Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kasa gane kan shi, cikin rashin fahimta tace" menene ba zai yu ba?"



Bai yi magana ba, ya mike rike da takardan a hannunsa ya shiga taka step biyu² har uku³ ma.



Da kallo ta bishi cikin mamakin wanna sabon sanjin nasa na damun ta, a hankali ta mike cikin mutuwar jiki ta bi bayan sa, sai dai a rufe kofar yake, wanda sai da hannun sa ne zai bud'e kasancewar sa mai thumbprint ne.



Tana iya hango shi kwance yayi ruf da ciki ta kofar glass din, tayi² ya bud'e yaki.


A sanyaye ta koma part din ta, wanda tamkar gini guda ne saboda girman sa, komai na buk'atar rayuwa akwai aciki, daya daga cikin bedroom din part din ta shiga nan ta tarar da akwatunan ta a jere, bathroom ta shiga tayi wanka, kana ta fito, ta sanya wani simple tsad'add'en material onion color, ta d'aura dankwali , ko mai bata shafa ba, Saboda bata da kuzarin hakan, still kyaun ta ya fito.



Zama tayi ta zurfafa tunanin ta, amma ta kasa fahimtar inda kalaman sa suka dosa, haƙa zaliƙa ɗamuwar sa..



Har dare bai fito ba, tayi kukan har ta koshi, ɗomin ko bud'e idanunta ta kasa yi, bangaren Fadeel kuwa sallah kadai ke tayar dashi, sosai ya shiga matsanancin damuwa, wanda har ya rasatunanin yi, , burinsa yanzu ya samu mafita ɗamuwar ɗaƴa afƙo masa.



Sai karfe 9 na dare ya farga da Fadeelah'n shi, a zabure ya mike, ko ina na part din ɗa yake ya duba bata nan, cikin sauri ya nufi part din ta, ya tarar da ita kwance hannunta dafe da cikinta.

Cikin sauri, kana da damuwa a fusk'ar sa yace "wiffy?"



A hankali ta yi kokarin bud'e idanun ta, saurin mayar wa tayi ta rufe sakamakon yajin ɗata ji yana mata, tamkar yar baby ya daga ta cak! kana ya zauna a kujeran da take tana k'irjin sa, cikin muryan galabaita tace "sauke ni! Ka sauke ni!! Ni wajen Mommah zan koma, me ye amfanin tarrayan mu matuk'ar zaka dinga boye min damuwar ka? Na dauka damuwar ka tawa ce, ashe ba haka bane?" Ta fada tana kokarin sauka, amma ta kasa domin babu k'arfi a jikinta, haka zalika shima, kawai dai jarumta ce irin tasa, Saboda dukkanin su babu wanɗa yasha koda ruwa ne tun safe.




Cikin damuwa yace "yanzu fadeelah zaki iya rabuwa da ni? zaki iya tafiya ki barni? Bayan kin san banda kowa sai ke? Ke ce hasken idaniyata, kece mai bani farinciki, please kar min haka" ya karasa yana sauke numfashi.



Sosai ƙalaman sa suƙa karƴa mata zuciƴa Amma ta maze, cikin dakiya da barazana tace "eh! Idan baka fadamin silar wanna damuwar taka ba, zan tafi na barka, tafiƴa mai nisa ƙuwa"






Kamkame ta yayi yace "No please karki yi haka, zan gaya miki kinji?, amma first sai kin ci abinci. Am so sorry! hakika ban cika miji na gari ba, na yi wa matata horan yunwa, nasan baki ci komai ba tun safe"




Bai jira amsar ta ba, ya fita, babu jimawa ya dawo dauke da tray mai dauke da abinci marasa nauyi wanda ya dace mutum yace da d'aɗɗare.




Ɓa musu ta buɗe baki ya fara bata chips da egg sauce, dama sosai yunwa ya ci ta, Idanunta sai yawa suƙe a fusk'ar sa tana ɓin shi ɗa kallon asalin ƙauna, shi kam labb'anta dake tauna ships din ya kurawa ido.



Sosai taci, ƙana ta riƙe hannƴensa tana girgiza masa kai alamun ta ƙoshi.


