Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake kira a karo na uku nan ma shiru. Ga dai fuskar ta d'auke da murmushi Kamar ka kirata ta amsa.

Hannunta ya rike, take yaga ta saki, gaban sa ya fadi, sake rike dayan hannun yayi yaga ta kuma saki, hannunsa ya d'ora a k'irjinta yaga bata bugawa.

"_innalillahi wa innah ilaihi raju'un, mahmah!!!_" yace cikin karaji yana jijjjiga ta, sai dai shiru bata ko motsa ba, sam k'wak'walwa hadi da zuciyar sa taki yarda da abinda take gaya masa, hakan yasa shi daukar ta zuwa asibiti domin a duba ta.



Cikin tashin hankali ya shigo asibitin, Mahmah dauke a kafadar sa yana kuka sosai, daidai lokacin doctor Gabriel ke k'ok'arin shiga motar sa domin aikin dare yayi jiya yana son tafiya gida, kallon daya yayi wa fadeel, take yaga Mahmah a kafadar sa, gabansa ne ya fadi, fasa shiga motar yayi ya nufi wajen Fadeel kana ya kwala wa wasu nurses kira, aka dora Mahmah cikin gadon nan na asibiti aka turo ta cikin sauri zuwa emergency...





Hannu Fadeel doctor Gabriel ya kamo zuwa office d'insa yace ya zauna yana zuwa,
Kana Cikin sauri doctor Gabriel ya nufi dakin da aka shigar da Mahmah...
Nan ya shiga dubata cikin kwarewa, sai dai ina rai yayi halin sa, Mahmah is gone forever, Mahmah ta tafi, tafiya ta har abada.

_kullin nafsin za'ikatul maut_ (dukkan mai rai sai ya dandani zafin mutuwa) domin babu alamun numfashi a tare da ita.



Kansa ya dafa, yace "Jesus Christ! is innocent woman is dead!!!" Sosai kuwa yaji mutuwar ta, duk da kasancewar sa ba Musulmi ba, amma yaji wani tsoran Allah na shigar sa.



A sanyaye ya koma office d'insa ya tarar da Fadeel zaune abin tausayi, zama yayi yana kallon Fadeel cikin tausayawa, duk da bai taba ganin sa ba sai yau, amma suna yanayin kama da Mahmah ya aiyana aransa afili kuwa hannu Fadeel ya riko yace "my friend sai haku'ri domin...."
Ai kafin ya karasa Fadeel ya katse shi da cewa "don't tell that my Mahmah is dead doctor, because I will squeeze your Bone's like an Orange (kada ka kuskura kace Mahmah nah ta mutu, domin zan ma_matse kasusuwanka tamkar na lemon bawo" Fadeel yace cikin fitar hayyaci kana cikin kuka har wani shidewa yake.


Girgiza kai doctor yayi cikin tausayawa yace "the truth is that..." sai ya dan shiru kana ya cigaba "your mother is dead!"



Afirgice Fadeel ya mik'e yana kokarin furta wata kalma, amma ina sai ya tafi luuuuuuu sakamakon wani irin jiri daya debe shi, take ya fadi tsumamme....


Cikin wani sabon tashin hankali doctor ya dauke shi zuwa emergency aka fara bashi taimako gaggawa...


Bayan yayi masa komai harda alluran bacci sai da ya nufi office din doctor Mahfouz, sai dai sam baya nan.
Fita ya sake yi ya nufi dakin da aka kwantar da Fadeelah, gaba d'aya ta sake fita kamanin ta, maganar Daddy yaji yana cewa cikin kuka "doctor tayaya zaka ce idan ba a samu *koda* nan da minti talatin ba zan rasa 'yata, bazan juri kallon 'yata ta mutu ba, ka cire duka nawa kodar ka sa mata, banda wata 'ya sai ita Mahfouz!"

"Professor sai hakuri fa, kalli abinda na'uran ke fada, nayi iya k'ok'ari na..." Suna cikin wanna halin, kirjin Fadeelah ya fara sama da kasa har wani jijjiga gadon yake. Yayinda na'uran ya tsawaita kara...


