Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

serving spoon din yayi yace
"toh gayamin, me zaki ci?" Yana mamakin zaban abincin data fara yau kwana hudu kenan.

Turo baki tayi tace "wanna kazar daka taba hadamin a daran farkon mu ka tuna?" tace tana tande lebe.

Shafa kansa yayi, shi ina zai iya tuna yanda ya hada kazar "anya wiffy zan iya tunawa kuwa?"

"Toh ni wallahi shi nake so" tace tana bata fuska.

"Ok ok bari na hada miki"

Murmushi tayi tace "toh ka gama cin abinci tukunna"

"Are you sure zaki iya jirana in kammala cin abincin?" jinjina masa kai tayi, ta zuba masa abincin, ta bashi a baki ya shiga ci ya kuwa ci sosai ya kora da fresh milk hadi da ruwa kana suka nufi private kitchen dinsu.


Sosai yayi kokari wurin hada kazar gudun kada tace ba irin shi bane, bayan ya gama ya zuba mata a tray kana ya daukar mata lemo mara gas domin tace bata son mai gas yanzu....
Falo suka dawo nan ya ajiye mata a gaban ta, hannu baka hannu kwarya haka ta dinga yagar naman ta ma ki bari ya bata, wai baya bata da sauri, bai gama mamaki ba sai daya ga ta tashi da katuwar kazar nan kaf, har da tauna kasusuwan, lemo ya mika mata ta shanye tas tana sauke ajiyar zuciya.

"Ya ishe ki?" ya tambayeta

Jinjina masa kai tayi tace "thank you so much my one" ta fada tana dora kanta kan kafadar shi, bayan mintuna goma yaji tana kokarin zamowa, sauri taro ta yayi, domin yasan bacci tayi...

Kwantar da ita yayi kan doguwar kujera, kitchen ya kai tray din, ya kuma debo ruwa a bowl ya wanke mata hannu, bayan ya zubar da ruwan yazo ya zauna yana kallon ta, yana kuma lura da sauyen-sauyen ta.

Kasa hakuri yayi ya kira doctor yazo ya duba ta. Babu jimawa doctor yazo ya yi gwaje_gwajen sa yace zai kawo result da yamma, Fadeel yace baya iya jira, ya daure ya kawo masa yanzu daya duba, likitan bai musa ba ya tafi, Fadeelah kuwa bata san abinda ake ba, domin bacci take Sosai.

Awa daya da rabi doctor ya kawo result, jikin fadeel na rawa ya bud'e result, ai fadin zallan farinciki d'aya kawata fuskar sa bata lokaci ne, sosai Fadeel ya shiga murna ganin Fadeelah'n shi da shigar ciki, sujaddul_shukur yayi, kana ya mike ya shiga tsallen murna, wanda hakan ya tashi fadeelah...


Cikin muryar bacci tace "Fadeel what's it, Lafiya?"


Jin muryar ta ya sanya shi zuwa gaban ta ya ce "you are pregnant fadeelah, you re carrying my baby in your womb" yafada yana nuna mata result din, cikin farincikin mara misaltuwa.


Abin dariya Ita ma mikewa tayi ta rike hannunsa suka shiga tsallen murna, sai da suka gaji suka zube kan kujera suna mayar ɗa numfashi, kallon juna suke murmushi shimfud'e a fusk'ar su, a hankali suka matso da fusk'ar su dab da juna, suka hade bakin su waje d'aya.


Kafin dare kuwa kowa ya sani, domin fadeel ya gama Kiran kowa ya fada musu, har da Daddy da Mommah kuwa, a daran kuwa dady da Mommah suka zo duba ta, Daddy ya shiga tsokanar ta wai princess din shi ta girma ta kusan zama uwa. Dariya tayi tana shigewa jikin Mommah cikin kunƴa.




**********

Ta bangaren Jameel kuwa ya sake nutsuwa sak'amak'on mutuwar haulat, wata yarinya data dade tana son shi ya amince zai aure ta, duk da ba wani sonta yake ba, amma yasan With time zai so ta, shi kam yanzu tsoron zina yake hakan yasa shi zaban yin auren..
A daran su na farko ya fahimci ita din ba budurwa bace, amma bai da ta cewa domin abinda ya aikata ne yake dawowa kansa, sosai ya kara kyamar zina, yana kuma fatan idan Allah ya basu zuri'a kada y'ay'an su su kasance masu aikata wanna mummunan zunubin...



Ta bangaren minister Sa'id kuwa har gida yazo ya roki Daddy kan ya yafe masa, domin shine ya saka aka nutsar da Kayan shi cikin ruwa, ya biya matukan jirgin ruwa kudi masu yawa, ya kuma sake gaya masa muguntar da suka sake shirya masa na kashe Fadeelah ko Fadeel, sosai dadi yayi mamakin hakan, lallai duniya abin tsoro ne, tabbas minister Sa'id bai cancanci zama aminin sa ba, hakan yasa shi cewa kada ya kara zuwa kusa dashi, cutar da shi da yayi kuwa ya yafe masa.
Jiki ba kwari minister Sa'id ya tafi cikin nadama, Yayinda ya kara godewa Allah daya bashi Fadeel a matsayin suruki, yana kuma godewa Allah da ba Jameel bane mijin princess din shi (fadeelah). Wasu lokutan abinda muke ki shine alkhari a garemu....




