Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki ta sanya domin garin da sanyi sosai...



Gado ta haye tana mai lumshe idanun ta masu cike da kewar Fadee din ta...



Ɓabu jimawa ta fara jin motsi daga window(taga) alamu mutum na haurowa, bud'e idanunta tayi, yayin da taji gabanta ya tsanan ta fadu'wa, domin tana ƙara jin motsin mutum na kara ƙunsanto dakin...




Shiru tayi ta ma kasa motsi Saboda tsananin tsoro ɗaya lullube ta, gashi window a bud'e yake bata rufe ba...



Bata gama firgicewa ba, sai ɗurowar mutum ɗa ta ji, ta kuma gani a dakin, sanye yake da irin shigar ta sai dai nasa ɓaƙaƙe ne. Yayinda ya rufe kansa zuwa fusk'ar sa da hulan rigan, kafar sa sanye da fararen canvass na company'n *dolce and gabbana* wanda kudin sa ya kai 451,507.




Tsananin tsoro, jikinta har wani mugun rawa ƴake, domin a tunanin ta aljani ne, saboda tsayin ginin ɗa mamaƙi ace mutum ya hauro har saman inda take kuma ta taga.



Mikewa tayi tsaye ta ɗuro ɗaga ƙan gadon, idanunta sun kawo ruwan hawaye... Ganin yana kusanto inda take yasa ta fara karanto d'uk add'uar data zo bakin ta, kana ta bud'e murya zata ƙwala ihu domin bai daina zuwa kusa da ita ba.

cak! Mutumin ya tsaya kana a hankali ya zame hular rigar baya, take K'yak'yyawar fusk'ar sa ta bayyana, yana sakar mata murmushi hadi da ware mata karfaffan hannayen sa alamun ta zo gare shi.




Haɗiye ihun tayi, tana ware idanun ta, ganin shi a lokacin da bata zata ba, domin bata kashe fitilun dakin ba, hakan yasa kallo daya ta yi masa ta shaida shi...

Take farinciki ya maye gurbin tsoron, da mugun gudu ta isa gare shi, rungume ta yayi yana jin nutsuwa na saukar masa. ƴayinda yake jin bugun zuciyar ta bai dawo dai² ba, alamun ta tsorata sosai kenan...


Ɓakin sa ya d'aura a daidai kunnenta dake tashin k'amshi yace "Am so sorry! Na baki tsoro ko? Fadeel ne relax ok" ya karasa cikin sanyayyar murya mai cike da kulawa hadi da tsantsar soyaaya.




Jinjina masa kai kawai take, kana tace "ba komai, ya aka yi kasan ina kewar ka? Kazo a lokacin da nake matuk'ar bukatar kasancewa da Kai"




Murmushi mai sauti ya saki, kana yace "you have no idea of how i miss you! hakan ya hana ni bacci har na zo gareki matata, but am so sorry I scared you"



Wani mugun son sa ne ya karu a zuciyar ta, sosai take son yanɗa komai nasa ya sanja gwanin burgewa tamkar an sauya sa ne, a fili kuwa tace "it's fine karka damu my one, amma meyasa ka bi ta window ka shigo?"


"Ɗaga gida na ma ta wata hanyar na biyo, domin bana son masu tsaro na su ce zasu biyo ni. Saɓoɗa yanzu lokacin hutun su ne bai kamata na shiga hakkin su ba, dana zo estate din ku ma Shiru, babu kowa daga waje, har na juya zan tafi, domin bana son tashin kowa, kawai na hango wanna hanyar, na gwada shigowa kuma Alhamdulillah naga ta kawo ni part din ki"


Murmushin alfahari da mijin ta ta saki kana tace "amma meyasa baka biyo ta kofa ba, zan bud'e maka ai, shine ka wahalar min da kanka ka bi bango, amma bada kafa ka taho bako?" ta karasa a dame kana cikin gaskiyar ta


Fusk'ar ta ya kamo duka cikin tafin hannayen sa yace " I thought kin yi bacci ne shiyasa ban biyo ta kofa ba, da keke na zo" ya amsa mata a tak'aice.