"Are you sure you ok?" Fadeel ƴa tamɓaƴeta.





"Yeah!" Ta amsa cikin siririyar murya, kana ta karbi tray din, ta ɗora ƙan cinƴar sa, ta fara ciyar dashi itama..

Bayan sun gama ya dauke ta cak! zuwa saman stairs domin yau a nan part din yake son su kwana...





Ɓayan sun yi wanƙa, suka shirya cikin pyjamas kala daya farare, kwanciya tayi cikin matuwar jiƙi domin har yanzu jikinta ba kwari. Fadeel ƙuwa ɗanna lock_code yayi a ƙofa ƴaƴi addu'a kana yazo ƙan gadon ya kwanta a ɓayanta, ta ji kwanciyar tasa amma tayi luf, mirginawa yayi ya dawo da ita saman sa.




Ajiyar zuciƴa suka saƙi a tare, bayanta ya shiga shafawa a hankali.



Cikin wata murya dake bayyana tsantsar damuwa ɗa ƴaƙe ciƙi yace "wiffy kin san nace doctor yayi miki check up, har da blood test ko"




"Eh" ta fada gabanta na fadu'wa da k'arfi, wanɗa ɓata san ɗalili ɓa.



Wani wahalallan numfashi ya sauke kana yace "na shiga tashin hankali sosai my Darling, ban taba tunanin hakan ba, a safiyar yau lokacin kina bacci doctor ya kawo result din, blood group dinki ya nuna SS ne" ya fada muryar sa na rawa.





Murmushi ta saƙi ta ce "yes nau! na san blood group dina kenan, amma ba kowa ya sani ba, domin baya sani wanna rashin lafiyar irin na masu blood group din" ta karasa thinking is nothing...







Da mamaki yace "Wiffy! Wanna ba abin rashin damuwa bane, kin san mu dauki alkawarin haifawa Mahmah jikoki, har kin ce zaki basu labarin ta, Fadeelah tell me, ta yaya zamu haifi yaya masu lafiya bayan dukkanin mu *SIKILA NE! Nima blood group dina SS ne. Dole na damu, ya karasa wasu hawaye masu dumi na zubo masa......





*follow and vote me on wattpad @NoorEemaan*🙏







Share fisabilillah habibtie's




Noor
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)




*WATTPAD*
@NoorEemaan





https://facebook.com/groups/943534712916776/masu
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



EDITING IS NOT ALLOWED❌



Page 63-64


A zaɓure fadeelah ta miƙe zaune saɓoɗa wani mugun tsalle da k'irjin ta yayi, sakamakon aɓinɗa taji Fadeel din ya fada.


Tamƙar statue haƙa ta tsaya kallon sa, rawa bakin ta yake, ƴayinda hawaye ke bin kuncin ta tamkar an balle famfo, so take ta furta wata kalma amma ta kasa, ganin hakan ya sanya Fadeel mikewa zaune ya rungumeta, sai a loƙacin wani kuka mai ciwo ya kufce mata, su kam suna ganin rayuwa, daga wanna kaddaran sai wannan, amma yaya zasu yi, ko wani bawa da tasa kalar zanen kaddaran...


Ta jima tana kukan har zafin jikin ta ya d'awo, fadeeel ma hawayen yake ya kasa koda rarrashin ta ne.



Sun dauki lokaci mai tsayi haka suna kukan, daga karshe baccin wahala yayi nasaran daukar Fadeelah, still cikin baccin tana sakin sheshekan kukan.



Fadeel kuwa yadda ya ga rana haka yaga dare, sosai ya zurfafa tunanin wurin nemo musu mafita, a haka har aka kira sallar asuba...



Fadeelah ya fara hurawa iskan bakin sa, tabe baki tayi tamkar zata yi kuka, domin da alama ta fara jin dadin baccin.


"Wiffy!" Ya fada cikin kunnen ta.


"Uhmm" she replied trying to open her sleepy eyes.


"It's time for salat, wake up mu fara nafila kafin a tayar.


A hankali ta mike, sai a lokacin duk abinda ya faru jiya ya shiga ɗawo mata k'wak'walwarta.


