Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zama ya daga tsadaddiyar wayar sa ya kira daya daga cikin escort d'in sa, magana biyu zuwa uku yayi ya katse wayar...




Babu jimawa escort biyar suka shigo da manya_manyan jaka guda biyar, da kyar suke dagawa saboɗa nauƴi, gaban Daddy suka dire, kana suka fice cikin girmamawa....



Kallon karin bayani da mamaki Daddy yayiwa Fadeel, ba tare da ya iya furta ko da harafi daya ba...


Ba bata lokaci Fadeel yace "hakika Daddy asarar daka yi, babu mai iya biyan ka, ko ya maye maka ɗa mafi alkhairin sa sai Allah'n daya baka, wandannan kudaden billion dubu sitti ne, ka yi amfani da shi domin kara farfado da business dinka"



Shiru wajen ya dauka tamkar ruwa ya cinye su, sosai mamaki da kyawun zuciya irin na Fadeel ya kama shi, cikin wani mamakin Daddy ya fisgo maganar kamar haka "A'a ka bar shi, ka barshi please nagode kwarai, akwai yan kudade a hannuna zan yi amfani dasu"



Tabbas Daddy is a changed person now, domin managar sa cikin sanin mutunci da darajar dan Adam yake yinsa yanzu, Fadeel ya aiyana a ransa kana a fili yace "please Daddy ka karba, ba dan ni ba, idan baka karba ɓa, hakan na nufin baka dauke ni d'a ko nace suruki a gareka ba"



Sosai kunya da nadama suka sake rufe Daddy, tabbas ya ji kunya ba kadan ba, wanda yake cewa baƙin talaka fakiri shine yau ya bashi taimakon zunzurutun kudi har billion dubu sitti...



Cikin sanyi jiki yace "sam ba haka bane, amma duk tarin wulakancina a gareka har sai da ka taimaka min da kudi har haka kai...."



Katse shi fadeel yayi da cewa "na manta komai Daddy, ban taba rike ka a raina ba, fadeelah ita ce jinin jikina, dole na so komai nata, bare kai da kake ɗa ɓabban matsayi a gareta, sannan kudin nan ba taimakon ka nayi ba, ka dauka cewa tamkar fadeelah ce ta baka a matsayin ta na 'yarka, nima d'a nake a gareka, ka karba please Daddy hakan zai sa naji dadi"



Kasa magana Daddy yayi, sai rungume Fadeel daya yi zuwa jikinsa, ba tare da ya sani ba, yaji hawaye na zuba a idanun sa, sosai yaji Fadeel ya burge shi kana ya samu muhallin a zuciyar sa, ji yake dama hannun agogo ya dawo baya, ya goge tsana, cin fuska, hadi da wulakancin daya yi masa a baya...



Cikin hikima ya goge hawayen sa Saboda kada a gane, amma ina ya makaro domin fadeel ya ji digowan hawayen a jikin sa...




Cikin sanyin murya Daddy yace "Allah ya yi maka albarka, ya baka dukkanin farincikin rayuwar ka, ka yafemin, abubuwan dana aikata agareka, na san...."



Katse shi Fadeel yayi da cewa "babu komai Daddy baka min komai ba, ni zan tafi na bar fadeelah ita kadai" ya fada feeling free domin baya iya 6oye tsananin son da yake wa Fadeelah'n shi ko a gaban waye...


Murmushin farinciki Daddy yayi, yana jin farinciki sosai, domin 'yar sa daya tilo ta samu miji mai tsananin nuna kulawa da so a gareta, tabbas wanna abin farinciki ne.



Kallon Fadeel yayi yace "alright! my regard to my princess please, amma bata da masaniya kan abinda ya faru dani ko? domin bana son hankalin ta ya tashi"



Jinjina kai fadeel yayi alamun "eh" domin shima bazai so tashin hankalin wiffy din shi ba.



