Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT)
(ADMIN OF ADMINS)
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
09030159301
[7/17, 10:43] Washa: 💎💦💎
💝


GARKUWA
(RELIANCE)


FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W💝


💎MMN USWAN.💎


Dedicated to sweet sis mardiya ka'oje


happy Sallah to all Muslims Sisters and brothers In Islam.

May Allah protect us and accept our Ibada Ameen ya Allah.


Bissmillahi Rahmani Rahim


1

"Zahra xan sha ruwa Zahra.

"Zahra ruwa Zahra.

"Da sauri Zahra taxo tana cewa baffa!!!!! Baffa me kake bukata baffa?

"Baffa yasake cewa ruwa.

"Duk da haka Zahra bata jiba saida ta kara kunninta kusa da bakin baffa snn taji abinda yake fadi.

"Baffa yana mgnr ne cikin yanayi na karayar harshe.

"Da alamu dai lokaci yake jira.

"A guje Zahra taje ta dibo ruwa a randar dake sakarkari ta dawo.

"Tallafowa baffa kai tai yadin dago snn ta dauki kwanin shan ruwan ta bashi.

"yana sha yai wani irin ajiyar zuciya, gaba daya idanusa duk sunyi sama wayarsa ta karye.

"Me dashi Zahra tai ya kwanta.

"Yana kwaciya tai wani irin nushi.

"Snn ya kamo hannu Zahra da karfi ya rike, Baffa yana mgnr ne cikin wani irin yanayi.

"Zahra na gani haka tafara kwalla.

"Baffa yace Zahra banida abinda da xancewa ubangiji sai godiya.

"Daya azurtani dake, Zahra inaso ki kasance yarinya me hakuri da juriya duk yanayin da kika tsinci kanki.

"Zahra ki kasance me biyyaya ga nagaba dake.

"Zahra duk abinda zakiyi kiji tsoron Allah.

"Ni tawa taxo karke, Zahra kiyi hakuri da rayuwa.

"Kada kibiyewa zugun mutani kice zaki bijirewa hajjo.

"Hajjo tamkar uwa take a gunki.


"Zahra inaso kiwa hajjo biyayya ki dauketa tamkar itace uwa mahaifiyarki zahra.

"Kinji ko Zahra.

"Zahra ta fashe da wani irin kuka tana fadin naji baffa, Baffa in Allah ya yarda xaka tashi.

"Baffa cuta ba mutuwa bane baffa.

"Baffa kada katafi ka barni baffa, Baffa banida kowa saikai baffa.

"Baffa kaine gatana baffa, baffa kada kaimin haka baffa.

"Baffa yace zahra ina Hajjo?

"Zahra tace Hajjo na gidan mai gari.

"Baffa yace ruga ki kirami ita.

"Da sauri Zahra ta mike hade da cewa to Baffa.

"Ko takalmi Zahra bata tsaya sawa ba a guje ta ruga xuwa gidan mai gari.

"Ko sallama Zahra batai ba haka ta amka kasu tana cewa ina kizo.

"Gani Zahra da tai a birkice,wani irin tsaki tai hade da cewa to bakar agunguma me kuma ya faru?

"Jin haka jikin Zahra yai sanyi, a sanyaye take mgnr tace baffa ne yace kizo.

"Hajjo tace me zanmasa kuma?

"Babu dama aga mutum yafita shan'iska, Sankace tawa uwar yake tsinanamin.

"Haule kawar Hajjo tai wani irin shewa hade da cewa mutuniyata kenan baki da dama fa.

"Idan banda abinki mutumi da yake fama da kansa me kikeso yai maki?

"Murmushi Hajjo tai snn tace idan banda abinki Haule raifa dangi goro.

"Haule tace kinada gaskiya mutuniyata.

"Juyowa Hajjo tai hade da dakawa Zahra tsawa tana cewa bacemin a gaba kibagu.

"A sanyaye Zahra ta juya...

"Da sauri Haule tace aa ba haka xa'ai ba.

"Jeki kice tana xuwa.

"Ko tankawa Zahra batai ba, haka tafita tabar gidan.

"Zahra na fita su Hajjo da Haule sukai shewa hade da tafawa.

"Zahra na komawa gida ta sami baffa yana faman mutsuke3.

