Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

❤️❤️KADDARATA😔✍🏼📚
Story and written by nanah m sha'aban✍🏼❤️
Wannan littafin sadaukarwa ce ga iyayena Muhd lawan sha'aban daCar Aisha Muhd Yusuf
Page 1
Misalin karfe daya da rabi nadare samira ta tashi dawani matsanancin ciwon kai Wanda ya haddasa mata da zazzabi mai zafi juyi kawai take akan makeken gadon da yake manne da bangon dakin ga damuwar gobe zaa daura mata aure d yaya fahid Wanda tasan duk duniya babu wanda ya tsaneta sama dashi tun tana er karamarta yake nuna mata tsantsar kiyayyah wanda tarasa dalilin dayasa yake nuna mata tsanar nan tuno maganganun daya fada mata jiya da daddare tashiga yi daya aiko yusuf dan karamin kaninsu yace yakirata bayan tashiga dakin saukar baki gabanta na faduwa dan idan taga yaya fahid tamkar taga mala'ika sam bata son suhadu dashi tun tana karama har yanxu da takai shekara 19 tun daga ranar kuma da su ummah suka yanke shawarar zasu hadani aure dashi taga wata sabuwar kiyayyah wadda tafi ta da yafara nuna mata bayan na zauna akasa kaina a sunkuye jikina sai bari yake yakalleni cike da kiyayyah fal idanunsa sannan ya zauna a kan kujerun alfarmar dake zagaye a daki yasa kafarsa daya kan daya yace samira kike dasuna ko meye kinje kin kulla munafirci zaa hadani aure dake ko to ki tabbata dacewa karma kitaba sawa a ranki waini fahid zan daukeki a matsayi matata danni kamar baiwata na daukeki ke koh baiwata mah tafiki mahimmanci a gurina wllh na tsaneki na tsaneki sam bana son ganinki jinake kamar nakasheki kuma idan mah kina farin ciki zayi mana aure to kisani gidana yafi makabarta dan zan gana miki a zabar daban taba yimiki bah banza yar kauye kazama kawai mara kamun kai er gidan talakawa wllh da in aureki gwanda na dauri karya kuma koda an kawoki gidana karki sake ki nuna min Wannan mummunar fuskar nan taki dan bana son ganinta ko dan Yana gama fadar haka yasa kafarsa ya hankadata sai da ta fadin har sai d goshinta yafara fitar d jini d gudu ta tashi tafita daga dakin tana kuka tashi tayi zaune jiri na dibarta kuka tashiga yi mai sauti amman babu Wanda yasan mah tanayi dan daga ita sai ubangijin da ya haliccemu ne kadai yasan tanayi dan babu mai jinta dakin ita dakadai ce tunda bikin yazo mommy tasa aka ware mata bangarenta daban dan acewar mommyn a hakane zata samu ayi mata gyaran jiki innalillahi wa inna ilaihi raju'un tashiga maimaitawa ya Allah ina rokanka da kyawawan sunayenka ya Allah kaikace mu rokeka zaka amsa mana ya Allah ina rokanka ka dauki raina tun kafin akaini gidan yaya fahid nasan irin kiyayyar d yayi min ba karama bace yaki min tsanar da tun a rayuwarsa bai taba yiwa wani irinta bahh a kullum maganarsa dayace idan har suna magana wani akan ya rage yimin irin wannan kiyayyar yace ya tsani samira tsanar da ban tawa yiwa wani ko wata bah narasa Menayi masa narasa takarasa maganar cikin kuka a kana jin kasan na tsantsar bakin ciki d kuma Dana sanin sanin yaya fahid a rayuwarta tayi kukanta mai isarta sannan ta tashi cikin jin jiri tashiga toilet alwala tayi sannan tadawo ta shimfida dadduma duk d tanajin bazata iya yin sallar a tsaye bah amman a haka ta tada sallah sai d tayi raka'a 2 sannan tashiga yin addu'ar Allah yakawo mata sauki d zaa raba wannan auran kafin gobe
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m sha'aban❤️✍🏼
Page 2-3
Bayan ta idar d sallah tashafa addu'a akan daddumar ta kwanta cike d damuwa ahankali hankalinta yafara kwanciya tafara jin dan sanyi a zuciyarta sam ko kadan bataji zata iya komawa bacci tana nan kwance aka fara kiraye kirayen sallar asuba cike d rashin kuzari ta tashi tayi sallar asubah kan gadon nata takoma zauna tazabga tagumi hawaye fal idanuwanta ita tasan haka kaddararta take bazata taba yin farin ciki a rayuwarta ta duniya bahh tun batasan kanta bah tafara fuskantar matsalolin rayuwa kaddarori suna zuwan mata ko wacce d irin tata tashin hankalin Kifa kanta tayi akan gadon duk addu'ar dataxo bakinta yinta take a haka bacci barawo yayi azan gaba d ita
Waye fahid??