Jinjina kai tayi cikin gamsuwa tana sauke ajiyar zuciya, hakika ba iya k'yau, haduwa, aji, Fadeel dinta ya karo ba, har da jarumta....




Tana cikin wanna tunanin taji ya sunkuceta ya nufi kan gado da ita, idanun su kafe dana juna.


Zama yayi, ƴayinda take kan cinyar sa, tamkar baby doll. ganin ta ƙafa masa ido bata ko kiftawa ya Sanƴa shi hura mata iskan bakin sa mai k'amshin mouth spray na vanilla.



Lumshe ƙyawawan idanun ta yi cikin kunya, murmushi ya saki kana a hankali ya nufi tattausan labb'anta ya bata light kiss, a tare suka saki ajiyar zuciya....



Sun dauki mintuna a haka ba tare da yayi magana ba.
Can ya zaunar da ita kan gadon kana ya dora kansa a cinyar ta, gashin sa mai tauri irin na Africa take shafawa a hanƙali hadi da yi masa tafiyar tsutsa, lumshe ido Fadeel yayi wani maganadisun dadi na ratsa shi, sun dauki awa d'aya a haka kana ya ji Shiru, can ƙuma yaji Fadeelah ta fado k'ansa...



Murmushi ya saki domin ya fahimci bacci tayi, a hankali cikin dabara ya dawo da ita jikinsa ya rungumeta, yana ji dama a gidan sa ne suka kasance a haka ƴanzu, amma yasan hakan bazai yu ba, dole sai Daddy ya san waye shi sannan zai tafi da matar sa...



Idanun sa ne ya kai kan wayar ta, hannu ya mika ya dauki wayar, ya sanya lambar sa ya kira, take number ta ya bayyana a screen din wayar sa.

Nan ya yi saving da *my Darling* kana ya ajiye mata wayar, agogo ya duba yaga karfe goma sha biyu har ɗa mintuna hamsi...



Dan waro ido yayi, domin bai yi tunanin lokaci ya ja har haka ba, kokarin kwantar da ita yayi amma ta k'amk'ame shi..., fusk'ar sa ta dan nuna mamakin hakan, domin bacci take sosai...



Ƙara gwaɗa ƙwantar da ita yayi, nan ma ta kara rungume shi tana bata fusk'a.


Ƙomawa yayi ya zauna kan gadon still dai tana manne a faffadar k'irjinsa, yana dan ɓuɓɓuga bayanta...



Mintuna goma suka sake shudewa a tunanin sa zuwa yanzu zata amince, a hankali ya shimfud'a ta a gadon....
Ihu ta saki cikin shagwa'ba hadi da magagin bacci tace "stay with me, karka tafi please Fadeeeeeel"




"Nima ba a son raina zan tafi ba, kalli kiga karfe dayan dare ƴa wuce fa"



Zaro ido tayi domin bata dauka lokaci ya kure har haka ba, mikewa tayi tace "Toh ina tsoron ka tafi cikin daren nan fa, ka kwana gobe da safe sai ka tafi"




Girgiza kai yayi yace "Hakan bazai yu ba Fadeelah. I have to go, babu abinda zai faru in sha Allah, Kiyi min add'ua kinji, I love you!" Ya karasa yana kusanto ta kana ya kama lips di'n ta ya shiga bata kisses na mintuna uku kacal, kana ya sake bin ta window yana sauka a hankali har ya dira kasa...


Bayan ya gama sauka ya dago kansa ya ƙuwa hango ta tsaye bakin window tana daga masa hannu, fusk'ar ta dauke da murmushi...

kiss ya hura mata, kana ya hau keken sa ya bi ta hanyar daya shigo ya fita...



**** ***** *****



Bayan kwana d'aya da safe professor Imran mai naira na zaune a part din shi yana duba wasu takardu wayar sa ta shiga ringing...

Sunan minister Sa'id ya gani baro baro a jikin screen din tsad'add'iyar wayar sa...



Sosai yayi mamaki domin rabon da ƴa yi waya tun ranar da suka yi bataciyya dashi, ba tare da ya kawo komai a ransa ba ya daga kiran...


