Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina son ganin Fadeelah ta"



Sosai doctor ya tausaya masa hakan yasa yace "I understand your condition, but take it easy, you can see you are not wearing cloth, lemme get you some cloth and then book a flight for you)(na fahimci yanayin ka, amma ka bi a sannu, kaga dai baka da kaya a jikin ka, bari na samo maka kayan sawa, Sannan na yi maka booking jirgi)"




Jinjina kai Fadeel yayi, takalmar sa da wayoyin sa, da kuma wasu abubuwan sa masu muhimmanci ya gani saman wani wardrobe, a hankali ya mika hannun sa ya dauki check book, kana ya rubuta kudi daƴa san zai isa a yi booking jirgi da siya masa kayan, mikewa Kelvin smart yayi, ya fice cikin sauri...



Wajen booking flight kelvin smart ya fara zuwa, yayi sa'ar samun wanda zai daga zuwa Nigeria a daran yau, komai d'aya kamata yayi, ya biya, kana ya nufi wani hada'dden boutique ya siya masa wando, riga, jacket, p.cap, boxer, singlet, perfume man shafawa, sabulu da soso, a wani kyakyyawan jaka aka yi masa packing komai kana ya fada motar sa ya nufi asibiti...





Kwance ya tarar da Fadeel, kayan ya ajiye a gefe yana yiwa Fadeel sannu, Kana ya mika masa ticket din yana fada masa cewa karfe takwas na dare jirgin zai tashi zuwa Nigeria...



Da taimakon Kelvin smart ya yi wanka, domin ko taka kafar baya iyawa sosai, domin har yanzu jinin bai zauna a jikin sa yadda ake so ba, ba kamar nashi na halitta ba...



Bayan ya gama shirya wa cikin kayan, Kelvin smart ya fesa masa turare,kana ya shiga bashi shawarwari ta yanda zai dinga kula da jikinsa, da cin abinci mai kawo jini sosai da dai sauran su...



Sosai Fadeel yayi godiya ga doctor kelvin, domin yayi masa taimako sosai, wayar sa, hoton aikin da aka masa wanda aka dinga dauka da bayanai yanda aka yi komai na ciki, wanda ka'idar asɓitin ce haka, ana daukar hoto da bayanai, da dai duk wani abu mai amfani sa cikin wanna K'yak'yyawan jakan da aka saka masa kaya a boutique, ya sanyawa Fadeel kayan a ciki, number'n Fadeel din Kelvin smart ya karba, domin yace lallai sai ya gaisa da Fadeelah a waya, domin soyayyar su na burge sa matuka, ba musu Fadeel ya sanya masa domin ya cancanta, haka ya dinga deɓewa Fadeel kewa yana jan shi da hira har agogon America ta buga 7:00pm




Da kyar Fadeel ke jan kafarsa har wajen mota, domin tamkar mai koyon tafiya haka ya dawo, dan ma yana ɗa jarumta da ko iya taka kafar ba zai iya ba, Kelvin smart ne ya kai shi har airport, rungume sa fadeel yayi suka yi K'yak'yyawar sallama har sai da kelvin smart ya ga tashin jirgin su kana ya koma hospital din su....



***************



*NIGERIA*
A hankali yake saukowa daga matataƙalar bene.... Bayan ya gama saukowa ya bud'e jakar nan da kelvin smart ya bashi, ajiyar zuciya ya sauke ganin wayoyin sa, domin da bai san ta yanda zai isa gida ba, in dai ba taxi zai hau ba...



Gashi da yawan mutanen wajen basu san cewa shine the famous billionaire Architecture FFM ba, sakamakon p.cap d'aya rufe rabin fuskar sa..



Hannu yasa ya dauki wayar ya kunna, hoping to see charge, luckily ya kuwa samu 98percent, Sosai yaji dadin hakan, ya kuma san wanna aikin doctor kelvin ne, domin yasan cewa chajin d'aya zo dashi ya kare, saɓoɗa shekara d'aya ba wasa ba, babu jimawa network suka hau kan wayar, dama bai cire layukan ba...




