Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hada breakfast sun jera a part di'n Mommah domin mafi yawan lokuta anan suke breakfast, Daddy ne ya shigo sanye da wata shadda tsad'add'e sai maiko take, Mommah da ke zaune a parlour ta dago k'anta, ganin shine sai ta dauke ƙai, murya a daure ta gaishe shi, da murmushi a fuskar sa ya amsa, kana ya d'ora da tambayar ina Fadeelah, bata bashi amsa ba ta daga tsadaddiyar wayarta ta dora a ƙunne hadi da cewa

"hello! sweetheart breakfast is ready, muna jiran ki"


"Mommah am ok, bana jin yunwa" daga dayan ɓangaren fadeelah ta karasa cikin damuwa, sanyin muryar, hadi da shagwa'ba, har wani bata fuska take.






"I said ki zo muyi having breakfast, me kika ci da zaki ce you're ok?" Mommah na gama fadin haka ta yanke kiran.




Professor da ya zuba wa Mommah ido baya ko kiftawa ya lumshe su, hakika yana matuk'ar son matar shi, yana kuma son su dawo kamar da, amma ya rasa me zai ce mata, babban abin da yasa ta samu muhalli a zuciyar sa shine tsananin son da kauna da take yiwa tilon 'yar sa.....




Daga bangaren Fadeelah kuwa, a hankali ta mike tana bata fusk'a, sanye take da wasu riga da wanɗo masu taushi ash color, na company *NIKE* hular rigar ta rufe dogon gashinta ɗashi, kana ta tsaya gaban zanen Fadeel, sumba mai tsayi ta manna masa a labb'ansa, kana ta maida duban ta ga zanen Mahmah, tuna mahmah yasa hawaye zuba daga idanunta, Sumba itama ta manna mata a goshi da kumatun ta, kana ta bar dakin tana daidaita nutsuwar ta hadi da share hawayen ta.





Elizabeth ta tarar tana gyaran hada'dde kuma yalwataccen falon ta, murmushin ƙarfin hali ta sakar wa Elizabeth d'in, martani Elizabeth ta mayar mata kana cikin turanci tace

"ma'am good morning"


"Morning Elizabeth" fadeelah ta amsa kana ta bar part din.


Da kallo Elizabeth ta bi fadeelah ita dai
Allah ya d'ora mata kaunar fadeelah, ba kuma komai ya janyo hakan ba, sai rashin wulakanta mutane da bata yi, tana ƙuma mata fatan Allah ya yaye mata damuwar ta, domin ta fahimci tana ɗa damuwa.
A fili kana a hanƙali tace

"ohh wanna rayuwar, kowa da kalar ƙaɗɗarar shi"




******



"Good morning Dad!"
" Good morning Mommah"


Fadeelah ta fada a tare, tana zama gefen su, amsawa suka yi fuskar ko wannen su dauke da murmushi...



Mommah ce ta fara mikewa ta isa dinning table din, sannan Daddy da Fadeelah suka Mike su ma...



A nutse suke jin abincin su, baka jin karan komai sai na spoons, fork, da knife. Sun yi nisa a cin abinci amma, banda fadeelah da ke tsakura kadan-kadan, daman ita ba gwanar cin abinci bace, yanzu ƙuma rashin cin abincin ta ya sake raguwa fiye dana da.



Gyaran murya Daddy yayi, idanunsa kan na mommah yace "Nan da jibi in sha Allah za a yi baikon *FADEELAH DA JAMEEL* sannan bayan aminina Sa'id ya dawo daga Qatar za ayi bikin nasu, wanda ina jin zai iya daukan shekaru d'aya ko wata goma kafin ya dawo".








Wani kwarewa fadeelah tayi, Yayinda k'irjinta ke bugawa da k'arfin gaske, cikin sauri daga Daddy har Mommah suke kokarin sanya mata glass cup mai dauke da ruwa a baki, Daddy'n ne yayi nasaran bata, sosai ta sha ruwan tana sauke numfashi Yayinda ta ji dakin na juya mata....



Sosai itama Mommah taji ba dadi, amma ya zasu yi kaddarar ce ta zo da hakan, kallon fadeelah tayi ɗa hawaye ke daf da zuba a idanunta, girgiza mata kai tayi kana tayi mata alama da ido kan kar tayi magana sannan kada ta bari Daddy ya fahimci halin da take ciki.....




