Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rike mata hannu suka shige ciki.

"Haidayr yana kashe mashin shima ya shigo bayan sun gaisa ne maryama kecewa dama na jiyone dubaku sbd tun jiya nakeji wasu irin labari a gari tun jiya din naso xuwa amma aiki ya hanani sae nace ba nabari idan muhadu a skull xan tambayeka da naje kuma banganka ba shiyasa nace bari na biyo gida kawai.

"Haidayr yace eh wlh daga nan ne ya fadi mata amma be fadi mata actually abinda ya faruba" harda rashin mgnrsu da Zahra saeda yafadi.

"Juyowa maryama tai gun zahra hade da cewa suhanalillahi haba Zahra menene kuma haka idan wani laifi yai maki basae kifadi masa ba amma menene abin gaba dashi.

"Kuka Zahra tasa uncle Haidayr dake zaune kusa da'ita hannu yasa ya rungumeta da sauri Zahra ta tureshi" ido suka hada da maryama.

"Hada baki sukai sukai ta bata hakuri hade da nasiha amma besa ta dae na kuka ba da uncle Haidayr yaga haka fita yai yaje ta waje ya makale yaji ko xatai mgn amma duk a banxa.

"Da maryama ta gaji mikewa tai hade da daukar hijab dinta ta sallami Haidayr da mm tanufi gida.

"Shima uncle Haidayr tun daga lokacin ya daena shiga har kanta" itama Zahra bata nuna ya dameta ba.

"Haidayr ne ma yafita shiga damuwa akan kin kulasa da batayi.

"Sae dae idan dare yai tashi yakeyi ya xuba mata ido wani lokaci ma har shafe mata fuska yakeyi da zaran tai motsa sae yacire hannunsa.

"Bayan sati da safe uncle Haidayr ya tube ya shiga wanka ita kuma mm tana dakinta ita kuma Zahra na zaune tana shafa mai gani uncle ya shiga wanka da sauri ta mike tasa riga da hijab hade da daukar kayanta kala biyu ta kunle a dankwalin tafice tabar gidan.

"Ko da uncle Haidayr yafito daga wanka yaxo daki yana shiga yaga babu Zahra be damuba sbd yai tunani taje dakin mm dauko wani abune.

"Yana cikin shafa mai karaf idonsa yakai gun akwati ganisa yai bude babu kayan da yawa a ciki"da sauri yaje yana dubawa yaga babu wasu daga cikin kayanta kuma babu hijab duba dakin kofa yai yaga babu takalminta a guje yaje dakin mm yana tambayarta ko taga fitar xahra.

"Mm tace aa.

"Daki yakoma yasa riga da wando ya fita waje yana dubata.

"Can nisa Zahra ta hangoshi da sauri ta canxa hanya sae da yaxo ya wuce snn itama taci gaba da tafiyar ta.

"Tana cikin tafiya tasake hango maryama da uniform a jiki xata skull sake boyewa tai sae da maryama ta shige snn Zahra ta fito.

Haidayr yana fita gidan su maryama yaje yai sallama" bbn maryama ne yafito har kasa uncle Haidayr ya duka suka gaisa bayan sun gaisa ne uncle yake tambayar maryama.

"Bbnta yace aiko bata dade da fita xuwa skull ba" amma lpy?.

"Murmushi karfin hali uncle yai snn yace dama medakinane nake tunani ko taxo nan.

"Bb yace aa gaskiya bataxo nan ba"dama kayi da'ita xataxo nan ne?.

"Uncle yace eh nima dama key ne nakeso na amsa sbd nayi mantuwa ne a dakin shiyasa.

"Bb yace ayya gashi bata kariso ba.

"Uncle yace babu damuwa" ni natafi bb.

"Bb yace to sae anjima.

"Haidayr na tafe yana cewa to inane Zahra taje ace taje gidan su?.

