Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewarsa aikinsa shine gatansa shine uwarsa shine ubansa marayane gaba da baya, a hannun k'anin mahaifinsa ya tashi Wanda shima talaka ne abincin da zasuci wuya yake masu."
Kuma a hakan ya aurawa sulaiman 'yarsa fareeda Wanda suka tashi cike da soyayyar junansu."

Da taimakon Allah kamar da wasa aka fitar da form d'in soja fareeda ta sayar da kayan d'akinta tabawa mahaifinta ya sayawa sulaiman form d'in,
Cikin ikon Allah sunansa ya fito, wnda gashi a yanzun ya fara wadata a aikin soja, domin ya sayawa k'anin mahaifinsa k'aton gida ya kuma bud'a masa babban shago na sayar da atamfofi."

Kai tsaye mahmud ya tunkari wurin inda akeyin liyafar domin kiran sulaima, yusra tana ganinsa takar masa murmushi tana Neman ta bar wurin tazo wurinsa,
Alhaji Atiku na ganin hakan yayi saurin rik'o hannunta ya dawo da ita a inda take yana mata magana k'asa k'asa Wanda su kad'ai sukasan abunda suke cewa."

Mahmud bai damu dasuba kai tsaye wurin sulaiman ya nufa yashiga yimasa magana cikin harshin turanci cewa fareeda tazo gata can tana jiransa."

Jin hakan sai da yasaki murmushi jin dad'i yacewa Mahmud ya kaita masaukinsu da ke nan cikin gidan can layin sojoji, ya ajiyeta,
Had'ida kawo mata ruwa da abinci tasha kafin yazo."

Murmushi Mahmud kawai yyi ya juya ya tafi,
Idon yusra akansa tanajin wata kalar wutar k'aunasa tana ruruwa a zuciyarta domin mahmud jarumi ne daga ganinsa zaiyi jarumta wurin tafiyar da macce a kan gado."

Tunshigowar fareeda wurin idon Alhaji Atiku ya sauka a kanta, yana ganinta yaji gaba d'aya hanlinsa ya tashi so yakeyi kawai yajishi ya kad'aice da ita."

Mahmud na tafiya ya kalli sulaiman ya masa nuni da hannu a lamar yaje wurin matarsa ya kuma zaro kud'i cikin aljihunsa dubu ashirin ya mik'a masa yace kasaya mata kayan motsa baki."

Cike da murna sulaiman ya runsuna ya karb'a yana godiya, yatafi wurin fareeda."

Da isarsa mahmud yana fitowa daga d'akin,
Cikin murna sulaiman ya tareshi yana dariya yana fad'a masa Alherin da Alhaji Atiku yayi masa."

Gaban mahmud ya fad'i ya zaro ido yace "ina fatan baiga shigowar fareeda ba?'

Sulaiman yasaki dariya yace "maiya faru idan har ya ganta?"
Mahmud yace "no bakomai tambaya ce kawai nayi, yayi wucewarsa, yana tunanin tambas Alhaji Atiku fareeda yagani tunda har yabawa sulaiman kyautar kud'i, Dama hakan yakeyi da zarar ya kyallara ido yaga matar yaronsa in dai har ta kwanta masa zai dinga yiwa yaron nasa Alheri na Jan hankali."

*******************

Bayan an watse daga wurin liyafar kowa yakoma wurin aikinsa,
Alhaji Atiku da shalale sai zuba mashi shagwab'a takeyi akan wutar son mahmud dake ruruwa a zuciyarta."

Ransa ya b'aci ganin ynda shalele take zubar da hawayenta akan wani d'a namiji kuma yaronsa, Wanda yake da iko dashi har da mahaifinsa."

Janyota yayi a jikinsa ya shiga share mata hawayen da ke zuba a fuskarta yace "daga yau kukanki ya k'are indai akan mahmud ne."

Wayarsa ya d'auka yashiga kiran number Alhaji Hassan mahaifin mahmud."

Abba yana ganin wayar Alhaji Atiku tunkafin ya d'auka sai da yasaki dariya snn ya daga wayar had'ida sallama,
Alhaji Atiku ya amsa masa yana mai sakin fara'a a fuskarsa."

Bayan sun kammala gaisuwar ne Alhaji Atiku yake shaida masa gobe yyi sauri yazo garin Abuja akwai meeting da zasuyi game da harkokin siyasa."

