Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin an kirata da hajiya lallai idan baka dashi ka sha kallo...


Daidai kan kofar gidansu mai akori-kura ya tsaya kana ya fito ya shiga sauke mata kayan, sai daya sauke duka kana ya fara shigar su cikin gidan, ya kuwa samu Fadeel zaune gaban murhu yana fifita wuta da alama girki yake... Da kallon mamaki Fadeel yabi mai akori-kura, ba tare da ya iya furta koda kalma daya ba, domin ya gama bayar wa batan gida mai akori-kuran yayi, ajiye muficin yayi ya bi bayan mai akori-kuran... Wani zallan mamakin ne ya sake kama shi ganin Mahmah a tsaye. "Mahmah" ya kira sunan ta muryar sa na bayyana mamakin da yake ciki..


Murmushi mahmah ta sakar masa ba tare da tace komai ba, kallon ta kawai yake kamar yaga sabuwar halitta, ganin idon mai akori-kura ya hana shi yin magana
Bayan mai akori-kura ya gama shigar da kayan, Mahmah ta zaro dubu biyu ta bashi, da wani mamakin dauke a fuskar sa ya sake bin Mahmah da kallo ko ina ta samu kudi? godiya sosai mai akori-kura ya dinga zuba wa yayin da Mahmah ta ja hannu shi suka shiga gidan, kan tabarma ta zaunar da shi ita ma ta zauna kana tace "nasan damuwar ka Fadeel, na kuma san tambayar dake bakin ka...."


Nan ta shiga bashi labarin haduwar su da Fadeelah, amma ta biyo abinda doctor Gabriel yace, shima yayi mamaki ya kuma ji haushi da tsanar nurse din, domin babu abinda ya tsana kamar a wulakanta masa uwa koda kallon banza ne, baya so.


Ajiyar zuciya ya sauke a fili kana yace "amma Mahmah da baki karbi kudin ta ba, ni bana so wani ya miki abu matukar bani bane, ina kuma fatan Allah yasa na kai minzanin da za kiji dadi har ki bawa wasu, sai wani yaba ta kike dan baki ga fadeelah ta bane, na tabbata ta fi wanna komai da kika lissafo" ya karasa cikin yanayi na shagwa'ba...


Dariyar Farincikin mahmah ta saki, saboda Kalmarsa ta karshe.
Ta san shi sarai yana da zuciyar nema sannan baya dogara da mutum, wanna karsashin nasa na burgeta sannan tana alfahari da hakan, kuma zata cigaba da alfahari da hakan ko da bayan ranta ne.


"Fadeel my son kamar yadda na gaya maka banso karban kudin ba, kai ma kasan halin mahmah'nka, sanya wa tayi cikin ledar maganina batare da ta jira ba ta tafi, kuma a duniyar nan kana ganin akwai macen da zan yaba ko zan so da zata wuce Fadeelah'n Fadeel dina?" Ta karasa cikin sigar tambaya kana ta cigaba "kawai yarinyar na da girmama na gaba da ita hadi da sanin mutuncin dan Adam, hakan yasa maganar ta ya shiga zuciyata matuka, amma duk da haka na fi jin Fadeelar Fadeel dina a zuciyata"


Murmushin farinciki ya saki kana ya rungumeta cikin kaunar ta yace. "Muga maganin ki Mahmah, har yau kin ki gaya min wani irin ciwo kike" Fadeel ya fada da damuwa saman fusk'ar sa.
Ledan maganin ta boye domin sam bata son ya sani, ta rufe zancen da cewa "wai me dan albarka ke dafa wa Mahmah'n sa ne?"


Murmushi yayi yace "taliya zan dafa miki kada ki dawo kina jin yunwa, gashi wutar ma taki kamawa sosai"


"sannu dan albarka, ai sauke wanna girkin zanyi, tunda har kalanzir(kerosene) na siyo galan daya, sai inyi mana jar miya da naman kazar nan, ai Allah ya yayi wa wanna yarinyar albarka, yaushe rabon mu da miyar stew (dage dage)" ta kai ayar maganar tana shiga daki domin boye maganin kamar kullum gudun kada Fadeel ya gani, kana ta fito ta fara kokarin dora musu girki....