"Shima bbn maryama tunda uncle Haidayr yake mgn bb beyarda da mgnr ba"amma sae yace idan tai tsami maji.

"Gidan su Hajjo uncle yaje har ciki ya shiga da sallamarsa Hajjo na daki tafito suka gaisa sae tace lpy ko?.

"Uncle yace dama Zahra nazo dubawa ko taxo nan..

"Da sauri Hajjo tace zahra bacewa tai?" Shiru uncle Haidayr yai be tanka ba.

"Sae Hajjo tace gaskiya batazo nan ba" idan banda abinka menene xaisa kabawa kanka wahala akanta waya sanima ko yawan duniya taxo...

"Mikewa uncle Haidayr yai hade da cewa in Allah ya yarda bazataga yawon duniya ba snn yafice.

"Shewa Hajjo tai hade da cewa wahalaile kawai.
[7/17, 10:43] Washa: πŸ’ŽπŸ’¦πŸ’Ž
πŸ’



GARKUWATA
(RELIANCE)


FASAHA ONLINE WRITERS F.O.WπŸ’.



MMN USWAN



DIDECATED TO SIS MARDIYA KA'OJE.


20



"Uncle yana fita gida ya koma yana tafe yana tunani kala2"Hade da tambayar kansa shidai a iya sanisa babu wani abu da ya hadashi da Zahra, kuma ina kyautata mata iya karfina idan ma akwai matsala nasan baya wuce takuran da mm ke mata kuma idan da sabo ya kamata ace ta saba.


"Amma in ba shiba nasan a bangarena banida wata matsala da'ita kuma nasan Zahra yarinya ce mai hakuri" sae dae abinka da d'an adam yau da gobe sae Allah amma duk inda take ina rokon Allah ya tsaremin ita aduk inda take snn kuma ya baiyana min ita.


"Da haka har ya'isa gida"yana shiga da sauri mm ta taresa da kaganta?" Uncle Haidayr yace wlh mm har yanxu banganta ba.

"Mm tace subbuhanallah xama be ganmuba bari na dauko kyaleta mutafi.

"To kawai uncle Haidayr yace.

"Daki mm ta koma ta dauko kyale hade da jawo kofofin gidan snn suka fita" suma fita mm tace akoma gidan su Zahra tasake tambaya da kanta.

"Uncle be musaba yace to.

"Suna isa uncle Haidayr tsayawa a waje yai ita kuma ta shiga daga ciki"da sallama ta mmn maryama ta amsa snn suka gaisa, bayan sun gaisa ne mmn uncle take fadin abinda ya kawota.

"Mmn maryama tace ayya Allah sarki wlh batazo nan ba"shi Mijin nata ya duba gidansu kuwa ko taje?".

"Mmn uncle Haidayr tace yace yaje nan dinma batanan.

"Mmn maryama tace kash abu beyi dadi ba itako wanga yarinya ina taje haka?".

"Mmn uncle Haidayr tace to wa ma yasani".

"Mmn maryama tace gashi yanxu malam yafita dana biku tafiya nimota ko Allah xaisa adace.

"Mmn uncle Haidayr tace aa haka ma mun gode"Bari na tafi.

"Tace to Allah ya baiyanata.

"Tace amin.

"Snn sukai sallama.

"Mm tana fita uncle Haidayr yace bana fadi maki nariga nazo nan ba kuma sunce bata nan.

"Mm tace aa Aley kasan baya bata da kadan shiyasa nace musake xuwa.

"Kodae xamu koma gidansu ne?" Musake dubawa?".

"Da sauri uncle Haidayr yace wahhh!" Allah ya sauwake.

"Na tabbata duk inda Zahra xataje zata iya xuwa amma banda gidan wannan muguwar matan wanda bata nufin ta da alkairi sae sharri.

"Shiru mm tai hade da jijjina mgnr uncle Haidayr snn tace Allah ya kyauta.