To Abba yace yana mai d'auke da fara'a da jin dad'i a fuskarsa, snn sukayi sallama ko wanne ya kashe wayarsa."

Ya juya ya kalli yusra yasaki dariya mai sauti yace "nayi mki Alk'awarin bazaki tab'a Neman wani Abu kirasaba, ki sanyawa rayuwarki a gobe za'a tsayar da ranar aurenki da Mahmud ko yaso ko baya so wnn matsalarsa ce."

Washe gari bayan Abba ya sauka garin Abuja sunshiga meeting da manya yan siyasa, anan take da San hannun Alhaji Atiku aka tsayar da Abba a matsayin d'an takarar gwamna. Kasan cewar Alhaji Atiku shikeda jama'a dan haka ko wanne d'an takara yakeyi masa biyayya."

Sauran mutunen wurin sun Amince da zab'en Alhaji Atiku anan aka umurce Abba da ya biya kud'in k'ungiya naira milyan talatin."

Abba yayi shuru domin baya da miliyan talatin, ganin shurun da yayi yasa Alhaji Atiku ya fahimce cewa baya dasu, yasaki murmushi a ransa domin hakan yakeso ya gani."

Anan take Alhaji Atiku ya cika cak d'in kud'in ya bayar."

Zaro ido Abba YAYi cike da mmki zaiyi magana Alhaji Atiku ya dakatar dashi alamar yayi shuru idan aka tashi akwai maganar da zasuyi."

Bayan kowa ya watse daga meeting d'in akabar Alhaki Atiku da Abba a office d'in Abba sai godiya yake zuba masa wanda har yarasa abunda zai fad'a."

Alhaji Atiku ya dafa kafad'arsa yace dainayi mun godiya hakan ta isheni, kasani duk abinda nayi maka ban fad'i ba saboda kai abokinane kuma aminina na gaskya. Komai nawa ina iya mallaka maka shi a kyauta"

Wnn dalilin yasa saboda mu kuma dank'on zumunci mu ya d'ore har d'iya da jikoki na yanke shawarar mu had'a 'ya'yanmu Aure mahmud da yusra."

🌹 *DEEJAMA*🌹







Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)







*33*






Abba yayi murmushi ya kalli Alhaji Atiku yace " kayi tunani mai kyau, Alhaji Atiku
Amma sai dai bntari numfashinka ba,
Sai dai d'anka Mahmud yana da wacce zai aura 'yar k'anena marigayi husaini Wanda muka d'aukarwa junanmu Alk'awarin tun kafin Allah ya karb'i rywarsa zamu had'asu aure domin k'ara dank'on zumunci mai d'orewa."

Alhaji Atiku yayi murmushi mai cike da wata manufa, yace " bakomai zan bata hak'uri akan cewa duk ynda take sonshi ta hak'ura da shi, Allah ya bata dangana."

Abba duk yaji ba dad'i da yatuna da irin halaccin da taimakon da Alhaji Atiku yayi masa."

Idan ya hana mahmud ya auri yusra tambas ya nuna rashin halaccinsa garesa."
Alhaji Atiku ya mik'e tsaye a hasale ya kalli Abba yace "to Alhaji hassan ni zantafi sai munyi waya kuma."

Abba ya rik'o hannunsa ya dawo dashi ya zauna yayi murmushi yace Alhaji Atiku ka fahimce mana kasan girman Alk'awari Wanda idan bancika shiba Allah zai iya kamani ta ko wacce hanya."

Banak'i mahmud ya auri yusra bane, yusra da muhmud dukansu 'ya'yana ne,
Na Amince Mahmud ya auri yusra,
Amma bayan ya aureta ko yaushene ko nan da shekara nawa ne zai aure Ummie yyi ta biyu da ita."

Sai a lokacin Alhaji Atiku yasaki dariya yace "wnn ba Matsala bace aidama namiji macce hud'u aka umurce sa da yyi, amma dani da kai munsanya rangwanci mun zauna da macce d'aya,
Suka sanya dariya suka tab'a."