Ɗukawa yayi, kana ya yiwa su Mommah sallama, albarka suka sanya masa, kana ya fita, yayinda suka bi shi da kallon alfahari, har wajen mota Daddy ya raka shi,... fadawa mota yayi bayan sun sake sallama da Daddy, a jere motocin sa suka bar gidan.




A hanya magriba tayi musu, hakan yasa suka faka motocin su a gefen hanya kamar yadda Fadeel ya bada umarni, babban masjid din dake gefen hanyan suka nufa bayan sunyi alwala, yayinda wasu da ba muslimai ba cikin escort din suka tsaye jikin motocin, suna jiran su Fadeel su idar da sallar, bayan mintuna goma sha biyar suka fito, bude masa motar aka yi, kana escort's suka fada sauran motocin, wuta suka bawa motar kana suka nufi BANANA ISLAND gidan Fadeel....




Zaune ya tarar da Fadeelah ta kurawa babban cinema ido, amma sam ba Kallo take ba, domin hankalin ta baya wajen....

waya na makale a kunnen sa ya shigo, da alama da alhaji Sufyan yake, jin muryar sa ya sanya Fadeelah dawowa daga duniyar tunanin da ta afka, ajiyar zuciya ta sauke kana ta nufi shi, ba tare da yayi magana ba ya ware mata hannun sa daya, kasancewar dayan na makale da waya, da gudu ta shige jikinsa ya rufe hannun sa, sun dauki mintuna goma suna waya da alhajin, har yace a bawa fadeelah su gaisa, babu musu ya kara mata wayar a kunne, bayan sun gama gaisawa ya katse wayar, cillar da wayar yayi kan hada'dd'en kujerar falon...



Hannunsa zagaye da waist din ta yace "wiffy ya gida?"


Turo baki tayi cikin shagwa'ba tace "Bayan ka tafi ka barni da kewar ka, wai ina ma ka je?"


"Am so sorry my Darling, naje wata yar unguwa ce, amma ki sani duk inda nake kina makale a nan dina" ya fada yana nuna saitin k'irjin sa, rungume Shi tayi tana sauke ajiyar zuciya, ƴayinda dad'add'an k'amshin turaren sa ke ratsa kofofin hancin ta, sun jima a haka suna jin dumin juna, kana Fadeel ya rike hannun ta suka nufi wani sashe na gidan, wanna fadeelah bata san da shi, a kuma nan yake son su kwana yau....



_11:00pm_

A wahalce ya mirgina gefe yana sauke numfashi, babu abinda yake sai dafa marar sa, fadeelah ce ta kwantar da kanta kan k'irjin sa cikin sanyin jiki, domin romance din da suka yi having ya saka jikinta mutuwa ainun, numfashi ita ma ta sauke tana jin hawaye ya ciko Idanunta, lumshe idanun ta tayi sak'amak'on shafa bayanta da yake, hakan ya bawa hawayen damar zubowa, cikin sheshek'ar kuka tace "My one zuwa yaushe zaka cigaba da azabtar da kanka, Allah ya gani ni ban hana ka hakkin ka ba, sai ma kai da kake ta ki, bana son ganin ka cikin wanna mayuwancin hali irin haka, na...."



"Shhhhh!" Yace yana dora soft hand dinsa saman tattausan labb'anta alamun tayi Shiru.


"Bazan iya ba fadeelah, bana son mu haifi ɗa da cuta, ina tsoro matuka, amma ina da mafita daya, zan sama mana mafita ok, stop crying"


Cikin kuka tace "ta yaya zan daina kuka bayan kana wahala, toh ka dawo da numfashin ka daidai" ta fada tana kallon yanda yake fitar da numfashi hurrily...



Dariya ta bashi, "banda abin ki my Darling ba fa ni nake yi ba, amma na daina kinji" ya fada shafa yalwataccen gashin kanta da bai fiye cika ba, haka ya dinga kwantar mata da hankali, har bacci ya dauke ta, shima baccin yayi da kyar, da niyyar dole ya samo musu mafita, duk da abinda yake shirin yi yasan akwai hadari sosai, inma ya rasa ransa ko ya rayu, amma tabbas bai da mafita sai na yin hakan...