"Haka sukai ta yawo duk inda ya kamata su ganta sunje amma basu ganta ba"uban gajiyar da mm tai.

"Gani tagaji ne yasa uncle Haidayr yace su samu gun ta huta"can gefe ya hango wata bishiya a gefen hanya yace suje ta huta mm tace to.

"Suna zaune suna mgnr abinda ya damesu duk mgnr da sukeyi hankalin uncle Haidayr yana kan hanya ko Allah xaisa ya hango Zahra.

"Basu dade da xama ba yar'skull suka taso maryama hade da sauran yara suna tafe suna hiransu.

"Daya daga cikinsu ne hango uncle Haidayr zaune da sauri tace lahhh!" Ga uncle Haidayr can zaune.

"Sauran duk suka juya hade da cewa sannu uncle Haidayr ina yini.

"Yace lpy klau har kun tasowa?".

"Sukace eh uncle.

"Uncle yace to sae gobe.

"Sukace Allah ya kaemu hade da tafiyarsu.

"Maryama dake cikinsu dawowa da baya tai ta kariso inda suke hade da gaida mm bayan sun gaisa ne take tambayar uncle Haidayr lpy na ganku anan?".

"Mm dake zaune a gefe tace kedae bari kawai wlh tun safe muke niman innawuro bamu gantaba har yanxu.

"Zahra tace subbuhallilah ina ta shiga haka?".

"Mm tace to wa yasani kuma duk inda ya kamata muduba mun duba amma bamu ganta ba har gidan Ku muntafi da gidansu amma duk bata nan.

"Maryama tace to fa Allah ya kyauta.

"Mm tace amin.

"Maryama tace yanxu abinda ya kamata ayi shine tashi xakiyi kije gida mm uncle Haidayr xairakani gida na canxa kaya snn sae mutafi nimanta.

"Mm tace aa yar"'nan sae dae mutafi tare.

"A lokacin ne uncle Haidayr yace aa mm kitafi kawai kinga mubar gida babu kowa kuma gashi anfara kiran sallah kitafi kawai mu xamu tafi da maryama kada kidamu.

"Mm tace to shikenan Allah yasa adace.

"Duk mikewa sukai mm tai hanyar gida su kuma suka kami hanyarsu.

"Suna tafe ne maryama tace uncle kodae wani abune ya hada ku da Zahra?".

"Himm yace snn yace wlh maryama nidae a iya sanina babu abinda nake mata na cutarwa duk abinda xai bata mata rai ina kamfa2 dashi" ni dae abu daya na sani shine tunda Zahra tai bari bansake gane kantaba nayi iya kokarina dan na shawo kanta naji abinda ke damunta amma taki ko ranar da kikaxo kema kin ga halin da muke ciki da'ita.

"Maryama tace haka ne Allah ya kyauta.

"Uncle yace amin.

"Suna isa kofar gida maryama tace uncle bari na shiga na canxa uniform sae nazo mutafi.

"Yace to sae kinfito.

"Maryama na shiga da sallama bbnta ya tareta da kindawo maryama?".

"Na dawo bb"ya gida?".

"Gida alhamdllh.

"Snn tace bb kaji mgnr bacewar Zahra?".

"Bb yace naji' amma da farko da yaxo kasa fadimi yai sae da talatu taxo shine take sanarwa mmnki.

"Uhm kawai maryama to snn tace bb! Dan Allah uncle Haidayr yana waje yana jirana ina dawowa daga makaranta ne na gansu shida mmnsa shine nace ita ta koma gida shikuma yaxo muje nimanta amma sae na dawo gida na sanar daku.

"Bba yace to babu damuwa maryama.

"Maryama tace to bb.

"Mikewa tai ta shiga daki ta" tana shiga hurga jakar ta tai akan gado batare da ta juya ta kalli gadon ba snn taci gaba da tube uniform din dake jikinta.