Fahid babban danne ga ministan kudi na jihar Abuja Alhaji Ibrahim bukar sai kuma kannansa umar shine mai binsa sai Ibrahim mai sunan mahaifinnasu Wanda suke kiranshi da daddy sai kuma dan karamin kaninsu yusuf mahifiyarsu hajiya rahma 'yace ga sarkin garin bauchi wanda su biyu allah yabasa amatsayin 'ya'yansa hajiya sadia itace babba sai hajiya rahma, rahama macece mai son mutane ko kadan bata d wulakanci kyakkyawace sosai dan idan kaganta zakayi zatan balarabiya ceh mahaifinnasu mai martaba Abdullahi Yana son rahma saboda kyawawan dabi'unnata kwata kwata batayi halin yar uwarta sadiya bah dan sadiya macece mai kyamatan mutane kuma t tsani talakawa mahaifin fahid Alhaji Ibrahim yaga hajiya rahma a gidan er uwarta sadiya dake garin Abuja dayake mijin aunty sadian abokinsa neh dan haka baiyi kasa a gwiwa bah gurin fada mata Yana sonta bah itama ta amince cikin kannanin lokaci akayi biki aka gama ya gina mata tafkeken gida a cikin garin abujan tsayawa kwatanta irin yadda gidan ya tsaru bah mah bata bakine dan bazai taba kwatantuwa bah haka aka zuba mata bayi a gidan kai kace gidan wani sarkinne Fahid kyakkyawane na akin karshe dan kamar mahaifiyarsa kadebo gaba daya yayi karatunsa akasar newyork tun daga sec har zuwa university duk a can yayi yatasone cikin gata dan kakanninsa har iyayensa duk suna ji dashi fahid yarone miskili dan sam yammata basa gabansa duk da irin yadda yammatan suke kokarin suga sun mallakesa a matsayin miji saudat er aunty sadia wacce itace erta tafarko itace take son fahid din kamar hauka dan har samunsa tayi tafada tada mata shi kuma yamuna mata bai shirya fara soyayyah yanxu bah kuma baya ra'ayinta a matsayin matarsa gwanda tun dare bayi mata bah tasamu wanda yake sonta ya aureta amman duk da haka ita ko kadan baza iya cire soyayyarsa bah a zuciyarta saboda tana ganin su din Yan uwane indai iyayensu sukaji zasu goyi bayanta kodan zumincinsu yayi karfi sosai
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by nanah m sha'aban❤️✍🏼
Page 4-5
Wacece samirah
Samira yar asalin wani kauyece mai suna fayauna mahaifinta bukar isah d mahifiyarta Aminatou haifaffun kauyenne mokobtane dan ga gida ga gida suke bai wani sha wahalar neman aurenta bah tunda daman suna son junansu mahaifin bukar ya mutu tun baa haifeshi bah su tarane a gurin mahaifiyarsu maza hudu mata biyar haladu shine babbansu sai mai bi masa Ayuba, zubairu, sai kuma bukar matan kuma lantana, zilai, abu, talatuwa sai kuma autarsu falmata koda bukar yaxo yafadawa mahaifiyarsa yana so ya auri Aminatou tayi farin ciki kuma yabasa goyan bayanta dan tasan yarinyar akwai hankali d nutsuwa yan uwansa mah sun nuna farin cikinsu haladune kadai ya nuna kin amincewarsa amman yasan ko ya nuna kin amincewarsa bazasu taba goyon bayansa bah dan haka yabar abin acikin ransa bangaren iyayen Aminatou mah sunyi matukar amincewa d aurenta d bukar din dan kowa a kauyen yana shedar bukar mutumin kirkine kasancewar ita kadai Allah yabasu suna d rufin asiri baa wani bata lokaci bah akayi aurensu suka tare a gidan d bukar din ya gina dayake yana d zuciyar yi madaidaicin gidane ciki d falone sai bandaki d gurin wani dan karamin waje d yaware dan dafa abinci watansu hudu d aure mahaifiyarsu bukar tarasu mutuwar data girgiza kowa a dangin