Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauran yai ya zubasu a cikin leda snn ya dauka zuwa dakin Zahra.

"Bayan sun gama cin abinci ya bata magugunarta tasha sukadan yi hira snn kowa yaje daki kwanciya a lokacin ne ya dauko ledar zannuwar yabawa Zahra yace tacire guda hudu ragowar kuma na maryama ne.

"Da murnarta ta bude ledar tana budewa taga babu wanda takeso a ciki' ashe tunda maryama take zaban zannuwar a kasuwa Zahra taga wanda takeso a ciki a zuciyarta tace koda uncle yace nazaba wanga ne zanzaba gaba daya sune Mm ta kwashe.

"Hawaye ne kawai suka xubo mata batare da ta tsaya zaba ba cirewa kawai tai ta'ije a gefe hade da cewa nagode snn ta kwanta.

"Jikin uncle yai sanyi matsewa kawai yai yace lfy Zahra?" Batare da ta juyaba tace babu komai' shima kansa jikinsa yai sanyi shiru yai besake mgn ba.

"Ita ko Zahra hawaye kawai takeyi a kwance shima da yaga haka beyi tunanin matsowa kusa da'ita ba kowa kwsnciyarsa yai.

"Da kuwa tunda ta idar da sallah tace masa ina kwana bata sake masa mgn ba koda yai mata bazata amsa ba tana kwance a daki ko parlour taki fita koda aka hada abin karyawa kin fita tai banle ta karya uncle ne ya dauka ya kawo mata daki hade da cewa Zahra tashi ki karya.

"Tanajin mgnr sa rufe ido tai kamar mai bcc shima da yaga haka murmushi kawai yai yafita ya koma gun su maryama suka karya.

"Bayan sun gama karyawa ne ta kwashe kayan ta wanke ta gyara ko'ina snn ta wanka ta shirya tafiya gida' gani tun fase Zahra bata fitoba kuma gashi tashirya komawa gida yasa tace uncle lfy kuwa Zahra bata fito nan ba?" Murmushi yai hade da cewa yau kawarki kunle takeyi.

"Maryama tace dan Allah kirami ita mana.

"Haidayr yace kishiga tana jinki dan ba bcc takeyi ba.

"Da sallama tashiga lokacin Zahra na zaune a bakin katifa suna hada ido dariya sukai wa juna snn maryama tace Zahra yau me yahsnaki fita kika kunshe kanki kamar daddawa.

"Murmushi Zahra tai snn tace babu komai.

"Maryama tace haba wakalli bamu haka dake fa dan Allah fadimi.

"Nan Zahra tafara harda kukanta tana fadin sbd Allah kiduba fa muna dawowa dakin mm yashige da kayan koda ba wanga haka uncle yake koda abu yasiye saeya fara Kawa mm ta zaba kafin ya kawomi ba karamin zafin hakan nakeji ba amma sae na dan ne sbd koda nai mgn cewa zaiyi mmnshi ce fa.

"Murmushi maryama tai snn tace dan Allah Zahra kiyi hakuri ga duk abinda uncle zaiyi maki kinsan fa bakida kowa sae shi banle ma da kuka dawo nan babu wanda kika sani daga mm sae uncle kuma idan banda abinki kikayi hakuri kika lallabesa zai siye maki wanda yafisu amma dan Allah kada hakan da yai ya dameki koda wasa banaso kinuna hakan ya dameki kinjiko.

"Da haka kishare hawayenki ki daena kuka nayi imani idan har kakai masa mgn uncle mesiye maki wanda yafishine kuma banaso idan kinga yaiwa mmnsa abu kinuna bacin rai sbd zaiga kamar bakin ciki ne kikeyi da mmnsa.

"Maryama tace kina jinako.

"Kai kawai ta daga mata".

"Maryama tace to share hawayenki" ni zatafi in Allah ya yarda kafin fi haihu zanxo na dubaki.

"Mikewa tai hade da cewa ni natafi.

"Duk abinda sukeyi uncle na makale a kofa yana jinsu' jin maryama tace ta tafine yasashi kaucewa a gun da sauri.

"Maryama na gaba Zahra na baya suka fito parlour suna fita dukawa tai ta sallama mm uncle kuma yana rike da jakanta rungumer Zahra tai hade da cewa sae na sake dawowa snn suka fita tana dagawa Zahra hannu.

