nagani na fad'a, duk ynda tace tana buk'atar gidan ya kasance ahakan akayi mata."

Wanda mahmud shi kuma yana ganin cewa da gske auren za'ayi ya, ya gina gidansa wanda yake ra'ayi a ransa, kuma ciki ya keson ya sanyata."

Shima gida ne ba laifi yyi kyau sosai."

Tunda dijama taji labarin auren mahmud ta tsinci kanta da Jin haushi, hakan zata samu wuri d'aya gefe d'aya ta rakub'e tayita kuka tarasa dalilin nata nayin kukan."

Cikin kwanankin auren duk ta rame ta fad'a saboda tunani idan kuma ta tambayi kanta dalilin yin kukan sai ta rasa amsa."

Inda shi kuma Khalil sai dad'i yakeji yana murna ganin mahmud zaiyi aure yasan da zarar yayi aure dole a aura masa dijama ta zama tashi."

Musamman lokacin da tsohuwa tazo
Yaji tana ruwan masifa a kan wnn auren da zaiyi domin ita har ga Allah bata son auren tafison ya auri dijama wanda suka tashi suna son junansu tun suna yara."

Abba yake bata hak'uri da banbaki yana nuna mata irin d'inbin Alherin da Alhaji Atiku yayi masa idan har aka hana Mahmud yak'i auren 'yarsa kamar anyi msa butulci ne."

Harda Khalil wurin bawa tsohuwa hak'uri akan tayi hak'uri Mahmud ya auri Yusra."

Ba yanda ta iya hakan ta hak'ura, akaci gaba da shirye shirye bikin dijama tana makaranta."

Tana Addu'ar Allah yasa kar'ayi masu Hutu sai bayan an kammala bikin snn."

Shirin biki kawai akeyi amma da zarar KA ganshi baka cewa akwai abunda yake damunsa dangane da bikin, yana so baya so bazaka iya zaganewa."

Yusra tashiga kokwanto da mmki ko dai ya hak'ura ne yanxun yana sonta?"
Tana mmkin yadda ya kyaleta ba fad'a ba cin mutunci hakan yasata a tunani da was_ wasi."

Shin meye a ainahin a xuciyarsa?"
ya hak'ura ne ko kuma..?" Anya?" Nasan mahmud miskilin kansa ne, dole akwai abunda ke yawo a kwakwalwar sa da zuciyar sa."

Dan haka ta yanke shawarar fuskantar sa, nan ta tsala ado na sosai me Jan hankali ta nufi Inda tasan zata sameshi a area su ta ma'aikata."

Taci sa'ar samunsa zaune ya d'ora k'afafunsa bisa table d'in da ke gabansa k'afarsa sanye da talkaman su irin na sojoji jikinsa sanye da uniform ko ciresu bai yi ba alamar bai jimima da dawowo ba,
Yana karkad'a k'afa ya hard'e hannu a k'irji, shi kad'ai yasan yanda yakeji a ransa."

Tayi ta sallama yajita ya kuma ganeta ya amsa sallamar amma ko ta inda take bai kallaba, balle yasan da mutum a wurin."

Tana ganinsa a hakan sai da gabanta ya fad'i, taji wani kalar sonshi yana dirar mata a Zuciya tace amma sai ta dake tace
"Hy sweet heart, ina wuni mahmud d'ina."

Yyi bnza da ita kamar da bango take magana, ta saki zuwa ta gabansa tana fuskantar sa amma har yanxun bai San ma tanayi ba."

K'amshin turarenta kad'ai ya isa ya kashe zuciya, amma mahmud tamkar gunki duk kyan nan tayi Wanda shi kansa yasan tayi kyau amma ko kallo bata ishisaba."
Sam bata burgeshi saima haushinta da yakeji tare da tsanarta a zuciyarsa."

Ai kuwa haushi ya kamata kyalenta da yyi a gashi a rywar yusra ta tsani
kyaluwa."

Ta fusata ranta ya b'aci ta shiga mita tana bala'i dan dai kawai ya kalleta ya kulata."