*** *** *** ***

A dan gagauce ta fito daga bathroom sanye da bathrobe fari kal, tsadaden lotion daya dace da kalar skin dinta ta fara murzawa a lallausan farar fatar ta, bayan ta gama ta sanya inner wears farare kal, ta bud'e closet dinta mai murfin glass gaba dayan sa, take uban kayan sawar ta ya bayyana wanda koda shekaru ashirin nan gaba zasu ishe ta a wadace, hannu ta dora a kugu tana bin kayan da kallo, karshe dai ta ciro wani pencil trouser hadi da wani fashion riga mai hannun armless, sai kimono mai shara shara hadadde black color, sai dan mafayin rolling karami duka na company *PRADA* bayan duk ta sanya kayan tayi rolling batare da ko digon makeup a fuskar ta ba, amma tayi kyau sosai mai jan hankali kuwa, bangaren da take ajiye zallan takalma ta nufa, wasu hills masu tsini ta sanya kirar *HELLS STUART WERITZMAN* wanda tsadar sa zai kai *$104,765* da ganin takalmin ma ba sai an fada ba kasan tsadadde ne, turaren *Majesty* mai dadin kamshi ta fesa sama sama hadi da daura agogon zallan zinari kana ta ɗauki wayar ta wanna karon kirar *Gold striker iPhone 3Gs supreme da kudin sa yakai $3.2million*, dan hand bag ta dauko kalar takalmin kana ta fice cikin sauri kamar ba takalmi mai tsini bane a kafarta, wanda hakan zai tabbatar wa mutum cewa ta saba da saka su...


Ɓangaren Mommah ta nufa ta same ta tare da Daddy zaune suna dan taba hira, sallama tayi duk suka amsa cikin kaunar ta fuskar su dauke da murmushi kana ta nufi Daddy ta bashi sumbata a kumatu haka zalika Mommah... Babu bata lokaci Daddy ya mike yana gyara zaman tsadaddiyar rigar shaddar jikinsa da aka yiwa ɗinkin zamani, sai shekarun sa suka sake buya, hannu Fadeelah ya kama suka fice bayan sun yi sallama da Mommah...


Suna fitowa farfajiyar gidan suka tarar bodyguard's dinta dama na Daddy tsaye jikin tsadaddun motoci jere reras har guda goma, cikin sauri bodyguards biyu suka bud'e masu kofofin wata mota kirar *FERRARI LA FERRARI* fari, kana bodyguards suka shiga sauran motocin taran suka fara fita daga gidan a jere, motar da su Fadeelah ke ciki shine a tsakiyar motocin taran domin tabbatar da tsaro.

Babban hall din da sukan yi meeting ko wani sanarwa wa ma'aikatansu da kuma sauran bushiness partners suka nufa... gaba daya kowa ya hallara su kadai ake jira, zama suka yi nan aka gaisa cikin wayewa kana suka fara tattauna abinda ya kawo su.
(Kasancewar duk meeting ko wani abu daya shafi dukiyar Daddy to da fadeelah yake zuwa domin a dukkanin kadarorinsa sunan ta ne)
WANNA KENAN


*** *** *** ***

Zaune suke a *ORIENTAL HOTEL* gaba d'aya sun manta kowa a duniya saboda hirar soyaayyar da suke babu kama hannun yaro, hakan yasa suke jin kansu tamkar su kadai ne a duniyar, kallo daya zaka musu kasan cewa su di'n masoyan asali ne masu so da tattalin junan su.
Cikin zakin muryar ta tace "har yanzu baka zo gidanmu ba, ban san meyasa ba, kuma Mommah da Daddy na basu da matsala" ta karasa a yangance, wanna mutum zai yi tunanin kirkirowa tayi, sam ba haka bane dabi'ar ta ce hakan.


Murmushin ƙarfin hali ya sakar mata, har ga Allah yana fargaban zuwa gidan su Fadeelah domin bai san a wani yanayi iyayenta zasu karbe shi ba. Kullum da kalar waya, kayan sawa, mota da zata yi amfanin da shi, duk da kasancewar sa talaka amma yasan tsadaddun abubuwa, domin a makaranta yayi rayuwa da mutane kala kala hakan yasa yake da sani kan abubuwan rayuwa da dama, duk da hakan yana fatan halayen iyayen Fadeelah ya zama irin na yarsu, saboda ba zai taba juran rasa ta ba, da kyawawan idanun sa ya tsare ta domin kwantar mata da hankali yace "Darling am sorry, in sha Allah zan zo gaida su Daddy soon"

Murmushi farinciki ta saki kana tace "da kuwa ranar nayi farinciki"
Martanin murmushin ya mayar mata zafaffan soyaayyar ta na ratsa shi, yana kallonta ta bud'e handbag dinta, waya ta miko masa tana kallonsa da murmushi, da kallo yabi wayar dake sanye a tafin hannunta banda daukar ido babu abinda take yi wanda ya kasance kirar *SUPERNOVA IPHONE 6* "ka rike ka dinga amfani dashi, kaga idan ma muna son ganin junan mu sai muyi video call ko?"