"Gani haka Zahra tasa kuka duk su biyun dariya suke mata har suka fice.

"Napep ne uncle ya tare xuwa bakin kasuwa tukun yaiwa maryama siyayyan tsaraba snn suka karisa tasha yasata a mota be tafiba sae da yaga tashinsu snn yaje kasuwa yai masu cefane yana fita daga kasuwa sukai karo da wani ya buge masa ledar hannu sa kayan miyar ta watse a kasa mmki ya kama uncle daga idon da zaiyi kawai garzaki ya gani.

"Shikuma garzali karawa karansa wuta yai sbd shi kansa besan ya aikata hakan ba sbd a make yake a guje ya bar gu.

"Dukawa Haidayr yai ya kwashe kayan miyarsa yanufo gida.

"Yana shiga dakin Zahra ya nufa yace ga cefane nan kifito kiyi abinci" mikewa tai batare da tai mgn ba taxo ta amsa tashige kitchen ta kunna risho tasa ruwan xafi kafin ta gyara kayan miya' Dakin mm ya shige tana ganisa tai kasa snn da xuwa.

"Yace yauwa mm'mm tace har tatafi ne?".

"Uncle yace eh".

"Tace Allah ya kaita lfy' yace amin snn yace mm kawo zannuwar nan naga wata tela har nai mata mgn tace nakawo.

"Mm tace gasu can ka dauka.

"To kawai yace snn yaje ya dauka yafita.

"Dakin Zahra ya shiga snn ya kirata tana xuwa yace kikawo kayan nan nakai a dinka maki' to kawai tace snn ta dauko tamika masa amsa yai ya fita yakaiwa telan da kansa ya zabawa Zahra style masu kyau na mm kuma yace dinkin manya za'ai mata.

"Tace babu damuwa tai masa lissafin kudi yabiyata cash snn yadawo gida ko mgn beyiba daki ya shige ya kwanta' Tunani kala kala yakeyi da gaskene garzali ne ya gani ko mai kama dashi ne?" Idan ko garzali ne to lalla akwai aiki a gabansa.

"Yana cikin hakan ne Zahra ta shigo dakin ganisa tai kwance ko motsi bayayi kuma ba bcc yakeyi ba.

"Da sauri tace uncle lfy kuwa?" Shiru Haidayr yai sbd bema ganta ba banle yasan tana mgn' har sau uku takirasa amma be amsa ba.

"Dukawa tai a gabansa hade da kamo hannunsa tana jijjigashi tana kiran sunan sa.

"A birkice ya mike zaune hade da kiran sunanta yana cewa yaya akai' idanunta ne suka ciki da kwalla tana fadin lfy me yasameka uncle?".

"Kamota yai yana fadin babu komai Zahra gajiya ne kawai gani kwalla sun xubo daga idonta hannu yasa yana share mata hade da jawota jikinsa yana fadin menene kuma nifa babu abinda ya sameni.

"Shiru kawai tai ta tsaresa da ido.

"Murmushi yai mata hade da rungumeta yana fadi kodae wlh inada aiki abu kadan sae kuka idan kikafi haka tsofa besan yadda zanyi ba tsohowa kawai.

"Dariya Zahra tai hade da cewa ni ba tsohuwa bace wlh.

"Uncle yace da gaske?" Yanxu abinda zanyi xaki iya?".

"Zahra na dariya tace akwai da gaske harma nafika.

Dariya Haidayr yai hade da cewa idan kuma nafiki sae kinmi kyauta.

"Zahra tace na yarda.

"Mikewa yai hade da kamota ta mike saeda yaje ya rufe kofa snn yadawo wayarsa ya dauka ya kunna wakar Mariya Haidayr yana rawa yanabi kamar shine yai wakar babu yadda beyiba akan Zahra tayi amma takasa sae faman dariya da takeyi.

"Kamo hannunta yai hade da cewa bari na taimaka maki hannu bibbiyu yariketa yace to bissmill rawa yake yana juyi da'ita.

"Inba dariya ba babu abinda Zahra keyi rungumarta yai hade da cewa kin gani ko yau zaki biyani kenan.

"Cikin dariya Zahra tace ni ina naga kudi uncle banle na buyaka.

"Haidayr yace bada kudi ba' Zahra tace da me?".

"Kashe mata ido yai.

"Kyalkyalewa da dariya Zahra tai hade da cewa to shikenan uncle.