Ɗariyar minister Sa'id ya fara ji kana yace "pro kenan! dama na kira domin na Sanar da kai cewa *wanna FFM the young architecture billionaire* daya yi mugun arziki cikin shekara daya da watanin nan, ba kowa bane face wanna talakan da ka ki bawa auran 'yar ka FADEELAH toh shine dai yanzu ya aure ta, ba tare da ka sani ba, hhhhhh, Saboda son aurawa 'yarka mai arziki har ya sa ka manta cewa Alhaji Sufyan Rufa'i bai tana haihuwa a duniya ba, na barka lafiya, ka bincika sauran da kanka"



Kit minister Sa'id ya katse kiran, yayinda ya bar Daddy zaune ya hada uɓan gumi tamƙar mutum_mutumi......



MU HAƊU RANAR ALHAMIS



Share✅

Comment✅




Noor iman💖


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*



🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)





*WATTPAD*
@NoorEemaan






https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



EDITING IS NOT ALLOWED❌



Page 59-60



........Daddy ƴa ɗauƙi mintuna talatin zaune ya kasa motsi cikin madaukakin mamakin.


Sosai ƙalaman minister Sa'id suka shiga dawowa kwanyar sa, ya kasa yarda cewa wanna bakin talaka fakirin ne ƴa dawo *the famous billionaire Architecture FFM* da labarin uban arziƙin yaron ya zaga duniya dama Fadeel ne? wanna talakan ne? cikin wata murya ɗake fiɗɗa tsantsar ruɗani yace "impossible, tayaya hakan zai faru?"



Tamkar wani zararre, domin har yanzu mamakin bai sake sa ba, haka ya nufi part din Mommah, har wani rawa bakin sa ke yi, ya kuwa ci sa'a ya ganta zaune a falon ta, tana kallon tashar Zee world.



Cikin rawar baki yace "kin...kin...ji...wai talakan ƴaron nan da Fadeelah ta k'awo shine yayi uban arziki, ya kuma auri Fadeelah? na kasa yarda da hakan, dan Allah ku warware min, tayaya hakan zai faru, ace yayi arziki cikin kankanin lokaci haka?". Daddy ya fada cikin rudewa



Wani ƙasaitaccen dariya Mommah ta saki, ido cikin ido tace " professor! a da nace babu abinda ya shafeni game da maganar auran Fadeelah! amma yanzu dole zanyi magana tunda RANAR dana jima ina jira ta zo.
Ka sani cewa komai lalacewar abu, matuk'ar yaji gyara ba shakka zai gyaru, yayi kyau fiye da tunanin mai tunani"


Kallon ta Daddy yayi irin ban gane ba? fahimtar hakan yasa Mommah cewa "ina nufin a da kana yiwa Fadeel kallon mutum talaka makaskanci, amma yanzu abun mamaki yazo har gabanka ka kasa gane cewa shine wanna bakin talaka fakirin.
Kasan miyesa ka kasa gane cewa shine wanna bakin talakan faƙirin?" Mommah ta tambaye shi ido cikin ido.



Tamkar wani karamin yaro haka Daddy ya girgiza kansa.

"Kudi! Kudi sune silan wanna sanjawar nasa daka gani, har ka kasa shaida shi, ina so ka sani cewa arziki riga ce, duk wanda Allah ya so sanyawa, ba shakka zai sanya masa.

Saɓoɗa Allah ya jarrabe shi da rashin babu, ba hakan na nufin yafi son ka bane, kaddarar sa ce haka, gashi ƴanzu Allah yayi masa dauƙaƙa fiye da tunanin mai tunani.
Ƙuma alkawarin Allah ya cika, fadeelah da fadeel sun mallaki juna. Ƙa kuma aura mata wanna bakin talaka fakirin da baka so, ba tare da ka sani ba, kaga ikon Allah ko? Ina mai baka shawara professor ka bi duniya a sannu, wanna arzikin da kake takama dashi za ka iya wayar gari kaga babu shi a tare da kai, ɓa fata naƙe maka ba.
shin idan mai kudi da talaka basa tarayya tayaya zamu cigaba? Wanna duniyar yanzu mai yace kudi yace lallai sai mai kudi dan'uwan sa ne zai rabe shi? Tayaya zamu cigaba, gabadayan ɗaga mai kudi har talaka duk daya muke a wurin Allah, babu wanda yafi wani, sai wanda yafi tsoron sa, dan haka think wiser and change professor, rayuwar nan babu komai cikin ta, in yau kaine gobe wanin ka ne" tana gama fadin haka ta wuce shi zuwa bedroom dinta.


