Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fawwalawa Allah komai, yana sane yana kuma ji, Sannan damuwa bata maganin komai. Da wanda zuciyoyin su ya dan yi sanyi.


Mik'ewa Mahmah tayi tace " 'yata me zan dafa miki?"

Murmushin k'arfin hali ta saki kana tace "ba komai Mahmah nagode"

"A'a A'a dole kici fa, ko kin bani zabi na girki miki duk abinda nayi niyya?"

Kasancewar bata son musu yasa tace "toh Mahmah"

Wajen madafa mahmah ta nufa ta fara kiciniyar dora musu girkin...

Ajiyar zuciya ta ji kusa da ita, hakan yasa ta kalli gefen ta, Fadeel taga ya matso kusa da ita, bata ce komai ba tayi kasa da kanta.

"My Darling" ya kira ta, shiru bata amsa ba.
"My Darling" ya sake kira nan ma shiru
'My Darling pleaseee" ya kira a karo na uku cikin magiya.

Idanun ta suka ciko da kwalla, a sanyaye kana a hankali tace "meye laifina? Me nayi maka daka zabi ka hore ni ta wanna hanyar? Ka tafi ka barni ba tare da ka tsaya munyi Kyakyyawar sallama ba, bayan kasan kwanaki mutuwa ta na kusanto ni, a haka kake cewa kana sona? Gashi ni na kasa jurewa nazo domin inyi sallama da kai ko hakan zai sa na samu salama a kabarina" Ta karashe maganar cikin wani mugun kuka daya taho mata. Saurin toshe bakinta tayi, domin bata son Mahmah taji sautin kukan nata..

Hawaye ke bin fuskar sa, ba kadan ba kalaman ta suka shige sa, bazata fahimci halin da yake ciki ba, shi kadai yasan halin tashin hankali da yake ciki right now.

Cikin murya kuka yace "am so sorry Darling, is not what you think, I swear you have no idea akan irin tashin hankalin da nake ciki, Fadeelah ban taba shiga tashin hankali irin wanna ba, duk minti daya da agogo zai buga, toh da zuciya ta yake bugawa, domin kwanakin mutuwar abar kauna ta, muradin raina yana kusanto wa" kasa karasa wa yayi Saboda wani mugun kuka d'aya taho masa mai karfin gaske, amma ya danne.

Sosai Fadeelah ta yarda da maganganun sa, domin cikin iyakar gaskiyar sa yayi ta, ita kanta ta rasa wa yafi son juna cikin su biyun???


Gaba d'aya kukan suke babu mai rarrashin wani, karshe dai Fadeel yayi k'arfin hali fara lallashin Fadeelah da kalamai masu sa nutsuwa da ratsa zuciya.

Shiru tayi sai ajiyar zuciya da take saukewa, abinda zai sanya ta farinciki yayi tunanin yi, mikewa yayi ya nufi dakinsa, ya dauko kayan zanan sa... Tun kafin ya fara zanen ta fara sakin murmushi, kasa da minti goma ya zana ta tsaf, hakan ya sanya ta cikin farinciki.

Kallonta yayi yace "my Darling ta ya ya kika gane gidanmu?"

"My one, kana tunanin garin masoyi yana nisa ne? Kana tunanin bazan iya bincikan inda kake ba? Kasani cewa inda so da kauna, komai zai iya faruwa, sannan komai zai yu, dan haka ka daina mamaki"

Cikin gamsuwa ya jinjina kansa kana ya sake cewa "Amma me yasa kika boye min wanna cutar taki har tsawon wanna lokacin?"