"Fadawa kan katifa sukai suna wasa Zahra nakan Haidayr sae faman tsikaranta yakeyi tana dariya.

"Bugun kofar mm ya katsesu da sauri ta mike taje tana bude kofa mm tace abinci yana konewa.

"To kawai Zahra tace snn tafita xuwa kitchen.

"Suna sati a gida habib ya kawo Sumayya gidan su Haidayr ita da goyonta Khadijat da far'ar mm ta taresu hade da amsar goyon bayan ta gaida mm sae takoma dakin Zahra dukkansu uku suka hadu suna hira.

"Sudan jima snn Zahra taje tasa abinci ta barsu suna hira da Haidayr ita kuma Zahra tanayi tana dubawa har tagama a plate daya ta hada masu sae na uncle daban sunaci suna hira.

"Sumayya bata koma gida ba saeda yamma da Habib ya taso daga aiki ya biya ya dauketa suka tafi' bayan sun tafine Zahra ta kauda kayan da sukaci abinci snn taje ta kwanta shikuma uncle yana dakin mm suna mgn har bcc ya fara daukan Zahra sae aka kawo light gani haske ya dameta yasata tashi ta kashe wutan.

"Hannu takai kan igiyar wutan dake bude tanajin yai mata shoki da sauri ta cire hannu gani wutar bemutuba sae tasake kai hannu wanga karo da karfi ta rike jin shokin ya fara girgixata ihu tasa tana kiran uncle.

"Jin ihunta yasa uncle fitowa a guje shida mm yana shiga dakin yaga ganta makale shokin yariga ya riketa a guje yaje ya kashe wutan gidan gaba daya snn yadawo ya riketa.

"Gaba daya tariga ta dauke wuta jikin Haidayr yana rawa ya shinfidata akan katifa a guje yafita ya siyo multina da madara yaxo ya hada mata yabata tasha' snn tadan dawo yace Zahra.

"Zahra tace na'am hade da fashewa da kuka.

"Rungumeta yai yana fadin is ok fita mm tai tabar masu dakin" cikin daren uncle ya siyo salataf yabi duk inda yasan a budene yarufe snn suka kwanta.

"Da safe kuwa asibiti ya kaita sbd a dubata koda doctor ya tambayi problem dinta cewa kawai yai shokin ne ta taka batare da tasani ba.

"Doctor ya dudubata yace babu komai amma dan Allah akiyaye.

"Uncle yace in Allah ya yarda.

"Suna fita daga asibiti Zahra tace lemo takejin sha' uncle yace kinga nanan ya kare Zahra tace akwai shi a can kasa.

"Haidayr yace to ai gani nakeyi kamar bazaki iya tafiya ba' da sauri Zahra tace zan'iya.

"Haidayr yace to shikenan.

"Haka sukaci gaba da tafiya sunayi suna hira har sukakai dari biyu Haidayr yaciro yamikawa mai lemon yacce abashi na dukka.

"Zahra tace uncle nanne naga bba Habu' uncle yace wai ke Zahra ina kika taba gani wanda ya mutu ya dawo.

"Kuka Zahra tasa tana fadin wlh kuwa da gaske ne uncle.

"Haidayr yai banxa da'ita taci gaba da kukanta.

"Mutumi da yake siyar da lemunne yace malam lfy kuwa?" Nan Haidayr ya kwashe komai ya fadi masa.

"Sae mutumi yace to kabari mana ka gani ko shidin ne tunda nima ba nine asalin me gun ba yaron shagone.

"Haidayr yace ina ainihin mai gun?".

"Yaron tace yafita amma yanxu zai dawo' Haidayr yace dan Allah ko kasan asalin garinsa?" Yaron yace eh to nasha jin yana cewa shi dan nan garin ne amma a kauye yake wai sunan garinsu dan'babba.

"Zahra naji haka ta fashe da kuka tana fadin wlh uncle shine.

"Wani irin kallon uncle yai mata da sauri ta hade kukanta tai shiru.

"Shiru shiru bedawo ba uncle yace shidae xaitafi idan ita xata xauna' kuka xahra tasa tana rokonsa suna cikin haka saega bba Habu yadawo.

"Da sallama ya kariso gun juyawar da uncle xaiyi bba Habu yagani da sauri ya rungumeshi kuka Zahra tasa tana kiran sunansa
[7/17, 10:45] Washa: πŸ’ŽπŸ’¦πŸ’Ž
πŸ’



GARKUWATA
(RELIANCE)



FASAHA ONLINE ERITES F.O.W.πŸ’



πŸ’ŽMMN USWANπŸ’Ž



DIDECATED TO SIS MARDIYA KA'OJE.