Daga k'arshe sukayi sallama,
Abba ya neme Alfarmar da aturo masa Mahmud ya sameshi a kano akwai maganar da zaiyi dashi,
Snn daga k'arshe sai ansaya ranar auren nasu."
Hakan suka rabu Alhaji Atiku zuciyar sa cike take da farin ciki shalelensa ta samu abunda takeso."

Alhaji Atiku yana Shigar da motarsa a harabar gidansa yaci karo da fareeda da sulaiman yana d'auke da d'ansu Ammar xaiyi masu rakiya zuwa Tasha domin su shiga mota zuwa sokoto."

Alhaji Atiku Yana ganinta yaji gaba d'aya hankalinsa ya tashi akanta burinsa kawai shine ya yajishi a kanta."

Kasan cewa fareeda cikakkiyar macce ce mai siga da haiba tana da jikinta irin na manya mata wanda duk namijin da yayi ido biyu da ita idai lafiyayyene sai yaji wani abu a tare dashi game da ita."

Horn ya dinga yimasu yana lasar baki kamar wani maye,
alamar SU dakata sulaima ya lura da abunda yake nufi yayi saurin yi mata magana sukaja gefe d'aya suka zauna."

Da sauri ya ajiye motarsa wurin ajiye motoci ya fito yanufesu idonsa akan fareeda yana mata wani kallo na k'urullah."

Fareeda na lura da kallon da yake mata anan take taji ta tsaneshi, bata son had'a ido dashi.'

Sulaiman ya sare masa alamar girmamawa, ya amsa masa yana murmushi still idonsa akan fareeda."

Ya kalli sulaiman yace "ina zakuje hakan?"

Sulaiman yace "ranka ya dad'e zanraka ta tasha ta shiga mota zata koma gida ne."

Alhaji Atiku yace "meyasa bazata dawo nan da xamaba kamar ynda wasu daga cikinku sukeyi?"

Murmushi kawai sulaiman yyi,
Alhaji Atiku yanuna masa wani d'aki inda ba kowa a cikinsa a can nesa da tsohon d'akinsu,

A kusa da wasu matan sojoji, yace ka ajiye matar ka a can duk abunda kuke buk'ata akwai a ciki."

Snn duk lokacin da ta buk'aci zuwa ganin gida tana iya zuwa ta dawo, INA ganin hakan ya fiye maku sauk'i."

Godiya sulaiman ya shiga yimasa tare da Addu'ar Allah ya k'ara girma."

Fareeda itama ta d'an k'ak'aro murmushin dole tayi masa godiya snn suka juya suka nufi inda ya nuna masu d'in."

Suna tafiya Alhaji Atiku idonsa a kan fareeda yana kallon yanda take tafiya k'ugunta na juyawa."

Mahmud da shigowarsa kenan yaci karo da Alhaji Atiku tsaye wuri d'aya yana kallon wani wurin yana lasar baki yana murmushi."

Inda yake kallo shima mahmud yabi wurin da kallo fareeda yagani da sulaiman suna tafiya,
Gabansa ya yanke ya fad'i domin yasan bbu Wanda yake yiwa wnn kallon sai fareeda daman yasan hakan sai ya faru."

Ya kuma matsawa daf dashi cike da takaici yace "ranka ya dad'e ko kasanta ne,?"

Cikin raxana ya juyo yana ganin mahmud ne ya had'e fuska yace "mekace Mahmud ne?"

D'an murmushi Mahmud yyi na gefen baki yace "no cewa nyi meya faru na ganka a nan tsaye?"

Alhaji Atiku yyi murmushi had'ida Sosa kai yace "kai nake nema, ka shirya gobe katafi kano Alhaji Hassan yana nemanka kuma idan katafi kabari sai ka huta kayi sati biyu snn kadawo."

Mahmud ya had'e fuska yace "ranka ya dad'e baxanyi sati biyu ba
Saboda baya daga cikin dokokin aikina in har bani da kaina narubuta hutuba
Na d'aukarwa k'asata Alk'awari xan tsaya nayi aiki a kan gskiya. Dan haka bbu wani dalili da zai sanya natafi gida na zauna na huta har tsawon sati biyu ."

Yana kaiwa nan bai jira Alhaji Atiku yyi magana ba yyi tafiyarsa, ya barsa a nan tsaye,
yana mmkin mahmud,
Tunda ya fara aikin soja har zuwa yanzun da yake a matsayin commondent bbu wani yaronsa dayake tsayawa gaba da gaba ya nuna baya tsoronsa ya kuma fad'a masa magana ynda yaga Dama kamar Mahmud, kuma abun mmki sai ya tsinci kansa da kasa yimasa hukunci."