Murmushi mai ciwo tayi kana tace " dalilina shine, babu abinda hakan zai kara, na kuma boye maka ne saboda hankalin ka zai tashi, sannan ina tsoron kada ka guje ni, wanna cutar tawa ya kai shekaru masu yawa, haka na taso na ganni dashi, a lokacin da cutar yayi muni ne aka fara neman wanda zai siyar min da kodar sa amma ban samu ba. Haka dai doctor na Mahfouz ya cigaba da dora ni kan magani hakan yasa nake samun saukin cutar, sai dana je last check up result dina ya nuna cewa kodar ta lalace sosai haka zalika dayan ya fara tabuwa, ban sanar da kowa ba, domin dukkanin wani dangin nawa basa son tada maganar cutar koda na. Sannan Saboda tashin hankali da zan sanya mutane yasa ban sanar da kowa abinda Doctor Mahfouz yace ba. Ganin cewa kwanaki na na daf da karewa ne shiyasa nayi tunanin sanar da kai..." Ta kai karshe tana sauk'e wasu tagwayen numfashi.

Iska mai zafi Fadeel ya furzar tausayin Fadeelah fal ransa.

Haka dai suka dinga hirar su ta soyaaya, yayinda damuwar su ke raguwa a hankali, ana haka Mahmah ta dawo da dauke da kwanuka biyu masu d'auke da tuwo hadi da miyar kubewa, ajiyewa tayi gaban su tana cewa
"Allah yasa 'yata ta iya cin wanna abinci"


Murmushi Fadeelah tayi, tana kallon abincin, matsanancin tausayin su na ratsa ta, dama mutane na iya cin irin wanna cimmar kuma su rayu? Zata iya cewa bata taba ganin abinci irin wanna ba, a fili
tace "zan iya ci Mahmah nagode"
ita kanta kawai fada tayi, za dai ta gwada ci domin faranta ran Mahmah, domin taga kaunar ta mai tarin yawa a idanun mahmah'n, haka ita ma sosai matar da kwanta mata arai tana kuma sonta.

Murmushin farinciki Mahmah tayi, Allah kadai yasan tarin kaunar da take yiwa Fadeelah'n, kallon Fadeel tayi tace " My son kai mata abincin dakin ka domin ta samu taci abincin a sake"

"Toh Mahmah" ya mike hadi da kai mata abincin dakin.
Dawo da kallon ta tayi ga Fadeelah dake zaune kai a kasa tace "tashi 'yata kije ki ci abinci ko"

A kunyace ta mike ta nufi dakin sa.
Tsaye tayi cikin mamaki tana bin dakinsa da kallo, gaba d'aya zanen hotunan tane manne a bangon dakin duka.

Murmushi take yi yayinda idanun ta ke kafe kan nashi, daya bayan d'aya, ko wani bango take bi tana kallon hotunan ta, tama rasa wanne yafi kyau, farinciki ya cika zuciyar ta. Muryar sa taji yace "my Darling taho kici abincin".
Ba musu ta dawo ta zauna fuskar ta d'auke da murmushi.


" Thank you" tace masa

"Kin cancanci fiye da hakan my darling" ya bata amsa.

Bata kara cewa komai ba sai murmushi da ta yi...
A karo na biyu ta kai hannu da niyyar gutsiro tuwon domin taci ta kasa, saboda zafin sa.

Murmushi ya saki, kana ya wanke hannunsa ya gutsiro tuwon hadi da dangwalo miya, sai ya shiga hura iskan bakin sa cikin tuwon na yan seconds kana ya nufi bakin ta dashi... A hankali kana a kunyace ta bude bakinta ya sanya mata tuwon.

Dan lumshe ido tayi domin ta yi tunanin zata ji daci, sai ta ji tsabanin haka, domin duk da babu komai cikin miyar daga Maggi sai yaji domin ko mai babu, amma mutum zai iya ci... Haka ya cigaba da bata, har tayi loma biyar kana ta kauda kai alamun ta koshi. Bai ce komai ba, domin yaga mugun k'ok'arin ta, domin bai yi tunanin zata iya cin ko da loma d'aya na abincin ba.

" kai ma kaci?" Tace dashi.
Ba musu ya fara ci, shi ma bai wani ci da yawa ba ya rufe, saboda har yanzu ba wai hankalin sa ya kwanta bane, amma ganin ta ya rage masa wani kaso na daga cikin matsanancin damuwar da yake ciki.