"Juyawar da xatai ta dauki xani ta hango Zahra kwance akan gado.

"Da sauri tace Zahra!" Zahra tace "na'am" maryama tace dama nan kikazo?".

"Zahra tace Eh.

"Bbn maryama jin ta kira Zahra yasashi shigowa dakin da sauri"shima kansa yai mmkin gani Zahra a dakin suna hada ido ya hauta da fadi itama mmn maryama ta shigo.

"Shiru Zahra tai tana hawaye"Yana cewa yanxu kin kyauta kenan sbd Allah yaro yana ganimu da mutunci kisa girmanmu ya xube ba saeyaga kamar boyeki mukai ba yace bakinmu daya dake ni gaskiya baki kyauta minba wlh Zahra kallonki nake tamkar maryama da na haifa a ciki.

"Kuma yaronga yana gani mutuncina duk inda yaganni bb sama bb kasa yanxu da wani ido kikeso na kallesa kuma me zanfadi masa har uwarsa fa saeda tazonan.

"Kuka kawai Zahra keyi harda sheksheka.

"Gani hakan mmn maryama tace malam ya'isa haka" tunda kaga tai haka akwai dalili kuma ido ta gani yasa taxo nan din, da bataje gidan wasu ko gidansu.

"Bbn maryama yace hakane amma kinsan bata kauta bako?".

"Mmn tace hakuri zakiyi.

"Yace to yanxu abinda nakeso dake Zahra tashi muje na rakaki gun mijinki kukoma gida.

"Zahra najin hakan tasake fashewa da kuka.

"Mmn maryama tace aa ba haka za'aba kamata yai a tambayeta dalili guduwa tazonan ta boye snn ta juya kanta tace ke Zahra lpy kika gudu daga gidan miiinki kikazo nan kika boye?".

"A lokacin ne Zahra ta kwashe duk abinda mmn uncle take mata ta fadi masu harda mgnr dibo ruwa ta karisa mgnr hade da fashewa da wani kuka tana fadin wlh kullin bata bari na huta kuma komai nai ban'iya ba.

"Dukkasu shiru sukai suna jijjina mgnr sbd sunsan kadan ne daga cikin aikin talatu.

"Maryama dake zaune gefen gado jawo Zahra tai ta rungumeta tana lallashinta.

"Cikin dabara ta manya bb ya lallabeta hade da bata maganganu masu dadi snn yace xanxo har gidan naku naga ita talatun amma yanxu tashi kibi mijinki kinjiko dan Allah Zahra kikara hakuri ita rayuwar aure dan hakuri ne duk wanda yai hakuri a rayuwa yana tare da rinjaye in Allah ya yarda bazaki bata danasa ba dan haka tashi muje.

"Jikin Zahra yayi sanyi sosae amma besa ta mike ba" maryama na hada ido da bbnta ya kashe mata ido alamar ta kamo mata hannu.

"Saida maryama ta sauka snn tarikowa Zahra hannu a hankali Zahra ta sauka daga gadon tasa takalmi da hijab batare da ta daukin kayanta ba haka suka fita suna gaba bb na baya har suka kai xaure.

"Da sallama suka shiga xaure juyowar da uncle Haidayr xaiyi yaga Zahra mmki ya kamasa yace Zahra dama kina nan shine kika barni nake ta wahalar nimanki?".

"Bba yace dan Allah aliyu kayi hakuri wlh nima kaina bansan zahra tashigo gidan nan ba sae bayan dawowar maryama snn muka sani amma kayi hakuri.

"Shiru kawai Haidayr yai be tanka ba.

"Bb yace maryama tabasu gun take hannu Zahra tai tashige ciki"snn bb yafara mgn da uncle Haidayr duk mgnr da yayi be bude masa ba a dunkule yake bashi har ya kare snn uncle Haidayr yace nagode bb.

"Bb yace ga matarka nan dauketa kutafi.

"Uncle yace to.

