Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai" Daddy ya fada yana nufar motocin sa.....





Ƙasa ɗa mintuna hamsin suka iso ƙatafaran estate din. Bayan ya shiga falon ya tarar da jama'a masu yawan gaske, ciki harda yan'uwan minister domin yayi musu farin sani.




Cikin mamaki ganin fuskokin su ba walwalwla yace "what's happening here? Mummy lafiya?"





"Ina fa lafiya Imran, kalli ka ga" Grandma ta fada tana nuna masa tarin akwatunan da aka kawo da farko, da ma wanda yan gidan su minister suka kawo.



Take ya kai idanun sa kan aƙwatunan yana jinjina yawan su, a tunanin sa duka Jameel ne ya kawo, da dan murmushi dauke a fusk'ar sa yace "mummy miye a ciki? I guess lefen princess ne" Daddy ya fada.





Girgiza kai Grandma tayi tace "Nooo! you're wrong Imran, wait bari na tambayeka maza biyu kaƙe son auran Fadeelah'n ne banda labari?"




Cikin zallan mamaki Daddy yace "maza biyu kuma? Tayaya zan yi hakan Mummy please ki yi min bayani?"






"ɓasan ta ƴa ƴa zanyi maka bayani ba, domin kaina ya kulle, amma kalli can, kaga wadancan akwatunan guda hamsin ɗin? toh wasu mata ne suka k'awo shi, bayan awa ɓiƴu ɓa jimawa dangin minister suka kawo akwatunan talatin gasu nan" ta fada tana nuna masa.





Kana ta dora da cewa "mun dauka lefen farko daga gidan su minister aka k'awo, sanin kanka ne bawai mun yiwa dangin abokin naka farin sani ba, hakan yasa muka dauka lefen farko da aka k'awo daga bangaren su ne, tambayar nan shine WAYE YA KAWO LEFEN FARKO???






Take gabansa ya fadi, Kan shi ya kulle, to kenan waye ya kawo lefen farko? Ya budi baki zai yi magana, wata mata cikin yan'uwa minister data kasance kanwar sa tace "mu fa baza a mayar damu k'ananun mutane ba a toh, ina aka taba haka? Dama kuna sane so kuke ku tozar ta mu, toh bazai yu ba, I repeat bazai yu ba!" Ta karasaà cikin daga murya da amon sa ke fidda zallan halin fushin da take ciki.






Nan hayaniya ya ƙaure tsakanin dangin biyun, sai dai cikin wayewa suka jifan juna da kalamai marasa dadi, musamman dangina minister da suka dau fushi ada yawa, Mommah dake kallon su ta saki boyayyen ajiyar zuciya, domin ba a'akadan ba taji dadin lefen wafarkon da aka kawo, sai dai murnan ta ragagge ne tunda bata san lefen farkon daga hannun waye ya fito ba?





Nan dangin minister suka gama fadin maganganun su marasa dadi kana suka tafi rai a bace, abu dai bai yi kyawun gani ba, ko akwatunan basu dauka ba.





Da kyar Daddy ya ja kafafun sa ya zube kan kujera, ya ma rasa tunanin yi, domin Kan sa ya kulle, ya ma rasa a wani yanayi ya ke ciki yanzu haka, maganar Grandma ce ta dawo dashi tunanin sa.





"My Son Imran, bari na kira wayar ita fadeelah'n tazo muji ko akwai wanda ta bawa ɗama kawo lefe ba tare da mun sani ba"




Bata jira amsar sa ba ta danna wa fadeelah....







Kwance take hawaƴe masu dumin gaske na zubo mata, kuka take sosai gwanin tausayi, kukan take domin tasan burinta, muradi, hadi da fatan ta na son auren Fadeel dinta ya kau, tunda gashi yan gidansu Jameel sun kawo lefe .



Ɗomin a lokacin ta iddar da sallah azahar kenan, ta ji shigowar dagin Jameel, har ta leke ta hango su daga nesa ana sauke aƙwatunan da take ganin su kamar ledoji Saboda rashin son wanda akwatunan ya fito daga hannun sa, duk k'yau da haduwar su kuwa.