Har shidan yamma Fadeelah na gidansu Fadeel, sosai wata shakuwa mai yawan gaske ya shiga tsakanin Mahmah da Fadeelah cikin wuni daya.
Sannan Mahmah ta debewa Fadeelah kewa, har take jin tamkar kada ta bar gidan...

Da zata tafi ta kawo kudi masu yawa ta bawa Mahmah amma sam taki karba, duk yanda Fadeelah tayi, Mahmah taki karban kudin.
Haka suka yi sallama cikin mutunta juna, sai a lokacin kukan Fadeelah ya dawo sabo domin ji take kamar sallamar karshe take yi dasu Fadeel, gani take kamar bazata kai sauran kwanakin daya rage mata ba.

Suna tsaye a kofar gidan su Fadeel, suna sallama cike da kewar juna, kuka mai suna kuka suke gaba daya, an rasa wa zai lallashi wani cikin su, karshe dai Fadeel ya bude mata murfin mota ta shige, kana ya kalleta murya a shake yace "zan kira ki idan kinje gida, I love you" yana fadin haka ya koma cikin gidan da mugun sauri.

Haka dukkanin gidajen biyun suka k'asance cikin damuwa, har garin Allah ya waye...


***★ ***★ ***★


Washegari Fadeel na zaune yayinda Mahmah tace "son ina so ka kwantar da hankalin ka, in sha Allah zaku rayu tare da Fadeelah har ku haifo min jikoki, bana son kayi wani abu akai hakan umarni nake baka, addu'a zaka cigaba da yi mata kaji?"

Jinjina kai yayi alamun gamsuwa
Shiru na yan mintuna Mahmah tayi kana ta sake cewa "ina son sake zuwa asibiti cikin satin nan, domin bana jin dadin jikina" wani shiru tayi kana ta cigaba
"ka kira 'yata kuwa?"

Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "eh na kirata, amma number ta baya zuwa tun jiya, amma bari na sake gwada wa"

Kara dialing number yayi har ya tsinke ba a daga ba, kara kira yayi a karo na biyu, yaji an daga.
amsar da aka bashi yasa shi mikewa zumbur gaban sa na wata mahaukaciyar bugawa....





_Gobe ma zanyi k'ok'arin baku sabon update matukar naga comments dinku, yeah two pages as promise, i love my fans_...



#share
#Edit
#vote

Editing is not allowed❌



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*



#NoorEemaan.

🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)


*Wattpad
@NoorEemaan

*EDITING IS NOT ALLOWED*❌


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


_akwai complete din labarin nan a Wattpad, ƙarku manta da following dina Please_😫❤️



Page 23_24

(Not edited)


Cikin wata murya da amon sa ke fidda zallan tashin hankali da yake ciki yace "mekika ce?" domin sam kunnuwansa basu yarda da abinda yaji ba.


Daga dayan ɓangaren Elizabeth ta sake cewa
"Nace Jikin ma'am ya tashi sosai, suna asibiti, tun uku na daren yau" ta karasa cikin gurbataciyyar hausar ta, yayinda Muryar ta ke bayyana halin damuwar da take ciki.




Ba tare da ya sani ba ya saki wayar kasa, kana shima ya sulale kasan, wani mugun kuka ya saki, tamkar ba namiji ba, itama Mahmah kuka take, kukan tausayin danta domin taji abinda Elizabeth tace.



Ganin kukan kara gaba yake ya sa Mahmah ta samu ta rungume shi da kyar tana cewa "my son, Fadeel! Stop all this, ka nutsu kaji me zan ce maka"




Cikin kuka yace "A'a Mahmah, bazan iya nutsuwa ba, muradin raina na k'ok'arin mutuwa, ta yaya hankalina zai kwanta, mahmah ki barni, ki barni na bawa Fadeelah *koda* ta, domin ta rayu, zan kasance cikin farinciki koda a kabarina ne idan Fadeelah na raye...."