Take kwalla suka ciko idanun ta, amma bata bari sun zubo ba, toilet suka shiga, suka d'aura alwala, praying mat (sallaya) ya shimfud'a musu kana suka tayar.




Sai ɗaya ji za a tayar da sallah a masallacin dake cikin gidan, sannan ya mike a dan gaggauce ya fita, Yayinda fadeelah ta mike ta bi jam'i.



Ɓai dawo ciki ba, sai 6:30am, karan ruwa yaji a toilet hakan ya sashi fahimtar wanka take, ɗuƙ yanda yake so yaga suna wanka da matar sa a ɓaƴi daƴa, amma yanzu bazai iya ba, saboda yasan dole mood dinsa zai sanja har ya kasa controlling din kansa, ƙomai ƴa waƙana, idan Allah ya bashi nasarar jefa kwan sa a mahaifar ta, baby'n yazo yana shan wuya a duniya ya zai yi? Ya sani fadeelah ce dukkanin farincikin sa, sannan zai iya rayuwar farinciki da ita ko da babu 'ya'ya.


Amma ya zai yi da alkawarin cikawa Mahmah burinta? domin mahmah ta cancanci fiye da haka, numfashi ya sauke kana ya fita zuwa wani bathroom, domin duk wani sashe na gidan akwai kaya da d'ukkanin abubuwan bukatar ɗan Adam.


Wanƙa ƴayi ya shirya cikin wani 3quarter ash color da rigar jersey armless, sliver color, na company'n *Nike*


Oiling Kanshi yayi ya taje, kana ya fesa turaren LOVE IN OUD FOR MEN.


Wajen fadeelah ƴa ƙoma, ya ƙuwa tarar da ita zaune tayi shiru, binta da kallo yake, ƙallon so da zallan ƙauna, sanye take da tsad'add'en palazzo trouser ja, da farar top, sai fashion hula jaa ƴayinda gashinta ya bazu a gadon bayanta, ƙasancewar ɓata ƴi parking ɗin shi ɓa.



Ɓabu ko digon makeup a fusk'ar ta, sosai jikinta ƙe tashin k'amshin *body mist na raspberry*



Kansa ya dora a cinyar ta yana kallon ta, sai a lokacin ta lura dashi, ajiyar zuciya ta sauke, ta kira shi ba tare da ta kalla shi ba "zaujee"




Lumshe kyawawan idanun sa yayi domin ba kadan ba yaji dadin sunan, kallonta yayi ya samu nasaran jefa Idanunsa masu cike da zallan sonta cikin nata.



Kallon ido cikin ido suke wa juna, ko kiftawa basa yi, daga karshe dai Fadeelah ce ta janye Idanunta, domin ta kasa jure ƙallon, sak'amak'on wasu abubuwa da take hangowa a idanun sa, wanda baki bazai iya furta ba, sai dai a bar wa zuciya.



Hannunsa ya miko mata, ta kama suka miki a tare, ta wata doguwar corridor ya bi sai gasu a wani hada'dden waje wanna dinning da sauraran abubuwan abinci ne a wajen, sosai waje ya tsaru fiye da tunanin mai karatu, tamkar dai wani tsad'add'en restaurant cikin VIP.



Ja mata kujera yayi ta zauna, kana shima ya zauna,, take wasu ma'aikata masu sanye da fararen kaya suka bayyana ɗa alama sune chef's.
Cikin girmamawa suka gaishe ɗa su fadeel, amsawa suka yi, kana suka fara kokarin serving dinsu.

Fadeelah tace "sorry! I will do the serving my self, don't worry" sosai suka yi mamakin saukin kanta, da murmushi a fuskar su suka ce "yes ma!" Kana suka fice cikin sanin makamin aikin su.



A nutse ta mike ta dauki serving spoon ƙana ta ɓude warmer domin serving dinsu, rike tsintsiyar hannunta yayi, da mamaki ta kalleshi alamun "what?"



"Baki cancanci ki wahala ba, domin baki Saba ba, bayan nan ma kin manta ke amarya ce da babu kamar ta" ya karasa cikin rada, so yake ya ɗawo da walwalwlar su, baya son wanna yanayin na su, zai yi kokarin ganin yana bata farinciki, duk da kaddaran daya shigo musu yanzu.