*WASHEGARI*

Da misalin karfe goma ta farka sak'amak'on hasken rana daya shigo ta window, sosai tayi mamakin nauyin baccin da ta yi, dadin ta ma tayi sallar asuba, ta kuma san kan sallaya wani baccin ya sake daukar ta, amma gashi ta ga kanta a gado, ta kuma san Fadeel ne ya dawo da ita kan gadon....





Kallon dakin tayi ta ga ba kowa, toilet ta fada tayi brush kana tayi wanka, fitowa tayi hannunta kan kugunta, tana tunanin ta ina zata fara dubo shi cikin uban gidan nan mai girma, fadi, hadi da tsaho...
Saboda part da dakunan da yawa, bata san wani wajen zata fara bi ta neme shi ba, take kuma tunanin kiran sa yazo kwanyar sa hakan yasa ta nufi daya daga cikin wayar ta dake kan gado, wata farar takardan ta ga an dora kan wayar, haka kawai taji gabanta ya fadi, ta fara koƙarin kiran wayar sa, sai taji zuciyar ta na azalzalar ta kan ta duba takardan, duk da gabanta na fadu'wa haka ta ware paper'n kyakyyawan rubutun Fadeel mai k'yau da tsari ne ya bayyana, cikin sauri ta fara karantawa kamar haka...



_my wiffy_

_I knew zaki ga wanna takardan, domin ke na rubuta shi, ban sanar dake ba, saboda nasan zaki hanani kice kece zaki yi, ina mai baki hakuri ban yi dan na bata miki rai ba, nayi ne domin shine kadai mafitan da muke dashi, bayan sallar asuba, a yau na bar kasar nan zuwa America, na tafi domin a canja min jinina kaf zuwa wani, ta hakan ne zamu haifi lafiyayyun yara, idan Allah ya nufa, add'uar ki nake nema, domin ban san tsawon lokacin da zan dauka ba, ban kuma san zan rayu ko zan mutu ba, bayan an chanja min jinin. Domin gabadaya jinina za a kwashe, a musanya min da wani jinin, domin blood group dimu ya yi match, ta hakan ne za mu rayu cikin farinciki, kada kiyi kuka please, I will miss you so much fadeelah, kaunar ki kadai ce da cikar burin mahmah ta sani yin hakan, kiyi min add'ua sannan ki kular min da kanki, FFM loves you_.....






*(Billahi banga ruwan comment ba, Baku ganin update ranar lahadi)*




Mu je zuwa Guys😎🔥


_Sai ranar lahadi idan mai kowa mai komai ya ara mana rai_.


Share fisabilillah



Comment din ku is needed



Noor Eemaan😍🔥


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*




🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)



*WATTPAD*
@NoorEemaan










https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


EDITING IS NOT ALLOWED❌



No editing🤒




Page 67-68

........Wani mugun ƙara mai hade da Salati fadeelah ta saki, kana ta shiga kuka mai sautin gaske gwanin tausayi, fadi take "fadeelah don't do this to me, Ka dawo, ka dawo please kada ka min haka, ka dawo mu rayu tare ko da baza mu haihu ba, bazan iya juran rasa ka ba, wanna aikin na da matuƙar hadari, ka dawo please Fadeeeeeeeeeeel" ta kara sa tana zubewa kan gadon ta shiga rera kuka gwanin tausayi, ta jima sosai tana kukan domin ta fi awa d'aya, har idanun ta ya fara yaji sosai ko bud'e su bata iya wa, sosai zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta.