musamman mah bukar dan yana sonta sosai aka share zaman makoki kowa yakoma gidansu sai laulayi yasa Aminatou agaba dan ko abinci taci sai ta amayoshi ga wani zazzabi mai zafi d ciwon kai datake fama dashi hankalin mijinta bukar yatashi dan kowajen aiki baya xuwa wannan ashe wata matsalar d sabuwar kiyayyah yakara shiga tsakanin bukar d Aminatou har yatara yan uwansa yana fada musu cewar Aminatou ta asirce dan uwansu gashi ko wajen aikinsa mah yadena zuwa ita kuwa Aminatou da mijinta bukar basu san maike faruwa bah haka haladu yatara yan uwansa suka nufi gidan bukar suna shiga suka Tatar d bukar yanawa Aminatou wanki ita kuma tana kwance a tabarma nan kuwa suka sa salati kuma suka tabbatar d cewar yayannasu ba karya yake musu bah Aminatou ta asirce dan uwansu bukar shi kuwa bukar tashi yayi fuskarsa dauke d murmushi yanawa yan uwannasa sannu da xuwa
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m sha'aban❤️✍
Page 6-7
Aminatou ta tashi cike d fara'a tana musu sannu d zuwa cikin tsawa haladu ya dakatar d ita da cewa ke dallah malama rufe mana baki Ayuba cike d bakin ciki yashiga sauke mata kwandon masifa abinda bai taba yi mata bah tunda yake sai dai gaisuwar mutunci yasukeyi Aminatou ashe daman haka kike kin asirice mana dan uwa sai yadda kikayi dashi kin hana shi yaje aikinsa yanxu kuma kin kwanta yana miki wanki da uban wanke wanke wanda kike nifin idan yaga miki wanki yayi miki toh kisa ni wllh baki isa bah kinyi karya asirin da kikayi masa dole sai kinje kin toneshi zubairune dashima yaga fusata wai yau dan uwansu ne mace tasa shi yayi mata wanki tabbas shima ya yarda asiri tayi masa dan ba yadda za'ay ace yaxauna agida yaki xuwa aiki kuma yaxo yana mata bauta kaga yaya Ayuba ay bazance sai ta karya asirin kawai ya saketa yanxunnan batare d bata lokaci bah haladu dayaga sharrin da yayiwa Aminatou duk yan uwannasa sun yarda dacewa asiri tayi masa sai yaji dadi bukar da yashiga mamakin mai yasa yan uwannasa sukewa matartasa haka ya juya yakalli Aminatou wacce ta durkusa kasa tafara wani matsanancin kuka tana sonyin magana amman takasa zuciyarsa takarye cikin raunananniyar murya yafara magana yaya haladu wai me kuke fada ne akan Aminatou kuna tunanin tayi min asirine shine naki zuwa aiki kuma nake mata wanki haba yaya Ayuba ko kun manta halin Aminatou a tunanina idan kukaji wani yana fadar maganganu irin haka akan Aminatou sai inda karfinku yakare kuma da kuka ga ina yi mata aiki bata d lpy kuma tare mukeyi d ita ni nace taje taxauna ta huta kunga abinda nake ce muku ko ai tariga ta asirceshi yanxu wai har ni bukar zaka dubi tsabar idona kace wai bata d lpy amman tana d lpyr kwanciya ko haladu yafada cikin daga murya yaya haladu indai kunxo kutadar min d tashin hankaline a gida dan Allah kutafi lantana dake gefen yaya haladu da ita d talatuwa suka fashe d kuka yanxu yaya bukar kai d kanka kake korarmu daga gidannan wanda d baka d buri irin kaga munxo gidanka cewar lantana haladu yakatseta d cewar haba lantana karki damu asirine kuma mu baxamu taba yarda bah sai takarya shi kuxo mutafi haka suka tafi cike d jin haushin Aminatou shi kuma haladu yana jin dadi yanxu yasan dole sai sun tilas ta bukar yasaki aminatou domin ya cinma burinsa akanta abangaren bukar kuwa karasawa yayi Aminatou