Bakin ta dake motsi kawai yake bi da kallo kana ya girgiza kansa alamun "a'a" bata fuska tayi kamar zata yi kuka tace "baka son abun hannuna ko?"


Girgiza kai yayi yace "ta ya ya zan ki abinda ya fito daga hannun abra kaunata? Kiyi hakuri kin ji bazan iya karba bane, I prefer na cigaba da amfani da wanna" ya fad'a yana daga dan itel d'insa.


Kallonsa take with much respect, ba kadan ba take matukar son wanna halin nasa, sam bashi da mataciyar zuciya kamar na wasu samari da suke son mace ta dinga yi musu hidima, tabbas ta ga Samari da yawa da suke son ta dan dukiyar ta, hakan yasa bata soyaayya amma daga haduwar ta da Fadeel ta fuskanci cewa ba duka aka taru aka zama daya ba. Duk da bata so yanda yaki karba ba amma ta jinjina masa kai kawai hadi da cewa "ok ba matsala"

Murmushi ya saki kana ya yi tunanin yin abinda zai faranta ranta, take ya fito da cardboard paper ya fara zana fuskar ta kamar yadda yake a duk lokacin da suka hadu.

Gyara zama tayi fuskar ta dauke da murmushi yayinda ya cigaba da zana ta.


Sai misalin karfe takwas na dare suka yi sallama... bakin mota ya rako ta ta shige tana daga masa hannu, kasancewar daga company ɗin su tace bodyguards dinta su wuce gida, duk da sun san sun karya dokar daddy, amma kuma basu yi jayayya da Fadeelah ba...

Daidai tangamemmen gate din estate dinsu ta danna horn mai gadi ya bud'e mata, babu bata lokaci ta danna hancin motar ciki, sai da ta daidaita parking ta fito hannun ta dauke da cardboard paper, gabanta ne ya dan fadi ganin bodyguards dinta tsaye cirko cirko kansu a kasa yayinda Daddy ke tsaye gaban su fuskar sa daura tamau da alama balbale su da fada yake...



(Not edited)

In sha Allah zanyi kokarin baku update gobe, nagode sosai da kaunar da kuke nunawa books dina😍



Share fisabilillah
Comment comment comment



Saboda Allah vote and follow me on wattpad @NoorEemaan 🥺❤️




Editing is not allowed❌


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(Its all about love, scracife, hatred and destiny)


*First edition*


_by NoorEemaan_📚✍️


Wattpad
@NoorEemaan





Juma'at Mubarak to all Muslims ummah,
Allah ya sa damu da Alkhairi cikinta, yasa muyi kyakyyawar karshe, mu kuma cika da kyau da imani. NoorEemaan na kaunar ku my fans❤



_I must say this....😃 What a coincidence! a ranar da nayi typing wanna page din Friday ne, which is last year, ikon rabbi kuma Gashi nayi reposting again still that Friday_😻




Page 13-14


............A sanyaye ta karaso gaban su, daidai lokacin Daddy ya dagawa bodyguards dinta hannu alamun su tafi, ba musu suka fice kasan su a kasa alamun girmamawa, yayinda suka ji relief na ganin Fadeelah, akasin hakan kuma da sunan su gawa a hannun Alhaji Imran.



Bin bayan Daddy Fadeelah tayi har main parlour, hannun sa goye a bayan sa ya juyo gareta kana ya jefa mata tambaya kamar haka " a iya sanina 'yata mai bin umarni na ce, sannan bata da wurin zuwa daga company sai gida, sannan yaushe kika fara fita ke kadai ba tare da bodyguard ba princess? Did you know thousands of enemy we have out there? (Kin san dubanin makiyan da muke dashi a gari?)" Ya karasa a dame, yana nuni da yatsa, duk yanda yaso yi mata fada abin ya gagara, matsanancin soyaayyar 'yarsa ta hana shi yi mata fada domin sam baya son ganin bacin ranta koda na sakan daya ne.


Ajiyar zuciya ta sauke, domin abinda tayi tunani daban, tabbas ta san cewa kaunar da yake mata yasa yake bata tsaro domin kula da lafiyar ta. Cikin zallan son mahaifin ta kana murya a sanyaye tace "am so sorry Daddy, bazan sake fita ba tare da bodyguard ba, na fita shakatawa ne, ganin ba nisa nayi sosai da gida ba yasa nace su taho gida" ta karasa cikin shagwaba da marairaita ta yadda zai fi tausaya mata.