_karku manta wanna novel din ba sabo bane, zaku iya samun complete din sa a Wattpad_😘



Manage pls🙏❤️😫


Afuwan habibtie's in sha Allah daga yanzu ranakun posting sun dawo sau uku a sati, domin wallahi busy da nake ciki ya sanya hakan, bana da lokaci kwata kwata wallahi, ku tayani add'ua kan abinda nake yi yanzu, Allah ya bani sa'a.
ina fatan zaku min haku'ri... Ranakun posting din sune kamar haka monday, Thursday, Sunday. Amma matuk'ar na samu lokaci a sauran ranakun da ban ambata ba, toh zaku iya ganin update, amma kusa a ranku cewa ranakun dana ambata wato litinin, alhamsi, da lahadi suna ranakun da tabbas zaku ga posting.






Ngd sosai da kauna da kuke nunawa books dina, ku sani a addu'oi'n ku👏 Noor na muku sahihiyar kauna💞










#Share
#Comment
#Vote


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*




🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*


*Wattpad*
@NoorEemaan


EDITING IS NOT ALLOWED❌


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

*(Assalama alaykum ya jama'a ina gaida ku my fans a ko ina kuke a duniya da Wanda na sani da wanna ban sani ba. Na fara posting din novel dina na farko mai suna RAYUWAR FAHEEMAH nasan wasu sun fara karantawa, wasu kuma sun karanta... dalilin daya sa na sake reposting din labarin Saboda abubuwan daya kunsa, Wanda zan so kowa ya karanta ya amfana, sannan a lokacin da nake littafin mijin Ammina ne sila nayi posting dinshi, sai dai rashin lokaci yasa nake turowa da yawa wani har readmore goma, fiye da haka ma nayi posting a lokaci d'aya, ma'ana complete din labarin na dawo dashi page 10 gaba daya kana a kwana goma. Hakan yasa bakowa ya karanta ba, Saboda yana da yawa sosai, shiyasa yanzu na sake reposting din shi, a yanda yake page by page. A cikin labarin akwai fadakarwa, wa'azantarwa, tsantsar mugunta, soyaayya mai tsafta da babu algus a ciki, da dai sauran su. Dan haka ku biyo ni comment dinku kadai nake bukata already ina da complete din novel din)*


Page 41-42


..........jinjina wa Mommah kai fadeelah tayi tana kokarin rarrashin k'anta.
Daddy ya kalli Fadeelah zai yi mata magana wayar sa ta fara ringing, hakan yasa ya mike ya fita ba tare da yayi maganan ba, kasancewar yana da appointments da wani business partner din shi....




Fadeelah na ganin fitar Daddy ta fashe da kuka mai ban tausayi, taso wa Mommah tayi ta dawo kujerar dake kusa da na fadeelah'n. cikin rarrashin ta shiga yi mata da kalamai masu kwantar da hankali, hadi da nuna mata amfani da tasirin bin umarnin mahaifi....




******** ******** *******


*RANAR BAIKO*



Zaune fadeelah take fuskar ta ba walwala gaban wata kwarariyyar make up artist tana tsantsara mata kwalliya...


Fadeelah kuwa daurewa damuwar ta take Saboda kada mutane su fuskanta, a yau daya kasance ranar baikon ta da Jameel sai ta rasa k'arfin guiwar cewa ɗa saƙa ran Fadeel dinta zai dawo gareta....





A wani had'add'en hall da a masu hannu da shunin ma ba kowa zai iya kama wajen ba saboda tsananin tsadar wajen...



Fadin kyau da haduwar wajen bata baki ne, haka zalika yawan mutanen da suka hallacin wajen bazai fadu ba, kai kace bikin ake ba baiko ba.



Sosai fadeelah tayi kokari wurin jure damuwar ta, Yayinda Jameel dake gefen ta sai faman shige mata yake....



Bata nuna komai ba, sai murmushi yake wanda na k'arfin hali ne. Domin sosai Mommah ta ja mata kunne kan kada ta Nuna komai domin ƙaɗa jama'a su fahimta





Sai takwas na dare suka tashi daga taron, bayan anyi fixing date din biki shekara daya, wanda a dalilin tafiyar minister Sa'id din yasa a kasa lokaci mai tsayi har haka.





Bangaren Daddy kuwa ya dan samu farinciki da nutsuwar zuci, ganin cewa anyi baikon Domin a tunanin sa idan fadeelah ta auri Jameel din zata manta da fadeel din.



Domin sarai yana lura da walwalar ta ya ragu sosai. Amma ina bazai iya bata abinda take so ba, wato auren wanna baƙin talaka fakiri a Cewar sa.