"Da sauri ta karisa gunsa hade da cewa Baffa jikin ne?

"Baffa Baffa Baffa.

"Wayyo Allah Baffa na, Baffana kada ka tafi ka barni.

"Baffa idan katafi ka barni mutuwa zanyi Baffa.

"Baffa sai faman hasa2 yakeyi.

"Zahra na gani haka dagosa tai ta rungume duk tana yine tana kuka.

"Baffa sai salati, salati yakeyi babu kabkabtawa har yacika.

"Yana cikawa Hajjo na sallama.

"Gani ya daina shure2 ne kuma wayarsa ya karye idanu na kallon sama baki a bude.

"Wani irin ihu Zahra tasa, Tana fadin nashiga uku na lalace.

"Shikenan tawa ta kare.

"Baffa katafi ka barni, yadda innata ta tafi ta barni.

"Jin haka yasa Hajjo ta kariso da sauri.

"Gani Baffa bayako shurawa yasa sa wata uwar ihu tana fadin shikenan Haruna, Haruna lokaci yayi Allah ya jikanka yasa ka huta yasa iyakacin jinyar kenan.

"Shinfidashi sukai ita da Zahra.

"Nan da nan bada bata lokaci ba akai masa sutura aka kaisa makwancisa.

"Zahra babu abinda takeyi sae kuka, ko abinci ma bata iya ciba sbd kuka.

"Maryama kawar Zahra tai lailaishi har tagaji.

"Yar'uwar mmnta duk sunxo daga ruga.

"Maryama da yar'uwan mmn Zahra tare suke zaune har akai addu'ar uku.

"Bayan addu'ar uku ne yar'uwar mmn Zahra sukace abasu Zahra sutafi tare.

"Malam Habu kanin malam Haruna yace baza'a basu ba.

"Daya daga cikinsu itace uwarsu daya ubansu daya da mmn Zahra tace dan Allah abata Zahra sbd ita kadai take gani a matsayin yar'uwanta.

"Malam Habu shima yace ita kadai yake gani a matsayin dan'uwarsa.

"Dan Allah yanaso su barta a hannunsa.

"Kanwar mmn Zahra tace ba naki taka bane wlh ina gujewa yarinyar ga shiga wani haline.

"Sbd Hajjo ba imanine da'ita ba.

"Tun ubanta nan ma ya aka kare banle bayanan.

"Shiru malam Habu yai sbd yasan halin Hajjo sarai ba imanine da'ita ba.

"Zata iya jefa Zahra cikin kowani halin.

"Amma kuma idan har yabari suka tafi da'ita bazata samu wani ilimin kirkiba.

"Sbd ba zaune suke gu daya ba.

"Dayan matar dake gefene tace malam Habu kana jina kuwa?

"Malam Habu yace ina jinki.

"Ni dai dan Allah kubarmi Zahra a hannuna, in Allah ya yarda babu abinda zai sameta.

"Kuma nayi maku alkawarin lokaci lokaci zan rinka kawo Zahra kuna gaisawa.

"Jin haka kanwar mmn Zahra kuka tasa tana fadin Allah ya jikanki zainaba, Allah yasa kin huta.

"Itama zahra kuka takai sosae.

"Maryama dake gefenta sai faman lailashinta takeyi.

"Bayan la'asar suka tafi gida.

"Zahra da maryama sukai masu rakiya har bakin rafi.

"Kudi masu yawa suka bawa Zahra snn sukai sallama suka tafi.

"Zahra kuka tai sosae, suma haka.

"Maryama ne ta riko mata hannu suka koma gida.





Mmn uswan ce
[7/17, 10:43] Washa: 💎💦💎
💝


GARKUWATA
(RELIANCE)


FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W.💝


MMN USWAN


Didecated to sweet Sis mardiya ka'oje


2


"Bayan addu'ar bakwai, Akaxo rabon g'ado.

"Ga malam Habu da kanwar mmn Zahra da mai gari da ita kanta Zahra sai Hajjo.

"Limami mai rabo g'adon saida ya fara da addu'a snn yace a fito da abinda mamaci ya bari.

"A lokacin ne Hajjo tace tana da mgn.

"Duk jama'ar dake gun sukace bissmillah.