Ringing din wayar ta ne ya dawo da ita nutsuwar ta, sunan *Grandma* ta gani yana yawo a jikin screen din, hakan nan ta ji gabanta ya bada ras! Har dafa saitin zuciyar ta tayi tace "ya Allah!" Kana a sanyaye ta latsa Kore hadi da d'aura wa kan kunnenta, cikin matsanancin dauriya, sai dai duk da haka muryar ta rawa yake tace "Hello Grandma"




Grandma ƙuwa yau ko grand-daughter babu tace "fadeelah maza kazo yanzu your presence is needed urgently" tana fadin haka ta katse kiran.





Da kallo ta bi wayar tana jin gabanta na tsananta bugu, saƙamaƙon jin murƴar Grandma cikin wani yanayi.





mikewa tayi a sanyaye ta nufi bathroom, wanke fusk'ar ta tayi kana ta dauki wani madaidaicin towel ta goge fusk'ar ta, kana ta fito.







Duk da Grandma bata gaya mata a wani part din take ba, amma hakan nan taji jikinta ya bata taje part din Mommah.



Cikin sanyin murya tayi sallama, wani faɗuwar gaban ne ya sake risketa sak'amak'on ganin tarin lefe zube a kasan tiles, Yayinda tashin hankali ya saƙe bayyana karara a fusk'ar ta, ta tabbata cewa da doctor Mahfouz zai auna BP dinta a yanzu, da tabbas sai jinin ta ƴa hau fiye da tunanin mai tunani, domin ganin lefen ƙusa da ita ya fi ƙomai ɗaga hankalin ta.




Ganin yan falon gabadaya ita suke kallo hakan ya kara mata faɗuwar gaba.






Cikin dauriya ta karasa kusa da Mommah ta zauna, kana kasa² tace "Grandma gani"






Fuskantar ta sosai Grandma tayi tace "Fadeelah shin bayan Jameel akwai wanda ya kike so har ya riga su jameel din kawo lefe? ko ƙuwa" Grandma ta faɗa tana nuna lefen.





Gaban ta ne ya sake bada dam! Cikin rawar murya tace "A'a" tana kokarin controlling hawayen dake daf da zuba a fusk'ar ta.




Domin idan bata ce a'a ba, me zata ce? Bayan bata san a wani duniya Fadeel yake ba, bare tace shine, ba ma wanna ba, ina Fadeel din ta zai iya kawo lefen da ko jameel din bai kawo irin sa ba?.




Cikin wani daurewan kai wata mata cikin ahalin professor tace "anya mutanen da suka kawo lefe da farko ba batan kai suka yi ba?"





Nan fa hayaniya ya sake kaurewa wasu na cewa ta yaya zasu yi batan kai a irin wanna babban estate din da kowa ya san dashi... Da dai sauran maganganu.





Fadeelah dai kanta na kasa cikin daurewar kai, ta wani bangaren ƙuma tana jin sanyi a ranta, sai dai murnan ta ragagge ne domin bata da tabbas din za a fasa bikin ta da Jameel.





Tun da suka fara magana sai yanzu Mommah dake bubbuga bayan fadeelah tace "Akwai number'n daya daga cikin matar da suka kawo lefen da na karba, ina tunanin ta haka ne komai zai warware"






Cikin zakuwa Daddy yace "please do call her now"


Bai samu amsa ba, sai ma wayar ta data fidda ta danna wa matar kira, bai wani jima da ringing ba ta dauka



"Assalama alaykum" cewar Mommah.




A tausashe wanna matar tace
" wa'alaikumu salam" ɗama na san zaki kira" matar tace tana sakin murmushi.




Dan zaro ido Mommah tayi tace "kin san ɗama zan kira? Kenan ba batan kai kuka yi ba, kamar yanda muƙe tunani?"