Number'n babban escort d'in sa ya kira, ya kuwa ci sa'a ya samu...



'Am at murtala international airport now" abinda ya iya fada kenan ya katse kiran.

Ɗaga bangaren escort ɗin kuwa sosai yayi farinciki, duk da bai san ina fadeel din ya tafi ba, amma yaji dadi ainun daya ji ya dawo, nan fa ya shiga sanar da sauran, cikin kankanin lokaci gidan ya dauka cewa boss din su ya dawo, kara gyara gidan suka yi, duk da kullum sai sun yi gyaran, amma wanna na musamman ne, Yayinda chef's suka shiga yin aikin su na girki, escort din sa kuma suka nufi airport cikin sauri.




Tun daga nesa Fadeel ya hango su sun shigo, hakan yasa shi mikewa a hankali, domin ya kasa jure tsayuwar har sai da ya zauna, cikin girmamawa da murna duk suka gaishe shi, da murmushi a fusk'ar sa ya amsa, motar suka bud'e masa ya shige, kana suka bar airport din...




Bayan isar su gidan, sosai dukkanin ma'aikatan sa suka kawo gaisuwa, a mutunce ya amsa musu, kana ya nufi bedroom d'in sa da kyar, ya duba ko ina bata nan, part dinta ya nufa nan ma bata nan, wasa wasa ya shiga zagaye dakunan gidan amma babu Fadeelah'n sa, sosai tashin hankali, damuwa, hadi da mamaki ya kama shi ya shiga tunanim ina taje? zama yayi a bakin matataƙalar bene yana sauke numfashi domin ba k'aramin kokari yayi wajen neman ta ba, tunanin tambayar ma'aikatan gidan yayi, sai kuma ya fasa domin baya son su san cewa baƴa da masaniya inda Matar sa take, tunanin kiran ta ya sake fado masa, amma sai ƴa fasa, ya kuma yi tunanin zuwa estate din su ya duba ko tana can, da kyar ya mike ya koma part din shi ya yi wanka yayi brush, kana ya Sanja wasu kananun kaya marasa nauyi.....



*******



Zaune suke a parlour'n Daddy gabadayan su. Mommah, Daddy da Fadeelah, fada Mommah take mata sak'amak'on damuwar da take yawan saka kanta, domin abin ya fara affecting dinta, gashi kullum cikin rashin lafiya take, cinyar Mommah ta fada ta shiga rusa kuka, ita kam hakurin ta ya fara karewa, ace shekara daya da kwana d'aya babu mijinta babu labarin sa, ga gaban ta da ta ji yana fadu'wa sosai a yau din..
tausayin ta ne ya kama Mommah sai ta shiga rarrashin ta, Daddy na zaune yana kallon su ya ma kasa magana Sak'amak'on shima rashin dawowar Fadeel din ya fara damun shi sosai...


Suna cikin wanna halin, a bazata, ba tare da sun yi tsamanin ba, suka ga ya turo kofar ya shigo bakin sa dauke da sallama...


A razane dukan su ukun suka maida kansu ga entrance din shigowa, Fadeel suka gani tsaye jikin kofa yana bin su da murmushi Yayinda idanunsa suka ciko da kwalla ganin Fadeelah'n sa, cikin mayuwancin hali.

yes! shine a tsaye, duk da ya dan rame, ga kuma tabo a jikinsa a duk inda aka manne masa na'urori da ya bashi jini, but he still remain the handsome Fadeel with a good heart. Daddy ya aiyana a ransa...



Fadeeelah kuwa Murza idanun ta tayi taga tabbas shine tsaye a gabanta ko kuwa? hakan yasa cikin sauri ta mike ta nufi shi, da gudu ta dane shi yar jakar hannun shi ya wullar, ya rungume ta tsam, sosai ta fasa kukan farincikin ganin mijin ta abin sonta a lokacin data fidda rai da samun sa, shima sosai ya k'amk'ame ta, duk da rashin kwarin jikinsa sai d'aya rungumeta so tight domin ganin ta yasa har wani k'arfi yaji yana shigar sa, fadi yake...