Haka ta kasance har karfe hudun yamma, sallar azahar da la'asar ma a zaune tayi ta, domin ko k'arfin tsayuwa bata da shi, tun safe bata sa komai a cikinta ba, minti d'aya biyu sai kaga hawaye ya balle mata gwanin tausayi...




bayan sallar ishaq ta ga yunwa na kokarin yi mata illa sannan ta rarrafa bakin hada'dd'en medium size fridge ta dauko yogurt mai mixed fruit, bakin ta na rawa haka ta kafa baki ta sha sosai fiye da rabi, kana ta dire robar a gefe tana sauke numfashi tamkar wacce tayi tseren gudu....



Ta kai mintuna goma a zaune cikin mayuwancin hali kana ta Mike da kyar ta koma kan gado...



Sosai wani mugun sanyi ke shiga jikin ta, gashi dama bata saka kaya ba, domin tun towel din safe shine har yanzu a jikinta, haka ta yi ta zumbula yalwataccen hijab take sallar da shi...



Da kyar ta ja duvet bedsheet ta rufe jikinta da shi tana sauke huci da numfashi irin na masu zazzabi....



Ta bangaren masu aiki kuwa sosai sukayi mamakin ganin su Fadeelah basu taba abinci safe, rana, bare na dare ba, domin basu da matsaniƴa kan Fadeel baya kasar, gashi Fadeel bai bawa ma'aikatan sa damar shiga part part din gidan a akodayaushe ba, musamman bedrooms din.

rashin taɓa abincin ya dan basu tsoro amma sai suka dauka ko basa gidan ne, domin sun san waye Fadeel ya kan fita wani zubin bai sanar da su ba, musamman idan ba lokacin aikin su bane, domin a Cewar sa baya son shiga hakkin ma'aikatan sa ...






*WASHEGARI*

Har yanzu fadeelah bata bar kukan ba, sai ma abinda ya karu, domin fadeel ya sabar mata kwanciya a jikin sa musamman d'addare, hakan yasa ta ga daren jiya yayi mata nisan gaske...




Wanka tayi da kyar, tayi brush kana ta sanya wani palazzo trouser da wata riga daya zo mata guiwa, wanda bai kamata ba, sai tayi rolling da black Veil, wani flat palm sandals ta sanya a kafarta, komai a sanyaye take yin sa, amma hakan bai boye kyan ta ba, wani babban sunscreen (glass or tabarao) ta saka a fuskar ta domin ya boye kumburin fusk'ar ta....




Waje ta fita, sosai tayi kokarin danne hawayen ta, nan ta tarar da tarin ma'aikata, security, hadi da escort din sa, wasu a tsaye wasu a zaune, wasu na zaga gidan domin tabbatar da tsaro....





Cikin girmamawa suka shiga gaisheta, amsawa tayi tana kokarin k'ak'aro murmurshi, tun kafin ta isa wajen har sun bud'e mata kofar wata had'add'iyar *Mercedes Benz* ash color domin ta shiga...



Kallon wanda ya bud'e motar tayi, tace "ku barshi zan fita ni kadai karku damu"



Kansa a kasa cikin girmamawa yace "sorry madam, bazai yu ki yi tuki ke kadai ba babu tsaro, domin yallabai ya ja mana kunnen kan hakan tun washegarin ranar da kika tare, please ki yi hakuri ki barmu muyi aikin mu kamar yadda boss din mu ya bamu umarni" Ya karasa cikin tsantsar ladabi.




"ok fine" fadeelah tace tana zama cikin motar a sanyaye, yayinda sauran suka fada sauran motocin domin bata tsaro, a jere reras suka bar gidan, "estate dinmu muka nufa" abinda tace wa driver kenan ta lumshe idanun ta Yayinda hawaye masu zafi suka ciko Idanunta ta, tsananin kewa da tsoron rasa shi ne suka yiwa zuciyar ta kawanya....





Jin tsayuwar motocin ya tabbatar mata da sun iso estate dinsu, cikin hikima ta share hawayen ta, kana ta daidaici muryarta tace wa driver'n daya tuko ta su tafi idan zata dawo bodyguards din estate dinsu zasu dawo da ita, cikin girmamawa ya amsa, already an riga an bud'e mata kofa, hakan yasa ta sanya kai ta fita....




