Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi masa sannan tace yaya haladu wa kakeso ka aura murmushi yayi yace kemana Kinga ana arba'in sai a daura mana daure saboda bana son ko...... cikin masifa ta dakatar dashi kadauka bani d hankali bani d tunani bansan me nakeyi bah toh karka manta d aminatou kake magana wacce a kullum baka d buri kai d yan uwanka irin kuga kun rabani d bukar toh yanxu ya mutu shine zaka kwaso min wasu gajiyayyun kafafuwanka kace min zaka aureni tohm bazan aureka bah kai ko mafarki nayi na aureka wlh wlh sai nayi tir d allah wadanshi kafice min a gidan tun kafin natara maka mutane
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban❤️✍🏼
Page 12-13
Duk dacewa haladu yaji zafin maganar d aminatou tafada masa baisa ya yaga bakinta bah shi abinda yasa yake nunawa yan uwansa su tsaneta shine yasami damar auranta da bukar yasaketa idan suka tilasta masa haka yaja jiki yatafi duk jikinsa babu laka ita kuma takoma dakinta ta dauki samira dake shan baccinta ta dorata akan cinyarta bayan ta zauna akan gadon tunanin mijinta bukar tashiga yi tana kuka tamkar ranta zai fita awani bangaren kuma tana ta kokarin ta kuntatawa haladu ada ta yadda sunyi mata wulakanci amman yanxu bazata yadda bah a kwana atashi yanxu shekarar samira biyar ta girma sosai ta debo kamannin babanta bukar sak amman farin aminatou tayi yarinyar kyakkyawace gata d hakuri duk yara d manyan yan kauyen suna sonta sosai har gida suke zuwa su dauketa dayake kullum yarinyar tsaftsaf zaka ganta abangaren haladu kuwa kullum sai yaxo gurin aminatou amman bata fita wani lokacin idan ya aiko yaro ya kirawota haka zata kora yaron sai dai yaga yaro ya fito da gudu yahuce shi ranan nan daya gaji sai ganinsa tayi a tsakar gidan tana yiwa samira wanki tana sanye d hijabi dayake bata rabo da hijabi dan wani lokacin harda shi take kwana ita kadai ce dan ma'u yar gidan innah taxo ta dauki samira tun daxu dasauri ta mike tana kallonsa ranta abace watau abin haladun yakai har ya shigo mata cikin gida batare d ixini bah yanxu d awani yanayi yaganta pha kiyi hakuri na....... Cikin masifa tace kaga dakata yaya haladu kai baza'ace yayan bah haladu karka kara cewa komai kawai fitar min a gida ni bansan kai wane irin maye bane na rabu dani bazan iya aurenka bah fita ko nayi maka ihun kwarto ta bude baki zatayi ihu yace kinga yi hakuri karki yi ihu zan fita haka ya fita xuciyarsa cike da son aminatou wani uban ashar ladidi matar haladu tayi dan safara kanwarta takawo mata gulmar taji ana kuskus din cewa haladu yana son aminatou ay wlh aminatu bata isa bah ni danake d boka dukusau ay yau dinnan Aminatou bazata kwana araye bah nan safara tasaka shewa yawwah aunty shiyasa nake sonki kwai ki kawar da shegiya ki nuna mata ke ba sa'arta bace murmushi tayi wanda kana ganinsa kasan na mugunta ne ko da taje gurin bokan yabata kullin magani yace daya tayi wanka dashi daya kuma ta tabbatar d cewa aminatou bata sallah sai ta xuba mata a abincinta daya kuma a ruwan da zata sha haka ta dawo gida tana tunanin toh taya zaay tasan aminatu bata sallah bayan ita da ba xuwa gidanta take bah sai kuma tayi murmushi d ta tuna kanwarta safara dan tasan ita kadai ceh zata iya yi mata haka akwai ta d makirci da kuma iya tuggu

❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by nanah m sha'aban❤️✍🏼