ASSALAMU'ALAIKUM.

ZANYI AMFANI DA WANGA DAMA NA ISAR DA SAKO GAREKU.

ALHAMDLLH NAGODE DA ALLAH YA DORANI AKANKU DA SABODA NIDA HAKKINKU SHIYASA KUKAYI SHUKA IDON MAKARWA' NAYI IMANI BAKUSAN INA TARE DA KUBA YASA DA KUMA HAKKINKU DA BANI DASHI.

NA FARKO DAI BANCE WANI YA KARANTA NOVEL DINNA DOLE BA RA'AYI NE IDAN KAI NIYA KA KARANTA IDAN KUMA BAKAI NIYABA KABARSHI BABU WANDA ZAIMAKA DOLE.

NA LURA KUNFISO AITA ZUBA MAKU KARYA NIKUKA BANIDA WANNAN RA'AYIN KUMA MUTUM BE'ISA YA SANI ABINDA BANYI NIYABA IDAN KAIFI DAYA NAKE.

IDAN KUNGA BEMAKUBA SABODA BABU KARYA ACIKI KUBAR KARANTAWA BABU DOLE.

MU WRITES DA MUKE BATA LOKACIN MU DAN NISHADATAR DAKU BAMUYI KORAFIBA SAIKU DA KUKE GANI DAGA SAMA SHINE HAR KUNADA BAKIN ZAGINMU.

NIDAI WLH DUK WANDA YAKARA ZAGINA ABAYAN FAGE BANYAFE MASABA SABODA IN A GABA NANE NAYI IMANI BAZAN KYALEKABA SAI INDA KARFINA YA KARE.

GODIYA TA MUSANMAN GA DUKKANI DAUKAKIN MASOYANA NA KUSA DANA NISA WANDA NASANI DA WANDA BANSANI NAGODE SOSAI DA IRIN SOYAYYAR DA KUKE NUNAMIN ALLAH YABAR KAUNA DA ZAMUNCI ALLAH YA CIRE MANA KUSHE DA HASSADA A ZUKATANMU
ALLAH YA DOKAMU KAN MAKIYARMU AMIN.

MAGANAR CMM KUMA KADA KUGA NAYI KORAFI AKAI CMM SHIKE KARA MANA KARFIN GWIWA WAJAN RUBUTUNMU IDAN KUMA KUKAI SHIRU SAI MUGA KAMAR BAKUYI FARIN CIKI DA LABARIN BANE
DAN ALLAH A GYARA.

NAGODE




28



"Haidayr yace bb ashe kana raye baka mutu ba shine duk mu dauka wutar nan takama dakai a ciki.

"Murmushi bb yai hade da cewa Aliyu ina raye ban mutu ba kasan mutu baya mutuwa batare da kwanasa yakare ba duk wanda kaga ya mutu tofa kwanasa ne yakare.

"Haidayr yace hakane bba.

"Snn bb yace mekukazoyi anan?" Cikin jin kunya uncle yace asibiti mukazo bba.

"Bb tace subbuhanallah waye ba lafiya?" Haidayr na murmushi yace Zahra ce na kawo.

"Bb yace amma jikin da sauki ko?" Haidayr yace alhamdllh snn uncle yace ga beach can muje mu zauna bba.

"Bba Habu yace kuda kuke kan hanya kada dare yai maku' Haidayr yai murmushi snn yace ai nan muka dawo sbd nasamu aikin police shiyasa na dawo nan da zama.

"Dakawa Zahra tai har kasa ta gaidashi' shima cikin fara'arsa ya amsa snn ta mike.

"Bba Habu yace alhamdllh masha Allah na tayaka murna sosae Allah ya sanya alkairi ya kuma kareka daga sharrin makiya.

"Haidayr har da rsugunawarsa yana fadin amin bb nagode'snn bb yace a wani uguwane kuke?" Haidayr ya fadi masa.

"Shima bb Habu yafa nasa uguwan snn yace yanxu kuje gida naga rana tayi in Allah ya yarda zanzo har gida nida maidakina muga gu.