Sosai ma'aikatan gidan suka gaishe ta, kowa fusk'ar sa dauke da murmushi da farincikin ganin ma'am dinsu da ta san darajan mutane, sosai ta dinga sakar musu murmushin yake domin bata son kowa ya fahimci halin damuwar da take ciki...





Part din Mommah ta nufa, tana daf da shiga Parlon mommah ta ga kukun Grandma to zo fita, hakan yasa ta tsaya suka gaisa kana matar ta dora da fadin "ya muka ji da asaran da mai gida yayi, toh Allah ya tsare gaba ya kiyaye"




Sosai zallan mamaki ya kama fadeelah, wani asara kenan Daddy yayi? Ta aiyana a ranta, amma sai bata nuna ba tace "Alhamdulillah"



Cikin sauri ta nufi part din Mommah, cikin wani sabon tashin hankali, ta kuwa tarar da Mommah zaune, tare da Daddy...



Cikin sauri ta fada jikin Daddy tana saukin wani kuka mai dauke da abubuwa da dama... Cikin tashin hankali mommah da Daddy suka hada baki wurin fadin



"Subhanallahi! Sweetheart, princess, meya faru?"






Wani kuka mai sautin gaske ta kara saki tace "Mommah! Daddy! Fadeel ya...ta...fi...ya barni"




"Innalillahi! ya tafi ya bar ki, zuwa ina?" Mommah ta fada hankali a tashe, gabanta na fadu'wa, sak'amak'on bata san amsar da Fadeelah zata basu ba...



Sai da Fadeelah ta saki wata sheshek'ar kuka kana tace "y...ya...ta..fi....a Sanja masa jinin sa zuwa wani blood group din, domin shima blood group din sa SS ne"




"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" suka fada hankali a tashe, domin sun san had'arin dake cikin aikin, duk da sun san cewa fadeelah SS ce, amma basu taba tunanin shima Fadeel din SIKILA bane sak'amak'on yana da ginanan jiki, ga kuma yanda bikin yazo, hakan yasa babu wanda hankalin shi ya kawo kan suyi blood group test irin wanda ma'aurata masu son mallakar junansu ke yi yanzu...





Daddy kasa magana ma yayi, domin sabon nadama, da kaunar Fadeel din ne ya rufe shi, tabbas Fadeel na matuk'ar son gudan jinin sa, tunda har zai iya zuwa a cire masa jinin sa kaf a sanya masa wani, duk da yasan hadarin dake cikin aikin, ya kuma godewa Allah da Fadeel ya kasance cikin ahalin sa, domin samun kamar sa a wanna al'ummar tamu da wuya, haka kuma rasa shi a Al'ummah babban rashi ne.





Mommah kuwa sosai ta dinga taya fadeelah kuka, domin wanna maganar da Fadeelah ta zo musu da shi ya shige ta matuk'a.





Duk jikin su a sanyaye yake, ga kukan fadeelah yaki karewa sannan suka hau lallashin ta hadi da kalamai masu kwantar da hank'ali, Shiru tayi lamo jikin Daddy tana sauke numfashi, sosai suka tausaya mata, Daddy ya kuma ji dadi da Fadeelah ta samu muradin ranta (fadeel) da bai san halin da zata shiga ba, domin rashin ganin sa kadai ya sa ta shiga wanna halin, ina ga bata mallaki shi ba?...




"Daddy wani asara kayi naji kukun Grandma na mun jaje?" fadeelah ta katse masa tunani da muryar kukan ta...



Daddy bai so ta sani ba, domin kada hankalin ta ya tashi, amma yanzu dole zai sanar da ita, saboda zancen duniya bata 6uya...