Hakan ya juya yayi shigewarsa ciki, da shigarsa yaci karo da yusra zaune akan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya da k'atuwar wayarta a hannunta da alamar chatting takeyi,
tana zaman jiran shigowarsa domin daga yau ta gaji da Alk'awarin da yake mata akan cewa mahmud natane amma kuma har ynxun baizama na ta d'inba kullum idan tayi ido biyu dashi jitakeyi kamar taje ta rungumeshi ta kuma jin wani sabon son shi yana dirar mata a zuciya."

Yana ganinta yasaki dariya tare da fad'in shalelen daddy Albishirinki Nazo mki da wani Albishir Wanda sai kinbani kyauta."

Mere baki tayi had'ida ya mutsa fuska tace "ina saurarenka daddy."

Yanayin ynda ta amsa masa sai baji dad'iba. Amma kuma sai ya tunkareta ya zauna kusa da ita,
Yace "yau mahaifin Mahmud yazo mun zauna dashi ya Amince mun da cewa ya yarda mahmud ya aure ki"

Wani irin tsalle tayi had'ida kwatsa ihu ta fad'a kan jikinsa cike da murna, tace "daddy yaushe aka sanya ranar bikin namu."

Ya kalleta yasaki dariya domin yaji dad'in ynda ya ganta cikim farin ciki,
Yace "ba'a sanya ranaba sai nan da kwana biyu idan mahmud ya dawo daga kano inda yake nemansa sai nkira mahaifin nasa mu sanya ranar bikin naku.":

Kuma k'ank'ame shi tayi tana dariyar jin dad'i tana fad'in "ina sonka daddy na saboda kana bani duk abunda nkeso, muddun ka aura mun mahmud hak'ik'a kagama mun komai a rayuwa."
Daddy ina son mahmud so mai tsanani soyayyar da bantab'ayin irintaba, hawaye suka dinga zuba a fuskarta."

Yashiga shafe mata hawaye yace "daina kuka kinsamu mahmud, mahmud ya zama naki."

************

Bayan Abba ya dawo gida yake gayawa mommy an tsayar dashi a matsayin d'an takarar gwamna, da kuma irin d'inbin alherin da Alhaji Atiku yyi masa da yabiya masa makudan kud'in kungiya da aka nema."

Mommy taji dad'i sosai ta kuma sanyawa Alhaji Atiku Albarka."

Sai da tayi shuru ta natsu fuskarta cike da farin ciki snn Abba ya kuma kiran sunanta cikin natsuwa, yashiga shaida mata manufar Alhaji Atiku akan yaransu."

Anan take fuskar mommy ta canxa tace "Sam bazai yuwoba yarinyar da bata da tarbiya, za'a had'ata da mahmud."

Anan Abba yashiga lallashinta yace tayi hak'uri "tabari Mahmud yazo idan anyi masa magana ya nuna baya ra'ayinta to bazamuyi masa doleba sai dai Alhaji Atiku da 'yarsa su hak'ura.

Idan kuma ya Amince saikiyi hkr kibisu da Addu'a, ita shiriya ta Allah ce."

Mommy taja bakinta tayi shuru Dan ita har ga Allah bata son mahmud ya auri yusra."

****************

Akwana a tashi ba wuya a wurin Allah Deejama anshiga ss2,
Ilimi ya samu Arabic da boko,

Duk Wanda yasan deejama a da ya ganta a yanxun ba zai ganetaba, domin ta girma ta waye ta zama cikakkiyar budurwa 'yar birni maiji da kanta."

Duk wata halitta ta cikakkiyar 'ya macce ta fito mata gata dogowa fara kyakkyawa k'irjinta ya cika hakan k'ugunta idan kagani masha Allah."

Deejama ga aji domin a halin yanzun bata fiya son yawan magana ba sosai
Amma har idan taga za'a shiga hak'inta Zata dawo dijamarta ta ainahi ta kwatarwa kanta 'yanci."