"Am so sorry Fadeelah, ki yafe min kinjiiiiiiii, I know you have pass through a lot, am so sorry for that" ya karasa yana rungume ta da k'yau, Yayinda yake jin nutsuwa na saukar masa....



Da alama sun manta Mommah da Daddy na zaune.
fadeelah kuwa cewa tayi "meyasa kayi wanna abun mai hadari my one? ka tafi a shekara d'aya ban gan ka ba, ni na dace nayi wa wanna sanjin jinin, ka sha wahala sosai a tarayyar mu, da ni ka bari nayi wanna Sadaukarwa a soyayyar mu"




Murmushi mai sauti ya saki kana yace "Am so sorry Fadeelah, i swear ban san nayi shekara d'aya a kwance ba, a lokacin da Doctor ya sanar dani nayi shekara d'aya ba karamin tashin hankali na shiga ba, domin nasan kina cikin damuwa, kuma ni bazan iya juran ganin ki a wanna halin ba, ni ya dace nayi, domin kin cancanci hakan, kin manta Mahmah ta ce mu haifa mata jikoki, idan ban yi hakan ba Tayaya zamu rayu da zuri'ar mu cikin farinciki? Idan kuma so kike na auri wata sai mu haifi yara kin ga bazasu kasance SIKILA ba...." Ya fada domin tsokanar ta..
.


Duka tayi masa a baya, sai kuma ta shiga shafa wajen da ta dake shi, tamkar yar baby tace "toh ai da ni Mahmah tace ka haihu" ta karasa cikin salo na kishi, sosai hakan ya bashi nishadi, kara rungume ta yayi yace "I love you so Much my Darling wiffy, I can't live without you Fadeelah"


"I so much love you too my one, you re my everything" sosai yaji dadin kalaman ta hakan yasa ya fara dan juyi da ita a jikin cikin shaukin sonta...





raf raf raf... Mommah da Daddy suka Shiga yi musu tafi Yayinda hawaye ya cika idanun su na zallan tausayin su, sosai kuma soyaayyar su Fadeelah da Fadeel ta birge su Mommah...





Sosai Daddy yaji dadi ya kuma yaba da wanna pure soyayyar da fadeel ke wa gudan jinin sa.




Sai a lokacin suka tuna ashe basu kadai bane a falon, kunya ne ya kama su biyu, a hankali ya tsunkuya ya dauki jakar d'aya watsar, kana ya nufi wajen su, hannun fadeelah cikin nasa, yana kokarin dukawa domin ya gaishe su, Daddy yayi saurin rungume Shi cikin alfahari da son sa, tabbas Fadeel shine masoyi na hakika, ya kuma kara godewa Allah da bai rasa fadeel cikin zuri'ar sa ba....




Sosai suka yi masa barka, hadi da nuna farincikin da dawowar sa lafiya, fadeelah ba kunya ta manne a gefen sa, domin ji take idan ta matsa daga wajen sa, zata neme shi ta rasa...



Jakar hannun sa fadeelah ta karba, ta bud'e, kuka ta saka ganin yanda Fadeel yake kwance kamar gawa a hoto na'urori manne a jikin sa, bata kara kallon hoton ba Saboda tausayi...