Cikin saurayi doctor Gabriel dake tsaye yace "an samu kodar, a shirya shiga da ita aiki yanzu"


Gaba daya suka juyo gare shi, take murmushi ya wad'atu kan fuskokinsu, tsabanin dazu da wasu ke kuka wasu na cikin damuwa, domin Mommah har bata iya bud'e idanun ta saboda zafi ".



Wani kallo da doctor Gabriel yayi wa doctor Mahfouz take ya fuskanci Mahmah ta mutu, duk da yaji dadi Fadeelah zata rayu, amma yaji mutuwar Mahmah matuka.


Babu bata lokaci aka shigar da Fadeelah aiki, cikin gaggawa domin mintunan daya rage mata sauran kadan.


Bangaren doctor Gabriel kuwa, bayan an cire kodar Mahmah, ya nemo wasu dattijai mata da maza wadanda suka yi zurfi a ilimin addini, suka nufi gidan Mahmah, yayinda gawar mahmah ke cikin ambulance din asibitin.
Domin ayi mata wanka, duk da kasancewar shi ba muslumi ba amma, yasan duk wani muslumi idan ya mutu ba a son ajiye shi, an fi so ayi gaggawar kai shi gidan sa na gaskiya. Wanna kadai zai iya yiwa Mahmah, tunda danta yana gadon asibiti a kwance.

Kasancewar lokacin da Mahmah ke zuwa asibiti, adreshin gidan ta na rubuce a file dinta hakan yasa bai sha wahalar gano gidan ba.


Babu bata lokaci aka shigar da ita ciki, take yan unguwar suka fara shiga gidan musamman da suka ji jiniyar motar asibiti.

Bayan anyi wa Mahmah wanka an shirya ta cikin liƙƙafani kana aka fito da ita hadi da yi mata sallah, duka doctor Gabriel na cikin motar sa, wani tsoron Allah na shigar sa, yayinda hirar da suka yi da Mahmah ya shiga dawo masa a fili ya furta " hakika madam kinyi Sadaukarwa mai girman gaske". Sai ga Hawaye a idanun sa.


Bayan an dawo daga kai ta mutanen da suka hallaci jana'izar ta suna da yawan gaske, sai dai fatan mu ce Allah ya jikan ta.

Doctor Gabriel ya bawa dattijan nan daya samo kudi masu yawa, suka ki karba, domin suma imani da tsoron Allah ya kara shigar su.

Amma mamakin take yaji addinin musulunci ya burge shi sosai.
Inda mutanen ke zaman makokin ya nufa, take yace yana son shiga musulunci, kabbara mutanen wurin suka sa, yayinda limamun unguwar tasu ya musuluntar da doctor Gabriel, aka ce wani suna yake so a sanja masa take yace *Aleeyu haidar* domin a sunan muslimai yana kaunar sunan sosai...


Take doctor Gabriel yaji kamar an yaye masa wani zunzurutun nauyi akansa, wani yanayi mai dadi kana marar mitsaltuwa na shigar sa, nan liman ya kara wayar da kan shi game da addini musulunci ya kuma ce masa dole ya nemi islamiyya na manya domin ya kara sanin menene addini musulunci. Take ya amsa da in sha Allah domin ko liman bai fada ba, yana da niyyar hakan, domin shi mutum ne mai riko da addini, ko da a lokacin da yake cikin addinin su na kirista ne(Christian), haka zalika yanzu ma daya shiga addinin muslunci, addini mai haske, zai dage da ibada.



Haka yayi sallama dasu ya tafi cikin yanayi mai dadi da yake jin kansa a ciki, duk da murnan sa ragagge ne, saboda mutuwar Mahmah.


Asibiti ya koma domin yana son kula da Fadeel, hakika bai cancanci a bar shi ba kowa tare da shi ba...