***** ****** ******




Fitowar ta daga wanka kenan sanye da bathrobe Yayinda k'anta ke sanye da *shower cap* lotion ta murza kadan a farar fatar ta, wani tsad'add'en oil perfume ta shafa a jikinta, kana ta taje k'anta hadi haɗi da yi masa oiling ta yi parking din shi ta gefe.




Closet dinta na zallan glass ta zuge ta ciro wasu had'add'un English wears na company *Armani* gown ne mai tsukakken sama Yayinda kasan ya bud'e sosai white color.




Hada'dd'en Falon ta ta fito ta zauna tunani Fadeel dinta makale a ranta, tuno wasu lokuta da suka yi having a baya yasa hawaye hadi da murmushi suka subuce mata a lok'aci daya...




"Shikenan my one ka tafi kenan, shikenan bazan kara ganin ka ba, shikenan bazamu mallaki juna ba, shiƙenan bazamu cikawa Mahmah burinta ba...?" A fili take wadanan kalaman hawaye masu zafin gask'e na zubo wa daga cikin su....



Wayar ta dake kan cinyar ta ya dauki kara, hawaye fusk'ar ta ta sharen ta, kana ta kai idanun ta kan fuskar wayar, number'n jameel ta gani, wani bata rai tayi Yayinda zafin da zuciyar ta ke mata ya karu.



Kamar tayi rejecting call din, sai kuma tayi picking ba tare da tayi magana ba...



"Ina part din baki" abinda taji jameel din ya fada kenan.




Ta kai mintuna goma a zaune kana ta mike cikin dauriya ta yafa veil kana ta fice cikin sanyin murya jiki domin sam bata da kasala ko daya a jikin ta.




Bayan yan mintuna ta isa part din, domin akwai dan nisa tsakanin part di'n ta da part din baki...


Kamar kullum yana Hakim ce kan daya daga cikin had'add'un kujerun falon. Kallon daya zaka masa ka fahimci cewa shi din dan nasu kudin gaske ne.



Da wani mayen kallo yake binta dashi, Yayinda murmushi ke shimfud'e a fusk'ar sa. Sanin darajar Sallama yasa fadeelah tayi masa, ya amsa still idanun sa kafe a kanta, mikewa Yayi ya isa gabanta daf da ita kamar zai shige mata jiki, dan jan baya tayi tana daure fuska.




Cak ya tsaya, kana ya dan bata fusk'a yana cewa "come on! Babe kamar ba wayayya ba, miye a ciki, just want to hug you.
kin manta an mana baiko yanzu?".




Hararar da bata san ta iya ba ta jefa masa kana tace " please and please na roke ka, bana so! Na sha gaya maka bana son irin wanna wayewar mudin shine wayewa, dan anyi mana baiko ba shi ƙe nufin cewa kana da right din taba wani sashe na jikina ba" ta karasa cikin fada, dama ranta a bace yake.





"Oh! Babe ni kam kina bani mamaki, wasu talakawan ma yan kauye suna da wayewa kan wanna fanin ɓare ke, meye a ciki? Bafa wani abu zan yi miki ba, fine naji zan hakura har muyi aure, amma ki bari even kiss da hug (sumbata da runguma) ki bari nayi miki mana meye a ciki uhm" ya karasa cikin sigar lallashi, hakika so da sha'awar fadeelah na cin sa sosai, ta kuma ki bashi damar ya dan kashe kishiruwar sa ko kadan ne...




"Ba wani abu a ciki kace? Ko dai kana take sani ne wanda haƙan zunubi ne babba, kasan abu ba kyau still kana aikata shi, Toh ni bazan iya ba, domin wanna zunubi ne, kai ma ina mai baka shawara ka daina aikata hakan"




Wani murmushi ya saki yana shafa gemunsa, bawai maganganun ta sun shige shi bane, domin shi bai yarɗa cewa akwai zunubi cikin kiss da hug ba. Shiru yayi na mintuna biyu kana yace "OK fine, ki zo mu fita outing ko?"

"No Thanks! Bana bukata, if you don't mind I will take my leave now, Excuse me" tace bayan ta jefa shi da wani kallo ta bar part din gabadaya....