Hakan yasa Khalil ya kuma fad'awa cikin matsanancin Sonta, wnda a yanda yakeji akanta komai yana iya aikatawa in har zai sanya ya mallake ta

Deejama itace macce da yake tsarawa rayuwarsa xai yi rayuwar aure da ita
Deejama tana d'aya daga cikin Matan da samun irinsu sai antona, domin da zarar kayi ido biyu da ita zaka fahimci akwai wani sirri a tare da ita Wanda ba ko wacce 'ya macce ke tare da shiba."

Ya dad'e yana ganinta a mafarkinsa, ya dad'e yana nemanta Ashe k'anwarsa ce jininsa ce, 'yar uwarsa ce Dan haka duk duniyar nan ba Wanda ya isa ya hanashi ya aure deejama."

Duk wani katanga da Abba yake masa a kanta, duk wani killaceta da akeyi idan aka gansa yashigo gida to ayi agama domin babu wnda ya isa ya aure dijama Indai yana numfashi a doron k'asa."

*****************

Abba Ganin hankalin da deejama tayi da natsuwarta, yasa Abba yaji dad'i sosai ya kuma samun natsuwa da ita,
Wnn dalilin yasa ya saya masu mota d'aya ita da fateema ya Sanya aka koyawa ko wannensu, idan dijama ta zo Hutu itake amfani da ita idan kuma ta koma makaranta fateema ke amfani da ita."

A yanxun anyi masu hutun zangon k'arshe wanda daga sun koma zasu shiga ss3

Zaune take a babban falon gidan sanye take da k'ananun kaya riga da wando 'yan fakistan Wanda sukayi mata kyau, hannunta rik'e da k'atuwar wayarta Wanda Abba ya saya mata, kunnenta sanye da airface tana sauraren karatun Alqur'ani tana tilawa had'ida gyad'a kanta duk Wanda ya ganta hakan sai ya rantse da Allah wak'a ce take saurare tana gyad'a kai."

Hkan Al'adarta take bata son sanya manya kaya irinsu Atamfa ko lass ko shadda a jikinta tafi son k'ananun kaya, a cewarta mnya kaya nauyi suke mata ajiki."

Fateema ce tafito cikin shirinta sanye take da atamfa ta yafa gyalenta irin Atamfarta yellow, hannunta d'auke da handbag d'inta tafito ta kalli inda dijama take kwance a kan doguwar kujara kamar wata sarauniyar kyau, tace "sister nashirya mutafi kawai."

Kallonta dijama tayi tayi murnushi tace " kin karb'o kud'in a wurin mommy?"

Fateema tace "ai tun jiya Abba ya bamu kud'in yace idan basu isaba muyi masa waya a can wurin shoping d'in zai turo akawo Mana wasu kud'in."

Girgiza kai tayi bata kuma yin maganaba illah ta d'auki mayafin kayanta tayi Rollin dashi fuskarta ta fito kamar balarabiya suka shiga sukayiwa mommy sallama suka fito, dijama ta shiga mazaunin direba ta tayar da motar suka tafi."

Bayan sunyi shoping d'in a hanyarsu ta dawowa gida motarsu ta tsaya akan titi, dijama dake driven ta dafe kai cike da takaici ta juya ta kalli fateema tace "sister meke faru haka?"

Fateema tace "mufita mugani."

Hakan suka fita suka bud'e motar suka shiga d'an gyara wurin da suke tsammanin shike basu matsala,
Suka dawo suka shiga motar dijama ta kunna ai kuwa ba mmki gani sukayi motar ta tashi."

Basu d'aga daga inda sukeba horn kawai sukeji yana tashi gabansu da bayansu, abun mmki dibawar da xasuyi gosulo ne mutane cincirindo gabansu da bayansu suna jiran SU kauce daga kan titi."

Hankalin fateema ya tashi ta zaro ido waje tace "munshiga uku sister diba kiga mutane ynda suka zagayemu duk mu muka tsayar dasu, Dan Allah sister tayar da motar muyi tafiyarmu mubasu wuri."

Deejama tayi murmushi domin ita abun burgeta yayi ganin duk itace sanadiyar tara wnn gosulon."

Tace wlh ban tashi tafiyarba a yanzun."

Sai ma tabud'e glass d'in tsakiyar motar ta tashi tsaye ta fito ta sama tana kallon cincirindon mutanen da ke wurin d'aya bayan d'aya."