*_(Kusani cewa, a rayuwa wani kaddara baya samuwa sai da wata kaddaran, toh hakan ke faruwa a novel din kyautar koda ku dai cigaba da bin alkalamina...)_*




_Yau nayi typing mai yawa, billahi banga comment dinku na k'ok'arin tarwatsa waya ta ba, zan dauki hutu😹 ina jiran ra'ayinku akan page din yau, Mahmah is dead_.😫





#share
#comment
#vote



Noor Eemaan loves you all my beautiful fans

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


#Nurrr


🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(it's all about love, scracife, hatred and destiny)


Story/written by
NoorEemaan
07082281566




https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


*Wattpad*
@NoorEemaan







EDITING IS NOT ALLOWED❌


*(Assalama alaykum my lovely fans, nasan wasun ku baku ji dadi da Mahmah ta mutu ba, domin wasu sun gaya min, wasu ma sun ce sai da suka zub da hawaye, ni Noor a lokacin da nake typing wajen sai dana yi kuka domin wajen is very heart touching I know. Amma littafi na riga ma tsara shi, rubutuwa ya rage min kawai, domin haka labarin yake, soyayya ce, sadaukarwa, tsana/kiyayye hadi da kaddara. A rayuwa ba a taba samun farinciki kullum, haka ke faruwa a *kyautar koda*.
*Da sannu zaku fahimci darassin dake cikin labarin, ina godiya sosai da add'uar ku gareni hadi da comments dinku masu sugar*😹
*Allah ya bar kauna da zumunci*)
Noor Eemaan loves you all❤️



Page 25-26

(Not edited)

Kwanan Fadeel hudu a gadon asibiti ya farka da sunan Mahmah ɗauƙe a bakinsa, yayinda idanunsa ke a rufe.


doctor Aleeyu(Gabriel) dake tsaye yana kokarin cire masa karin ruwa yayi saurin dawowa gaban gadon yana fadin "sannu ka tashi?"


A hankali fara bud'e idanunsa, saurin mayarwa yayi ya rufe sakamakon wani haske d'aya cika idanun sa... Ya d'auki mintuna goma kana ya fara ware idanun sa a hankali ya sauke su kan doctor Aleeyu...


Take k'wak'walwarsa ta tariyo masa komai, wani ihu ya saki kana ya fara buga kansa da karfen gadon yana fadin "Mahmah don't do this to me, please Mahmah ki dawo gareni, banda kawo sai ke, ki dawo please, doctor kace Mahmah na ta dawo gareniiiiiiiii" ya ja Kalmar karshen gwanin tausayi.


Cikin sauri doctor Aleeyu ya rike shi hadi rungume shi yana bubbuga bayansa alamun rarrashi...
"Shikenan Mahmah ta mutu, shikenan Mahmah ta mutu, shikenan bani da uwa a duniya likita? "

Haka ya dinga maimaitawa yana kuka sosai gwanin tausayi. Doctor ya dauki tsawon lokaci yana rarrashin Fadeel kana yace masa ya yi sallah dake kansa domin yau kwanan sa hudu a kwance.




Ba musu ya miki, sai dai ya kasa tsayuwa kan kafafunsa Saboda rashin kwarin jiki hakan yasa doctor Aleeyu taimaka masa har zuwa toilet.

Bayan duk ya iddar da sallar dake kanshi ya shiga yiwa mahaifiyar sa add'ua, yana kuka sosai, shima doctor Aleeyu sai ya kama kuka domin duk wanda ya kalli Fadeel dole ya tausaya masa.

Hankici(handkerchief) doctor Aleeyu yasa ya share hawayen fuskar sa, kana a fili yace "abokina kayi hakuri, tabbas mutuwa na da daci musamman ga wanda aka yi wa, nima da kake ganina banda uwa banda uba a duniya, duk sun mutu kuma a rana d'aya sak'amak'on hatsarin da suka yi. Hakika ban taba ganin mutum mai kyawun zuciya hadi da tawakkali da yarda da kaddara Kamar mahaifiyar ka ba, hakan ya janyo hankalina na shiga musulunci a ranar da ta rasu..."