Share fisabilillah



Comment






I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


🍇🍇KYAUTAR KODA🍓🍓
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)


*First edition*








EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




#Ending




Page 79-80


*Bayan Wata Takwas*


A yau Fadeelah ta fara nakuda, babu bata lokaci suka nufi asibiti, Fadeel ya gama tayar da hankalin shi.




★★★

K'a'idar asibitin idan mace zata haihu sai mijin ta na dakin haihuwar shi ma sanye da kayan asibitin kamar yadda fadeelah ta saka.





Add'ua yake tofa mata hannunsu sarke dana juna ta ki sakin sa, sai faman cije lebe take sakamakon azaban daya ishe ta.




Chan tayi nishi, sai ga kan 'ya ya taho, kasa kalla Fadeel yayi Saboda tausayi, dama haka uwa ke shan azaba idan zata haihu, a hakan wasu y'ay'an ke kasa yin ladabi biyayya ga mahaifiyar su? Wani imani ke kara shigar sa.




Kan yar na fadowa ta canyara kuka, wani nishin ta fara yi, kan wata 'yar ya fara tahowa, wani nishin ta kara yi kan da ya taho wanna karon namiji ne, mamaki ne ya kama Fadeel da jinjina iko da k'arfi buwayi gagara misali, babu Wanda ya taba tunanin fadeelah zata haifi yaya uku a lokaci d'aya, domin cikinta bai da uban girman nan, hawayen farinciki ne ya Zubo masa, at last, yes at last, a karshe sun cikawa Mahmah burinta, sumbatar fadeelah data gama jigata ko hannunta bata iya dagawa yayi, ita kam bin shi take da kallo tana murmushi Yayinda itama hawayen farinciki ke bin gefe da gefen fusk'ar ta.




Duk da jinin dake jikin yaran hakan bai hana shi daukar su daya bayan daya ba. Kafin dare asibiti ya cika, kowa sai son barka, Daddy kasa boye farincikin sa yayi, ya kara tabbatar wa, fadeelah da Fadeel tarayya su alkhairi ce.



Alhaji Sufyan Rufa'i da Daddy Kyautar ban girma suka bawa triplet (yan uku) din fadeel, su Mommah da sauran yan'uwan na dangin Fadeel dana fadeelah sun cika asibiti, yan uku fa sun sha kyauta masu tsada kuwa, wasu gidajen, wasu kudade, wasu motoci haka kowa ya dinga bada tashi Kyautar, kowa ka gani cikin farinciki yake, kwanan Fadeelah hudu aka sallamesu.


Cikin masu kyauta har da Jameel ya aiko da nasa, fadeelah taki karba, amma Fadeel ya hana ta yace yin hakan ba kyau, komai ya wuce, ko da baza su yi amfani dashi ba, sai ta kyautar, akan taki amsa.


Hakan kuwa akayi, ta karba, suka ce wa dan aiken yace "An gode"



*RANAR SUNA*

A wani babban hall mai cin mutane dubu dari biyar suka yi sunan, ko ina jama'a ne an cika kowa ka gani fuskar sa shimfud'e da farinciki, yan uku da suka ci sunan Mahmah, sunan Mommah da kuma sunan baban Fadeel, shirye cikin wasu had'add'un kuma tsadaddun kaya, ta farkon kamanin Mahmah sak ta dauko tamkar an tsaga kara, ta biyun ta dauki kamanin fadeelah, yayinda ta uku ta dauki kamanin fadeel ana musu lakabi da *ta farko little mah, ta biyu Amnah, na uku kuma amjad*




Daga baya na hango fans din ƘƳAUTAR ƘOƊA sun sha kyau cikin shigar tsadaddun material blue and sliver, sai faman cin fried Rice da kaza suke, wasu kuma na cin tuwon sakwara da miyar egusi yaji nama, kowa dai abinda ya zaba yake zubawa yaci da kansa.



Nan na hango su Darma, oum Abdul-rahman, sis suwaiba, Nafessah Aleeyu (feenah) Fatima Ali Adam, biejarh, sis nabeela, hajency, hajiya Rukayya, sis laylerh sis hassana, maman sudais, narnah, sis Aisha, sis Fatima, sis sadeeyerh, sis Mariam jumare, wai gaskiya kuna da yawa. Kyautar koda fans sun yi kara sosai a sunan yan uku, har wajen fadeelah da Fadeel suka je aka dauke su hoto da yan uku....😂lolz



Bayan suna fadeel yayi wa Alhaji Sufyan Rufa'i albishir da cewa ya bashi Amnah kyauta halak malak da zaran Fadeelah'n sa ta gama shayar da ita, sannan su little mah zasu dinga zuwa yi masa hutu, sosai fadeelah ta ji dadi, domin Alhaji sufyan ya cancanci hakan.