Bai kulata ya mik'e yayi mata kallon banza ya ce,
"Inaso kisan Mijin da zaki aura, mutum ne da ko fishina da b'acin raina baki kai in baki shi ba."

Kina da lokaci har yanzun in kina so zaki iya tsira daga sharrin auren Mijin da bai sonki ba,
Don kuwa baxaki iya jurar wulak'anci da zaki fuskantaba."

Cikin muryar kuka tace "meyasa baxaka soni ba?"
Me na rasa?"
Duk abinda akeso ga macce ina da shi, kadubeni da kyau ta mik'e tsaye tana juyawa gabansa."

Ya kalleta a wulak'ance yabata amsa kai tsaye yace "bakida komai, kije kije ki sake kallon kanki in kin duba da kyau zakiga ke d'in nakashasshiya ce, maccen da bata da asali mai kyau, maccen da ta gama tallan kanta da tsiraicin ta ga mutanen duk duniya ta hanyar mummunar shiga da kike,

Maccen da take mu'amala da maza tamkar mata,
Maccen da bata kishin kanta balle addininta,
Mace mai jin kai, macce mai girman kai da nuna isa, macce fitinanniya mai jin tafi kowa, illolin dake tattare dake sunfi rashin illarki yawa."

Ke baki isa kisa in k'i yiwa mahaifina biyayya ba, zan aureki amma ki shirya fuskantar mummunar rayuwa tare dani ba."
Tabbas kina samun duk abunda kike so, amma ki sanyawa rayuwar cewa bazaki tab'a samuna ba, domin a duniya ba komai ake nema ake samun sa ba.'

Yana gama fad'i ya mik'e ya fita a fusace zuciyarsa na k'una."

Cikin muryar kuka tareda d'aga murya tace "saurara kaji gskya ka fad'a ni ina samun duk abunda nkeso a haka rayuwata take life style d'ina kai baka isa kasa in canja ba,

Burina ya cika kuwa in dai na aure ka nayi nasarar sakaka aure na ko kana so ko baka so, nayi nasarar tursasa namiji kamar KA miskili mai nuna ba Wanda ya isa ya juyashi ko yasa shi ko ya hanashi auren macce da baya so,

Kyauna kuwa ina da tabbacin ko ynxun bai burgeka ba nan gaba in na mallake ka zan fara birgeka,

Tafice ta gabansa tayi tafiyarta ta gyaleshi cikin bakin ciki da takaici,

Tabbas yusra tayi nasarar cutar da shi, ta samu yadda takeso amma fa bazan kyaleta ba dole itama nakasa ta a inda zaifi mata ciwo

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_) πŸ˜…






Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)




*37*





*LAST PAGE*
*SAI BAYAN SALLAH ZANCI GABA IDAN ALLAH YASA MUNA DAGA CIKIN MASU YAWANCIN RAI DA LAFIYA,*
*INA KUKE FRIENDS D'INA KU MATSO KUSA KUJI DUK WNDA YASAN UMMU SAFWAN TA B'ATA MASA RAI DAN ALLAH KU GAFARCENI, ALLAH YA AMSHI IBADARMU YA INTAMU CIKIN INTATTUN BAYIN SA AMEEN*πŸ‘πŸ‘πŸ‘






Hidimar biki akeyi saura sati d'aya a d'aura aure."

Dijama tana lissafe, kullum cikin kuka take da damuwa friends d'inta sunyi tambayar duniyar akan ta fad'i abunda ke damunta
Amsar da take basu d'aya ce babu komai, itama ta rasa abunda yake sanya ta kuka da damuwa."


Wasa wasa har dijama ta kwanta ciwo saboda damuwar da tasanyawa ranta." Duk ta rame tayi bak'i."

Hidima akeyi gadan gadan ana saura kwana uku d'aurin aure Abba yaje makarantar domin ya d'aukota ayi bikin da ita."

Yayi mmkin ayanda yaga dijama ta koma, hankalinsa ya tashi da kan shi ya d'auketa ya sanyata a mota ko gida bai nufa ba kai tsaye asibiti ya nufa da ita."