Nan Daddy ya shiga sanar da ita dalla² daga asarar da yayi, wa'azajin mommah a gare shi, da zuwan Fadeel gidan, hadi da uban kudin da Fadeel ya bashi, komai dai ya sanar mata.




Ai fadin zallan mamakin fadeelah da farincikin ta bata lokaci ne, taji dadi da Daddy ya gane gaskiya, ta kuma yi mamaki kwarai da Fadeel ya bawa Daddy zunzurutun kudi amma ko sanar mata bai yi ba, in fact batama san cewa yazo estate din su ba...




Sosai ta nuna mamakin ta, wanna hakan ma ya bawa su Daddy mamaki ganin bai sanar wa fadeelah uban kudin daya bayar ba, sosai hakan yasa Fadeel kara samun waje a zuciyar su, tabbas da za a samu masu kyawun zuciya irin na Fadeel a al'ummah da an samu cigaba sosai..




Haka dai suka Shiga lallashin fadeelah har aka samu bacci ya dauke ta kan cinyar Mommah, domin duk maganar nan da suke hawaye ke zuba a Idanunta....



*****************




*AMERICA*

Hada'dd'en asibiti ne mai girman gaske, gabadaya ma'aikatan su farare ne, ma'ana masu jajayen kunnuwa ne, ko wannesu sanye da uniform farare kal, yayinda majinyacin su ke saka light blue...




Kwance Fadeel yake babu riga ko daya a jikinsa, sai wani kyalle fari da aka rufe al'auran sa da shi, yayinda wasu wayoyi masu yawa ke manne a duk wata gaɓa ta jikinsa inda jini ke yawo, an ɓula duk wani maguɗanar jini dake jikinsa an saka wayoyi a a ciki, ta nan jinin ke shiga jikinsa.

ga jini masu yawa leda-leda rataye kan wasu karfuna a tsaye irin na karin ruwa nan, luckily cikin kudirar Allah aka samu blood group O+



A yanda yake kwance zaka dauka matacce ne, domin baya motsi, banda zuciyar sa dake bugawa babu abinda ya bambam ce shi da matacce...




******************************



NIGERIA (LAGOS)

*Bayan watanin goma sha daya*

Fadin tashin hankali da damuwar fadeelah bata lokaci ne, kuka kuwa shine abokin hirar ta, sannan hoton zanen Fadeel dake part dinta shine abinda yake debe mata kewa.



Bata taba tunanin fadeel zai dauki wata uku bai dawo gareta ba, amma gashi yanzu 11month babu amo babu labarin sa, tun su Mommah na lallashin ta har suka zuba mata ido, domin suma abin ya fara damun su jin Fadeel din shiru, gashi sun sa anyi bincike har yanzu ba a gano asibitin da yake ba.






Ta bangaren ma'aikatan gidan da escort din sa kuwa, suna ganin alert duk wata hakan yasa basu damu ba, domin a tunanin su wata tafiya mai muhimmanci sukayi domin fadeelah bata koma ba, a cewar ta bata amfanin zaman gidan ba babu gwarzon ta a gare da ita, dama kuma fadeel ya kai albashin ma'aikatan sa na tsahon lokaci banki, duk da bai san tsahon lokacin da zai dauka ba, amma sai da ya kai kudi masu yawa wanda kowa zai samu albashi har na shekara daya da watanin, kana ya bada account number din kowa yace duk wata ana biyan su, zai bar kasar zuwa wani lokaci, kasancewar da bank din yake amfani hakan yasa ma'aikatan na samun salary dinsu duk wata....




*************


Sosai Fadeelah ta dawo so silent babu hayaniya, domin idan ba hirar Fadeel Mommah ko Daddy zasu mata ba, bata magana da kowa, sosai suke tausaya mata, domin ita ba jiki ba dama, gashi kuma damuwa ya kara zuketa.....