Da kallo jameel ya bita, duk da yaji ba dadi yanda ta fice, bayan yau yazo da niyyar zai dan kashe k'ishiruwar sa, a tunanin sa tunda anyi musu baiko zata dinga amince da shi.(kaluɓale ga yammata, ɓa wai dan anyi muƙu baiƙo ko sa rana da saurayi ki amince ya dinga taba ki ba, haƙan zunubi ne, kuma taɓɓas bazai ga darajar ki ba, Allah ya sa mudace ya tsare imaninmu, ya bamu ikon koyi da hali irin na fadeelah)





Bayan fadeelah ta koma part dinta, sosai ta sha k'uk'a, ɗomin tsaf ta fahimci Jameel din, Abinda fadeel dinta bai taba gwada yi mata ba kenan. Ta ya ya ma zata iya son wani da namiji bayan Fadeel? Mutumin da ke mata tsabtattaciyar kauna da babu algus, hakika samun irin su fadeel dinta a duniya yana da wahala.
Haka ta wuni kuka hadi da tunani barkatai.






*BAYAN WATANIN TAKWAS*


Haka rayuwa ta cigaba da juyawa, Wasu na farinciki, wasu na walwala, sai dai babu farinciki mai dorewa a rayuwar ko wani bawa, dole Akwai ranar da mutum baya samun farinciki, ko ya tsinci kan shi a yanayi mara ɗaɗi.





Ta bangaren Fadeelah kuwa babu abinda ya Sanja daga damuwar da take ciki sai ma abinda ya karu musamman tuno cewa kwanakin aurenta da Jameel yana ta gab ɗa ciƙa, domin sauran watanin hudu yanzu haka, ga har yanzu babu wani labari game da fadeel din, number'n sa ma baya zuwa, ta kuma ki hakura da kira duk da tasan cewa number'n bata shiga.....




Gaba daya komai ya gama fice mata a rai musamman da babu gwarzon masoyinta Fadeel a kusa da ita......





Manage please🙏 a tsaye ina ciƙin tafiya nayi muku wanna din ba yawa.


In sha Allah ranar lahadi ma zan sake muku sabon update kamar yanda nace.




Thank for reading my novel
Kyautar koda




NOOREEMAAN
07082281566


Share fisabilillah

Comment

Vote


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*




🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*


*WATTPAD*
@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


_ina ta ganin karin followers a Wattpad, which I'm very happy, jazakallahu khair masu following, wandanda basu yi ba, Please do follow me on Wattpad, @NoorEemaan thanks.👍🥰




Page 43-44

Misalin ƙarfe takwas na safe ne, Fadeelah na kwance a dakin ta, kewa da zafaffan soyaayyar gwarzon masoyinta Fadeel ke nuƙurƙusanta, ƴayinda hawaye masu zafin gasƙe ke zuba a cikin idanuna ta....




Take tunanin zuwa gidan su fadeel ya zo ranta, tana fatan iɗan ta je ta ganshi a bud'e, ta kuma samu fadeel ɗinta a cikin gidan...



Cikin wani kuzari daya zo mata ta mike ta fada bathroom bata wani jima ba ta fito, lotion kadai ta murza kana ta sanya wani palazzo trouser pink da riga black, wani hada'dd'en jacket kimono ta sanya kana ta rufe kanta da wani siririn mayafi, tsad'add'un takalmi da agogo ta sanya, body spray mai sanyin k'amshi ta fesa kana ta bar dakin......




Tana fitowa ta ga bodyguards dinta tsaye, ganinta ya sanya suka yi nufe ta, hada'ɗɗen mota silver color ta nufa, waiwayewa tayi ta kallesu kana tace
"am karku damu yanzu zan dawo" A yanɗa ta ɗaure tayi magana zaka yi zaton ba taɗa ɗamuwar ƙomai.



Cikin girmamawa daya daga cikin su yace "please ma'am kiyi hakuri ki barmu muyi aikin mu, domin idan boss ya samu labari ke kadai kika fita, toh zamu shiga matsala wanda zai iya kaimu ga rasa aikin mu"





Tausayin su taji ya kamata, ajiyar zuciya ta sauke, domin Daddy baya gari, amma taɓɓas zai san ita kadai ta fita.



"Ok fine muje" Fadeelah tace musu haka, domin bazata so a dalilin ta su rasa aiƙin su ɓa.




"Mun gode ma'am" suka ce fuskar su dauke da murmushi.



Itama murmushi tayi kana ta fada motar bayan daya daga cikin su ya bud'e mata, a jere reras kamar ƙullum motocin suka bar gidan...


*******



Abinda ya sanya gabanta matsanancin bugawa bayan isar su kofar gida shine ganin kofar gidan a kulle still da kwado kamar waccen karon, hawaye masu zafi ta share, sosai ta daure bata yi kuka ba domin guards dinta dake wajen....




