Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

acewarsa zuwa wani sati yakeso ayi bikin.
"Duk da uncle Haidayr bashi da wasu kudi a hansa amma benuna damuwarsa ba"Cewa kawai yai babu damuwa bba Allah yarufa asiri.

"Duk sunace amin"Daga nan bba Habu ya zaiyana masu yadda sukai da maigari harda kukansa.

"Murmushi kawun uncle Haidayr yai snn yace kyaleshi kawai idan yasan wata ai besan wata ba"da sauri kamar yya malam Ibram?

"malam Ibram yace abinda za'ayi shine tashi xakai yanxu kaje gun maigari kace masa ka'amince da auren sushirya mgnr biki wani sati kamar yadda ya hurta.

Bayan kabar gun maigari sae katafi gidan liman shima kai masa bayani duk abinda ake ciki kada kaboye masa komai"In Allah ya yarda nasan babu wanda zai fadi mawa" mukuma zamuje mushirya idan Allah ya kaimu ranar duk xamu harlara agun daurin auren daganan duk yadda za'ayi sae ayi ko ya kagani?

"Bba Habu yace hakan yayi amma masifar maigari da d'an sa garzali nake tsoro.

"Ibram yace masifar banxa'duk masifar da zaiyi idan anriga an daura ta banxace.

"Malam Habu yace hakane to babu damuwa Allah yai mana jagora.

"Sukace amin.

"Ibram yace to ya mgnr sadaki?

"Nan suka daedata mgnr sadaki amma bb Habu cewa yai bazai amsaba sbd bayaso kowa ya sani uncle Haidayr yabar kudin a gunsa idan yaso bayan biki sae yasiye mata da kansa..

"Uncle Haidayr yace babu damuwa"nan sukai sallama hade da godiya suka mike malam Habu yai gun maigari sukuma su Haidayr sukai gida.

"Itako Zahra tunda uncle Haidayr yatafi mgnr kenan sukeyi shida Zahra"kuka sosae Zahra keyi Maryama tai lailashi har tagaji.

"Da Maryama taga kukan yaki karewa sae tace Zahra wai kukan menene kikeyi haka? Uncle Haidayr dinne bakiso ko yaya?

"Nidae a iya sanina bantaba kamashi da wani laifiba mutum ne mai natsawa da rikon addini gashi kuma son kowa kin wanda yarasa wlh Zahra idan kika bari har ya subuce maki da wahala kisake samun kamarsa.

Shiru Zahra tai har saeda Maryama takare mgn snn Zahra tace wlh Maryama tsoronsa nakeji uncle Haidayr mugune babu wanda besansaba da mugunta.

"Murmushi Maryama tai hade da cewa ke wlh bazan maki muguntarba idan kinga mai lallashin matarsa to shine.

"Himm kawai Zahra tace"daga nan sukaci gaba da tattanawa.

"Malam Habu da fara'arsa ya'isa gun maigari bayan sun gaisa maigari yace ina fatan kazomin da mgnr sa bikin ne ko?

"Malam Habu yace kwarai da gaske ranka ya dade yadda kace haka za'ai.

"Bakin maigari har kunni yace to to to alhamdllh masha Allah" yanxu kamar yaushe kenan kake gani yadace?

"Malam Habu yace nidae inda a sonane zuwa wani sati nakeso.

"Cikin murnarsa maigari yace to babu damuwa Allah yasa mukai.

"Fadawar dake gun duk sukace amin.

"Daganan malam Habu ya mike xuwa gidan liman shima yai masa bayani babu abinda ya boye masa.

"Dayake shima limamin mai fahimtane cewa yai babu damuwa Allah yarufa asiri.

"Malam Habu yace amin snn yakoma gida"yaiwa matarsa bayani komai itama tayi murna sosae saedae kuma tsoron abinda xaibiyo baya da maigari"daga nan tace yaje riga gun dangin mmn Zahra ya sanar dasu mgnr baki.