"I said stop Fadeel! Bazaka mutu yanzu ba in sha Allah, haka ita ma Fadeelah baza ta mutu ba, baku cancanci mutuwa yanzu ba, ku duka biyun zaku rayu cikin farinciki"



"Ta ya ya hakan zai yu Mahmah? dole idan ban bawa Fadeelah *koda* ta ba, mutuwa zata yi, idan kuma hakan ya kasance zan kashe kaina, sannan bazan taba yafe wa kaina ba har abada"



"Son kasani cewa ni Mahmah'n ka bazan cutar da kai ba, umarnin nake baka kada ka bayar da kodar ka, shin kana tunanin fadeelah zata ji dadi ne matuk'ar tasan cewa kai ka bada kodar ka? ita ta rayu, kai ka mutu"
Sam bazata ji dadi ba, domin ta na buk'atar ka a rayuwar ta"....



Share hawaye tayi kana tace "zan je asibiti domin a duba ni, ina kara maimaita maka, kada ka bada kodar ka wa Fadeelah, Allah zai kawo mafita in Sha Allahu".


Tana gama fadin haka ta mike hadi da daukar hijab d'inta ta fice...



Kansa ya shiga bugawa da bango da k'arfin gaske, har jini ya fara bin gefen fuskar sa, sai dai ko daya bai ji zafi ba k'amar yanda zuciyarsa ke masa matsanancin zafi tamk'ar an watsa masa narkakkiyar dalma. Gaba daya ya fita hayyacin sa, tamkar wani sabon kamu...


★★
Zaune Mahmah take cikin adaidaita sahu, ji take kamar tayi tsalle ta ganta a asbitin. Duk gudun da matukin keke napep din keyi sam bata gani.
Bayan wasu mintuna suka iso, sauka tayi hadi da mika masa kudin sa, ta nufi cikin asibitin...


Tun daga hospital din ta ga canji mai tarin yawa, domin security's, bodyguards, hadi da sojoji ke zagaye cikin asibitin. Take jikinta ya bata cewa Fadeelah na asibitin. A ranta tace " ikon Allah, ashe asibiti daya muke zuwa checkup tare da Fadeelah"


Tana shiga cikin asibitin taga wasu mutane masu yawan gaske fuskokin su cike da damuwa, kallo daya ta musu ta fahimci cewa su din dangin Fadeelah ne, sai wani magidancin mutum dake tsaye idanun sa na zubar da hawaye wani baturen likita nayi masa magana wanda bata jin me suke cewa, take jikinta ya bata cewa mahaifin Fadeelah ne domin ga kamanin nan baro-baro.



Direct office din doctor Gabriel ta nufa, yana zaune kuwa, yana wasu rubuce _rubuce a littafin kundin marasa lafiya, dago kansa yayi kana ya amsa sallamar hadi da cewa "a'a madam, ya kika zo yau? Ai ranar checkup dinki jibi ne, have a sit please"



Murmushin k'arfin hali Mahmah ta saki, kana ta zauna Kamar yadda yace, ajiye biron hannunshi yayi hadi hade hannunsa cikin na juna, alamar ita yake saurare.


Ajiyar zuciya ta sauke kana tace "likita meye amfanin zuwa na checkup? Bayan lokacin mutuwa ta na daf da zuwa, idan ban manta ba, kwanaki dana zo ka sanar dani cewa cancer da nake fama dashi a lungs dina ya dawo so chronic, har ya fara taba wani sashen, sannan zan kuma iya rasa raina a ko wani lokaci, haka ne doctor?"


cikin tabbaci hadi da tausayi likitan yace "tabbas hakane" dan jan numfashi tayi kana ta cigaba "duk da ina jin ciwo mai tsanani gaske a yan kwananin nan, amma sam ban nuna wa dana ba, kuma har in koma ga Allah banason yasani. Likita bana iya bacci har gari ya waye a yan kwananin nan, ina ji a jikina kwana kin mutuwa ta yazo daf"... wasu hawaye ne suka zubo mata kana ta cigaba "wata alfarma nazo kayi min"


Sosai jikin doctor Gabriel yayi sanyi, duk da kasancewar sa ba muslumi ba, amma yasan kaddara, sosai yake jinjinawa Mahmah domin tana da tawwakali, ya kuma yaba mata, domin tsananin son da take yiwa danta ne ya hanata sanar dashi cutar da take fama dashi tsawon shekaru masu yawa.