"Bb ya karisa mgnr ne hade da juyawa ya shige ciki.

"Bb na shigewa uncle Haidayr yaje jikin bangon da Zahra ke rabe ya kamo hannunta.

Hannu uncle Haidayr yasa ya kamo mata nata" da sauri ta fisge hannunta hade da igijesa.

"Murmushi uncle Haidayr yai snn yasake riko mata hannu.

"Tasake kwance hannu hade da fashewa da kuka.

"Gani haka yasa uncle Haidayr kamo mata hannu da karfi ya jawota suka bar gun Zahra tayi kokarin kwance hannunta amma takasa.

"Gani hakan yasa Zahra fadi a kasa takama birgima a kasa"da uncle Haidayr yaga haka tanada niyar da tara masa jama'a hannu yasa ya ciccibota ya dagata yaci gaba da tafiyar sa.

Sae ta kaimasa cixo a hannu.

"Uncle ywce wlh idan kika cijeni sae na mareki.

"Cikin kuka tace to ka dauke ni nayi tafiya da kaina.

"Snn ya dauketa yana dauketa ta sake fisge hannu taza gudu.

"Da sauri ya tarota hade da cewa dan Allah Zahra menene kikeyi haka?" Cikin kuka Zahra tace wlh ni babu inda xani" ni bazan koma gidan ba.

"Jin haka ya fisgo hannunta hade da cewa wlh saekin tafi.

"Haka yaci gaba da janta har sukakai gida"suna shiga cikin gida turata dakinsu uncle yai gani tana kokarin fita da sauri shima ya shiga snn ya rufe kofa.

"Gabansa Zahra taxo ta tsaya tana kokarin sa hannu ta bude kofar" dauketa da mari uncle Haidayr yai hade da igijeta kan katifa.

"Ihu Zahra tasa hade da kiran wayyoo Allah na na shiga uku na lalace wayyoo umma wayyoo baffana" baffana katafi ka barni kaxo ka taimakeni baffana haka Zahra ta dunga yi tana birgima akan katifa.

"Mm najin haka da sauri taxo ta na buga kofar uncle yace babu komai kitafi kawai.


"Jikin uncle Haidayr yai sanyi zuwa yai ya dagata hade da rungumeta da karfi a jikinsa yana lallashinta yana cewa haba fatimatu Zahra'u shugaban matan aljanna shalelen ma'aiki" haba babyna dan Allah ki daena kuka haka kinji Zahra.

"Jin irin rikon da yai mata yasata narkewa a jikinsa kuma ta daena ihu saedae hawaye kawai sbd yadda uncle Haidayr yake yimata.

"Uncle yace yauwa ko kefa yanxu fadimi waye ya tabamin ke?" Fadimi ko wayeshi.

"Cikin shakshekar kuka Zahra tace ba mm ne ba daga snn tafara zaiyana masa duk abinda mm ke mata da wanda yasani da wanda besani ba harda mgnr cikinta.

"Ran uncle Haidayr ya baci mikewa yai hade da cewa ina xuwa zahra yana fita gidan kawu Ibram ya nufa kai tsaye har cikin gidan ya shiga da sallama.

"Kawu Ibram ya amsa snn suka gaisa bayan sun gaisa ne kawu yace Aliyu lpy kuwa na ganka haka?".

"Haidayr yace wlh kawu mmce takeson kashemin aure.

"Kawu yace subbuhanallah kash! Abu beyiba garin yaya Aliyu?".

"Uncle ya kwashe komai ya fadiwa kawu Ibram babu abinda ya boye masa hade da cewa wlh kawu yanxu da haka zara'u tana nan ta tsaya akan gida xata bari wai tagaji da xaman gidan.

"Da sauri kawu yace aa baza'ai haka ba tashi muje gidan"mikewa uncle Haidayr yai suka nufin gida.