Washe gari malam Habu yaje riga gun dangin mmn Zahra sanar dasu mgnr bikin Zahra"itako Abu shiga gun Hajjo tai ta sanar da'ita .

"Murna sosae Hajjo tai"ba murnar auren Zahra takeyi ba murnarta daya ne sbd koba komai xataji dadin cin duniyarta da tsinke ita kwartonta maigari.

"Tun daga lokacin aka shiga wasan buya tsakani Zahra da uncle Haidayr kwata2 tadaena fita ko'ina banle su hadu koda garzali ne yaxo bata fita haka yake kare tsayuwarsa idan yagaji yakoma gida.

"Duk yadda uncle Haidayr yaso mgn da Zahra Zahra taki yarda suhadu saedae idan mgnr ta damesa yafadiwa Maryama ita kuma taxo ta fadiwa Zahra.

"Tun ana sauran kwana biyu biki iyayaen Garzali suka kawo kaya gidan malam Habu"malam Habu kin amsa yai a cewarsa sae ranar daura aure.

"Ranar juma'a bayan an sauko daga masallaci ne daurin aure"gashi kowa sun hallara daga dangin garzali har dangin uncle Haidayr abokaninsa ko ba karamin shirine sukai masa ba harda anko sukayi.

"Ba karamin mmkine garzali yaiba gani uncle Haidayr da abokansa kuma duk sunsha kwanciya a gun daura auransa.

"Liman yana isowa aka nimo wakilin ango Ibram yace gani"daya daga cikin fadawar maigari shima yace gani.

"Uncle Haidayr ko yasha kyau kamar bashiba abinka da wayayye.

"Nan dae daurin aure ya kankama bude bakin liman sae sukaji yace an daura auren fatimatu zahra'u da aliyu Haidayr.

"A birkice garzali ya mike hade da cewa mekace?

"Limami yasake memetawa har sau uku"a take garzali ya yanke jiki ya fadi sumanme.

"Suko abokan uncle Haidayr dagashi sama sukai suna murna.
[7/17, 10:43] Washa: πŸ’ŽπŸ’¦πŸ’Ž
πŸ’



GARKUWATA
(RELIANCE)



FASAHA ONLINE WRITES F.O.WπŸ’



πŸ’ŽMMN USWANπŸ’Ž


DIDECATED TO SWEET SIS MARDIYA KA'OJE



11



"Abokan Garzali suna gani abokinsu ya fadi wanwar sumeme"Suka hau rarumo limanin zasu haushi da duka.


"Liman na gani haka sabewa yai yabargu batare da sungine ba'"ko kafin su ankara yariga yabar gun.


"Suma malam Habu a guje yabar gun"Abokan uncle Haidayr da suka rage suma kama abokinsu sukai xuwa gidansu.

"Daya daga cikin fadawar maigari a guje yaje ya sanarwa maigari lokacin maroka da mabusa sunyi dandaxo a kofar gidan maigari sae faman kirari suke masa"Shiko sae faman barin naira yakeyi.

"Gani bafajensa a guje yasa maigari dakatar da likin da yakeyi"Dan jin abinda bafajensa xai fadi, Cikin rawar jiki bafaje yace ranka ya dade..

"Kasa karisawa yai ya tsaya yana hakki.

"Cikin kosawa maigari yace menene Maude?

"Maude yace ranka ya dade ansamu matsala.

"Jin haka duk mutanin dake gun suka saki gangar da sukeyi suma sunaso suji abinda ya faru.

"Maude yasake cewa ansamu matsala..

"Maigari yace matsalar me aka samu?Badae an daura auren ba?

"Maude yace kwarai aure fa ya dauru sae dae...

"Jin ance an daura aure masu busa suka dora daga inda suka tsaya harda masu algaita suna fadin garzali yaxama ango.

"Maude yace aure fa ya dauru amma bada garzali ba...

"Cikin gigita daya daga cikin marokan yace mekace Maude?

"Maude yace aure ya dauru amma bada yarima garzali ba"Da Aley D'an nan yahin tunga.