ya shiga rarrashinta d bata hakuri ta dago tana kallonsa daman sai danace maka ka dinga tafiya aikinka karka damu dani tafada tana kara fashewa dasabon kuka amina kinfi min komai mahimmanci banxan bata barin a irin wannan halin bah ina sonki ina sonki yafada yana goge mata hawaye murmushin jin dadi tayi duk da irin yadda takeji zuciyarta na tarasa yanxu dai ki tashi ki shiga daki in karasa wankinnan shuru tayi dan so take tace masa kawai yabar wanki zata karasa amman kuma tasan halinsa bazai yarda bah kamar yasan me take tunani yace ko dai bazaki iya tashi bah na daukeki dasauri tatashi tashiga dakin cike d jin kunya haka yatashi yakarasa wanki yayi wanke wanke dai dai lokacin d yagama yaji anfada kiran sallar magribah alwala yayi ya leka dakin sallah yatarar d ita tanayi yace mata matata mai jin kunyar mijinta zan tafi masallaci sai na dawo takusan yin dariya amman tahadiyeta shi kuma yafita xuwa masallaci
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m sha'aban
Page 8-9
Washe gari bukar yana zaune yana taya Aminatou ninke kayan da suka wanke jiya tadan kalleshi tayi murmushi dan a duk lokacin d suke tare dashi takan ji wani matsanancin farin ciki ko da kuwa ace tana cikin damuwa yau bazakaje gona bah ta tambayeshi kanta a sunkuye yadan dago yakalleta inda sabo yajiga d yasaba Aminatou tunda sukayi aure bata taba kiran sunansa bah ko kuma tace mai gida kamar yadda suke cewa matan garin sai dai tayi masa magana kai tsaye eh bazanje bah yabata amsa yana ninke doguwar rigar d tarage baa ninke bah ta dago takara dubansa akaro na biyu haba meyasa naji sauki pha dan allah kaje kaga yanxu su yaya haladu zafina sukeji suna ganin kamar ni nahana kaje aikin tafada tare d durkusawa a kasa gwiwoyinta na bisa kasa dan tasan idan har bahaka tayi masa bah bazai yarda yaje bah yakalleta sannan ya miki tare d shigewa uwar daki sai d yayi shirin xuwa gonar sannan ya fito a inda yabarta anan yasameta ya girgixa kai sannan yace mata tohm zan tafi gona sai na dawo koh dariyar farin ciki tayi tace nagode sosai sai kadawo Allah ya kiyaye hanya murmushi yayi yace Amin matata yafita achan kuwa wajen gonar haladu, ayuba zubairu duk sun xauna suna jiran suga ko zaixo idan kuwa bai xo bah wllh yau sai yasaki Aminatou ta tafi gidansu tun daga nesa suka hango bukar haladu yace kunga dayake yau taga damar yaxo gashi nan yaxo ay yaya haladu ka kyaleshi wllh mu sai mun karya asirin d tayi masa dan bazamu yarda bah ayuba yafada cikin bacin rai dan yanxu wata sabuwar kiyayyah yakeji a xuciyarsa ta Aminatou tana ratsashi zubairu dan takaici bai iya cewa komai bah bukar kuwa yana xuwa ya tsugunna.har kasa ya gaishesu duk dacewa yana tsananin jin zafin abinda sukaje suka yi musu jiya amman wannan dolene tunda sun girme mishi au ay nadauka da kaxo bazamu samu damar tsugunnawarka bah jiya mah naga korar karen d kaiyi mana saboda wannan tsohuwar najadur matar nan taka inji zubairu kuyi hakuri yaya ayubah ay ba sai kabamu hakuri bah nariga d nasan bah acikin hayyacinka kake bah kutashi muyi abinda yakawo mu haladu yace duk suka tashi suka shiga yin aikin shi kuwa bukar hankalinsa na gurin matarsa yabarta ita kadai gashi bawani samun sauki tayi bah haka yayi aykin a gurguje yayi musu sallama yatafi gida yana shiga gidan d