"Hajjo tasa kuka tana f'adin dama tun lokacin da Haruna ke raye yasan da mgnr,Har cewa yai xai sanar dakai amma...

"Da sauri malam Habu yace wahhh????? niii??

"Hajjo tace eh.

"Malam Habu yace ina jinki.

"Hajjo taci gaba da cewa lokacin da zai kara gini d'akunan ga harda kudina a ciki...

"Da sauri malam Habu yace karya aradun Allah karya kike.

"Babu wani kudin ki a ciki.

"Kuka Hajjo taci gaba dayi, tana cewa kungani ko.

"Dama nasan xa'ai haka sbd lokacin na hanashi kudin yacemi babu damuwa xai sanar dakai.

"Malam Habu yace yasin karya ne.

"Hajjo na h'ada ido da mai gari suka kashewa juna ido.

"A lokacin ne mai gari yace tunda kaga hakan da gaske ne.

"Malam Habu yace karyane wlh.

"Saida malam yai gwaran murya snn yace to mudai yanxu bamuda abinda da xamuce a cikin wannan al'amari sbd babu Haruna inda yana rayene komai xaixo da sauki.

"Kanwar mmn Zahra tace gaskiya ne.

"Snn yaci gaba da cewa shidai a rayuwa duk abinda xakai kasa tsoron Allah ya ciki.

"Duk abinda xaka aikata yazama ka shirya ta cikin turban gaskiya.

"Tunda haka tace kai malam Habu me kagani?

"Malam Habu yace kwaran kwatsan aradun Allah karya takeyi.

"Sbd tunda nake da d'an uwana babu abinda yake boyemi,duk abinda zai aikata sai munyi shawara a tsakanimu.

"Kuma har Allah ya dauki ransa be taba sanar d'ani akwai wata mgnr kudi daya amsa a gunki ba.

"Hajjo tace to tunda haka kace babu damuwa, Ni dama gani nai yanada kyau a saukewa mamaci nawin dake kansa.

"Amma tunda haka kace babu damuwa na hakura.

"Ta karisa mgnr ne da mikewa xata bar gun....

"Da sauri malam yace aa Hajjo baxa'ai haka b, dawo ki zauna.

"Hajjo tace aa malam na hakura kawai.

"Mai gari yace kedai dawo akace ko.

"Snn ta dawo ta xauna.

"Malam yace kai malam Habu inaso na roki wani alfarma a gunka.

"Malam Habu yace ina sauraranka.

"Sai malam yaci gaba da cewa dan Allah dan annabi inaso hakuri abata hakkin ta tunda bata yafeba.

"Shifa bashi da kake gani komai kankantarsa yana hana kwanciyar kabari.

"Koda dukka tace natane gara a bata a huta??????

"Malam Habu da sauri yace minkace?????

"Malam yasake memeta masa.

"Da sauri yace wlh Allah kwaran kwatsan bata i'sa ba, saidai bayan raina.

"Gani hakan malam yace dakata bafa cewa nai abata dukka ba.

"Malam Habu da yaga hausan ta gagareshi juyawa yai harshe fullaci.

"Inda yake shiga ba nan yake fita ba.

"Dukkansu shiru sukai har saida ya numfasa snn malam tace haba malam Habu da iliminka da wayewarka shine kake haka.

"A wata tunanin koda duk dukiyar marigayine Hajjo tace nata xaka bata sbd soyayyyar dake tsakaniku.

"Amma har katsaya kaya gardama da'ita.

"Me akai akai abin duniya?

"Kada fa kamance wanda ya tare yanajin so haka ya tafi ya barshi banle ita da take tunani xataci banxa.

"Wlh malam Habu ina me tabbatar maka dukan wanda yaci dukiyar maraya baxai kare da duniya lpy ba.

"Tunda tace haka abata,kada ka damu Allah xan bata wanda yafi haka.

"Dukkan mu nan munayine babu wanda yasan abinda Allah zaiyi gobe.

"Babu wanda yasan me gobe Zahra zata xama.

"Fatanmu da'ita Allah ya albarkaci rayuwarta.

"Ya kuma jikan iyayenta.

"Malam Habu yace ameen.

"Itako Hajjo ko a jikinta.