Wani murmushi da har sautin sa ya fito matar ta sake yi tace "ko daya, am sure gidan da muka kawo lefen FADEELAH gidan professor Imran mai naira ne, karki damu magabatan danmu zai so in Sha Allah domin ya gana daku"






Cikin wani sabon rudani mommah tace "Toh wayeku? Sannan waye dan naku? meye sunan sa? Domin an saƴar da ranar auren fadeelah ɗa dan gidan minister Sa......"







Da murmushi matar ta sake katse mommah tace "duk muna da masaniyar hakan, sannan sanin waye mu da danmu zaku ji in Sha Allah, kiyi haku'ri da zaran iyayen sa maza sun zo zaku ji komai, sai anjima" kit matar ta kashe wayar.






Da kallo Mommah tabi wayar kamar zata gano matar a Cikin sa, kana ta bi su da Daddy da kallo da suma suka kafe ta da idanu domin tana da tabbacin sun ji abinda matar tace a hands free ta saƙawayar.





"Toh su waye su? Da uɓan me suke takama da basu fada ba yanzu?" Grandma tace cikin isa da fushi.






Shiru kowa yayi domin sun rasa abin cewa kasancewar kowa kansa ya kulle, Daddy shima ya zama speechless ya rasa abin cewa, bama zai iya fassara yanayi da take ciki ba, amma bazai ce komai ba, sai magabatan yaron nan sun zo kamar yadda matar tace.





Grandma ta koma part di'n ta, Daddy ma ya fita, haka sauran yan'uwan suka fara fita har falon ya rage daga Mommah, sai fadeelah.




Dago ta Mommah tayi wanda zuwa lokacin hawayen ya gama wanke kyakyyawar fuskar ta daya yi fayau, cikn tausayin ta Mommah tace "sweetheart ya isa haka! Kina jina?" Jinina kai fadeelah tayi alamun "eh".





" Good! Nasan 'yata bata karya, ki gayamin shin babu wanda kika yi dashi zai kawo lefe, duk da da kamar wuya, amma kaina ya d'aure dole ne nayi miki wanna tamɓaƴar"




K'uk'a fadeelah ta rushe dashi tace "I swear, Allah Mommah babu wanda nake tare dashi, Fadeel ya tafi ya bar ni, ya manta dani, ban san waye wanna ba, ban san waye shi ba, basan Shi ɓa".... Ta karasa tana fadawa jikin Mommah, ta ci gaba da kuka, Mommah bata hana ta ba, ta kai awa daya tana kuka sosai kana bacci ya dauke ta tana sauke shesheka duk da a cikin bacci ne, shafa bayanta Mommah keyi cikin tsananin tausayin ta....





Haka duka ahalin professor Imran mai naira suka kwana cikin wani yanayi da suka kasa fassara shi, musamman wadanda abin ya shafa, su basa murna, sannan basa bakin ciki gasu nan dai, yanayin bazai fassaru ba...


★★★

*WASHEGARI*

LAGOS
*IKEJA GRA*


Hada'dden kuma babban gida ne, kai wanna ya wuce gida ko estate sai dai a kira shi da unguwa guda. Girman sa, tsayin sa hadi da fadi'n sa bazai faɗu ɓa. Gini ne na zamani wanda mutum zai yi tunanin a turai ne.





Fadin sassa da yawan sashe na gidan bazai fadu ba, Saboda yawan sa, waje da cikin gidan security's ne masu kirar k'arfi cikin blue da white uniform, ma'aikatan gidan da yawan su bazai fadu ba, ko wanna
sanye da unform ja da fari.






*A wani sashe na gidan*

Kwance yake sambal sanye da dogon wando kirar Dolce and gabbana Yayinda bakin fatar sa ke ta shining da glowing wanda kallo daya mutum zai masa ya fahimci ba k'ananun kudi yake narkawa wurin gyaran fatar sa ba. Ga kwantance gashi dake kwance luf kuf a k'irjinsa, Yayinda kansa mai dan tauri irin na yan Africa ke ta shining da kyalli, ya sha wani askin zamani daya fara fidda zallan kyawun sa.





Cikin matsanancin kewar ta, da zunzurutun sonta dake dawainiyya dashi kusan shekara daya da watanin kenan.