Mota ta fada ta umarce su da cewa su tafi gida, haka ta dinga kallon titi tamkar mai ƙirgin motocin da suƙe falfala gudu kan titi, sai dai sam ba motocin take kallo ba, tunani mai zurfi ta fada....




Bayan sun isa gida ta nufi part di'n Mommah domin a nan kadai zata samu nutsuwa, domin jin kanta take tamkar zai rabe gida biyu Saboda tsananin ciwo....





Jiƙin Mommah ta faɗa ta shiga rera kuka sosai gwanin tausayi, buɓɓuga bayanta Mommah keyi ba tare da tace komai ba, domin ta riga ta san damuwar Fadeelah'n baya taba wuce na Fadeel ɗinta, har yamma tana part din, Mommah taki barinta ta tafi part din ta saɓoɗa ƙaɗa damuwar tayi mata yawa.






****** ***** ***** *****




Haka ta cigaba da jinyar zuciyar ta tana kokari matuk'a gurin yin tawwakali hadi da yarda da kaddarar daya shigo rayuwar ta, add'ua kam kullum sai tayi shi kan Allah ya bayyana mata Fadeel domin bazata iya rayuwar aure da Jameel ba, baza ta iya ba, domin shi mutum ne da bai da kyakyyawan halayya da duk macen kwarai zata so......





*BAYAN WATA HUDU*


A Yau minister Sa'id ya d'ira a Murtala international airport ɗaƙe Lagos, gabadaya airport din cike yake da mutane masu hannu da shuni wadan da suka zo taryar sa, cikin su kuwa akwai Jameel da Mummy'n sa sai wasu yan yan'uwansa na jiki, bayan yan gaishe gaishe daya wakana tsakanin mutanen da suka zo taran sa, da yi masa barka da dawowa ya fada daya daga cikin motocin dake jere reras, haka zalika Jameel da Mummy duk cikin motar ta minister ya shiga suma suka shiga inda sosai jameel da Mummy suka nuna jin dadin ganin sa, bare ma Jameel daya san cewa tabbas yana gab da mallakar Fadeelah tunda dai shekaran dayan da Daddy yace ya cika gashi har ya dawo.....




Bayan duk yan sannu da zuwa su tafi, Jameel ya samu Daddy da maganar auran Fadeelah dariya irin nasu na manya minister sa'id yayi yace "my son kenan, zumudi yayi maka yawa, toh ina sane da kai, kuma ko sati biyu bazaka kara ba, zaka mallaki fadeelah"...




Cikin farinciki daya kasa boyuwa a fuskar Jameel ya rungume dad yace " wow! Dad thank you so much "



Har hangowa kansa yake yana making love da Fadeelah bayan anyi daurin auren su, domin ba kadan ba yake azabtuwa da matsanancin sha'awar fadeelah'n. shekara dayan nan daƴa wuce tamkar shekaru goma haka suka huce a idanun sa, amma yanzu sakayau yake jin sa zai samu abinda yake so, domin ba shi da aufi kan maganar Daddy'n sa...




Bangaren Fadeelah kuwa ta shiga tashin hankali mara iyaka, a ranar da Daddy'n jameel ya dawo daga Qatar ta gani an hasko a plasma, sosai ta sake shiga tashin hankali domin ba makawa za a yi bikin su da Jameel, ga Fadeel shiru har yanzu kusan shekara daya da watanin kenan.



Ta rame domin kallo daya mutum zai Mata zai hango zunzurutun damuwa a tare da ita, ko abinci bata iya kaiwa bakin ta, kullum Mommah cikin rarrashi da nasiha take mata.



*Bayan kwana uku*


Yau kwana uku da dawowar Daddy'n jameel, hakan yayi daidai da ranar da yan gidan su jameel zasu kowa lefe, gaba daya gidan ya cika da alhalin professor Imran mai naira har na Adamawa, ko ina security ne domin yanzu an karo su, Saboda biki da za a gudanar, sosai Mommah ta daure tana shiga sha'anin biki domin kada yan uwan Daddy sun fahimci bata son auran, domin har ga ranta bata son hadin Jameel da Fadeelah sosai take tausayin halin kuncin da damuwar da fadeelah'n ke ciki...




Misalin karfe sha biyun rana wasu tsad'add'un motoci guda goma sha biyu suka shigo cikin estate din professor Imran mai naira, tabbas duk wanda yaga motocin nan yasan ba k'ananun kudi aka narka wurin mallakan su ba, daya ɓayan daya mutanen ciki suka fara fitowa wanda zallan mata ne, sai drivers din motocin da suka kasance maza, nan mazan suka shiga fito da lefen ɗaga motocin wanda ya k'asance akwati hamsin ne cif masu kyau da tsari...