"Fatan ta kawai shine taga ta mallaki gidan Haruna da kuma gonarsa.

"Inba h'aka tai ba bata da wani hanya tunda ba haihuwane a tsakaninsu ba.

"malam yace to Hajjo ko zamu iya sani iya adadin kudin dake tsakaniku?

"Shiru Hajjo tai san tace gaskiya kudin sunada yawa sbd kiwo nane duk na haka na siyar na bashi kudin.

"Karaf maigari yace fadi konawane kudin, idan ma kina tunani gidan bazaikai yawan kudinki bane ai ga gona sai a sa akasuwa hakada duk a biyaki.

"Hajjo tace gaskiya idan ban mance ba xasukai three hundreds thousand....

"Da sauri malam Habu yace kai Hajjo kiji tsoron Allah Hajjo karfa ki mance koda kikazo aure gidan nan ko katifa babu dagake sai mashinfidin kaba kilazo dashi.

"Cikin tsiwa Hajjo tace saime sarkin tone tone.

"Malam yace aa malam Habu kyaleta kaway.

"Hajjo tace wlh malam sababbin gini can da suke gefe da kudina yayisu.

"Malam Habu yace to yanxu inaso ki masu kudi sai a biyaki.

"Malam yace kai yanxu malam Habu kanada kudin da xaka biyata a take ne?

"Malam Habu yace ban dashi amma tunda akwai gonar gadonta koshi sai a siyar a biya mata.

"Malam yace aa baxa ai haka ba.

"Ina ma laifin kace a sa masu katanga tsakini.

"Shiru malam Habu yai betanka ba.

"Malam da maigari suka mike xuwa cikin gidan.

"Duk dakunan saida suka shiga suka duba snn malam yace tunda abu ya xama haka ita Hajjo ta dauki dakunan guda biyu a madadun kudinta.

"Shikuma filin kasan an barmata a matsayin timilin takabarta.

"Shikuma abinda yakama daga filin tsakar gida har ixuwa bayan gida da dakin hade da gona na marigayi Haruna yaxama na Zahra.

"Megari yace shikenan ma haka yafi.

"Daga nan kowa ya watse,bayan fitan mutanine Hajjo ta shiga kayan d'akin ta kwasowa Zahra kaya ta watsa mata a kasa hade da cewa kwashe ki medasu dakin ki.

"Tunda anriga da anraba kowa yasan ma zauninsa.

"Duk kayan gidan nan da kike gani nawane hallak mallak ban yarda ki tabamin suba koda wasane.

"Abinci kuma bakida da kwanu a gidan nan. Sbd tun ubanki na raye nake ciyar da kaina na ciyar dashi dake.

"Duk da haka be dubi irin wahalar da nakeyi ba, babu yadda banyi dashi akan na dora miki tallaba amma ya hana.

"Sbd haka sai kisan abinyi duk yadda kikaga xakiyi sai kije can kiyi.

"Idan ma karuwanci xakiyi oho ke kika sani.

"Gida dai yadda yaxama mallakina idan naga kafarki anan bakin kofar dakina wlh icce xansa na karya mikishi.

"Shigiyar yarinya me taurin kan tsiya irin na ubanta.

"Nida kene wlh.

"Ita dai Zahra babu abinda takeyi sai kuka.

"Dakawa tai ta tsintsice kayan ta hade da wata yar'figigiyar tabarman kaba takai dakin da aka ce shine tana.

"Daki ne yar' madaidaiciya wanda akai masa rufi da asabari hade da gumagumai itatuwa.

"Saida ta shinfida tabarman kabanta snn ta zuwa kayan a ciki.

"Zama tai gefe tana ninkesu daya bayan daya tana sasu cikin dankwalin ta.

"Tayi tana hamma sbd yunwa, da haka har takare.

"Tana karewa gefe ta kwanta ta fada duniyar tunani kala kala.

"Kwalla ne kawai ke gangaro mata da gefe ido.

"A zuciyarta tana fadin ohhh! Ni Zahra yadda Allah yaso ganina kenan.

"Nakoma babu uwa babu uba ohhh!ni Zahra.

"A lokacin ne Zahra ta fasa da wani irin kuka me tsuma zuciya.

"Uwa uba ga uban yunwar da takeji.