"Suna shiga har dakin mm suka shiga shida Haidayr" Haidayr na zaune ta bakin kofa mm tace Ibram kai ne a gidan tamu da rana haka?".

"Yace wlh kuwa"mikewa tai ta dibo masa ruwa bayan ya sha sukai gaisa snn kawu yace talatu dama ba wani abu ya kawoni ba, yarone ya kawomin karanki.

"Mm tace wani yaro kuma?" Kawu yace aliyu mana yace kin takura masa shida matarsa gashi sanadiyar haka har matarsa da gudu tabar gidan.

"Salati mm tasa hade da fashewa da kuka tana fadin yanxu sharrin da xakai min kenan kaida matarka Aley?".

[7/17, 10:44] Washa: πŸ’ŽπŸ’¦πŸ’Ž
πŸ’



GARKUWATA
(RELIANCE)



FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W
πŸ’.


πŸ’ŽMMN USWANπŸ’Ž


DIDECATED TO SIS MARDIYA KA'OJE.



21


"Yanxu sharrin da zakaimin kenan kaida matarka Aley?". To Allah yagani bada wata manufa nake mata haka ba" amma tunda abin ya zama haka in Allah ya yarda bazan sake sa maka ido ko baki ba aduk abinda xakuyi kai da matarka banle kukai karata ko tabar gidan sbd ni.

"Amma kuma inaso kasani aliyu nice na haifeka na dauki cikinka har tsawon wata tara har yakai na maifeka nida mahaifiyarka mukai dawainiya dakai har lokacin da Allah yai masa rasuwa sbd kasamu ingantanciyar rayuwa yasa na jiginar da duk wata jin dadin rayuwa na tsaya tsayin daka d'an naga kazama abin kwantance kuma alhamdllh ba fariya nayi ba niyi imani idan bakazo na daya a kyauyen nan ba xakazo na biyu wajan ilimin addini dana xamani duk da nasan ba wayona bane kuma ba dabarata bace amma yau irin sakayyar da xakamin kenan babu komai nagode tashi kaje Allah ya baku xaman lpy.

"Tunda daga lokacin hayewa gado tai ta kwanta batare da ta nuna bacin rai ko fushi ba kukanma ta daena.

"Gani haka yasa Haidayr fashewa da kuka yana fadin dan Allah mm kiyi hakuri wlh ba haka nake nufi ba dan Allah inaso ki fahimceni mm...

"Hannu kawai ta daga masa alama yai mata shiru.

Bude baki zaiyi mgn wani irin kallo tai masa yasa mgn.

"Gani hakan yasa kawu cewa talatuwa dan Allah inaso ki saurareni kuma ki fahimceni ni banazo nan dan na bata lamari bane"na zone dan gyara kuma inda nasan haka abin xaixama wlh da banxo.

"Snn ya juya kan aliyu yace kai Aliyu kayi hakuri kuma daga yau bazan sake sa maka baki akan mgnr gidan nan ba ko akan menene kuwa nagode.

"Mikewa yai zai fita a dakin mm" da sauri tace aa Ibram ba haka nake nufi ba.

"Kawu yace to menene?".

"Mm tace karatafa yakai kama cewa bayaso ina sa masa baki tsakanisa da matarsa kuma nace bazan sake ba tunda bayaso.

"Kawu yace aa talatu fushi kikeyi mana.

"Murmushi mm tai hade da cewa fushi me zanyi?" Sbd ya fadimin gaskiya ni nagode wa Allah ma dayasa suka fadimi da naje cikin mutani axo ana nunani da yatsa ace nakori sarkuwata.

"Haidayr yace wlh mm ba haka nake nufiba.

"Itama tace Aley nima ba fushi nayi ba baka fahimceni bane tashi kaje Allah yabaku xaman ply.

"Duk yadda kawu yaso yayiwa mm bayani amma taki hakuri haka yagaji ya kyaleta ya tafi.