sallama yaganta tana yin shara d sauri yakarasa yana kokarin karbar tsintsiya tace Haba dan allah kabarshi ay nakusa gamawa tafada tana tattare sharar taxuba a cikin bola kamanta yayi suka shiga daki sati biyu d zuwan su haladu gidan bukar suka kirashi yaxo gidan haladune yafara magana bukar tunda wannan abin na Aminatou kara cigaba yake toh yanxunnan basai anjima bah kasaketa wannan umarni nake baka bukar yakalli haladu yace yaya haladu bazan iya sakin Aminatou bah dan baa binda tayi min kuma ina son matata san da ban taba yiwa wata ya mace bah au mu kake fadawa kana son matarka bazaka iya sakin tabah zubairu yafada tare d mikewa ya nufo inda bukar yake gadan gadan ayuba ne yatareshi yana cewa kyaleshi zubairu bah laefinsa bahne asirine ya fada idonsa ya cicciko d kwallah
❤️❤️ KADDARATA😔✍🏽
Story nd written by nanah m sha'aban❤️✍🏽
Cigaban page 8-9
Cikin sauri bukar yatashi yay tafiyarsa gidansa Dan idan ya cigaba d ganin d kuma sauraran abinda suke cewa toh zaa iya batacciyah Kuma baya son hakan yafaru a tsakaninsa shi d Yan uwannasa akwana atashi cikin aminatou ya shiga watan haihuwa koh yau koh gobe farin ciki a gurin bukar baa cewa komai abangaran haladu kuwa bacin rai d takaicin bukar ya ki sakin matarsa aminatou yataru yayi masa yawa gashi tun daga ranar indai ya kira bukar baya xuwa saboda yasan dai akan maganar d baxata taba yiyuwa zaiyi masa bah dan haka ya shiga neman wata hanyar d adole sai bukar yarabu d aminatou ko yana so koba yaso saboda a cewarsa shi yadace ya auri aminatou tun kafin su fara soyayyah d bukar Amman rana tsaka yaje yana fada musu zai aureta wannan shine dalilin da yasa haladu yakeson bukar ya rabu d aminatou shi ya aureta awata ranar lahadi ranar d aminatou bazata taba mantata atarihin rayuwarta bah bashari mai shagon kusa d gidan iyayennata yaxo ya sanar musu d cewa an nemi anni d babbapha anrasa tun ranar jumma'a watau mahaifan aminatou tayi kuka har ta gaji bukar shima yayi kukan ya shiga bata hakuri dayi mata alkawarin zai nemosu duk inda sukaje ta kwantar d hankalinta haka yafita yana nemansu ciki d wajen kauyan amman babu su kuma babu labarinsu haka ya kamo hanya yadawo gida hankalinsa duk atashe yasan irin zafin d aminatou takeji dan shima mah yasan zafin rashin iyaye Amman gwanda shi yasan mutuwa sukayi Amman ita kuwa baa san nata iyayen ko suna raye koh sun mutu bah yana shiga gidan ta tareshi a bakin kofa tana tambayarsa angansu farar fuskarta duk tayi jajahur sabida kuka girgiza mata Kai yayi alamar aa rutsewa tayi d wani kuka koh shi kanshi bukar din kukan yake dan haka yakamata suka shiga daki yana rarrashinta domin a duniya baya son yaga kukan aminatou ko kadan tun ana neman su babbapha d anni har aka dawo aka dena dan har kauyukan dake kusa dasu bukar yaje akace gaskiya babu wasu sababbin fuskoki dasuka shigo Dan haka aminatou tadauki hakan amatsayin kaddararta Kuma tana rokan Allah yasa d rabon zasu gana anan gaba kafin ya dauki ranta a ranar wata alhamis aminatou ta tashi d matsanancin ciwon mara haka bukar ya tashi yaje ya kira innah makobciyarsu dayake suna mutunci d ita sosai tana xuwa tace ay haihuwace tafada masa abubuwan d zaije ya siyo yatafi da tafiyarsa ko minti biyar baiyi bah aminatou ta haifi katuwar yarta mai kama d ubanta sak yayi farin ciki d yadawo ya tare aminatou tahaihuwa innah ta yankewa yarinyar cibiya ta gyarata ta shiryata cikin wasu kayan jarirai d bukar yaje birni takanas ya shiyo su dayawa tamika mishi yar anan take yayi mata huduba yasa mata suna samira dan yana tsananin son sunan basuna kowa bane a danginsa haka mah dangin aminatou