Murmushi mai taushi ya sakar mata, wanna maganar da ta yi ya wanke masa dukkanin damuwar daya dauki awanni cikin sa, "its ok my princess, sannan ki dinga barin wayar ki a bude saboda irin haka, domin dana samu wayar ki da hankalina bai tashi haka ba"



Murmushi tayi, domin soyaayya ta dauke mata hankali har ta manta da wata aba wai waya "in sha Allah Daddy zan kiyaye, ina Mommah nah?"



"Tana part d'inta tun rana kanta ke ciwo, ita ma hankalin ta gaba daya ya tashi da rashin dawowarki... ni nace taje ta kwanta ta samu huta, yanzu zanje part dinta domin sanar da ita kin dawo saboda hankalinta ya kwanta, ke ma je ki huta good night" ya fad'a yana bata sumbata a goshinta....




Handbag dinta kadai ta ajiye kana ta dauki gum(gam) data siya takanas domin manna hotunan da yakan zana na fuskarta a duk haduwar su.


Tsaye tayi tana bin zanen da kallo wanda yanzu sun dawo shida reras, har yau ta kasa gane wanne yafi kyau cikin zanen domin dukkansu ba baya wurin kyau, murmushi take saki akai- akai hirar da suka tayi dazu ke dawo k'wak'walwarta, daga karshe ta cire kayanta ta fada wanka bayan ta kunna wayoyinta, ta jima sosai a toilet duk cikin sunan wanka kana ta fito daure da towel, lotion mai k'amshin gaske ta shafa kana ta sanya pajamas masu kyau pitch color na company *NIKE* dan karamin hijab fari half sunnah ta sanya, wata yalwataccen jallabiya kirar saudiya ta dora kan pajamas din kana ta tayar da sallah...

Bayan ta iddar ta cire jallabiyan ta haye gado, take wayarta ta dauki kara, lumshe ido tayi kana ta bud'e a nutse murmushi dauke kan fuskarta domin tasan Fadeel ne, domin shi kadai ta sanyawa wanna ringing tone din, latsa Kore tayi ta kara wayar a kunnenta hadi da furta "Assalama alaykum" cikin zazzakar muryarta.

"Wa'alaikumu salam" ya amsa yana kara curewa kan 'yar yololuwar katifarsa da alama muryar tace ta haddasa masa shiga wanna yanayin

"My darling yakike, ya gajiya, Fatan kin je gida lafiya?"duka ya jero mata tambayar a lokacin daya.
A shagwa6e tace "Alhamdulillah, wallahi my one na gaji sosai, amma yanzu na fara warwarewa sak'amak'on jin muryar muradina, muradin raina, Yes my heart desire".
Murmushi ya saki cikin wani sabon shauki yasake k'amk'ame jikinsa kana yace "I hope ina tare dake, I hope yanzu mu ma'aurata ne dana yi miki tausa" ya karasa cikin rada.

Murmushi mai sauti ta saki, tana ji ina ma Ina ma su din ma'aurata ne, da hakika sun gina rayuwar aure mai cike da so hadi da birgewa.

"Darling kaunar ki zata haukata ni, kinsan har mafarkin nake akan ki kullum, jiya da asuba Mahmah tazo tashina Saboda na makara taji ina ta kiran Fadeelah cikin bacci, dan Allah ki rike mun amanar kanki bazan iya juran rasa ki ba a rayuwa, ji nake tamkar dan soyaayyar ki kadai aka halicce ni" ya karasa cikin iyakar gaskiyar sa.

Pillow ta k'amk'ame a kirjinta, maganganun sa na shiga jini da tsokar jikinta har wani tashi sigar jikinta ke yi alamun maganganun na shigar ta sosai.



Cikin wani salon so tace "my one, kasani cewa babu kowa a birnin zuciyar Fadeelah fiye da Fadeel dinta, sannan Abadan da'iman muna tare, mutuwa ce zata raba mu in sha Allah"


Ajiyar zuciya mai karfi ya sauk'e daya sanya taji wani sabon so da tausayin sa, cikin muryar rada yace "Darling mutuwar ma nafison ta d'auke mu a lokaci daya, ko kuma ni na fara mutuwa domin bazan juri rasa ki a rayuwa ta ba..."