"Shima uncle Haidayr komawa daki yai yana shiga bakin katifa ya samu ya xauna hade da xabga tagumi hannu bibbiyu.

"Da sauri Zahra taxo inda yake zaune ta zauna kusa dashi snn tace uncle lpy?" Me yafaru?".

"Haidayr yace babu komai Zahra me kika gani?".

"Zahra tace gani ka xauna kayi tagumi kamar akwai matsala.

"Murmushi kawai yayi mata batare da yakai xuci ba hade da cewa kainane yake ciwo shiyasa.

"Zahra tace ayya sorry uncle amma kasha magani kuwa?" Tayi mgnr ne hade da shafe masa kai uncle Haidayr yace bari magani ninan tukun ba kowani ciwone zakasha magani ba sbd akwai lokacin da zaikai wanda koda kasha ba zaiyi aikiba.

"Shiru Zahra tai snn tace to kwanta bari naje na sanarwa mm.

"Da sauri yace aa barta kawai nasamu sauki ma.

"Jawo hannunta yai yace zo mu kwanta dorata yai akan kijinsa hade da shafe mata baya a lokacin ne Zahra tace uncle daxu naji kaman mm na kuka.

"Uncle yace anya mm kuwa?" Zahra tace"Eh lokacin da akwai kawu.

" uncle yace kai ba ita bane" Zahra tace Allah kuwa uncle da gaske.

"Tun daga lokacin be sake tanka mata ba shafeta kawai yaci gaba dayi batare daya bude ido ba duk abinda yake mata idonusa a rufe yake har bcc ya dauketa.

"Gani bcc ya dauketa yasashi kwantar da'ita a hankali ya shinfidata kamar yar'goye sbd kada ta tashi.

"Yana shinfidata tashi yai zaune ya xuba mata ido yana kallonta" ada uncle Haidayr betaba tunanin zai taba jin yanason Zahra ba sbd ya aureta ne dan wata dalili.

"Dalilin kuwa shine d'an yaga yadda garzali xaiyi idan aka rabashi da Zahra sbd yasan ba karamin so yakewa Zahra ba" hakan yasashi auren Zahra d'an daukar fansar walakanci da garzali yai masa shida bbnsa a lokacin da yaje amsar ragowar kudin gonarsu yanaso yabiya kudin makarantar sa amma yanaji yana gani garzali yace kada bbnsa ya bashi kudin hakan ba karamin xafi yai masa ba.

Tun daga lokacin ya tsani garzali da bbnsa kuma yake niman hanyar da zairama shiyasa da yaji mgnr aurensa da Zahra kuma yai sa'a tace bata sonsa shiyasa yai amfani da wannan damar ya auri Zahra amma badan yana sontaba duk da ba wani aibune da ita ba dan kawai yaga yadda garzali zaiyi ne.

"Amma a yanxu yadda yakeji Zahra a zuciyarsa beji zai'iya rabuwa da'ita ba saedae mutuwa" sbd Zahra yarinya ce amma ta'iya abinda wata babban macen ma bata iya ba must especially wajan mu'amala duk wata salo da iya style kala kala Zahra ta'iya kamar bashine ya koya mata ba mafi yawancin lokuta idan tai masa wani style shikansa har mmkinta yakeyi haka take masa har sae taga ya gamsu.

"Hakan yasa a ko wani lokacin yakeso kasancewa da'ita kuma koda sau nawa xaixo mata bata gajiya ko korafi.

"Shiyasa yake iya kokarinsa wajan yaga ya kyautata mata yadda take kyautata masa" amma gashi mm tana niman rabashi da'ita.

"Da irin wanga tunani yai tayi har aka kira sallar la'asar mikewa yai ya dauki buta yafita yaje yai tsarki hade da alwala snn yadawo daki yatada Zahra tayi sallah shikuma yatafi masallaci.

"Zahra na fita sukai karo da mm itama ta fito daga bayi suna hada ido mm ta daure mata fuska.