"Shiru Zahra tai tana tunani ta inane xata fara?

"Idan tace gidan Bb Habu shima fama da kansa yakeyi.

"Yau acine gobe sai ta Allah.

"In kuma maryama ne ita wannan bata da matsala amma kullin kenan xata rinka ci a gidansu?

"Gaskiya hakan bedace ba, koba komai yau da gobe sai Allah.

"Shiru tai tana kwalla,cann da tatuno da kudin da kannin mmn suka bata da sauri ta mike ta dauko xanin da ta daure a ciki.

"Tana kwance bakin xani ta ga kudin da sauri ta dauka tai waje.

"Bakin tasha taje ta siyo abinci rogone da dakankiyar kuli kuli.

"Gefe guda ta samu ta xauna taci, saida ta cinye tsaf snn ta juya xuwa gida.

"Tana cikin tafiyar ne suka hadu da maryama kawarta tana dawowa daga makaranta.

"Gefe guda suka samu suka tsaya sbd ba hanyar gidansu dayane ba.

"Maryama tace Zahra meyasa bakixo school ba?
[7/17, 10:43] Washa: 💎💦💎
💝


GARKUWATA
(RELIANCE)


FASAHA ONLINE WRITES W.O.W.💝


MMN USWAN


DIDECATED TO SWEET SIS MARDIYA KA'OJE


3

"Shiru Zahra tai.

"Maryama tasake cewa Zahra dakefa nakeyi.

"Nisawa kawai Zahra tai.

"Maryama tace Zahra.

"Zahra tace na'am.

"Sai Maryama tace Zahra hakuri zakiyi da yanayin da kika tsinci kanki a ciki.

"Ita rayuwa ta gaji haka, Yau gareka ne gobe ga wani.

"Amma idan kika dauki abinda sauki haka rayuwa zata maki ciki sauki.

"Shifa rashin iyayen ba kankine fa rauba haka kuma ba xaixama karauba.

"Al'uman annabi dubu nawane yanxu suke rayuwa ba tare da iyayensu ba?

"Mafi yawancin yara yanxu masu rayuwa da iyayensu kadan ne.

"Ita dai Zahra babu abinda takeyi sai kuka.

"Maryama tace haba Zahra ko abinda ya sameni be'isheki wa'axiba Zahra?

"In baki mance ba Zahra watana biyu da aure fa mijina ya mutu.

"Daga saina dawo sai gawa.

"Ki tunafa irin soyayyar da shakuwa dake tsakanimu da Hafiz.

"Lokacin da mukai aure da Hafiz duk a tunanina na samu abokin rayuwata na har abada ashe ba haka abin yakeba.

"Zahra kinfi kowa sani yadda nakeso Hafiz amma dole na hakura.

"Idan ma nace baxan hakura yaya xanyi.

"Sbd haka dan Allah Zahra kiyi hakura kinji Zahra Allah ya jikan Baffa fa inna.

"Zahra tace uhmm Maryama kenan.

"Matyama tace menene acikin rayuwar?

"Zahara tace Maryama gara kefa, Tunda kinada iyaye a raye.

"Maryama tace hakane Zahra amma rashin miji akwai zafi,koda auran kiyayya kukai banle na soyayya.

"Zhara ba lailai bane kisan irin zafin da nakeji akan rashin Hafiz.

"Wlh Zahra Hafiz namiji, duk macen da tasamu Hafiz a matsayin miji babu abinda ya rage mata saidai taiwa ubangiji godiya hade da fatan xaman lpy.

"Zahra duk mace da tasan dadin dakinta koda na kwana daya ne,Ba xataso ta dawo gida da zama ba.

"Amma tunda haka Allah ya kaddaromi babu yadda xanyi.

"Tun ina kuka zahra har nazo na hakura hakan ma yasa na koma makaranta sbd yage tunani.

"Zahra ta sake cewa Maryama kenan kefa duk iyayenki suna raye daga uwa har uba, Ni kuma fa babu ko daya gashi kenan Inna Hajjo tace tunda aka raba gado tace saidai na rinka ciyar dakai na.

"Sbd Allah Maryama wa nake dashi da xai rinka ciyar dani?

"In ba karuwanci takeso nayi ba.