Lumshe kyawawan idanun sa masu haske da kyau yayi, kana ya bud'e su,,, ya sauke kan zanen hoton ta dake kafe a ko wani bango na dakin.....



Share

Comment

Vote


Noor Eemaan
07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*




🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)



*WATTPAD*
@NoorEemaan








EDITING IS NOT ALLOWED❌



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



Page 47-48

Ɗan cije leɓen sa yayi, yana jin matsanancin kewar ta, na cigaba da ratsa jijiya, soƙa, da jinin jiƙin sa.





A hankali ya sauke black shining legs d'insa kasa ya mike, cikin tafiya mai cike da aji da kasaita ya karasa gaban hoton ta ya kura mata idanun sa masu cike da tsantsar kaunar ta, a hankali ya dan ranƙwafo tamk'ar ita ɗin ce a gaban sa ya bawa zanen wani hot kiss mai tafiya da hankali.



A hankali ya motsa bakin sa can kasan makoshi ya furta "I miss you badly!"



Zura hannuwan sa yayi cikin aljihu yana bin ko wani hoton ta da kallo ɗake manne a bangon. Ƴa jima sosai yana kallon hoton kana ya nufi had'add'en bathroom d'in sa, ba dan ya gaji da kallon su ba...





Cikin nutsuwa ya sauke wandonsa kasa, ya jefa a washing machine kana ya nufi gaban shower ya kunna, ruwan ya shiga dukan naked black shinning body d'insa, domin sam baya ra'ayin shiga jaku'zzie (jaccuzi) yau.
Lumshe kyawawan idanun sa yayi yana jin dadin saukar ruwan a jikin sa, duk da ruwan sanyi ne, ga kuma lokacin da sanyi a gari, amma sam bai damu ba, domin ruwan sanyi ba bakon sa bane...




Hada'dd'en bar soap ya fara murzawa a baki Kuma lafiyayyen fatar sa, domin bai fiye son shower gel ba a yawan lokuta, ya dauki 30minutes yana wankan kana ya fito da bathrobe fari kal yayin da ruwa ke diga a sumar sa mai yawa....




Lotion daya dace da black skin d'insa ya shafa a fatar sa, kana ya fito da boxer hadi da white singlet ya sanya, perfume na company'n *black gem* mai suna *TRINITI MEN POUR HOMME* ya fesa kana ya sanya wasu had'add'un English wears, wando jeans baki, sai wata riga daya kama shi red color ya sanya, sai canvass black irin na maza duka dai na company'n *NIKE* .
Agogon *luxury brand* sliver color ya sanya, oiling din kan shi yayi ya taje. kana ya fesa hair spray.




Wani stylish sunglass brown color ya sanya a fuskar sa, komai cikin nutsuwa yake yi, tamkar yanda ya kasance mai nutsuwar, sai dai a yanxu komai nasa ya Sanja ya zama cikin class yake yin sa.




Had'add'un wayoyin sa ya dauka kana ya fita, nan ma'aikatan sa suka shiga gaishe shi, a nutse kana a mutunci yake amsa musu, cikin sauri motocin sa dake fake reras guda goma sha ɓiƴu ya nufi daya ɗaga ciƙi, kafin ma ya karaso sun bud'e masa, shiga yayi kana bodyguard's ɗin sa suka fada sauran motocin. Sun yi tafiya mai tsayi kana suka iso babban gate din da aka jima da wangala musu shi....




Still dai akwai tafiya mai tsayi kafin suka iso babban titi, kamar yadda rashin magana ya zama dabi'a a gare shi yanzu, ya bud'e baki yace


"Abuja gidan alhajina muka nufa" ya fada a tak'aice.



"Noted sir!"


Driver ya fada cikin girmamawa, nan ya dauki hanyar, hakan yasa sauran motocin fahimtar cewa gidan alhajin zasu...





Sunyi tafiya mai nisa, domin tsakanin Lagos da abuja akwai 'yar tafiya hakan yasa basu isa da wuri ba... Ba kuma ya son hawa jirgi a Cewar sa.