Ajiyar zuciya ya sauke cikin tausayawa yace "ina jinki, wani alfarma kike so nayi miki matukar bai fi karfina ba zan yi miki shi"


"Nagode doctor Gabriel, nasan cewa Fadeelah na asibitin nan ko?"


"Cikin zallan mamaki likita yace "Fadeelah! Fadeelah dai mai dauke da cutar koda? diyar professor Imran mai naira, ina kika Santa?"


Duk da Mahmah bata san sunan mahaifin ta ba, amma tana da tabbacin ita ce, a fili tace "kwarai ita nake nufi"




"Eh kwarai tana nan asibitin tun cikin dare aka kawo ta" doctor Gabriel ya fada.



"Toh alhamdulillah, alfamar da nake so ka min shine, matukar Allah ya dauki raina, ina son a cire *kodata* a sanyawa Fadeelah"


Azabure likita ya mike daga kan kujerar yace "What!!!?"
"Madam kin san mikike cewa kuwa? Duk da cewa kina daf da barin duniya Kamar yadda result dinki ya nuna, ba wai hakan na nufin ki cire kidney dinki ki bayar ba, meye dalilin ki na yin hakan? Allah na iya canza komai idan yaso" Doctor Gabriel ya karasa cikin tashin hankali daya bayyana a fuskar sa karara.

Wani murmushin karfin hali Mahmah ta kara saki kana tace "kwarai nasan me nake yi, zan sadaukar da koda ta wa fadeelah saboda kauna hadi da tausayi da nake mata, yes I will scracife my kidney to her, domin ita din farinciki dana ce, zan kuma iya bata *kodata* ko da ace lafiya ta lau bana tare da lung's cancer dinan (cutar daji ta makwogaro) ina kara neman alfarman ka please doctor" ...




Wani gumi doctor ya share, sosai yake mamakin matar, zuciyar ta mai kyau ce, Saboda farincikin danta zata sadaukar da *kodar ta* wa Fadeelah, wanda har yau ba a samu kodar ba, kuma sosai take cikin halin ciwo mai munin gaske domin bata san waye a kanta ba.



Muryar Mahmah ce ta katse masa tunanin sa cikin kuka tace, "doctor! ka tabbatar da cewa Fadeelah bata mutu ba, ita din farincikin dana fadeel ce. Bata cancanci mutuwa yanzu ba Saboda halayenta masu nagarta, bata cancanci mutuwa yanzu ba, domin rasa irinsu al'ummah babban rashi ne. Ni nayi niyya, tun daga ranar dana ji sauran kwanakin ta a duniya, a ranar naga tashin hankali a idanun dana, tun daga ranar na sadaukar mata da koda ta"



Ajiyar zuciya ta sauke kana ta cigaba da cewa



"Doctor! Inaso hakan ya zama sirri tsakanin na da kai, har a gama dashen kodar, kada ka sanar da kowa dan Allah" Mahmah tace tana hade hannun ta alamun roko.



Shiru doctor yayi, a kafatanin rayuwar sa zai iya cewa bai taba ganin mace mai kyawun zuciya irin Mahmah ba, Saboda farincikin wasu zata iya Sadaukar da komai nata, kodar da ake nema ido rufe, shi take rokon sa akai? Sannan bata bukaci ko sisi ba, tabbas matar nan ta cancanci yabo mai girman gaske...




Wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke kana yace "madam na amince da abinda kika ce, zan kuma rike miki wanna sirrin, bazan gaya wa kowa ba, har a gama aikin" ya kai karshe wasu kwalla suka zuba masa, wanda na tsantsar tausayin Mahmah ne, ga ramar ta ya fito fili sosai, alamun cutar na cinta from the inside.



A matsayin sa na likita yaga cases da yawa na patients, amma babu wanda ya daga masa hankali hadi sa shi kuka Kamar na Mahmah, hankici ( handkerchief) yasa yayi saurin share hawayen sa.



Murmushi fall fuskar Mahmah tace "nagode sosai doctor Gabriel"


"Mu ke da godiya madam, Allah ya saka miki da aljanna, amma yanzu zamu je wajen likitan Fadeelah'n wato doctor Mahfouz domin mu tattauna maganar dashi. Ya karasa cikin sanyin jiki.




Ba musu ta mike suka nufi office din doctor Mahfouz di'n.



Zaune suka tadda doctor Mahfouz cikin zurfin tunani, domin cutar Fadeelah bai taba daga masa hankali irin daga daran jiya zuwa safiyar yau ba. Tun fadeelah na da kananun shekaru yake a matsayin likitan ta. Har rashin yana jin zafi, yana kuma tsoran ta rasa ranta, gabadaya ya gama sarewa yana jiran ta Allah ta kasance, domin yayi iya k'ok'arin sa.



Shigowar su Mahmah ne ya katse masa tunanin sa, babu bata lokaci doctor Gabriel ya sanar dashi komai, sosai yayi mamaki da murna ya kuma ji tausayin Mahmah kwarai, duk da burin sa kenan *a samu kodar da za a datsa wa Fadeelah*
Amma sai ya samu kansa da jin ba dadi wanda hakan baya rasa nasaba da kyawun halin mahmah wata zuciyar ta bashi tabbacin hakan.
ya kuma yi musu alkawarin har a gama aikin shi ma ba zai fadawa kowa ba, kamar yadda Mahmah ta bukata.



Mahmah ta bukace ganin fadeelah, duk da ba mai shiga saboda ba a son hayaniya a kusa da ita amma ba musu ya amince duk suka shiga hadadden dakin da aka kwantar da ita. Sosai Mahmah ta tausayawa Fadeelah, domin ta fita hayyacin ta sosai, banda na'uran nan dake Reading cewa tana da sauran numfashi tabbas za a dauka ta mutu ne.



Hannunta Mahmah ta riko tace "Allah ya baki lafiya 'yata, Allah ya tashi kafadunki, Allah ya kara muku kaunar juna ke da dana abun sona Fadeel, nasan ina daf da mutuwa, amma zan kasance cikin farinciki a gidana na gaskiya matuk'ar kuna raye cikin farinciki, ki kulamin da Fadeel, na baki amanar shi, domin ke kadai ce zaki bashi farinciki idan na mutu, ki min alkawarin zaku haifa min jikoki..." Kuka ne ya ci karfinta, haka zalika doctor Gabriel da doctor Mahfouz sai da suka share hawayen tausayin ta...




Daga baya ta bar asibitin ta koma gida, halin data ga Fadeel a ciki yayi matuk'ar daga mata hankalin ta, take ta rike shi, suka nufi chemist aka yi treating ciwon kansa...


★★
Bangaren Daddy kuwa zaune yake yana kuka sosai, tamkar karamin yaro, bai taba tunanin akwai abinda kudi baya iya siya ba sai yau, domin duk mahaukatan kud'add'en sa basu yi masa rana ba, tunda ga yarsa na kwance a gadon asibiti cikin mayuwancin hali domin bata san wanda yake kanta ba, da taimako na'urori take numfashi.


Wani matashi ne ya fito daga wani daki, ya kalli Daddy cikin girmamawa yace " yallabai kana iya shigowa"
Mik'ewa yayi cikin sauri ya nufi dakin gabatar da shirye_shiryen, kasancewar yazo gidan TV ne.