Daddy da mommah ma sai da suka kalla duka, sun tausaya masa matuka, da kyar aka samu fadeelah tayi shiru, nan ya shiga gaya musu komai daga zuwan sa ƙasar, bai kara sanin komai ba, sai Jiyan d'aya farfado, sun yi mamaki ainun, Sannan sunyi farinciki ganin an samu nasarar aikin, ya jima sosai a gidan suna hira, domin har kitchen Mommah ta shiga da kanta ta dafa masa wake da allaiyahu d'aya ji naman rago, kana ta hada masa smoothie na kankana, ya kuwa ci sosai, domin a America abu mai ruwa ake bashi, shima ta cikin wanna abin da ake durawa wa majinyaci abinci ya ci (na manta sunan abun, fatan kun gane)



Sun kai awa uku suna hira cikin farinciki kana Fadeel ya bukaci su tafi gida, Yayinda Mommah ta hada wa fadeelah wani hadi na musamman na gyaran jiki, ta kuwa shanye duka, dama kullum haka take mata, cikin tea, fruit salad, da smoothie take sanya mata maganin gyaran jikin, amma sam fadeelah bata sani ba, domin maganin da zaki, duk da ta jima kuwa tana jin wasu sauye² a jikin ta amma, sam bata san cewa maganin Mommah ne yake aiki ba....




Har haraban estate din, mommah da Daddy suka raka su, cikin girmamawa escort din sa duka suka gaishe da Daddy da Mommah, a sake suka amsa, nan aka bud'e musu motar, fadeelah ce ta fara shiga kana Fadeel ya shiga shima, a jere reras motocin sa suka bar gidan, ƴayinda su fadeel suka shiga dagawa su Mommah hannu..., kwalta suka hau, kana suka dauki hanyar banana island inda tamfatsetsen gidan Fadeel yake....





Share fisabilillah habibti'es



Comment



*(Follow and vote me on wattpad @NoorEemaan)*



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)



*WATTPAD*
@NoorEemaan





EDITING IS NOT ALLOWED ❌❌❌




Page 71-72




Tafiyar mintuna talatin ya kawo su banana island gidan, tsayuwar motocin ya sanya su Fadeelah sanin cewa sun zo cikin giɗan.


A hankali ta dago kanta daga kan kafadar Fadeel tana kallon shi ganin bai da niyyar fita.



A shagwa'be tamkar yaro dan shekara biyar yace "wiffy ki goya ni please"




Dariya ta fashe da shi, shagala yayi da kallon ta, Saboda dariyar tayi mata kyau ainun.

Gimtse dariyar ta tayi tace "my one ta ya ya zan iya goya ka" ta fada tana kara jin wata dariya na taho Mata.



"Wato dariya kike min ko? Kisan Allah sai yanzu na fara jin rashin kwarin kafar nan, domin a lokacin da Doctor Kelvin ya fada min shekara ta d'aya a gidan nan, hankalina ya tashi sosai,burina kawai nazo gareki, sai yanzu na fara jin rashin kwarin kafar, ko taka ta bana son yi" Fadeel ya fada yana kallon beautiful face din ta.


"Toh naji zan goya ka, hau toh" ta fada tana juya bayan ta, dariya sosai ta bashi wanda rabon sa dashi tun kafin ya tafi america, fusk'ar ta ya riko, a tausashe yace "wasa nake wiffy, banaso karamar siririyar matata ta balle"


Turo baki tayi jin yace karama, mannawa labb'anta kiss yayi kana yace "muje"


"To tsaya" tace tana fita da sauri, dayan bangaren ta zagaya, da taimakon ta ya fito, hannunsa ta dauka ta zagaya ta cikin ta, yayinda ta dora daya a kan kafadunta, suka shiga takawa, Yayinda ma'aikatan gidan suka Shiga kawo gaisuwa, duk inda suka wuce sai an gaishe su, a mutunci kamar yadda dabi'unsu yake suke amsa gaisuwar.


Bangaren Fadeel suka nufa, a hada'dden falon sa suka yada zango, zaunar dashi tayi tana sauke numfashi gajiya, hakika fadeel karfaffa ne....

"Allah my man dana goyaka dana balle wallahi kamar yadda kace"



Dariyar da bai yi niyya ba, ya saki...