Katse shi tayi da cewa"gwara ta dauke mu a lokaci daya, mu tafi tare, nima bazan juri rasa ka ba my one, we are made for each other I love you"


"I love you so much too my Darling, ki kwanta kiyi bacci, ki yi mafarkina bye muaaahh" ya karasa da sakar mata sumbata ta wayar


Wani sanyi dadi ke ratsa ta hakika babu abinda ya kai kasamu masoyi mai son ka tsakani da Allah. "love is sweet when it's new, sweeter when its you fadeel, and sweetest when it's pure" ta fada a bayyane fuskarta d'auke da murmushi, addu'ar kwanciya bacci tayi kana ta rufe jikinta da duvet babu jimawa bacci mai dadin gaske masu cike da mafarkin Fadeel ya d'auke ta...


*WASHEGARI*
suna zaune a dinning table suna breakfast, Fadeelah sai murmushi take ita kadai har Daddy ya farga yayi gyaran murya hadi da cewa "My beautiful princess, wanna murmushi fa ke kadai? kwanan nan na kasa gane miki fa, You seems over happy" ya fada shi ma da murmushi kan fuskarsa alamun farincikin daya tsinci 'yarsa a ciki yayi masa dadi...



"Atoh professor nah, taya ni tambayar ta, domin yanzu hardly kaga fuskar sweetheart ba murmushi, ya dai kamata ki gaya mana what's the secret behind" Mommah tace tana kai Irish omelette bakinta.



Dariya tayi cikin jin kunya, kana tace "babu komai Daddy, Mommah"

"Haka dai kika ce, amma bari idan tayi tsami zamuji koma menene, ko professor nah?" Ta fada tana kallon Daddy.

"Haka yake my first Lady" Daddy yace cikin salon su na manya.



Fadeelah kanta a kasa tana cin chips dinta daya bayan daya, yayinda take tunanin shin ta gayawa Daddy'n ta cewa ta samu mahadin rayuwar ta, a life partner ko a'a?....✍️




_In sha Allah gobe ma zan sake baku sabon update da sannu zamu shiga cikin labarin..._
_Amma two pages as promise tunda reposting muke_


*Thanks my people da kulawar ku gareni a sakamakon jina shiru da kuka yi jiya, i was damn busy ko data ban kunna ba jiya, wadanda suka yi min mgn private dama groups, ina godiya sosai*



Share

Comment

Vote

Editing is not allowed❌


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


🍇🍇ƘYAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)


_by Noor Eemaan_📚✍️


Wattpad
@NoorEemaan



Page 15-16

Sau ba adadi ta budi baki da niyyar yin magana, sai taji wani abu mai nauyi ya rufe bakinta, karshe dai ta yanke hukunci bari zuwa nan gaba sai ta sanar da shi komai...




Bayan ta gama breakfast ta koma bangaren ta, da tunanin idan ta dawo zata leka part din kakanin ta da sauran ahalin gidan su gaisa domin yau kwana hudu kenan bata leka su ba, kasancewar akwai tazara mai yawa tsakanin parts din... Da wanna ta shiga toilet, cikin jaku'zzie ta fada, lumshe ido tayi ruwan dumin na ratsa ta, *L'occitane verbena shower* ta fara murzawa a farar fatar ta, kasancewar ta kusan yin latti yasa tayi wankan a gurguje ta fito daure da pink towel, lotion take shafawa idanunta kafe kan hotunan zanenta dake manne a bango, murmushi take saki ba tare da tasan tana yin hakan ba.



Inner wears ta saka, kana ta dauko wata hadaddiyar gown na company *Giorgio Armani* banda walwali babu abinda rigar ke yi, dan veil din rigar ta yana a kanta kana ta dauko takalmi wage da handbag duka na company Giorgio Armani din.



Duk da bata son yin make-up sosai, amma haka nan ta ji yau tana sha'awar yi, a tsayen ta fara goga hada'dd'en powder dinta daya dace da skin color d'inta sannan ta sanya k'walli hadi da goga pink lip gloss, fadin kyau dada haduwar fadeelah bata baki ne, ita kanta sai data yaba duk da ta san ita din mai kyau ce, amma tabbas *idan kana da k'yau ka kara da wanka* inji malam bahaushe.