Tamkar status haka professor ya tsaya, ya kasa motsi har Mommah ta shige, yama rasa tunanin daya kamata yayi, brain d'insa ya toshe.



A hankali ya sulale kan kujera ya zauna, gabadaya daya ya ma rasa a wani yanayi yake ciki, sosai mamakin arzikin Fadeel cikin kankanin lok'aci ya dake shi.


Ta bangaren Mommah kuwa tana shiga dakin ta, ta saki ajiyar zuciya, sosai tayi mamakin ganin tunda ta fara magana professor bai katse ta ba, bai kuma ce mata komai ba, ta kuma ji dadin amayar masa da magananun daya jima makale a ranta...



*WASHEGARI*


Da misalin karfe goma sha daya na safe Alhaji Sufyan Rufa'i tare da aminin sa hadi da kaninsa suka yiwa estate din Daddy tsinke kamar wancan karon.



Cikin mutuntawa da girmamawa Daddy ya karbe su...., ba tare da alhaji Sufyan ya boye masa komai ba, ya fadama sa komai dangane da Fadeel din.

Sannan cikin hikima tamkar gugan zana ko nace indirectly alhaji Sufyan ya ke bawa Daddy shawara mai hade da nasiha kan bin duniya a sannu da kuma illar wulakanta talaka, tamkar yadda Mommah tayi masa dai, sai dai cikin hikima Alhajin yake masa magana.



Maganganun sun shiga Daddy matuk'a, dama tun jiya da Mommah tayi masa magana jikinsa ya fara sanyi.
Abin mamaki Daddy'n bai ce komai ba, da kuma dukkanin alamu ya amince Fadeelah ta zama mata ga fadeel din.



Nan suka kara fahimtar juna, inda alhaji Sufyan yace jibi fadeelah zata tare a gidan mijin nata, kamar yadda fadeel ɗin ya bukaci hakan.



Babu jimawa kuwa suka yi sallama dasu alhaji Sufyan din, domin a yau din zasu koma abuja...



Hajiya Mommah ta dukufa da kara gyara yarta da ingantatun magunguna natural, ƴanzu fiye da rabin abincin da Fadeelah take ci a rana ya d'awo fruit masu Gina jiki, da kuma gyara mace hadi da bata ni'ima.




*************


A yau Da misalin karfe 4:00pm Fadeelah ce sanye da wani tsad'add'en atamfa, dinkin riga da skirt, kana aka lullube ta da alkyabba golden yellow daya dace da atamfar jikinta.



Sosai Mommah ta gyara Fadeelah babu abinda ke tashi a jikinta sai k'amshi mai sa nutsuwa.



Daddy, Mommah, da kuma Grandma sune zasu kai ta gidan fadeel K'amar yadda suka tsara. Fadeelah ƙuwa ta manne wa Mommah da Daddy sai kuka take, duk zumudi da son kasancewa tareda Fadeel amma yau tana ji tamk'ar ta fas, ganin da gaske zata bar gidan iyayenta.



Mota d'aya duk suka shiga, wanda sabo ne dal Daddy yace a fito dashi domin kai Fadeelah'n sa gidan mijinta. Sai sauran motocin goma wanda babu kowa a ciki sai bodyguards dinsu, haƙa suka fita a jere ....


Basu wani jima ba, suka isa hada'dden kuma katafaran gidan Fadeel, ko nace unguwar Fadeel kamar yadda alhajin Sufyan yace (😜)



Sosai daddy yayi mamaki ganin ƙƴaun gidan ɗa haɗuwar sa, ƙuma ace mallakin Fadeel ne? aɓin ɗa mamaƙi wani abu mai kama da kunya hadi da nadama ke kokarin ratsa shi.