Haushi ya kama mutane wani mutum matashi ya hasala ya fito ya nufota yana nunata yana fad'in "ke 'yar gidan ubnwaye da zakiyiwa mutane tsaye a kan titi saikace gidanku anayimaki magana kin kuma gyale mutane."

Ta kallesa ta ya mutsa fuska cikin tsiwa tace "ni 'yar gidan ubanka ce idan kuma ka isa kacika marar kunya kazo ka janyemu daga nan."

Ai kuwa mutane kamar jira sukeyi kowa ya taso yana fad'in abunda ke cikin ransa itama tana mayar masu tace kuma bazata janye daga kan titinba sai dai kowa ya kwana anan."

Hankalin fateema ya kuma tashi ta fashe da kuka da ta kuma juyawa ta kalli mutanen dake wurin,
Tashiga had'a dijama da Allah akan suwuce sutafi idonta yana zubar da hawaye ita dai fateema bata son tashin hankali da hayaniya."

Dijama ta doka mata tsawa tace "yimun shuru sanlatacciya to bantashi tafiyarba."

Mahmud da Ya yafito daga Abuja duk a gajiye yake, ya matsu ya Ganshi ya isa gida domin ya watsa ruwa ya huta gashi indai ya kammala abunda yakeyi yau zaikoma bakin aikinsa ko kwana baZaiyiba saiyaga iyakar Alhaji Atiku domin ya gano manufarsa a kan fareeda."

Wnn gosulo ya tsayar dashi saiyi yakeyi yana kallon agogon hannunsa dogon tsaki yaja yana mmkin abunda ya haifar da gululon har ynxun ba'a fara tafiyaba kowa yana nan ynda yke atsaitsaye."

Hayaniya yajiyo a can gabansa inda baya iya hango abunda ke faruwa amma da alamar kamar fad'a ne akeyi."

Ya bud'e murfin motarsa ya fito yana sanye da uniform d'insa na soja, da saurinsa ya dinga ratsa mutane yana k'ok'arin isa inda yakejin fad'an na tashi."

Da kyar yasamu ya isa wurin abun mmki deejama ya gani tsaye akan mota sai tsiwa take yiwa mutane ta tare hanya."

Dibonsa ya kai a cikin motar wa zai gani fateema ce zaune wuri d'aya sai matsar hawaye takeyi."

Dijama na juyowa cikin masifa tayi ido biyu da yaya Mahmud yana k'ok'arin isowa inda suke daga ganinshi a hasale yake."
Ta zaro ido waje cike da tsoro tace "sister munshiga uku yaya mahmud."

Fateema ta juya ta kallesa cike da tsoro shike nan kin janyo mana duka.'

Da sauri deejama ta shiga mota taja da k'arfi, ko kafin mahmud ya kawo wurin su tabar wurin a guje."

Kallo yabisu dashi ya girgixa kai yayi masu alamar zansa sameku a gidan."
wato duk da ake cewa dijama tayi hankali mai hali baya fasa halinsa."

Mutanen wurin suka fahimci ganinsa ne yasa tabasu hanya ai kuwa suka shiga yimasa godiya, shi kuma yana basu hak'uri."

Snn kowa ya fara tafiya, wurin uxurinsa."

🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'yar gidan tsohuwa_)πŸ˜…






Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)





*34*


*Bntab'a tinanin hakan kuke bin labarin nan ba, kai amma naji dad'i so sai ina godiya gareku masoyana Ummu Safwan na sonku irin sosai d'in nan, ina fatan kunfara shirye2 Azimi Allah kasa zakuzo har zamfara kukawo mun kayan Aximi nah ngd Sosai da kulawa😍😍😍*






A guje suka iso gida dijama nayin parking har rigaggen fita sukeyi daga motar, da
gudu suka wuce mommy a falo suka shige d'akinsu suka turo k'ofa had'ida sanya key."

ko wacce ta fad'a kan gado tana sauke mumfashin gudun da tayi, fateema ta kalli dijama tace "kingani sister ynxun kinjanyo mana duka a wurin yaya Mahmud."

Dijama ta kalleta tasaki dariya tace "tab amma dai wallahi ke matsoraciya ce, ke da tsayawa zakiyi ya dakeki?"
Ai wallahi muddun kikaganni na tsaya yaya Mahmud ya dakeni to ba k'aramin mamayata yayi ba."