Emergency aka nufa da ita aka bata gado tare da sanya mata ruwa had'ida yi mata allurar bacci."

Sai da tayi bacci snn likita yashiga yi mata aune aune, karon farko ya gano damuwa ce tayi mata yawa har ta kusan haddasa mata da ciwon zuciya."

Cikin mmki Abba yace "damuwa?"
Ya Shiga tunanin a duniyar nan meke damun ummie?"

Me ummie ta nema ta rasa a rayuwa?"
Yasan dijama marainiya ce damuwar rashin iyayen baxai hadda samata ciwon zuciya ba, tabbas akwai abunda yake damunta Wanda take b'oye mana."

Sai a lokacin ya tuna da bai sanar da kowa yazo da ita asibitiba."

Mommy ya kira yake shaida mata a lokacin tsohuwa tana kusa tanji duk abunda ake fad'i a wayar tun kafin mommy ta kashe wayar tsohuwa ta mik'e tsaye tana salati tace shi kenan mamuda ya kashe mun dijama sai da nace karya kaita bak'ar makarantar can ta kwana amma ya kafe a can zai kaita to ai ga irinta nan sauran kad'an ta mutu ba dan da Allah yasa hassan ya tafi yau ba, da sai dai akawo mana gawarta."

Mommy ta kashe wayar tace "inna ki kwantar da hankalinki ba laifin makaranta bane ciwo ne kawai Allah ya d'ora mata, ba kuma laifin mahmud bane."

Kai tsaye hanyar waje tsohuwa ta nufa da mayafinta a hannunta duk ta rud'e."

Khalil taci karo dashi ya shigo da mota yyi parking,
Yana ganinta hakan mayafi a hannu da alama a rud'e take ya saki dariya yace 'yar tsohuwa sai ina kuma haka naganki a rud'e mayafi a hannu?"

Kai tsaye ta wuce shi tana masifa, tana fad'in dan Allah matsa kabani wuri kake tambayata tunda ba ajiyeni kayiba. Ta nufi wurin motarsa tana Neman bud'ewa ta shiga."

Dariya ya dinga yi mata har da duk'ewa yana fad'in "wai yau meke damun tsohuwa ne."

Mommy tafito cikin shirinta zata tafi asibitin tana ganin tsohuwa tana k'ok'arin bud'e motar khalil dake rufe tashiga shi kuma yana gefenta sai dariya yake mata."

Mommy ta doka masa tsawa snn yashiga hankalinsa tace "maxa KA bud'e mata k'ofa tashiga kaja mutafi ka kaimu asibity dijama aka bawa gado bata da lfy."

Cikin tashin hankali ya xaro ido waje ai bai san lokacin da ya bud'ewa tsohuwa mota ta shigaba itama mommy ta Shiga da sauri ya shiga shima yaja motar da sauri ya nufi asibity."

Abba shi kad'ai zaune kusa da dijama Wanda sai bacci takeyi da ka ganta zaka gane ciwon ya dad'e a jikinta."

Waya yakeyi da mahmud yana fad'a masa halin da dijama take ciki,

Wani irin razana mahmud yyi Wanda sai da abokanan aikinsa suka kallesa,
Sai fad'in yake meyasa meta Abba?"
me akai mata?"
waya tab'a ta?" metake so?"

Ajere yake yiwa Abba wad'an nan tambayoyin wad'anda bai San yana yinsuba."
Ganin hankalinsa ya tashi Abba yace KA kwantar da hankalinka Mahmud da sauki ciwon ba wai irin sosai d'in nan bane."

Cewa yyi no Abba gani nan tafe yanxun nan ya kashe wayarsa ya mik'e cikin hanzari ya Shiga motarsa bai jira umurni daga Alhaji Atiku ba domin Mahmud har jira yakeyi yyi laifin da za'a koreshi daga aikin yake so."

Kai tsaye hanyar kano ya mik'a."