Cikinsa ya shafa yace "Fadeelah yunwa nake ji, kuma girkin matata nake son ci, amma bana so ki wahala"



Murmushi ta yi tace "ba wani wahala my man, zan dafa maka kaji" ta fada tana nufar kitchen, duk da tayi mamakin jin cewa yana jin yunwa, amma ba abin mamaki bane idan akayi duba da chajin jinin da akayi masa, ga kuma maganin Karin jini wanda yake sa shi cin bacci sosai...


Sai da ta bacewa ganin sa kana ya dauke kansa. Bangaren fadeelah kuwa private kitchen din ta ta nufa, tsaye tayi tana tunanin abinda zata girka masa da bazai dauki lokaci ba, Saboda kada fadeel din ta yaji yunwa....


Tuwon semovita da water leaf soup daya sha naman kaza, stock fish, cat fish hadi da crayfish ta shiga hadawa, bayan awa d'aya da mintuna goma sha biyar ta gama komai, har da lemon kankana da saka ice block hadi da watermelon flavor tayi blending dinsu kana ta saka cikin wani jug mai k'yau hadi da kananun cups din sa, gabadaya part din ya dauki kamshi sosai...


Kimtsa kitchen din tayi, ta wanke abubuwan data bata, kana ta dauki tray din ta fito, zaune ta tarar da shi kamar yadda ta barshi, sai dai wanna karon hannun sa dafe saman fusk'ar sa, jin takun tafiyar ta ya sanyi shi bud'e idanunsa yana sakar mata murmushi, martani ta mayar masa, kan center table ta dora tray din....


"Sorry na barka kai kadai ko?" Tace tana zama a gefen sa.



" dont worry, Sannu kinji wiffy na sa ki aiki, kamshin girkin ki yasaka saliva dina diga, saura kadan ki ganni a kitchen din ki "


Murmushi kawai tayi tace "ka cancanci fiye da haka my one, yanzu da abinci zaka fara ko wanka?"



"Hmmmmmmm... wanka zan fara yi" ya fada yana kallon Hada'dd'en POP din saman dakin.


dawo da kallon sa gare ta yayi "kema kina bukatar wanka wiffy" ya fada yana mika mata hannunwan sa, taimaka masa tayi suka nufi bedroom d'in sa, ruwa ta hada masa a jaku'zzie bayan ta saka bath soak, fita tayi ta hango shi tsaye jikin kofar bathroom, kallon shi tayi tace "me yasa baka zauna ba, kafar ka fa"



"Rashin ganin ki yasa na taso domin zuciyata ta samu kusanci da taki zuciyar"



Murmushi ta saki mai sauti, ta hade hannayenta a k'irjin ta, sun jima suna jifan juna da kallon kauna, kana ta riko hannun sa suka shige toilet din, sai da ta tabbatar ya shiga cikin jaku'zzie kana ta ruga a guje ta nufi dayan bathroom, duk da kiran da yake mata kuwa, domin ta fahimci so yake su yi wanka tare...



Dariyar ta ta gimtse sanda suka yi tozali da juna, gashi ya riga ya ganta da towel babu halin gudawa, amma taji kunya kam, domin towel din karamin ne sosai....


Gaban shi tazo ta zaunar da shi, duk yanda take jin kunya haka ta daure ta fara shirya shi, domin idan bata taimaka masa ba, hakika bata kyauta ba, kananun kayan shan iska ta sanya masa, bayan ta shafa masa mai, body spray mai dadi ta fesa masa, kana tayi oiling gashin sa ta taje masa, sosai kuwa yayi k'yau tamkar black America.



Itama lotion ta shafa, body spray data fesa masa itama ta fesa a jikinta, kayanta ta saka wani straight fitted gown mai spaghetti hand, hadi da saka head band golden color, kamar yadda gown dinta ya kasance golden.



Light makeup tayi, daga hoda data shafa, sai kajol(kwalli) hadi da lipstick maroon color daya sata yin wani sihirtaccen kyawu d'aya zai narka zuciyar Fadeel...

Bayan ta mayar da make up kit din mazaunin sa, take ta juyo gare shi...