Haka zalika Grandma kasa haku'ri tayi duk izzar ta sai data yabi tsarin gidan. Mommah kuwa murmushi farinciki take yi, ta ji ɗaɗi ta Allah ya nuna mata wanna ranar da take iya hango wanna yanayi musamman mai kama da nadama a idanun Daddy.
Ɗuƙ ɗa girman kansa bai bari ya fito fili ya nuna komai ba, amma wanda ya san Daddy farin sani tofah zai hango wanna yanayin a tare dashi.



Fadeelah amarya kuwa tana lullube da alkyabba bata ga ƴa ƴa tsarin gidan ƴaƙe ba.

Sunyi tafiya mai nisa a mota kana suka isa part din Fadeelah daya gaji da haduwa, wanda fadin kyaun sa bata lokaci ne. Nan ma Daddy ya kara shan mamaki uban arzikin Fadeel din.


Akwatunan ta hamsin bodyguards suka shigar wani room tare da taimakon ma'aikatan gidan...



Sosai Mommah ta yi wa yarta nasiha, da shawarwari, da ƙuma dabarun zama da miji...


Sai da suka zo tafiya Fadeelah ta fara kuka sosai, nan fa ta tada hankalin su, daddy fadi yake "I will miss you my princess, ki kula da kan ki kinji? Allah ya baku zaman lafiya a raƴuwar Auranku" ya ƙarasa yana rungumar ta.



Haka ma Grandma har da kwallar ta, Daddy kadai ne yayi k'arfi hali bai yi kuka ba, Mommah ta sai data sha kuka sosai...




Haka Fadeelah ta zauna a inda suka barta, ma'aikatan duk suka kawo gaisuwa hadi da tambayar ta me take so a kawo mata.


"Ba komai karku damu" shine amsar data basu ta mayar da Idanunta ta rufe, ɗomin wani ɓa ɗaɗi taƙe jin jikin ta.



Sai bayan isha Fadeel ya d'awo sanye da shadda blue color dan uban su dinkin babbar riga, har kofar part din Fadeelah escort d'insa suka rako shi, ƙana suka koma...

Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin daya yi tozali da ita zaune a kasa ta dora kanta kan daya daga cikin had'add'un kujerun falon da alama sallar tayi.



"My Darling!" Ya kira ta cikin wani unique voice, a ƙuma lokacin daya iso tsakiyar falon ta.


A hankali ta dago kumburarrun idanun ta da suka sanja launi ta sauke su kan shi.


Tattausan murmushi ya sakar mata, kana ya ware labb'ansa yace "come to your husband fadeelah"


Da gudu ta isa gare shi tana fashewa da kuka sosai.


"Ya salam! Kukan me kike yi? I thought yau ranar farinciki ne a garemu? so why are you shedding tears uhm?" Ya tambaya a ɗame kana cikin kulawa..


"Ka barni inyi my one! Kukan farinciki nake, Alhamdulillahi tatimun salihat, Alhamdulillah ala kulla halin" ta karasa tana kara kamkame Shi.



Murmushi ya saki, Yayinda fusk'ar sa ke fidda zallan annuri, wanda farincikin ganin fadeelah'n sa a cikin gidan sa ya sanya shi hakan...



Ya jima yana rarrashin ta, har tayi shiru amma yaji jikinta da alamun zafi.


Fusk'ar ta ya kamo yace "wiffy kin jima kina kuka ko? Ga jikin ki yayi zafi"

Shagwa'be fuska tayi kana ta turo cute lips d'inta tace "Toh basu Mommah da Daddy bane suka tafi suka barni"


Dariya ta bashi, amma ɓai ƴi ba, sai murmushi ɗaƴa saki, lokuta da dama yana matuk'ar son shagwa'bar ta, domin tamkar yarinya yar shekara 10 haƙa take dawowa a idanun sa.



Kasa hakuri yayi har ya kamo lallausan labb'anta data turo ya tsotsa na sakan 10 kacal.