Duk wayar da yakeyi Yusra na kusa dashi bai San tazoba, ganin yanda ya firgice a nan take yana waya da alamar akwai Wanda baya da lafiya a cikin familynsu ta bishi da kallo ta ce Allah ya sauwak'e." Tayi yafiyarta."

Khalil yana yin parking a harabar asibitin bai ko jira su mommy suka fito ba,
ya rigasu fitowa da saurinsa ya nufi inda yake tunanin an ajiyeta, tsohuwa da mommy suna bayansa biye, mommy na kallonsa cike da mmki."

Kai tsaye d'akin ya nufa yana zuwa wurin gadonta ya nufa, da niyar ya rik'ata ya rungumeta,

Abba dake kusa da gadon ya dakatar dashi da cewa "khalil wai meye hakan ne?"

Turus yaja ya tsaya yana kallonta idonsa a kanta yace "Abba meke damunta ne?"

Abba yace "sai kaje KA tambayi likita yyi maka bayani."
Bani zaka tsare kana tambaya ba kamar Wanda ya aikoni."

Tsohuwa ta turo k'ofa suka shigo tare da mommy kai tsaye wurin dijama ta nufa tana shafa gefen fuskarta tana fad'in "shikenan mahmud ya kashe mun ke,
Dama sai da na ce ba na son makarantar nan amma aka k'i bin maganata sbda an d'aukeni tsohuwa 'yar k'auye to ynxun ai ga irin abunda nayiwa gudu kenan."

Mommy da Abba shuru sukayi, ba fad'an tsohuwa ba maimaita magana. Jinini😊

Khalil yace "dan Allah tsohuwa bacci takeyi idan kinsan fad'anki zakiyi kifita daga waje karki Tayar da ita daga bacci."

Ai kuwa kamar khalil ya hura mata wutar fasifa tashiga yi, "ubanka ne zai fita wajen bani ba,
Kai tsayuwar me kakeyi a nan duk KA wani d'aga hankalinka sai kace Wanda aka cewa ta mutu."

Bai tanka mata ba sai ma ya fita ya nufi office d'in likita domin ya tambaye shi meyake damunta."

Likita yyi mashi mayani kamar yanda yyiwa Abba,
Khalil ya fito yana mmki to me zai sanya dijama damuwa?"

Hakan dai jiki ba kwari ya nufi d'akin da take a kwance,
Kujerar da Abba ya tashi a nan yaje ya zauna had'ida tsora mata ido yana kallonta cike da tausayi."

Jinsa yakeyi kamar yaje ya rungumeta yayi ta lasarta saboda so da k'auna da kuma tausayi ta da yakeji."

Dijama kuma sai bacci takeyi, fuskarta tayi wani haske karan hancinta ya kuma fitowa ta rame sosai sai kuma
ta kuma yin kyau."

Awa uku suka kawo Mahmud garin kano, saka makon gudun da yakeyi baji ba gani kamar baya a hanyacinsa."

Kai tsaye asibitin ya nufa inda Abba ya fad'a masa, kai tsaye d'akin ya nufa muradinsa shine ya ga halin da dijama take cikinsa."

Yana shiga d'akin cikin wani taku, Wanda sai da ya dai dai ta natsuwarsa snn ya shiga da sallamar sa,
Gaba d'aya ido ya dawo kansa cike da mmki, ya akayi yasani?"

Murmushi yyi ya durk'usa ya gaida momy da tsohuwa, tare da yi masu ya mai jiki?"

Mommy tace gata can tunda mukazo take bacci har yanxun bata farka ba."
Har khalil ya gaji da zamansa ya yatafi ya dawo."

Mik'ewa yyi ya nufi wurin gadonta,
Ya k'ura mata ido cikin na tsuwa yake kallonta cike da tausayinta, ganin duk yanda ta rame ta fita hayyacinta,

Yaja dogon ajiyar zuciya ya juya ya kalli mommy yace "mommy me likita yace "dan gane da abunda yake damunta?"