"Duk jama'ar dake gun sukace wani Aley badae d'an wajan Ibram ba? Maude yace shifa, Dayan yasake cewa Aley malamin makaranta boko?

"Maude yace Kashh shifa nake nufi.

"A take maigari ya birkice yana fadi karyane wlh shi d'an gidan uban wayene da har zasu hada baki sumin haka to wlh dagashi har malam Habu sae sunci ubansu.

"Kama harya yai zuwa gidan malam Habu kafa babu ko takalmi.

"Daya daga cikin maroka sukace yoookuwa jama'a auren yarima garzali d'an maigari dae be dauruba ba...

"Kafin ya karisa tuni maigari ya kaimasa nashi a baki"Daga nan ya hausu da duka, fadawar dake gun suka rike maigari hade da bashi hakuri.

"Shiko maigari sae faman cewa yake nine za'a kawowa iskanci? To wlh basu isa ba"Saena nuna masu kuskurensu.

"Gani abinda maigari keyi yasa maroka watsawa kowa ya kami gabansa.

"Suko mata dake cikin gida kowa sae fadin albarkacin bakinsa yake fadi"Masu Allah yakara suna cewa masu Allah ya kyauta suna cewa, Suna cikin hakan kenan saega abokan garzali sun kinkinmo kamar gawa Haule na gani yadda aka shigo mata da yaro kamar gawa ihu tasa hade da fashewa da kuka.

"Shinfidashi akai a tsakar gida masu hayaki sunayi masu addu'a ma duk sunayi da haka dae har suka samu ya farfado"Yana farfadowa babu abinda yake ambata sae sunan Zahra a birkice ya mike xai fita a guje, da sauri abokansa suka rukoshi dannesa sukai mmnsa ne taxo kansa tana bashi mgn harya numfasa.

"Itako Zahra gidan malam Habu ta koma da zama tun ana sauran kwana biyu biki"Maryama ko tayi rawar gani d'an ta cicciki yabo duk wasu kayan aiki na mata wanda tasan Zahra xata bukata ta siye mata wasu kuma a cikin kayanta ta cire mata.

"Kudin da uncle Haidayr yabawa Zahra koda xata bukaci wani abu hade da tirmin xani uku da sune Maryama ta hada taiwa Zahra dinkin fitar biki,Sauran kudin kuma ta rike mata akan bayan biki tabata.

"Yar'uwan mmn Zahra suma sunyi mata gara iya karfinsu masara kwanu ashirin dawama haka sae zanin gado daya da labulaiya guda biyu da ledar kasa yadi biyar"Hade dasu daddawa barkono manshanu magi star leda daya da gishiri karamin ledar dankwate leda uku.

"Shiko malam Habu tunda ba wani kudine dashi ba babu abinda yasiye mata"Saedae nawin abincin akaci da bikin shine ya dauka hakan ma yasashi cewa bayan la'asar akai amarya gidan mijinta daganan kowa yatafi gidansa.

"Itako Hajjo cewa tai sisinta baxaiyi ciwon kaiba"Tunda ba moranta takeyi ba.

"Gidan su uncle Haidayr biki gadan gadan sukeyi duk da ba wani kudine dasu ba amma sunyi kokari kota gun abincin da akaci.

"Ana idar da la'asar akaiwa amarya wankan zuwa gidan miji"Zahra tai kuka har taji ba dadi"Ana gama shiryata kanni mmnta da matar malam Habu suka kaita dakin malam Habu har kasa ta duka kanta lulube da mayafi malam Habu yace to zahra'u yanxu dae kintashi daga sahun yara kinkoma ta manya dan Allah zara'u kiyiwa mijinkin biyayya ki rike maraicinki koda wasa banaso naji ance yakawo karanki.

"Kan Zahra na kasa babu abinda takeyi sae kuka"Gani kukan da takeyi yasa Abu da kanni mmnta kuka.

"Nasiha sosae kawu yai mata snn yace sutashi su tafi.