Zare labb'ansa yayi... cikin wani sexy voice yace "dole yanzu zan kira likita domin ya duba min ke, kada wanna zafin jikin ya dawo fever"



"Kaiiii my one! I Will fine basai ka kira doctor ba"


"A'a ban yarda ba" yace yana dialing number'n likita...


Bata kara cewa komai ba, sai lafewa a jikinsa ɗata ƴi tana sauraran dad'add'an k'amshi dake fita a jikinsa...




Babu jimawa likita ya zo, nan Fadeel yace ya duba masa matar sa, yayi mata blood test ta yanda za a san abinda ke damunta, baya son a bata magungunan ko yi mata allura kai tsaye ɓaɓu gwaji...



Nan fa likitan ya dibi jinin da sauran gwaje² kana yace gobe zai kawo result, sai yan magungunan daya bata domin taimaka mata kafin goben.

Abincin da chef's din suka jera a dining suka ci, kana ya bata magungunan ta sha, babu jimawa kuwa bacci ya dauke ta..



Tashi da ita yayi a jikinsa ya haura upstairs...


Wanka yayi ya sanja kaya zuwa pyjamas ƴayinda ya shiga zare kayan Fadeelah a hankali gudun kar ta tashi, alkyaban da atamfar ya cire mata, sai inners wears daya barta ɗa shi...



Wutar dakin ya kashe, sai dim light daya bar musu, Add'uar ƙwanciƴa bacci ya tofa musu, kana a hankali ya dora ta a k'irjinsa, yana sauke numfashi irin na farincikin nan, abinda ya jima yana jira ya zo, finally gashi da Fadeelah'n sa manne da juna a gado daya, kana a daki daya.



Sanin cewa bata jin dadi ya sanya shi barin ta ba tare da yayi mata komai ba, burinsa yanzu ta samu sauki, domin sam ko ciwon kai baya son ganin ta tana yi.





WASHEGARI
10:00am


Tun bayan sallar asuba Fadeelah ta koma bacci, bata farka ɓa har yanzu...

Goma da mintuna ashirin doctor ya kawo result din Fadeelah, nan yayi wa FADEEL bayanin cewa rashin bacci da damuwa da ta yi fama dashi a ɓaƴa ne suka tarar mata, wanda sai yanzu yake nuna kan sa, sannan zafin jikinta ma zai sauka kukan da ta sha ne ya kawo shi.




Nan tausayi da kaunar Fadeelah'n sa suka saƙe ratsa shi, godiya yayi wa likita, ya karbi result din.



Bayan ya sallame likita ya tafi kana ya zauna a falon ya bud'e result din, abinda ya gani a rubuce ya sanya k'irjinsa wata mahauk'aciyar bugawa....





Share


Comment




_Har yanzu Sadaukarwa bai kare ba_

Ku biyo ni, jan yanda zata kaya😎




My readers
Noor loves you all💋


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*



🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)







*WATTPAD*
@NoorEemaan








https://facebook.com/groups/943534712916776/masu
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



EDITING IS NOT ALLOWED❌




Page 61-62


........kara Murza idanun sa ƴayi, domin ya taɓɓatar da abinda ya gani, take ya saƙe sauƙe idanun sa kan result ɗin.



Sosai idanun sa sukayi jajur, jiyoyin saman ƙansa sun fito sunyi rudu-rudu hannunsa yasa ƴa rufe fusk'ar sa dashi, yana mai jin bugun zuciyar sa na karuwa.



Ta ɓangaren Fadeelah kuwa, a hankali ta bud'e idanun ta masu cike da bacci.
ta ji dadin jikinta yanzu, sai kasala da take ji ƙawai, kallon gefen ta tayi ta ga ba kowa, mikewa tayi a hankali tana yamutsa fuska...



Sai a lokacin ta lura an cire kayan da ta kwanta dashi, murmushi ta saki, domin tasan wanna aikin Fadeel ne



Ƙyawawan kafafun ta, ta sauke kasa ta shige toilet, brush tayi, kana ta wanke fusk'ar ta da bar soap.