Page 14-15
Anan take tasa danta lawalli yakirawo mata kanwartata tana xuwa tafada mata abinda boka yace mata tadora dacewa nasan ke kadai zaki iya yimin wannan abin dariyar mugunta safara tayi tace haba aunty ay ki kaddara dacewa wannan yar iskar aminatou ta mutu kawai ki bani kullin magungunan zanje na dinga shishshige mata har sai na tabbatar da cewa bata yin sallah zan zuba mata a abinci kuma na samata a ruwan wanka ahaka sukayi sallama tun daga ranar safara take xuwa gidan aminatou sai yamma wani xubin dare take tafiya aminatou duk da cewa bata yarda d safara bah amman haka ta batarta akwai ranar d su ayuba sukaxo sukayiwa aminatou rashin mutunci safara tana nan wai acewarsu tayiwa dan uwansu bukar asiri yanxu kuma ya mutu shine tadawo kan babban yayarsu haladu ita kuwa aminatou bata iya cewa komai bah har suka tafi dan inda sabo yariga da ace tasaba d halin su yaya ayuba ita kuwa safara suna tafiya ta fashe d kukan munafirci tana cewa yanxu aunty aminatou ahaka kike zaune agidannan kullum sai su yaya ayuba sunxo suyi miki rashin mutunci gsky bazan iya tsayawa ina ganin ana wulakanta mace mai sanin darajar mutane mace mai hankali da nutsuwa kowa a kauyannan yana shedarki ni nasan baxaki iya yiwa kowa asiri bah yakamata suma su san haka matsowa aminatou tayi kusa d safara tana taba hakuri samira dake hannun safara tafara kuka aminatou ta dauketa ta zaunar d ita tadauko mata abincinta tasa mata agabanta wani irin kallo safara tayi mata azuciyarta tana fadar lokacin mutuwarki yakusa kin isa ki auri mijin yayata ay kinyi kadan ita kuwa aminatou tun daga ranar tacire duk wani shakku d take akan safara Allah sarki baiwar Allah toh su safara basu samu sunyi galaba akan aminatou bah har sai d samira takai shekara 7 aranar jumma'a safara taxo gidan tasamu aminatou kwance take tambayarta lpy kuwa tace ciwon mara take Alhamdulillah yau burin aunty zai cika tafada acikin zuciyarta amman dan ta tabbatar tace ayyah ay inajin bakonki na wata ne zaixo eh wllh aminatou tafada samira dake gefen aminatou tace sannu innah to samira allah yayi miki albarka bari inxo inkawo miki abinci koh inyaso sai inje insiyo miki magani to nagode safara tana fita taxubo mata abinci ta kunce zaninta data kulla maganin d boka yabasu dayake kullum dashi take xuwa gidan ta sa maganin sannan takaiwa aminatou sai d tabbatar tafara ci sannan tafita acewarta ta siyo mata magani amman tana fita gidan auntynta taje take sanar mata yaufa aminatou zata sheka duniya tadora d cewa wai nan acewarta magani zan siyo mata dariyar mugunta matar haladun tayi tace ay bata d wani magani dan daga yau bazata kara kwana a duniyar bah abangaren aminatou kuwa safara tana fita tafara wani aman jini duk samira ta rude dan haka tafita d gudu tashiga gidan inna tana fada mata innarta tana aman jini kafin su shiga gidan har aminatou ta mutu Allah sarki rayuwa kenan babu wanda bai ji mutuwarta bah haladu kuwa lokacin d yaji mutuwarta faduwa yayi ya suma sai d aka yayyafa masa ruwa sannan yafarfado haka aka shafe zaman makoki aka gama haladu yace zai dauki samira haka aka tattara kayan samira ita kuwa matar haladu tayi alkawarin ganawa samira a zaba tunda taje gidan wanke wanke shara har wanki tana yi abinda innarta bata taba sata bah ga kuma tallah safe d rana duk yayanta takoya musu musgunawa samira bata bata