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by nanah m sha'aban❤️✍🏼
Page 10-11
Sai kuma taje ta gyara Aminatou sannan tafito zata tafi bukar yana ganin innah ya taso daga kan bancin da yake yana dauke da samira a hannunsa godiya ya shiga yi mata har sai d ta dakatar dashi haba bukar ay Aminatou tamkar diyata na dauketa dan haka karka karayi min godiya dan babu godiya a tsakaninmu yace toh inna hakane daga nan sukayi sallama d ita ta tafi gida a xuwan d yammah zata kuma dawowa dakin ya shiga ya zauna kusa d ita hannuwanta ya rike yana cewa aminata kinyi min abinda bazan taba mantawa bah nagode nagode sosai kadena min godiya kagodewa allah da yabamu ikon kasancewa d juna har muka kawo wannan lokacin d muka fara ganin 'ya'yanmu tafada tana yi masa murmushi ido yakafeta dashi d taga kallon yayi yawa ta katseshi d cewa kaje kagayawa su yaya haladu kar suji awani gurin mukara yin laifi jaririyar ya mika mata yana cewa ay basu damu dani bah babu bukatar kuma na dinga shishshge musu haba hakan bai kamata bah kasan dai cewa su din yan uwanka neh hmm to zanje in fada musu koh d yaje yafada musu babu wanda yace masa barka bare Allah yaraya haka yataso yataho cike d bakin cikin abinda su yaya haladun sukayi masa amman yayi alkawarin bazai kara takawa yaje gurinsu bah haka itama Aminatou zai hanata zuwa toh anyi suna wanda duk yawan cin makobtan su neh sukaxo sunan matan su yaya haladu babu wanda yaxo a cikinsu hakamah su talatuwa watan samira biyu mahaifinta bukar yashiga fama d matsanancin ciwon ciki nan d baya fita aminatou ta rude matuka d ganin irin yanayin d mijinnata yake a kullum maganarsa itace ta kula d samira tasata amakaranta kuma koda ya mutu karda tabari yarsa tayi kukan maraici a duk lokacin d yake fadar haka Aminatou takan fashewa d kuka yanxu idan bukar ya mutu ya zatayi d rayuwarta shi kadai yarage mata a duniya ga iyayanta bata san inda suke bah kwanan bukar goma yana cikin wannan rashin lapiyar allah yayi masa rasuwa awata ranar litinin da safe aminatou tayi kuka har tagaji lokacin d labarin mutuwar bukar ta isa ga yan uwansa sun rude hatta haladu mah kuka yake sosai duk d cewar a yanxu xai sami damar cika muradinta na auran aminatou bayan sadakar bakwai aminatou tana rike d samira saboda kuka tasaka domin sai a yaune mutuwar ta dawo mata sabuwa wani yarone ya shigo tare d yin sallama kallo yaron tayi batare d ta amsa masa bah wai haladune yace a sanar dake zai shigo cike da mamaki ta dago yaya haladu kuma tafada cike d mamaki sannan tamayarda dubanta ga yaron tace kace ya shigo yaron ya amsa d cewa toh yafita tashi tayi tasa hijab tafita xuwa tsakar gida dan taji dame yaxo a bangaren haladu tunda yaro yaxo yafada masa abinda aminatou tace ya shiga gyara malum malum dinsa wacce tasha guga yana shiga yatarar d ita a tsaye bayan sun gaisa bai boye mata bah yasanar d ita abinda ke tafe dashi wani malalacin kallo

Please Login or Register in order to submit comment