"Haidayr be musaba yace to bba' bba ya dibi fruit da yawa yabawa su Haidayr ya rakasu har bakin titi ya tsare masu napep ya biya uncle yai godiya sosae snn suka tafi.

"Suna cikin tafiyane Zahra tace to badama na fadi maka ba kace karya nakeyi' Haidayr yace ni bance karya kikeyi ba amma kinsan kamanni da yawa a duniya ko?" Idan muka tsaya yazama bashi bane fa.

"Zahra tai shiru.

"Suna isa gida mm ta taresu da sannunku da dawowa tana zaune a parlour akan tabarma.

"Dayake mai girmane suma zama sukai' mm tace ya maijikin?".

"Uncle yace tasamu sauki a nan ne uncle yake fadi mata suga bba Habu a bakin asibiti harma ya basu kyautar su lemo.

"Cikin mmki mm tace malam Habu fa kace?" Uncle yace kwaro da gaske.

"Nan dae sukai ta hira dukkansu kowa na fadin albarkacin bakinsa.

"Bayan kwana biyu bba habu yaxo gidan su Zahra shida matarsa bayan su gaisa suka din taba hirar mutani kauye snn yatafi yabar matarsa yace da yamma takoma gida.

"Kafin uncle ya fara xuwa aiki cikin kayan daya dinka masu ita da mm yace susa daya daga ciki gidan su iyayen Habib daga nan ya kaisu gidan Habib basu dawo gida ba sae yamma.

"Uncle yana cika sati biyu yafara xuwa aiki wata yana karewa suka samu salary har gidan Habib yaje ya roki Habib cewa yanaso Sumayya taje ta siyo masa kayan baby.

"Habib yace babu damuwa nan tai masa lissafi ya dauki kudin ya bata.

"Haka ya dauka ya bata'washe gari da safe taje kasuwa tai masa siyayyar daya dace ta kawowa Zahra' tunda zahra ta shiga watan haihuwa duk sati uncle yake kaita asibiti kafin yatafi aiki yake kaita baya bakinta anan zama yakeyi ya jirata har sae ta kare snn ya medata gida shikuma yatafi nasa aikin.

"Ranar wata asabar tun misalin magrib Zahra kejin ciwon mara amma ta danne har takare abinci ta rabawa kowa nasa Haidayr yace takai masa nasa parlour tana kaiwa ta'ije ta shige dakinta ta kwanta sae faman juyi takeyi akan katifa.

"Uncle yana gama cin abinci yaje daki' Zahra najin motsinsa murjewa tai kaman ba ita ke juyiba ba yana shiga tubewa yai ya kwanta snn yace kinyi sallah ne?".

"Zahra tace aa.

"Yace tashi kije kiyi'to kawai tace da rurufe ta sauka daga katifar dakar take Jan kafa har tashiga bayi tai alwala taxo ta zauna zata fara sallah kenan uncle yace ta tashi tsaye tayi.

"Da kar take iya mgn tace bazata iya yi a tsaye ba.

" haka tai tayi ita kanta batasan abinda take fadi a cikin sallar ba uncle kuma bcc yariga ya kamashi' haka tai ta dogarawa batare da tasan raka'a nawa ne tai ba tanayi tana hawaye da taga bazata iya karisawa ba mikewa tai tabar sallah haka.

"Tana mikewa ta tube kayan jikinta tarage daga ita sae zani ko pan bata bari ba' cikin ido bcc batare daya bude ido ba uncle yace xoki kwanta.

"To kawai tace masa haka ta lalaba taje ta hau katifar amma taki xuwa kusa dashi'shima be damesa ba sbd a lokacin bcc yariga yaci karfinsa.

"Haka Zahra tai ta juyi tana hawaye cikin idon bcc idan uncle yaji alamar motsi sae dae yasa hannu ya lalubota hada da kiran sunanta.

"Itama tana gani haka sae ta daena juyin da takeyi idan taga ta koma bcc sae taci gaba' da haka har 2AM yai labour zanga zanga sauka tai daga kan katifar takoma kasa sae faman yawo a daki takeyi tana kuka.

"Kamar a mafarki uncle yakeji kukanta a gigice ya falka ganinta da yai hakan yasashi tashi da sauri yaxo inda take ya dafe mata kafada hade da tambayar lfy?".