Murmushi ne ya subuce mata, tace "my one saɓoda ni na taso a gidan gata, hakan baya nufin bana yan kananun aikace² duk da Daddy na hana ni, domin a cewar sa muna da tarin ma'aikata, amma Mommah bata barina, ta kan sa mu shiga kitchen wani zubin, amma ba kullum ba, mun fi yi musamman idan daddy baya kasar " ta karasa tana ƙallon sa.


Murmushi ya subuce masa, tabbas yana ganin darajan Mommah domin ta rike masa fadeelah'n sa tamkar ita ta haife ta, ya kuma ƴi mamakin jin cewa fadeelah ta iya shiga kitchen, sosai fadeelah ke burge shi, domin bata da wulakanci ƙo dagawa irin na wasu yaran masu hannu da shuni.



Kamar yadda ya fada shi yayi serving dinsu da abincin, suka fara ci... Turo baki fadeelah tayi, "menene wiffy?" ƴa tambayeta with care.


"Kaga su Mommah da Daddy basu kira ni ba ko? ni ban ma san a wani sashe na giɗan nan na ajiye waƴar ba.



Murmushi yayi yace "kila saboɗa kada kiyi musu kuka shiyasa basu kira ba, crying-crying baby" ya karasa a zolaye.


Dariya tayi suka ci abincin, banyan sun gama suka bi wata hanya, take suka bayyana a wani hada'dd'en lambu mai cike da kayan itatuwa iri daban² ga wani ruwa fari kal dake bulbulawo daga gefen, ƴayinda wasu duwatsu masu kyalli suke zagaye da inda ruwan ke bulbulowan sosai haƙan ƴa ƙara kawata wajen...



Wano hada'dden kujeran zama tamƙar 3sitter, irin na gargajiya amma an kawato shi da zamani wanda ya hadu fiye da tunanin mai karatu suka zauna akai, sai lelo yake dasu, garden din nada sanyi sosai, babu abinda ke tashi sai k'amshin furanin dana kayan itatuwa, dora kansa yayi a cinyar Fadeelah suna jin yanayin mai dadi na ratsa su, sun kuma samu saukin damuwar su..



************************


BAYAN SATI DAYA

Ta bangaren Daddy kuwa, yana cikin matsanancin damuwa da hankalin sa ya kasa dauka, gabadaya ƴa ɗawo zararre, Saboda a daran jiya yana zaune aka kira shi ana sanar dashi cewa kayan da yayi odar su gabadaya sun nitse a babban ƙogi.



Taƙe tsad'add'en wayar sa ya fadi kasa, gabadaya jikinsa ya fara rawa, domin bai taba sanin cewa akwai wata kalma mai suna DAMUWA KO RASHI ba.

Domin duk abinda yake bukata yana ganin cewa yana da dukiyar da zai mallakesu, amma yau gashi dukiyar da yake takama da ita ya rasa kaso mai yawan gaske daga ciki...



Tamkar dan jariri ya dinga kuka wiwi, domin ya rasa kudi masu zunzurutun ƴawa, fiye da tunanin mai tunani masu yawan gaske kuwa


domin BILLIONS DUBU SABA'IN ya fitar ya siyi kayan, domin yasan zai samu ninkin ribar abinda ya fitar, amma ace tashi daga yayi asarar su, da zallan damuwa tabbas!


Gabaɗaƴa estate din ya dauka, yan'uwa sun cika part din ana jaje, sosai gidan ya dawo tamkar gidan mutuwa, kowa fuskar sa babu walwala hatta da masu aikin gidan, Grandma har taso ta fi daddy zarewa ma, Mommah ce mai k'arfin hali rarrashin su, ya kuma hana a sanar da Fadeelah, yace bayason hankalin ta ya tashi...


★★★


10:00pm

Mommah ɗa Daddy na zaune a part din shi, aƙa hasko abinɗa ƴa faru da professor a TV. Gabadaya gari ya dauka, sai hirar abinda ya faru aƙe daga masu Allah ya kiyaye sai masu jaje...