"Idan ma tana tunani Baffa Habu ne Baffa Habu shima ta kansa yake, ba kullin suke sanwa ba.

"Shiru Maryama tai tana kallon Zahra har ta kare.

"Snn maryama tace idan sbd abinci ne kike damuwa Zahra nayi maki alkairin duk sanda mukai abinci xan rika kawo maki gida...

"Da sauri Zahra tace aa kada ki kawomin gida.

"Maryama tace sbd mee Zahra?

"Himmm kawai Zahra tace.

"Sai Maryama tace sbd Hajjo ko?

"To kada kiji komai Zahra idan mun tashi tafiya makaranta da safe saiki fara biyowa ta gidan mu kici kina gama ci sai mutafi skull kiji ko.

"Murmushi kawai Zahra tai.

"Snn maryama tace ya batun xuwa makarantarki gaskiya ya kamata kifara xuwa skull yanxu Zahra.

"Zahra tace to naji Maryama amma....

"Maryama tace amma me?

"Zahra koda kince xaki zauna a gida gani nai babu wani aikin da xakiyi a gidan kuma koda kin zauna a gidan bazaki karu da komai ba.

"Amma idan kikaje skull koba komai xai debe miki kewa ko Zahra.

"Zahra tace to naji maryama Allah ya kaimu goben.

"Maryama tace ameen.

"Snn Zahra tace yauwa Maryama kin fadiwa uncle Haidayr rusuwar Baffa na kuwa?

"Maryama tace Allah Zahra dan Allah kiyi hakuri wlh mancewa nai.

"Da sauri Zahra tace na shiga uku Maryama tunda hakane to gobe babu inda xani...


"Da sauri Maryama tace sbd me?

Zahra tace Maryama kinfi kowa sani uncle Haidayr mugune.

"Murmushi Maryama tai snn tace Zahra karki damu idan Allah ya kaimu gobe tun kafin a fara shiga class muje mu sameshi muy masa bayani.

"Da sauri Zahra tace nidai babu inda zani sbd tsoron sa nakeji.

"Maryama tace karki damu ni xanje nai masa bayani da kaina.

"Zahra tace to shikenan Allah ya kaimu.

"Nan suka fara tafiya suna tafe suna hira har suka kai inda kowa zaiyi hanyar gidansu.


***** ******* *****

ASALIN MARYAMA
"Maryama year"cikin garin d'an babbane Sunan mahaifinta Salele,Salele haifenfen cikin garin d'an babba ne yanada sufan asiri daidai gwargwado.

"Yanada mata daya da yara biyu Maryama da kaninta me suna audu.

"Maryama itace babba sai audu dake binta.

"Maryama tana da saurayi me suna Hafiz, Hafiz da Maryama suna matukar son juna.

"Hafiz yarone me kwaxo da xuciyar niman na kanshi.

"Tunda Hafiz ya tashi yaga bashi da uban, Allah yai masa rasuwa shiyasa ya dage wajan niman na kansa.

"Lokacin damina biya yakeyi ai masa noma shikuma ya shigon provision d'insa.

"Dama itace asalin business d'insa tun yana yaro, lokacin akan table har Allah yasa yabude shago.

"Tun Maryama batasan kanta ba Hafiz yake matukar sonta,har tai girma koda Hafiz ya sanarwa Maryama abinda ke ransa amsarsa tai hannu bibbiyu.

"Abu kamar da wasa soyayya me karfi ya shiga tsakaninsu.

"Koda skull aka tura Maryama saiya biya shigonsa.

"Gani hakane yasa bbn Maryama yace idan da gaske Hafiz keyi to yafito.

"Shima Hafiz tunda yaji haka beyi kasa a gwiwa ba ya tura iyayensa gidan su Maryama.

"A lokacin tana J.S.S.3 ne tana gama junior waec akai mata aure.

"Suna gama junior waec akai wa Maryam aure,Zahra'u ce babban kawar amarya.

"Itako Zahra daya ke Baffa yanaso tai karatu shiyasa ya hanata tsayawa da kowa.

"Kuma ya hanata bin kawaye inba maryama ba, itama tunda tai aure Baffa yacewa Zahra ta ta daina zuwa gidan ta.