Fadeel ya dago jajayen idanunsa ya kalli doctor Aleeyu, jinjina masa kai doctor'n yayi alamun "Haka ne"

tabbas idan yace bai ji dadin cewa wani ya shiga musulunci ta silar Mahmah ba yayi karya, sai dai bazai iya nuna jin dadin sa a fili ba Saboda matsanancin damuwar da yake ciki



A hankali ya budi baki yace "dan girman Allah doctor ka gaya min wani irin cuta ke damun Mahmah tsawon shekarun nan bata taba gayamin ba" Fadeel ya kai karshe yana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya gwanin tausayi.



Furzar da iska doctor yayi daga bakinsa kana yace " hakika mahaifiyar ka bata son ka san da cutar ta , kuma duka Saboda kada hankalin ka ya tashi ta boye maka, a yanzu dai babu bukatar boye maka"

Numfashi ya sauke kana ya cigaba "mahaifiyar ka na dauke da *cutar daji ta makwogwaro* (lung's cancer) tsahon shekaru kenan, a lokacin data fara zuwa asibitin nan cutar ya fara cin karfin ta. Sai dai ba kudin yi mata aiki a lokacin domin kudin aikin ya kai million biyu da rabi. Rashin kudin aiki yasa cutar ta ci karfin ta sosai......" nan dai ya cigaba da bawa Fadeel labarin abinda ya sani gami da cutar Mahmah, hadi da Sadaukar da *kodar ta* da ta yi.




Babu Abinda ke fita a idanun Fadeel sai hawaye masu zafin gaske, dama haka mahaifiyar sa ta sha wahalar rayuwa? Haka ta boye masa ciwo duk don farincikin sa? Ta Sadaukar da kodar ta just because ya zama cikin farinciki, ya rayu da abar son sa fadeelah.

Kuka ya ci sosai, har ya fara ganin biyu_biyu sakamakon wani mugun ciwon kai da ya saukar masa, jajaye kuma kumburarrun idanun sa ya dago ya kalli doctor yace "please wani kabari aka binne Mahmah na? Ina son zuwa, ina son yi mata add'ua, ina son zuwa please doctor!!!!" Ya kai karshe cikin wani kukan daya ci karfin sa.



Wasu hawaye doctor Aleeyu ya share na zallan tausayin Fadeel. Cikin dauriya yace " a gaskiya bansan wani makabarta bane, kasancewar lokacin ban karbi musulunci ba, hakan yasa ban bisu ba, amma bari na kira wani a nan asibiti yake aiki tare suka je" ya fada yana kara wayar sa a kunne.....



Babu jimawa matashin yaron yazo, ya fadi sunan makabartan da unguwar da yake, ya kuma ce zai iya raka Fadeel d'in.

Da kyar fadeel ya budi baki yace "nagode zan iya zuwa da kaina"


Ba musu matashin ya koma bakin aikinsa, Mikewa Fadeel yayi da kyar yace "thank you doctor for everything" kana yana hada hanya, haka ya fita daga asibitin a haukace.... Doctor Aleeyu (Gabriel) nayi masa magana kan cewa zan iya tafiya kuwa? amma ina yayi nisa bazai ji kira ba....




Tafiya yake cikin makabartan tamkar wanda yake kirga kasa dake shimfud'e a kasan wajen, hawaye ke zuba a idanunsa, wani tsoron Allah hadi da imani na kara shigar sa, wanda ya sanya kofofin gargasan jikinsa bu-budewa yanayin daya sanya wani sanyi sanyi ke shiga jikinsa. Aransa yake aiyana cewa shima wata rana haka zai kasance anan, haka zai tafi, tafiya ta har abada, kamar yadda Mahmah ta tafi ta barshi.





Tun daga nesa ya hango signboard mai d'auke da sunan Mahmah. Gaban kabarin ya tsugunna, wanda aka mulmule da siminti dake da sauran sabonta har yanzu, domin duk wanda ya gani zai san cewa mamacin bai dade ba.

Wani kuka ne ya taho masa mai karfin gaske daya kasa rike shi, sosai yake kukan mai taba zuciya, kana ya rarrashi kansa tuna cewa ba a son ayi wa mamaci kuka.