Haƙa zalika sakonin sun fi dubu biyar suna ta shigowa wayar Daddy daga abokan kasuwancin sa dama aboƙan arziki, ko daya ya kasa bada reply, sai dai idan sun ƙira Mommah ko suyi mata text, message shima ba kowa ta bawa amsa ba, domin abin da yawa...



A hankali ta dago Idanunta ta kalli Daddy, gabadaya cikin awanin 48 ya sanja har wata rama yayi, take taji tausayin sa, an ce tsakanin miji da mata sai Allah amma hakan bazai hana ta gaya masa gaskiya ba.


Zuwa SunnahTv ta sanja channel din, domin rage masa damuwa, ta kuwa yi sa'a ana wa'azi ne kan yarda da kaddara da kuma kasancewa mai haku'ri da duk yanda rayuwa ta zo maka...



Gyaran murya tayi tace "professor, ka yi haku'ri wanna abun yana daga cikin zanen kaddarar ka, Wanda bawa bai isa ya tsalla ke ba.


Kaga irin abinda nake yawan gaya maka, wanna dukiya Allah ne ya baka shi, zai kuma iya amsa a duk lokacin daya so.

RAYUWAR nan babu komai a cikinta, cikin seconds kalilan Allah zai iya sanja K'yak'yyawa zuwa mummuna, ya kuma sanja mummuna zuwa kyakyyawa...


A akan me toh zaka ce baka ga inuwa da talaka, Allah ɗa kan shi ya ƙarrama dan Adam, wane mutum dazai wulaƙanta hallitar Allah?



A yau ga misali ka gani a kanka, ina dagawa da dukiyar da ƙaƙe iko da taƙama dashi? Shiyasa nace kabi duniya a sannu!

Da yawa daga cikin masu dukiya irin ku basa fidda ZAKKAH bayan hakkin Allah ne, dole a fitar. Wasu kudin su ya kai yin zakkah amma basa yi, basa taimako mabukata, basa taimakon marayu ɗa sauran su.
Ɗa kuƴi haka, ƙu gwanmace kuyi wani abu wanda darajar ku zai karu a idon abokan ku masu hannu da shuni.
Tayaya masifa baza su yi yawa a Al'ummar mu ba, I tell you akwai gidajen da basa d'aura tukunyar tuwo a gidan su saboda rashin babu, I tell you akwai ahalin da rana zai fito ya faɗi amma basu saƙa koɗa loma daya na abinci a baki ɓa tabbas akwai da yawa, wallahi aƙwai, kuma na san ka sani, amma da ku taimaka marasa shi ku gwanmace kuyi facaƙa da kudin da ƴin abinda bashi da wani amfani, dan haka think Professor! ka sanja, ka daina wulakanta talaka, kai taimaki marasa shi, ina mai tabbatar maka zaka ga sanji da haske a rayuwar ka ta duniya dama lahira. Idan kalamai na sun bata maka rai kayi hakuri, amma gaskiya ce dole na fada domin na fita hakkin ka.
Sai da safe na barka lafiya" Mommah ta karasa tana barin falon...



A kafatanin rayuwar Daddy babu kalaman da suka shiga kwanyar sa, kana suka samu muhallin zama a zuciyar sa kamar wanna ba.


Sosai wani mugun nadama ya shige shi, abin ba a cewa komai, ya jima a zaune cikin zurfin tunani, wulakanci da yayi wa fadeel da Sadaukar ɗa ƙodar ɗa Mahmah taƴi ga tilon 'yar sa yafi komai tsaya masa arai, sai yanzu yake nadama mai tarin yawa.




Sai karfe biyun dare ƴa ɓar falon, ya shige bedroom din shi, toilet ya shiga ya yi alwala yazo ya shimfud'a sallaya ya shiga jera nafilfili abinda ya dauki shekaru rabon shi da yi wato SALLAH'N DARE, daga karshe ya dora da karatun Qur'an.




**********

Zaune take kan cinyar sa, Yayinda ya zagaye hannayen sa, kan shafaffan cikin ta.