abinci sai dai ragowa awani xubin kuma haka zata fita waje idan makobta sun xubar d abinci xata diba taci duk abinda ake labari yana xuwarwa inna amman bata d halin taimakawa samira dan akwai ranar d taje takai mata abinci haladu yana xuwa matarsa tace ay tana xuwa tana xiga samira tayi mata rashin kunya har gida yaje yayiwa inna rashin mutunci d gargadin ko ahanya taga samira karta kara nunawa tasanta duk irin wahalar d matarsa takewa samira shi bai sani bah akwai ranar d tadora mata talla d safe haka ta fita tana tafe tana kuka dan yunwa takeji wajen kauyansu ta nufa inda zai sadata d bakin titi umar ne kannin fahid yake tuki cikin nutsuwa dayake yaxo duba mahaifiyar abokinsa bata d lpy dasuke service tare dashi dan yau suka gama yau kuma yake sa ran tafiya abuja kiransa akayi awaya wanda yayi dai dai d xuwan samira wajen mortar shi kuma yana tayi mata hon duk tabi tarude tarasa yazatai ta kaucewa matar garin yakauce mata ai kuwa tabigeta haka ta fadi sumammiya dasauri ya ajiye wayar d take ta ruri yafita yadauki samira sai asibin dake wajen kauyen wanda akauyan indai aka kaika wannan asibitin toh ansan babanka mai kudine sosai

❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban❤️✍🏼
Page 16-17
Kwanan samira biyu bata san wanda yake kanta bah shi kuwa umar tunda yakawota basamu yaje ya dubo mahaifiyar abokinnasa bah sai kiransa yayi yafada masa abinda yafaru yace bakomai kuma zaixo asibitin insha Allah kira mommynsa yayi itama yafada mata abinda yafaru yace harsai ta farfado yamaida ta gidansu sannan zai dawo gida mommy tace bakomai dan allah idan ta tashi kayi mata sannu kaji kuma ka kula d ita sosai yace toh mommy a kwana na uku ne samira tafarfado lokacin abokin umar, usman yaxo nan dukkansu sukayi hamdala umar ya matso yana mata sannu kuma yana tambayarta koh akwai inda yake mata ciwo ta girgixa kai alamar Aa tohm ina ne gidanku dan naje nasanar d iyayanki abinda ya faru nasan yanxu hankalinsu atashe yake Dan Allah karka mayardani tafada tare da fashewa d kuka umar yakalli abokinsa usman cike d mamaki shima usman din matsowa yayi dan shi baa kauyansu samira yake bah yana kauyan kusa dashi sune shiyasa bai santa bah haba kanwata meyasa kike kuka ko bakya so kikoma gida dasauri tace eh bana so fada tana kallo usman wanda shi yayi mata tambayar sannan takomar d dubanta kan umar ta saka gwiwoyinta akan godon asibitin tarike hannuwansa dan allah kawu katafi dani gidanka allah ko menene zan maka na iya wanki kuma harda shara mah duk zanyi maka karka komar dani gurin baba allah kasheni zatayi karki damu kinji kidaina kukan haka ina mahaifiyarki take cikin sauri tace innata ta mutu babbana mah ya mutu a gurin baba haladu nake anan tabasa labarin irin wahalar d baba take bata kuma ta dora da cewa yanxu idan nakoma kasheni zatayi zata yankani umar mutum ne mai tsananin tausayi kuma ya tsani yaga ana wulakanta yara kanana dan haka tuni yafara xubar d hawaye kuma yayi alkawarin bazai taba mayar d samira bah zatafi da ita dan yasan mommynsu zata karbeta hannu bibbiyu shima kansa usman numfasawa yayi tare d dafa kafar umar yace dan allah abokina idan d hali katafi d yarinyar nan gidanku karka ce zaka mayar d ita ay usman ko baka rokeni bah wallahi bazan taba narinta anan garin bah zan tafi d ita dasauri samira tace nagode kawu Allah yasaka a