"Kuka kawai Zahra keyi takasa mgn taci gaba da zagaye dakin gani haka bude kofa yai yaje ya kira mm
[7/17, 10:45] Washa: πŸ’ŽπŸ’¦πŸ’Ž
πŸ’




GARKUWATA
(RELIANCE)



FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.πŸ’



πŸ’ŽMMN USWANπŸ’Ž




DIDECATED TO SIS MARDIYA KA'OJE.



39




"Mm tana xuwa a bakin kofa ta tsaya tace ya kamo innawuro tafito to kawai uncle yace hade da shiga dakin yace Zahra ta fito inji mm.

"Ka kawai Zahra ta kada masa alamar aa dan bazata iya ba' uncle yace kodae na rike kine?" Shiru Zahra tai tana share hawaye dake xuba daga idon ta.

"Komawa uncle yai yasanarwa mm bazata iya fita ba' da kar mm ta shiga dakin gani halin da innawuro take tasan labour ne takeyi kamata tai tace ta tsuguna Zahra tace bazata iya ba.

"Da taga hakan sae tace uncle ya kama mata ita dakar datamu Zahra ta tsuguna snn tace uncle yafita a dakin.

"Komawa parlour yai ya zauna amma bini bini saeya leka da haka sukai tayi har asuba ana kiran sallah Zahra ta haihu baby girl uncle yanajin kukan baby da sauri ya mike yaxo ta cikin labule yake lekawa duk da haka Zahra na duke bata tashi ba sbd mahaifa bata biyo ba.

"Uwa tana fadowa mm tace ta hau kujera ta zauna itama kici taje tasa ruwan xafi snn taxo ta dauki baby ta dorata akan katifa ruwa yana xafi uncle ne juye masu yakai masu toilet mm tace Zahra tashiga ta dauraye jikinta ita kuma taiwa baby wanka.

"Da safe uncle ya bugawa Habib ya sanar masa haihuwa da bba Habu duk sukai masa barka' matar bb Habu taxo da matar Habib sukai masu barka matar bba Habu ne kewa Zahra wanka da baby snn taje gida haka tai ta zawaro har suna kullum idan tazo bata komawa gida sae yamma.

"Kwana uku da haihuwa uncle yaje ya sanarwa kawu ibram da maryama ranar suna yarinya taci sunan mm maimunatu duk da ba wani dadewa yai a garin ba amma saeda yan'gun aikinsa sukazo sosae hakan yasa suka bawa Sumayya aikin abinci na daban uncle yayi kokari sosae a gun shidimar suna babu laifi saedae makiyi itama Zahra kudi ya bawa Sumayya yace ta siyewa Zahra kayan fitar suna masu kyau ita kuma ta siye mata kala uku atamfa da shadda sae lace akae mata dikuna masu kyau daedae jikinta harda iyayen Habib sukazo suna.

"Maryama tayi kokarin sosae wajan aiki.

"Washe garin suna uncle ya dauki Zahra da baby sukaje asibiti gani doctor bayan doctor ya dubata yace babu kowani matsala maguguna kawai ya rubuta masu na Karin jini da kuma wanda zaisata cin abinci sosae snn kuma yace suje gu nurses din dake gefe za'a yiwa baby immunization.

"Uncle yace to.

"Maryama na rungume da mamy sukaje akai masu koma snn suka dawo gida.

"Bayan sun dawone tace uncle ya rakata zataje duba result dinta sae uncle yace tunda hakane nima bari na dauki na Zahra na duba mata nata haka ya dauki scratch card din Zahra sukaje gani result din yayi kyau yace ai masa printing out maryama tasamu 8 credit ita kuma Zahra tasamu 7 amma duk sunada maths English civil government chemistry etc

"A hanyar dawowa ne uncle yake tambayar maryama tunda result din yayi kyau yanxu me zatayi?" Maryama tace ita yanxu school of nurse takeso na cikin garin nan, uncle yace amma kinsan da tsada ko?".

"Maryama tace babu damuwa bbnta yace ko nawane nan zai biya mata' ita yanxu matsalar ta batasan wani a nan ba banle ya tsaya mata hakan ne ma yasa bata damu da taxo duba result din ba inba yanxu da yayi hanya ba.

"Uncle yace akan maranta ko akan inda zaki zauna?" Maryama tace dukka. Sae uncle yace babu damuwa idan gun zama ne ga gidana sae muzauna tare mgnr makaranta kuma akwai wanda zanmasa mgn sae yai maki hanya.

"Maryama tai murna sosae hade da godiya snn tace to uncle tunda hakane me zaihana kasa Zahra itama.