*DKNY(golden delicious millions dollars fragrance)* shine turaren da Daddy ya kawo mata tsaraba daga USA wanda kudin sa 1 million ne, sannan shine turaren mai mafi tsadar gaske wanda babu kamar sa a yanzu. Fesawa tayi Sama_sama tana yaba kamshin turaren mai sa nutsuwa, hakika DKNY yaci kudin sa, glass ta sanya a fuskarta brown kana ta fito bayan ta dauki wayar ta kirar *falcon supernova*
Ganin tayi latti sosai yasa bata koma part din su Daddy ba, direct ta nufi inda motoci ke fake suna jiran ta, kamar kullum motar da ake tanada domin ita kadai ne, wanna karon *Bugatti La voiture Noire* aka bud'e Mata kalan fara, yayinda duk suke gaishe ta cikin girmamawa, fuskarta a sake kana da murmushi ta amsa, zama tayi aka rufe mata kofar, gate man ya wangale masu gate suka fara ficewa dayan bayan daya....


Idanunta na kan wayarta tana danne-danne, da alama chatting take kamar ance ta dago kanta ta ga wani kamar Fadeel ya taho a kafa, zare glass din idanunta tayi, "tabbas my one ne" ta aiyana a ranta idanunta kan Fadeel din tace wa driver "stop the car!" ba musu mai tuka ta ya tsaya, take sauran suma suka tsaya... Bata jira ba, ta balle murfin motar ta fito, har ya dan gota su domin sam bai lura da ita ba...

Tana jikin motar ta hard'e hannunta kan kirjinta ta kira shi a shagwa'be
"my one"
cak! ya tsaya, kana ya juyo murmushi d'auke kan fuskar sa. Takowa yayi ya dawo gabanta yace "my darling?"
Bata rai tayi cikin wasa tace "Shine kayi fuska ko, bayan ka ganni"
Murmushi ya kara saki shagwa'bar ta na tafiya da shi matuk'a "my Darling afuwan, sam ban ganki ba" ya fada cikin yanayin na dan ji nauyi, domin har kokarin boye kafarsa data yi butu-butu da kasa yake alamun ya sha tafiya sosai....


Dariya ce ta so kamata domin ta fahimce shi sarai, shi bai san duka wanna bai dameta ba, shi takeso, ba wai kyau, qualities ko wani abu daya shafe shi ba.

Kura masa ido tayi tana yaba kyawun sa, sam bashi da haske ko kadan, amma yana da mugun kyau da wasu fararen ma basu da shi, kallon kafar tasa ta sake yi kana ta dawo da kallonta kan fuskar sa tace "ina kaje haka?"
Shafa kansa yayi yace "Mahmah ce ta aike ni kai kudi gidan biredi, fatan sauraniyar Kyawawa ta tashi lafiya?"

Murmushi tayi, tausayin sa fall zuciyar ta tace "alhamdulillah, kai fa?"
"Same" yace a tak'aice.

Murmushi tayi wani lokacin tana son wanna halin sa na rashin son dagon magana, sannan tasan idan tace ya hau mota su ajiye shi gida ko bashi kudin mota tofah bazai yarda ba, ta rasa wani irin mutum ne dashi daya dau duniya da matukar saukin gaske, a fili tace "my one akwai maganar da nake so muyi da kai, it's very important"


"Ok ba matsala zamu yi waya, then muyi fixing wurin haduwa ko?"

"Toh shikenan bye na makara office" tace tana daga masa hannun ta.

"Zan yi kewar ki sosai darling, take care I love you"

"I love you too" tace tana shiga motar ta.

Yanda bud'e murya yanda zata ji yace "Darling kinyi kyau sosai, karki bari kowa ya kalli min Kyakyyawar fuskar ki fa..."


Dariya tayi domin Yadda ya bata rai sai ya dawo mata kamar wani yaro karami.


Kamar kullum a nutse ta shiga cikin company, duk suka gaisa da ma'aikata(staff) d'inta, kana ta wuce office

"wallahi abokina yarinyar boss na matukar tafiya da ni, naso ace tazo a matsayin wacce bata fi karfina ba, da ba shakka zan gabatar mata da kaina a matsayin masoyinta, domin sosai nake sonta" Cewar wani matashi dake sanye da kaya mai dauke da tambarin company.


Abokin nasa yace "kasan Allah, ina jin na fika son yarinyar nan, kowa a company nan maganar ta yake, mutane da dama sun ce matukar cutar dake damunta ya kai minzanin da ya gaza, to zasu iya Sadaukar mata da nasu ciki har dani, ban taba ganin mai son jama'a hadi da talakawa kamar yar boss ba".


Haka suka cigaba da hira duka dai kan Fadeelah, haka kullum

Please Login or Register in order to submit comment