"Maryama na rike da hannu Zahra suna tafe"Da yake ba nisane dasu ba, Hade da dangin uncle Haidayr'ya xuwa daukar amarya.

"Nan danan suka isa gudarsu yasa akasan sun iso"Bayan sun shiga ciki,Har Zahra tasa kafa zata shiga daki daya daga cikin tsofanfin da suka rakota tace saedae Zahra tashiga da kafar dama"Sbd niman sa'a.

"Dangin talatuwa da mauransu suka taresu masu jin hausa sunayi masu jin fullaci suma sunayi"Lafiyayyar tuwon shinkafa da man shanu aka kawo masu wanda yasha gishiri hade da kaji.

"Mata na cikin gida malam Habu da kansa yaxo yasa aka kira masa uncle Haidayr, uncle Haidayr yana fita ya duka har kasa suka gaisa"Bayan
suna gaisa ne malam Habu yace sukebe yanaso ganisa.

"Bayan sun kebene malam Habu yace Aliyu dama ba wata mgn bane yasa na kiraka, Akan Zahra ne"Dan Allah dan annabi Aliyu ga Zahra ne amana nabaka ita dan Allah koda bayan raina ne karikemin ita amana.

"Kafi kowa sani Zahra bata da uwa batada uban yanxu kaene kadan karage mata kaene a duniya dan Allah aliyu inaso kaxamewa Zahra garkuwa a rayuwa.

"Aliyu na duke a kasa yace in Allah ya yarda bba nima dan Allah katayani da addu'a Allah yabani ikon riketa amana"In Allah ya yarda bazaka sameni da rashan kyautatawa Zahra ba,ko tun dama na dauki Zahra tabbakar kanwatane banle yanxu da taxama matata.

"Malam Habu yace to aliyu Allah yabada xaman lpy.

"uncle Haidayr yace amin nagode"Snn sukai sallama, Malam Habu yakoma gida"Shima uncle Haidayr komawa yai gun abokansa.

"Gani dare yayi duk masu kawo akoma gidansu"Ranage daga ita sae Maryama sae da uncle Haidayr ya tabbata kowa ya watse snn ya kawo masu da gasashiyar nama hade da shayi"Shida wani abokinsa suka shigo lokacin Zahra na zaune can jikin bango ta rabe, Ita kuma Maryama zaune take akan katifa suna hira" jin sallar su uncle Haidayr ne yasa Zahra dauke wuta kamar bata dakin.

"Suna shigowa bakin katifa uncle Haidayr yasamu ya zauna kusa da Maryama yai kamar bega Zahra ba dake rafe jikin bango.

"Maryama ne tace uncle ango kenan"Murmushi uncle Haidayr yai hade da cewa Maryama ya akayi?

"Ita murmushi tai masa.

"Abokin uncle Haidayr ne yacewa Maryama ina amaryar tamu take?

"Jin haka yasa Zahra kara mannewa a bango"Daga kai uncle Haidayr yai yana kallanta"Gani kallan da yake matane yasata rufe fuska da mayafinta.

"Uncle Haidayr yana gani haka mikewa yai ya nufi inda take"Batare da ta ankara ba ji kawai tai anroko mata hannu.

"Maryama da abokinsa suna gani haka mikewa sukai suka fita suka basu gu"Gani sufita ne yasa uncle Haidayr jawo Zahra jikinsa hade da cewa amarya ta kenan, Zo ki xauna mana kada kafarki yai maki xafi.

"Jawota yai zuwa katifa"Gani yanayi kamar zai rungumeta yasa Zahra kwance jikinta da sauri taja da baya.

"Murmushi kawai yai hade da cewa saeda safe" shiru Zahra tai kanta nakasa.

"Yana fita kamo hannu abokinsa suka fita"Bayan sun fitane Maryama ta shigo'Suna hada ido da Zahra ta kwashe mata da dariya hade da cewa amaryan uncle Haidayr kenan.

"Daure fuska Zahra tai" Maryama tace menene abin daure fuska tun abai komai ba?

"Zahra tace kamar yaya Maryama?