aljannatul firdausi rugumeta yayi tare d cewa amin a ranar aka basu sallama suka dauki hangar abuja bayan sunyi sallama d usman tun a asibitin yakirawo mommy yace zasu taho d yarinyar d yakade yabata labarin d samirar tabashi kan irin wahalar d take sha a hannun facalar babarta ko da suka isa abuja hajiya rahma ta nuna farin cikinta dan bata d yarinyah mace kuma tana tsananin son yara mata ta dauki samira tamkar yarta ta tambayeta yasunanta tace sunana samira bukar tohm daga yau ki daukeni tamkar innarki kinji tace toh tasata a makaranta kudi dake jihar abuja fahid kuwa tun daga ranar dayayi ido biyu d samira yaji ya tsaneta daki guda aka warewa samira sai d bikin ta yaxo mommy taware bangare guda tace na samirane dan taji dedi shiryawa biki mommy tasan irin tsantsar tsanar d fahid yakewa samira amman ita a tunaninta da zarar ya aureta zai ajiye kiyayyar d yake mata a gefe
Wannan shine asalin fahid da samira
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by nanah m sha'aban❤️✍
Page 18-19
Kamar an tsikareta ta tashi dasauri kyawawan idanuwanta ne suka sauka akan agogon dake jikin bangon karfe 7:00 dai dai na safe adai dai lokacin kuma bugun zuciyarta ya tsananta bugu tasan rayuwar aure d yaya fahid tamkar rayuwar cikin kabari ce kai rayuwar kabari mah tafita dadi dan acikin kabari babu me takura maka sai dai idan kayi abinda bai dace bah Allah ya kiyayemu da sharrin duhun kabari Amin jitayi ana knocking din dakin dasauri tagoge hawayen idanuwanta tare d bada izinin shigowa aunty binta ceh tayi sallama ta shigo zaunawa tayi kusa da ita tana kallonta cike d tausayawa tace samira nasan irin damuwar dakike ciki amman kiyi hakuri insha Allahu wata rana sai labari fahid nasan yayi matukar tsanarki tsanar d bai taba yiwa wani mutum bah amman ina da tabbacin cewa wallahi zakice nafada miki fahid zai soki son da bai taba yiwa wata 'ya mace bah zaiyi miki son da bayan aunty rahma d yaya wallahi kece ta uku da zai so acikin rayuwarsa kisani cewa idan kiyayyah tayi tsanani toh tana rikidewa tazama soyayyah matsanani kidaina kuka kinji ita dai samira kawai jin aunty binta take taya zaay acewa yaya fahid din daya tsaneta ace shine wai wata rana zai so ta bata tunanin wannan ranar zataxo aunty binta kanwar Abba ce uwarsu daya ubansu daya macece mai faran faran da mutane jininsu yaxo daya d samira aunty binta bata bar gurin samira bah har sai d ta tabbatar ta tayi wanka taxo ta shiyata acikin las pink colour tayi mata kwalliya tayi kyau sosai sannan tafita tabarta zaunawa samira tayi akan kujerar dressing mirror tana kallon kanta a madubi zuciyarta fal da tunanin makomar rayuwarta yanxu dai ya tabbata babu makawa sai anyi aurenta d yaya fahid ko minti biyar aunty binta batayi bah yusuf ya shigo dakin da sallama ya gaisheta ta amsa cikin sakin fuska yusuf yarone kwata kwata shekararsa goma amman yana da tsananin hankali d nutsuwa gashi d girmama nagaba dashi aunty samira wai fauziyyah abdulaziz yar makarantarku taxo inji mommy cikin fara'a tace tohm yaron kirki kace ina xuwa yafita yana murmushi fauziyyah kawar samira ceh sunyi makaranta daya inda sukayi karatunsu akan orthopedic fita tayi cikin sauri tana ganin fauziyyah suka rungume juna dakinta suka shiga itama lallashinta tashiga yin d kwantar mata d hankali tohm shikenan fauziyyah nagode karfe 11 dai dai