"Babu yadda Hajjo batai ba akan ta rinka dorawa Zahra talla amma Baffa yahana.

"A cewarsa koda mutuwa yai aka dorawa Zahra talla beyafe ba.

"Maryama soyayya suke xuwa sosae ita da Hafiz abokansa har tsiya suke masa sbd rashin fitar da bayani.

"Kullin sunan a daki like da juya.

"Innar Hafiz tai fada har tagaji.

"Suna da tawa biyu da aure Maryama ta samu ciki, Tun daga lokacin wani sabon salon soyayya suka bude Hafiz ya hana Maryama aikin komai a gidan.

"Koda tuwo ne zata tuka sai Hafiz yace shine xaiyi.

"Da kar take shawo kansa yabari ta tuwa, yana xuba mata gari tana tukawa har sukace.

"Tun innarsa najin haushi harta saki jiki ta saba.

"Sbd koda fada tai masa in har akan Maryama ne kuka yake yimata, ita kuma a rayuwa bataso taga Hafiz yashiga halin damuwa.

"Shiyasa duk abinda xasuyi ido take xuba masu, Saidai idan taga xasuyi ba daidai ba sai ta kwaba masu.

"Ana gobe Hafiz xai yasu wasa sukai da Maryama harda guje guje Maryama na gudu Hafiz na biye da'ita daga karke bayan inna taje ta boye.

"Haka sukai ta juya inna kamar wata kukansu.

"Da inna taji haushi sai ta hausu da fada, Tana fada sbd Allah wani irin wasane kukeyi haka?

"Baka ko tsoron abinda ke cikinta yaxo ya samu matsala?

"Kuma idan banda rashin kunya irin naku na yaran yau akan idona kuke irin wannan wasa.

"Hafiz yace innata kenan to menene wataran basai kabari ba?

"Duk wannan abinda nakeyi wataranfa sai kabari wayarsa da kanki xakiso ganina amma lokacin nai maki nisa...

"Da sauri inna tace haba Hafiz wani irin mgn kakeyi haka?

"Hafiz yace wlh kuwa inna, gaske nakeyi.

"Jikin inna yai sanyi sai tace to Hafiz a kullin addu'a ta dakai shine na rigaka mutuwa bana fatan ka rigani mutuwa yadda bbnka ya mutu ya barni dakai haka nima nakeso na mutu na barka cikin iyalanka...

"Dariya Hafiz yai snn yace inna kenan.

"Ya garisa mgnr ne hade da mikewa ya koma dakin, Itama Maryama binsa tai dakin.

"Washe gari da safe bayan sun karya ne Hafiz yake sanarwa Maryama xai tafi birni siyayya kayan provision dinsa sbd kayan shigonsa sunyi kasa.

"Maryama tace to Hafiz babu damuwa Allah ya kaimin kai lpy.

"Hafiz yace amin.

"Fita Hafiz yai yaje ya sallami inna, Maryama na biye dashi.

"Bayan sun gama sallama ne har Hafiz ya fita sai yadawo ya rungumi Maryama a gaban inna.

"Inna na gani haka da sauri ta dauke kai tai kamar bata gansu ba.

"Maryama tace haba Hafiz meye kakeyi haka kamar baxaka dawo ba.

"Hafiz na rungume da'ita murmushi kawai yai snn yace Maryama kenan in Allah ya yarda yau xanbaki mmki.

"Maryama tace mmki kuma?

"Wani irin mmki ne xaka bani?

"Hafiz yace kodai kibari kawai xaki gani.

"Har Hafiz ya sake fita sai yadawo yace Maryama.

"Tace na'am.
"Hafiz yace dan Allah inaso kimin addu'a kinsan Allah gaggawar amsar addu'ar masoyi.

"Murmushi kawai Maryama tai snn tace Allah ya kaika lpy kuma ya dawomi dakai lpy.

"Hafiz yace amin matata.

"Hannu ya daga yana yimata bye bye har yafice.

"Duk abinda sukeyi inna na jinsu juyawar da xatai ne su hada ido Allah bebata iko ba.

"Hafiz befi minti 30 da fitaba su inna da Maryama dake zaune a tsakar gida suna aiki suka jiyo sallama.

"Har

Please Login or Register in order to submit comment