Towel tasa ta goge fuskar ta dashi, kana ta fito, zuge wardrobe d'insa tayi, ɗaƴa k'asance na glass, gabadaya kayan sa ta gani a ciki, a hankali ta zaro wani T-shirt dinsa, fari, sanyawa tayi taga ya sauko mata har saman cinya, kara zuge glass din tayi ta rufe kana ta fita daga dakin, domin ta ji Shiru babu motsin shi...



Tun daga nesa ta ganshi, haka kawai taji gabanta ya fadi, cikin sauri ta karasa gare shi, hannun sa daya rufe fuska ta cire, a hank'ali ya dago k'ansa idanun su ya sarƙe dana juna...



Take wani ɓugun zuciya ya ƙara riskan ta, ganin yadda idanun sa sukayi jajur tamkar an watsa masa barkono



Hankali tashe tace "ya Allah! Fadeel lafiya? Talk to me what happened?" Ta fada tana kamo fusk'ar sa cikin tafin hannayen ta.




Cikin sauri ya rungumeta yana matse ta sosai a faffadan k'irjinsa, ya shiga sauke ajiyar zuciya a kai kai...



Taji zafi yadda ya rungumeta, domin ba runguman wasa yayi mata ba, amma bata hana shi ba, saɓoɗa halin ɗa ta gan shi a ciki, ga bugun zuciyar sa da take ji, ya fi komai daga mata hankali.




Bayansa take shafawa a hankali, tana busa masa iskan bakin ta, kara kamkame ta yayi tamkar zai balla ta. (yi a hankali dai, kasan fadeelah siririya ce, ko ya kuka ce fans?😁)



Sun dauki mintuna ashirin a haka kana tayi kokarin raba jikinsu, amma tamkar jaririn goye ya kara matse ta yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.




Cikin damuwa tace
"ka sake ni muyi magana, please my one"



Shiru taji ɓabu amsa, sai saukar abu mai dumi da ta ji a bayanta, da k'arfi ta kwace jikinta tana kallonsa, sosai hankalin ta ya kara tashi ganin yadda hawaye ke zuba a idanun sa, ɗuƙ ɗa idanun sa a lumshe suƙe.





Hannu tasa ta shafa hawayen fuskar sa, take itama hawaye suka zubo mata, sai ta fara sheshek'ar kuka, tace "Hawaye? ɗa gaske Hawaye nake gani a idanun gwarzon mijina? Miya yi zafi haka? Please tell me meke damun ka, wani abu ne ya faru?"




A hauƙace tamkar mayuwancin zaki ya motsa ta jikin sa, lallausan labb'anta ya kamo ya fara kissing din ta hurrily.....


Gaba daya sun birkita juna, good 30minutes suka dauka a haka, har ya dauki wata hanyar, ya tuno abinda ya gani a result din ta, hakan ya sashi mirginawa gefe yana sauke numfashi...




Fadeelah kuwa duk da ta tsorata da yanayin sa, amma haka ta mike zaune ta dauki rigar ta dake yashe a kasa, ta sanya kana ta mike ta zauna kan cinyar sa, duk da tana jin kunya da tsoro tace "miye sa ka fasa? hakkin kane fa" domin ita ta dauka damuwar ta sa kenan.




Rikitattun idanunsa ya lumshe yana sauke numfashi, kana a hankali tamkar mai tsoro Magana yace "No!"

Cikin daurewar kai tace "why no? Why are you behaving strange? I thought damuwar kenan. Toh ka gayamin damuwar ka, ka sani a rudawa sosai" ta karasa muryar ta na rawa, alamun tana daf da sakin kuka.




Fahimtar hakan ya sashi dora kanta kan k'irjin sa yace "am sorry! Karki kiyi kuka kinji? Zamu cikawa Mahmah burinta, in sha Allah..., ina bazan iya ba, bazan jure ba, hakan bazai faru ba...." Ya karasa yana rungumeta da kyau cikin fitar hayyaci...



Cikin sauri ta dago kanta jin kalaman sa na karshe, gabadaya yau

Please Login or Register in order to submit comment