"Maryama tace himm Zahra har kinsa ina hango wannan lokacin" Wlh har nafara tausaya maki.

"Cikin gigita Zahra tace Maryama bangane ba? Dan Allah kinmin bayani.

"Murmushi Maryama tai snn tace wlh Zahra lokacin da nai aure ranar da marigaji zaifara kwanciya dani har kusan suma nayi sbd axaba"Gashi kuma yadda nake gani uncle baxaiyi sauki ba.

"Zahra najin haka ta fashe da kuka tana fadin nashiga uku Maryama yaya zanyi? Dariya Maryama tai snn tace ke dan Allah abinda xafi na lokaci dayane kawai"Idan kika daure bama zakiji zafinba.

"Ita dae Zahra bata dae na kuka ba"Gani haka yasa Maryama lailashin Zahra hade da cewa wasa nakeyi Zahra idan ma yanayi ba lailaine kisaniba"Duk da haka Zahra batabar kuka ba haka Maryama taci gaba da bata mgn har ta numfasa sukaci namar da uncle ya kawo masu"Snn suka kwanta.

"Washe gari daedae da ranar kasuwa uncle Haidayr shida Maryama suka tafi kasuwa yace Maryama ta xabawa kawarta katifa maikyau"Haka ta zaba mata snn yabiya, Ra gowar kudin kuma suka kara mata abubuwan da bata dasu.

"Bayan sun koma gida Maryama ne ta gwara mata dakin tsaf da yamma uncle Haidayr yai cefane Maryama tai masu girki ta zubawa kowa nasa na uncle Haidayr kuwa ciki kula akasa masa"Bayan ta gama tai wanke wanke snn tashirya xuwa gida"Uncle Haidayr ne da abokinsa suka raka Maryama har gida hade da yimata godiya.

"Da dare aka rako uncle Haidayr daki shida abokansa biyu Zahra najin sallamarsu da sauri ta dauki kyalenta ta rufe kanta" suna shiga a bakin katifa suka xauna'shima uncle Haidayr xama yai kusa da'ita saeda sukayi addu'a snn kowa ya jero nasa bayanan daga uncle Haidayr har Zahra shiru sukai suna sauraronsu har suka kare snn uncle Haidayr yace nagode, Daga nan sukai sallama suka fita hade da miko masa kunshin kaza a leda.

"Suna fita uncle Haidayr ya rufe kofa snn yaxo kusa da Zahra ya xauna yana cewa Zahra har kinyi bcc ne? Yadae tambayeta ne kawai amma yasan ba bcc takeyi ba.

"Kasa2 ta amsa hade da cewa aa" sae uncle Haidayr yace tashi kije kiyi alwala, da sauri tace nariga nai sallah fa" Uncle Haidayr yace ina sane da kinyi sallah.

"Mikewa tai taje tai alwala snn tadawo"Shima tafiya yai yaje yai alwala yana dawowa yajasu sallar nafila raka'a biyu, bayan sun idar ne ya dora hannu akanta yai masu addu'a.

"Saeda yagama addu'ar sa snn yace Zahra"Zahra tace na'am.

"Snn yace tukunan sallah guda nawane?" Sae tace rukunan sallah guda goma sha hudune Na 1 Tsayawa tare da iko 2 Kabbarar harma 3 Karatun Fatiha 4 Yin ruku'u 5 Dagowa daga ruku'u 6 Yin sujjada akan gabobi bakwai 7 Daidaituwa a cikinta 8 Zama tsakanin sallah, sujjada ta biyu 9 Natsuwa a cikin dukkan 10 Jarantawa rukunnai 11 Karatun tahiya ta karshe 12 Zama domin ta 13 Salati ga manxo (S.W.A.) 14 Sallama ta biyu.

"Tunda Zahra tafara kallanta kawai uncle Haidayr keyi har takare" snn ya ce da kyau kin San wajibantan kenan da sharudodi.

"Zahra tace eh.

"Uncle Haidayr yace ashe dae matar tawa malamace.