So yake ya sanar da ita abinda ya faru, amma baya son damuwar ta, bayan wanda suke ciki, domin yau kwana uku kenan daya samu labari abinda ya samu Daddy.



"Kallon shi tayi tace " my one anya su Daddy na lafiya kuwa? naga baɓu wanɗa ƴa ƙira ni"



"Cikin sauri yace "eh suna lafiya, so suke ki saba da gidana sannan ku fara kira, domin karki ce kin fasa zama a nan, ki ɓarni " ya fada domin kwantar mata da hank'ali.


Murmushi ta saki tana jin nutsuwa a ranta, sak'amak'on abinda yace, hannu ya mika ya dauko wani kyakyyawan jaka mai kyalli ɗaƙe gefen su ya dora kan cinyar ta.


Karba tayi tana bin shi da kallon mamaki, budewa tayi taga wayoyi ne masu tsadar gaske guda goma, bakwai android sai uku keypad amma mai tsadar gaske, sai kuma kalolin rigar waya(pouch) masu k'yau da kyalli zubin mata, ya siya mata diffrent colors ɗomin ta dinga sanjawa.




Cikin su akwai *Stuart Hughes iPhone 4s Elite gold wanna tsadar sa yakai $9.million, sai falcon supernova wanna kudinsa yakai $6.2million sai iPhone 8pink diamond $48.5 million, sai Gresso las Vegas jackpot wanda kudinsa yakai $1million, sai supernova iphone 6 wanda kudin sa $3millon, sai million goldish de million wanda kudinsa ya kai $1.5 million, sai black diamond iphone wanda 10 kudinsa yakai $18.6million* Da dai sauran su...




Sosai fadeelah tayi shiga zallan mamakin, she can't even say a word. Ganin wanna uban wayoyin haka, wasu ma sun fi nata tsada ma.

"My one duka wayoyin nan nawa ne?" Jinina mata kai yayi cikin tabbaci.


"Amma sunyi yawa, baya ma ina da wayoyin amma ka siyi wadan nan" ta fada domin ganin ya kashe kudi masu yawan gaske.



"Na san kina da wayoyi ai hajiya Fadeelah! amma bana son kiyi amfani da wandan can, so nake kiyi amfanin da wanda na siya miki da kudina. Ban saniba ko tsadar wadannan ne basu miki ba, amma ina so komai na wad'ata ki dashi, koda bazai kai tsad'ar wadanda kika saba amfani dasu ba, amma ina son kiyi amfani da abinda ya fito daga hannuna domin hakkin nane hakan, duk namijin kwarai baya damuwa da dukiyar da matar sa take dashi, matuƙar yana shi toh ya zama hakkin sa ya sauke, sai dai idan bukatar taimakon juna ya tashi bashi da halin komai tofah wanna ba laifi su taimakawa juna" ya karasa yana dora habansa kan kafadar ta.



Cikin jin dadi tace "lah! zaujee sam baƙa fahimce ni ba, a ganina tunda aƙwai waɗancan nawa toh, bai kamata ka ɓata kudi ƙa siyi wasu ba, a ganina gwara ayi wani abun da kudin, ba wai ina nufin sun min kaɗan ɓane, ko kuma ina nufin tsadar su bai yi min ba, amma kayi hakuri kajiiiii" ta ƙarasa cikin iyakar gaskiyar ta.



Sai yanzu ya fahimce ta, tabbas shi shaida ne fadeelah ba mai rainuwa bace, shima ya fada ne kawai domin jin abinda zata fada, jinjina mata kai yayi kana ya bata light kiss a kumatu yace "na mayar miki da dukkanin sim dinki ciki, da sauran abubuwan amfanin ki, sannan na goge su daga wadancan wayar na kyautar dasu, zaki iya amfani da wadannan domin duk na caja su, na so baki tun washegarin auran mu, na sha'afa saboda abubuwan da suka sha min kai, in sha Allah da mun sake samun nutsuwa zan siya miki wasu..."



Kallon shi take with more admiration tace " a'a wallahi wadannan ma sun isa haka my one, Allah ya saka maka da alkhairi fil duniya wal Akirah, Allah ya...."