"Zahra bata kawo komai a ranta ba shigewa tai tai tsarki tafito tai alwala tashige daki tai sallah tana idarwa taxo dakin mm da sallama ta shiga dukawa tai snn tace Mm!.

"Mm tace na"am.

"Zahra tace meza'a dora?".

"Mm tace aa barshi kawu keda bakida lpy.

"Zahra da fara'arta tace lahhh!" Mm ai nasamu sauki sosae.

"Itama da fara'arta tace madalla Allah ya kara sauki.

"Zahra tace amin.

"Mm tace jeki idan megidanki yadawo sae ki tambayesa abinda yakeson ci sae ku girka abinku.

"Murmushi Zahra tai snn tace to mm" yanxu yatafi masallaci bedawo ba bari na gyara miki daki kafin yadawo.

"Kafin mm tace komai tuni Zahra tariga ta kwashe kayan dake kan gadon ta xuba akan tabarma saeda ta kakkade gadon snn ta sanya mata wani zani gadon ta kwashe kayan ta ninke tasa agefe inda mm ke ijewa snn ta share mata dakin tas tana gamawa mm tace nagode innawuro Allah yai maki albarka.

"Zahra tace amin mm bari naje na duba ko yadawo.

"Mm tace to.

"Zahra na shiga daki taga uncle har yadawo ya kwanta a rigingine tace har kadawo batare daya dagoba yace nadawo..

"Zahra tace uncle meza'a dorane?" Uncle yace jeki ki tambayi mm.

"Zahra tace mm ce tace nazo na tambayeka duk abinda kakeso shine za'ayi.

"Shiru uncle yai besake mgn ba kuma be motsa daga inda yake kwance ba nazarin mgnr da Zahra ta fadi masa kawai yakeyi.

"Gani shiru da yai ne yasa Zahra cewa uncle bakace komai ba snn yace ba akwai ragowar tuwo ba?".

"Zahra tace Eh.

"Uncle yace shine za'aci.

"Zahra tace to shikenan juyawa tai zata fita uncle yace ina zaki?".

"Zahra tace zanje na sanar matace.

"Uncle yace dawonan ki zauna.

"Zahra tace to uncle" dawowa tai ta zauna kusa dashi.

"Da dare bayan isha'i uncle yaje ya siyo kayan shayi biredi manya uku sae kayan shayin da sugar tun agun yaraba yasawa mm nata daban nasuma daban ruwan shayi kuma yana plast yana dawowa gida bayan ya zauna babban kofin da Zahra ke bashi ruwa a ciki yace ta dauko masa aikine ya xubawa mm nata snn yace Zahra ta dauka ta kai mata.

"Zahra tace to mikewa tai ta dauka takai mata tana shiga tace mm gashi iji uncle" tana kwance batare da ta tashiba tace menene?".

"Zahra tace shayine mm.

"Mm tace aa kusan shayi ba damuna yai ba dauka ki kaimasa kukara.

"Zahra tace aa mm dayawa fa yasiye kitashi kisha koda kadan ne.

"Mm tace aa innawuro da dae kinje dashi kukara.

"Zahra batace komai fita tai taje ta sanarwa Haidayr yadda sukai da mm dama duk yana jinsu duk abinda sukeyi.

"Mikewa yai hade da kamo hannunta yace xomuje kitayani bawa mm hakuri" Zahra tace dama kaimata laifine?".

"Yace eh".

"Akan me?".

"Yace nima bansani ba xodae muje kawai.

"Kamo hannu yai yace xomuje kawai.

"Suna shiga Haidayr ya duka har kasa gani hakane yasa Zahra itama da duka kusa dashi duk suka hada baki sukace dan Allah dan annabi mm kiyi hakuri ki dan Allah mm.

"Duk da sunbata dariya amma dan newa tai snn tace

Please Login or Register in order to submit comment