"Murmushi kawai Zahra tai.

"Kara watsawa yai kusa da'ita jelar kitson kanta da ya fito daga dankwali hannu uncle Haidayr yasa hade da cewa bari na gwara maki dankwali kiko?

"Da sauri Zahra taja da baya.

"Gani haka yasa ya tsaya a inda yake zaune" Snn yace ai kina period ko?

"Shiru Zahra tai sbd tambayar yai mata wani iri.

" uncle Haidayr yace kodae kinfi ganewa da al'ada ko?" Sae Zahra tace na'am".

"Kanta a kasa tace " eh, ina yi".

"Sae yace kwana nawa kikeyi kina yi?".

"Cikin jin kunya Zahra tace uku ko hudu.

"Idan kin yi kin gama yaya kikeyi?".

"Shiru tai kanta a kasa.

"Uncle yace kodae sallah kawai kikeyi?".

"Zahra tace aa.

"Inayin wanka.

"Sae yace wani irin wanka? Kodae na sabulune kikeyi?".

"Zahra tace aa.

"Snn yace ina sauraranki.

"Zahra tace "Da farko zan sami ruwa mai tsarki sai nayi tsarki sosae gaba da baya, snn sae na wanke daga kan cibiyata zuwa gwiwowina na kafa, tare da cewa 'NAWAITU GUSULUL AZHA".

"Sae uncle yace saunawa zakiyi wankan?".

"Tace sau uku.

"Uhm! Kawai yace" snn ta karisa masa, tana gamawa yace alhamdllh masha Allah naji dadi da kikasan wanga abubuwan"Amma meyasa naga baki xuwa makarantan islamiya?

"Zahra tace lokacin da baffana yananan ina xuwa amma da yamutu Hajjo ta hanani xuwa.

"Allah ya kyauta kawai yace"snn yace matso muci nama.

"Da sauri Zahra tace aa nakoshi.

"Uncle yace haba Zahra wanga nama nefa.

"Zahra tace eh nakoshine kawai.

"Uncle Haidayr yace to shikenan"Budewa yai yaci kadan snn ya dauki ledar ya ije a gefe, mikewa yai ya cire rigar sa.

"Gani tana zaune taki tashi kixo mutakwanta" ta sauri Zahra ta kwance hannunta tana komawa da baya, gani abinda takeyi ne yasa uncle Haidayr daukar mayafinta ya ninke mata ya dora akan rigarsa babu yadda uncle Haidayr beyiba amma Zahra taki yarda su kwanta da yaga tana niyar fita waje sae yace kixo mukwanta babu abinda xanyi maki.

"Tsareshi da ido tai tana kalansa"da uncle Haidayr yaga haka kara rufe kofar yai dakyau snn yaje ya hau katifa ya kwanta" rufe ido yai kamar mai bcc amma ba bcc yakeyi ba.

"Itako Zahra ta dauka bcc ne yai
"Gefe guda ta samu ta rabe"uncle Haidayr yana kallanta kyaleta yai saeda bcc yaci karfinta snn yaxo ya kamata ta hau katifa ta kwanta.

"Shima kwanciya yai batare daya tabetaba haka suka kwanta har asuba"snn yatashi yaje yai alwala yaxo yai sallah.

"Bayan ya'idar ne ya yadata ta tashi tai sallah itama.
[7/17, 10:43] Washa: πŸ’ŽπŸ’¦πŸ’Ž
πŸ’


GARKUWATA
(RELIANCE)


FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.πŸ’


πŸ’ŽMMN USWANπŸ’Ž


DIDECATED TO SWEET SIS MARDIYA KA'OJE


12


"Zahra na'iadr da sallah ta mike hade da nade sallaya ta'ije a kan akwati"Snn ta samu gefe ta rabe.

"Uncle Haidayr yana kwance akan katifa yana kallanta"gani yadda ta rabe a jikin bango ne yasa uncle Haidayr yace xoki kwanta ki hura mana"Zahra tace aa ai ba gajiya nai ba.