Labb'anta ya kamo ya shiga kissing din ta, domin bai ga abin godiya ba, matuk'ar Allah ya hore mishi, zai cigaba da wadata ta da dukkanin wani jin dadin rayuwa, domin ta cancanci fiye da hakan...



Ɗa yamma ya shirya zuwa estate wajen Daddy, amma sam bai sanar da Fadeelah'n inda za shi ba, har bakin kofa ta kara shi suka yi sallama cike da son juna, nan ya shiga daya daga cikin motocin sa kirar *Lamborghini zonda sian FKP* baki, sannan sauran motocin escort d'in sa suka faɗa sauran motocin, a jera reras gwanin burgewa suka nufi *IKOYI*, unguwar su Fadeelah.....





Share fisabilillah habibtie's


Noor🔥
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*




🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)




*WATTPAD*
@NoorEemaan






https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



EDITING IS NOT ALLOWED❌



*A gaskiya ina godiya a gare ku habibtie's da kaunar da kuke nunawa kyautar koda har da papi ne! ina godiya sosai ga readers din wanna tagwayen littafan nawa ɗa wanda na sani da wanda ban sani ba, ina muku son so fisabilillah, Nooreemaan taku ce, Fadeelah da Fadeel ma naku ne😁*




Page 65-66


Tsakiyar yalwataccen farfajiyar cikin estate din motocin Fadeel suka tsaya, kana daya daga cikin escort d'in sa suka yiwa security din estate din magana kan ya nemawa fadeel iso wajen Daddy surukin sa ne ya kawo masa ziyara, ai fa babu bata lokaci security ya nufi falon professor ciƙin sauri domin ya sanar da shi...



Zaune Daddy yake a falo, ƴayi Shiru tamkar mara lafiya, har wata rama yayi gwanin tausayi, tare da shi akwai Mommah, Grandma, da wasu yan uwa sa dake cikin estate d'in.



Cikin girmamawa security'n, yace "boss! mijin ma'am ne yazo"



Cikin zallan mamaki Daddy ke kallonsa, bayan tarin wulakancin da ƴa yiwa yaron nan har yazo gaishe shi, kallon security yayi, a sanyaye yace "let him in"




Cikin girmamawa security ya juya ya koma, kana ya sanar da su Fadeel cewa Daddy yace ya shigo.



Cikin takun nutsuwa da birgewa ya nufi falon Daddy, bud'e masa kofa escort d'in sa sukayi, kana suka gaishe da Daddy cikin girmamawa suka fita, sosai Daddy yayi dadin hakan, gaban Daddy Fadeel ya durƙusa, gabansa na faduwa ya gaishe shi, wani yanayi ne ke shiga jikinsa, har wani tashi tsigar jikinsa yake, sosai wani tarin nadama ya rufe Shi, hannu ya mika wa fadeel alamun suyi musabaha...


Sosai zallan mamaki ya rufe Fadeel, amma bai nuna ba, hannun ya mika wa daddy'n sukayi musabaha cikin girmamawa, still dai kansa na kasa.



Mommah dake kallonsu tayi murmushi daya taho da zubar hawayen ta, wanda na zallan tausayi ne, ta ma rasa wa take tausayawa a cikin su.



Gaishe da su Mommah yayi cikin girmamawa, amsawa suka yi, fusk'ar su dauke da murmushi, domin sun san FADEELAH ta more miji...



Hannun shi Daddy ya kama ya zaunar shi kan hada'dd'en kujeran kusa da shi, yana jin farinciki na ratsa zuciyar sa, hakika ba kudi kadai bane dajarar mutum, mutunci da sanin darajar dan Adam ma wani abu ne, wanda bai fahimci hakan ba sai yanzu, sosai yaji dadin girmamawan da Fadeel ya bashi bayan duk tarin wulakancin da ƙasƙancin daya masa...





Nan Fadeel yayi masa jaje sosai, ya kuma yi masa add'uar Allah Ya tsare gaba. Amsawa Daddy yayi har cikin ransa ya ji dadi, hakan ma su Mommah...




Mintunan sa goma da

Please Login or Register in order to submit comment