A fili ya fara furta cewa "Mahmah you re gone, gone forever, kin tafi kin barni, ki tafi kin barni a wanna duniya mai cike da kalubale, kin tafi kin barni bana da sauran kowa daya rage min" . ajiyar zuciya ya sauke tamkar yaron goyon daya ci kuka ya koshi kana ya cigaba " ina sonki Mahmah, ina matuk'ar kaunar ki, your son fadeel loves you.
Ina fatan kina cikin farinciki da salama a yanzu, har abada kina cikin k'irjina da dukkanin wani sassa na jikina, kin yi Sadaukarwa mai girman gaske saboda farincikina, ina kaunar ki uwar da babu tamkar ki a duniya, Allah ya jikan ki Mahmah nah..." Nan ya shiga yi mata add'uo'i kana yaja wata alama da wani dan karfe daya gani a kasa, kan siminti, domin iska zai iya d'auke signboard din. Wanna alamar daya zana zai taimaka masa wurin gane kabarin Mahmah....


Mikewa yayi ya nufi gida. Sosai gidan yayi masa girma da fadi ainun, haka ya kudundine kan yar katifar mahmah matsanancin kewar ta na ratsa zuciya da jinin jikinsa......



*** *** ***


*BAYAN WATANIN BIYAR*


A haka rayuwa ke tafiya. Kwanaki na juyewa zuwa satittika, satittika na juyewa izuwa watanni, haka zalika watannin na juyewa izuwa shekara.

Yanzu babu laifi Fadeel ya dau dangana, tun ranar daya bar makabartan nan baya zuwa ko ina daga masallaci sai gida, haka zalika baya iya cin komai daga ya tafasa ruwan black tea (bunu) shikenan, shi ma sai ya ji Cikin sa na kugin yunwa zai sha, gaba daya ya dawo wani mara son hayaniya ko magana baya son yi, kuma har yanzu bai san a wani hali Fadeelah ke ciki ba, duk da sonta na nan daram a ransa...


A yau yayi tunanin gyara gidan, domin tunda Mahmah ta rasu gidan bai ga tsintsiya ba. Tsakar gida, da toilet ya gyara, kana ya nufi dakinsa ya fara gyarawa, bayan ya gama ya dawo dakin mahmah ya gyara mata tsaf, jakar kayanta dake a hargitse ya nufa da niyyar gyarawa wasu takardu suka fado.....


Rubutun Mahmah ya fara tozali dashi, sai wasu takardun asibitin. Ajiye takardun asibitin yayi a gefe, ya dauki na rubutun nata ya fara karantawa Kamar haka:

_my lovely son Fadeel_


_ina fatan kana cikin koshin lafiya, nasan bayan raina zaka ji komai. Ina fatan zaka yafe wa Mahmah'n ka a dalilin boye maka ciwon da nake fama dashi tsahon shekaru, na boye maka ne saboda bana son ka kasance cikin damuwa. Ina fatan dana abin sona baya fushi da Mahmah'n sa?_

Share hawaye yayi kana cikin muryar kuka yace "bana fushi dake mahmah bazan taba fushi dake ba, ina son ki sosai Mahmah na" kara share hawayen yayi, sai dai wani na koran wani, hakan yasa ya cigaba da karantawa bai damu da zubar hawayen ba.


_na hana ka bayar da kodar ka wa yata Fadeelah ba dan komai ba, sai dai ku rayu cikin lafiya da farinciki. Shin idan ban Sadaukar da koda ta ga abar son dana ba wa zai Sadaukarwa mata? Ka sani cewa ina cikin farinciki a lokacin da na bayar da koda ta ga fadeelah. Ina yi muku so mai yawan gaske. Kada ka karaya kan soyaayyar fadeelah ya kai jarumin dana, ka jajirce da dukkanin iyawarka har ta zama mallakin ka, nasan ku biyun zaku zamo the best couple ever da za a yi alfahari da ku a duniya... Ka kasance cikin farinciki dana, ka kula da fadeelah, ku kula da junan ku, ina farinciki da taraiyyar ku, sannan ina muku fatan alkhairi, ka gaida min yan jikokina idan sun zo in sha Allahu. Ina kaunar ka Fadeel, Mahmah loves you, fatan alkhairi._



Kurawa takardan ido yayi hawaye masu dumin gaske na sake zubo masa, shafa wani sashe na rubutun yayi, da ya dan yi jurwaye wanda da alama hawayen Mahmah ne ya diga kan takardan a lokacin da take rubutun..