A lokacin da Alhaji sufyan da matar sa suka ji wanna sadaukarwa da fadeel yayi musu kukan farinciki suka saka, domin tabbas sun ji dadi ko ba komai zasu rage kewa, tabbas duk wanda Allah ya jarabta da rashin haihuwa zai ji ba dadi taɓɓas, amma hakuri shine ya dace mutum yayi, ga shi kuma sun ci ribar hakurin, tun kafin Amnah ta koma gidan suka ware mata daki babba suka saka mata kayan wasa iri,-iri na yara....




*One Year later*



*SAUDI ARABIA*

A hankali suke saukowa daga jirgi, fusk'ar su ɗauke da murmushi, Yayinda hannun su ke sarke dana juna, suna kallon yadda little mah, Amnah, da Amjad suke sauka daga jirgi da sauri-sauri.




Sanye Fadeel da Fadeelah suke cikin shigar kananun kaya, yan uku sanye cikin riga da wando iri daya sun yi kyau sosai, ga wayo kamar ba yan shekara d'aya ba.




Fadeelah tana nan yanda take bata yi kiba ba, sai ma Fadeel daya dan yi kadan, amma kallon daya zaka musu kasan cewa suna cikin kwanciyar hankali.





Kamar yadda ko wani shekara akwai kasar da suke tafiya hutu, wasu lokutan da Alhaji sufyan da matar sa wanda suke rike da Amnah kana suna nuna mata kauna iya kauna.


wanna karon saudiya suka taho domin sauke farali, amma banda su Alhaji Sufyan Rufa'i.

daga nan suyi yawan bude ido, wasu had'add'un motoci biyu ne suka zo daukar su, a wani hada'dden hotel suka sauka.





A washegari suka fara gabatar da ibada, sosai suka yi ibada, da dare yayi su tafi masauki, a haka suka gama tsaftataciyar ibadar su, sai dai fatan Allah ya amsa.



Wuraren tarihi kala-kala suka je, sunyi videos da hotuna kala-kala , Amnah kuwa ta dauki babban tablet dinta tana video call da su Alhaji Sufyan rufa'i hadi da nuna masu wurare, domin sosai take son su Alhaji Sufyan rufa'i ta ma fi sabawa dasu fiye da iyayen ta...

duk inda suka je sai yan uku sun ce "mummy, Daddy, ina ne nan?" iyayen su shiga basu labari, sosai suka yi having fun.




Daga nan suka je wuraren siyar da abaya, da gwala-gwalai da azurfofi ya siya musu.




daga nan suka dawo masaukin su a gajiye bayan ta yiwa yaran wanka, Fadeel ya shirya su cikin kayan bacci, suka kwantar da su a dakin da suka kama kasancewar mai two bedroom ne, kamar kullum haka suka dinga taya y'ay'an nasu hira har bacci ya sauke su, add'ua suka tofa musu, suka lullube su hadi da kashe wuta suka bar musu dim light.




Fadeel ya kamo hannun matar sa suka nufi nasu bedroon din, bayan sunyi wanka a tare suka fito, kayan bacci suka saka, tana manne a kirjin sa yace



" i love you wiffy, you re my everthing"



" i love you too my one, you re the best husband ever"



Murmushi yayi ya kara rungume ta yace " my Darling ya kamata a yau na Samar wa su little mah kani ko kanwa, nasan kin gaji amma please ki bani....."


Bata bari ya kai karshe ba ta kama lallausan lips dinsa ta fara birkita shi
da salon ta, nan da nan suka Lula duniyar ma'aurata..





#hamdan lillahi




Share fisabilillah to others




Comment dinku is needed




Special thanks to all kyautar koda fans, son so fisabilillah habibtie's💞

_na so zayyano duka groups din da kyautar koda yaje domin na nuna special thanks dina a gareku, buh Lokaci bai bani dama ba, amma ina so ku sani duk inda kyautar koda yaje, da makarantar kyautar koda ina son ku fisabilillah_💖😘



A nan na kawo karshen novel dina mai Suna kyautar koda, kurakuran ciki Allah ya yafe min da ni da makaranta, fadakarwan ciki Allah ya bamu ladan.



sannan zan so cin ra'ayoyinku a kan littafin ƙƴautar ƙoɗa da darasin dake ciki.



⚠️caution⚠️

Littafin kyautar koda hakkin mallakan NoorEemaan ne! Ban yarda a juya min shi ta ko wace siga ba, idan kunne yaji.....





NoorEemaan ce🔥😍
07082281566




Sat, October 2O21




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment