Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanen babban ne, sannan akwai tazara mai dan yawa tsakanin mu, babu mai ganin zanen wani...




Mutum daya ne daya kasance baƙin fata dan garin Ibadan ya min murna, kana ya fada min cewa "na maka murna sosai bro, congratulations! tabbas a rayuwa kada ka taba raina ko wulakantawa mutum komai kaskanci shi kuwa, hakika na koyi wani darasi daga gareka.." Yana fadamin haka yana ficewa daga wajen...



Nan sauran suma suka tafi cike da jin haushina ko nace tsana ta, domin naga hakan ta idanun su.




Bayan awa d'aya Alhajin ya fito yace mu koma gida, fusk'ar sa dauke da murmushi kana da sauran mamakina kan kwarewa ta, domin zanen yayi kƴau mai ban mamaƙi



Bayan munyi sallah, mun ci abinci a part di'n alhajin, ya mike ya shige bedroom d'in shi, babu jimawa ya d'awo dauke da wata madaidaicin jaka ya mika min....


Fuska ta da alamun tambaya nace "menene wanna alhaji"




Murmushi yayi yace "hakika kai gifted ne, kana da talent na zane sosai, kayi matuk'ar iya zane, wanna jakar mai dauke da million hamsin naka ne, ma'ana shine hakkin ka na zanen"




Sosai na shiga rudu, domin ban taba tunanin samun koda million ɗaya ba, cikin rudewa nace "Alhaji nawa ne million hamsin? dan Allah ka fadamin, zai Kai na iya mallakan Fadeelah ta? kudin zai isa da har Daddy zai bani auren Fadeelah?" Na fada hawaye na ciko idanuna, domin a lokacin burina na mallake ki.....




Sosai alhajin yayi mamakin ganin ban yi murna samun makudan kudaden nan ba, sai ma sunan ki daya ji na kira, hakama matar sa.


Hannuna ya riko yace "hakika akwai abubuwa da dama cikin tarihin rayuwar ka, wacece wanna fadeelah'n sannan waye zai ki baka auren ta?, ka fadamana labarin ka nayi alkawarin taimaka maka da dukiyata da ma duk wani abu da zaka bukata"...




Ban musa ba, na basu tarin rayuwata, dama labarin soyaayyar mu, kin san menene? Ya tambayi Fadeelah, girgiza kai tayi Yayinda taƙe k'irjin shi har yanzu.





Gani nayi alhaji yana zub da kwalla, matar sa kuwa rushewa tayi da kuka, wanda na zallan tausayi ne...



ɓaƴan wasu mintuna yayi gyaran murya yace "idan kace zaka yi aure da duk kudinan daka samu, Tayaya zaka yi arziki? Tabbas mallakan Fadeelah a matsayin mata shine cikar farinciki ka, amma ba yanzu zaka je gareta ba, business zaka yi da kudin nan, sannan zan maka hanya ta yanda duniƴa zata san cewa kai babban architecture ne! hakan zai sa cikin lokaci kankani sunan ka ya daukaka, har ka dinga samun kudaɗe masu yawan gaske, idan arzikin ka ya sake bunkasa sai ka fara gina gida, Bayan nan ka zuba motoci, Bayan ka gama hada dukkanin abinda kasan cewa mahaifin ta zai baka auren ta, sai muje kwatsam"...




*******************************



Sosai suna na ya ɗauƙaƙa a duniya, a matsayin *Architecture FFM* duk yanda yan jaridah da yan gidan TV suka so hira dani ban bari ba, kana ban bari sun dauki hoto na ba, ina mamakin wai nine yau yan jaridah ke rububi akai, hakika idan baka da shi a duniya ka zama dan kalllo.....




Sosai na yarda da shawaran alhajin, cikin lokaci kankani na fara bushiness, ga manyan zane na masu kudi da nake ta samu abin har yawa yake min...



In tak'aice miki, cikin watanin kalilan nayi arzikin da ni kaina ban san yawan su ba, abu na farko dana fara yi shine gini na, wanda na zane ne da hannuna, na kuma yi shi a garin lagos domin nan nake sha'awan zama, sannan na zubo motoci da duk wani abun more rayuwa, na zuba ma'aikata, hadi da bodyguard's masu bani tsaro kamar yadda alhaji yace lallai sai na samu bodyguards domin tsaro......





a lok'acin dana shiga katafaran gidana sai dana yi kuka tuno Mahmah nah.
A dalilin rashin babu(kudi) cuta ya cita har ta koma ga Allah, sai bayan ranta nayi arziki da ban taba mafarki ba, sai kuma ma tuna haka Allah ya kaddara mana....







Daga wanna lokacin alhajin ya dauke ni tamkar Ɗan sa, daga baya yake fadamin duk tarin dukiyar sa, Allah bai basu haihuwa ba, amma mutum bazai gane hakan ba, domin suna zaune cikin farinciki, sun ƙuma fawwalawa Allah lamarin su.







A lok'acin dana ji cewa anyi baikon ki da Jameel na kusan zaucewa, domin ina sa ayi min bincike akan abinda ya shafeki..... Babu bata lokaci na samu Alhajina nace dan Allah ya taimaka su je tambayan min auren ki domin bazan jure rasaki ba a karo na biyu...



Sosai alhajina ya kwantar min da hank'ali, yace akwai shiri na musamman da yake yi, yana so komai yazo a bazata, yace na yarda dashi, na bar komai a hannun sa, ban sake cewa komai ba, amma kullum tunanin ki nake, ina fargaban rasaki, ga kuma tarin sonki dake nukurkusata, sau da dama ina son zuwa gareki alhajina ya hana yace na bari komai ya tafi kamar yadda ya tsara....




Makudan kudade da ban san hadadin su ba na bawa matar Alhajina domin ta hada min lefe, cikin kankani lok'aci ta fita kasar waje ita da wata kawarta da kanwarta suka hado....




A ranar da loƙacin dasu Jameel za su kawo lefe duk muna sane, hakan yasa alhajina yace a kawo nawa kafin su jameel su kawo nasu, hakan zai kawo rikitarwa.....



Nan matar Alhajina dama yan'uwan ta da wasu kawayenta suka k'awo lefen, Bayan kwana biyu muka zo estate dinku Alhajina yayiwa Daddy bayanin cewa yayi haku'ri, mun yi nema cikin nema amma ba laifin sa bane, Dan sa ya na matuk'ar son fadeelah da dai sauran su....



Abu biyu ne ya bani mamaki, Daddy bai ki amincewa ba, ban saniba ko dan alhajina yafi mahaifin Jameel dukiya ne, Allah masani.
Sannan abu na biyu Daddy bai gane ni ba, bai gane cewa nine wanna bakin talaka fakirin bane...



Naso zuwa gareki a ranar da muka zo wajen Daddy, still alhajina ya hana yace na bari sai ranar daurin aure domin inyi miki bazata....



Ajiyar zuciya Fadeel ya sauke kana ya cigaba...

har yau da aka d'aura mana aure, daddy bai san cewa nine Fadeel ba, ina matsayin dan Alhaji Sufyan Rufa'i ne a wajensa.....



BACK TO STORY


Kara rungumeta da kyau yayi, yana jin farincikin mallakar ta a matsayin mata, yace

"wanna shine tarihin Bayan rabuwar mu a tak'aice...."







Muje zuwa da sauran chakwakiyya😎😎😎


A tayani share dan Allah👏🏻



Share fisabilillah




Comment



Vote




NoorEemaan
07082281566


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*



🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)




*WATTPAD*
@NoorEemaan





EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



Page 55-56

Kukan zallan farinciƙi Fadeelah ta sanya, a ranta tana mai godiya ga Allah. Ita ba arzikin ɗa yayi ya sanya ta farinciki ba, dawowar sa gareta a matsayin miji yafi komai yi mata sugar. Duk da ta san cewa akwai kalubale a gaba, amma bata wani damu ba, tunda sun zama ma'aurata ƴanzu burin su ya cika.



Duk da arzikin da yayi a kankanin lokaci abin mamaki ne, taɓɓas bata manta lokacin da ake yawan labarai a gidan TV kan *The young billionaire architecture FFM* bata mantawa a falon Mommah suna zaune aka hasƙo labarin, shi Kanshi Daddy sai daya jinjina arzikin wanna matashin, ashe Fadeel dinta ne bata sani ba, duk da yayi fiye da arzikin da Daddy zai so, amma shin zai amince suyi zaman su cikin kwanciyar hankali kuwa? Ta aiyana a ranta, sanin cewa bata da amsa ya sanya ta share, kana a fili tace "Am so happy my one, Allah na gode maka, da gaske kai ka aureni? Wayyo dadi!" Raba jikinsu tayi ta nufi zanen hotunan dake manne a bango.

Daidai kan na mahmah ta tsaya, ta goge kwalla sakamakon tuno Sadaukarwa mahmah a gareta wanda kullum da shi take kwana take tashi, tabbas Mahmah ta zama sashen jikinta, Yayinda Fadeel ya zama jinin jikinta.



Shafa fuskar zanen Mahmah'n take yi tana kokarin controlling hawayen dake zuba a idanun ta.


Cikin murya dake bayyana tarin kauna hadi da kewar mahmah tace "Allah ya jikan ki Mahmah, Allah yasa kin huta, Mahmah ƙiƴi farinciƙi... a yau Fadeel din ki ya cika miki burin ki, mun zama ma'aurata, nasan kina farinciki a inda kike yanzu, ina kaunar ki mahmah nah, muna kaunar ki duka" ta kara sa tana share wasu hawaye masu dumin gaske.


A ɓazata ta ji Fadeel ya rungumeta ta baya, hannunwansa duka biyun ya d'aura saman shafaffan cikin ta. Cikin wata murya da amon sa ke fidda tashin wani miki a zuciyar sa yace "Ameen ya tawwabul raheeem, amma kin manta baki fada mata cewa zamu Haifa mata jikoki ba, sannan zamu kasance tare har abada, har mu koma inda take a yanzu, duk runtsi duk wuya muna tare" ƴa ƙarasa cikin wani cool voice ƴayinda idanunsa suka kara yin jaa...



Murmushi mai tafe da hawaye ya taho wa fadeelah a lokaci daya, cikin muryan kuka tace "eh mahmah! Zamu haifa miki jikoki, sannan kullum sai na basu labarin ki, na sani cewa baza su taba ganin ki ba sai ɗai a hoto, amma zasu rayu da son ki a jinin jikin su, sannan ni da Fadeel zamu kasancewa the best couple ever, we love you Mahmah" ta karasa tana juyowa hadi da rungume Fadeel.



Shi ma rungumeta yayi ya shiga bubbuga bayanta har tayi Shiru tana sauke ajiyar zuciya. A hankali tace "My one menene ma'anar FFM?"

Murmushi mai sauti ya saki, lumshe idanun sa yayi yace "it means *FADEEL, FADEELAH, MAHMAH*" ya amsa a tak'aice...


"Wow!" Tace tana jin farinciki samun masoyi kuma miji kamar Fadeel.



Slowly cikin zazzakar muryar ta tace "Am so happy for you, I love you so much"


Wani shaukin sonta ne ya shiga ratsa jijjiya da jinin jikin sa, martani ya mayar mata kamar haka "I love you too, fiye da tunanin mai tunani, ina matukar kaunar ki my Darling wifffy"



Murmushi ta saki, komai na Fadeel dinta ya sanja, magana, tafiya, kallo, murya, komai nasa ya dawo cikin wani aji da salo mai tafiya da hankalin duk wata lafiyayyen mace.....



Hannun sa ta kamo suka zauna kan hada'dd'e kuma katon gadon ta, kallon ta yake yana jin wani farinciki a ransa, ta yi masa kyau fi da tunanin mai tunani, still hakan bai hana shi ganin ramar da ta yi ba.


"I love your hennah Darling" Fadeel ya fada yana sumbatar had'add'en jan kunshin hannun ta.


Murmushin zallan farinciki tayi, ta kai idanun ta kan kunshin, tunda aka yi mata kushin bata ga kyaun sa ɓa, haslima haushin sa take ji, sai a yanzu ta fara ganin kyawun K'unshin, wanda baya rasa nasaba da bayyanar gwarzon masoyinta kuma mijinta fadeel.



Kallon shi tayi tace "my one amma ka kai ziyara wa yan'uwan mahmah da na baba ko?"


Take yaji ranshi ya baci a dan kausashe yace "ban je ba, ba kuma zan je ba, Tayaya kike tunanin zan iya zuwa? Sun manta damu, sun manta cewa ina raye ma, sun ma san mahmah ta rasu? Basu sani ba, saboda rashin zumunci, ƙo ɗan sun ga a cikin dangin talakawa ne mu shiyasa basa ziyartarmu, tell me tayaya zan je wajen su, sam bazan je ba, idan ina dake, ina da komai Fadeelah, idan kika Haifa min 'ya'ya sune zasu kasance duniya ta ɗa dangin na, hakan ya ishe ni rayuwa Alhamdulillah! Ki bar zancen su please" ya karasa yana sauke numfashi....





Ganin yadda yake magana ya sanya fadeelah sanin cewa ranshi ya baci matuka, domin bata taba ganin fushi ko bacin ran shi ba sai yau, Hakika dangin sa basu da zumunci, amma a hankali zata dinga yi masa magana domin ya je garesu, saɓoɗa hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar.



Hannun sa ta riko a fili tace "na bari toh, saki fuskar ka please" ta karasa a shagwa'be.

Murmushi ya saki yace "na saki toh, are you Happy now?"

"Yes! My one" ta amsa cikin wata had'add'iyar murya daya sanya shi jin wani yanayi na musamman a tare da shi, a hankali ya matso daf da ita, baya tayi kadan, sai ya bi ta ya kwanta a kanta, hakan yasa ta zube kan gadon...



Dan waro ido fadeelah tayi ganin bai taba kwantanta irin haka da ita ba, ko da su biyu ne ƙadai a wajen. Amma tuna matsayin sa a gareta yanzu ya sanya ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, amma sosai ta ji wani kunyar sa ƴa shige ta.


Ganin ya nufo labb'anta ya sanya ta runtse idanun ta, dakatawa yayi yana murmushi mai sauti ganin yadda tayi, hannunsa ya kai ya shiga shafo tattausan labb'anta yace "bana son gulma faaa, na san kin ji ma kina son Fadeel ya sumbace ki ai, dan haka ki bud'e idanun ki" ya karasa cikin wani romantic voice.


"Ya Allah! Fadeel zai kashe ni da salon sa, hadi da kunyar sa, komai nashi ya Sanja ya dawo gwanin burgewa fiye da baya" ta fada a ranta.


A fili kuwa tace "yaushe ka koyi sharri my one? ni ban taba wanna tunanin ba, Allah faaaaa" ta karasa tamk'ar yarinya yar 13years...


Ɓata zata ba, unexpected ta ji ya kamo lallausan lips di'nta mai fidda k'amshin Mouth Wash na Lavender ya fara kissing di'nta in a passionate and romantic way...



Sarkin kunyar kuwa bata san lokacin data shiga bashi hadin kai ba, gaba daya sun shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa, ji suke dama sun dauwama a duniyar da suke ciƙi ƴanzu, ɗomin yanayi ne mai dadi da bazai fadu ba. Sosai ƙuma suka birkita gadon dama kansu....



Bayan mintuna goma sha biyar... har ƴanzu suna abu daya, ganin ya fara zurmewa da yawa ya sanya Fadeelah zare labb'anta da suka yi mugun jaaa, domin fadeel bai mata da wasa ba, tamkar lollipop yake sha...



Ganin ta cire labb'anta ya sanya shi lumshe fitinanun idanun sa masu dauke da zallan sonta hadi da kwadayin kasancewa da ita, kansa daya gama hargitsewa ya dora kan k'irjin ta yana sauke numfashi domin babu k'arfi ko daya a jikinsa....
Hannunta na kan gashin sa tana murzawa a hankali Yayinda idanun ta ke a lumshe, sosai suke jin shauki hadi da jin dadin kasancewa a haka.



"Wiffy" Fadeel ya kira ta slowly

"Uhm" ta amsa cikin murya kasala

"Kinyi enjoying kiss din ko?" Ya fada cikin tsokana...

"Ya salam! My one dama baka da kunya, please kabari kana bani kunya faaaa"


Bayan lokuta masu yawa daya k'asance cikin kunci da damuwa sai yau ya yi dariya mai sauti, domin ba kadan ba ta bashi dariya. "Toh mena yi na rashin kunya yanzu?"

"Ni dai ka bari bana so" ta fada tana turo cute lips d'inta


Dagowa yayi ya bata light kiss a lips d'inta, hakika fadeelah'n sa daban take cikin mata, duk da kasancewar ta wayayya domin daidaikun kasa ne bata je ba, kana duk wata wayewa tana da shi, haƙa ma ilimi, amma hakan bai hana ta zama mara ƙunƴa ba, sosai kuma hakan ke burge shi domin kunya ado ne ga mace....


A fili cikin tsokana yace "ba wani bakya so, Bayan kamar zaki cinye min ba....."


Da gudu ta sauka ɗaga kan gadon ta ruga toilet.... Kwanciya yayi a gadon ya shiga dariya, domin sosai Fadeelah'n ke bashi nishadi yau.



Fadeelah kuwa ajiyar zuciya mai dauke da murmushi take ta saki a bathroom.... Ta kai mintuna biyar a wanna yanayi kana ta tube kayan jikinta tayi wanka da hada'dd'en *shower bath* dinta, kayan jik'in ta ta mayar, domin bata son fita da bathrobe ya ganta haka, sosai kima, girma, haɗi da kunyar sa ta karu a Idanunta musamman yau din daya zama miji a gareta...


A hankali ta rike handle din kofa ta fito, waro ido Fadeel yayi yace " me zan gani ni fadeeel, amarya ba makeup a fusk'ar ta, tukunna ma wanka kika yi? ko dai ko dai" ƴa karasa ciƙin zolaya


Turo baki tayi kana tayi murmurshi domin ta dauka wani abu ne ya sa shi waro ido, a ranta tana mamakin dama Fadeel dinta ya iya tsokana haka, bata bashi amsa ba, domin ta san kawai so ƴaƙe ya sata ƙunƴa.


Zuwa tayi gefen sa ta zauna, wani nishadi na shigar ta, ganin sa kusa da ita yafi komai yi mata dadi a yanzu...


"Wait a minute! Anya kinyi breakfast kuwa? Domin dana shigo part dinnan naga kamar an shirya breakfast a dining area da alama kuma babu wanda ya taba" Fadeel ya fada idanun sa kan fadeelah


"A'a ban ci ba, farincikin ganin ka ya sani na manta" ta fada cikin iyakar gaskiyar ta, domin wallahi ta manta wani abu wai shi abinci...

Murmushi ya saki kana yace "duk da haka bai kamata kina min wasa da nan ba" ya fada yana shafa cikinta, kana ya mike


"Ina zaka? Karka tafi dan Allah!" Ta fada a dame.


Murmushi mai sauti ya saki yace "ba tafiya zan yi ba, yanzu zan dawo kinji" ƴa fice zuwa dining area ya bud'e duka warmers din, karshe dai porridge din Irish potatoes da zallan naman kaza ya zuba mata, kana ya hada mata tea mai kauri, kan wani tray karami ya jera su kana ya nufi dakin...


Daidai ya bud'e kofa kenan zai shiga, hakan yayi daidai da sanyo kan Fadeelah waje domin zuwa dubo shi ganin ya dade...

Kansu ne ya gware ɗa na juna "auchhhhh!" FADEELAH ta fada tana dafa kan.


Cikin sauri ya ajiye tray din, Allah yasa ma bai bare ba... "Sorry! Sorry!! my bride, ban san kin taho ba" ya fada a dame yana Murza mata goshin daya dan yi jaaa abunka da farar fata jiki bai saba da wahala ba...



Ganin yadda ya damu ya sanya tace "ni faaa bana jin zafi, ka bar murzawa"

"Kina ji mana, gashi wajen yayi jaa" ya fada kamar zai yi mata kuka


Dariyar ta mai birgewa tayi tace "da gaske ba zafi"

"Are you sure?" Ya tambayeta

"Yes I am" ta amsa tana jifan shi ɗa ƙallon kauna


Ajiyar zuciya ya sauke kana ya mika hannu ya dauko tray din ya dora kan cinyar sa, cokali mai yatsu ya dauka ya raba dankalin hudu kana ya cake yanka daya da fork din, hadi da kaza ya nufi bakin ta....

Ta bude baki ya sanya mata, haka ya shiga ciyar da ita har ta koshi, ƙuma taci sosai, kana ta shanye tea din tana sauke numfashi tun bayan rabuwar su da Fadeel bata kara cin abinci cikin kwanciyar hankali ba, sai yau.... Domin a lokacin damuwa baya barinta taci...



Bayan awa d'aya ya mike domin tafiya, fadeelah ta fara matso hawaye ita kada ya tafi ya barta, domin a ganinta idan ya tafi baza ta kara ganin shi ɓa....


"Kwantar da hankalin ki, gida kawai zan je fa zan d'awo, nasan kina tunanin zan bar ki ne, ina zan iya barin matata in tafi? So chill, zan d'awo domin mu ga yadda abubuwa zasu kasance, tun da burinmu ya cika ya kamata zuwa yanzu Daddy yasan waye mijin 'yarsa na ainahi..."





Jinjina kai tayi cikin gamsuwa kana ta raka shi har bakin down stairs, nan ma basu rabu ba sai da ya kashe mata jiki da salon sa sannan ya tafi cike da kewar ta da sonta.....



Yana fita yaga body guards d'insa tsaye jikin motocin sa, dan dafa Kai yayi shaf ya manta ma suna jiran sa, har yanzu gidan a cike yake, sai dai ba kamar dazu ba, daya daga cikin motar ya fada kana suka fice a jere reras....



Bangaren Fadeelah kuwa tana tsaye jikin window har motocin sa suka fice, ajiyar zuciya ta sauke tana fatan kada wata matsala ta sake kunno musu, ta kofar baya ta bi ta nufi part din Mommah, domin duka kayan ta na fitar biki yana wajen Mommah'n...

Ta kuma yi mamaki rashin kiran ɗa Mommah bata mata ba, har wani sauri take domin taje ta sanar da Mommah dawowar gwarzon masoyinta Fadeel a matsayin miji a gareta........






Muje zuwa my beautiful people😍



Share fisabilillah


Comment


Vote




Noor Eemaan loves you all Habibtie's💋
07082281566



Tuesday September 28
1:41am



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracifes hatred and destiny)




*WATTPAD*
@NoorEemaan






https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


EDITING IS NOT ALLOWED❌


No editing🤒


Page 57-58


Tana shiga part din Mommah, nan kowa ya shiga bin ta da kallo cikin mamaki, ganin yadda walwala ya kawata fusk'ar ta, sabanin dazu da kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci tana ɗa ɗamuwa.



Murmushi fadeelah take saki ba tare da tasan tana hakan ba. Direct bedroom d'in Mommah ta shige, ta kuwa same ta tana kokarin sanja kaya zuwa wani dan ubansu lace wanda kudinsa zai kai million daya da doriya, dago kai Mommah tayi ta sakar mata murmushi, martani Fadeelah ta mayar mata kana ta bata rai cikin shagwa'ba tace

"Mommah ko ki neme ni ko?"


Murmurshi ta ƙara saki tace "tayaya zan nemi ki bayan kina can tare da mijin ki abin sonki Fadeel... Ina sane na barku ku gana sosai ai"


ihun murna Fadeelah ta saki ta rungume Mommah, ciƙin maɗauƙaƙin mamaƙi tace " yaya aka yi kika san Fadeel ne ya aureni? Mommah please ki gayamin kinjii" fadeelah ta karasa cikin zumudi.



Raba jikinsu Mommah tayi suka zauna kan hada'dd'en gadon daƴa ƙawata daƙin yayinda fadeelah ta kurawa Mommah ido cikin mamakin ta yanda aka yi ta sani...


Fuskar Mommah dauke da murmushi na zallan farinciki tace " a lok'acin da ake rikicin waye ya kawo lefen farko, nima hankalina ya tashi sosai, nan na sake kiran wanna matar wacce ta kasance matar Alhajin sufyan. Cikin dare na roke ta da Allah ta gayamin waye ya kawo lefen...
Matar bata boye min ba, ta gayamin komai, sannan tace kada na fada wa kowa domin shi Fadeel tare da alhajin sa sun shirya yi miki suprise, sosai nayi farinciki mara mitsaltuwa ganin zaku mallaki juna, kuma gashi finally burin fadeelah ɗa Fadeel ya cika"



"Wayyo! Mommah dama kina da labari baki gayamin ba, Mommah am so happy, bazan yadda zan yi expressing farincikin ɗa naƙe ciƙi ba"



Sai kuma fusƙar ta ƴa baƴƴana ɗamuwa tace "amma Mommah yaya kike ganin daddy zai d'auki maganar nan, zai aminci kuwa? Ina fargaban hakan Mommah"



"Kada ki damu kanki sweetheart, ina mai tabbatar miki Fadeel zai samu karbuwa wajen professor wanna karon, ba dai arziki bane kuma gashi Allah ya bashi fiye da zaton mutum, dan haka ki kwantar da hankalin ki kinji ko?"


Jinjina kai Fadeelah tayi fusk'arta dauke da murmushi, nan suka cigaɓa ɗa tattauna maganar.......




***** ***** *****




Bangaren minister Sa'id kuwa sosai hankalin shi ya sake mugun tashi, musamman daya samu labarin daurin auren Fadeelah ɗa wani, ba da Jameel ɗan shi bane.



Ga jameel ya tada hankalin su, ya hargitsa ko ina na gidan irin na sangartattun wasu y'ay'an da basa samu kwaba tun suna kanana.


Babu abinda minister Sa'id da matar sa suke sai kokarin lallashin sa, amma ina K'amar kara zuga shi suke.



Nan fa minister ya kara jin zafin abinda professor Imran mai naira yayi masa, bai taba tunanin amintakan dake tsakanin su bai kai aminta ba sai ƴanzu, tunda gashi ya tsalle shi ya bawa wani auran Fadeelah'n....



Nan ya d'auki alwashin sai ya bincika, ya kuma bibiyi rayuwar yaron da aka aura wa fadeelah'n. Ɗomin yaji shi dan uban waye ne, saɓoɗa sai yanzu tunanin sanin cewa Alhaji Sufyan Rufa'i bashi da 'ya ko ɗa a duniya ya zo masa....

zuwa ƴamma estate din ya rage yan'uwan na jiki wandanda suke nesa, wanda su ma gobe zasu tafi...




Ɗa misalin ƙarfe tara na dare fadeelah ta fito ɗaga toilet sanye da bathrobe, lotion mai saukin zafi ta shafa a lafiyayyan farar fatar ta, kana ta fesa tsad'add'en body spray mai suna *lalique* bayan nan ta shafa oil perfume mai suna *fogg abnat* wani mugun k'amshi mai sa nutsuwa ke tashi a jikinta, wasu riga da wando masu kauri na company'n *Dior Burberry* red color ta sanya, kana ta saka wani hula mai kyau baki, sai irin gajeren Safan nan shima

Please Login or Register in order to submit comment