Dan ina ganin har ya koma Abuja bazai sanyani a idoba bare ya dakeni."

Fateema tace "to yaxamu yanxun?"
Dijama tace "ke dai kibarmun komai a hannuna duk abunda kikaga nayi kema kiyi domin kisamu ki tserewa dukansa."

Fateema tace "to cike da tsoro, bayyane a fuskarta."


Cikin mmki mommy tabisu da kallo da alamar tambaya d'auke a fuskarta,
Mik'ewa tayi zata nufi d'akinsu domin taji meya samesu suke gudu haka?"

Sallamar mahmud ta tsayar da ita, da yashigo yana zarar ido ina xai gansu,

Anan take samu amsar tambayar ta akansu,
illah ta nunawa Mahmud d'akinsu tace suna ciki sun kulle sun sanya key."

Girgixa kai yyi yace zaku fito ne kusameni yau sainayi maganin rashin jinku, musamman ke dijama."

Snn yasamu wuri ya xauna akan kujera had'ida durk'usawa ya gaida mommy cike da girmamawa."

Mommy ta amsa mashi cike da kulawa had'ida tambayarsa aikinsa."

Lafiya glau yace " had'ida tambayar Abba da Khalil."

Mommy tace "Abbanka ya fita amma ba nesa ya tafiba ynxun zai dawo."

Khalil shima ya fita yace mun ya tafi
gidansu Ahmad abokinsa."

Ta kallesa tace "laifin me su fateema suka aikata a wajen ne."

Anan yashiga bata labarin gosulon da suka had'awa mutane akan hanya."

Mommy ta rik'e baki cike da mmki tace "wad'an yara Allah ya shiryamun su."

Mahmud yace "Ameen."
Amma duk na rik'asu sai sungane kuskuren da sukayi."

Snn yace "yawwa mommy wai Neman me Abba yake yimun maike faruwa ne?"

Mommy ta mere baki da ta tunada da domin auren yusra ake nemansa."
Tace "nima bansani ba kabari kawai sai Abban naku ya dawo."

"To yace "had'ida mik'ewa tsaye yace "bara nashiga na nayi wanka naci abinci kafin Abba ya dawo."

***************

Alhaji Atiku yana ganin mahmud yayi sallama dashi ya tafi
, ya sauke ajiyar zuciya dama ganinsa ya hanashi zuwa wurin fareeda domin ya aiwatar da nufinsa."

Amma ynxun tafiyar nan tashi tabashi damar yin duk abunda yakeso da ita batare da wani shamaki ba."

Misalin k'arfe biyar ya rubuta posting letter ya aika aka kira masa sulaiman ya mik'a masa takardar, sulaiman yana dubawa yaga anyi posting d'insa a can nesa da gari, wani bank ne zaije ya kula dashi."

Murmushi yyi ya kalli Alhaji Atiku yace "ranka ya dad'e mainayi kuma akayi posting d'ina."

Murmushi Alhaji Atiku yayi ya juya kujerarsa yace "bakayi komaiba sulaiman Alheri ne zaka samo a can, wnda saikayi farin ciki da hakan, ka kwantar da hankalinka karka damu bawani dad'ewa zakayiba sati d'aya ne zuwa biyu zakayi sai ka dawo."

Murmushi sulaiman ya kuma yi yace "nagode ranka ya dad'e Allah ya k'ara girma, ya juya ya fita."

Alhaji Atiku yabi bayan shi da kallo, yana murmushin samun nasara."

Misalin k'arfe 7:pm sulaiman ya gama shirya kayansa tsaf a kwati, ya kalli fareeda dake rugume dashi ita Sam bata son yatafi ya barta,
Yashiga bata hak'uri da kwantar mata da hankali cewa ba dad'ewa zaiyi ba sati d'aya ne zaiyi ya dawo ta kula da kanta."
Ya duk'a yyiwa Ammar kiss a goshi wnda yake kwance barcinsa kawai yake yi,

Snn ya fita fareeda tayi masa rakiya har motarsu ta ma'aikata ya shiga ya tayar tana d'aga masa hannu har yafita daga gidan snn ta koma cikin

Please Login or Register in order to submit comment