Fadin kyau da tsaruwar gida alhajin bata lokaci ne, sanin waye shi da matsayin sa a gidan hakan yasa suka wangale masa gate din. Take motocin sa mai dauke da sunan *FFM* a ɓaƴa suka shiga faka motocin su a haraɓan giɗan kasancewar ba jimawa zasu yi ba.





Bud'e masa motar suka yi ya sauke kafar sa, kana ya fito gaba daya, Cikin tafiyar kasaita hadi da tsantsar aji ya nufi general falo, inda anan yake sammanin alhajin yake.




Ya kuwa same su tare da yar tsohuwar matar sa, sai dai kasancewa suna da dukiya da su kansu basu san hadadin sa ba ya boye shekarun su matuka.





Murmushi alhajin ya sakar masa haka ma matar sa, shima martani ya mayar su, Cikin tsokana kamar yadda alhajin ke kiran sa yace "the great younger billionaire, har ka iso?"




Kujerar dake kallon nasu ya zauna kana ya dan rissina a zaunen cikin girmamawa yace "barka da rana alhajina, barka da rana hajiya"




Hade baki suka yi wurin amsawa kana alhajin yace "yanzu zamu tafi lagos din, amma ta flight zamu, already a can zamu hadu da su alhaji Aminu a airport din, ka sanar da guards dinka suyi gaba, ko angon fadeelah?" Murmushi mai taushi ya saki yana jin farinciki mara mitsaltuwa da sunan karshen da alhajin nasa ya kira sa.







Take ya fidda tsadaddiyar wayar sa ƙirar *Vertu Signature Cobra* ya sanar wa shugaban bodyguard's d'insa cewa suyi gaba....





Take ma'aikatan gidan suka cika masa gaban sa da kayan snacks dana marmari, bai wani ci da yawa ba ya ture, domin shi ba ma'abocin yawan cin abinci bane dama can.



Bayan awan sa ɓiƴu da zuwa gidan. Alhajin ya ƙoma part din sa ya sanja kaya zuwa shadda tsaɗaɗɗiƴa, dinkin babban riga kasance cewa dama da kananun kaya yake zaune tun ɗazu.



Nan suka yi sallama da hajiya tayi musu fatan dawowa lafiya kana suka fita. Motocin alhajin ne suka kai su airport babu jimawa jirgin su ya daga zuwa lagos...





Bayan sun sauka, nan suka tarar da alhaji Aminu da alhaji Abdallah. Take suka shige motocin sa wanda already bodyguards din sun isa lagos ɗin.




Haka ya lumshe idanun sa Cikin tunani barkatai ɗa suƙa cika kwanyar sa, sai dai yana jin farinciki domin yana ganin cewa zai mallaki muradin ransa soon.




Basu dauki tsawon lok'aci ba suka iso estate din professor Imran mai naira. Nan take motocin sukayi parking a tsakiyar haraban gidan...



Har suka iso bai bud'e idanunsa ba, sai dai tsayuwar motocin ya tabbatar masa da cewa sun iso kenan.


A hankali ya ware idanun sa da suka fara Sanja launi. Tuno a yanda, da ƙuma yanayin daya bar gidan a wasu loƙuta ɗaƴa shuɗe ya sanya kwalla ciko idanun sa, a hank'ali ya fito yana jin faduwar gaba na abubuwa da dama, amma sam bazaka fahimci hakan ba Saboda jarumtar sa....



Wajen su alhajin ya karasa ya tsaya, ganin cewa babu dacewa su shiga kai tsaye hakan yasa alhajin kiran wani security dake ta shawagi a farfajiyar gidan, Cikin girmamawa security ya karaso domin yaga wadannan mutanen ba kananun mutane bane.





"Am... Is professor Imran around? I mean your boss" Alhajin yafada domin yaga siffar sa irin ta yare ce wanda da alama ma baya jin Hausa...



"Yes! Yes Sir" security'n ya fada cike da girmamawa.



"Ok please sanar dashi yana da baki urgent"



"Ok sir" security ya amsawa alhajin.