aka daura auran samira bukar dakuma fahid ibrahim bukar akan sadaki 200k nan pha kukan samira yadawo sabo dataji an daura aureta d yaya fahid shikuwa yaya umar tausayin samira yahana shi sakewa da mutane duk dacewa ga yan uwansu na kusa dana nesa duk sunxo fitowa yayi daga cikin dakin bakin dasuke ciki yana neman wanda zai kirawo masa samira kausar yar gidan aunty binta yagani yace taje takirawo mata samira a babban falo yazauna inda yake kusa d bangaren samira tana fitowa ta ganshi akasa tanemi guri ta xauna yace aa ta tashi taxauna akan kujera zaunawa tayi ya kalleta yaga duk idanuwanta sun kumbura nan yashiga yimata nasiha dakuma rokonta da tayi hakuri da tayi hakuri d dukkan abinda yaya fahid din zaiyi mata yadora dacewa nasanki da hakuri tohm kikara akan wanda nasanki dashi kinji kanwata tohm kawu nagode haka ta tashi takoma bangarennata Babban falone wanda aka wadatashi da kayan more rayuwa zaune yake akan tafka tafkan kujerun dake zagaye da falon ransa duk abace yake tunda yaje yadawo daga daurin auren d abbane yasa shi dole sai dayaje kafafuwansa yadora akan center table yana kadasu ahankali fahid neh wanda ya tsunduma d tunanin irin wahalar da zai bawa samira lokaci daya kuma yatashi sai d yacire malum malum din daurin auren sannan yatashi yafita daga cikin gidan gaba daya anyi biki anci ansha samira tasaka suturu masu tsada duk acikin gidan akayi bikin wajen karfe 7:00 nadare motocin daukar Amarya sukayi fakin acikin aharabar gidan haka aka saka samira mommy na kuka itama samirar kukan take tana kankame d mommy dakyar aka iya banbareta daga jikin mommy suka jo motocin suka nufi gidan Amarya samira
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by nanah m sha'aban❤️✍🏼
Page 20-21
Bayan ankaita gidanta dake nan abuja suna da dan nisa da gidan mommy shima katafaran gidane sosai falo biyu neh sai kuma bedroom shima biyu sai kitchen sai toilet din baki dan akowa wane bedroom akwai toilet acikinsa sai kuma wani daki daban wanda yake dauke da katon freezer an zuba kayan ciye ciye acikinsa a daya daga cikin bedroom din suka sakata bayan aunty binta takara yimata nasiha sannan aka watse aka barta ita kadai zuciyarta cike da fargaba yau gata ga yaya fahid daman agaban su mommy yana ci mata mutunci yana wulakantata dan mah mommy idan yafara tana dakatar dashi cikin fushi tohm yanxu babu mai dakatar dashi duk abinda zai mata babu wanda zai ceceta sai ubangijinmu Allah zuciyarta tafara raya mata data kulle dakin da makulli dasauri ta tashi tasakawa dakin key........... Tunda yafito daga cikin gidan yahau kan titi yafara wani mahaukacin tuki, tuki yake xuciyarsa kamar tafaso kirjinsa tafito saboda bakin ciki a wani gurin sayar da wuka yayi packing yafito wata sharbebiyar wuka yadauka gayawa jini nahuce sannan ya fiddo kudin dabesan nawa baneh ya dankawa mai sayar da wukar yafada cikin mota yafara tuki ahankali maganar mommy tafara yimasa yawo akunne Wallahi fahid idan kasake kasaki samira zaka gamu da fushina zan cireka daga cikin 'ya'yana inda Abba dake gefeta yadaura da cewa samira tamkar 'yarmu take ina maka da nasiha da karka cutar da ita kasani idan har ka cutar da ita kana ganin bama nan toh kasani cewa Allah yana ganinka kuma bazai taba barinka bah Allah yabaku zaman lpy wani tsaki yasaki xuciyarsa natun xirashi dayaje ya kashe samira kawai