******************


AMERICA

1 MONTH LATER

A yau Fadeel yayi shekara daya da zuwan sa America, hakan kuma yayi daidai da shekaran sa daya a kwance ba tare da yasan a wace duniya yake ciki ba, likitoci sun fara damuwa ganin har yayi shekara daya bai motsa ba, sosai suka damu...

tun kafin a fara aikin sunan fadeelah'n sa ne a bakin sa, sosai suka tausaya masa, domin basa son wahalar sa ta tafi a banza, musamman babban likitan mai suna KELVIN SMART domin sai da Fadeel ya bashi labarin soyaayyar sa da Fadeelah ya amince za a yi masa aikin Saboda hadarin dake ciki, kasancewar sa bature, dama an san turawa da sanin darajar soyaaya hakan yasa ya amince domin ya yarda da reasons din fadeel din, taɓɓas samun irin wanna soƴaaƴar da wuya, koda cikin su turawa ne, ace uwa da ɗa duk sunyi sadaukarwa mai girman gaske...



Zuwan KELVIN SMART na hudu kenan a safiyar yau domin duba fadeel ko ya farka, saboda ya fara jin tsoro... a hankali ya tura kofar zallan glass din ya shiga, kamar a mafarki ya ga Fadeel ya fara motsa kafafun sa......





Share fisabilillah




Comment




✨Noor larab ce✨




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*




🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*First edition*








https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



EDITING IS NOT ALLOWED❌



Page 69-70


(Not Edited)


Sai kuma hannun sa, cikin sauri kelvin smart ya karasa wajen sa, farinciki fall fusk'ar sa, cikin sauri da sanin makamin aiki ya shiga zare na'urorin dake manne a dukkanin jikinsa inda aka manna.



A hankali ya fara ware idanun sa, saurin mayar wa yayi ya rufe ruf, sak'amak'on hasken daya cika idanun sa...


"Easy, take it easy" KELVIN SMART ya fada yana shafa kansa.


Ya dauki mintuna goma, kana a hankali ya shiga bud'e idanunsa sa, tar ya sauke su kan fuskar Kelvin Smart


"Welcome back to the world the lover boy" Kelvin smart ya fada cikin farinciki..



Jinjina kan sa Fadeel yayi yana murmushi irin na masu jinya, ji yayi jikinsa na masa wani iri, wani zafi da bazai iya mitsaltawa ba, tamkar ciwo a jikin mutum ana fama masa...




A hankali ya mike zaune yana sauke numfashi, wani bowl da toothpaste hadi da brush Kelvin smart ya kawo mishi, sosai yayi brush din bakinsa, toilet kelvin smart ya zubar da ruwan daya wanke baki dashi kana ya dawo...



Wani kujera mai kyau dake gefen gadon ya zauna a kai, kana ya kalli fadeel yace "how are you feeling now? (Ya kake ji yanzu? )"



Lumshe ido fadeel yayi, kana ya bud'e su, karon farko bayan shekara daya ya furta "yeah! not to bad, I have to go home urgently, cos I know my wife is worried already, but for how long have i been here?(eh babu laifi, ina son zuwa gida da gaggawa, domin nasan matata na cikin damuwa tuni, amma tsayin wani lokaci nake wajen nan?)"


Murmushi Kelvin yayi, yana jinjina son da Fadeel ke wa fadeelah'n sa, kana yace " you have been here for one year now(kana nan tsawon shekara daya yanzu)"





"What? Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" ya fada cikin tashin hankali, ganin wai har yayi shekara daya a wajen nan babu Fadeelah'n sa, mikewa Yayi a zabure duk da uban zafi daya ji amma bai damu ba, burin shi ya bud'e ido ya ganshi a Nigeria, kusa ɗa fadeelahn'sa...



"Wait! Take it easy, where are you rushing to? (Tsaya! Yi a hankali, ina kake saurin zuwa haka)" Kelvin smart ke wanna maganar...


A rikice Fadeel yace "I have to go doctor, my wife is worried, I want to see my fadeelah (zan tafi likita, matata a dame take,

Please Login or Register in order to submit comment