Mommy tace "ban tambayi Abban ka ba,

Tsohuwa da tayi shuru cike da jin haushin mahmud shiyasa ma a lokacin da yashigo da ya gaida ita ko amsa masa batayiba sai ma harararsa da takeyi Wanda shi kuma mahmud bai lura da hakan ba,
domin ganin takeyi duk shine silar ciwon ta tunda ya kai ta makarantar bacci."

Mik'ewa yayi ya nufi office d'in likita,
Ya tambayi likita abunda yake damunta."

Likita ya shiga fad'a masa abunda ya fad'awa Abba da khalil,
Hannu mahmud ya dora a kuncinsa ya yi tagumi yashiga tunanin meyake damun dijama?"
Me tasanyawa rayuwarta hakan ne Wanda har zai haifar mata da ciwon xuciya."

Godiya yyiwa likita ya taso ya fito ya koma d'akin nata,


Abunda basu saniba tun da Mahmud ya shigo d'akin k'amshin turarensa ya daki hancin dijama tun a lokacin ta farka daga bacci da takeyi."

Zai shigo d'akin kenan ya hango khalil zai k'araso cikin saurinsa kamar baya ganin gabansa."

Tsayawa yyi sai da ya k'araso a bakin k'ofar sann khalil ya lura da Mahmud, wani fad'uwar gaba yaji, amma sai yyi k'ok'arin saita kansa yace brother yaushe kazo?"

Murmushi Mahmud yayi ya dafashi yace "d'an uwa rabin jiki, ai KA manta dani ko 'yar wayar nan KA daina kirana."

Khalil yayi murmushi yace "ai ban isaba wlh na manta da kai exam ce ta ta hanani sukuni."

Mahmud yace "eyya To Allah ya yabada sa'a."

"Ameen khalil yace had'ida Rigan mahmud shigewa d'akin,
Mahmud ya bi bayansa suka shiga a tare."

Kai tsaye khalil wurin gadonta ya nufa, yana fad'in mommy bata farka ba har yanxun?"

Mommy tace "bata farka ba,
Ko sai ankira likita ne?"

Shima mahmud wurin gadon ya nufa yana fad'in "ina ganin allurar da akayi mata ce ta bacci itace bata sake taba."

Dijama najin muryar mahmud a kusa da ita, a hankali ta shiga bud'e idonta ta d'orasu a kansa, tana kallonsa idonta ya cika da hawaye."

Shima idonsa a cikin nata ya kuma tsayawa daf da ita yana fad'in "sorry dijama sannu karkiyi kuka Allah shi zai baki lafiya,

Ya sanya hannunsa ya shiga share mata hawayen fuskarta, yana mata sannu ji yakeyi kamar ya cire mata ciwon ya dawo da shi jikinsa, wani kalar tausayi yake mata Wanda bai San yana dashi ba."

Nuni tayi masa da tanaso ta mik'e zaune, rik'ata yyi ta mik'e zaune had'ida gyara mata gashin kanta Wanda ya zubo ya rufe mata ido."

Wani rad'ad'i khalil yakeji yanda yaga Mahmud yana rik'a dijama kuma mommy da tsohuwa duk suna zaune a gefe d'aya suna gani basuyi magana ba
Amma ya lura idan shi yake mata haka da tuni an dakatar dashi, tare da nuna mashi b'acin ransu."

Amma ga Mahmud nan komai ba'a ce masa ba har da wani gyara mata gashi yakeyi, a maimakon yaga bacin rai a fuskar mommy saima gani yyi tana kallonsu tana murmushi a fuskarta."

Hankalinsa ya koma a wurin dijama a lokacin da take cewa "tana so ta sha ruwa."

Da sauri khalil ya mik'a hannu ya d'auko ruwa ya tsiyaya mata a cup ya bata,
Ko kallon inda yake batayi ba, mahmud take kallo gani tayi ya kuma yi mata kyau duk ya canxa mata kamar ba shiba."

Khalil yaji haushi tare da bak'in ciki, ya nufi wurin bakinta da niyar ya bata ruwan tasha."

Wata harara ta wurga masa mai cike da tsana snn ta kau da kanta gefe had'ida nok'e kafad'a alamar bata sha."