kowa yahuta yana isa gidan kai tsaye ya nufi hanyar dayake tunanin anan aka saka samira hannunsa dauke d wukar ya tura kofar dakarfi amman yajita a rufe watau kulle dakin tayi yafada a xuciyarsa nan pha yashiga bugun kofar yana fadin tabude dakin dayaga taki ya nufi hanyar bedroom dinsa samira kuwa dataji alamar takun tafiyarsa taleka ta window ganin sharbebiyar wukar dake hannunsa yasa tayi saurin jaaa dabaya innalillahi wa inna ilaihi raju'un yaya fahid kasheni zakayi Ashe kiyayyar dakake min takai ga har zaka iya kasheni tabbas dolene nasan inda dare yayi min kwance take akan mommynta tana kuka kamar ranta zai fita saudat ceh takalli mahaifiyarta tace mommy yanxu shikenan yaya fahid bazai taba zama mallakina bahh haba daughter karkice haka kinji dolene rahma tayarda da aurenki da fahid kotana so kobata so nayi miki alkawari kekadai ceh zaki zama matar fahid kinsan dai irin kiyayyar d fahid yayiwa wannan shashashar yarinyar nan mommy taya kike ganin mommyn yaya fahid zata yarda da aurena da fahid kinaji dai abinda tace mana dakikaje kika fada mata kina son a hada aurena da yaya fahid tanuna cewar tafison wannan tsintacciyar magen ta aureshi tace sai dai yaya umar ya aureni shima Abba d kikaje ya fada miki abinda mommy tafada miki mommy cike d bacin rai tace daughter wallahi koh tahalin yayane sai ya aureki sai nayi abinda fahid zai saki samira kuma dole rahma ta tako da kafafuwanta taxo neman aureki kuma tabani hakuri haka saudat tashiga yin dariya dan tasan halin mommynta sai tayi yanda tayi ta auri fahid dan haka tafara daukan kanta tamkar matar fahid
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban❤️✍🏼
Page 22-23
Abangare samira tun ranar da taga yaya fahid da wuka bata yarda tafito bah ko window bata lekawa kwana uku kenan Dan madaidaicin frigde din dake dakin Ana take samu tasaka Abu acikinta dayake mommy tasa ansa mata frigde a dakin ko idan da daddare tana son Abu basai tafito falo bah drink da cake sune abin cinta shikuwa fahid tun ranar dayaje yabugawa samira daki taki budewa nan pha yaji wata sabuwar tsanarta kuma ya kudurce acikin xuciyarsa indai samira tabari suka hadu ba abinda zai hanashi bai kasheta bah yanxu mah shine acikin dakin yana shirin xuwa office babban likitane wanda agarin suke matukar ji dashi dan yakware a aikinsa sosai fitowa yayi rataye da jakarsa akafadarsa yakalli kofar dakin samira yace hmmm ai baxaki taba dauwama a daki bahh kuma indai kere na yawo zabo nayawo wata rana dole zaa hadu yana gama fadar haka yana tafiyarsa tunanin samira dakuma halin datake yahana shi yin komai yasan yanxu yaya fahid yana chan yana wahalar da ita maganarsu dasukayi da yaya fahid din ce tadawo masa ranar daurin auren da daddare ya shiga dakin yaya fahid din shi kadaine a dakin dan yahana kowa shigowa sallama yayi masa ya amsa masa batare da yasamu ko kallo kirki daga gurin yayannasa bah dan yasa akan wannan yarinyar yaxo yayi masa magana durkusawa yayi akan gwiwarsa yana fadar yaya fahid kadubi girman Allah dakuma son dakake yiwa annabinmu annabi Muhammad s. a. w karka cutar da samira kaga dai nafarko samira maraini yace bata d kowa sai mu wallahi nasan samira zatayi maka biyayyah kaga umar meye nawani durkusa min kaga wannan abin dakake neman a gurina bazai taba yiyuwa bah bana sonta kuma wani dakake cewa marainiya ceh