Kan kayan Mahmah dake hargitse ya dora kansa, lumshe idanun sa yayi hadi da kamkame takardan a k'irjinsa, waka ya fara rera mata kamar haka:



🎻🎻_wanna naki ne Mahmah_.....

_Rayuwa nayi nazari duk wanda ya zamto a raye, wata ran sai ya rasu ko yana so ko zai zubda hawaye. Duniya ba wajen zama ne ba, aro aka bamu ba jaye-jaye, mu rike Allah gwani mafita ne ga mazon na fiyayyye_.......


_Rayuwa ta sai a hankali, na rashin mahaifiyata. Na zama kamar banda hankali ku dubeni bani da gata. Hakuri ya zama faralli ya Allah jikan mahaifiyata_....


_wayyo! wayyo!! Ya Allah jikan mahaifiyata. Innalillahi wa innah ilaihi raju'un, Allah ya jikan ki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi_...........

_innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah ya jikan ki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi_......

_Allah nagode. Kullin nafsi za'ikatul mautu, duk mai rai tilas ne ya mutu . Sai dai ni du'a'in neman hutu Allah ya yafe mata_........

_kuka ka daina ka share hawaye abokina. Dani da kai zata zo kanmu watan wata rana, ka zo mu roki Allah, in muyi sallah nasan zaya kalla ya Allah! Mutuwa nazan tana da zafi, hakuri dazaka yi shi ya fi. Wanda ya mutu bazai dawo ba, add'ua zamuyi shi zaya je gareta....ya Allah!_

_innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah ya ji kanki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi. Wayyo! Mahmah, wayyo!! Mahmah, wayyo!!! Mahmah nah, wayyo Mahmah nah, wayyo Mahmah nah_....

_duk abinda nakeso cikin duniyar nan Mahmah tana bani, yanzu bata nan na lalace dare da rana kullum tunani. Burin rayuwa in zauna da mahaifiya dan ita ce garkuwa mai share duka damuwa. Wayyo! Mahmah, wayyo!! Mahmah, wayyo!!! mahmah nah, wayyo Mahmah nah!!!! Innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah ya jikan ki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi_.......🎻🎻

Haka ya gama wakar hawaye masu zafi na zubo masa, suna bin gefen da gefen fuskar sa suna shiga kunnuwan sa, dumin na ratsa kwanyar sa.
Da haka wani wahalallan bacci ya yi gaba dashi...




Bai jima da yin baccin ba, motocin fadeelah da body guard dinta suka tsaya kofar gidan.
Kofa aka bud'e mata ta fita kana ta shiga cikin gidan bakin ta dauke da sallama... Sai dai shiru babu amsa, hakan yasa ta nufi cikin dakin da ta gani a bud'e.....




#Share fisabilillah
#comment
#Vote




Please Vote and follow me on wattpad @NoorEemaan



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

🍇🍇KYAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, sacrifice, hatred and destiny)


_by Noor Eemaan_📚✍️



*Wattpad*
@NoorEemaan







EDITING IS NOT ALLOWED❌



*(Please&please kuyi following nawa a Wattpad👏 @NoorEemaan)*




Page 27-28


(Not edited)

Dai-dai 6akin ƙofar ɗakin ta tsaya, ta sake sallama cikin zazzak'ar muryarta. Amma shiru, hakan yasa ta leƙo da ƙanta cikin dakin.

A ƙwance ta hango fadeel, ya rame sosai ya sake yin ɗuhu, cikin sauri ta cire tsaɗaɗɗen takalmin kafarta na company *GUCCI* ta shige dakin.