Baki Fadeel ya bud'e yana kallon ta, sosai tayi masa k'yau tamkar an sanja masa ita, kasa hakuri yayi har sai da ya ware mata karfaffan hannayen sa, da murmushi a fuskar ta shige jikinsa ya mayar da hannu sa ya rufe.

Ajiyar zuciya ya sauke yace "my Darling kin yi kyau sosai, fiye da yanda bakina ba zai iya fadi ba, I love you the mother of my unborn children"


"I love you too Fadeel" tace tana lumshe ido Saboda k'amshin turaren jikinsu dake ratsa kofofin hancin ta.

Sun jima suna hirar soyaayar su, kana suka nufi parlo domin ya ji abinci, kasan centre carpet ta suka zauna bayan ta shimfud'a ledar cin abinci, a baki ta dinga bashi har ya koshi, sai ta siyaya masa lemon kankana ya sha sosai kuwa yana santi, ta dinga shan dariya kuwa, shima kuwa ya ciyar da ita har ta koshi...

Har dare haka ta dinga dawainiyya da shi hadi da bashi kyakyyawar kulawa...


***********


Ta bangaren Jameel kuwa, sosai damuwar sa tayi yawa, ya rame sosai, har hakan ya daga hankalin su minister... Baki jameel da minister suka hada kan kawar da mutum daya daga duniya, tsakanin Fadeel da Fadeelah ta hakan ne zuciyar jameel zai kwanta, wanda ya san ya rasa ta ko bata duniyar akan wani ya rayu da ita yana raye, tunda kidnapping dinsu ba abu bane mai sauki tunda kullum suna cikin tsaro...




A ranar sa suka gama hada plan dinsu, da yamma haulat ta kawo musu ziyara kamar kullum suka aikata zinar su son ransu babu tsoron Allah...



Da bayan magariba sunyi wanka, haulat ta fada mota, suka yi sallama... Haulat ta yi nisa da tafiya, ta yi karo da wata akori_kura, take motar tayi raga_raga, take haulat ta amsa kiran ubangiji, nan fa go slow ya hadu sosai, wani mutum ne yaga tsadaddiyar wayar ta yashe a kasa screen din ta fashe sai dai ba sosai ba, dauka yayi, luckily babu security kan wayar, number jameel ne Karshen kira hakan ya shi kira number'n...


Zaune jameel yake da wasu tantiran samari yana fada musu yanda aikin zai kasance kamar yadda shi da minister suka tsara... Ringing din wayar sa ne ya katse masa maganar sa...

Ganin number haulat ya sashi dagawa, abinda yaji mutumin ya fada ne ya sanya gaban shi wata mahauk'aciyar bugawa ba tare da ya shirya wa hakan ba.


Wani nauyi yaji kansa yayi masa, ba tare da bata lokaci ba ya figi mota sai inda aka yi masa kwantance. Ai ganin gawar haulat ya so juye k'wak'walwar sa, hakika bai taba jin mutuwa data shige shi kamar na haulat ba, ya kasa yarda haulat da suka gama zina mintuna da suka wuce ce ta mutu, kuka yake da idanun sa sosai, take kuwa ya kira lambar iyayen haulat din kasa da mintuna ashirin suka zo hankali su a tashe, ganin gawa 'yar tasu ya sanya hankalin iyayen ta tashi sosai, ubanta ne yayi k'arfin hali, amma uwar har da birgima a kasa, jameel kuwa tamkar ruwa ya cinye shi, babu abinda ke fita a idanunsa kamar hawaye, cikin dumbin al'ajabi, asibiti aka kaita, aka sake gwada ta, nan aka tabbatar rai yayi halinsa, a asibiti duk suka kwana, jameel ya manta wani abu mai suna bacci, daya rufe idanunsa haulat yake gani, cikn dare d'aya gabadaya ya burkice...