"Sae yasake cewa to bako gaisuwa? A lokacin ne taji wani iri sbd ita kanta mance wa tai"Dukar dakai tai kasa snn tace ina kwana, saeda yai murmushi snn tace ply klau kintashi lpy?

"Tace lpy klau"Snn yace jeki ki gaida mmn ,Daganan kiduba kota tashi.

"To kawai Zahra tace hade da mikewa"Dakin mmnsa tanufa da sallama tashiga har kasa ta duka snn tace ina kwana, Da fara'arta ta amsa hade da cewa kuntashi ply?

"Zahra tace ply klau"Mmn tace madalla.

"Mikewa Zahra tai ta koma daki"Tana shiga uncle yace har kungama gaisuwar?

"Zahra tace eh"Komawa tai ta xauna,shima uncle din mikewa yai yaje gaida mmnsa' gani yafita Zahra ta mike tafara gwara gado hade da share tsakar dakin ta kakkabe ko'ina.

"Dakine ciki daya dan madaddaci wanda yasha blue din fenti amma babu silim rufi akai masa da fale fale snn aka bishi da gora aka jera a sama" bakin kofa kuma akai masa fenti da farin kasa nan ne dakin amarya sae wanda yake kallon dakin Zahra shikuma nan ne dakin mmn uncle Haidayr tsakanin dakin uncle Haidayr dana mmn bewuce taku biyar ba sae bayi dake gefe.

"Uncle Haidayr zama yai a dakin mmnsa sukai hira sosae"Itako Zahra tana gamawa hada kayan wanke wanke tai ta fita taje tana wankewa tana gamawa tai sharar tsakar gida' bayan ta kwashe snn takoma dakin ta zauna.

"Bedade da zama ba Zahra tashigi'gani uncle a dakin yasata koma bakin kofa ta tsaya" uncle yace kishigo mana" shiru tai bata tanka shiba.

"Gani hakan sae yace tunda baxiki shigiba to mikomin kofi nasiyo shayi" dole yasa ta shigo ta dauko kofi ta mike masa"yana fita da sauri ta dauki tai kwalliya hade da sa kaya bakin katifa ta zauna.

"Be dade ba yadawo yana shiga da kansa ya dauko wani kofi ya xubawa mmnsa snn yacewa Zahra ta tashi ta kaiwa mm"mikewa tai hade da xaro hijab tasa' saeda taba snn ta dauka takai mata ko kafin tadawo yariga ya xuba mata a kofi hade da ragowar namanta na jiya da bata ciba ya aje mata a gefe.

"Tana shigowa ganisa tai yana shikaryawa gun tasamu ta xauna" uncle yace ga naki dauki ki kamarya' To kawai tace amma taba dauka ba.

"Gani hakan yasa uncle mikewa kamar wanda zai dauki wani abu" gabanta yaxo ya zauna dab da'ita suna kallon juna snn yasa hannu ya jawo kofin shayin hade da ledar biredi da naman, Bude ledar uncle yai ya dauki nama yakai mata baki.

"Da sauri ta dauke fuskanta hade da cewa aa uncle kabari zanci da kaina" uncle yace aa banyarda ba, Zahra tace Allah kuwa.....

"Kafin ta rufe baki tuni uncle ya cusa mata namar a baki" Snn ya dauko kofin shayin yakai mata baki duk yadda taso taki amsa uncle yaci karfinta a hankali yake bata hade da janta da hira har saeda tace da koshi snn ya kyaleta yakarisa nasa karyawan.

"Suna gamawa kwashe kofinan tai taje da dauraye snn ta dawo dasu daki" tana ijewa uncl ya kamo mata hannu yana cewa ki tayani aiki' littafan students ne ya dauko wanda besamu yai masu marking a school ba shine ya kawo gida, karanta masa takeyi one by one assiment daya basu wanda sukai daedae ya amsa yai marking wanda kuma beyi daedae ba ijewa yakeyi gefe.