Zaune yayi idanunsa na zub da kwalla yana fadin "a taimaka min, wani ya siyar wa 'yata da *kodarsa* ko daya ce, tana cikin matsanancin halin ciwo, banda wata 'yar sai ita, jama'a ku taimaka min, ku taimaka min, ku taimaka min dan Allah!!!" Ganin kuka yaci k'arfin sa, yasa aka katse daukan, hadi da watsa shi duniya... Domin bukatar Daddy kenan.

kudi masu zunzurutun yawa ya saka, daga million hamsin, zuwa ko nawa mutumin ke so ya fada zai bayar, ko da duka dukiyar sa ne zai bayar.
Su kansu yan gidan TV sun zub da hawayen tausayin sa, domin duk fadin lagos kowa yasan tarin dukiyar *professor Imran mai naira* sannan an sa izzar sa hadi da jin kansa, amma yau shi da kansa yazo gidan TV neman taimako.

Abin da matuk'ar mamakin ba shakka son da yake yiwa yarsa mai yawan gaske ne.




Sosai aka watsa daddy duniya har wasu gidajen Tv da radio, gari ya dauka ko ina maganar ake, sai dai har bayan kwana biyar ba'a samu wanda ya zo da niyyar zai siyar da kodar sa ba.

Wanna kenan.





*** *** ***


Yau kwanan Mahmah biyar a kwance jikin ya matsa mata sosai, domin har tashi bata iya yi, Fadeel ya dawo tamk'ar wani zararre, uwar sa mafi soyuwa agareshi na Cikin wani hali, ga Fadeelah'nsa a gadon asibiti, sosai yayi rama, domin baya iya cin komai, haka zalika Mahmah sai abu mai ruwa take iya kai baki, shima da kyar take hadiya...

da daddare ta dan samu sauki har ta dan yi hira da Fadeel, ya kuma ji dadi domin tunda ta kwanta bata iya magana. Sai dai wasu maganganun da take yi, mai kama da wasiyya, sai dai sam bai kowa komai a ransa ba.


"Mahmah please ki bari na kai ki asibiti, zan fita ko ina ne domin neman kudi"


Murmushi mai ciwo tayi, ita a jikinta tana jin lokacin mutuwar ta yazo, cutar dake damunta yayi mugun cin karfinta, domin yazo gabar da ba za a iya yin komai akai ba. Toh meye amfanin zuwa asibiti???



A fili tace "my son Fadeel, kada ka damu sannan bana so ka fita nema saboda ka kai ni asibiti, babu bukatar hakan, ina maka so mai tarin yawa dana farincikina. Allah ya dauwamar da farincikin a rayuwar ku, kai da 'yata Fadeelah, I love you son" ta kai karshen maganar cikin murmushi irin na marasa lafiya.




Wasu hawaye ne suka zubo masa, duk da ba a cikin nutsuwar sa yake ba, amma yaji kalaman ta har Cikin kashin sa, ya ma kasa magana sai sumbatar hannunta hadi da goshinta da yayi, itama kuma ta daga hannunta ta shafa tarin sumbar sa d'aya kara yawa hadi da hargitsewa saboda gyaran da baya samu...


Ta kara cewa
"ka bani labarin soyaayyar ka kai da 'yata"

Duk da baya cikin farinciki amma sai daya yi murmushi daya taho da zubar hawayen sa, Kamar yadda ta bukata, ya fara bata labari so da tarin kaunar da yake mata, hadi da labarin irin soyaayyar da suka gudanar.

Kallonsa Mahmah take tana murmushi, har ranta soyaayyar fadeel dinta da Fadeelah na burgeta, tana musu fatan Alkhairi a rayuwa...



*** *** *** ***



Washegari har tara na safe fadeel yaga Mahmah bata tashi ba, domin da asuba bayan ya d'ora Mata alwala tayi sallah, tace zata yi bacci ya taimaka mata ta kwanta.

Kunu daya dama mata ya nufi dakinta da niyyar tashinta ta sha.




Gabanta ya tsugunna ya kira sunan ta shiru, "Mahmah!!!" Ya

Please Login or Register in order to submit comment