Da misalin karfe takwas na safe aka sadata da gidan ta na gaskiya, ganin an rufe haulat da kasa ya sake daga masa hankali, take ya zube a Kasa yana kuka, duk gayu da kwalisar haulat yau babu shi, gata kwance cikin kabarin ta daga ita sai halin ta...


Wani imani da tsoron Allah ya shiga ratsa Jameel, nadamar munanan aiyukan sa ya fara yi sosai, ko bacci baya iyawa cikin dare, ji yayi duk wata k'yalek'yalar rayuwa ta daina burge shi, take ya soke contract din kisan daya so a yi wa su fadeel....


Ganin jameel ya yada makaman yakin sa ya hakura ya sanya shi ma minister ya zubar da komai cikin nadama, tabbas mutuwar Haulat ta daki jameel, minister da mummy'n sa kasancewar duk sunyi mata sani na sosai...


Jameel kuwa sai yanzu ya fara jin son haulat a ranshi, ya kuma yi nadama da bai karbi soyaayar ta da hannu biyu-biyu ba, sosai lokutan da sukayi having ya shiga dawo masa, nan ya hakura da Fadeelah ya kuma fadawa minister cewa ya hakura har abada...


***********************



THREE MONTHS LATER



Zuwa yanzu fadeel yasamu sauki sosai, yana iya taka kafar sa yanda yake so, da taimakon Allah da kulawar da Fadeelah take bashi, domin sosai tayi kokarin wurin bashi kulawa da kuma girka masa abinci masu Karin jini hadi da kara lafiya, tabon jiknsa kuwa saura kadan² domin akwai cream mai goge tabo da duk dare kafin su kwanta fadeelah take shafa masa....


Kamar yau sune zaune a falo, kallon ta yayi yace "wiffy Kin san ina nakeso muyi honey moon?"



Girgiza kai fadeelah tayi tana murmushi kasancewar yanzu ta saba da shi sosai duk da babu wani tarayya aure da ya shiga tsakanin su har yanzu, amma ta rage kunyar sa ba kamar da ba....


Kusa da kunnen ta yazo ya rada mata "suprise!"


Dariya tayi bayan ta saka masa dafaffen kwai cikin bakin sa tace "I like surprises"

"Really?" Yace yana dage girar sa.

"Yeah" ta amsa masa itama.

"Then tashi muje" ba musu ta mike... yace "ki zura hijab kawai kan kayan jikin ki, duk sauran abubuwan da zaki bukata akwai a can" dan karamin jaka kuwa ta saka musu wayoyi, charges, Bluetooth ta rufe zip din jakar suka fito, mota suka fada kamar kullum tare da rakiyar escort suka fita...


Abinda ya bawa Fadeelah mamaki shine ɗa ta ga sun nufi unguwar su Fadeel na ɗa, so take tayi magana domin ta tabbatar da unguwar ne, amma tayi Shiru... Tsayuwar motocin su a wani hada'dden gida Duplex daya tsaru sosai tamkar a turai ya katse mata tunanin ta...



Juyowa yayi gare ta, yace "Fadeelah kin tuna wanna gidan?"


Cikin sauri ta girgiza kai domin har ga Allah bata fahimta ba...

Kallon gidan yayi, ya hadiyi wani abu mara dadi yace "gidan da muka rayu da mahmah ne a ciki, na sanja ginin gidan ne, domin har abada bazan manta da gidan nan ba, haka kuma idan Allah ya azurta mu da '/y'ay'a zamu dinga zuwa nan muna kwana biyu, haka zai sa mu dinga tunawa da mahmah" ya karasa yana dora kan shi a kafadar ta...


Sosai tayi mamaki ganin mugun chanjin da gidan yayi, hakika duk abinda ya samu gyara komai lalacewar sa zai gyaru, a yau ta sake tabbatar da hakan, shafa kansa take itama tana jin kewar mahmah na ratsa zuciyar ta sosai, iya motar da suke ciki yayi horn, take mai gadi ya wangale

Please Login or Register in order to submit comment