Meya hanata zama gurin dangin ubanta da uwarta kaga umar tun kafin raina yabaci nayi maka abinda bazaka taba mantawa bah katashi kabarmin daki numfasawa umar yayi tare da gyara kwanciyarsa gashi mommy tahana shi zuwa gidan wai yabari bah yanxu bah su samu sudai daita kansu mommy kenan yaya fahid bazai taba yarda su dai daita da samira bahhh yafada cikin raunananniyar muryarsa samira kuwa dataji karar fitar motarsa daga cikin tayi hamdala sannan tafito jakarta tadauka takoma dakinta dasauri takara sawa dakin key wayarta tadauka acikin jakar taga missed din mommy yafi 30 bin kiran tayi bayan sun gaisa take tambayar dafatan dai komai lpy keda yayannaki lpy klau mommy yanxu mah yafita office tohm Masha Allah amman meyasa nake jiranki amman baa dauka mommy nasa wayar acikin jakane kuma na nemi jakar banganta bah sai yanxu ok tohm sannan sukayi sallama bazata iya fadawa mommy abinda kefaruwa bah sabida bata so tayi masa magana kuma abin yayi tsanani tayi alkawari bazata taba yarda tafita daga dakin bah yauma sabida wayarta ne kuma tasan mommy zata kira taji lafiyarta
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by nanah m sha'aban✍🏼❤️
Page 24-25
Mahaifiyar saudat ce zaune akan daya daga cikin maka-makan kujerun dake zagaye afalon nata gefe guda kuma mahaifin saudat dinne sai kuma saudat din itama akan kujerar sanye take cikin wata Riga wacce zaa iya cewa da ita gwara babu sai kuma wando da yayi matukar matseta yadan haura gwiwarta kadan tunda saudat taje kasar waje karatu takoyo komai nasu kuma abangaren iyayennata basu damu da irin shigar datake yi bah ko kuma mu'amalar datakeyi da maza dan har agaban mommynnata idan wani yaxo gidannasu irin wadanda sukayi karatu akasar wajen takan rungumeshi kuma tayi masa kiss💋ita kuwa sai dai tayi murmushi tace irin taku wayewar kenan haka wata ranan idan ta shirya zata fito cikin shigarta dabata dace bah dan wata rana daga ita sai wando da bai kai gwiwarta ba tace mata zataje club sai da tace adawo lpy hk zata kwana achan idan tadawo sai dai tayi mata sannu d xuwa harda tambayarta ya Hanya wadannan sune kadan daga cikin halayyar saudat dakuma mahaifiyarta shikuwa mahaifinta sadiya taga asirceshi sai yanda tayi dashi duk halayyar saudat bawacce hajiya rahma bata sani bah dan idan tayiwa yar uwar tata akan bai kamata taringa barin saudat din tana shiga irin haka kuma tana fita saboda ita macece sai tanuna mata babu ruwanta da ko yatake tafiyar da tarbiyyar yayanta dan hajiya sadia macece da bata son laifin yaranta shiyasa ko da taxo neman a hada aurensu da fahid tanuna rashin amincewarta tace sai dai umar shima umar din kawai tafada ne hajia sadiya yayanta biyar saudat sai kuma ahmad sai ra'isa dake binsa sai ra'is, ra'isa da ra'is yan biyu ne sai kuma yar karamar kanwarsu bahijjah Ahmad kwata kwata bai da hali mara kyau kuma sam baya jin dadin abinda yayarta shi takeso tamayar da rayuwarta abin kyama akan dai maganar auren fahid d saudat din suka tattauna tadora dacewa kuma bance kaje kasami alhaji Ibrahim din dakansu zasu kawo kansu yakamata kafara shiryawa auren 'yarka dan nan ba dadadewa bah zata zama amarya tohm hajia sai da tabashi ixinin tafiya sannan yatashi yatafi hajia sadia tamayar da kallonta kan saudat wacce sai murmushi take tana taunar cingum

Please Login or Register in order to submit comment