"duk mark din da yakeyi idonta na kai har yaxokan na Maryama lekawa takeyi taga irin marking da zaibata gani yasa mata 10 over 15' snn kuma yadawo yasa mata 18 over 20" Dama dokan uncle Haidayr ne duk wanda note dinsa yai complete 14 ne xai bashi assiment kuma 20 making attendes and exam da haka har suka maga.

"Suna gamawa ya maidasu ciki jakarsa ya mike mata yace ta ije da haka yaita janta da hira rana tai gani rana yayi yasa uncle Haidayr mikewa zuwa dakin mmnsa yana tambayarta abinda za'a dafa" sae tace babu abinda za'a dafa tunda akwai ragowar tuwon biki sae yakare snn asa wata sanwa sabo a gida.

" uncle Haidayr be tanka mata ba' Sbd idan da sabo yasaba da halinta" Har ya juya zai fita, Mm tace Aley.

"Juyowa yai hade da cewa na'am sae tace dama garan nan ne nakeso ka kwaso akawoshi dakina" uncle yace dakinki kuma?" Tace eh.

"daga lokacin besake mgn ba tafiya yai ya kwaso ya kawo dakin"gefe ta nuna masa tace ya'ije a gun, yana gama kwasowa yakoma daki sukaci gaba da hirarsu" gani har la'asar babu wanda ya leko mm da kanta taje kofar dakin hade da sallama uncle ne ya amsa sae Mm tace Zahra ta tafito.

"Zahra najin haka da sauri tamike tafita" tana fita mm tace taje ta hura wuta ta duduma tuwo' To kawai Zahra tace snn takami hanya gun sa sanwa.

"Icce taje ta dauko tafara hura wuta"tanaji yana mutuwa da yake lokacin ruwane kuma ruwa ya daki icce' da kar tasamu ya kama idanunta ko duk sun kade suyi jawur sbd hayaki. Gani yakama sae takoma daki"Ashe tana komawa yasake mutuwa bata saniba.

"Uncle yana gani yadda idanunta sukai jawur harda kwallanta yakama cemata sannu" Shirun da mm taji yasata lekawa tana gani wutar ya mutum zuwa tai har bakin kofa ta hau Zahra da fada'Zahra najin haka da sauri tafita daga dakin takoma gun wutar taci gaba da hurawa.

"Tun daga snn bata koma dakin ba har saeda tuwun yai xafi snn taje ta sanarwa mm"mm da kanta taxo ta raba tuwun tasawa kowa nasa snn tace ta dauki na mijinta takai masa hade da nata.

"Tana ije masa nasa a gabansa snn tasamu gu ta ije nata gefe ta samu ta xauna shiru tai tana tunani" har sau uku uncle yana kiranta amma bata jiba' da uncle yaga haka hannu yasa ya tabota, a gigice ta dago kai.

"Snn yace tashi ki dibomin ruwa.

"Mikewa tai taje ta dibo masa ruwan ta kawo masa" shima kansa jikinsa yai sanyi sbd yadda mm ta hauta da fada kamar wanda tai wani laifi.

"Tunda Hajjo takai kabari gidan su Haule mmn garzali cewa malam Habu ne yace kada abawa garzali auren Zahra"Shine yasa garzali yasha alwashin gani bayan malam Habu da iyalansa" dan haka suka yanke shawaran cikin daren yau zasuje su samasa wuta su kashesu gaba dayansu"Ita kuma Zahra duk hanyar da zaibi saeyabi ya dauketa koda be samu aurenta ba saeya bata mata rayuwa.

"Babu yadda uncle Haidayr beyiba Zahra taci abinci amma takici" Hakan yasa shima besamu yaci sosae ba.

"Da yamma lokacin yafita sallar isha bayan ya'idar da sallar ne snn yabiya yasiye mata gasanshiyar nama yakamu hanyar gida" ko kafin ya'iso har Zahra ta'idar da nata sallar ta kwanta.
"Da sallama yashigo dakin ganinta akwance yasashi ije namar yaje yaiwa mm

Please Login or Register in order to submit comment