Gabansa ta tsugunna da nufin tashin sa, sai ta tsaya caƙ! saƙamaƙon ganin takarda rungume a ƙirjinsa. A Hankali ta kai hannu ta zari taƙardan, haka kawai taji zuciyar ta na azalzalarta ta karanta ko ganin abin cikin taƙardan.



Mikar da takardan tayi sak'amak'on dan cuƙurƙuɗewan da yayi ta fara karantawa...... Tun kafin tayi nisa da karatun ta fara hawaye tamkar an balle famfo. Sai da ta zo karshen karatun ta kasa rike kukan da ya kufce mata, dama Mahmah ce ta Sadaukarwa mata da *kodar ta?* Saboda su kasancewa a raye cikin farinciki? Kaunar da Mahmah ke mata ko tace take musu ya kai haka? Meyasa doctor Mahfouz bai sanar mata? Surutai ta dinga yi a ranta, yayinda kukan ta ke karuwa domin abin ya taba zuciyar ta matuka.



A hankali Fadeel ya Fara bud'e jajaye kuma ƙumɓurarrun idanun sa sakamakon kukan ta da ya ji ya sauke su kanta, Kallonta yayi na yan mintuna ya maida idanunsa ya lumshe.....


Bakinta ne ya fara rawa, so take ta furta masa wata kalma ta kasa, kallon sa take yayinda zuciyar ta ke kara karyewa. Ya dawo kamar bashi ba, ya fita a kamanin sa ainun. Gashi yaki kulata, sai dai hakan bai mata ciwo ba, domin mutuwar uwa ba karamar abu bane...



Cikin sauri ta bar gidan ta fada mota hadi da bawa driver umarnin ya kaita asibiti. sanin cewa asibiti daya take zuwa ya sa shi cewa "yes ma'am" Cikin sauri hadi da girmamawa. Haka motocin suka bar unguwar a jare kamar ko yaushe.



Bangaren fadeel kuwa, yana jin fitar ta ya bude idanunsa ya bi kofar da ta fita da kallo. Wasu hawaye masu dumi suka biyo kuncin sa, idan yace bai yi kewar ta ba yayi karya, amma baya son kowa ya rabe shi a halin da yake ciki, yana bukatar privacy, yes yana bukatar kebancewa.



A hankali ya mike ya dauko kayan zanen sa, ya fara zana Mahmah kana ya zana fadeelah cikin mintuna ashirin. Hotunan biyun ya ajiye kan cinyoyin sa bayan ya gama zanen, ya kafe su da ido hawaye na zuba daga idanunsa, daya kalli zanen mahmah sai ya fashe da kuka, idan kuma ya kalli zanen fadeelah sai ya sa dariya, haka ya dauki tsawon lokaci yana yi tamkar wani mai tabin k'wak'walwa.
Hakika yana farincikin Fadeelah ta rayu, yana kuncin Mahmah ta mutu.



***

Tun cikin mota ta kira doctor Mahfouz ta sanar dashi tana tafe. Bayan isar su asibitin direct office d'insa ta nufa. Ta kuwa tarar dashi a ciki. Bata tsaya bata lokaci ba ta fara jero masa tambayoyi...

Doctor Mahfouz bai yi kasa a guiwa ba ya shiga sanar mata da komai da komai. Har wani sama _sama numfashin ta keyi saboda kukan da take. Cikin kukan tace "doctor meyasa ka boye min? Ka boye mana? da ban samu wasikar nan na karanta ba ta ya ya zan sani? I know fadeel won't tell me, Kwanan Mahmah nawa da mutuwa?" Duk ta jiro masa tambayoyi cikin matsanancin damuwa da mamakin irin tarin kaunar da Mahmah ke mata, domin sam abin yaki bace wa a zuciyar ta.



Ajiyar zuciya doctor Mahfouz ya sauke kana yace "yau watanta biyar da rasuwa. Wato Fadeelah ni kaina abin yayi matukar taba ni, a lokacin da aka rasa wanda zai siyar miki da kodar sa hankali na ya tashi sosai, a ranar da matan nan(mahmah)

Please Login or Register in order to submit comment