Mahmud ya amshi ruwan ya nufi bakinta yace "kisha ko kad'an ne mana."

Abun mmki sai ta bud'a baki mahmud ya yashiga bata ruwan sai da tasha ta k'oshi snn ta janye bakinta."

Mahmud ya juya ya kalli mommy yace mommy da akwai abinci a zuba mata?"

Mommy tace "fateema na kan hanya zata kawo yanzun."

Khalil tsaye ya k'ame wuri d'aya wani kalar kishi yaji yana azalzalarsa, anan take idonsa ya soma rikid'ewa ya fara komwwa zuwa launin ja."

Mommmy na lura da yanayin da yake ciki, amma sai tayi kamar bata ganeba."

Suna hakan likita ya turo k'ofa yashigo, ya sameta hakan alamar sauki ya samu da mmki yake tambayarta ya hakan?"

Murmushi kawai tayi, bayan ya kuma yi mata aune aune ya ga gaba d'aya ciwon zuciyar ya sauka,
Murmushi kawai yyi ya kalleta yaga ynda mahmud yake bata kulawa kamar mata da miji,
Murmushi ya kuma yi Domin ko ba'a fad'a masa ba yasan wnn dake zaune shine silar damuwarta."

Likita yyi gyaran murya yace "ya kamata kowa ya watse ya koma daga waje abar mutum d'aya Wanda zai kula da ita, domin tana buk'atar Hutu."

hakan yyi dai dai da shigowar Abba da fateema d'auke da kulolin abinci."

Mommy ta mik'e tsaye ta kalli tsohuwa tace "inna waza'a bari a wurinta ya kula da ita?"

Abba yace "mahmud ya tsaya ya kula da ita kafin zuwa anjima,

Khalil najin hakan yyi saurin juyawa ya kalli Abba da rinanun idanunsa,
Abba shi baima lura da yana wurinba. Sai a lokacin ya lura da shi da sukayi ido biyu."

Abba yace "khalil me kakeyi a nan KA wani tsaya masu a kai, fito kaje massalaci ga sallah magariba can ana kira."

Tsohuwa tace "ai kuwa shima Mahmud d'in bai kamata a barshi a wurin ba saboda idan aka barshi kuma k'ara sata zaiyi,

Mahmud ya sanya dariya yace "tsohuwa kifita a harkata kinga ko da nazo ban kulaki ba, kema ya kamata ki kyaleni kamar ynda na kyaleki."

Tsohuwa tace "kai d'in banxa,
Dole KA kyaleni tunda Kasan abunda kayi, saboda mugunta iri taka, kai a makarantar kwana kayi karatu ne?"

Dariya mahmud yasaki bai kuma kulata ba, dijama najin tsohuwa ta dage sai mahmud ya fita ya bar d'akin, sai dai ita ta zauna tayi jinyar tata."

A hankali ta koma ta kwanta a kan gado ta janyo hannun mahmud ta rik'e gam had'ida lumshe idonta ta rufe su."

Abba na ganin hakan ya saki murmushi irin nasu na mnya ya bud'e k'ofa ya fita, mommy ta bi bayansa,

Likita ya kallesu yyi murmushi tunaninsa ya zama gaskiya,
Ya kalli tsohuwa da bata lura da abunda ke faruwa ba yace "tsohuwa ya kamata ki shafawa kanki lafiya domin Wanda kike jinya ta zab'i Wanda takeso ya zauna a kusa da ita."

Sai a lokacin tsohuwa ta lura da ynda dijama ta rik'e hannunn mahmud GAM kamar Wanda zai tsere mata.

Tsohuwa ta mere baki tace indai mahmud gaki gashi

Dafe da banjo khalil ya bar wurin domin shima ji yakeyi zuciyarsa tana wani harba masa saboda wani kalar rad'ad'i da yakeji."

A tare suka bar d'akin tare da tsohuwa sai masifa takeyi da dijama a cewarta ta zab'i mahmud Wanda yake gana mata wahala yake dukanta ta barta."