"Murmushi kawai hade da cewa maryama kenan kinfasan a gidan haya muke kuma gashi shekara yanxu babu wiya ya zagayo hakan yasa bansa komai a gidan ba nafiso idan na tara kudina na siye koda ciki biyu ne duk abinda za'ayi sae ayi.

"Maryama tace hakane uncle amma in Allah ya yarda bazai gagara ba' murmushi yai snn yace to maryama idan Zahra tafara xuwa makarantar yayi za'ai min da mmna.

"Dariya maryama tai hade da cewa baga mm ba.

"Shima dariya yai snn yace wato dae kin nunamin kinfi son kawarki akan mamy na kenan.

"Duk sukasa dariya uncle yace to bari maga yadda za'ayi.

"Maryama tace Allah ya gano mana alkairi.

"Haidayr yace amin.

"Da haka har suka isa gida' da yamma lokacin uncle yana dakin mm ita kuma maryama tana dakin Zahra shine maryama take fadiwa Zahra yadda sukai da uncle.

"Zahra tai murna sosae.

"Da uncle yaje aiki shine yakewa Habib mgnr yanaso ya samarwa Zahra da maryama school of nurse.

"Habib yace idan wann ne baza'a samu Matsala ba sbd yayan mmnshi ta hannunsa akebi idan za'a amshi addmision'. Haidayr yace yanxu ya kake gani za'ayi?".

"Habib yace bari na kirasa muji.

"Yana kiransa bayan sun gaisa yai masa bayani sae yace babu damuwa amma yanxu suje su siye form su cika sbd ankasa rufe siyar da form din idan yaso zaiga abinda zaiyi.

"Nan sukai masa godiya sukai sallama.

"Da uncle ya koma gida yaiwa maryama bayani tace to akwai wasu kudi taxo dashi amma bata saniba ko zaikai tasiye form din.

"Uncle yace tabar kudinta shi zai siye mata.

"Bata musaba sae dae godiya da tai masa' uncle yace abinda ya kamata tai taje gida ta sanar bb suma Susan abinda ake ciki.

"Maryama tace to Zahra nada sat biyu da haihuwa maryama ta koma gida sae da uncle ya kaita tasha snn ya karisa gun aiki.

"Yana shiga office dinshi ya tarar da wani cause ankawo wasu criminal wasu barayi suka shiga gidan wani alhji sukai wa matarsa fyade snn kuma sukayi fashi.

"Nan uncle yasa ayi masa binciken inda suke zaune.

"Bayan Zahra tai arba'in tafara sallah koda ya dawo daga aiki ganinta yai tana sallah a daki mamy kuma tana kwance akan katifa tana wani zama yai a bakin katifa ya dauki mamy yana mata wasa.

"Bayan Zahra tai sallama ne tai masa snn da dawowa yace yauwa snn da gida mikewa tai taje ta hada masa suwan wanka snn taxo ta amshi mamy.

"Ta mika hannu kenan zata amshi mamy uncle ya jawota jikinshi kadan yarage ta fadi a jikin mamy da sauri uncle ya kaudata gefe snn ya haye kan Zahra suna kallon juna ido cikin ido yana cewa dama kinfara sallah shine bansani ba kodae rowa kikeso kinmin eye Zahra.

"Uncle yana mgnr ne yana hura mata cikin kwayar idonta' Zahra najin gabansa ta mike da sauri ta igijeshi ta dauki mamy ta rungume tashi yai shima ya dawo kusa da'ita duk mgnr da yai mata banxa dashi tai.

"Da yaga haka tashi yai yaje ya tube yashiga wanka bayan ya fita daga wanka ta kawo masa abinci yaci snn ya amshi mamy sukaje dakin mm hira.

"Suna shiga itama mm amsarta tai tana fadi maikama da bbnta' dariya uncle yai snn yace mm dakefa tai kama.

"Ciki wasa mm tace aa kaidae fadi gaskiyarka na daure duk wanda yasanka kuma yaga maimunatu basae yai tambaya ba.

"Cikin dariya uncle yace nidae nafi gani kamanniku.

"Mm tace haba dae yaro nafa rigaka shan iskan duniya.

"Dariya uncle yai suna cikin hira ne mamy tasa kuka mm ta aikata gun bbnta ' shima da yai lalashin yaga bata

Please Login or Register in order to submit comment