Nan aka yi ta shigar da akwatun nan tareda taimakon ma'aikatan gidan. Bayan sun gama shigar da akwatunan ciki ne sannan matan suka shiga ciki, nan aka yi gaishe-gaishe kana su Mommah suka gabatar masu da snacks, abinci, da drink's iri daban -daban wanda aka tanada domin su kadai...



Bayan duk sunyi abinda ya kamata aka sanya sati biyu masu zuwa, kana suka tafi cike da mutun ta juna, gabadaya yan'uwan professor da ma wadanda suka karbi lefe da ɗai sauran su babu abinda suke banda yaba lefen, duk da kasancewar su masu hannu da shuni amma tabbas ba ko wani mai kudi bane zai iya akwati har guda hamsin ba...




Bangaren Fadeelah kuwa kuka ta shiga rera wa sosai mai taba zuciya, domin taji hayaniyan yan kawo lefen, duk da bata fito ɓa, kenan da gaske zata tabbata Matar Jameel, ba muradin ta Fadeel ɓa? Kenan da gaske ta rasa masoyinta na gaske, mai so da kaunar ta domin Allah? Cikin karaji hadi da fitar hayyaci, a fili tace " Fadeeeeeeeeeeeeeel please ka dawo gareni, kada ka bari Jameel ya aureni, ka dawo mu mallaki juna, ka dawo mu cikawa Mahmah burinta, dan Allah ka dawoooo!" Ta karasa cikin kuka mai matuk'ar taba zuciya....






Bayan awa d'aya da tafiyar yan kawo lefe, wasu had'add'un motoci guda takwas daga gidan minister suka shigo cikin gida, dauke da lefe, bayan sun gama parking motocin aka shiga fito da lefen wanɗa ya k'asance akwati talatin ne, suka fara shigar wa cikin gidan....




Kallon-kallo aka shiga shiga yi tsakanin yan gidan su jameel da su Mommah, zuciyar ko wanne da tunani da yake, ba komai ya janyo hakan ba sai ganin akwatuna had'add'u guda hamsin dake zube a falon.




Kasa hakuri daya daga cikin yan'uwan professor Imran tayi tace

"bayin Allah shin ba ɗazu ƙuƙa kawo lefe ba?, ya muka ga an kawo wasu akwatunan?"



Sosai kan dangin minister Sa'id ya daure, wata tsohuwa daga cikin su tace "ai mu ma abinda ya daure mana kai kenan, domin ba mu muka kawo wadanccan lefen ba" tsohuwar ta fada tana nuna akwatuna d'azu....



Nan fa kai ya sake daurewa, aka shiga rudu, domin a tunanin su Mommah lefen da aka kawo dazu daga gidan su jameel ne, amma sai aka samu tsabanin haka....

To kenan su waye suka kawo lefe?

Nan take Grandma ta fidda tsadaddiyar wayar ta ta bugawa professor Imran mai naira kira....




*_Afuwan habibtie's nasan kuna kokari wurin jirana, taɓɓas nasan hakan, ina godiya sosai da kauna, rashin lokacin yasa bakwa jina kamar da, ma'ana bana posting k'ullum kamar da, da sannu zamu gama labarin, yanzu kyautar koda ya soma_*🔥🔥🔥




Nooreemaan
07082281566


Share
Comment
Vote

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*





🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*





*Wattpad*
@NoorEemaan







EDITING IS NOT ALLOWED❌



*Ina matuk'ar jinjina kokarin ki wurin yi min comment mai yawa kullum, therefore I dedicated is page to you my love(DARMA)*


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



#Suprise



Page 45-46

Cikin daurewar kai Grandma tace "Imran where are you? Ka zo yanzu, there is something fishy here"




Professor Imran dake tare da minister Sa'id a wani had'add'en wurin shakatawa ga Champaign da snacks zube a gabansu suna hira cikin wayewa irin ta aminan juna.
Cikin mamaki yace "mummy(Grandma) lafiya dai? toh gani nan yanzu, right away"





Idan sa na kan wayar yace "mummy na nema na yanzu, bara naje ma karasa maganar some other time" cewar Daddy.





"Toh fa, Allah yasa lafiya, ko dai mu tafi tare ne?" Cewar minister.




"No karka damu bari naje, zamu yi waya

Please Login or Register in order to submit comment