Masifa kawai takeyi tanufi wurin mommy da Abba suka shiga bata hak'uri,

Ta gabansu Abba khalil ya wuce ya nufi motarsa ya figeta da k'arfi Wanda gaba d'aya hankalin mutanen dake cikin asibity ya dawo kansa, cike da tsoro mutane suka bishi da addu'a Allah ya sauke shi lafiya.

Abba na ganin hakan hankalinsa ya tashi shima ya shiga tashi motar ya bi bayansa."

Ido tsohuwa ta zaro waje cike da ayar tambaya ta kalli mommy tace "Hajiya Bilkisu shin wai meke damun khalil ne shi kuma?"

Mommy tace "wlh inna nima kaina bansan abunda yke damunsa ba wani lokacin sai yyita wasu abubuwa gashi nan dai."

Tsohuwa tace "to Allah ya kyauta ya kamata shima akaishi wurin likita ya dubashi daga ganinsa akwai abunda yake damunsa."

Gudu khalil yakeyi har baya ganin gabansa, Allah ne kawai ya tsareshi ya kaishi gida lafiya."

Yana yin parking Abba shima yana tsayawa da tasa mota,
A tare suka fito, Abba ya nufeshi a fusace ya d'aga hannu ya kwad'a masa mari har sau biyu."

Yace "bakada hankali be?"
Kake gudu da mota haka akan titi baka damu da rayuwarka bane,
Ya mik'a mashi hannu yace bani key d'in motata, tunda bakasan dajarar rayuwarka ba."

Khalil ya dafe kunci cike da b'acin rai da bak'in ciki yace "duka a gidan nan ni kad'ai aka tsana, nikad'ai ake nunawa rashin so ya kamata akashe ni kawai kowa ya huta."

Abba ya bishi da kallo yace "khalil mu mahaifan KA mune bama sonka?"

Ni kake fad'awa magana?" To nagode."

Abba ya koma mota ya shiga ya ya nufi asibity."

Dijama kwance a kan gado hannunta rik'e da hannun mahmud
Wanda shima ya tsinci kansa da kasa cire hannunsa daga nata sai ajiyar zuciya suke saukewa a tare."

A hankali ya janye hannunsa daga nata ya wanda yasa tayi saurin bud'e idonta sukayi ido biyu dashi idonta cikin nasa wanda ko wannensu ya kasa d'auke ido da ga kallon d'an uwansa."

Cikin jarunta ya tashi ya daga kan kujerar da yake ya koma gefen gado a kusa da ita ya zauna, still idonsa a kan nata suna kallon junansu, murmushi ya sakar mata had'ida hura mata iska a ido yace " wnn kallon fa na meye?"

Runtse idonta tayi tana mai sakin murmushi, a fuskarta,
Sunkuyawa yayi yasanya hannunsa ya shiga gyara mata gashin kanta. Da ya kuma zubowa a gaban goshinta, tare da Shafa beautiful face d'inta,

K'amshin turarensa ya daki hancinta, bugun numfashinsu yana mugun numfashin junansu."

Gaba d'ayansu suka tsinci Kansu cikin wani yanayi mai wuyar misaltuwa,
D'an k'aramin bakinta yagani yana motsi tana murmushi, bai San lokacin da ya tsinci kansa da d'ora nashi baki akan nataba ya sakar mata kiss."

Ko mai ya tuna oho yayi saurin tashi daga kan gadon ya dawo kan kujera ya zauna tare da saita kansa.

Ya kira sunanta a hankali ta bud'e idonta tana murmushi ta kallesa,

Yace "likita yace ciwon zuciya yake son kamaki, meyake damun?"

Me kika nema kika rasa a duniya?"
Ko akwai wani Abu da kikeso wanda har kike iya b'oye shi a ranki baki iya fad'a wanda har zai haifar mki da ciwon zuciya?"

Ko aure kike so?"

Tayi saurin girgiza kai had'ida turo baki, alamar shagwab'a."

Ko kinfara soyayya ne saurayin yace baya sonki?"

Idonta ya cika da hawaye tace "A'a

Please Login or Register in order to submit comment