Babu jimawa ya fito yace professor ya ce su shigo...




Gabadaya suka nufi inda suka ga security'n ya fito, hada'dd'en falon Daddy suka zauna suna jiran fitowar sa, domin falon ba kowa suka same shi...



Bayan mintuna biyar takun takalmin daddy ya fara kusanto su, hakan yasa yaji gaban sa ya yanke, sai dai ba kamar baya ba, domin tuna irin abinda ya faru a irin wanna yanayin ne ya dan daga hankalinsa, sai dai kansa na kasa bai dago ba, hakan kuma mutum bazai fahimci yanayin sa ba ɗomin idanun sa na sanye da sunglass ne.





Dan waro ido Daddy yayi a lokacin da yayi arba da Alhaji Sufyan Rufa'i mutumin da ko ina ake fadin arzikin sa, yana da uban dukiya mai ban mamaki, sai dai bai d'aura wa kansa girman kai ko wulakanta mutum ba, ya dan yi mamaki ainun ganin sa Cikin estate din nasa, kuma a falon sa....



Karasa yayi ya mika wa alhajin Sufyan Rufa'i hannu cike da girmamawa, haka ma sauran aminan sa suka gaisa.


gaishe shi wanna saurayin yayi, Daddy ya amsa a sake cikin kulawa.


Nan Daddy ya zauna su ka dan taba hira irin na manyan mutane, kana alhaji Sufyan ya yi gyaran murya yana kallon Daddy yace "hakika Imran na san munyi wani abu da bai dace ba, duk da ta wasu bangarorin iɗan aka duba babu laifi, amma a gaskiya munyi nema cikin nema ne wanda a ka'idar addini musulunci haramun ne, amma dana ya jima yana kaunar 'yarka, so bana wasa ba, ya rayu da kaunar ta, matuk'ar aka bari fadeelah ta auri wani toh ba shakka zan iya rasa Dana, domin kaunar da yake mata. mune dai magabatan yaron da aka fara kawo lefen sa. Ina fatan zaka yi wa magana ta duba ta fahimta" alhaji Sufyan Rufa'i ya karasa yana kallon Daddy...



Shiru Daddy yayi, wani yanayi daya kasa fassara shi ya shiga ratsa shi, hak'ik'a ba zai iya kallon fuskar alhajin yace bazai iya bawa dansa auran Fadeelah'n ba. Domin alhaji Sufyan Rufa'i mutum ne da wasu masu arzikin ma ke fatan ya rabe su. Babban damuwar sa shine amminin sa minister Sa'id bai san yanda zasu ƙarƙe ba.


Kallon sa ya kai ga dan Alhaji Sufyan dake zaune yana dan danna wayar sa a wanna karon, tabbas wanna shine surukin nuna wa sa'a, Daddƴ ya aiyana a ransa...





Kallon alhajin yayi yace "ba matsala alhaji Sufyan, naji bayanin ka, sai dai akwai yaron minister Sa'id da aka samu musu rana tare, amma zan tattauna da aminin nawa Sa'id, in Sha Allah babu wata matsala" Daddy ya fada cikin taɓɓaci.





Saurayin nan kuwa cak! Ya tsaya a lokacin da Daddy ya ambaci dan minister, wani matsanancin kishi ya dirar masa, sai dai sam mutum bazai fahimta kai tsaye ba.






Haƙa dai suka cigaba da tattaunawa akan maganar auren, inda suka yanke cewa ayi bikin nan da sati biyu kamar yadda aƙa saka ɗa farƙo.



Bayan sun gama maganar ne, suka yi musabaha hadi da sallama cike da mutunta juna kana suka fice gaɓa ɗaƴa har Daddy'n.



A haraban inda motocin su suke faƙe suka tsaya, shi kan shi Daddy ya jinjina yawa da tsadar motocin.



Bayan Daddy ya koma ciki ne alhaji Sufyan Rufa'i yace ƙalli saurayin cikin zolaya ƴace "toh angon two weeks mu zamu koma kauyenmu(abuja), amma ƙa ɓamu aron motar ka daya zai ajiye mu a airport idan babu damuwa yallabai" alhaji ya karasa a zolaye Yayinda alhaji Abdallah ɗa alhaji Aminu suka sanya musu dariya...



Cikin wani haɗaɗden muryan sa, da amon ya sanja fiye dana baya yace "ni Alhajina kana sani kunya, umarnin ya kamata ka bani, take zan aiwatar da abinda kake so, zan ma kai ku airport din da kaina" saurayin nan ya fada.



"A'a a'a karka damu, driver daya ma zai ishe mu zuwa airport din, kaima ka wuce naka unguwar ka huta (haka yake cewa gidan nasa saboda tsananin girman sa)"




Murmushi daya bayyana white teeth d'insa yayi, domin ya san alhajin nasa da zolaya, a fili kana murya kasa-kasa yace "Alhajina ina son ganinta, kewar ta zai min illa idan na tafi ban ganta ba"



Jinjina kai alhaji yayi duk da sun yanke hukuncin sai bayan daurin aure zai bayyana Kan shi gare ta, amma ya fahimci yanayin sa, hakika is not easy at all...



"So kenan ya zaka yi? Kasan dai yanda muka tsara komai, bana son a samu matsala, idan ma za a samu is better ko bayan daurin auren ne duk abinda zai faru ya faru, yanzu kayi hakuri muje nan da sati biyu ne ƙawai, she will be yours for ever in Sha Allahu"



Cikin gamsuwa ya jinjina kansa, kana suka shige motocin suka bar estate din.





Bangaren Daddy kuwa bayan ya raka su alhajin ya dawo cikin falon sa, ya ga kiran minister Sa'id, cikin dan sanyin jiki ya dauka, yana shirin yin maganar ƴaji muryar minister "hello professor ya haka? Abinda kayi yayi daidai kenan? Dama kasan cewa akwai wanɗa ka riga ka bawa auren 'yarka amma ka bari dana ya bata lokacin sa a kanta...."




Taran numfashin sa daddy yayi da cewa "minister calm down ba haka bane, sam bana da masaniya kan kawo lefen ko wani da na bawa auren fadeelah, bayan Jameel. ina taƙaice maka ƴanzu nan alhaji Sufyan Rufa'i suka bar estate ɗina domin dan sa ne ke son Fadeelah'n"


Daga dayan bangaren dan zaro ido minister Sa'id yayi, domin indai alhaji Sufyan Rufa'i babban kasuwar da Duk duniya tasan shine tofah akwai matsala...




Cikin basarwa yace "wani alhaji Sufyan Rufa'i din?"




Daddy yace "babban dan kasuwar nan dai shi nake nufi, a gaskiya na kasa ce masa a'a, sanin kanka ne alhaji Sufyan Rufa'i ba irin mutanen nan bane da mutum zai ki mu'amala dashi bane, domin girma da darajar sa a duniya ba kadan bane..."




Cikin fushi minister Sa'id ya katse Daddy ɗa cewa "yanzu professor Saboda ka ga wanda ya fi dana dukiya shine zaka yi mana butulci? Toh ka sani wallahi tallahi ba za a yi haka dani ba, Jameel ɗai Fadeelah Yake so, kuma dole ita zai aura, wanna ai tozarci ne, ko ta halin kaka ne ƙuwa, ka rubuta ka ajiye jameel sai ya mallaki 'yarka!"





Ran Daddy ya baci, dama arziƙin abota minister Sa'id yake ci shiyasa yayi masa Shiru tun dazu



"Kaga minister ya ishe ka haka! Fadeelah 'yata ce, kuma yanzu nace ba zan bawa danka ba, dan alhajin zan bawa, dama can Ni na lallashi princess ta amince da auran Jameel din, ɓa so taƙe ba, toh yanzu nace na...."



_i'm seeing a lot of msgs and comments, Amma ban san wanne zan yi reply ba saboda yawan su, but naji dad'in addu'o'in ku da fatan alkhairin ku gareni, love You all_❤️🥰



Share


Comment


Vote


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN

Please Login or Register in order to submit comment